YAKANA BOOK 1 CHAPTER 2 BY SUMAYYAH ABDULKADIR

 YAKANA BOOK 1 CHAPTER 2 BY SUMAYYAH ABDULKADIR

ba, a kan diya mace. 

Sai dai shi a ce ana son sa yana hura hanci, kada hakan ya janyo raini, baya fatan hakan ya kasance sakayya ce Allah ya yiwa dimbin matan da ke binsa agindi-agindi don ya so su yana yakice su. Tare da yi musu wulakancin da ko a hanya suka ganshi bazasu yi fatan ace sun san shi ba. 

Ya fahimci dalibar (obstetric and gynaecology) ce, daga (ID Card) din ta. Yadda ya ga rana haka ya ga dare, ko na second daya bai runtsa ba. So da kaunar student (daliba) Hadiza na narkar mai da zuciya. 

Abin kamar sihiri, daga ranar bai kara ganin Hadiza ba, bai kuma san ya zai yi ya tambaya ba, tunda ko sunanta bai sani ba. A matsayinsa na babban likita, mai juya sauran likitocin bangaren su, ba karamin zub da kima bane a ji shi yana tambayar wata yarinya cikin masu daukar darasi a wurin su. Duk da haka bai fidda rai ba, yana da yakinin watarana Allah zai 

sake hada shi da yarinyar ko da a mafarki ne. 

Ita kuwa Hadiza ba ta dawo TH ba sai bayan sati uku, tana gida tana Jinyar Maman su da suke kira Yaya, da ke fama da ciwon hanta. Tana ganin likita a Murtala, har suka kwantar da ita sati guda. 

Kawarta Surayya ke daukar musu Jacca tana kuma sanar da ita duk abin da ke faruwa ta waya. Ranar monday Maman su ta ji sauki sosai, don haka ta shirya ta dawo. 

Ba zato babu tsammanin shi, yana ganawa da wata patient din suka shigo ita da Surayyah, ya zare gilashin idonsa a hankali, ya saki wata sassanyar ajiyar zuciya irin ta wanda ke neman abu, ya wahala ya dade, kamin ya samu. Duk hankalin sa da attention din sa sai ya koma kanta, ya manta abin da ke gabansa, ya samu kansa da rudewa. Abin da bai taba yi ba a kan diya mace, akwai wani sassanyan 

kallo cikin kwayar idon Hadizah, da ba duk mata Allah ya mallakawa ba. Suka gaishe shi cike da girmamawa, sannan suka samu kujeru suka zauna. Hadiza dai a darare take, ko kanta ba ta dago ba. Daga gefe-gefen idon ta take satar kallon likitan da ya hargitsa mata tunani ‘yan kwanakin nan. Tunda ya kore ta ba ta kara samun nutsuwar zuciyarta ba, har zuwa yau da ta sake tozali da shi a karo na biyu. 

Ta tambayi kanta, shin ko mutane nawa ne a duniya irin Dr. Bakori? Yana da wasu ilhamomi na musamman a tare da shi da ba ta taba ganin su a da namiji ba, ko yadda yake duban mutane daban ne da na sauran likitocin da ta sani. Tsarin maganar sa cikin seriousness shi ne babban abinda ke burge ta da shi, ga kamun kai da sanin mutuncin kai, hadi da rashin son wasa ta ko’ina. Dr. Sulayman Bakori, ya shiga cikin rukunin wasu mutane da take ganin matukar kima da mutuncin su, sannan kuma ya bi ya 

manne a zuciyarta, ta yadda dai-dai da minti daya ta kasa manta shi cikin satittikan da ta yi tana jinyar Mamanta. 

A gurguje ya basu laccar ya kuma sallami mara lafiyar da suke tare da ita. Suka mike da nufin su tafi, baya fatan wannan damar da kubuce masa, don haka bai yi kwauron baki ba, ya yi ta maza (in ji mata) ya ce da Hadiza cikin wata irin lallausar murya da ya kasa yarda cewa tashi ce. 

“Wato fushi kika yi? Kika daina halartar karatun ki sabida na kore ki a kan kin yi min laifi?” 

Ta yi ajiyar zuciya a hankali ba tare da ta juyo ba, ta ce, 

“A haba Doctor! Wane ni in yi fushi? Mum dina aka kwantar a_ hospital kuma ni nake jinyar ta sai jiya aka sallame mu”. 

Ya nuna tausayi tsantsa a_ kan kyakkyawar fuskarsa, ya ce, “Ayya! 

Ta juyo ta yi mishi murmushi, suka yi 

ido hudu da dan Inna Halima, wani chemistry yayi aiki cikin ‘yan dakikai, ya kimsa wani al’amari mai GIRMA a zuciyoyinsu mai wuyar bayyanawa. Gwiwoyinta suka yi sanyi, zuciyarta ta karye, duk wata soyayya da Allah ya halitta a zuciyarta ta hadu ta tattare waje daya. To haka shi ma. Jikin shi ya ba shi wannan ita ce matar auren shi, wadda za ta samar mishi da ‘ya’yan da zai yi alfaharin fitowar su daga tsatson ta. Ya ce 

“A bani address zan zo in duba Mamar mu”. 

Daga ita har Surayyah sai suka yi mutuwar tsaye, domin abune da ko da wasa basu taba kawowa ba. Kowa ya san shi da halin ko in kula da yake nunawa a kan mata, wanda ke burge kowa. Don haka sun sha mamaki. 

Ita Hadiza ta kasa magana, sai Surayyah ce ta rairayo mishi adireshin Hadiza. Ya ce, 

“Idan na zo wa zan ce?” 

Ta ce, 

“Hadizah!””. 

Ya ce, 

“Hadizahh, am I welcome?” 

Ta yi murmushi ta ce, ” 

You are welcome!!”. 

Tun daga ranar kakkarfar soyayya ta kullu, kullum suna tare, a gida ne ko a ofis. Abin ya soma bayyana ga abokan aikin shi da abokan karatun ta, da manyan likitoci mata da ke yi mishi asirtacciyar soyayya. 

Wannan ya janyo ma Hadiza hassada karara a wajen mafi yawan abokan karatun ta, to ita ma sai ta share su, saboda ta san Surayyah kadai ke kaunar ta saboda Allah. 

uren su, wani abu ne da ya bar dimbin tarihi a asibitin Malam Aminu Kano, domin mafi akasarin likitocin cardiology kabilu da Hausawa sun halarta. Ba a taba ganin daurin auren da ya tara ‘yan boko tsantsa, likitoci ziryan a unguwar Karkasara irin na Hadiza ba. Suka tare a gidan Sulaiman da ke cikin asibiti, cikin wata irin soyayya mai wuyar fassarawa. 

Aure ne auren soyayya mai tsabta, wanda babu ha’inci, yaudara ko karya a cikin ta. Ya sha mamakin samun Hadizah a cikakkiyar mace (birgin) musamman in aka yi la’akari da matakin karatun ta. Ba gaskiya bane 

zargin da ake yiwa ‘yammatan (medicine), kawai dan iska dan iskan kansa ne, amma da yawa abin da ya kai su shi ne a gabansu. 

Cikin shekaru uku da auren su ta yi mishi tukuicin kauna da Munib da Muniba, wannan ya kara sayowa Hadiza matsiyaciyar kauna a zuciyar Sulaiman. Daga baya ne da ya kammala ginin da yake yi a Janbulo suka koma, daga nan ne likitocin aka rufe bakin mahaifa ruf, aka _ fuskanci cigaba. Hadiza ta kare karatun ta cikin nasara, da taimakon mijinta. Ita ce (oberall) a year din su. Da gudu aka rike ta a (labour room) wato dakin haihuwa. Sannan ba ta tsaya a nan ba, ta ci gaba da halartar kwasai-kwasai a akan bangaren ta. Har kawo matakin da ta ke kai a yau, na cikakkiyar likitar mata. 

2K 2K OK 

Karfe hudu na yammacin ranar litinin 

aiki ya tsagaitawa Dr. Hadiza, babu yawan marasa lafiya, don haka ta soma hada ‘yan komatsanta don barin asibitin. 

Tun safe yau kanta ke damun ta da ciwo, gida kawai take so ta Je ta huta. Amma dole sai ta fara ganin Sulaiman tukunna, akwai wasu kudi da take son karba a wajen sa za ta biya ta kai ma Fati tayi (registration). 

Ta bude motar ta kenan ta zuba shirgin hannun ta, wata Nurse ta karaso da gudu tana haki tana kiran ta, “Dr. Hadizah!” 

Ta juya tana kallon ta har ta karaso. ” leeees Don Allah ki taimaka, wata ce aka kawo yanzun nan da alama ba za ta iya haihuwa da kanta ba, sai bleeding (zubar jini) take”. 

Ta kama kanta dake sarawa ta ce, “Lokacin tashina ya yi, yanzu Dr. Surayyah za ta Zo……… ” 

Nurse din ta katse ta, 

“Ki ceci rai kamar yadda kika saba, sakayyar ki na wajen Allah! Daga 

matar har Babyn suna cikin hadari, ga shi babu likita ko daya duk sun shiga meeting. Sannan Surayyah babu wanda ya san lokacin da za ta karaso”. Hadizah mai sanyin zuciya, matar ta kashe mata gwiwa da tausasan kalamanta. A take ta manta da ciwon kanta, ta rufe motar ta koma gun mai haihuwa. 

Wannan halayyar ta ce da ta sha banbam da ta sauran likitocin labour room da kowa ke kuka dasu. Zuciyarta mai laushi ce, shi ya sa daga likitocin har Nurses zuwa labourers ke son ta, suke jin dadin aiki da ita. Hadiza is simple, komi nata a saukake yake. 

Da gaske ne matar ba za ta iya haihuwa ba. Ta kai matuka wajen galabaita, ta soma ba ta dukkan taimakon da ya dace. Tana cikin aikin Dr. Surayyah ta iso, suka tsaya a kan matar nan. 

Cikin dan lokaci sun yi nasarar fitar da jaririn amma ba rai. To alhamdulillahi an samu uwar. Tana zare safar han

nunta ta ce da Surayyah, “Ko da ban zo gobe ba, don Allah ki kular min da matar nan, haka kawai nake jin tausayin ta, dube ta yarinya karama, ga dukkan alamu ba ta isa auren ba suka yi mata. Allah ne ya taimake ta sun zo asibiti da wuri, da babu mamaki BBF ya same ta”. 

Surayyah ta ce, “Matsalar mutanen karkararmu kenan, ban san yaushe za su hankalta ba. A kullum fadakarwa ake a radio da talabijin, amma kamar ana kara zuga su. Allah ya kyauta. Balle ma me zai hana ki zuwa idan da rai da lafiya?” 

Ta girgiza kai ta yi dan tsaki, ta ce, “Bana jin dadi ne”. 

Surayyah ta ce, 

“To Allah ya kawo sauki, a shafa min kan Munib”: 

Da haka suka yi sallama ta fita. 

Da yake yau kowa a motar shi ya zo, wato itada Sulaiman, kasancewar lokutan ayyukan nasu sun banbanta. 

Akwai tazara sosai daga inda ta yi parking zuwa cardiology. Tana tukin tana duba agogon ‘gucci’ da ke daure a damtsen hannun ta na hagu. Yau Dr. Sulaiman aikin kwana gare shi, kudin Fati sun tsaya mata a rai, ga shi jakarta (is empty). Sannan is too late ta je banki ta fitar da kudi (lokacin ba ATM). 

Ba al’adar ta ba ce tambayar Sulaiman kudi ba, saboda duk wata yana cika mata account ba tare da la’akari da albashin ta ba. Ita da kudin ta sai dai ta yiwa iyayen ta da ‘yan uwanta hidima, amma duk wani nauyin rayuwar ta Sulaiman ya dauke shi. 

Sau tari, ta kan ji kawayen ta da ba suyi aure ba irin su Dr. Surayyah, na tattaunawa a kan abinda ya hana su yin aure, su kan ce da ka yi aure shi ke nan ka shiga matsalar da namiji (wulakanci, rashin tsayawa ga mace daya, rowa da sauran su). 

To ita dai yau shekaru biyar cif, ba ta ga ta inda nata da namijin ya kuskuro 

ta ba; 

Matakin iliminsa bai sa shi ya zamo cikin kowanne irin aikin ashsha ba. Bai sa shi ya zamo mai tauye mata hakki ba, bai sa shi ya zamo mai girman kai a gare ta ba. Kullum tambayar shi, “No problem Haddizah (babu matsala Hadiza)?” 

Ta kan tambayi kanta, yadda neman mata ya zamo ado ga akasarin mazan wannan zamanin, masu matakin rayuwa irin nashi, mai ya sa ban da Sulaiman? Duk da kasancewar shi mutun mai tsananin bukatar diya mace. Ta yadda duk juriyar ta wani lokacin har ta kan nuna gazawar ta. Ta taba tambayar shi cewar, “Don me ba zai kara aure ba?” 

Sai ya kankame ta. Ya ce, 

“Haddizah you are okey for me, in dai ba za ki yi min rowar, ni’imtaccen jikin ki ba……… ” Ta ce, 

“Doctor gani nake ina kwarar ka, you seem not o.k…….. ” 

A hanzarce ya ce, 

“Ni na gaya miki?” 

Ta girgiza kai. Ya ce, 

“To kar ki kara yi min wannan zancen, silly girl kawai”. 

Ta yi murmushi, da tunanin ta ya zo nan. Dai-dai lokacin da ta iso cardiology, ta yi parking a inda aka tanada don adana motoci ta fito rike da jakarta. A nutse ta karasa (male ward) inda office din Sulaiman yake, ta tura kofar bayan ta murda tare da sallama. 

Da alama aiki ya kacame masa, yana ta rubutu cikin file-file dake gabansa, ya daga kai yana duban ta duba na so da kauna, kuma na nutsuwa kamar yana son karanto ainihin damuwar da ke fuskarta. 

Ya mike ya baro kujerar sa ya zauna a masangalin kujerar da ta zauna, ya zare mata gilashi, ya ce, “Ya ya ne Dr. Hadiza, you look edhausted!” (Da alama kin gaji likis). 

Ta lumshe zara-zaran gashin idonta ta 

ce, “Migraine ke damuna (ciwon kan barin kai guda)”. 

Ya kai lallausar tafin hannun shi goshinta, har sai da ta ji wani shock kamar yau ya fara taba ta. Ta yi saurin ture hannun sa, za ta yi magan Dr. AbdulJahi ya turo kofar ya shigo, da sauri ya koma yana “edcuse me plzzz……. {” Duk suka yi murmushi. 

Ya ce, 

“Kin sha magani?” 

Ta girgiza kai, 

“Ina so in je Karkasara ne”. 

“Amma lafiya na gaba da komai ko?’ Ta ce, 

“Zan biya emergency in amsa kamin in wuce”. 

Ya kai hannu cikin rigarta wai zai ji temperature na jikin, ta yi saurin rike hannun ta ce, “Haba Sulaiman…….” Shi ma ya ce, 

“Haba Hadizahbh….! Ni kadai zan kwana fa, babu dumin jikin ki Hadizah…..?” 

Ta yi murmushi ta rusunar da kwayar 

idon ta cikin jin kunyar furucinsa, domin dai ita mace ce mai tsananin kamun kai a gaban mijinta da jin kunyar sa, kai ka ce basu haihu tare ba. Yace 

“Ke kwanta in duba ki, ban yarda dake ba, har yanzu ba ki cire wannan loop din ba”. Ya soma laluben ta. Ta rike hannun shi ta ce, “Wallahi na cire”. Ya ce, “To ko ke fa? 

“Ya’ya nake so Haddizah, ki yi ta cika min gida dasu. Bani da harshen da zai iya bayyana hakikanin son da nake miki, you are my life Hadizah….., kada Allah ya rabamu……. ” Ya shiga nuna mata son, practically, (a aikace) irin yadda bai taba yi ba. Murmushi tayi. Ta ce, “Sulaiman naka son ka sani, amma baka san nawa ba. 

Sannan ban san yaya zan yi in fassara ba. All I can say (abinda zan iya cewa shine) ina son ka Sulaiman son da nake yiwa raina……’ 

Ya kai hannu ya toshe mata baki, wayar shi ta yi kara ya juya yana amsa 

call din amma bai saki hannunta ba. Ya gama ya kashe ya maida aljihun shi, yana yi mata wani sassanyan kallo ya ce, 

“Ki yi min alfarma ki taya ni kwana ko hira ce ki dinga yi min ina aikin”. Ta ce, “Ka yi min afuwa Baban Munib, Fati zan kai ma kudi za ta yi registration gobe”. 

Da sauri Ya ce, 

“Registration din Fati ya fini?” 

Ta bude baki ta rufe da hannun ta, ta kasa cewa komai. Ya tsare ta da sedy eyes din sa, masu kassara ta, ba shiri ta sunkuyar da kai, don ba ta iya jure kallon idanuwan nan na Sulaiman din ta, masu rikirkita kowacce lafiyayyar diya mace, balle ita matarshi ta sunnah, data fi kowa sanin sirrinsa na zahiri da badini. A raunane ta ce, 

“Ban so ka yi min wannan fahimtar ba”. 

“Sai wacce kike so in miki?” 

“Irin wadda ka saba, understandable (ta fahimta)”. 

Ya yi murmushi ya mike daga kujerar ya koma mazaunin shi, duk ya shafa mata mayataccen kamshinsa na _ turaren ‘Chris Adams’. Nutsuwar matarshi da haibarta na burge shi, magana take cikin nutsuwa da haiba, kamar ba daga bakinta furucin ke fitowa ba, dauke da matsananciyar kauna a cikin kwayar idanun ta. Son ta da kaunar ta na kara kwarara a zuciyarsa, ya rasa inda zai sa kansa. Ya kama kanshi da hannuwan shi biyu. Ya ce, “Hadiza bana so ki tafi ne, sai in ji ni lonely kamar maraya…….. !” 

Ta ce, 

“Alfarma za ka yi min Sulaiman, muna tare muddin rayuwar mu”. 

Ya mika mata hannu ta kama, ta isa gare shi. Ya miko mata kumatun shi yace, “Kiss me plzzzz……772”. 

Ta ji kunya sosai, ta boye kanta a kafadun shi, ita ba ta iya wannan keke-da-keken ba. 

Ta ce, “Kudin da zan kai mata za ka bani Su

laiman, ba kudi a waje na”. 

Ji yake in zai iya ba ta ranshi, to zai ba ta. Balle duniyar da abin da ke cikinta. Bai tambaye ta me za ta yi dasu ba, ko adadin da take so, ya kwaso duk abin da ke cikin aljihun shi ya zuba a jakar ta. 

Allah sarki! Kamar ba za su rabu ba, a lokacin har duhun dare ya shigo, likitoci uku ne da ke karkashin sa suka kwankwasa suka turo kofar suka shigo. Dole Hadiza ta dau jakarta da lab-coat hadi da gilashinta ta fita, yana kara jaddada mata ta yi tuki da kula. Dan banzan go slow ne ya tare ta a titi, ba ta isa gidansu ba sai tara da rabi, Maman su da suke kira Yaya, tana zaune a tsakar gida da rediyo a hannun ta tana sauraron Jakar Magori. Autan su Abdulyassar yana gefe yana hada motar kara. 

Yaya Babar su Hadiza ba wata tsohuwa ba ce cancan, don irin auren wurin nan aka yi mata, shekarun ta 

arba’in kenan. 

Hadiza ta yi sallama Yaya ta amsa, Abdulyassar ya watsar da _ kayan wasan shi da gudun shi ya kwaso ya rungume ‘yar uwar shi, kasancewar ta mai jan su a jiki tare da nuna musu kauna. Yana tambayar ta ina Munib? Daga can dakinta na ‘yammatanci, wanda a yanzu ya zan mallakin Fati, sautin Abdurrahaman Sudais ke tashi a hankali cikin suratul Al-Imran, wannan ya tabbatar mata Hafiza Fati Ja‘afar na gida. 

Ta samu gefen Yaya ta zauna, Yaya ta mike daga kwanciyar da ta yi bisa tabarma. Kai da ganin kyakkyawar fuskarta ka san ta ji dadin ganin diyar tata, ta ce, “Da daddaren nan Hadiza?’ Ta ce, “Wallahi Yaya, Dr. ne ya tare ni, na kawo ma Fati kudin ne”. 

Ta ce, “Amma kin kyauta, don da ta yi ma Yayan ku maganar ta waya ya ce ba zai samu zuwa Kano wannan satin ba, ga shi baban ku kwanan nan kasuwar ta ja baya, kuma ta ce daga 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *