YAKANA BOOK 1 CHAPTER 5 BY SUMAYYAH ABDULKADIR

 YAKANA BOOK 1 CHAPTER 5 BY SUMAYYAH ABDULKADIR

ba, ko na tafi tunanin halin da kike ciki ba zai barni in mai da hankali a kan karatun ba”. 

Ta yi murmushi, “Cewa_nake watarana aure za ki yi Fati?” 

Nan da nan Fati ta yi kicin-kicin da fuska, ta juya mata baya ba ta ce komi ba. 

Hadiza ta ce, “Ko baki ji ni ba? Aure za ki yi Fati dole ba da jimawa ba, don haka ki tsaya ki gina rayuwar ki kamar yadda muka gina tamu, bana so saboda amfanin kaina ke in tauye ki. Don haka na baki kwana biyu ki yi tunani, an fara sai da JAMB na wannan shekarar, don haka ki nutsu ki kama abin da zai taimake ki ranar da bani. Duk wata kauna da dan uwa na gari zai nuna wa dan uwansa kin nuna min ita, sakayyar ki na wajen Allah.

 

Sai dai ba zan bari ki kari rayuwar ki baki dandani zakin ilimin ko auren da na dandana ba, dole in samar miki future kafin Allah ya yi hukuncin da ya So a kaina….” 

Fati ta yi saurin juyowa ta dubi Hadiza, domin a da ta bata baya ne. Ba ta gane abinda take nufi ba. Hadiza ta yi murmushin karfin hali ta ce, “Fati zan gaya miki wani abu, amma bana so ki daga hankalin ki, bani da lafiya Fati, amma don Allah ko Yaya ban yarda ki gayawa ba balle Sulaiman. Fati na dade ina fama da ciwon kai wanda nake yi lokaci-lokaci, Sulaiman ya sani ina yawan fama da (migrain) amma bai taba zurfafa bincike ba, don ban taba gaya masa yadda nake ji ba. Ba tare da sanin sa ba na je wajen Dr. Bunza mijin Surayyah, da ke likitan kwakwalwa ne, cikin sirri ya yi min bincike mai zurfi inda ya sanar dani ina fama da kansar kwakwalwa (brain cancer)”. 

Fati ta zazzaro ido ta sulale ta zauna a kasa, ta kai hannu ta dafe kirjinta, sai ga hawaye suna shatata! Hadiza ta yi murmushi ta matso da kujerar ta inda Fati take, ta dora hannu a kanta. 

“A‘a, Fati kada mu yi haka da ke, ama

nar rayuwata nake gaya miki, wadda bani da wanda zan bawa sai ke. Ba wanda zan iya gaya ma wa Sai ke, ciwon bai yi tsanani ba, kuma ina shan magani a boye, ko Surayya ba ta sani ba. 

Fati abin da ya sa na gaya miki don ki tallafa min ne, Sulaiman likita ne wanda ke bukatar kwanciyar hankali don samun (confidance) wajen gudanar da aikinsa na ceton rayuwar al’umma, idan ya ji wannan maganar ba zai taba samun kwanciyar hankali ba. 

Fati Sulaiman yana sona, sosai, irin son da zai iya bani rayuwar shi, bana son abin da zai dagula masa lissafi, ki rike min amanata, ki rike min ‘ya’yana, ki basu tarbiyya irin taki kada ki bari Sulaiman ya tagayyara a bayana. Ina son shi yadda yake so na, na so in Ci gaba da rayuwa tare da shi, in ci gaba da haifa mishi ‘ya’ya kamar yadda yake so, amma ban san ya ya Allah zai yi dani da rayuwata ba. Ki rike min 

Sulaiman Fati bana so rashi na ya tagayyara shi…….. ” 

Zuwa wannan lokacin duka ‘yan uwan biyu sharbe suke, na hawaye da majina. Girki 

yana ta kauri, amma ba su kula ba. Fati ta rage sautin kukan ta, ta ce, “Shi brain cancer ba’a warkewa?” 

Hadiza ta ce, “Ba a warkewa gaba daya, ko ya lafa zai tashi, amma ina kula da shan magani”. 

Fati ta yarfe hawaye ta ce, “Wannan ba abun boyewa bane Yaya Hadiza, ki daina fidda rai da rayuwa saboda ciwo. Insha Allah ke za ki aurar da Munib da Muniba, ya kamata ki sanar da Dr. domin ya taimaka miki da addu’a, duk wani hali da zai shiga ai shi musulmi ne ya san duk son da yake miki ya san bai kai wanda Ubangijin ki yake miki ba. If the condition become worst, ba zai taba yafe 

Hadiza ta yi shiru tana mamakin 

Zurfin hankali irin na Fati, yarinyag karama sai tunanin manya. Ta ce, “Zan duba shawarar ki Fati, Allah ya kara. min YAKANAH, ya_ bawa ‘ya’yana tarbiyya irin taki. Ai dai za ki kula min dasu ko Fati?” 

Cikin kuka ta ce, “Yaya Hadiza ki daina yi min wannan maganar, bani da jarumtakar sauraron ta…… “, 

Ta ce, “Na rantse da Allah idan baki yi min wannan alkawarin ba nima ba zan bi shawarar ki ba”. 

Cikin makyarkyatar murya ta ce, “Eh…….eh……na yi alkawarin zan kula dasu”. 

Ta ce, “To nima zan bi shawarar ki, amma ba yanzu ba. Tashi sauke tukunyar can tana kauri”. 

Ta share idonta ta mike ta sauke, ilahirin jikinta sai rawa yake. Ta kashe komi ta maido Hadiza falo, ta yi dakin su ta rufe ta fada kan gadon su ta soma girka kuka. Ta ga kukan ba zai amfane ta da komai ba, sai ta je bandaki ta dauro alwala, ta shimfida sallaya ta 

soma Sallah, a kowacce sujjadarta tana yiwa Hadiza addu’ar Allah ya ba ta lafiya. 

Wayar Hadiza ta yi kara, a lokacin tana bisa sallaya tana azkar, don haka ba ta daga ba har ta tsinke. Sai ya yo tedt, ta dauka ta duba Sulaiman ne yake gaya mata suna bisa hanya har da Inna Halima za ta zo ta duba ta kuma za ta ga likita, don haka a gyara mata daki don za ta kwana biyu. 

Hadiza ta ji dadin zuwan Inna, domin Innar Sulaiman mutum ce har mutum, ma’abociyar raha da sanin mutunci. Don haka ta kira Fati a waya ta ce ta kara yawan abinci da ta aje a falo, ta kuma canza shimfidar gadon dakinta, don kullum a gyare yake Fati ba ta wasa da tsabtarsa. 

Tara na dare dai-dai suka shigo, Inna dauke da Muniba da tayi barci a kafadunta. Hadiza da Fati suka yi mata sauka ta ban girma. Sai lokacin kwanciya ne aka kai ruwa rana da Inna, don ta ce ba za ta zaunawa 

Hadiza a daki ba, sai tare da ‘yan jikokinta, dole suka kyale ta. 

Duk juyin da Inna ta yi a wannan dare, Fati take gani a kan sallaya, ta yi sallah, ta yi lazimi. Da asubahi kuwa ta soma rero (Suratul Yaseen) da sauti irin na Khusairi. Sannan ne ta dan samu barci. 

Karfe shida ta fada kitchen ta soma aikace-aikace, Inna na hankalce da damuwar da yarinyar ke ciki, ta rasa abin da ke damun ta kankanuwa da ita haka. 

To haka a washegari ma, har cikin kitchen wannan yarinya ba ta rabo da hijabi da carbi, tun tana burge ta har ta koma bata tausayi. 

Washegari litinin bayan sun yi kalaci, Inna da Sulaiman suka wuce asibiti in da za ta ga likitan ido, ba su dawo ba sai da rana ta take, yana sauke Inna ya juya. 

Sun fara cin abinci ita da Hadiza a kan darduma irin traditional carpet din nan 

na fata, an kuma shimfida ledar cin abinci. Don Fati ba ta cin abinci cikin mutane, loma ta farko, ta biyu, ta uku Hadiza ta soma kelayo amai kamar ta amayar da ‘yan hanjinta. 

Da sauri Fati ta shigo, Inna na rike da Hadiza, ita kuma ta kawo ruwa da roba Hadiza ta kuskure bakin ta. Fati ta sa moper ta gyare wajen, ta koma kitchen don hidimar abincin dare. 

Ko me take yi cikin kitchen bakinta ba ya rabo da ambaton Allah, duk a kan lafiyar ‘yar uwarta. Ita dai Inna haka nan ta ji Fati tana burge ta, tana bata sha’awa. Zahidah ce, babu duniya a gabanta, gata da dan banzan kyau da fata lafiyayya, amma ba sa gabanta, lahira take nema da harshen ta da goshin ta da gwiwoyin ta, ba ta furuci Sai wanda ya zame mata dole, ko in an tambaye ta. 

Amma a kwanaki bakwai da ta yi, Inna Halima babba ce mai cikakken hankali, ta lura Sulaiman ko ganin Fati a gidan shi ba ya son yi, don dai ba 

yadda zai yi ne, kuma bai son abin da zai bata ran Hadiza. 

Suna falo ita da Sulaiman misalin karfe sha daya na dare suna hira a nutse irin ta da da mahaifi, ta ce, “Wai ni mai sunan Malam me yarinyar nan kanwar Hadiza ta yi maka ko kallon ta ba ka yi? Dazu da safe ina kallo tana gayas da kai ka dauke kai ka fita, haka tun zuwana ban taba ganin ka yi mata magana ba, balle wasan nan irin na mijin ya da kanwarta. In kana wuri ta shigo sai ka tashi, in kana falo ta ganka sai ta koma ta yi ta zaman daki. Ita da ganin ‘yar uwarta sai in baka nan, mene ne manufar hakan?” 

Ya juyo yana kallon Inna ya ce, “Wacce yarinya kike magana?” 

Ta ce, “Fatima”. 

Yace, “Fati wai?” 

“Eh, ita”. 

Ya rausayar da kai ya ce, “Raini ne bana so, kuma ni ban iya wani wasan kanin miji ko kanin mata ba”. 

Ta yi sakale tana jin sa, ta ce, “Hala 

wani laifi ta yi maka? Har Hadiza na lura ranta yana baci da irin halin ko in kulan da kake yiwa ‘yar uwarta. Ban san ka da bakar zuciya ba, kada ka a fara a kan Fatima, domin mutum ce cikin ‘yammatan da babu irin su a yanzu, wannan yarinyar tana da halayen ‘yan aljanna, ka yi a hankali baka sani ba ko waliyya ce”. 

Shi abin ma sai ya ba shi dariya, ya ce, “A wannan kalatacciyar duniyar tamu dama akwai sauran waliyyai Inna?” 

Ta harare shi ta ce, “Dariya ma kake min?” 

Ya yi saurin cewa, “A’a, yi hakuri Inna”. 

Ta ce, “To ka gyara ma’amalar ku, zai fi kyau a ce akwai kyakkyawar alaka a tsakanin ku saboda Hadiza, in ta gaishe ka ka dinga amsawa cikin walwala da sakin fuska, wanda ya rike ibada ba ya wulakanta a duniya da Jahira. Baka sani ba ko ta fi ka matsayi a wajen Allah, ka canza takun ka a kanta, ai ba haka na ga kana yiwa su 

Ruma ba, to matsayin ta daya dasu a gare ka, ka ji na gaya maka”. 

Bai ce komi ba ya jawo wata hirar, don dai a sauya wannan. He is not interested at all (Fati is not the kind of person) wato ba ta daga cikin irin mutanen da yake son yin mu’amala dasu. Haka nan jinin su bai hadu ba, don yana son Ya, ba dole sai ya yi wata kakkarfar alaka da kanwar ta ba, bayan wadda musulunci ya ce, ai ba sa’ar wasan shi ba ce kanwar shi ce. Kwana bakwai din da Inna Halima ta yi jinyar Hadiza suke ita da Fati, komai ta ci sai ta amayar, ga zazzabi da ciwon kai mai zafi, sai ta rike kanta idan ciwon ya motsa mata tana wani irin kuka mai keta zuciyar duk mai imani. 

Sulaiman da farko bai sani ba, don ya dauka laulayin ciki ne irin wanda ta saba, kuma ciwon baya tasar mata da daddare lokacin da suke tare kenan. Ita ma Inna ta lura ta san laulayi ne na sabon ciki, amma wannan buga kan da 

Hadiza take yi a jikin bango da kukan da take yi na azaba ta fahimci akwai dai wani abun, amma tana ganin dukkan su likitoci ne sun san abin da ke damun ta, kuma ta ga Hadiza tana shan magani, sai ba ta yi magana ba, amma dai ba ta taba ganin irin wannan laulayin cikin ba. 

Don haka ta kara sati saboda lafiyar Hadiza wadda ta daina cin komai sai ruwan bakin lipton da ruwan tsamiya. Gaba daya ta rame ta fita hayyacin ta, ba ta taba yin cikin da yake wahalar da ita irin wannan ba. 

Tun Sulaiman bai gane ba har ya fahimci Hadiza ba ta da lafiya sosai, wannan ya wuce laulayi kuma wannan (migrain) yana bukatar bincike. 

A daren ya fito daga wanka yana tsane kanshi da dan kankanin towell, tana kwance rigingine a gefen gado, cikin doguwar rigar barci mai santsi mara hannu ruwan madara, kyawawan kafafunta da cinyoyin ta a mike sambal, a haka sai ka rantse lafiyar ta kalau ba ta 

tare da wata lalura. 

Son matarshi da kaunar ta na kara girgiza zuciyar sa, yana hargitsa gangar jikinsa. Ta kure fanka da A.C amma ba ta daina zufa (gumi) ba. Da sauri ya karasa zarga igiyar pyjamas din shi ya yiwa kanshi kyakkyawan matsuguni a bayan ta, ya daura hannu a kan goshin ta, zafi rau! Dole ya hadiye nashi bukatan ya soma ba ta kyakkyawar kulawa ta hanyar sanya karamin towell a ruwa yana goge mata kanta don zafin kan ya ragu. Sannan ya soma bin gabban jikinta da message don ta ji dadin kasusuwan ta. Ya juyo ta ya rungume ta yana furzar da numfashi da sauri da sauri, ya sake cewa, 

“Cikin kowanne hali, INA SON KI HADIZAH!”” 

Ta bude idanunta a hankali, wadanda suka kankance suka yi jawur tana kallon abin son ta, shi ma kallon ta yake kallon yaya zan yi da raina? Ya ce a galabaice, 

“Gobe zan dauko Dr. Bunza ya duba 

ki”. 

Gabanta ya yi wani irin faduwa, ta runtse idon ta da karfi ta ce, 

“Bana so, kada ka dauko shi, idan kuma har ka dage sai ka dauko shi to zan koma Karkasara’”. 

Ya girgiza ta da karfi ya ce, “What do you mean (me kike nufi)? In barki a gida kina ciwo ban nema miki magani ba? Ai Allah sai ya tambaye ni, tyayen ki da suka danka min ke su tuhume ni. Wannan ciwon kan bana wasa bane yana bukatar bincike”. 

Ta ce, “Ai ba yau na fara ba, kuma da na sha magani shi ke nan _ yake lafawa”. 

“Ina maganin? Dauko min in gani”. 

Ta ce, “Ya kare dazu, da safe nake shirin in aiki Fati ta siyo wasu”. 

Yace, “Wane magani ne?” 

Ta yi shiru. 

““Tambayar ki nake yi, ina maganin? Ya ya sunan sa?’ 

Ta ce, 

“Panadol”. 

A mamakance ya maimaita “Panadol?” 

“Eh”. 

Ya ce, 

“You are silly ko in ce you are nonsense Doctor! I did not beliebe YOU… “(kina shirme, ke shashashar likita ce, ban yarda dake ba). 

Ya tashi a fusace ya fizgi waya ya kira Dr. Bashir, ‘consultant’ na ‘psychiatrist’, Surayya ce ta dauka, bai ko amsa gaisuwar da take mishi ba ya ce, “Ina mijin ki?’ 

Ta amsa 

“An kira shi a ‘emergency’ kuma ‘he is on call’ yanzu ya fita, ya manta wayar”. 

Ya kashe wayar ya cillar ya zauna a gefen gado ya dafe kai, Hadiza na kuka a hankali tana kara hargitsa shi, ya ce a fusace, 

“Enough…….is enough Hadizah! Ki gaya min fisabilillahi mene ne babbar matsalar ki?” 

Ta ce, 

A mamakance ya maimaita “Panadol?” 

“Eh”. 

Ya ce, 

“You are silly ko in ce you are nonsense Doctor! I did not beliebe YOU… “(kina shirme, ke shashashar likita ce, ban yarda dake ba). 

Ya tashi a fusace ya fizgi waya ya kira Dr. Bashir, ‘consultant’ na ‘psychiatrist’, Surayya ce ta dauka, bai ko amsa gaisuwar da take mishi ba ya ce, “Ina mijin ki?’ 

Ta amsa 

“An kira shi a ‘emergency’ kuma ‘he is on call’ yanzu ya fita, ya manta wayar”. 

Ya kashe wayar ya cillar ya zauna a gefen gado ya dafe kai, Hadiza na kuka a hankali tana kara hargitsa shi, ya ce a fusace, 

“Enough…….is enough Hadizah! Ki gaya min fisabilillahi mene ne babbar matsalar ki?” 

Ta ce, 

“Nifa na gaya maka laulayin ciki ne, Sai migraine wanda ba yau na fara ba, kuma ka san shi dama ina da magungunan da nake sha a kan shi, wannan zazzabin da haraswa laulayin ciki ne irin wanda na saba, zan gaya maka karya ne? Yau da bakin ka Sulaiman kake cewa baka yarda dani ba?” Jikinsa ya dan yi sanyi, ya rage sauti ya ce, “To ta ya ya zan ce zan kira likita da ya san matsalar ki ya duba ki ki ce a’a? Sai in dauka wani abu ne daban kike boye mini”. 

Ya yi mata wani irin murmushi da har abada ba zai gushe daga zuciyarta ba, ta dauke kai alamar ta yi fushi. Ya bi bayan ta a hankali ya kwanta, suna raba zazzabin tare. Akwai wani abu wai shi ‘hot kiss’ da Hadiza ba ta sani ba daga Sulaiman sai a yau, ya mantar da ita rashin lafiyar ta, ya dauke ta ya jefa a duniyar soyayya, ta manta cewa ita nakasasshiya ce, ta manta damuwar ta na cewa lafiyarta na hannun Allah, ta dauka cewa, tana a Dr. Hadiza ne ta 

baya. Ba za ta mance da wannan ranar da Sulaiman ya zubar da hawayen shi a karo na biyu a kanta ba. 

Na farko saboda ta nakasa, na biyu na dimbin soyayyar da yake yi mata. To wanne ne zai kasance na uku??? 

2K KK OK 

nna ba ta koma Bakori ba sai bayan watanni biyu, lokacin laulayin Hadiza ya ragu, tana yi mata dabaru irin na manya har ta samu sauki. 

A lokacin cikin ya shiga wata hudu, sannan ne laulayin ya tsaya. Sannan ciwon kanta ya jima bai tashi ba, saboda Dr. Bunza ya sauya mata magani, Fati ce ke zuwa ta karbo ba tare da sanin Sulaiman ba. 

Ganin ciwon ya dade bai tashi ba sai Hadiza ta watsar da shawarar Fati ba ta gayawa Yaya ba, shi dama SuJaiman tuni ta binne shi ya kuma yarda cewa migraine take. 

Cikin Hadiza wata bakwai, ya fito ya 

yi tororo kamar watanni tara. Haka za ka ganta fus! A cikin wheel chair tasa cikin a gaba tana kallo tana mamakin sarautar Allah, wanda ya ga damar ta haihu a cikin halin da take ciki. So da kulawa wurin Sulaiman kamar ya yi mata nakuda. 

Watan Aprilu ya kama, wanda ya yi dai-dai da EDD din ta, cikin dare wani azababben ciwon kai ya tashe ta, ta soma bubbuga kanta a jikin gado, kafin a yi haka ta yi dogo suma jini ya kece kamar da bakin kwarya. 

Duk wani kokari da zai iya shi ne kiran Dr. Abdullahi ko Dr. Surayyah a waya, amma hannun shi ya kasa kama wayar saboda dimaucewa. Sannan shi ya manta kansa balle ya yi tunanin wane irin taimako zai ba ta a matsayin shi na cardiologist wanda kuma ke da general knowledge a kan komai. 

Sai ya sunkuto ta ya nufo harabar gidan, ya shimfidar a bayan mota. Malam Ilu ya wangale mishi ‘gate’ ya fita, cikin ranshi yana cewa kai wan

nan yarinya kina cikin jarrabawa kalakala, Allah ya baki lafiya. 

Da taimakon innalillahi…….. da yake ta ambato ya samu nutsuwar da har ya iso AKTH, aka karbe ta a bangaren ta wato dakin haihuwa, su Dr. Surayyah, Dr. Abdullahi suka rufu a kanta, ba ta san inda kanta yake ba. Suka soma ba ta duk wani taimako da ya dace don ta haihu da kanta kamin su yi bincike a kan wata matsala daban da suka hango wadda da alama dadaddiya ce. 

Amma duk iya kokarin su sun tabbatar da ba za ta iya haihuwa da kanta ba, don haka suka miko mishi takardu don ya sanya hannu a shiga da ita tiyata. Da kyar yake iya sarrafa ‘yan yatsun shi a lokacin da yake rattaba hannun, zuciyar shi ta riga ta bushe da tashin hankali. 

Yana tsaye aka turo ta a kan gadon daukar marassa lafiya zuwa dakin tiyata, bai yi tunanin gayawa kowa ba sai da safe, kasancewar ba shi da nutsuwar yin hakan. 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *