WATA SHARI’A CHAPTER 15

WATA SHARI’A






CHAPTER 15




A Katsina kuwa Umar ya gama maganar komai yanzu sunajiran ranar shiga kotu ne kawai, Ummimah yanzu ta dan samu kwanciyar hankali amma ba sosai ba, Saboda gani take yanzu wannan itace damarsu ta karshe idan har basuyi nasarah ba tofa shikenan, Addu’ah ta rika sosai sannan kuma mamanta ma tana tayata.
Ana gobe za’a shiga kotu ne Haydar ya fara zazzabi, Sosai jikinshi yayi zafi sai rawar sanyi yakeyi, Matukar tashin hankali Sultana ta shiga saboda tunda take da Haydar bai taba yin zazzabi mai zafin wannan ba, ya makalewa Safiyya da ita kawai yake yarda, Harta da ita Sultana d’in baya yarda k0 Umar babanshi.
Hakan yasa daren ranar ya nacewa Safiyya yace lallai sai tare da ita zai kwana, Babu yanda Sultana batayi dashi ba akan ya kwana tare da ita amma sam yaki yarda harda su hawaye, Ganin yana neman ya fasa mata kuka yasa ta mikawa Safiya shi tace ya kwanta tare da ita.
Har sun kwanta Sultana taje d’akin Hafsa ta d’auketa saboda bai kamata Hafsa ta kwana ita kadai a daki ba,
Sannan kuma a musulunce ma babu kyau su kwana tare da Hafsa saboda shekarunta sun wuce na ma’aurata su kwana ma da ita, Dakin Safiyya ta kaita ta kwantar,
Ta samu Haydar ya makalkale Safiyya tsam kamar ance za‘a kwace masa ita,
Cike da tausayi ta kwantar da Hafsa daga can gefe sannan ta tofesu da addu’ah ta koma d’akinta,
Haka kawai takejin wani irin yanayi maras dadi,
Kawar da duk wani tunani tayi tare da barin d’akin ta nufi inda Umar yake. Ta sameshi ya tasa takardu gaba yana rubuce rubuce, Cike da soyayya tace ‘Sannu da aiki honey”,
‘Yauwa wifey kema sannu” ya fad’a yana mata murmushi.
“Bakaga yanda Haydar ya mannewa Safiyya ba, kamar wanda akace za’a kwacewa ita, Nikam bansan wace irin soyayya Haydar yakewa Safiyya ba, Bansan ya zayyi idan zatayi aure ba, Saboda dai macece dole wata rana zatayi aure, koni bana mata fatan tayita zama a karkashinmu ba tare da tayi aure ba”, ‘lnsha Allahu kafin tayi aure ma yayi wayo, kinga babu maganar wahalar rabuwarsu kenan” Umaryajefo mata amsa bayan ya rufe takardar da yake rubutu akai din. ‘ ‘Hakane honey, har ka gama aikin ne?“ Ta tambayeshi bayan ta haye bisa gado saboda bacci takeji sosai yau.
‘Ko ban gama ba ai dole in daina in kula da iyalina” ya bata amsa had’e da hayewa gadon shima.
“Nikam dama kaci gaba da aikinka, saboda bacci nakeji sosai yau, harda wani irin ciwon kai nake tsabar baccin dake idona’ ta karisa maganar cikin hammar bacci harda dan guntun hawayen hamma.
“Nima dai baccin nakeji sosai, kiyi baccinki to barin karisa saura kadan sai nima in kwanta, bana son in fita gobe ban gama wannan aikin ba”, ‘Ok good night dear” ta fada bayan taja blanket ta rufa. 3:30am
Wasu mutane uku ne fuskokinsu sanye da mask kwayar idonsu kawai ake iya gani, Hannayensu rike da bindigogi kanana ba masu girma ba, Kayan jikinsu kuwa complete black ne. A hankali hade da sando suke tafiya har suka iso bakin gate, Kasantuwar a rufe yake yasa daya daga cikinsu ya zaro wani karamin abu daga aljihunsa. A daidai inda sakatar take ta ciki ya zira siririn abun babu bata lokaci kuwa kofar ta budu. Shiga ciki sukayi har yanzu sanda sukeyi, Kofar da zata sadasu da cikin gidan ma a rufe take,
Yanda yayima gate haka yayi yanzu ma, Aikuwa suka shige cikin gidan a hankali daya daga cikinsi ya kunna ‘yar fitila maras haske sosai.
Tsaye sukayi cak kasantuwar sun rasa dakin da zasu dosa,
Sundai san an basu tabbacin Sultana akeso su kashe amma kuma ga jerun dakuna nan basu san ta inda zasu nufa ba. ‘ 
Dakin dake fuskantarsu suka taka a hankali suka shiga, Ummimah da Mama ce kwance suna bacci, hakan ya tabbatar masu da babu Sultana a ciki. Fita sukayi daga nan suka doshi dayan dakin, Zarah da Rabiatu ne suma sunata kwasar baccinsu. 
Dan guntun tsaki daya daga cikinsu yayi sannan suka juya suka fita daga dakin. 
Na can nesa da parlor’n suka shiga inda suka samu Safiyya da Haydar kwance, sai Hafsa acan daga gefensu suna bacci, Wannan ya basu tabbacin Sultana ce saboda sukam ba’a lissafa masu da akwai mai rainon yara a gidan ba. 
Murmushi sukamajunansu sannan wani ya nemi inda ake kunna hasken dakin ya kunna. Yana kunnawa kuwa Hafsa tayi saurin tashi zaune saboda ita dama indai akwai haske to ba zata iya yin bacci ba, Zaune ta tashi sai rarraba ido take hankalinta tashe take kallonsu, Ita a zatonta ma ko a dakinta take dan bata san sanda Sultana ta dawo da ita dakin Safiyya ba. 
Matsawa tayi inda Safiyya take ta bubbugata da karfi kuwa ta tashi zaune, Daya daga cikinsu wanda da alamar shine oga ya zare mask dinshi hade da yin wani 
shu’umini murmushi yana kallon Safiyya, “Barr. Sultana ko? Karki damu saboda damuwarki zata iya sakawa kiyi ihu, ihunki kuwa 
zai iya kawo karshen rayuwarki”. 
Cike da tsoro Safiyya ta dade bakinta ta samu kanta da kasa fada musu ba ita bace Sultana ba. 
Hafsat ta bude baki zatayi magana kenan ogan yayima wani signaI ya fesa wata powder a daidai fuskar Hafsa, take kuwa ta fadi sumammiya a bisa gadon. Hankalin Safiyya ya kara tashi, Tana so tayi kuka amma tana tsoron karsu mata wani abu, 
Karkada kai kawai take alamar kar suyi mata wani abu, 
Wani bakin kyalle suka fiddo tare da fesa garin powder din nan a jikinshi sannan suka kulle mata bakinta dashi. 
Kan bindiga wani ya kwala mata aikuwa itama ta sume sai jini ke fita daga kanta kamar anyi yankan wata dabba, Tun daga nan bata kuma sanin abunda ya faru ba. 
Daukarta sukayi suka nufl waje da ita a hankali dan kar a jisu, saida suka fita suka sakata a mota sannan Haladu mai gadi yaji karar motar, 
Da sauri ya taso a rikice, ganin kofar gate a bude ne ya kara rikita rayuwarshi, Dakinshi ya koma ya dauko makamai sannan ya fita waje, 
Hasken motar kadan kadan yake hange har suka bule, 
Sosai yaji haushi ya koma dakinshi yayi tagumi, 
Baccin da bai koma ba kenan saboda yana tunanin abunda yasa ya iske kofa bude bayan kuma shi ya tabbatar daya rufeta kafin ya kwanta, 
Sannan kuma ga karar mota da yaji wadda asukwane suka bar area’n unguwar. 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *