WATA SHARI’A CHAPTER 6

WATA SHARI’A 






CHAPTER 6




Fitilar hannuna na ringa haska motocin gaban gate din, amma kuma duk wadda na duba babu Gentle a cikinta, 
Dan haka na kara matsawa daga gaba ina hashaskawa still dai babu ita, 
Cike da tashin hankali na kashe fitilar wayar tawa, na latsa kiranta saidai kuma naji ana shaida min da babu kudi kona flashing a wayar, 
Hankalina ya kara tashi, kamar zautacciya na ringa kwala mata kira amma shiru ne. 
Har kusan Faculty of Humanities naje da yake shine daga gate din hostel babu nisa saishi amma babu ita, 
Motoci biyu na hanga daga can nesa aikuwa babu shamakin komai na doshi wurinsu, 
Dalle fitilar nayi ata farkon amma sai samari matasa na gani cike da motar, zasu kai kimanin mutum takwas zuwa goma, harma mamakin yanda motarta daukesu nayi, 
Hakuri na basu sabida naga kamar basuji dadin haskewar ba. 
“Ke ubanme yasa kika haskemu da fitila? Ko mu sa’anninki ne?” Wani daga cikinsu ya 
tambayeni cike da muryar maye, alamar yasha ya bugu sosai. 
“Kuyi hakuri ‘yar uwata na fito nema ne, nayi zaton ko itace anan” na fada cike da 
tsoronsu bayan na doshi inda d’ayar motar take. 
Basu kuma cemin komai ba har na isa wurin d’ayar motar, 
Haske cikinta nayi saidai kuma banyi sa’ar kallo ba, 
Saboda mace da namiji ne a bayan motar sunata aikata alfasha gasu tsirara haihuwar uwarsu, 
“Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un!” Kawai na fad’a cike da tashin hankali, saboda sam basa cikin hayyacinsu sun lula can wata duniyar. 
Har nayi shirin juyawa zan tafi naci tuntube da takalmi, 
Haskawa nayi saboda harda shirin kadani yayi, 
Cike da mamaki na kalli takalmin na kara kallonshi, 
“Wannan ai takalmin Gentle ne” na fada a fili“ bayan na tsuguna k’asa ina kare mashi kallo, 
Daga cam gefe na hangi gyalenta da dankwalinta, 
“Ya Salam” na sake furtawa saboda sam ganin abun nake kamar a mafarki. 
Tamkar bana cikin hayyacina na koma jikin gilashin motar na ringa bubbugashi da karfi, saboda ni a tunanina kota karfi da yaji ne aka turata cikin motar. ‘ 
Duk bubbugawar da nakeyi shirune sabida har yanzu basu dawo hayyacinsu ba, Kafar takalmin nata d’aya na fara bubbuga gilashin dashi take kuwa suka zabura su 
duka biyun a tare, 
Da sauri mazan dake cikin waccan motar sukayi wurina, 
“Waike wace irin sakaryar yarinya ce? Ubanme kike a wurin nan? Ina ruwanki dasu?” Wani daga cikinsu ya fada kamarzai fado min, 
Saurin matsawa nayi gefe hannuna aka ina tsala ihu ina fadin “jama’a ku taimaka mana, sun tura ‘yar uwata a cikin mota”, 
Kasantuwar babu giccin kowa yasa babu wanda yajimu, 
Da hanzari cike da kunya macen ta miyar da kayanjikinta bayan namijin ya sauka daga gareta, Fitowa daga motar sukayi su duka biyun suna tambayar abunda ya faru. 
Gaba d’aya wutar kaina ta d’auke lokacin dana dora idona akan Gentle sai rarraba ido take tana fadin “wai miye haka kukeyi  Muna tsaka da jin dadinmu zaku nemi tsayar damu” har a lokacin bata kula dani dake gefe ba ina binta da kallon mamaki. 
Cike da tashin hankali nace “Salmah! Kenan da saninki kika shiga motar nan ake aikata alfasha dake?”, 
Kare min kallo tayi ta tabbatar da nice sannan cikin halin ko in kula tace 
“Ehh da sanina ne sai kuma me? Ke Aisha bari kiji in fada miki, tun wuri ki fita daga sabgata idan ba haka ba kuma wallahi ni kadai nasan matakinda zan daukar miki”. 
