WAYE ANGON BOOK 2 CHAPTER 15 BY MARYAM JAFAR KADUNA

hakuri da Momyna ba, ina son Mamana. Ki taimaka min Rafia.” Duk cikin kukan take fada, tanayi tana yarfa hannuwa. Dariya ta kusan Kwace wa Rafi’ar, saboda jin shirmen da take karanto mata, an linketa baibai kuma ta linku duk don a tsoratata.

Itama ta biye mata. Sai kawai ta hade rai ta ce, “Mun shiga uku Mabaruka! Ya zamu yi idan Momy ta cire hannunta a kanmu? Uwa fa ba abar wasa ba ce, ba abar yarwa bace.”Ta Kara rikicewa ta ce, “Wallahi zan matà duk abin da . take so, ina tsoron kar ta rabu da ni ita ce gatana.”Tayi jim sannan ta ce “Gaskiya ni kaina na tsorata. Mabaruka, kan namiji ki rabu da mahaifiyarki, wacce tun kafin ki zo duniya take dawainiya da ke?

Take tattalinki har zuwanki duniya, har yanzu ma rana daya ki ka yarda namiji ya raba ku kin shiga uku, zai iya wulakantaki ya juya ki son ransa.

Don ganin har ki ka iya rabuwa da ita don son da kike mishi, ki rasa inda za ki sa ranki kiji sanyi ko ma ya sakoki ki rasa in da za ki zauna ma. Yanzu ma to ina za ki samu kudin da za ki biya ta, tunda dai Sulaiman kike so? Kin ga sai a biya su sai kije ki auri Sulaiman din.” Ta fadi kan gado zaune jagwab tare da rafka tagumi hawaye na tsiyaya, ta kasa cewa komai.

Rafi’ar ta zauna tare da dafa kafadarta ta ce, “To me ki ka ce?” Ta juyo ta kalleta a natse tsawon dakiku.

Sannan ta share hawayen taja majina ta ce, “Shi kenan

na yarda.”

Ta fito da idanuwa “Kin yarda da me? Kin yarda ki auri

Sulaiman din ki rabu da Momyn?”

Ta kalleta ta ce, “A’a na yardazan zauna da Imran, zan je gidansa a kan na rabu da Mamana.”

Farin ciki ya sauka a zuciyar Rafia bata taba zaton haka daga wurinta ba.

Ta jinjinawa Momy da wannan hikima tata, kafin ta ce wani abu ta ce “Amman da sharadi.”

Tayi saurin kallonta “Wanne sharadin?”

Ta ce, “Ba zai taba samun farin ciki na rana daya ba tare da ni, da yin auransa da rashinsa daya ne, ba zai ga amfanin auransa ba. *A haka suka kwana wannan ranar, tun kuwa da asuba ta

tafi dakin Momyn a marairaice ta durkusa gabanta inda ta sallame sallah.

Ta ce, “Don Allah Momy ki janye maganarki, wallahi na yarda na amince da auransa, ina sonki bana son rabuwa da ke.”

Matuka taji dadin hakan, amman a fili sai ta ce, “Ni na

riga na gama maganata, ba neman amincewarki nake ba, hukunci ne na riga na yanke. .

Lokaci ya Kure miki, lokacin da nake son amincewar

taki ai wulakanta ni ki kayi.

Imran dai ba zai rasa matar aure ba kusa-kusa ba da nisa Tayi dif! Tana jin nauyin hakan. Ta sake cewa “Ko ba zaki je ba kin fasa?”

•Ta girgiza kai “A’a.” Ta fada da sauri, sannan Momy ta’се,To mike kije.”Ta mike jiki a mace, zuciyarta cike da takaicin hakan.

• Kan dole ta doshi dakin nasa.

Ta shiga yin knocking. Shi kuwa ya koma bacci kenan ya dauke shi, ya ji dukan kofar.

Daga kwancen ya ce “Waye?” Ta ce, “Ni ce.” Ya yi,

•matukar mamakin jin muryarta, amman ya sake cewa “Kece wa?”Ta zumburo baki tare da hararar kofar tamkar shine a tsaye a gun. Ta ce cikin Rufula “Ni ce Mabaruka.” Ya yi murmushi tare da dirowa daga gadon ya tunkarota. Yana bude kofar ta wuto ciki da sauri, ya maida ya kulle yana mamakin zuwanta da sanyin safiyar nan. Ya zauna bakin gado yana kallonta, ya. ce “Lafiya.

Mabaruka na ganki yanzu?”

Tayi shira kanta a kasa, sai kuma ta ce “Daman Momy…” sai kuma ta fasa cewa daga Momyn tuna yanda suka yi da ita.

Tayi cak! Tana tunanin ta ya za ta faro maganar?

Ya ce, “Ina jin ki, menene?” Ta dan dago ta kalle shi,

Kiftawar ido ta kuma dauke kanta ta ce.

“Daman nazo in fada maka na amince.” Ya ce “Kin amince da me kenan?”

Haushi yazo mata wuya, don me yake son kureta? Ta dai daure da kyar ta ce “Da aurenka.”

,Abin yazo masa kamar daga sama, ya aka yi haka to? Ya dubeta ya ce, “Me yasa ki ka amince? Ko an tursasa miki ne?”Tayi saurin cewa, “A’a; don kaina ne kawai.”

Sam bai yarda ba, duk yanda aka yi aikin Momyn ne,

Hmmm