WAYE ANGON BOOK 2 CHAPTER 13 BY MARYAM JAFAR KADUNA

yinta, so, ake haukata min da kenan? To ba zai yiwu ba.

Ita kuwa Mabaruka sai dare sannan ta farka, tun baccin da ya dauke ta. Sayauta tashi, sai dai damuwarta wuni daya duk ta fada tayi zuru-zuru tayi jugum tunanika kala-kala marassa dadi suka dameta, sai dai zaryar hawaye. Rafi’a na gefenta duk yanda taso ta jata da labari amman ,sam ta kasa shawo kanta, ita kadai ce ke labarinta. Dole ta yankewa kanta shawarar ta kwana a nan tare da ita.

Suka tsayar da magana tsakanin Momy da Daddy sai uban gayya Imran, akan tarewar matarsa gobe insha’Allahu. Ya yi jim! Yana jin damuwa a ransa da tsoron abu daya game da hakan, Daddy ya lura da shi ya ce “Akwai matsala ne?”

Yace, “Um to! Akwai Daddy.” Ya ce, “Me kenan?”

Ya ce cikin damuwa yana kallonsu.

*Ban san ya zamanmu zai kasance da ita ba. Ina tsoron kar ta hallakar da kanta a kaina kamar yanda take fada. Na lura har zuwa yanzu. bata sona ko kadan, ko ganina bata sonyi

A duniya bata da makiyi kamata, dubi fa irin haukan da tayi yau duk don an tabbatar mata da nine mijinta? To yanzu kenan muna nesa da juna, ina ga muna tare da juna? Zamu yi rayuwa da ita ta kusanci kuma har abada.”

Yana magana abin tausayi.

Da Daddy da Momy suka tausaya masa. Amman Daddy ya ce “Kai namiji ne Imran me karfin zuciya, kada ganin haka yasa ka sare. Mabaruka matarka ce an riga an daura: baka da zabi a yanzu zama da ita dole ne, sai kayi hakuri da juriya zaka ci nasara, za ka samu abin da ka ke so daga gareta.

Batun tsoro duk ka aje shi a gefe, ka sa a ranka zaka iya duk kurari ne ita kuma ba za ta kashe kanta ba kasa ido kuma ka gani.”

Ya yi jim har yanzu da yana jin shakku a ransa, soyayyar nan fa ba dole zai iya hakuri da ita koda hakan shi ne ajalinsa ya gwammace farin cikinta a kan nasa, gwanda ita taji dadi a kansa.

Daddy ya katse Imran.

“Calm down my son, ka zama jarumi mana ba komai ba ne hakan anyi ba iyaka, kuma abu ya zama tarihi.” Kafin ya ce wani abu Momy ta ce, “Kada ka ce haka mana Imran, tunda har an zo wannan matakin kar ka sare ka ci gaba da hakuri nayi maka alkawarin Mabaruka zata zama yanda kake sonta. Maganar hakuri ma bata taso ba a nan.”

Duk yanda za su kwantar masa da hankali dà ba shi kwarin gwiwa sun yi har ya ji kwarin gwiwar yasa a ranshi yanzu ma ya fara sonta da nacin zama tare da ita har abada.

TO MU SAI DAI MU CE MUJE ZUWA, MUGA WANNE IRIN ZAMAN ZAAYI?

A haka dai suka tsayar da maganar gobe za a kai masa matarsa, don ma rikicin da aka samu ai da ta dade a gidanta, Yanzu kuma tunda abu yazo karshe ba wani bata lokaci gobe a tattarata akai masa shi kenan, don ma tsiyar da tayi ai da yau za a kaita daga kotun direct.

Dare har ya fara, Momy ta shigo dakin ta dubeta fuska a daure ta ce, “Ki biyo ni dakina.” Daga haka tai ficewarta.

Ta tashi zaune tana turo baki cikin fushi da kumburi, sai da ta gama jan jiki sannan ta mike ta fice. Rafi’a ta bita da kallo.

Momyn na zaune bakin gado ta shigo ba tare da ta kalleta ba ta ce “Rufe kofar ki shigo.” Ta tura Kofar tare da Karasowa, taja ta zauna dosane bakin gadon ta sunkuyar da kai, can Kasan makoshi ta ce cikin fushi “Ga ni.”

Ta kalleta da kyau ta ce, “Ai na ganki maganar ce banga damar yi miki ba, yanda kike jin kin isa da kanki nima haka nake jin na isa da kaina, bare gidana ki ka same ni gidan mijina, Karkashin mijina wanda Karkashinsa nake sa ran samun Aljannata. Ko nan gidanku ne ke?”

Ta dago tana kallonta da sake nanata maganar a ranta, ta katseta “Da ke nake nan gidan ubanki ne?” Tayi jim sannan. ta ce “A’a gidanki ne ba gidanmu bane.”

Ta harareta sannan ta ce, “To kin san gidana ne kike min iko da isa kina nuna min tamkar gidan ubanki ne nan?”

_Ta dago. da sauri tana kallonta cike da mamaki, anya

,Momynta ce?

Ta ce, “Kalle ni mana! Na fada nan ba gidanku ba ne kara ki akai har ki ke zaune cikinsa kici abinci mai kyau wanda ki ka zaba, ki sa tufafi mai kyau da tsada irin wanda kikeso, duk kuma ba gumin Babanki ba, ko nasa ne?”Ta ce, “Mom…’

* Ta katseta “Bani amsakawai.”

Ta ce, “A’a ba nasa ba ne.” Ta ce, “Da kyau! Kin ga kenan a matsayin agola ki ke ba ‘yar gida ba ce kara ki aka yi.”

Maganganun sun mata zafi matuka, amman

kasancewar mai fada mata ba ta wasa ba ce ko musu bata isa tayi mata ba, dole taja tayi shiru zuciyarta tana mata zafin maganganun.

Momy ta ci gaba da cewa,

“Shi ne kin san hakan har kike iskancinki son ranki ba inda iskancinki ya tsaya sai ga masu gidan, duk halaccin da suka miki da gatan da suka miki, don kin samu ko? Ki dube ki ki gan ki, kin san matsayinku ba daya ba dasu bare shi makiyin naki, gabansa gaban mahaifinsa gaban yar uwarsa da shi ne mafi soyuwa a gurinsu sun gwammace su rasa komai a kan su rasa shi, amman ke shine abin wulakantawarki.

To dubi kanki ba ki fi shi komai ba, kyau, asali, ilimi da

kudi sai ma shi ya fiki duka hudun bare ki masa isgili, har yana bin ki shi yana sonki da kyautatawa amman ke kina nuna masa tsana saboda iskanci da rashin hankali har da kidahumanci.

Sam baki da godewa Allah a rayuwarki, ba ki san baiwa

Hmmm