Kallonta nayi cikin ido saboda an kunna security light na cikin makarantar, 
“Kiji tsoron Allah Salmah, ki sani iyayenki da suka kawoki makarantar nan fa sun damka miki amanar kanki ne, idan kikaci amana kuwa sai amana ta kamaki, zina Salmah? Wa‘iyazu billah! Da idona na ganki kina aikatata, sam banyi tsammanin halin naki har yakai haka ba” 
na fashe da kuka sosai ina kara mamakin Salmah. ‘ 
Cike da izgili namijin da suke masha’ar tare yace 
“To wai ita wannan wacece ne Gentle? Taya zaki bari tana fad’a miki magana anyhow?”, 
Ban ko kalleshi ba saboda banga abunda zan kalla ga mazinaci ba, 
Dan haka na koma gareta, 
“Kin cuci iyayenki kin kuma cuci kanki, kiyi gaggawar tuba ga Allah saboda Allahu gafurur-raheem ne, idan kika bi sharudd’an tuba mai yiwuwa ne ya yafe miki”. 
“Ke wai ina ruwanki danine? Idan ma abunda yafi zina nayi ina ruwanki? Kija kazamin jikinki ki kara gaba” Gentle ta fada cike da masifa. 
“Ke har kinada bakin kiranjikina da k’azami? Ai babu babban kazamin jiki bayan na mazinata, k0 kun manta Allah mad’aukakin sarki yace “wala taqrabuz-zinah”, 
Karma mu kusanci zinar bare har mu aikatata, dan haka dan Allah kiyi hak’uri ki rabu da wannan yaran, Salmah ki koma halayyarki ta baya wadda kika baro gidanku da ita“ na kara fashewa da kuka ina kara tuno kawancenmu da ita tun usuli
“Aisha Kibar wurin nan tun kafin in daukar miki mataki” ta sake fada tana kallona cikin idona. 
“Bazan tafi in bar wurin nan ba Salmah sai idan tare dakene, ki d’auki duk matakinda zaki d’auka dan bazan iya tafiya in barki ke kad’ai ba saboda zaku iya komawa kuci gaba da aikata mugun aikinda kuke kanyi”. 
Kyakkyawan mari saurayin nata ya d’aukeni dashi, Take na ringa ganin bishi bishi kamar zan fad’i k’asa, Dakewa nayi na had’iye hawayen daya flto min, na k’udura a raina bazan tafi inbar Salmah a wannan halin ba. 
“Ka kyaleta AK, nasan maganinta” ta fada tare da sake juyiwa ta fuskanceni, “Wallahi sai nasa anyi miki fyade matukar baki bar wurin nan ba”. 
A wasa na dauki abun saboda wannan maganar ban taba zaton zata fito daga bakinta ba, kuma ni nayi zaton bacin raine ya sakata fad’in haka, Dan haka naci gaba da tsayuwa ina jiranta tazo mu tafl. 
“Khalifx kuyi mata fyade kuma na rokeku karku sassauta mata, nasan zaku iya ku jata kukai dajin can inda babu haske” Gentle ta fada tare da komawarta cikin mota itada saurayin nata wanda naji ta ambata da Ak. 
Kamar wasa wannan kartin suka ringa jana da karfin tsiya suna kara turani cikin daji, 
Hankalina ya kara tashi sosai ganin da gaske suke abunda Gentle ta sakasu suyi min shid’in zasuyi. 
lhu nake sosai ina fadin “Ya Allah ka kareni daga sharrinsu, Baba, Mama kuzo zasu rabani da ‘martabata’ (Ummi Aisha), amma shiru sabida wurin ihunka banzane saboda babu wanda zai iya jina. 
Samari takwas saida sukayi min fyad’e, idan wannan ya gama sai wannan yazo yayi babu sassauci, Gashi kuma cike da rashin imani sukeyin abun, sosai nakejin azaba,tun ina ihu har ihun ma ya daina fita sai sabbatu da nakeyi wanda bansan abunda nake fad’i ba. Bayan mutum takwas d’in sun gamane na k’arshen yace “Manu saura kai, kazo ka gama da ita mu kaita mu jefar, sabida babu alamar ma tanada Rai
Sama sama nakejin maganganun nasu, 
Wanda suka kira da Manu yace “haba ai wannan rashin imanin naku yayi yawa, taya zakuyiwa yarinya fyad’e har ku takwas? Tunda nake a rayuwata ban tab’a jiba ko a labarai, dan wannan yarinyar ma bana tunanin tana numfashi, gaskiya ta mutu kuma dole zata mutu, gardawa takwas ba wasa bane
“Kai wawane matsalata dakai Sarki Manu, komai kai kace tausayi, an fada maka a iskanci akwaa tausayi ne?” Wani daga cikinsu ya fad’a. 
“Aini kasan duk iskancina bana yiwa mace dole, sai idan ita ta amince tace taji ta gani sannan nake mu’amala da ita, sab’aninku da aikinku kenan yima yaran mutane fyad’e” wanda suka kira da Sarki Manu d’in ne yayi wannan maganar. 
Duk abunda akeyi na zama niba rayayyaba ba kuma matacciya ba, Allah dai ya bani ikon 
sauraren maganganunsu amma kuma ko idona bana iya bud’ewa. 
“Shikenan ai ku d’uketa ku jefar cikin dajin nan, saboda da alama dai ta mutu wannan 
gawace”, Inajin sun fadi haka gabana ya tsananta bugawa, 
Saijin muryar Manu naji yayi yace a a karku jefarta cikin daji dan Allah, ni ku barni in kaita daga can gefe, yanda za’a iya ganinta cikin sauki sai a sallaceta”. 
Daukata kuwa yayi yakai daga can gefen titinda zai zartar da mutum cikin humanities, a hankali ya ajiyeni tun daga nan baccin wahala ya d’aukeni wanda ban kuma sanin inda kaina yake ba. 
Farkawa nayi na ganni kwance a bisa gadon asibiti, A hankali na fara bud’e idona saidai kuma idon yak’i bud’uwar tsabar kumbura daa yayi, Sannu sannu na fara tariyo abunda ya sameni wanda yake mummunan abu ne, Kuka na fasa da karfi tare da mimmikewa a bisa gado ina fad’in “Baba’. Mama“ Shikenan sun rabani da martabata, sun keta min mutuncina wanda k0 wace mace take tutiya dashi, wayyo Allah Babana!” Na rintse idona sosai ina k’ara tuno yanda suka ringa yi dani. 
Cike da natsuwa wani likita ya shigo hannunshi rik’e da file, Sallamah yayi idona rintse na amsa sallamar, “Alhamdulillah anyi ta barka tunda kin tashi, sannu ko?” Likitan ya fada tare da zama 
bisa kujerar da aka tanadar domin zaman likitoci idan sun ziyarci maras lafiya. 
Jin ya zauna yasa a hankali na fara k’ok’arin bude idona, Idon ya bude saidai ba duka ba, saboda wani irin mugun kumburi ne yayi. 
“Sannu kinji Aisha?” Ya fad’a tare da ajiye file d’in akan cinyarshi. 
Kai kawai na daga bayan na gyara kwanciyata, ina mamakin yanda akayi har yasan sunana Aisha. 
“Yajikin naki?” Ya sake fad’i kyakkyawar fuskarshi d’auke da murmushi, “Alhamdulillah” kawai na fad’a a takaice, 
“To masha Allah! Ina fatan dai kinsan abunda ya sameki”, 
Ban bashi amsa ba sai wani irin kuka dana sake barkewa dashi ina kara duba kayan 
dakejikna, saboda harsu ji nayi na tsanesu baki daya. 
“Anyway, an kawoki asibitin nan ne kwana biyar da suka wuce, daga School Clinic akayi refer dinki zuwa wannan asibitin a lokacin tamkar baki da rai, saboda ma an fidda tsammanin zaki rayu, 
Ganin ciwonki kamar yafi karfin clinic d’inku saboda manyan likitocin naku duk sun tafi hutu basu dawo ba yasa aka kawoki nan, 
Ina so ki ajiye hankalinki ki saurareni, karki sake yin kukan nan ki danganawa Allah komai, saboda dukkan abunda kikaga ya samu bawa to mukaddari ne daga Allah, babu wani bawa wanda yafi k’arfin k’addara, dan haka ki saurareni da kunnen basira zan miki 
bayanin komai”. 
Kai kawai na d’aga masa, ammafa hawayen dake futa haryanzu na kasa tsaidashi daga 
sintirin da yake a bisa kumatuna. 
Medical glasses dinshi ya cire ya sakalashi a lab court d’in daake jikinshi, 
Ya kura idonshi cikin nawa, da sauri kuwa na dukarda kaina k’asa, sabida wani irin kwarjini naji yamin, 
“Bayan nurses na makarantarku sun kawoki na karbeki emergency nida abokina Dr. Khalid muka fara duddubaki, 
Saidai kuma bamuyi tunanin ciwonki ba, kawaidai mun karbeki ne muka fara yi miki gwaje gwaje inda a take muka gane cutar hawanjini datayi miki sabon kamu dan da alama bata wuce kwana d’aya da kamaki ba, 
Bayan mun gamane kamar ance in kalla kawai naci karo dajini a bisa cinyoyinki, baki d’aya cinyar tayi sharkaf da jini harda gullamarsa. 
Hankalina ya tashi sosai nace da Dr. Khalid “kaga babbar matsalar yarinyar nan”, Sosai mukaji tausayinki, nan da nan muka fara duddubaki inda mukaci karo da raunuka sosai a k’asanki wanda tunda nake a rayuwata ban tab’a ganin ko mai kama dashi ba, Na tabbatarda wannan fyade ne akayi miki, kuma ba wai mutum d’aya ko biyu ne sukayi aikin ba, saboda yanayin wurin ya rarake sosai da sosai. 
Bansan lokacinda na fashe da kuka ba saboda kin matukar bani tausayi, sannan kuma gaki yarinya karama baki wuce 17 ba amma an lalata miki rayuwa, 
Aune aune mukayi sosai anan muka tabbatarda baki d’auke da kowace irin cuta, kawaidai raunukan ne da kikaji, 
Harga Allah banyi tunanin zakiyi rayuwa ba, 
Ganin yawan jinin da kika zubaryasa nayi miki awon jini nan na tabbatarda bakidajini sosai, 
Dan haka na d’ibi nawajinin kasantuwar zan iya badashi ga kowa na saka miki, 
A tak’aice dai kwananki biyar a asibitin nan kuma bakya cikin hayyacinki, shine yanzu wata nurse tazo gittawa taji muryarki kina sabbatu ta kirani, 
Naji dad’i sosai da kika tashi sabida jinki nake tamkar ‘yar uwata tajini, saboda duk abunda zai samu wani ko wata sai mutum yayi tunani idan ga wani nashi abun ya faru ya zayyi? Shiisa akeso mutum ya zama mai tausayi da jink’ai ga mutane baki d’aya”.
Harya gama maganar kaina na bisa k’irjina ban sauke ba, sai wani irin rad’adi da zuciyata keyi hade da tafarfasa, 
Na rasa me zanyi inji dad’i, kasana kam baya ciwo sosai saboda yamin alluran kashe zaf’, 
Kaina sai azabar ciwo yake yana min barazanar fashewa, 
Sunan Allah kawai nake ambato saboda yanayin da nakejin kaina kamar bani ba. 
“Inaso kibar wannan al’amarin a hannun Allah, shi yasan wanda suka miki wannan abu kuma shi zai saka miki, abun yazo da sauk’i tunda babu cutar data sameki, ki daina kuka kinga har hawan jini ya sameki, ina miki gudun kar tashin hankali yasa zuciyarki kamuwa da wata cuta har tayi silar rasa numfashinki”. 
Cike da karfin hali nace 
“Likita mutuwa itace babban burina a halin yanzu, banida sauran wata martaba, an wulakanta min rayuwa, ina fatan mutuwa tazo ta tafi dani akan wannan halin da nake ciki”, 
Cikin sigar rarrashin yace, 
“Ki daina irin wannan maganar Aisha babu kyau kace kafison ka mutu, yana daya daga Cikin imani fa wato mutum yayi imani da k’addara mai kyau ko maras kyau, dan Allah ki 
lallabi zuciyarki, ita kaddara bata taba tsallake bawa. Allah yasan halinda kike ciki kuma shi zai saka miki”. 
Cike da gamsuwa da maganarshi nace “babu komai likita, na yarda cewa wannan ‘kaddarata ce‘ (My dear Zarah bb), na barma Allah komai shine kawai zayyi min sakayya” 
na share hawayena da tafin hannuna. 
Sallamah mukaji anyi tare da bud’e kofar dakin, Zarah da Rabiatu ne suka kunno kai a cikin d’akin, room d’insu shine kusa da namu sannan kuma suma course mates d’inmu ne, Tun lokacinda Gentle ta fara sake hali wurinsu na fara komawa saboda sunada kyawawan halaye irin wanda nakeso k’awayena su kasance dasu, Wani lokacinma idan Gentle bata kwana a hostel ba room d’insu nake tafiya in kwana, suma mun shak’u dasu amma ba sosai ba. 
D’aga kai nayi na kallesu bayan sun shigo likita ya amsa sallamarsu, File dinshi ya d’auka sannan ya miyarda gilashinshi yace “Allah ya k’ara sauki kinji”, “Ameen” na fad’a a hankali tare da miyar da kallona gasu Zarah. 
Cike da tausayi Rabi’atu ta kalleni ta kawar da kanta daga gareni saboda kukan daya kufce mata, 
Zarah ce tayi k’arfln halin cemin “sannu Aisha ashe kin tashi”, 
“Ehh na tashi yanzu” na bata amsa, 
“Toya jikin naki?” Ta fada cike da tausayi, “Da sauk’i”. 
Rabiatu tajuyo bayan ta goge hawayen itama tamin yajiki, 
Zarah tace, 
“Kamar wasa fa a ranar da dare muka jiki shiru har sha dayan dare bakizo dakinmu ba, bayan kuma kin saba koda ace ba wurinmu zaki kwana ba kina shigowa ki mana saida safe, 
Jin shirin yasa muka leka room d’inku amma babu kowa a ciki, 
Zaman jira mukayi dan a tunaninmu ko kin tafi toilet ne, 
Shiru dai har dare ya nitsa sosai saiga Gentle ta shigo, 
Da sauri a tare muka mik’e Rabi’atu tace mata “tun d’azu muke nan zaune munajiran ‘yar uwarki bamu san inda ta shiga ba”. Tsaki kawai tayi ta kama kunce kayanta ko a jikinta, 
Kallon Rabiatu nayi itama ta kalleni, 
“Dan Allah ki mana magana ko hankalinmu zai kwanta, kin san inda taje?“, 
Cike da zafin rai tace min “kai da Allah malamai ku shafa min lafiya, gata nan na nada a kaina nayi gammo da ita sai ku sauke”, 
Cikin karfln hali nace mata 
“Me yayi zafi Gentle? Hakkin zaman tarene ai, dan Allah kiyi hak’uri ki sanar damu inda take idan kin sani”. 
Budar bakinta tace “wallahi idan baku shafa min lafia ba kuma zansa a maku yanda akayi da ita”.Hankali tashe muka fita daga d’akin bamu sake furta komai ba, Iya tashin hankali mun shigeshi, a daren ranar a rintse babu wacce ta rintsa a cikinmu, Dan haka washe gari muna gama sallar asubah muka fita nemanki, 
Mune har block C muna nemanki amma babu ke babu alamarki, 
Dama kuwa bamuyi tunanin zamu sameki acan d’in ba, saboda munsan ke ba mutum bace mai yawon zuwa wuraren mutane, Ba
A hargitse muka fita bakin gate din hostel, 
A lokacin har gari ya fara haske, 
Securities d’in gate muka tambaya ko sun ganki amma duka amsar d’ayace basu ganki ba, 
Wani Baba mai fad’a sosai nasan kin ganeshi, 
To harda cewa yake wai “wata kilama yawon iskancinta ta tafi shine zakuzo kuna wani nemanta”, 
Wallahi ya bani haushi sosai harsaida naji kamarin makeshi in huta, 
Da haka muka fita daga area’r hostel d’in baki d’aya muka tinkari humanities. 
A can gefen titi muka hangi mutum dunkule kamar marsa rai, Cikin tsoro muka fara takawa har muka isa wurin, Dubawar da zamuyi kuwa sai mukaga ashe kece, Gaki kwance male male cikin jini kamar an d’iba an zuba miki, Hannuwa muka d’ora aka muna neman agaji, Can muka hangi wayarki da ‘yar purse d’inki a gangarenda zai shigar da mutum dajin nan, Bamu jira komai ba Rabiatu ta sabeki a kafad’a mukayi School clinic dake, Su kansu hankalinsu ya tashi sabodajinin da sukaga yana fita daga jikinki kamar an bud’e famfo, Ganin abun yafi k’arfinsu yasa aka sakaki a mate muna biye dasu aka kawoki wannan asibitin, Ni na fad’a masu sunanki nayi signing a wata takarda sannan likitan daya fita d’in nan shida wani guda suka hau dubaki, Kullum sai munzo amma mu tayar baki farfad’o ba, saidai kuma likitan yana kok’arin kwantar mana da hankali ganin yanayin halinda muke cikinsa, Mun sanar da Gentle abunda ya sameki amma tsaki kawai tayi ko ajikinta, Yanzu haka fitowarmu kenan daga exam din kuma munma HOD na Biology 
complain cewa bakida laflya, yace idan kinji sauki ki sameshi za’asan yanda akayi ayi miki“. 
Nannauyar ajiyarzuciya na sauke bayan Zarah ta gama bani labari, nakara tsanar Gentle sosai a raina, 
Sai yanu nake dana sanin amince mata ta zama kawata, ga irin muguntar data bini da 
ita, Na kara tuna nasihar da Babana yayi min akan in guji abota da yaran masu kud’i, 
bawai duka aka taru aka zama d’aya ba, amma kuma wasu daga cikinsu basu da tarbiyya. 
Gashi kuwa na gani da idona, naga kalar ketar da babbar kawata ko ince aminiyata tayi min, 
To ba anan kadai abun ya tsayaba Aunty Sultana, duk ta wannan ma mai sauki ne akan wasu abubuwan. 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *