YAKANA BOOK 2 CHAPTER 2 BY SUMAYYAH ABDULKADIR

 YAKANA BOOK 2  CHAPTER 2 BY SUMAYYAH ABDULKADIR

wadda ta fi wata a matantakar sai dai ko kazama da mai tsafta. 

Fati ke mai tsafta ce, har a makaranta tun daga firamare har sakandire an fahimci tsaftar ki an kuma sha baki kyauta a kanta. Wannan kadai kika rike jigo ne a gidan aure, kuma ya ishe ki ki yaki zuciyar kowanne da namiji ba Sulaiman kadai ba. 

Kamar yadda kika ce baki da abin da za ki burge Sulaiman sai in ce a’a, Fati kina da shi, HANKALI da sanin CIWON KAI sune manyan halayen da ke burge namiiji……… Fati ta dago ido tana kallon mahaifiyar ta, “Yaya kina nufin Baban Munib bai fi karfina ba?” 

Yaya ta yi murmushi a karo na uku, ta ce, “A doke kam idan za ku gabza ai ya fi karfin ki, amma a zaman aure bai fi karfin ki ba. Tunda kema mace ce kamar Hadiza, kuma a hakan da kike ba sai kin yi wata kwarkwasa ko kwalisa Sulaiman zai so ki ba. A‘’a, maintain your own kualities (rike taki sigar). 

Kwalisa, kwarkwasa da yanga ba sa burge namijin da ya san ciwon kansa, sai hankali, ilimi da sanin ciwon kai. Wadanda dasu ne Hadiza ta samo zuciyar Sulaiman ba appearance (kamantuwar ta ba). 

Saboda haka Fati ki kwantar da hankalin ki, ki yi biyayya ga mahaifin ki, Alkur’anin ki, ba zai bari ki tozarta a rayuwa ba…..!!”. 

Ta mike ta yi murmushi cike da jin dadin kalaman mahaifiyarta, ko ba komi ta ba ta kwarin gwiwa cewa, itama mace ce kamar sauran mata 

ba mata ta rako duniya ba. 

Ta cire mata inferiority compled, har ta ji za ita iya jure duk wani hali da za ta tsinci kanta ko daa ce hasashen Yaya ba su zamo gaskiya a kan nata al’amarin rayuwar ba. 

Da kanta Yaya ta zaunar da ita a gabanta, ta sa kibiya ta tsefe mata gashin kanta da ya yi masifar dauda ya duddunkule saboda rashin gyara har tsayin kwanaki arba’in da biyar. Fati sai yawan gashi amma babu tsayi irin na asalin Kanawa, sannan ga shi da karfi kamar reza, sabida ba ta tava shafa mishi relader ba, da za ta shafa mishi din da ya mike ya zama mai ban sha’awa. 

Fa’iza ta yi sallama ta shigo tana cewa, “Wai da gaske ne abin da nake ji?” Ta tsuguna ta gaida Yaya ta amsa. Fati na hararar ta ta sake cewa, “Don Allah Yaya da gaske ne? Yau an daurawa Fati aure?” 

Yaya ta yi murmushi ta ce, 

“Eh, haka Allah ya nufa””. Ta ce, 

“To, Allah ya sanya alheri”. Yaya ta ce, “Amin”. 

Fa’izah kawar Fati ce, tare suka yi makarantar kwana a G.G.C Kano, kuma gidansu nan cikin layinsu yake babu nisa zuwa gidan su Fati. 

Yaya ta ce dama yanzu zan tura Abdulyassar ya kirawo ki, ki zo ki rqaka ta wajen wankin kai, na san in na bar ta a haka za ta tafi gidan mijin. Daga nan ku biya ayi mata kunshi”. 

Fa’iza ta ce, “Gaskiya kam, kawo in karasa mata tsifar”. 

A daren sai ga kannen Dr. Sulaiman da wata kan

war Inna sun kawo akwatuna hudu shake da kaya, ga shi ba su gayawa Yaya za su kawo ba balle ta tara masu karva. 

Ta kama baki ta ce, “Yanzu Allah sai da aka takura Sulaiman da yin lefen nan yana fama da halin da yake ciki?” 

Ruma ta ce, 

“Ai babu komi, abune da idan ba mu yi ba, ba zamu ji dadi ba”. 

Yaya ta ce, 

“To Allah ya amfana, ya sa an yi a sa’a, ya kuma tabbatar da alherin da aka kulla, amin”. 

Fati kwana ta yi sallah, in ‘yar ta yi kuka sai ta dakata ta kula da ita har ta koma barci, sannan ta ci gaba, Cikin sujjadarta tana mai rokon Allah koma mene ne zai zo cikin rayuwar ta ya zo mata da sauki. 

Washegari ko tsakar gida ba ta leko ba, don gidan ya cika da ‘yan uwan Yaya da dangin Malam, saboda kowa da Hadiza a zuciyar sa babu wanda yake yin hayaniya. 

Karfe uku na rana Fa’iza ta kawo mata kayan da za ta sanya, wani leshi mai taushi rawan zuma da kananun stones da ta kai Diallo (Zoo Road) aka yi mata dinki edpress, amma ya yi kyau sosai, ya amshi dan karamin jikinta. 

Fati siririya ce, kuma ba ta kai tsayin Hadiza ba, komi na halittar ta (natural) kamar fata, gashi da hakora yiri-yiri, kuma farare kal wadanda ba ta wasa da kuskure su da listerine (mouth wash) a duk lokacin da ta goge su. Shiyasa suke farare 

tas, kamar kankara 

A can gidan Sulaiman shi ma cike yake da nashi ‘yan uwan, suna ta gyare-gyare, suka gyara gidan tsaf, dama tuni an kwashe kayan Hadiza har gadaje da (wardrove) an valle an fitar dasu an kai gidansu. 

Malam Ja’afar ya ba da daki guda aka kulle su, Inna tasa aka sayo katuwar katifa aka aje a dakin da a yanzu ya zama mallakin Fati kamin a yi mata jere. 

Kai! Rayuwa!! Ran dan adam ba a bakin komai ba, kowa ganin al’amarin yake kamar almara, masu yiwa Hadiza addu’a na yi, masu kokawa na yi, masu korafin anyi gaggawar yiwa Sulaiman wani aure na yi. Amma a bayan idon Inna, don kowa ya san irin son da Sulaiman yake yiwa Hadiza. 

Shi kam bai ma gidan yana asibiti tun safe, ya kama wayoyin shi ya kulle kada Inna ta neme shi. Don a daren jiya ta shaida mishi wai shi zai je da kanshi Karkasara ya dauko Fati da yara, shi kuma ya kudire in har shi zai yi hakan, to wallahi sai dai idan ba za ta zo gidan ba. 

Zuwa karfe hudu ran Inna ya soma vaci da rashin samun Sulaiman a waya, sai dai ta yi mishi uzri. Ta sani sarai sun takura shi, wanda su sun tabbatar abin alheri suka yi, sun gyara zumuncin su da iyayen Hadiza, sun kawo wadda za ta rike ‘yan jikokin su da gaskiya, sannan sun aura mishi mai kama da Hadiza, kuma shakikiyarta. 

Akwai gatan da za su yi mishi da ya wuce wan

nan? Ta kudurce a ranta za ta tsayawa Fati da addu’a da yakin zuciyar Sulaiman har sai ya so ta kamar yadda yake son ‘yar uwarta. 

Don haka sai Inna Talatuwa kanwar Malam da su Ramatu ne suka taho dauko amaryar a motar mijin Ruma, don motar shi da ita ya fita, ta Hadiza tuni an sayar sai ta amfanin gida rufe cikin tampol. Cikin girma da mutuntawa aka basu amarya. Yaya ta ce a bar mata yaran bayan sati daya za a kawo su. 

Ruma ta ce, 

“Yaya baki yiwa Fati nasiha ba”. 

Ta yi murmushi ta ce, 

“Duk nasihar da zan yi mata na yi mata jiya, Al

lah ya sa ta je a sa’a”. 

A dakin Malam Jaafar kowa ya fita ya bar su, ganin irin kukan da Fati ke yi kamar ana zare mata rai sai zuciyar shi ta motsa. Ya ce,. “Fadimatul-Zahra’u, ki daina kuka, ban aurar da ke ba sai a hannu na gari, hannun dana san cewa ba zan tava yin dana sani ba”. 

Har aka iso gidan, wanda ba bakonta ba ne tana tauna maganar Babanta, me ya sa Yaya da Baba suke son Dr. Sulaiman haka? Me ya sa kowa ya budi baki kyakkyawan kalami yake yi a kanshi? Me ya sa ita ba ta ganin kirkin nashi da nagartar tashi? Kenan ita kadai yake yiwa rashin kirki, to laifin me ta yi masa? 

Babu wanda zai ba ta amsar sai Sulaiman din kansa, wanda ta tabbatar har abada ba za ta ji am

sar ba in har sai shi din ne zai amsa mata. 

Inna ta tarbe su ta rungume ta, ta kama hannun ta har dakin da a yanzu ya zan mallakin ta, ta aje ta a bakin katifa. Fa’iza da Karima kawayenta na gefen ta, wannan ya shigo wannan ya fita, amma ita tunanin ta ya tafi ga Baby Nanah wadda ta baro a wajen Yaya, ta shaku da yarinyar sosai ta yadda har take mantawa cewa ba ita ta haife ta ba, ta alkawartawa ranta za ta roki Inna ta karvo mata ita gobe ba za ta iya yin kwanaki bakwai ba tare da ita ba. 

Zuwa karfe goma na dare gidan ya yi shiru, masu tafiya sun tafi, masu gajiya sun kwanta barci. Su Fa’izah duk sun tafi, Inna ta shigo dakin rike da kulolin abinci guda biyu, ta ce, 

“Kin yi barci ne Fati?’ 

Ta mike zaune rike da carbi a hannun ta, ta ce, “A‘ah”. 

“To tashi ga abinci ki ci, tun dazu na so in kawo miki na san ba za ki iya ci cikin mutane ba”. 

Ta mike zaune ta karva, jellop din cous-cous ne wanda ya ji kayan lambu a filas din farko, sai farfesun kayan ciki da ya ji kayan kamshin gargajiya a daya filas din. Inna da kanta ta zuba mata ta soma Ci. 

Inna na kallon ta cikin tausayi, ganin yadda take cin abincin hannu baka hannu kwarya. Allah kadai ya san tun yaushe rabon ta da abinci, mai yiwuwa tunda aka yi mata zancen aure da mijin Yayarta. 

Ta gama ci ta kora da gwangwanin fanta, ta koma ta kishingida Inna ta yi mata sai da safe ta kwashe 

kulolin da plate din da gwangwanin fantar ta fita. Karfe daya na dare Dr. Sulaiman ya shigo gidan, ya tabbatar zuwa yanzu dai kowa ya kwanta balle a dame shi. Yana shiga dakinsa ya danno kofa ya murza key, hoton Hadiza cikin dan kankanin ‘frame’ da ke kan ‘side drower’ na gadon shi ya yi mishi sallama, tana murmushin ta ni‘imtacce cikin farar shirt din calvin-klien wato C.K. 

Ya zare falmaran din suit din shi ya zare tie ya fada a kan gadon, ba tareda ya cire takalmi da safar kafarshi ba, ya fizgo hoton ya rungume a kirjin shi, ya yi magana cikin muryar kuka, 

“Why do you leave me Hadizahh….? Mai ya sa kika voye min cewa kina da brain cancer? Likitancin ki bai gaya miki cewa babu ciwon da ba shi da magani ba? Hatta kanjamau ana nan ana kokarin nemo maganin ta. Mai ya sa baki jira ni mun tafi tare ba? You left me incomplete, shat

Ya mirgina ya kara rungume hoton ya feso wani irin huci mai zafi. 

“Da gaske Allah ba ya barin wani don wani, na tabbata da ba zai dauke ki ya barni ba. Ya za ai a ce na zama mijin kanwar ki? Wannan cin fuska da cin amanar soyayya har ina? Ba za a yi ta dani ba! I am for Hadizah only….!! Zan jira wa’adina Hadiza in iske ki acan mu ci gaba da rayuwar mu a inda babu mutuwa…. balle ta sake raba mu…… ” 

Ya lumshe ido, hawaye suka mirgino, ya bude a hankali ya kai ‘frame’ din ga siraran levvan sa, ya 

yi masa sumba, mai tsayi, da zurfi, kafin ya yi 

masa murmushi ya ce, “I love you HADIZAH….Cikin kowanne hali INA SONKI HADDIZAHH!!!” 

Masoyan Hadizar na da yawa, domin ita ma a 

can, Fadima, a dai-dai wannan lokacin, goshinta na gaban mahalicci, cewa take. “Ya Allah! Ka yi rahma ga baiwar ka Hadiza, ka yalwata kabarinta da haske da kamshi, ka yaye mata duhun kabari, ka shayar da ita ruwan Alkhausara, ka bani juriyar cika alkawarin ta duk da na san ba abu ne mai sauki ba………. ” 

Kafin gari ya yi haske tuni Dr. Sulaiman ya fice, sai karar motar shi Inna da ke lazimi ta jiyo. Ranta ya vaci sosai, ta dauki waya ta yi kiran sa, anyi sa’a wayar na bude ba shi kuma da huyjar kin amsa kiran Inna. 

Yana amsawa ta ce, 

“Dabbobin da ke cikin gidanka za su koma makyankyasar su, sai in ce Allah ya hada mu da alheri”. 

Kafin ya yi magana ta kashe. Ya juya wayar a hannun sa, “Dabbobi? Dabbobi? Su waye dabbobin? Eh, dole ta kira kanta dabba a gidansa, tunda har za ka iya fita tana cikin gidan ba ka gaishe ta ba”. 

Jikinsa ya yi sanyi, a hankali ya yi round ya juyo. Lokacin da ya iso gidan har sun faka kayan su suna sawa a motar Jibril mijin Ruma, tana kokarin fitowa yana kokarin shigowa suka yi karo, karaf, ya yi saurin ja da baya. 

Yace, “Inna ki yi hakuri in je in yi signing yanzu sai in dawo in kai ku”. 

Ta harare shi ta ce, 

“Ai ba kai kadai ke da mota ba, tunda ka iya ka kwana cikin gidan ka wayi gari ka fice ba tare da ka binciki halin da muke ciki ba ai dabbobi ka dauke mu. Ni matsa ka bani hanya bana son motar taka”. 

Ya soma magiya, 

“Ki yi hakuri Inna, mu koma ciki mu yi magana, wallahi dama ban yi niyyar dadewa ba zan je ne in dawo kuma ban san yau za ku koma ba”. 

Ta valla masa harara sai kuma ya ba ta tausayi. Wanda ya san Dr. Sulaiman a baya, ya kuma ganshi a yanzu, zai yi wuya ya shaida shi in ba ya yi masa farin sani ba. Duk da ya aske kasumbar da ta cika mishi fuska, hakan bai voye muguwar ramar da ya yi ba. 

Ita kanta muryar shi ta canza ta zama mara amo, kamar ta mai fama da mura. Dara-daran idanunsa sun zurma ciki. Kallo daya za ka yi mishi ka tabbatar da cewa har yanzu mutuwar matar shi ba ta gama dukan shi ba. 

Ta juya suka koma ciki, suka zauna a falo. Ta ce, “Ka kara YAKANAH Sulaiman, a kan wadda kake da ita. Ka rike Fatima da amana, domin amanar ce a hannun ka. Jiya baka je ka ga ya take ba, ya ta zo, meye matsalar ta baile lafiyar ta. Sannan yanzu ma ka fita ba tare da ka neme ta ba”. 

Ya yi shiru kansa a kasa, a gaskiya! An takura rayuwar sa, an kakaba masa abin da bai san ya 

zai yi da shi ba. Ba ya jin ko sautin shi zai iya bai ma Fati. Amma Inna gaskiya ta fadi, dole ya dinga bincikar lafiyar ta. 

A sanyaye ya ce, “Ki yi hakuri Inna, insha Allah, zan kula”. 

Ta ce, 

“To Allah ya yi maka albarka”. 

Ya ji dadi har kokon ransa, ya ce, “Za ku jiranin in je in dawo in kai ku?” 

Ta ce, “A’‘a, ka maida hankali kan aikin ka. Ga Jibril zai kai mu, sai mun yi waya, Allah ya hada mu da alheri”. 

Ya zaro kudi cikin aljihun sa ba tare da ya kirga ba ya mika mata, “Sai a ba Jibril ya sha mai”. Ya sake zaro wasu, “Wannan kuma sai a rabawa su Ruma, karshen watan nan zan zo insha Allah in abin da nake jira ya fito”. 

Ta ce, “Meye abin da kake jira?” 

Ya yi murmushi kadan, “Sai na zo din Inna”. 

Bayan fitar sa ta shiga dakin Fati, ta tarar da ita ta yi wanka ta sauya kaya, cikin doguwar riga kirar Omman ruwan makuba, ta makala dan kankanin hijabi fari iya wuyanta, fuskarta sumul babu ko tabon pimples ko daya, sannan babu wani make-up amma ta yi kyau sosai. 

Akwai wata voyayyar kauna da Inna Halima ke yiwa Fati, wadda ta dasu a ranta tun daga lokacin da ta fara zama da ita daki daya, ta fahimce ta, ta fahimci akidar ta. 

A wancan lokacin ta ce a ranta, ina ma ina da wani babban da in aura mishi Fati ko ya samu 

tabarrakin da ke tattare da ita, Khalid bai isa aure ba. To ashe dukkan su rabon Sulaiman ne, haka Allah ya tsara. 

Ta zamo daga gadon ta russuna tana gai da Inna, ta kama hannun ta suka zauna a gefen gadon tare, ta ce, 

“Mun kwana lafiya Fatima?” Ta ce, “Lafiya kalau Inna, ya ya gajiyar ku?” Ta ce, “Gajiya ta bi lafiya Fatima, mu za mu wuce Bakori, sai kuma Allah ya hada mu cikin alherin sa”. 

Idanun ta suka yi rau-rau kamar za ta yi kuka, Inna ta ce, “A’a, kada mu yi haka da ke, mun yi waya da Alti tana nan dawowa karshen wannan satin, ba za ki zauna cikin kadaici ba. Sannan ungo wannan”. 

Ta mika mata kwalin karamar waya kirar Nokia, ta ce “A hade take da caji da komai har layi an sanya, jiya na aika Jibril mijin Ruma ya siyo, duk wata matsalar ki kada ki nemi kowa ki neme ni. Sannan kada ki ji shayin gaya min komai wai don ina uwar Sulaiman, dukkanin ku ‘ya’ yana ne, baki da wata damuwa?” 

Cikin nishin kukan da ke son ya valle ta ce, “Damia…….. dama ina so a karvo min Nana ne”. Inna ta yi shiru kamar tana tunanin wani abu, can kuma ta ce, “Ki dai yi hakuri zuwa rana ‘i ta yau din, ko kin manta ke AMARYA ce? Ki huta kwana bakwai, ki kula da mijin ki. Rana ita yau za a kawo miki ‘ya’yan ki dukkan su. Allah ya yi muku albarka kan biyayyar da ku kai mana, kuma ya sa ‘ya’yan ku su yi muku fiye da ita. 

Kada ki yi wasa da GIRKI Fati, domin shi ne 

mafi saukin hanyar isa ga zuciyar miji. Na barku lafiya”. 

“AMARYA! AMARYA!!” 

Fati ta maimaita kalmar Inna. Bayan fitar Innar. Sannan ta koma ta kwanta rub da ciki a kan katifar ta “I’m not a bride Inna (ni ba amarya ba ce Inna). 

Ita amarya cikin farin ciki take, cikin sa take kwana, cikin sa take wayar gari, cike da soyayyar mijinta. Amma ni yaya na kwana? 

Kwana na yi cikin suyar zuciya da tunanin ‘yar uwata abar sona, wadda take min soyayyar da babu mai yi min ita a duniya, in ka cire iyayena. Bana kin sa shi yake kina, a kan laifin da ban sani ba. Ban san so ba balle in ce bana son sa. Amma ni meye laifina a kan auren da nima ba so nake ba? 

“Kulawar MATA yake nema…..”. 

Ta tuno furucin karshe na Hadizah. To ga ni na zama matar tasa Yaya Hadiza, wace irin kulawa kike nufi in ba shi? He is old enough ya kula da kansa, wanka zan mishi ko pampers zan cire masa? Goyon shi zan yi ko feader zan ba shi? Ban san wacce irin kulawa kike nufi ba. 

Ta kai bayan hannu ta shafe hawayen ta, banda GIRKI kamar yadda Inna ta ce, in za a kashe ta ba ta san wata edtra kulawa ta daban da mace ke yiwa miji ba. Sannan ba ta iya shisshigi da cusa kai a inda ba za ta yi kwarjini ba. 

Bayan tafiyar su Inna gidan sai ya yi shiru, babu 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *