YAKANA BOOK 2 CHAPTER 7 BY SUMAYYAH ABDULKADIR KARSHE THEND
Www.bankinhausanovels.com.ng
suka hada a bayan ran marigayiya Hadiza, wadda har gobe, jibi, har gata basu daina yi mata addu’a ba.
Dr. Sulaiman yana Abuja, sai week end yake zuwa musu, sai ko in duk sun samu hutu suma su ke bin shi.
Ranar wata litinin kwana daya da tafiyar Sulaiman nakuda ta kama Fati, suka nufi asibiti ita da Alti, yaran duk suna Karkasara.
Kafin magariba ta haifi sankacecen danta mai kama da Baban shi har farcen kafa. Sai waya Dr. Surayyah ta yi mishi cewa baby ya iso. Sai ga shi a washegari kamar an jefo shi, ya tadda Fati da baby a ‘aminity’, sai dai dakin cike yake da ‘yan uwanta. Sai daga nesa yake jifanta da murmushin ‘bani da abin da zan gode miki’.
Ita ma murmushin take masa da su kadai suka san ma’anar abin su.
Ba da son ranshi ba Yaya ta wuce da ita gida inda za ta yi wanka, don Alti an aiko mata rasuwar danta a kauyen su Kukawa, don haka za ta tafi a washegari.
Dakin ta na da Yaya ta gyara mata suke wankan, Munib dan kankanba ya kasa sukuni saboda ya yi kani namiji dan uwan sa. Bini-bini zai ce a ba shi ya dauke shi, ita kuma Fati ba ta gajiya da mika mishi.
Kawarta Fa’iza ta zo mata barka wadda ita ma an yl auren ta tuni, suka wuni sur suna hirar bayan rabo, don Fati ta zamewa Fa’iza abin sha’awa ganin yadda ta yi kyau ta kara girma, yanda duk wanda ya dube ta duba daya zai tabbatar tana da
kwanciyar hankali a gidanta. Savanin ita da kishiya ta sa ta gaba, ta hana ta zaman lafiya. Fati na tausar ta tare da ba ta shawarwari na gari. Ranar suna yaro ya ci sunan Malam, wato Ja’ afar. Malam ya roke su kar su voye mashi suna su kira shi da Jafarun shi.
Juma’a yamma lis, Dr. Sulaiman ya iso Kano daga Abuja, kai tsaye gidan surukan sa ya fara dosa. Bayan motar shi dankare da himilin tsaraba, Yaya ta yi mishi shimfida da sabuwar tabarma, ta sunto baby da ke bayan ta ta mika mishi.
A lokacin Fati ta fito daga bandaki, ta yi daurin kirji ta rufu da tawul, ta sha dukan ganye, jikin nan ya kara zama fresh, fatar nan ta kara zama mai taushin gani a ido.
Ta kasan ido ya dube ta, sai ya ga duk ta canza mishi, ta kara zama yarinya danya sharaf. Da alama ba ta da damuwa, sun barshi da kadaici, sai fama yake da biro da takarda.
Yaya ta shige kitchen ta barsu, ai kamar jira yake ta tashi ya yi ma dakin Fati tsinke. Tana tsane gashin kanta da tawul ya bude mata dukkan hannuwan sa bayan ya aje babyn a cikin katifar sa. Ta rufe ido tana dariya, sai shi ne ya karaso ya rungume ta tsantsan a hankali, yana fada mata kalaman da suka zama sirri ne a tsakanin su tana murmushi. Cikin ranta addu’a take Allah ya barta da Sulaiman dinta, ya dorar da rayuwarsu cikin daukaka da soyayya, kamar yadda ta faro, har zuwa ranar da suka daina numfashi.
FoR RK
SHEKARU GOMA SHA BIYAR A GABA!
T aron rantsar da sabbin ministoci da mai girma
shugaban kasa President Umaru Musa ‘Yar Aduwa zai gabatar a yau a hotel din NICON NOGA, har da babban likitan zuciya da kasarmu Najeriya ke ji da shi, wato Dr. Sulaiman Sulaiman Bakori, wanda aka rantsar a matsayin Ministan Lafiya na kasa baki daya. Ranar Litinin, ashirin da shida ga watan Maris, na wannan shekarar.
Dr. Fatima Ja’afar, H.O.D Islamic, a jami’ar
Abuja, cikakkiyar mace ‘yar kimanin shekaru talatin da bakwai da haihuwa, uwar ‘ya’ya biyar a halin yanzu, in ka hada da manyan ‘ya’yan ta Munib, Muniba da Nana Khadija sun zama su takwas kenan. Tana sanye da bakar abaya kirar Bahrain da mayafinta, hannunsu sakale dana juna suka isa ga mazaunin su, daukacin Ministocin da ake shirin rantsar wa suna tare da matansu da rakiyar ‘ya’yansu, to haka suma, Muniba, Nana Khadija, da Ja’afar. Ya yin da suka baro Mufida, Mufid da Ibrahim da dan autan su Abdulhak a gida, cikin kulawaar tsohuwa Alti.
Bayan mai girma shugaban kasa ya rantsar da
Ministocinsa, aka zarce da gagarumar walima. Ba su baro dakin taron ba sai dare, suna kan hanyar isowa gida wayar Munib ta shigo, wanda ke can kasar ‘Srilanka’ yana karatun harhada magunguna.
Ya ce, “Daddy kun manta dani, ko waya an fi sati ba wanda ya yi min. Yanzu nake jin abin alheri a BBC, congratulations Daddy!”
Ya ce, “Kwantar da hankalin ka Munib, zirgazirga ta hana mu neman ka. Ina mai yi maka albishir da cewa, muna tafe dukkanin mu cikin satin nan, sai ka tanadar mana better’.
Ya yi ihu ya ce, “Allah Daddy da gaske?”
Fati ta amshe wayar ta ce, “Amma sai in point din ka na wannan semester ya kai 4.00, if not, babu wanda zai zo”.
Ya ce, “Wallahi 4.60 ma na samu Mummy”.
Ta ce, “Ah, lallai zuwan kowa ya zama dole, tunda duk muna cikin hutu”.
Ja’afar ya amshe wayar ya ci gaba da ba shi labarin duk shagulgulan da ake yi a yau. Munib ya ciji yatsa ya ce, “Ayya! Na yi missing….”. Daga nan sai Muniba, ita kuwa Nana ta ce, ba za ta yi magana da shi ba tunda baya yi mata waya sai budurwar sa kawarta Naina.
Daddy ya harare ta ya ce, “Bana son sakarci, shi ba shi da wata budurwa dan makaranta ne”.
Ta ce, “Amma yake yi mata waya yake yo mata tsaraba in zai zo?”’.
Ya ce, “Ba kanwar shi ba ce? Ke ba ya yi miki?” Ta ce, “Wallahi Daddy nata ya fi yawa, har da kati an rubuta I LUV YOU”.
Fati ta tintsire da dariya, shi kuma Dr. Sulaiman sai ya rasa ta cewa, yaran zamani sai a barsu, da wayonsu ake haifar su.
Ya dubi Fati da wani irin sassanyan kallo, “Momin yara, wai da gaske ne?”
Ta rausayar da kai ta ce, “Shirmen Nana ne, Naina Bunza, tana da shiga ran kowa sosai, suna shirt da Munib sosai sabida kokarinta.”. (Diyar Dr. Surayyah).
Ya ce, “Ba zan yi mamaki ba in son nata yake, ai jin kanshi yake matured (balagagge) kamar kowa’’. Dariya ta kama Fati, sai da ta murmusa sosai.
Sun isa gida yara kowanne ya kama harkar gabansa, ya cacumi Fati su kai sama ana biyan bashin soyayya, wadda hidimar kwana biyu ba ta bari ba. Suka ci gaba da amsa sakonnin taya murna da fatan alheri daga ‘yan uwa da abokan arziki, har tsayin sati daya.
Ranar juma’a jirgin MEA International ya tashi
dasu zuwa Srilanka, har filin jirgi Munib ya taro su, ya dauki Abdulhak ya rungume suka karasa zuwa makarantar su bayan sun yi booking din hotel din da za su sauka. Farin cikin Munib ba sai an fada ba, ya rasa inda zai sa iyayen shi da ‘yan uwan shi. Dr. Sulaiman ya yi bincike sosai kan karatun shi, ya yaba sosai da hazakar da yaron ke nunawa. Kwanan su uku suka wuce Saudiyyah suka yi Umarah, sannan suka dawo gida.
Da albashinta da ta ke tari, da kuma taimakon Dr. Sulaiman, Dr. Fatima Ja’afar, ta bude makarantar Islamiyya ta yara maza da mata a nan Abuja, da aka sanyawa suna NANA KHADIJAH ISLAMIYY AH. Haddar Alkur’ani mai girma ake yi tsantsa, sai sauran littattafan addini irin su Ishmawi, Bulugul Maram, Sirah, Hadith, AlAkhdari, Fikh da harshen larabci. Ana zuwa daga karfe biyu na rana zuwa shida na yamma, ba ta da abin da za ta ce da Dr. kuma Minista, Sulaiman dan Sulaiman, sai godiya da addu’ar alheri, domin ya gama cika mata burinta na son yada ilimin Alkur’ ani da hadisi, kamar yadda ta ke buri. Ya lulluve ta da duk wasu alhairori na rayuwa, ya lulluve ta da so da kauna. Gaskiyar Babanta ne Alkur’aninta ba zai bari ta tozarta ba!. Ta san Sulaiman ba ya son ta ya aure ta, kuma ba zai tava son wata diya mace kamar yadda ya so Hadiza ba, amma tana tantama a halin yanzu, idan son da yake mata bai zarce wanda ya yi wa Dr. Hadiza ba.
A alfarma ta soyayyah, ta san ba ta cancanci Dr. Sulaiman ya so ta a wancan lokacin ba, amma ya so ta saboda hakuri, juriyar ta da YAKANAR ta. Ya so ta sabida kyawawan halayenta. “Mene ne YAKANAH?” Na tambayi Malamarmu, Dr. Fatima Ja’afar Mai-Yadi.
Ta yi murmushin ta mai motsa zuciya, ta ce,
“Takori ba ki san Yakanah ba?”
Na ce, “Ina zan sani Fati? Sai ku malaman ad
lini”.
[a yi smiling ta ce, “Nima daliba ce
SUMAY YAH! Sai dai in sanar da ke dan abin da na sani a dalibtaka ta”.
Na ce, “daure ki sanar dani Aunty Fati, komi kankantar sa. Domin al’umma zasu so su san me ita wannan kalma ta YAKANAH take nufi?”.
Ta yi murmushi tana dubana ta ce;
MECE CE YAKANAH?
Ita YAKANAH ba kasaifai ake ganin ta a wajen yawancin mutane ba, YAKANAH ita ce take daukaka darajar mai yin Ibadah, ta kai shi wani matsayi na daukaka a wajen Allah. YAKANAH ita ce tushen dukkanin aiyuka na gari, wato daukacin ayyukan kirki suna fitowa ne daga cikin ta.
Mutum mai YAKANAH shi ne mai yin babban jihadi ko gwagwarmaya da kansa wajen watsi da abubuwan da rai da zuciya ke so, saboda neman yardar Ubangiji, da neman dadin falalar sa, tare da nuna biyayya a gare shi.
An ambaci irin wadannan mutane a cikin Alkur’ani mai girma, kamar cikin suratul Al-Imran (3:17) Al-Nisa’i (4:25, 127-128), Fussilati (41:34) da sauran su.
Irin wannan babban jihadi da kai ana yin sa ne tsakanin mutum da zuciyar sa (Nafs Al-Ammara), domin sauya ta ya zuwa (Nafs AlLawwama), sannan ya zuwa zuciya madaukakiya (Nafs Al-Mutma’innah).
Saboda haka madallah da ita wannan baiwa ta YAKANAH, domin tana kai masu yin Ibadah zuwa ga matakin shiga cikin rukunin salihai wadanda a koyaushe suna masu yin godiya a kan
dukkanin abin da ya zo musu daga Allah. YAKANAH it ce kololiyar takwa wato tsoron Allah. Takwah kuma ita ce mai kore tsoron haduwa da Allah (wanda ba ya jin kunyar ubangijinsa kuma mai savon sa, shi ne mai zama cikin fargabar haduwa da Allah).
Daya daga cikin ma’anar YAKANAH ita ce, ka dinga kallon kanka a matsayin kai ba kowa bane a cikin jama’a, kuma kowa ya fi ka, saboda haka YAKANAH tana nuni da rashin kasancewar mutum cikin halin GIRMAN KAI!
Misalai: Idan ka kasance mutum ne kai mai YAKANAH ta gaske, a duk lokacin da ka gamu da wani mutum wanda baka san shi ba, komi lalacewar sa, sai ka ce da kanka a cikin zuciyar ka.
‘“Watakila matsayin wannan mutum a wajen Allah ya fi nawa”.
Idan kuwa ka gamu da yaro kankani, sai ka cewa kanka, “Ka ga wanda ba ya savon Allah, ni kuwa ina yi”.
Idan kuwa ka gamu da wanda ya girme ka, sai ka ce, “Ka ga wanda ya jima yana bautar Ubangiji tuntuni kafin ni”.
Idan kuwa ka yi kicivus da mutum mai dimbin ilimi, sai ka ce, “Ga wanda aka yiwa baiwa da abin da ni bani da shi, domin ya fi ni ilimi, kuma yana aiki da ilimin sa, amma ni ko ya ya dai?”
Idan kuwa ka yi karo da jahili, sai ka ce, “Dubi wani yana savon Allah cikin rashin sani, ni kuma ina yi cikin sani. Ga shi kuma ban san yanda karshen sa zai kasance ba, kuma ban san nawa
karshen ba. Ko me zai zama a nan gaba? Allah shi ya fi kowa sani”.
Idan kuwa ka gamu da kafiri, sai ka ce da kanka, “Wa ya sani? Watakila nan gaba ya musulunta kafin ya mutu, kuma wa ya sani ko ni kuma in mutu a kafirce?”
Ire-iren wadannan maganganun gaba daya suna nuni da halin mutumin da YAKANAH da tawali’u suka baibaye shi, yake kuma cikin hali na binciken kansa a koyaushe.
Dalilin irin wannan tunani a zuciyar wannan bawan Allah shi ne, yana cikin yanayi na rashin yarda da kansa. Tare da rashin tabbas game da abin da zai abku wajen haduwar sa da Allah. Ire-iren wadannan tunani kuwa suna nuna karfin imani ne da dogaro da Allah madaukakin sarki wanda shi ne tushen kaskantar da kai.
A kowanne lokaci idan bawa ya kaskantar da kansa, Allah zai kare shi daga masifu, kuma ya ba shi sirrin “Ikhlasi” Wato nacewa da son bin hakikar gaskiya a dukkannin al’amuransa na yau da kullum. Daga wannan mataki ne mutum zai kasance cikin mutane ‘yan kadan wadanda suka samu yardar Allah tare da kusanci da shi. YAKANAH ita ce kofar da ake bi ta cikinta zuwa wurin da baiwar Allah da rahamar sa _ suke muhimmancin YAKANAH ga musulmi kamar kwatankwacin vargo ne a cikin kashi. YAKANAH tana a matsayin vargo na Ibadah, kuma sauran ayyuka suna a matsayi na kashi. Bayin Allah wadanda ake kira ‘zahideen’ masu cike da da’a da tsantsenin duniya, tare da ‘nasi
keen’ masu sadaukar da rayuwar su domin bautar Ubangiji, dukkannin su suna ji da wannan baiwa ta YAKANAH.
Bayin Allah masu YAKANAH basa yin maganganu barkatai, basa yin tsegumi ko wata muguwar magana a game da wani a bayan idanun sa, su kan fadi abin alheri ne a game da shi. Ba sa shiga sharo ba shanu, kuma zuciyar su fes take. Ta kuma nisanta da miyagun dabi’u, kamar hargowa da JI DA KAI. Wato kirjin irin wadannan bayin Allah garau yake.
Duk maganar da irin wadannan bayin Allah masu YAKANAH suka fadi, ta dace dai-dai da abin da suka yi, suka kuma yi imani da shi.
Basu da wani abu da za su voye a Zuciyar su domin kada wani ya sani, wato basu da wani mummunan abu a tare dasu.
Bayin Allah ne masu zallar gaskiya da rikon ta, wanda duk ya yi hulda da irin su zai ga cewa basa fafutukar neman kuskure a kan wani, maimakon haka, a shirye suke wajen neman kuskure daga wajen su, wato a kan kansu.
Basa yarda su zauna tare da (marada) (masu kawo tsegumi). Don haka ‘yan uwa musulmi mu yi damara da kokarin kasancewa cikin bayi masu YAKANAH, mu rike addininmu, mu kama Alkur’nin mu, mu suturce jikinmu, domin samun dacewa a duniya da lahira. Kamar jarumar wannan littafi, Allah ya bamu iko amin summa amin. -Takori.