YAKANA BOOK 1 CHAPTER 3 BY SUMAYYAH ABDULKADIR

 YAKANA BOOK 1 CHAPTER 3 BY SUMAYYAH ABDULKADIR

wannan satin za a rufe”. 

Ta ce, “Baba bai dawo bane?” 

Yaya ta ce, “Ya dawo tun yamma, ya tafi dubiyar dan gidan Malam Abdu ne babur ya buge shi dazu”. 

Ta ce, “Allah ya sauwake, Fati na ciki ko”. 

Yaya ta ce, “Yanzu ta gama cin abinci ta shige ciki tana rehearsal, jibi za su yi musabakar jiha kuma ita za ta wakilci jihar Kano, kin san Fati ba daga nan ba”. 

Cikin alfahari da kanwar tata a zuciyarta, Hadiza ta tura kofar dakin cikin sallama, Fati ta diro daga gado ta rungume ‘yar uwarta tana yi mata oyoyo. 

Hadiza ta dubi Fati sama da kasa, ta zama cikakkiyar budurwa sosai. Ta kama baki “Fati girma haka?” 

Fati ta yi murmushi, kumatunta duka suka lotsa gwanin sha’awa, wushiryarta ta fito siririya da ita. 

Hadiza ta ce, “Wane course aka samu?” 

Ta ce, “Course din da na nema ne (Islamic Studies)”. 

Ta ce, “Masha Allah, da an je kuma sai a Samo saurayi, irin wannan girma haka Fati?” 

Ta ji kunya ta boye fuskarta cikin tafukanta, ta ce, “Ai hijabi zan ke zumbulawa irin mai hannun nan, kada ace ana so na”. 

Hadiza ta ce me za ta yi ba dariya ba, duk girman Fati baka raba ta da wauta. 

Ta kirgo kudi a jakarta naira dubu ishirin ta ba ta, Fati ta yi godiya ta ce, “Allah Yaya Hadiza kwana biyu ba’a kawo su Munib ba”. 

Ta ce, “Makaranta ta boye su, amma da anyi hutu suna nan tafe insha-Allah”. Sai sannan ne ta ga hakoran Fati. Ta ce, “Ashe kuma musabaka za a yi Fati ba labari? To Allah Ya ba da sa’a”. 

Ta yi murmushi ta ce, 

“Ameen”, 

Tana shirin fita Baban su na shigowa, 

ya ce, “A’ah, manyan likitoci ne yau a gidan namu? Ina matas da abokin?” Ta yi murmushi ta tsuguna har kasa ta gaida tsohon ta, ta ce, “Suna nan lafiya basu samu hutu bane, da sun samu za su ZO”. Yace, “Kinga kafar nan tawa kwanan nan bana jin dadin ta, har na gaji da hadiyar magani”. Ta ce, “Wane magani ne Baba? Likita ne ya rubuta?” Ya ce, “A‘a, maganin ciwon kashi ne kawai nake saya a wajen masu talla”. Ta kama baki, “Baba irin wadannan magungunan ba masu kyau bane, yawanci ma sun yi edpiry don Allah ka daina sha. Yanzu bari in rubuta maganin Fati ko Hamza su je su siyo”. Yace, “To na gode”. 

Ta baro Karkasara karfe goma daidai na dare, dauke da tazbihi a bakinta domin ba abu ne da ta ke so ko ta saba 

ba, wato (night dribing) tukin dare. 

Ta biyo ta titin Court Road ta hawo titin Gandu, ta yi kwana ta hau titin B.U.K Road. Ta iso Kabuga ta dau titin New-site wanda zai sadata da Janbulo. Babu wadatar motoci a titin. Daga gefen ta wayarta ta yi kara, sunan Sweetypie ya soma yawo a screen din. Ta yi murmushi ta mika hannun damanta ta dauka, ta rike sitiyari da hannun hagu cikin sanyin sauti ya ce, 

“Ya ya? Hope for now kina gida?” 

Ta yi ajiyar zuciya cikin karyayyar murya ta ce, “Na kusa dai, ina kan Iya abin da ya ji ke nan sai wata irin kara da ta fi kama da fashewar taya, ya yi kira “Hello!…..Hello….Hadizah!” Amma ba amsa. 

Motar ta hantsila ta shige karkashin wata trailer da ke cike da buhunhunan abinci, duk da kokarin da direban ya yi wajen kauce mata hakan bai samu ba, motocin da ke gabansu da bayan 

su duk suka yi birki cikin salati, tsirarun mutanen da ke gefen titi suka runtumo don kawo agaji. 

a hanyar katin shaida (ID Card) jami’an tsaro suka gano ko wace ce Hadiza. Don haka ba su sha wahalar samun nombar wayar mijinta ba, wanda ke can cikin gigicewa. Nan asibitin aka taho da ita cikin jinni, rai a hannun Allah. 

Likitoci biyar ne a kan Hadiza, sai Sulaiman cikon na shida, wanda ya manta wani abu wai shi karatun likita, komawa ya yi tamkar bai taba halarta 

aji ba. Shi da Hadiza da ke kwance babu maraba, illa shi a tsaye yake, sai dai jingine da garu (bango), wanda ya taimaka masa wajen daukar nauyin gangar jikinsa. A lokacin da za ka tsaga ba za ka samu ko digon jini a cikin jikinsa ba. 

Tashin hankali ba a sa maka rana! Haka wannan mummunan labari ya iske iyayen Hadiza da ‘yan uwanta ta hanyar Dr. Surayyah. 

A daren Mukhtar ya baro Kaduna zuwa Kano, a daren suka dungumo baki dayan su suka taho, sai dai basu samu ganin Hadiza ba. Har zuwa lokacin likitoci na tsananta bincike a kanta, haka suka kwana a barandar asibiti cikin tsananin sanyi. Fati sai kuka take kamar ranta zai fita tunda suka taho, Yaya na lallashin ta. 

Sai washegari da safe result din Hadiza ya iske Sulaiman da iyayen ta, bayan raunuka da ba za su kirgu ba, babu karaya ko daya a jikinta. Babban tashin hankalin wanda ya _ girgiza 

kowa shi ne, jijiyar bayanta wadda ta hada daga wuya zuwa bayan ta (spinal cord) ta tsinke, wanda ke nufin Hadiza ba za ta kara iya mikewa ba, ba za ta kara iya tafiya ba a gaba daya sauran rayuwar ta. 

Dr. Sulaiman ya mike tsaye ya nuna Dr. Samson da dan yatsa, “Ka san abin da kake fada, ban san cewa baka san aikin ka ba sai yau. Kuma shi ke nan daga yin accident sai ka nakasta min mata? Uwarka ce ba za ta kara iya mikewa ba, amma ba Hadiza ba……” Kai da ganin yadda yake maganar, kwayar idanun shi a juye, ka san ba a hayyacin sa yake wannan furucin ba. Samson ya sunkuyar da kai, duka likitocin babu wanda ya kara magana. Tausayi ne fal a zukatan su. Dr. Hadiza abar so ce ga kowa, suna jin dadin tarayya da ita, marasa lafiyan ta na yaba kokarin ta. Wannan accident da ya yi mata karan tsaye da kuruciyar ta, ya zamo nakasu ga dimbin taimakon da take bai ma al’umma. 

Malam Ja’afar mahaifin Hadiza da ke gefe shi ya soma tausar Sulaiman da kalami masu dadi da sanya imani, yana tuna masa muhimmancin yarda da kaddara. 

Sulaiman ya yi shiru, ya koma ya zauna a kujerar sa. Ya kifa kai cikin cinyoyin sa, amma har yanzu ya kasa yarda da abin da kunnuwan sa suka jiye masa. 

Wai Hadiza ta zama sai dai a kwantar a tayar ba za ta kara amfanuwa ba, ba za ta kara moruwa ba. Balle ta amfanawa kanta komai. Ita da ‘ya’yanta da mijinta sai dai gani da ido. Abin da suke gani kullum yana faruwa da al’umma yau Allah As-Samadu ya juyo da shi kansu. Dimbin ilimin su, karfin aljihunsu da tunanin su babu abin da zai iya a kai, domin ita wannan jijiya ba ta doruwa. Sai ya fashe da kuka. 

Malam Ja’afar ya mike daga kujerar sa ya isa ga Sulaiman, ya mikar da shi 

tsaye ya rungume. 

“Haba Sule! Kamar ba namiji ba? Namijin ma, likitan likitoci. Ba ka yi kuka a kan sauran al’umma da kuke kwana da yini kuna fama dasu ba sai a kan matar ka kadai? Su Allah ba ya son su ne yake dora musu lalura? Allah da ya halicci Hadiza ya fi mu son ta, shi kadai ya san dalilin sa na hukunta hakan a gare ta. 

Yau in Hadiza mutuwa ta yi me zamu iya ban da mu yi mata addu’a? Amma tana raye, a kalla muna ganin ta muna jin dadi, ka yi tawakkali ka barwa AIlah, ka zamo mai YAKANAH, sai ya yi maka tukuici da abin da baka zata ba. 

Kai za ka ba ta kwarin gwiwa, ta rungumi kaddarar da Allah ya dora mata. Amma idan ka fita karaya, wane ne zai karfafa wani?” 

Ya mika hannu yana share masa hawayen da suka kasa daina ambaliya daga kyawawan idanun sa. 

Dr. Ruth ta yi gyaran murya, ta dubi 

Dr. Sulaiman ta sunkuyar da kanta, kana ta dago ta ce, 

“Ina ganin idan Dr. Hadiza ta ji sauki, za ta iya ci gaba da aikinta ta hanyar amfani da wheel chair, idan har za’a samu wanda zai juri kawo ta da mai da ita”. 

Kiris! Ya rage ya lailayo ashar ya antaya mata, amma da ya tuna Malam na wajen Sai ya balla mata harara, a zuciyar shi ya ce, 

“Uwar ki za a sa a wheel chair ba uwar Munib ba”. 

Samson ya ce, 

“Shawarar Ruth abar dubawa ce, hakan zai debe mata kewa fiye da ta zauna a gida ba abin da take yi. Ko ba don zuwa aiki ba dole za a nema mata wheel chair ko da a gida ne”. 

Ba shi da abin cewa, don duk likitocin abin da suke cewa kenan. Malam dai baya ji saboda cikin harshen turanci suke maganar. Sulaiman ya tashi ya fita ya nufi ICU inda aka kwantar da Hadizah. 

A bayan kofa ya tsaya ya rabe, yana leken ta, ya kasa karasawa, ya kura mata ido yana ta’ajjibin yadda kwana daya rak! Allah ya_ jirkitar da kyakkyawar fuskar Hadiza, ko ina a jikinta rauni ne, nan plasta can plasta. Barci take sadidan, sai dai da gani ba na Allah da Annabi bane (na karfin allurai ne). 

Rabin fuskarta nade cikin bandeji, wadda ta kumbura ta yi sumtum kamar an hura (baloon). A hankali ya soma taku ya isa ga gadon da take kwance, ya ja kujera ya zauna dai-dai fuskarta yana fuskantar ta. 

Ya kai hannu bisa goshin ta wanda ke nade cikin bandeji, kamar an ce da ita bude idon ki. Suka yi ido hudu da Sulaiman din ta, ta dubi dakin ta dubi kanta, ta tabbatar a kwance take a gadon asibiti. Ta maido duban ta ga Sulaiman wanda ke binta da ido, da zuciya, ta ce cikin kankanuwar murya, “Accident na yi ko?” 

Ya daga mata kai. Ta dora hannunta 

mai rangwamen raunika bisa nashi dake goshin ta, ta sauke, don ji take kamar ya dora mata Dala da Gwauron Dutse. 

Ta yunkura da niyyar ta tashi zaune amma ta ji kamar ba jikinta ba, ya mike ya kama ta ya mikar da ita zaune. Ya janyo pillow ya tusa mata don ta ji dadin jinginar, ya tabbatar dai da gaske ne Hadizar shi ta zama disabled (nakasasshiya), sai jikinsa ya soma kyarma. 

Duk dauriyar da yake yi abin ya ci tura, da sauri ya rungume ta, cikin shesshekar kuka ya ce, 

“Cikin kowanne hali, INA SON KI HADIZAH”” 

Kuka suke dukkanin su babu mai rarrashin wani, don ita Hadiza ta tabbatar abin da zai sa Sulaiman kuka, to tabbata ba karamin abu bane, wannan shi ya gigita ta, ita ma ta fashe da kuka. 

Fati a gaba, Yaya, Malam, Hamza da babban Yayan su Mukhtar suka shigo, daga Hadiza har Sulaiman babu wanda ya san da shigowar su, shessehekar kukan Fati ne ya ankarar da Sulaiman cewa akwai mutane a dakin. 

A hankali ya zare jikinsa daga na Hadiza ya juya ya fita daga dakin ba tare da ya iya hada ido da surukansa ba. 

Malam Ja’afar ya karasa jikin gadon Hadiza ya kama hannun ta inda babu ciwo, ya ce, “Ki yi tawakkali Hadiza, ki zamo mai YAKANAH a dukkanin al’amuran ki, ki zamo mai godiya ga Allah a duk yanayin da kika tsinci kanki. Wannan ba shi ne karshen rayuwar ba, yarda da kaddara dole ne ga duk musulmin kwarai”. 

Cikin kuka mai tsanani ta ce, “Na ji Baba, amma don Allah ku fada min me ke faruwa dani? Sulaiman bai gaya min komi ba, sai kuka yake yi, kukan shi ya daga min hankali, ku fidda ni a duhu. Wani abu ne ya faru dani?” 

Malam ya sa habar babbar rigar sa ya share hawayen da suka ciko mishi ido cikin dabara wai kada Hadiza ta ga shi ma kukan yake, amma ta ganin. Hadiza ta musamman ce ko a cikin ‘ya’yansa, yana son ta son da bal yiwa su Mukhtar, ganin Babanta yana kuka sai ta kara tsananta kukan ta. 

Cikin tausasawa Mukhtar ya ce, “Cool down Hadiza, take it easy……. Ya shiga rattabo mata al’amarin da ya samu rayuwarta, ya kare da cewa, ““Wannan shi ne ya dagawa Sulaiman hankali, amma kamar yadda Baba ya ce ne, ki yi tawakkali, ki zamo mai YAKANAH! Wannan ba shi _ ne karshen rayuwar ba!” 

A matsayinta na cikakkiyar likita, tuni ta gano mummunan nakasun da ya samu rayuwarta wanda babu wani likitan duniya da zai iya maganin shi. Ta nemi hawaye a kwayar idonta ta rasa, ta nemi miyau don ta hadiya a kan harshen ta ya kafe karaf! Kamar 

Fati a gaba, Yaya, Malam, Hamza da babban Yayan su Mukhtar suka shigo, daga Hadiza har Sulaiman babu wanda ya san da shigowar su, shessehekar kukan Fati ne ya ankarar da Sulaiman cewa akwai mutane a dakin. 

A hankali ya zare jikinsa daga na Hadiza ya juya ya fita daga dakin ba tare da ya iya hada ido da surukansa ba. 

Malam Ja’afar ya karasa jikin gadon Hadiza ya kama hannun ta inda babu ciwo, ya ce, “Ki yi tawakkali Hadiza, ki zamo mai YAKANAH a dukkanin al’amuran ki, ki zamo mai godiya ga Allah a duk yanayin da kika tsinci kanki. Wannan ba shi ne karshen rayuwar ba, yarda da kaddara dole ne ga duk musulmin kwarai”. 

Cikin kuka mai tsanani ta ce, “Na ji Baba, amma don Allah ku fada min me ke faruwa dani? Sulaiman bai gaya min komi ba, sai kuka yake yi, kukan shi ya daga min hankali, ku fidda ni a duhu. Wani abu ne ya faru dani?” 

Malam ya sa habar babbar rigar sa ya share hawayen da suka ciko mishi ido cikin dabara wai kada Hadiza ta ga shi ma kukan yake, amma ta ganin. Hadiza ta musamman ce ko a cikin ‘ya’yansa, yana son ta son da bal yiwa su Mukhtar, ganin Babanta yana kuka sai ta kara tsananta kukan ta. 

Cikin tausasawa Mukhtar ya ce, “Cool down Hadiza, take it easy……. Ya shiga rattabo mata al’amarin da ya samu rayuwarta, ya kare da cewa, ““Wannan shi ne ya dagawa Sulaiman hankali, amma kamar yadda Baba ya ce ne, ki yi tawakkali, ki zamo mai YAKANAH! Wannan ba shi ne karshen rayuwar ba!” 

A matsayinta na cikakkiyar likita, tuni ta gano mummunan nakasun da ya samu rayuwarta wanda babu wani likitan duniya da zai iya maganin shi. Ta nemi hawaye a kwayar idonta ta rasa, ta nemi miyau don ta hadiya a kan harshen ta ya kafe karaf! Kamar 

bai taba gudana a cikin bakinta ba. 

Ta runtse idonta da karfi, tsawon mintuna biyar ba ta bude ba. Ita kadai ta san radadin da take ji a zuciyarta, ita kadai ta san azabtuwar da ruhinta ke yi, al’amarin ya shallake tunanin ta. Ba ta yi tsammanin al’amarin ya yi kamarin haka ba, lallai dan adam ba a bakin komai yake ba. 

Yau ne kake mai rai, gobe ne kake gawa. Yau ne kake da amfani, idan Ubangiji ya so, gobe ne ka zama tarihi. A rayuwar Hadiza ba ta taba tsammanin wata kaddara makamanciyar wannan za ta taba shafar rayuwar ta ba. To ina ruwan Allah! 

Ta bude idon a hankali tana kallon iyayen ta da ‘yan uwanta wadanda dukkanin su ke sharar hawaye, sai ta soma lallashin su cikin muryar ban mamaki, tamkar ba ita ba. Ta fi su karfin zuciya, ta fi su tawakkali, ta fi su YAKANAH. Ta karbi kaddarar ta da hannu bibbiyu, tana fatan Allah ya sa hakan ya zamo kaffara a gare ta, in 

kuma jarrabawa ce ya sa ta cinye jarrabawar ta. 

36 KOK 

Dole kanwar naki, Sulaiman ya sayo ma Hadiza wheel chair ana i gobe za a sallame su daga asibiti. Don duk raunin dake jikinta ya kame sai karfin jiki da dan abin da ba a rasa ba. 

Yaya ta so Sulaiman ya ba ta Hadiza ta wuce da ita gida inda za ta fi samun kulawar iyaye da ‘yan uwa, amma sai ya sa musu kuka. Da me zai ji ne? Da lalurar da ta kashe masa rayuwa, ko da rashin Hadiza a cikin gidan, wadda ta zamo wani bangare na rayuwar sa, kundin farin cikin sa, sannan barin jikinsa? 

Dole suka kyale shi da matar shi, amma sun ce Fati ta koma gidan ta zauna tare dasu, don ta dinga taimaka masa kula da Hadiza, musamman kasancewar sa ba mazauni ba. 

Sulaiman bai so ba, don shi tun fil’azal Allah bai sa mishi son Fati ba, saboda 

son da Hadiza ke mata. Yana kishin Fati, a ganin sa Hadiza ta fi son Fati a kanshi. Sannan zubin ta na zuhudu (gudun duniya) ya yi yawa, bai fiya son mutane irin ta ba, kasancewar shi (sociable). 

A tsarin halittar dan adam (personality), tana cikin rukunin al’ummar da ake kira (introbert). Ba ta iya hada ido da shi, kai da kowa ma, saboda kunya. Da wuya ka ga hakoranta, sai dai in guri ya kure ta yi murmushi, ‘dimple’ din da ‘cleft’ su lotsa, wanda shi ne muhimmin al’amarin da ke daukar hankalin dubban maza a kanta, sai dai kuma bai isa ya tsallake hukuncin da Yaya ta yanke ba. 

Haka Fati ta hado kayan ta tsaf, ta dawo gidan ‘yar uwarta da zuciyar ‘yan uwantaka. Zuciyarta cike fal da so da kaunar ‘yar’uwar ta, karatun da ta taso shekara da shekaru da burin yin sa, gashi ta samu, amma ta jingine shi ta sadaukar da rayuwarta kacokam da 

lokacinta ga rayuwar, ‘yar uwarta. Sulaiman ya ciccibo Hadiza ya fito da ita daga mota, Fati ta bude (boot) ta fiddo wheel chair a nade, cikin sauri ta warware, Sulaiman ya sanya ta a ciki ya tura a hankali zuwa cikin gida. 

Fati ta fiddo kayansu daga cikin motar ta rufe motar, ta soma diban kayan daya bayan daya tana shiga dasu cikin gida. 

Malam Ilu maigadi, ya yi sallama a falon, a lokacin Sulaiman na kici-kicin aza Hadiza a daya daga cikin kujerun falon, ba tare da ya juyo ba ya amsa masa. 

Ya zube har kasa yana jajantawa iyayen gidansa kaddarar da ta same su. Yana magana yana sharar hawaye, saboda yadda yake matukar kaunar Hadiza, saboda karamci da kyautatawar ta gare shi. 

Haka Goggo Allti ta fito daga kitchen, ganin Hadiza yau nade cikin kujera sai ta fashe da kuka, Sulaiman ya yi saurin ficewa a falon ya dau mota ya 

fita don dauko yara a makaranta. Hadiza ta dubi Alti ta yi dan murmushi, “Alti wane ne ya halicce mu?” Ta ce, “Allah (S.W.A)”. 

Ta ce, “To kinga in haka ne ke nan bamu da iko da kanmu sai abin da ya ga damar hukuntawa a gare mu, mu kuma dole ne mu zamto masu godiya idan har muna so imanin mu ya cika”. Alti ta jinjina kai tana mai jinjina karfin imani irin na uwargijiyarta. Hadiza ta juya ga Fati ta ce ta kal kayanta dakin ta, kasancewar a tsarin gidan likitocin babu wani edtra room, ita za ta yi amfani da na Sulaiman. 

Fati ta ce atafau ita dakin su Muniba za ta zauna tare dasu, ta kada ta raya amma ta ki, ta ciccibi jakarta ta yi dakin su Muniba. 

Fitar ta daga falon ke nan su Munib suka dira a falon, Baban su na biye dasu yana rike da jakunkunan su da food flasks din su. Suka tafi da gudu suka rungume Mamarsu, Munib da yake shine mai wayo ya ce, 

“Mummy yaya jikin ki? Daddy ya gaya mana kin yi accident kin ji ciwo kina asibiti ana yi miki allura?” 

Ya kai hannu ga tabon ciwon goshinta, “Sannu Mummy, kin ji?”. Ta shafa kansa ta yi masa murmushi bata ce komai ba. 

Ita kuwa Muniba bin jikin Mummyn ta yi ta lafe kamar mage, dama ita ba ta fiya magana ba. Zuciyarta kal da ganin mahaifiyarta da ta jima ba ta gani ba. 

Munib ya soma jan hannunta wai ta taso suje su yi kwallo (ball) kamar yadda suka saba, Sulaiman ya kau da kai, bai son ganin wannan abin tausayi, ya mai da hankali ga lallatsa wayar sa, baya son su ga hawayen sa. To ita ma Hadizar duk dauriyar ta sai da hawayen suka tsatstsafo, ta sa yatsun ta biyu ta dauke su, ta kama dukkan ‘ya’yan biyu ta rungume a kirjinta. Kukan zuci take wanda ya fi na fili soya zuciya. Ta ce, “Ku tafi wurin Anti Fati tana dakinku ku yi kwallon 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *