YAKANA BOOK 2 CHAPTER 1 BY SUMAYYAH ABDULKADIR

 YAKANA BOOK 2  CHAPTER 1 BY SUMAYYAH ABDULKADIR

Karfe goma sha dayan dare garin Kano ya yi tsit, sai iskar hunturu da ke kadawa. Malam Ja’afar ya dauko tabarmar sa ya shigo cikin gida daga soron kofar gida. 

Zai gifta ta dakin Fati ya jiyo shesshekar kukan ta, ya dakata ya daga labulen yana kallon ta, tana zaune a kan darduma ta kunshe fuskar ta cikin hijabi sai kuka take. 

Ya karasa shigowa cikin dakin ya ce, “Fadimatu kukan me kike yi?” 

A razane ta cira kai ta dube shi idanunta jawur, sun yi luhu-luhu alamar ta yi kuka har ta gode Allah. Malam Ja’afar ya zauna a wata ‘yar kujera da ke dakin yana fuskantar diyar sa. Nanah ta soma motsi alamun za ta tashi daga barcinta, ta soma ritriga ta.

 

Ya jima bai yi magana ba sai da Nana ta koma barcin ta ya ce, 

“Gaya min damuwar ki Fadimatu, ni mahaifin ki ne”. 

Ta share idon ta da hankici, ta ja shessheka kafin ta ce, 

“Baba babu komi”. 

Ya jima yana kallon ta, sannan ya yi murmushi ya ce, 

“Kina tuhumar mu da yi miki auren da baki so, auren mijin ‘yar uwar ki. Ki yi hakuri, alheri muke nufin ku da shi, ba za ku gane ba sai nan gaba, idan kun gano gatan da muka yiwa rayuwar ku”. 

Fati ta yi shiru tana sauraron Baban su, ta ga cewa wannan ita ce damarta ta karshe, daga gobe Za a zarga mata igiyoyin wanda ba ya son ta. Ta kai kanta kasa tana kuka sosai, ta ce, 

“Ku yi min alfarma Baba, Baba baka tava sani in yi wani abu na shallake maganar ka ba, amma a wannan karon ina so ka duba hujjojina. 

Baba Dr. Sulaiman ba ya sona, Baba Dr. Sulaiman ya fi karfina, bani da ilimin da zan jera da shi a matsayin matarsa. Baba Sulaiman ba zai tava son wata ba, bayan son da yake yiwa Yaya Hadiza. Baba kune baku sani ba, amma Dr. Sulaiman ya tsane ni, ban san laifin da na yi masa ba. 

Ban tava gaishe shi ya amsa ba, haka bai tava duba na a matsayin jinin Hadiza ba, balle ya yi Ja’akari da wannan ya kaunace ni. In dai don ‘ya’yan shi ne ai nima ‘ya’yana ne, zan ci gaba da rike su ba sai na zama matarsa ba”. 

Ya ce, 

“Amma za ki zama matar wani ko? Kuma babu wanda zai aure ki da zugar ‘ya’yan Yayar ki? Da ‘yar uwarki ta damka miki amanarsu? Na ji hujjojin ki Fati, amma nima ina so in tambaye ki. Wane abu ne Hadiza take da shi wanda ya kaita ga matakin zama matar babban likita irin Sulaiman? Tana ‘yar talakawa kamar ki?” 

Babu dogon tunani ta ce, 

“Timi”. 

Ya ce, 

“A ina ta samu?” 

Ta ce, 

“Fita ta yi ta nema”. 

Yace, “In haka ne ke mai zai hana kema ki fita ki nema?’ 

Ta ce, 

“Ba zan iya irin nata ba!” 

Ya yi murmushi ya ce, 

“Duk ilimi sunan sa ilimi, balle ilimin ki ya fi na kowa, ilimin Alkur’ani ne da ke wanda ya kunshi dukkan rayuwar duniya da lahira baki dayan ta, ke din nan ba abar wulakantawa ba ce ‘yar baiwa ce, mahaddaciyar Alkur’ani, wallahi-wallahi a rayuwar duniya da lahira ba za ki tozarta ba. Sannan don kina gaishe shi bai amsa ba, sai ki ce ba ya son ki? Me kika yi masa? Mutum ne mai kyakkyawar zuciya, shekaru dai-dai har bakwai da nayi tare da shi ban tava ganin wata halayya ta banza a tare da shi ba. 

