da kyautar da ya miki ba, kin watsar. Shi wanda kike wa bashi da wani dalili da za ki nace masa face matsaloli dankare a gidansa.
Sannan ni kin manta wacece a gurinki, kin manta matsayinki kin fifita ra’ayinki a kan nawa, kin zabi farin. cikinki a kan nawa.
Kin fi son saurayi a kan uwarki, wacce ta sha fadi-tashi da ke har kawo girmanki. Ko irin sadaukarwar nan ne ba za ki iya ba saboda ni kawai don na ce ki aure shi ba don yana da illa ba, sai ma ingancinsa da na ganar miki da irin farin cikin da za ki samu a gidansa.
Saboda son da yake miki wanda ko rabin rabi bai kai wanda ki ke wa wancan ba, amma kin rufe idonki kina ta yin rashin mutunci ko a jikinki.
Tun farkon maganar nan nake fama da ke da lallashi da ban baki amma har a ka daura aurennan ba ki ji zaki iya min biyayya ba, sai rashin kunya da ba ni kunya gaban mutane.
Har yau ki ka fito fili a kotu ki ka yi magana son ranki, an kaiki asibiti ki ka baro ki ka zo tsakiyar titi ke za ki kashe kanki saboda an hada ki da mai yankar naman jikinki kullum, abin cutarwa gare ki.
Kina son ki kashe kanki ki mutu kafura, kije gaban Ubangijinki wuta ta kasance makomarki, tun a nan kin sabawa Mahaifiyarki kin sabawa Mahaliccinki, kin ki karbar zabin da ya miki har ki ka kashe kanki.
Ba ki ma tsaya a nan ba, ki ka dawo bakin titi ki ka dinga ihu kina kururuwa a cikin dubban mutane, saboda ki tozarta ni ki wulakanta ni.
Bayan an saka ki a mota da kyar kin dawo gida kina hauka da kashe-kashen abubuwa wanda ba ubanki ya sai min su ba, ni nasa kudina na saya miki don jin dadinki, ki ka kulle kanki ke za ki kashe kanki, har ta kai ga karshe aka balle kofar aka fito da ke.
Ta tsagaita tare da mikewa ta durkusa ta dauki dorinar dake gabanta ta nufota tana cewa.
“To sai kin fada min kwakkwaran dalilinki na aikata wadannan, da kuma dalilinki na tsanarsa. Yau na gaji da iskancinki don ubanki.”
Idanuwanta suka fito, tsoro ya bayyana a tare da ita saboda ganin wannan sharbebiyar bulalar, jikinta ya hau rawa ta fara ja da baya a tsorace. Ba ta fasa biyo ta ba har sai da suka dangane da bango, ba shiri taji saukar bulalar nan mai azabar zafi har cikin kwakwalwa. Ta fasa wani ihu mai gigitarwa, a rayuwarta wannan shi ne karo na farko da ta taba dukanta da bulala a rayuwarta.
Tamkar ba ita ta haifeta ba, ta dinga dukanta ba ji ba gani iya Karfinta, sai da tayi mata lilis duk ta fasa mata jiki, jini ya kwakkwanta, hatta motsi ta bari bulalar duk ta ciccire.
Ta dinga kuka kanta na masifar ciwo.
Ta kawo kunnenta ta matse tana cewa.
“To bari kiji in gaya miki, duk asarar da ki ka sa nayi yau na kayan da ki ka fasa sai kin biya su tas! Sannan duk abincin da ki ka ci da suturar da ki ka sa har karatun da ki ka yi sai kin biyawa ubansa kudinsa, tunda ba na ubanki ba ne.
Me za ki yi da kayan uban makiyinki? Sakarya marar mutunci.”
Ta dinga kuka tara bata hakuri, hankalinta ya tashi.
Tunda take bata tada gamin fushin mahaifiyarta ba har da dukanta.
Mabaruka yarinya ce ‘yar fari, kuma ‘yar auta. Ba ta san wani abin ba maganganun Maman suka bata tsoro, a ganinta da gaske take don haka ta rude taci gaba da bata hakuri kamar ranta.
Momyn ta ci gaba da cewa, “Auran an fasa, amma duk abin da na lissafo miki sai kin biya su kayansu.
Ba za ki more su a banza ba, ke a ki morarki. Sannan ni kaina daga yau ki sa a ranki ba ki da uwa, uba kadai ke gare ki. Za ki tattara komai naki ki koma gunsa can ku karata da kannanki ba ruwana da ke zan manta da ke a rayuwata, kije can ubanki ya aura miki Sulaiman din da ya fini.”
Ai fa hankalin Mabaruka ya Kara tashi, ta gigice ta dinga gurza kuka tana rokonta tayi hakuri.
Ta durkusa gabanta hannu biyu tana rokonta.
“Don Allah don girmansa da zatinsa kar kiyi fushi da ni, wallahi zan yi abin da kike so, na tuba wallahi zan aure shi. Ba ni da kowa sai ke, ba ni da gatan kowa sai ke, don Allah kar ki rabu da ni zan aure shin wallahi na yarda.”
Sam taki sauraronta don ta Kara tsoratata, daman tasan za ayi haka, tasan Mabaruka da tsoro sam bata san barazanaba. Duk don ta rikitata yasa ta ce ta tashi ta bata guri ta gama magana, tunda safe ta bar musu gidansu. Kuma. ta biya su kayansu. Mabaruka ta ki tashi tana kukan tare da bata hakuri.
Ta ce, “Ki tashi ki ba ni guri na gama magana, tunda dai ba kya sonsa zan nemo masa mata ya aura wacce ta fi ki, ke kuma kije can gidan Sulaiman dinki.”
Ta ce, “A’a Momy, na tuba wallahi na fasa na hakura zan zauna da shi, kiyi hakuri in zauna da ke in na rasa ki na rasa komaina duniya.”
Haka dai ta dinga magiyar nan, Karshe dai turata waje tayi ta datse kofarta tana dariya.
Ta dinga dukan Kofar tana rokonta, tsawon lokaci da ta gaji da jan gwiwa ta nufi dakinta tana gunjin kuka.
Rafi’atu ta tashi a rikice ta rikota.
“Lafiya Mabaruka, me ya faru?” Kuka ya ci karfinta, ta kasa fada mata.
Da kyar ta iya cewa “Na shiga uku! Rafi’a Momyna tayi fushi da ni. Ta ce ta rabu da ni in bar mata gidanta kuma sai na biya su komai da naci.
Wai in koma gidan Babana, na bani Rafia ba zan iya
Hmmm