YAKANA BOOK 1 CHAPTER 1 BY SUMAYYAH ABDULKADIR
Asma’ul Husna
YAKANAH!-
A
gogon ‘alarm’ da ke gefen makeken gadon ya buga karfe shidda dai-dai na safe, Dr. Hadizah wadda ke kwance a gadon doguwa ce ba can ba, irin tsayin nan gare ta mai tsari da ban sha’awa. Tana sanye cikin rigar barci mai santsi fara sol. Ta yi mika a hankali tare da koro addu’ar (Alhamdulillahil lazee ahyana, ba’ada ma amatana wa ilaihin nushour). Ta mika hannu side din da maigidanta ke kwance, wayam! Tayi hanzarin mikewa daga kwanciyar don a zatonta, ta makara. Daga can kitchen ta jiyo motsin mai aikinsu Goggo Alti tana karakaina da kwanuka. Tana shirin mikewa ta ji motsin maigidanta Sulayman a
shower, don haka ta yi ajiyar zuciya mai sanyi, a kalla ko ta makara kadan ne. Ita ma ta fada bandakin don ta taimaka mishi wajen wanka.
Suka fito kowane daure da towell, shi iya kugun shi ita iya cinyoyin ta. Jiki ne da ita lukui-lukui kamar atafa. Jiki ne da shi na MANYA, kuma kasaitattun maza, wadanda suka dama, suka kutsa cikin ilimummuka daban-daban. Yana da duhu, amma duhun mazan Marocco ne. Dogo ne sosai ma’abocin karfi da kyawun sura ta ko’ina. Idan baka san asalin shi ba, za ka yi tsammanin ya fito ne daga Sirreleone, amma a zahiri Bakatsine ne dan asalin garin Bakori. Wadda Bakorin ta bi sunan shi, ta boye Sulayman-Sulayman din, ake kiran shi Dr. Bakori.
Ta bude wardrove ta dauko mishi bakaken Spanish-Suit mai hade da farin tie mai santsi. Ita kuma ta fiddo wata atamfa super shudiya mai ratsin rowan hoda da_ hasken – sararin samaniya, riga, zane da kallabin su, ta
dora da farar rigar su ta likitoci. Tuni ta fito a Dr. Hadizarta. Tana tsuke mishi tie ya ja zankalelen dogon karan hancinta in appreciation din (cike da jin dadin) irin kulawar da take mishi. Yace
“Allah ya bar min ke Dr. D.Z”. Ta ce “‘…Ya bar min kai nima, likitan zuciyata…..”.. Ta manna mishi kyakkyawar sumba a kirji, kasancewar ya kere ta a tsaho, ita iya kirjin shi ce. Ta dauko tashi rigar likitocin ta zagaya ta bayan shi ta rufa mishi, ya zura hannun shi kana a hankali ya janyo ta ya rungume ta. Sun dau tsawon lokaci a hakan, suna sakin ajiyar zuciya mai sanyi cike da matsananciyar kauna wadda biro ba zai iya rubutawa ba, kamin su saki juna ba don sun so ba, sai don tunanin dimbin al’umma masu larura da suka yi sammako suke jiran su.
Sai da suka gama kammalawa tsaf sannan suka fito, tana rike da gilashin idonta a hannu, ya yin da shi yake rike
da jakarta da brief case din shi. Kai tsaye dakin yaransu suka nufa, inda suka tarar tuni Alti ta shirya su tsaf, kasancewar yau garin an tashi da lullumin sanyi mai tsanani ya sanya ta sanya musu rigar sanyi mai kauri a ciki, ta sanya musu fararen socks ta rufe musu kafafu cikin farin cambas. Yaran su biyu ne mace da namiji, namijin dan kimanin shekaru hudu, macen ‘yar kimanin shekaru biyu da kadan. Dole in ka gansu sai ka sake marmarin kallon su, sun kuma baka sha’awa.
Munib sak Babansa, yayin da Muniba komi nata na Dr, Hadiza ne. To ba Mamin ba, ba Daddyn ba, kowanne ji yake da kyau tamkar shi ya yi kansa. Akwai shakuwa, fahimta da soyayya mai yawa a tsakanin wannan family. Hadiza ta rage tsawo ta russuna ta rungume Muniba,
“Gud morning my dear……. “Morning Mummyy….”. Munib ma ya ce
“Gud morning Daddy…..”.
Ya amsa da
“Morning my Munib, an tashi lafiya?” Su dukka suka nufi tebir domin yin kalaci.
Goggo Allti ta fito daga kitchen za ta wuce bangaren ta, daga Hadiza har Sulayman suka gaishe ta, kamin ita ta gaida su. Wannan dabi’arsu ce da ke karawa dattijuwar jin dadin zama dasu, saboda yadda suke ba ta girma kamar ba a karkashin su take ci ba. Hakan ne yake kara mata himmar kula musu da yaransu saboda Allah.
Hadiza ta bude ma’adanan abincin ta soma serbing kowannen su da abinda yake so. Sinasir ne da miyar ganye, sai farfesun kayan ciki, sai kuma soyayyen dankali da kwai domin su Munib da bazasu iya cin mai nauyin ba. Ga al’adarsu sun fi cin abinci mai nauyi da safe, don ba za su kara ci ba sai dare in sun dawo aiki, sai ‘yan ciye-ciye da ba a rasa ba a office.
Hankalin Dr. Sulaiman yana kan ‘ya’yan shi, sai da ya tabbatar sun koshi sannan ya ci nasa. Zuwa bakwai da rabi sun gama komai sun fito, suka yiwa Goggo Alti sallama suka wuce rumfar adana motocin su.
Akwai motoci har guda uku, daya ta Sulaiman, daya ta Hadiza, daya ta amfanin gida. Sai da suka aje yaran a makarantar su (Maitama Sule) da ke dab da asibitin da suke, wato (AKTH) sannan suka karasa cikin asibiti, kowanne ya nufi bangaren sa.
Dr. Sulaiman-Sulaiman Bakori shi ne consultant na (cardiology), yayin da Dr. Hadiza Ja’afar Mai-Yadi take likitar mata wato (gynaec) a labour ward take. Sai da ya fara sauke ta sannan ya wuce ofishinsa, ya soma attending dimbin cases din da ke gabansa.
Karfe sha biyu na rana ya zame ya je ya debo yara ya kai ma Goggo Allti, sannan ya dawo. Wannan shi ne tsarin
rayuwar su a kullum. AK
S
hekarun su biyar kenan da aure, amma har zuwa inda yau ke motsi, babu abinda ya canza na daga soyayyar da suke yiwa juna, sai ma abin da ya karu.
Hadiza dalibar shi ce irin yaran likitocin nan da ake koyarwa a (teaching hospital). Ya fahimce ta yarinya ce mai matukar kwazo a tsakanin tsararrakin ta. Wani abin mamaki da ya fara bincike a kanta ‘yar talakawa ce likis, amma iyayenta sun tsaya tsayin daka wajen daukar nauyin karatun ta, duk da tsadar shi kuwa, da dukkan iyawarsu.
Soyayya ce mai tsabta irin ta wadanda
suka wadata da ilimi suka gudanar kamin aure. Ga Hadizah ba karamar sa’a ba ce, kuma ba karamin abin alfahari bane samun mutun kaman Sulayman (as a husband). To haka shi ma. Hadiza ta tara duk wasu kualities da yake nema ga diya mace, ga dai kyau ga kyan hali, ga addini da kyakkyawar zuciya, sannan uwa uba ta samu ingantacciyar tarbiyya daga_ iyayen kwarai.
Iyayenta suna nan a_ unguwar Karkasara dake cikin birnin Kano, sana’ar mahaifinta shi ne yadiddika yake sayarwa, yana da shago a nan kantin Kwari.
Hadiza ita ce ta biyu a cikin ‘ya’yan gidansu, akwai Yayanta Mukhtar wanda ke aiki da (Zenith Bank) a Kaduna, kusan da tallafin shi ne Hadiza ta samu ta kammala karatun ta.
Duk da haka shi ma mahaifinsu a tsaye yake a kan karatun su, don yaga amfanin da karatun yayiwa Mukhtar. Sai kanwar ta Fati, budurwa ce ‘yar ki
manin shekaru sha bakwai, a bana ne ta kammala karatun sakandire. Sai Hamza da Yusuf, da dan autan su Abdulyassar.
Duk cikin kannenta Hadiza ta fi son Fati, wata irin yarinya ce mai sanyin hali, sanyin kyau da sassanyar zuciya. Akwai wata irin shakuwa ta musamman tsakanin Hadiza da ‘yar uwarta Fati. Jininsu ya hadu sosai ta yadda Hadiza ba ta iya shawara da kowa kan al’amuranta kamar Fati saboda hankalin ta.
Fati yarinya ce mai tsananin son addini da nutsuwa, ba ta da rawar kai ko kadan irin na ‘yammatan zamanin nan, komi nata cikin hankali da nutsuwa yake. Ita da Hadiza kamar an tsaga kara, sai dai Hadiza fara ce sol, yayin da Fati ta kasance wankan tarwada. Amma hatta yanayin tafiyar su da murmushin su iri daya ne.
Ss
ulayman Bakori, mutumin — garin Bakori ne ta jihar Katsina, daga kallo na farko mawuyaci ne ka bambance daga kabilar da ya fito, wani irin mutum ma’abocin cikar zati da kamala da duk wani nau’in daidaito na rayuwa, ga dimbin ilimi a cikin fannonin kiwon lafiya daban-daban. Ya ci sunan mahaifinshi ne don haka a gidan su ake kiran shi mai sunan Malam. Mahaifin shi Malam Sulaiman, Malami ne mai karantarwa, yana baiwa magidanta anguwar su karatun buzu. Duk wani da ya kwana ya tashi a garin Bakori ya san Malam Sulaiman Mai-Gafaka. Mutum ne da al’ummarsa ke matukar ganin girman sa, kuma ya yi fice a garin Bakori baki daya saboda ilimin da Allah ya ba shi, kowa yana daraja shi.
Shi ne da na biyu a gidansu, yayar shi Jummai ta rasu wajen haihuwar fari, sai kannen shi Ramatu, Saude da Ruma, duk suna gidan aure. Sai
Khalid wanda ke karatun sakandire a halin yanzu.
Sulaiman ya yi dukkan karatun shi ne da taimakon gwamnati da mahaifiyar shi Inna Halima, wadda duk lokacin da hidimar karatun ta tashi take fitar da kadararta ta siyar ta yi masa. In dan ta Malam ne sakandire ma kawai ta isa. Burinsa Sulayman ya zauna a gida ya tallafa mishi kasuwancin shi na fata, ya yi aure ya haifa mishi jikoki shi kuma zai yi masa komai.
Amma Sulaiman ya ki, ya dage ga son cimma burinsa na son zama likita. Ba abin da yake so a rayuwar shi irin yau ace ya zama likita yana yiwa mutane allura.
Irin yaran nan ne gifted tun suna kanana, wato ‘yan baiwa. Wata irin kwakwalwa gare shi da ba duk mutane Allah yake baiwa ba, duk inda yayi karatu malaman shi sai sun san shi, sun kuma ja shi a jiki, sun so shi saboda hazakar shi.
Ya yi gaba dayan karatun shi daga
jami’ar Najeriya (NSUKKA). Bayan ya kammala MBBS din shi ya yi nasarar samun_ scholarship zuwa jami’ar (Manchester) inda ya yi specializing a kan zuciya da duk abin da ya shafe ta. Bayan kammalawar shi da dawowar shi ya soma aiki da federal, hakan ne ya sa ake yawan canza mishi wajen aiki.
Ya fara ne da aiki a babbn asibitin koyarwa na Ibadan, daga baya suka mai da shi ABU Teaching Hospital. Nan din bai dade ba suka dawo da shi nan AKTH na Kano, inda Allah ya hada shi da Hadizah.
Haduwar su haduwa ce _ special kuma haduwa ba ta dadi ba. Yana tare da patient da ya yiwa aiki satin da ya wuce, Hadizah Ja’afar, da wasu abokan karatun ta suka shigo domin daukar lacca. Ko kallon su bai yi ba, balle ya tantance kamannin su, kasancewar Allah bai dora mishi lalurar yiwa mata kallon kurilla ba. Tsakanin
shi da kowacce diya mace, kallo daya ne, da kau da kai.
Suka samu_ kujeru. suka zauna, kowacce da jotter din ta da biro a hannu. Yana ta yi musu bayani cikin lafiyayyen turancinshi na _ Birtaniya mara surki, wani zubin ya yiwa mara lafiyar tambaya ta ba shi amsa.
Wata amsa da patient din ta bayar ta sanya su murmushi dukkanin su (ban da Hadiza), cikin kalaman ta za ka fahimci kwakwalwarta ta tabu sakamakon bacin zuciya da damuwa.
Ta ce,
“Likita nifa ‘yar sarauta ce ba mara lafiya ba!”.
(Wannan ne ya sanya su yin murmushi). Ya ce,
“Wacce sarauta gare ki don mu fara girmama ki?”
Gaba daya daliban suka yi dariya don yadda yake biye ma shirmen matar dole ya baka dariya. Ta ce,
“Sarautar Kano gare ni”.
Yace, “Wacce ke nan?” Ta ce,
“Nice ‘yar ruwatan Kano”.
Gaba daya suka yi murmushi, wannan karon ma ban da Hadizah, wadda a lokacin hankalinta baya tare dasu, yana ga halin da ta baro Mamansu a ciki na rashin lafiya mai tsanani.
Ba zato Dr. Bakori ya jefo tambaya, “Mene ne delusion?” Ya kuma nuna Hadiza da ya lura hankalinta ba ya tare da shi matsayin wadda za ta amsa mishi tambayar shi.
Ya yi mata magana ya kai sau uku ba ta san yana yi ba. Hadiza ta damu da Mamanta sosai, kasancewar ta jarumar Uwa mai hidimtawa rayuwar su, tun daga yarinta har a girman su. Yaya, (Sa’adatu), ba ta huta da dawainiyar su ba. Don haka jin ciwon ta suke tamkar a gangar jikin su.
Duka kawayen ta babu wadda ta zungure ta, don sun san da ta ji za ta ba da amsa a yabe ta kamar yadda manyan likitoci suke yabon ta a kullum saboda kokarin ta.
Ya buga tebir din gaban shi da karfi
har ta razana, ya nuna mata hanyar waje ya ce, ‘You can go out….. in kin gama tunanin kya dawo”.
Ta mike sumi-sumi ta fita, murna gun su Hafsat kamar su yi yaya, yau Allah ya nuna musu likitan da ya yi maganin ‘yar gaban goshin likitoci. Ya yi (referring patient) din zuwa psychiatric, su kuma ya sallame su.
Ya koma gida a wannan ranar, bayan ya gama duk abubuwan da ya saba na al’adar rayuwar shi kamin ya kwanta, kamar shan fruit da edcercise saboda shi da daddare yake edcercise din sa kasancewar da safe ba shi da lokaci.
Amma abin mamaki ya kasa runtsa idonsa, tunanin fuskar dalibar da ya kora a yau ke gilma mishi, ya hana shi sakat, ya hana shi sukuni, ya yi duk kokarin da zai yi don ya samu barci amma hakan ya faskara. Ya ko kasa runtsa idon sa, wani bakon al’amari ne mai takura zuciya da bai taba tsintar
kansa a ciki ba.
Hadiza ba wata muguwar kyakkyawa ba ce cancan, tana da kyau dai-dai nata, sai dai kuma yarinya ce mai aji na karshe. Fuskarta zagayayya mai dauke da dara-daran fararen idanu masu sheki da walainiya, hancinta kamar an sanya ruler an ja shi an daidaita shi a kan (obal -shaped) fuskarta. Bakinta dan karami kamar cokali baya shige ba. A kan tsinin hancinta tawwadar Allah ce da aka haife ta da ita, fara ce sol! Irin farin nan da wadataccen ilimin boko ke taimakawa wajen zahharar sa.
Bai taba ganin yarinyar da (lab-coat) ta yi ma kyau kamar Hadizah ba. Ba Sai ya tsaya wahalar da kanshi wajen tunanin abin da ke faruwa da shi ba, ya tabbata son Hadiza ne ke ratsa kowanne sako a jikinsa.
Abin haushin ko sunan ta bai sani ba, zuciya ta kwashe shi ya yi abin da ya zo ya dame shi. Bai taba tsintar kansa a kwatankwacin irin wannan yanayin