Tunda ya auri ‘yar uwar ki ba’a tava jin kansu ba, ba ta tava yin yaji ba, ba ta tava kawo karar shi ba. Sai ki yi tunanin me Hadiza ta yi ta samu 

mafificiyar soyayya a zuciyar mijinta, tunda kin zauna da ita, kema ki yi ki gani idan ba za ki samu ba?”. 

Ta share ido ta ce, 

“Baba ai ni gani na yake ‘yar kauye, ga shi ni kuma ba zan iya yin irin rayuwar su ba. Mai ya sa ba za ka gane ba? Don Allah Baba ka aura min ko wane ne, komi yawan matansa da yawan shekarun sa, na rantse zan zauna da shi, amma kada ka kai ni inda ba zan yi kwarjini ba, inda za a wulakanta ni, inda ba za a so ni ba….”. 

Ya yi murmushi ya ce, “Babu inda zan kai ki sai gidan SULAIMAN! Na kuma tabbatar miki ko a yanzu bai son ki, watarana na zuwa da za ya so ki. Kamar, ko ma fiye da yadda yake son ‘yar uwarki. 

Daina kukan nan kada ya haddasa miki ciwo, a duk sanda ki kai sujjada cikin sallolin farilla ki ce, “Allah ka sanya soyayyata a zuciyar mijina”. Za ki sha mamaki Fadima, ki sanyawa zuciyar ki salama, shi da yake namiji bai bijirewa iyayen shi ba sai ke? A’a kada mu yi haka da ke Fadimatu, na san ki, na san halin ki, na tabbata ba za ki bani kunya ba. 

Ki yi min alkawarin za ki zauna lafiya da mijin ki, ki yi min alkawarin za ki yi mishi biyayya, ki yi min alkawarin za ki ba shi soyayya irin wadda shakikiyar ki ke ba shi, ki yi min alkawarin ba za ki tava kai karar shi wani waje ba, ke ko mu din nan ban yarda ki kawo karar shi gare mu ba, balle iyayen shi. 

Duk abin da ya yi miki na rashin dadi ki yi 

hakuri, ki yafe mishi cikin zuciyar ki, ki yi mishi uzuri. Wannan halin YAKANAH kenan! Sakayyar ki na wurin Allah!!”. 

Tana kuka sosai ta ce, “Na ji Baba, kuma na yi maka alkawari”. 

Ya dora hannu a kanta, 

“To Allah ya yi miki albarka, ya ba ki juriyar rike ‘ya’yan ki, ya sa suma mahaddata alkur’ani ne kamar ki. Tashi ki dauro alwala ki ci gaba da neman yardar Allah da yardar mijin ki”. 

2K ok kk 

D r. Sulaiman yana tuki amma hankalinsa ba ya jikinsa, in banda tafasa babu abin da zuciyarsa ke yi, amma kamar wanda aka dinkewa baki ya kasa ce da iyayen shi komi wadanda ke ta hirarrakin 

su a kan karamcin iyayen Hadiza. 

Har suka iso gida ya kai su vangaren da ya tanada don bakin kwana, wanda ke daga wajen gidan. Inna kuma ta wuce dakin da yake na Hadiza. 

Ya fada toilet ya yo wanka, yana alwala cikin sink sai jini ya valle mishi ta hanci. Haka ya tsaya yai ta kwararar da havon, yana bin shi da ruwa. A duk lokacin da yake cikin takurar zuciya havo yake yi, ya soma yiwa kanshi taimakon gaggawa har jinin ya tsaya. Ya fito ‘bed room’ din su wanda ya zama kaca-kaca saboda rashin gyara, ya dauko wata rigar barcin Hadiza ya kwanta rigingine, ya dora rigar a kan fuskar shi yana shakar kamshin Hadizah na dindindin na turaren ‘escada-sentiment’. So da kaunar matar shi ke dawainiya da shi. Ya lumshe ido ya shafo makwancin ta, katon fili ya yi mishi sallama, wasu irin dumammun hawaye, suka mirgino ta gefen idon sa. 

A sannan ne tunanin shirmamman auran da za a yi mishi a gobe ya dawo mishi cikin kwanya, Eh! Shirmamme mana, don bai dauki wannan auren da sunan aure ba. 

Amma a yadda Inna da Malam suka sanya ransu da zuciyar su a auren nan in ya ce baya yi ya tabbata zai vata goma ne daya ba ta gyaru ba, don za su yi fushi da shi, sannan kuma ba za su fasa ba. Don Malam bai yin magana biyu, sannan ransu za ya vaci, kuma ba za su tava shiryawa da shi ba. 

Don haka maganar ya je ya ce da Inna bai yarda ba, ko bai amince ba, kamar yadda zuciyar shi ke 

ta kimsa mishi ba ta ma taso ba. Illa ya zuba musu ido su yi yadda suke so. 

Sai dai ya san yadda suka kawo yarinya, haka za su zo su dauki abar su. Shi mijin mace daya ne a duniya da lahira (Hadizah). Bayan ita bashi da sauran bukatar komi daga jikin kowacce diya mace, balle kanwarta duk da Allah ya halarta, amma ai da kunya, ya hada rayuwa da kanwar Hadiza, balle wannan yarinyar da bai san irin ta ba, sannan Allah subhana bai halicci zuciyar sa da kaunar ta ba. 

Ba kilin (clean) ba isasshen wanka a jikinta, balle aje ga ado irin na ‘ya’ya mata. Kullum cikin tsummokara! Yo tsummokara mana? Kyawun surar ta ya tashi a banza tunda ba ta san yadda za ta yi ta gyara kanta ba. 

Shi duk ma ba wannan ya dame shi ba, kawai ranshi baya son Fatima Ja’afar, duk da kasancewar ta kanwar Hadiza. Jikinsa ya sha ba shi akwai wani al’amari mai GIRMA tsakanin shi da yarinyar, tun daga sanda ya fara ganin ta, amma bai tava kawowa cewa aure ne ba. 

Yadda Fati ta kwana ido biyu, haka Dr. Sulaiman ya kwana ido biyu, kowannen su zuciya na zugi. Sai dai ita Fati ba ta kin al’amarin musamman in ta tuna da alkawarin da ta daukar wa ‘yar uwarta. Damuwar ta shi ne Sulaiman ba ya son ta, da dan karen tsoron zama dashi dankare a zuciyar ta. 

Shi kuwa tunanin yadda zai yi ya tsallake auren yake ba tare da ya vatawa iyayen shi ba, ya san a 

sake dai bai isa ya ce ya saki ba. Daga karshe ya yanke wa kansa shawarar da yake ganin ita ce za ta fissheshi. Don haka ya dan samu sa’idar da ya kwanta ya runtsa idon sa. 

Kwanciyar sa ke da wuya aka soma kiraye-kirayen sallar asubahi. Ya dauro alwala ya gabatar da raka’atainil fijri, kamin ya dora da farillar. Ya yi addu’o’in shi ya koma ya kwanta. 

Zuwa bakwai ya tashi ya feso wanka ya debi 

koriyar Gezner sabuwa kar sai sheki take, ya fesa turare ya zuba hular kube, ya fito kamar saurayi dan shekaru ashirin da bakwai, ba za ka ce shi ne ya aje su Munib ba, zuciyar shi wasai da hukuncin da ya yankewa zuciyar shi. Ya fito ya janyo kofar ya iso falo, nan ya tarar da Inna ta hada musu kalaci, kunun gyada da dafadukan taliya, kasancewar a gurguje ta yi. Ya je ya shigo da su Malam suka yi kalacin gaba daya. Daga nan suka nufo Karkasara. 

Kofar gidan Malam Ja’afar ya cika makil da jama’a wadanda suka zo addu’’ar arba’in din Dr. Hadiza, aka rarraba picies na alkur’ani aka yi mata sauka, aka yi addu’o’i na musamman. 

Daga nan kafin mutane su watse, waliyyai suka gabatar da daurin auren Dr. Sulaiman Sulaiman Bakori, da Fatima Ja’afar Mai-Yadi, a kan sadaki naira dubu ishirin kacal. Mutane suka yi ta mamaki tare da sanya albarka, domin an yi koyi da fadar ma‘aiki (S.A.W). 

Malam Ja’afar ya dubi Inna Halima ya ce, “Babu 

bukatar wata bidi’a, gobe Sulaiman ya zo ya dau matarsa da ‘ya’yan shi su tafi, Allah ya yi musu albarka”. 

Fati da ke uwar dakin Yaya tana jin duk abin da ke faruwa a gidan, ta takure a bayan labule sai gursheken kuka take, goye da ‘yarta sai makyarkyata take. Ta rasa inda za ta sa ranta ta ji dadi, shin rayuwarta da wadda za ta je ta tarar wace irin rayuwa ce? Shin meye makomar rayuwar ta? 

Ta tabbata, kuma a ko’ ina za ta yi rantsuwa a kan cewa Sulaiman bai son ta. Takura mishi aka yi. Yaya Hadiza ta dora mata nauyi da kananan shekarun ta ba za su iya sauke wa ba. Amma in ta tuno nasihar da Baban su ya yi mata a daren jiya, sai ta ji sanyi a ranta. 

Jin Inna na neman ta, ta yi saurin shigewa toilet. Inna ta daga labule ba ta ganta ba, ta ce da Yaya “bata nan, watakil ta shiga bayi”. Daga nan suka ci gaba da hira ita da Yaya a kan maganar lefe, ta ce za ta sa su Ruma su hado ko gidanta ne a kai mata. 

Yaya ta kafe a kan cewa wallahi sun yafe, ko tsinken Sulaiman ba za su karva ba. An riga an zama daya sai dai su bi yara da addu’a. Amma Inna ta kudire a ranta sai an yiwa Fati lefe irin wanda ake yiwa kowacce yarinya budurwa. 

Sai da su Inna suka bar gidan sannan Fati ta fito daga mavoyar ta, makota na ta shigowa suna yiwa Yaya ta’aziyya da Allah ya sanya alheri. Ta nufi dakinta ta shimfidar da Nana, sannan ta kwanta a gefen ta ba laka a jikinta. 

Yaya ta shigo rike da kwanon silba da damammiyar fura mai sanyi, ta zauna a gefen ta tana kallon yadda duk ta zuge kwana daya kacal. 

Ta ce, “Ungo fura tashi shanye ki bani kwanon”. Ta girgiza kai, “Bana son cin komi”. 

Yaya ta ce, 

“Haka za ki daure ki dura, zama da yunwa da vacin rai ba naki bane, tunda dai auren nan an riga an daura ya kuma dauru, sai ki saki ranki ki watsar da duk wani tunani wanda zai hana miki kwanciyar hankali. Karvi na ce”. 

Ta tashi zaune ta amsa, ta kafa kai tana sha tare da kokarin maida kukan da ya taho mata a dalilin furucin Yaya, “Aure ne an riga an daura kuma ya dauru….”. Wato dai da gaske ta zama matar Dr. Sulaiman mijin Yayarta. 

Sai da ta shanye furar ta share hawaye da ‘yan yatsunta, Yaya ta ce, “Kukan dai? Sai ki yi ta yi tunda kin ga shi zai fisshe ki. Haba, ayi yarinya da shegen kuka kamar Muniba? Yanzu ki tashi ki je ki yi wanka, ki sa kaya masu kyau ki je a wanke miki wannan dankararren gashin naki da yau kwana arba’in ba ki tsefe shi ba. Ko ni uwar Hadiza ban takura rayuwata yadda kika takura taki ba. Gobe za su zo su dauke ki, don Allah ki dan gyara kanki yadda za ki yi kyan gani, ki aje hijabin nan haka ki yiwa mijinki kwalliya…….” 

Ai kuwa sai ta valle da kuka, “Ni wallahi ba inda za ni, ni wallahi bana son sa……….. Yaya ta bige mata baki ta ce, 

“Don Allah in an kaiki ki sha poison kema ki mutu, ba zan kasa rayuwa ba!!!”. 

Ta juya ta fita. 

Ta tabbatar ran Yaya yai matukar vaci tunda har ta yi wannan furucin, tana kuka ta taso ta biyo ta dakinta, tana zaune a kujera ta yi tagumi. Ta zube a gabanta ta kama kafarta cikin rishin kuka ta ce, 

“Don Allah Yaya ki yi hakuri ki yafe min, wallahi ba zan kara ba”. 

Ta ce, “Ni me ki kai min da za ki bani hakuri? Ke aka yiwa laifi ke za a bawa hakuri. Me kika fishi ko me kike takama da shi da za ki ce bakya son sa? Ban da Allah ya kashe ya baki ai Sulaiman ba tsaran ki bane, ba za ki gano gatan da aka yi muku dukkanin ku ba sai nan gaba. Wannan shi ne karshen kauna da za ki nunawa Hadizah, ki rungumi iyalinta a bayanta, sai dai in dama ba son ta kike yi ba…….. 1” 

Ta kara sautin kukan ta, 

“Na tuba Yaya, na bi Allah na bi ku, na yarda zan zauna da Baban Munib ko ba ya so naa…….” 

“Shi ya ce miki ba ya son ki? Bana son mummunar fahimta, ko bai miki son soyayya ta aure ba, yana yi miki son ‘yan’uwantaka, wadda a hankali in kin sadaukar da kanki gare shi za ta rikide ta koma soyayyah!. 

Sanda aka aura min mahaifin ku ban san shi ba, ban tava ganin sa ba. Haka aka lulluve ni aka kawo ni, ko sunana bai sani ba nima ban san nashi ba. Amma kyautatawa da sadaukar da kai ya sa a yau ba abin da muke so da kauna sama da junan mu, har muka kai ga haifar ku daya bayan 

daya. Kina gani har yau bai tava yi min kishiya ba, bai tava vata min rai ba sai bisa kuskure. Vacin raina na nufin tashin hankalinsa, fushina na nufin tavarvarewar al’amuransa. Ki yi auren BIYAYYA ba SOYAYYA ba ki ga wacce irin riba za ki samu a cikin sa? Idan mun san babu riba ba zamu ba ki jarin ba”. 

Fati ta share hawayen ta, cikin zuciyar ta tana cewa, mazan da dana yanzu ai ba daya bane Yaya! Balle wadannan da suka hantse cikin ilmummukan zamani masu gigitarwa, suka saba ganin mata iri-iri dai-dai da rayuwar su. Ina zan iya burge shi balle har ya kaunace ni? Ina zan iya mai da kaina irin Yaya Hadiza? 

Yaya ta yi murmushi irin na manya wadanda suka san cewa ciwon ‘ya mace na ‘ya mace ne, sarai ta gane abin da Fati ke nufi; Hadiza ‘yar gayu ce, kuma wadda ta gogu cikin zuzzurfan ilimin boko, ita kuwa ‘yar Islamiyyah ce, wadda Allah da Annabi sune kawai a gabanta, wato dai ita ‘yar Arabiyyah ce wadda ta horu ta goge cikin ilmummukan addini daban-daban da fadin Allah da manzonsa. Wadanda ‘yan bokon irin su Sulaiman ke wa kallon ‘yan kauye, wannan banbancin a farrake yake. 

Tace, 

“Fati kowacce mace da kika gani da kissarta aka haife ta, sannan kowacce da yadda Allah ya halicce ta. Sai dai ra’ayi da akida sun banbanta. Amma fa duk sunan su daya (MACE), kuma abin da ke jikin wannan shi ne a jikin waccan, ba 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *