WATA SHARI’A
CHAPTER 22
‘K’ARSHE’
“A bisa shaidu da hujjojl’ da suka gabata, kowa yaji yanda mai laifi ta amsa laifinta da bakinta, sannan kuma…” shiru alk’ali yayi kasantuwar tari da yaci karfin YB,
Sosai yake tarin hardajini ke fita daga bakinshi,
Cike da tausayi kowa ke kallonshi,
Baifi minti goma a wannan halin ba rai yayi halinshi, Da k’arfi iyayenshi suka d’auki salati had’e da kuka, dama sun san haka na zuwa saboda yanayin ciwonshi babu alamar zai tashi ko kad’an.
An d‘auki kusan awa d’aya da mutuwar YB harma an tafl da gawarshi Jalingo sannan kotu ta sake zama.
“Kotu ta tabbatar da cewa Salmah ita ce ta saka akayima Aishatu fyad‘e, bayan nan kuma tasa an kashe mata ‘yar uwa wadda a dalilin haka babanta ya yanke jiki ya fad’i ya mutu, Indiyawa sunzo zasu duba lafiyar dumbin al’ummah wanda a cikinsu harda Amrah k’anwar Aishatu, dalilin saceta da Salmah tasa akayi yasa harlikitocin suka k’araci zamansu suka koma k’asarsu, Salmah tasa an sakawa gidansu Aishatu wuta har ya k’one k’urmus, tayi hakan ne da nufin Aisha da mamanta su k’one dan bata san basu ciki ba. Dan haka kotu ta yankewa Salmah Abubakar hukuncin d’aurin rai da rai a gidan yari, Sannan kuma iyayen Salmah wato Alhaji Abu Abu da mahaifiyarta zasu bada tarar naira miliyan goma, wanda a cikin miliyan goma d’in za’a ware kud’in da za’a fitar da Amrah zuwa k’asar Indiya, za’a fidda wanda Aishatu zata koma makaranta saboda Salmah ita tayi silar da aka koreta, sannan kuma za’a fitar dana gidansu da Salmah tasa aka k‘ona. Abdul k’adir kuma an yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda shi da kanshi ya furta cewa da hannunshi ya kashe Afrah, sannan kuma a gaban kowa yazo ya watsawa Salmah acid a fuska wanda fuskarta tayi dameji harma abun ya shafi idanuwanta. Sauran matasan nan kuwa wanda suka kasance kisa itace aikinsu kamar yanda kotu ta tabbatar, An yanke masu hukuncin kisa ta hanyar harbi da bindiga su dukansu. Sarki manu kuwa bashida laifi saboda kotu bata sameshi da laifi ko d’aya ba saima taimako da yayi, dan haka kotu ta wankeshi daga laifi. ldan Alhaji Abu Abu bayada kud’in tarar da aka yanka masa, kotu zata d’aureshi na tsawon shekaru uku, ko kuma za’aci gaba da tsaronshi har sai lokacin daya kawo kud’in. A k’arshe kotu na bama Aishatu Abubakar hak’uri akan abubuwa da dama, mahaifinta da ‘yar uwarta da suka mutu Allah yaji k’ansu, ‘yar uwarta maras lafiya kuma Allah ya bata lafiya yasa ayi aiki cikin nasarah”. Kabbara kotun aka d’auka baki d’aya mutanen dake ciki,
Kuka Gentle ta sake barkewa dashi da taji hukuncin da aka yanke mata, Ta tabbatar da zata fuskanci tsangwama sosai a kurkuku saboda damejin da fuskarta tayi, ta zama abun tsoro kamar ’dodon Jatau.‘ “Zan biya, ko miliyan d’ari ne Allah na amince zan bayar akan a d’aureni” Alhaji Abu Abu ne yayi wannan maganar hade da share guminsa. Murmushin dattako alk’ali yayi dan dama abunda yakejira kenan, da gangan yayi maganar yasan Alhaji Abu Abu ba zai yarda a d’aureshi ba saboda shi d’an siyasa ne, sannan kuma yanada mak’udan kud’in da ko fin haka aka nema sai ya bayar.
Ummimah, Amrah, mama, Zarah da Rabiatu kukan farin ciki kawai suke,
Barr. Sultana da Barr. Umar kuwa sai farin ciki baki har kunne,
Har inda Barr. Sa’eed yake zaune yana had’a gumi Umar yaje, Bayan ya mik’a masa hannu yace
“Kamar yanda kayi fatan Allah ya had’amu a ‘WATA SHARI‘AH’ gashi kuwa ya had’amu, yau gashi dan k’aramin Barr. Ya kayar da babban Barr.”
Murmushin k’arfin hali Barr. Sa’eed yayi tare da fad’in “Bana fatan Allah ya sake had’amu a ‘
WATA SHARI’AH.‘ A yau kam na tabbatar da kai ba
k’aramin Barr. Bane kai babba ne, dan zan iya cewa kama fini girma daga kai har matarka, tashi tsaye ma mu gwada tsawo inga ni da kai wa yafi wani girma?.” Ya kwashe da dariya tare da mik’awa Umar hannunshi sukayi musabaha. Haka suka rabu Barr. Sa’eed na k’ara girmama Umar da Sultana dan ya tabbakar dasu ba k’anana bane. ‘
Godiya Ummimah tayima Sarki Manu Akan irin halarcin da yayi mata,
“Karki damu dama najima ina neman ta hanyar da zan taimakeki, sai daga baya na samu labarin ke ‘yar katsina ce, shine na dage har na samu inda kike, na kuma samu labarin halayen Barr. Umar da matarshi, shine na samu lambarsu na fara tura masu sakuna akan su taimakeki, na kuma k’i bayyanar masu da kaina dan bana so wani abu ya biyo baya , nasan halin lawyers sosai saisa na b’oye masu kaina, sanin zan iya masu amfani yasa dana had’u dasu na fara mayen k‘arya wanda duk a lokacin cikin hankalina nake, na basu complimentry card d’ina sannan muka shiga ciki ni da abokina, hatta had’uwarda mukayi daku a traffic duk tsari ne, saida na fahimci komai zai faru sannan nabi bayanku da mashin d’ina”.
Godiya ta sake yi masa sannan tabar wurin cikin mamaki. Gidajen television sai faman d’auke d’auken hotuna da videos suke,
Har inda su Ummimah suke saida wani d’anjarida yaje da nufin yayi mata tambayoyi, Har tayi niyyar bashi amsa Dr. Raflq fuska murtuke ya k’ariso inda suke yace “Kai dallah malam ja can, matar auren kake soka d’auka ka yad’awa duniya?”
Kallon mamaki Ummimah ta bishi dashi, ‘Taya akayi ta zama matar aure da har ake hakilo kanta?‘ Ta tambayi kanta.
Barin wurin d’anjaridan yayi dan yaga Dr. Rafiq da gaske yake ba wasa ba.
“Kike kallona koke ba matar auren bace?” Ya tambayi Ummimah had’e da d’an guntun murmushi.
“Taya akayi wadda ko saurayi batada shi ta zama matar aure?”, “Wadda k0 saurayi batada shi? Dan Allah kice Allah kin tuba, ya budurwa kamarki zatace batada saurayi? Gaskiya wasa kike”,
“Sam babu wasa a maganata, ka yarda dani wallahi da gaske nake”. Murmushi yayi dan dama abunda yake so kenan yaji daga bakinta.
“Tun kam in ganki, sunanki da Iabarinki kawai naji hankalina ya kwanta dake, ki daure ki cije kiso Rafiqu, wallahi zai rik’eki da amana, na jima ina fatan Allah ya kawo min ranar da zai kawo min wadda yake so ya aura sai yau, ina fatan zaki karb’i wannan tayin Ummimah” Umman Rafiq ce tajefo wannan maganar a daidai isowarta inda suke. Shiru Ummimah tayi na tsawon lokaci batace komai ba, Kallon Umman Rafiq tayi sannan ta miyar da kallonta ga Rafiq d’in, Murmushi ta saki wanda har saida hakoranta suka bayyana,
Haka kawai ta sameta cikin nishad’i wanda rabonta dashi an d’auki tsawon lokaci, tun kafin komai ya faru da ita.
Wannan murmushin da tayi shi ya tabbatarda amincewarta,
Cikin murna k’anwar Rafiq ta rungumeta tana fad’in “Mungode da kika amince da soyayyar yayanmu, insha Allahu zamu kula dake tamkar ‘yar uwarmu ta jini”,
Batace komai ba saidai fuskarta kawai za’a kalla a tabbatar da tsantsar farin cikin da take ciki.
Suna nan tsaye sai ga nurses d’in makarantarsun nan su hud’u sunzo kowace tana kuka hannunta rik’e da takarda,
D’aya daga cikinsu tana fad’in Wai yanzu dan wulak’anci tun anan za’a bamu takardar sallamah? Shegen son kud’inmu ya kaimu ya baromu, yau gashi gwamnati ta d’auki nata hukuncin a kanmu tun kafin ayi nisa”. Da wannan surutan har suka bar wurin. Ummimah kuwa cikin motar su
Rafiq ta bisu suka rankaya sai gidansu Sultana cike da farin ciki dan dama kowa ya koma su kawai akejira.
‘Alhamdulillah! Nima kuma anan sai na d’igawa wannan labarin aya,wata shari’ah labari ne wanda zan iya cewa fiye da rabinshi ya faru da gaske. Saidai kuma wadda abun ya sama haryanzu gaskiya tak’i ta bayyana, rayuwarta ta wulak’anta kamaryanda ta Ummimah ta wulak’anta, an koreta a makaranta an nuna anfi k’arfinta ta hanyar dukiya, ‘yan uwa musulmai mu taru mu saka wannan baiwar Allah’r a addu‘ah k0 Allah zai kawo k’arshen mawuyancin halin da take ciki.‘
Godiya ga masoyana maza da mata, na nesa dana kusa, masu kirana, masu yimin text messages, masu bina ta pchart suna min fatan alkhairi harma da wanda Allah bai basu daman yimin magana ba nagode sosai da kulawarku