YAKANA BOOK 1 CHAPTER 6 BY SUMAYYAH ABDULKADIR
Da ya ga wannan ba za ta yi mishi ba, sai ya nufi ofishinsa ya murda kofar ya shiga, ya jingina da kofar ya soma tunanin wasu al’amura da ya lura Hadiza na boye mishi, da yawan waya da take yi da Dr. Bunza na mene ne? Sannan da kwayoyin maganin da ya gani a leda babu suna babu takardar su a karkashin gadon su.
Ya yi wani irin huci mai zafi, “Akwai wata matsala wadda da alama dadaddiya ce”. Ya tuno furucin Dr. Abdullahi. A sukwane ya bude kofar ya fita ya nufi ofishin Dr. Bunza a psychiatry. Dr. Bunza na rubuce-rdubuce a file suna hira da Dr. Karaye, Dr. Sulaiman ya bankada kofar ofishin ba tare da ya yi sallama ko neman izinin shigowa ba, ya kai wa Dr. Bunza shaka ya ce, “Gara in kashe ka, kafin ka kashe ni….”.
Dr. Karaye ya soma kokarin kwatar Dr. Bunza wanda ya sha_ shaka matuka, duk idanun sun yo waje. Ya ce,
“Ba zan cika shi ba, sai ya gaya min abin da ke damun matata, da magungunan mene ne yake dirka mata?”
Dr. Bunza ya ce,
“Ka yi hakuri Dr. Sulaiman mu yi maganar cikin nutsuwa”. Ya samu ya sake shi da kyar ya koma kujerar sa yana gyara wuyan rigarshi, yayin da Sulaiman ya yi mishi kerere a kai, idanun shi a jujjuye, shi dai kawai so yake ya ji mene ne matsalar Hadiza? Dr. Karaye ya ce,
“Ka yi hakuri ka zauna Dr. Bakori, Dr. Bashir ba zai cuce ka ba…… –
Ya juyar da juyayyun idanunsa a kan Karaye,
“Akwai wata cuta wadda ta wuce wadda ya yi min? Matata na dauke da cuta shekara guda amma bai taba gaya min ba? Ya biye mata suke yi min rainin hankali, na yi kama da wanda bai je makaranta bane Dr. Karaye?” Dr. Bunza ya ce,
“Ba haka bane Dr. Bakori, ina bisa aikina ne, akwai sirri tsakanin likita da
petient din sa, wannan shi ne hujja ta. Sannan Dr. Hadiza na da tata huyar, ta boye maka cewa tana da (brain cancer) don samar maka da kwanciyar hankali, ta ce idan ka ji babu kai babu sauran kwanciyar hankali, kuma nima na yarda you are not taking things easy (ba ka daukan abubuwa da sauki). Ka bini a hankali in maka bayani”.
Ya kunna computer inda (record) din Hadiza yake yana nuna masa yadda ciwon ya ci karfin ta a yanzu, da irin taimakon da ya ba ta. Shi kan sa Bunza sai da ya yi hawaye balle gogan, wanda gudun jini ya katse a jijiyoyin jikinsa.
2K 2K 2
K
arfe shida na safe Dr. Surayyah ta fito da jaririyar da aka cirowa Hadiza, kamar ta daya da Baban ta kamar ya yi kaki ya tofar, har duhun kalar nashi ne.
A lokacin ne jama’ar gidan su Hadiza suka iso, Dr. Surayyah ta sanar da su. Fati karfe bakwai na safe ta iso asibitin, ta baro yaran da Alti ta zo a (keke-napep). Dai-dai lokacin da aka turo Hadiza za a mai da ita ICU, ya yi dai-dai da sanda Surayyah ta mika mishi jaririyar ya ki amsa, sai Fati ce ta amsa.
Za a wuce da Hadiza ta rike hannun
sister Magajiya ta rada mata cikin nishi,
“Ina son yin magana da su…..”. Don haka sister ta dakata. Sulaiman da Fati suka garzayo gareta, kowanne ya fita hayyacinsa. Fati rungume da jaririya tsantsan tana ta tsala ihu.
Itama Fatin Kukan take.Hadiza ta runtse ido hawaye na zirara, ta ce, “Fati ina alkawarin mu?”
Cikin Kuka ta ce,
“Yana nan Yaya Hadiza”.
Ta kama hannun Sulaiman ta hada da na Fati, duk su Malam Ja’afar na kallo, ta ce,
“Fati har da shi a alkawarin fa………. Ta yi sharbe ta yarfar da majina da hawaye ta ce, “In kula da shi?
Yaya Hadiza ai shi babba ne?’
“Babba ba ya _ bukatar kulawa Fati…… ?”
Ta ce,
“Ban sani ba”.
Ta ce,
“To yana bukata, shi ma kamar Munib
ne, bambancinsu shine shi Munib kulawar UWA yake nema, shi kuwa Sulaman kulawar MATA yake ne
Ta yi murmushi ta runtse idonta, cikin azabar da take dandana. Sulaiman ya russuna ya sumbaci goshinta, “You will get well soon Hadizah…… , bana bukatar kulawar kowa sai taki, in ba taki ba na yafe, zafin ciwo yake sa ki yin irin wannan magana……… Ta girgiza kai ta kara manne hannun su ta ce, “Sulaiman-Fati………… ”
Dr. Bunza ya karaso ya tura gadon da kanshi yana ta yiwa sister Magaji fada. Yaya ta karaso ta karbi ‘yar da ke hannun Fati ganin tana neman kwala ta da kasa.
Dr. Sulaiman ya mai da hannun shi cikin aljihu, yana so ya yi kuka amma idanun sun bushe kamar soyayyar gyada marau-marau. Sai Malam Ja‘afar ya iso gare shi ya kamo hannun sa suka zauna tare, yana cewa,
“Karbi ‘yar ka sa mata albarka”.
Amma Sulaiman ya ki, sai kirjin shi da ke ta kai kawo kamar zuciyar ta ballo allon kirjinsa ta fito.
Ana shigar da ita cikin computer don a yi hoton kwakwalwar ta kamin likitocin su san me za su yi a kai, ta soma ta yi salati rai bakon duniya ya yi halinsa.
“Allah ya ji kan Dr. Hadizah!”
Abin da dukkanin likitocin suka furta kenan, a lokaci guda suna share ambaliyar hawaye daga idanuwan su, tare da kai hannu su rufe mata idanun ta.
2K OK KK
A n bawa Malam Ja’afar da Sulaiman gawar Hadiza cikin mota ambulance,
zuwa nan unguwar Karkasara. Inda daruruwar jama’‘a suka yi jana’‘izar ta. Mijinta da Mahaifinta suka sanya ta a kabarin ta, suna masu yi mata addu’ar fatan alheri, yafiya, afuwa da addu’ar Allah ya yi mata masauki da aljanna, Annabi ya san da zuwan ta. Su kuma ya basu imanin jurewa.
Sulaiman ya baiwa kowa mamaki, saboda yadda ya tsaya a kan jana’izar Hadizah, babu ko digon hawaye a idanunsa. Ba su san shi kansa kukan na zuwa ne idan an san abin da ake yi ba. To bai san me yake yi ba, bai san halin da kwakwalwarshi ke ciki ba.
Ya san dai kawai Hadizar sa ta rasu, sun kaita makwancin ta na gaskiya, bayan wannan bai san komi ba, bai san kansa ba, bai san a ina yake ba.
Ya dai bude ido ya gan shi a gidan su Hadizah, dakin Mukhtar, ba ya rintsawa, yadda ya ga rana haka yake ganin dare, ya wuni yana_ karbar ta’aziyyar ‘yan uwa da abokan arziki.
Tun a ranar Inna Halima, Malam Sulaiman da sauran kannen shi suka zo Kano, da su ake karbar gaisuwa har zuwa kwana uku.
Ranar lahadi suka juya Bakori cike da juyayin halin da Sulaiman ke ciki. Malam ya ce zai dinga aiko mishi da rubutu tsayin kwana bakwai. Ya ce, “To”. Wadda ta zama kalma mafi saukin fada a bakinsa, sai kuma bin kowa da ido, amma abinci da ruwa wannan kwanan shi uku bai dandana su ba.
Alti ma tana gidan ita da yara wadanda suka damu kowa da tambayar ina Momin su? Alhamis aka yi sadakar uku, Alti ta koma kauyen su tana kuka da hawayen ta, ta ce sai ranar sadakar arba’in za ta dawo.
Tambaye ni ina baiwar Allah Fatima Ja’afar Mai-Yadi? Tana can dakinta tana kuka, tana fama da jaririya, bini-bini ta hada madarar (SMA) ta dura mata, ta ba ta ruwan
zam-zam. Ba ta barin ta tayi kuka, idan ta bata madarar da ruwan sai ta sa ta a baya ta goye, ta zauna ta yi ta jijjiga ta, har sai ta samu barci, ta sakko ta ta sanya ta a gadon ta, ta zauna a gabanta ta yi ta girka kuka. Idan kukan ya ishe ta sai ta bude littattafan addu’o’in ta, ta yi ta karantawa tana rokon Allah ya kai ladan makwancin rabin jikin ta Dr. Hadiza Ja’afar MaiYadi.
Mutuwar Hadiza ta girgiza kowa a gidan nan, haka duk wanda ya santa ya koka ya gode Allah. Kada Dr. Surayyah ta ji labari, to ina ga wanda farin cikin rayuwar sa ya ta’allaka a wuyan ta? Ya ke kwana da ita yake tashi da ita, yake yi mata son da ko iyayen ta sai dai su ce su suka haife ta?
Don haka Doctor Sulaiman-Sulaiman Bakori, yana cikin wani irin hali da duk masoyinsa dole ya koka masa, in har yana da imani, ya bishi da addu’ar
Allah ya ba shi dangana da YAKANAH!
Tuni Mukhtar ya koma Kaduna, ranar da aka yi bakwai shi ma Malam Ja’afar ya ce ya koma bakin aikin sa. Ya bishi da “To”. Kamar yadda yake bin kowa da ita.
Ya tattara ya koma gidansa, shi kadai kwal kamar maye. Sai da ya gwammace da bai dawo ba, a lokacin da ya ci karo da wheel chair din Hadiza da kayan ta dake watse a dakin barcin su, a nan ne komi ya dawo masa danye, karo na uku da ya soma kukan da ya tabbatar har abada ba zai daina ba.
Haka ya kulle kansa, ba shi da abinci sai ruwan lipton wanda yake dafawa a kettle ya dura a flask ya wuni yana sha, babu ko tunanin sa sukari.
Cikin kwanaki ashirin da mutuwar Hadiza ya zama babu kyawun gani, kasumba ta cika fuskar sa. Duk wannan gayun ya daina shi, wanka ma ba kullum yake yi ba sai ya ji alamar
jikin shi na dan wari-wari, ya kashe wayoyinsa gaba daya, ya yi sallama da aikin sa, amma bai fasa kwana yana yiwa Hadiza addu’a ba.
Uwa, mahaifiya, duk ta rasa sukuni, tana can Bakori, hankalinta na Kano, ta san cikin kowanne hali Sulaiman yake yana cikin halin da yake neman matallafi. Kuma cikin halin da yake bukatar mai tausar sa, nuna masa kauna da kulawa.
Don haka yau ta tambayi Malam Sulaiman cewa za ta taho Kano wajen Sulaiman. Ya ce hakan ya yi.
Yana zaune a falo, daga shi sai wata dukunkunanniyar jallabiya ruwan makuba, da kofin ‘tea’ a hannun shi da ‘remote’ yana_ = kallon _tashar Saudiyyah, inda suke gabatar da sallar magariba. Aka danna kararrawa wajen sau biyar kamin ya yunkura ya aje kofin a kan side table ya bude kofar. Inna Halima ce tsaye cikin atamfa holland ta sha lullubi da koren mayafi
kalar atamfar ta, har ranshi ya ji dadin ganin ta, ya ba ta hanya ta wuce cikin falon, ya tsuguna ya gaishe ta.
Ba ta amsa ba sai kallon shi take cikin al’ajabi, “Haka ka lalata kanka Sulaimanu saboda Allah? To wannan rashin tawakkalin da kake shi zai dawo da Hadiza duniya ko me?
Ka sani Hadiza ta riga ta koma ga mahaliccin ta, ba za ta taba dawowa ba, ka fuskanci rayuwar da take jiran ka a gaba, ka zamo mai YAKANAH cikin duk halin da ka tsinci kanka.
Tsakanin ka da Hadiza yanzu addu’a ce, ba wannan lalata rayuwar ba. Idan Hadiza tana raye, ba za ta so ganin ka haka ba, ka yi hakuri mai sunan Malam. Shin yaushe rabon ka da cin abinci?’
Ya sunkuyar da kai bai yi magana ba. Ta jawo ledar da ta shigo da ita ta fiddo ma’adanan abinci guda biyu, ta bude ta tura masa, tuwon shinkafa ne lafiyayye da miyar taushe ta ji nama zuku-zuku, ta ce,
“Cinye maza ka bani kwanon”.
Ba musu ya dauka ya soma ci kamar Allah ya aiko shi.
Inna ta mike ta soma tattare bolar falon, ta share shi tsaf, ta shiga dakunan ta gyare ko ina, ta wanke masa toilet. Sanda ta gama ya dade da yin barci a carpet, ta zauna a gefen kansa tana tofa masa addu’a.
Yana tashi ta ba shi rubutun da ta zo da shi cikin jarka ya sha, ya mai da kai kan tuntun ya koma barci. Bai tashi ba sai la’asar, ta je bandaki ta hada mishi ruwan wanka cikin kwami, ta dawo falon ta same shi ya idar da sallar la’asar, ya mike kafa yana kallon ceiling, ta tsuguna a gabansa ta ce,
“Tashi ka je ka yi wanka, ka shirya muje mu ga mai sunan Hadiza”. Wannan karon ma bai yi musu ba, ya mike ya je ya yi wankan, ya zubo farar shadda dinkin Mohammed, ya dora hula fara sol amma bai fesa turare ba, ya fito ya tadda Inna ta idar da sallah tana lazimi. Ta yi addu’a ta shafa, ta
mike suka fito harabar adana motoci, duk motocin sun yi kura futuk! Alamar an dade ba a taba su ba.
Ya sa key ya fiddo motar dai-dai inda Inna take, Malam Ilu ya karaso da sauri ya gaida Inna, ya sa ‘duster’ ya karkade motar cike da jin dadin ganin yau Ubangidansa ya fito, wanda yake kwana cikin wannan gida shi kadai ransa, sai dai yana tausaya masa, don ya san rashin matar kwarai kamar Dr. Hadiza ba karamin abu bane.
Inna na baya shi kuma yana tukin suka nufi unguwar Karkasara. A dai-dai titin asibitin AKTH kamar an ce da Inna ta juya, ta hango Fati rike da hannun Munib da Muniba cikin kayan makaranta tana tare tasi, da alama ta dauko su ne daga makaranta.
Da sauri Inna ta ce,
“Ka ga Fati can tana tare mota, yi kwana mu dauke su”. Ya yi kamar bai ji ba, ya karawa motar shi gudu. Inna ta yi salati ta ce, “Baka ji ni bane? ‘Ya’yan ka fa ta dauko daga
makaranta!”.
Sai a sannan ya juya, tuni ta tare tasi suna kokarin shiga. Ya ce, “Ai sun shiga mota ma hadu a can”. Inna ta yi shiru tana mamaki, har suka iso gidan su Fati ba su shigo ba, don ba za ka hada motar gida da ta haya da ke yin tsaye-tsaye ba.
Tun daga soron gidan yake jiyo kukan Baby Nana Khadijah. Ya rintse ido tsigar jikinshi na tashi. Inna ce ta yi sallama ya biyo bayan ta. Yaya suka tarar tana ta fama da Baby Nana, wadda ke ta tsandara kuka kamar ta tsaga gidan ta ki karbar madarar da take bata.
Ta amsa musu sallama cikin sakin fuska da walwala, ta shimfida musu sabuwar tabarma, sannan ta mikawa Inna Baby Nana. Yaya ta dubi Sulaiman ganin yadda ya rame ya yi kasumba, sai ta ji hawaye sun ciko idon ta.
Ta ce,
“Me nake gani haka ni Sa’adatu? Su