WATA SHARI’A CHAPTER 5

WATA SHARI’A 





CHAPTER 5





A lokacin mun zama ‘yan mata cikakku masu jini a jika, 
Ba yabon kai ba ni kyakkyawa ce koda yake ba saina fada miki ba saboda kema kin gani da idonki, 
Sai a wannan lokacin diri na ya sake Iitowa sosai, 
Samari suka fara kawo min hari amma ni duk basa gabana, 
Babban burina bai wuce inyi zurfi a karatuna ba, inaso in zama wata mai matsayi a b’angaren education, hakan yasa ko a jamb dita na cike Bsc ed. Biology a Talent University Jalingo, 
Itama Gentle shi ta cike dukda ba shine burinta ba, amma kuma saboda taga hakan nakeso yasa itama tacewa mamanta lallai irin karatu daya take son muyi. 
A duk family d’inmu babu 
waada baisan Gentle ba, haka itama kaf family’nta kowa ya sanni, 
Maganarta d’aya dai Aisha Abubakar, kullum Ummimah, har wasu daga cikin danginsu itama suke kiranta da Ummimah sabida yawan fad’ar sunan da takeyi. 
Afrah da Amrah kuwa an girma, yanzu sune suka shiga ss3, mu kuma muna jiran sakamakonmu na jamb ya fito. 
Bayan sati biyu kuwa ya Iito, Alhamdulillah sakamako yayi kyau sabida na  samu 216, Gentle kuwa 190 ta samu, amma dai lafiya lau babu matsala, saboda 180 akeso k0 wane d’alibi ya kawo, 
Murna a wurinmu ba’a magana, har sadaka nayi saboda wannan sa‘ar dana samu, 
Babana kuwa Alhamdulillah! Yanzu company’n da yake ya dan tashi, saboda har albashinsu akan lokaci ake basu, dan haka mun dan warwawa sosai. 
Amrah ta samu sauki sosai kamar bata tab’a yin ciwon ba, dan haka muka kasance happy family bamuda matsalar komai duk da talaucinmu bai hanamu sakewa da walwala ba. 
Cikin mun fara shirye shiryen fara registration ne kwatsam ciwon Amrah ya fara dawowa, 
Iya tashin hankali mun shigeshi, saboda yanzu ya canja salo ma, harda jini take zubarwa sosai babu cobtrol, ga wannan yawan shan ruwan nata, sannan kuma saurin mantuwa, yanzu za’ayi abu yanzu zata mantashi, 
Ta zama tamkar tababbiya. 
Hankalim baba ya tashi sosai, hakan yasa ya kama hanyar asibiti ya nufi wurin likitan daya saba kula da Amrah, 
Bayan ya shaida mashi halin da ake ciki ya dafe kanshi, 
“Lallai yanzu ina ganin dole sai anyi aikin nan, saboda cutar ta fara zama chronic a jikinta, ina mai shawartarku indai kunada damar fitar da yarinyar nan waje to ku fitar da ita tun wuri ayi nata aiki, saboda inhar kuka zauna a haka da ita tofa zaku iya rasata”. 
Hankalin Baba ya tashi sosai, haka ya kamo hanya ya dawo gida babu nasarah, 
Cike da tausayin Amrah yayi mana bayanin yanda sukayi da likita, kuma gashi yanzu ma wai kud’in aikin sun karu, sun tashi daga miliyan biyu da rabi 
sun koma miliyan hud’u saboda kud’in jirgi da suka karu. 
“Allahumma ajirnaa fi musibati, wakhlifnaa khairin minha” kawai ke futa daga bakina, da muna murnar Amrah ta samu sauk’i, sai gashi kuma ciwo ya dawo mata. 
Haka rayuwa taci gaba da tafiya kowace rana sai na karanta mata suratul Yaasiin a ruwa tasha, hakan yasa ta ringa samun sauki sosai, amma kuma duk da haka bata daina zubar da jini ba, duk bayan sati biyu sai anyi nata karin jini. 
Da daru da komai na tafi makaranta, da nace bazanje ba saidai inyi asarar admission din, nayi niyyar zama in kula da ‘yar uwata, 
Saida Baba ya kirani yace 
“Bai kamata kiyi hakaba Aisha, wannan karatu da kika samu wata damace wadda bai kamata ki bari ta kufce miki ba, idan kuma kika bari ta kufce miki tofa samun dawowarta ba abune mai sauki ba, 
Kinga dai yanda nayi na hada kud’in registration d’inki, 
Sannan kuma zamanki a gida ba shine zai warkar da Amrah ba, kiyi hak’uri ki taf1 makaranta, ki ajiye hankalinki kiyi karatu, insha Allahu Amrah zata samu lafiya, ki cire duk wata damuwa a ranki, na siyo miki komai da zaki bukata suna d’akin mamanku na ajiye jiya dana dawo na samu duk kunyi bacci”. 
Wani irin hawayene ya k’wace min, bana komai bane face na tausayin Babana, ya gwammaci 
ya rasa komai ya kyautata mana, ya gwammaci ya kwana da yunwa mu kuma ya ciyar damu, ya gwammaci ya kask’antar da kanshi ga mutane duk dan ya samu abunda zai rufa mana asiri, lallai iyayenmu abun muji k’ansu ne, bai kamata muna wulak’anta iyayenmu ba, wai har sai kaga yaro babanshi yana magana shima yana magana. 
Hakuri Baba ya ringa bani har saida yaga nayi shiru, da yake mutum ne mai barkwanci saida ya sakani dariya sannan yabar d’akin. 
Bayan kwana uku kuwa na kama haramar shiri, 
Su Gentle sukazo saboda munyi da ita tare za’a kaimu a motar gidansu, 
Dan haka da sauri ta shigo tace 
in Fito ana jiranmu. 
Hak’uri na bata akan tayi min uzuri in jira dawowar Baba, saboda yace in jirashi akwai sakon da zai kawo min bazai dad’e ba. 
Ba tare da nuna gajiyawarta ha ta zauna har baba ya dawo, 
Bawan Alkah ashe waya ce ‘yar baby nokia yayo min fafutukarta harda sim card na MTN, 
Wani hawayen na sakeji amma ban barshi ya Fito ba, 
Har kofar gida suka yo min rakiyarmu, ciki kuwa harda Amrah dake kukan tafiyata. 
Shiga motar mukayi gidan baya nida Gentle, kasantuwar driver d’in gidansu ne yasa babu wanda ya zauna a gaba, 
Suna d’aga min hannu har motarmu ta fita daga kwana. 
Sai a lokacin kuka ya fito min, 
Sosai Gentle ke rarrasata amma naki yin shiru har sai lokacin dana gaji dan kaina sannan nayi shiru. 
Kusan awa shida muka d’auka sai gamu a cikin jigawa, sosai garin ya burgeni saboda yanada kyan tsari sosai, 
Har cikin makarantar aka kaimu, dama mun kama room dan haka wurin securities na hostel mukaje, number’n room d’in muka fada sannan aka bamu key aka shaida mana akwai katifa da gado a ciki. 
Gentle ta umurci driver dinsu daya tafl kawai, mu kuma muka kwashi kayakinmu muka ringa nufar block B dasu, babban haushin ma wai 3rd floor muke, na tsani hawan bene a rayuwata, 
Saida mukayi zarya uku sannan muka gama kwasar kayanmu, 
Salloli na fara gabatarwa, nan ma saida nacema Gentle ta tashi tayi sallah sannan tayi. 
Aunty Sultana wallahi ban zaton Gentle zata saka min da abunda tamin ba, ashe babu alkhairi a zuwana wannan jami’ar Ummimah ta fashe da kuka, 
Koda ta farga ashe Barrister Sultana ma ta dade da fara kukan, tun lokacin da Ummimah ke fada mata ciwon Amrah ta fara kuka. 
Da kyar ta samu ta share hawayen tace “ina jinki kici gabai 
“Bayan mun huta na saka wayata a chaji, tana jikin chajin 
na kunnata, koda na saka layina ashe harda katin dari biyu baba ya saka min, dan haka lambarsa kawai na saka dan inada ita a kaina, 
Ringing d’aya tayi kuwa ya d’auka, cike da farin ciki yace “‘yata Aisha”, Murmushi nayi nace “sannu baba, ya gida yasu mama?”, “Lafiya kalau kun sauka lafuya?”, 
“Alhamdulillah baba, mun dade da sauka harma mun huta”, 
“To masha Allah, ki gaishe min da Salmah d”in”, 
“To zataji baba, ya jikin Amrah”, 
“Amrah taji sauki sosai, gobe ma zamuje a k’ara mata jini”, 
“To baba Allah ya kara mata lafiya, a gaishesu duka” nayi hanging up na wayar, na fad’a ma Gentle sakon Baba na 
gaisuwa. 
Haka rayuwa taci gaba da tafiya mana, muna karatu sosai har first semester ta kare muka koma gida, kasantuwar hutun bashida yawa nan da nan muka koma School, 
Wannan komawar ce baki daya Gentle ta canja halinta, ta zama mace maras kamun kai, duk mazan course mates dinmu babu wanda bata hulda dashi musamman ma irin ‘yan iskan nan masu sauke wando kasa. 
Har ni dinma ta fara canja 
min fuska, kuma da zarar na mata magana sai ta nunar da babu ruwana da halinta, inyi irin ruyuwar da nake so itama in barta tayi wadda take so, 
Wannan canjin da tayi yasa wani lokaci in zauna in yita 
kuka, 
Saboda har kawancen ma ta daina yinshi dani, 
Ta samu wasu ‘yan iska sune abokananta. Wata rana mun tashi lecture 2pm, 
Tun fitata daga theater nake jiran Gentle ta fito mu tafi amma shiru batazo ba, gashi kuma ina azumi saboda ranar Monday ne, ga rana kuma anayi. 
Jinta shiru yasa na koma Theater d’in, a tsakiyar maza na sameta sai kashewa suke suna ihu, 
Jiki ba kwari na matsa inda suke nace “ke nake jira Salmah kin san azumu nake”, 
Budar bakinta tace “toni ina ruwana da azumin da kikeyi? Nace ki rakani ne iye? K0 kuma 
bansan hanyar hostel din bane?”. 
Da tsawa tayi maganar, tunda nake da ita bata taba yimin magana irin haka ba, 
“Ki tafi ai nima nasan hanya, wannan ma ai kinibibi ne ace wai dole sai tare dani za’a tafi”, 
Shewa abokan nata maza da mata suka saka, bansan lokacinda naji hawaye suna fita daga idona ba, 
Ban kuma fad”ar komai ba na Fita na nufi hanyar hostel ni kadai ina mamakin sauyin hali da Salmah ta samu lokaci d’aya. 
Bayan kwana biyar muka fara second semester exam, sam Gentle bata miyar da hankalinta, karatun ma bata zama bare tayishi. 
Wata ranar alhamis wadda 
bazan taba mantawa da ita a rayuwata ba, ta zame min bakar rana abun gudu ga kowane mutum. 
Zaune nake ina karatu kasantuwar wata chemistry exam da zamuyi gobe jumu’ah, 
Course din yanada matukar wahala kuma gashi 4 unit ne, amma sam ni bana jin wahalarsa saboda na iya kuma bana missing lecture din, 
Gentle kuwa ban taba ganinta ta zauna lecture d’inshi ba, k0 magana na mata saidai ta bini da bakar magana. 
Ji nayi bazan iya zama ba ita kuma bata iya ba dan bana son ta fadi a course din. 
Block A na tafi nemanta wurin wata kawarta amma kawar ta bini da kallon banza, 
Saida ta gama sannan tace “ta tafi wurin saurayinta AK” ta fada 
a tak’aice. 
Daukar hanyar fita daga hostel d’in nayi na nufi inda naga wasu samarib suna tsayawa hira. 

Mu tara

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *