YANAYIN RAYUWA CHAPTER 9

😔YANAYIN RAYUWA😱😭🌸💐🌷💐💐💐💐. CHAPTER 9 

 By halimatusadiya saleh. Da mamaki yan falon suke kallon shi,dad kam ko mgn ya kasa se ido,mom ko se addua take aranta Allah yasa kar dad yayi rejecting na abunda take so, dun har ga Allah kobadun wannan abunba taso Umar ya auri zali. Baba ya dago ya kalli yan da yanayin Umar ya chanza lkc guda, yace ” Umar zaka aure ta.” Dasauri Umar yace ” Ehhh baba.” Jinjina kai bayayi hade da murmushi irin na manya,gaskiya yaji dadi kuba komai zali zata huta da muguntan zuwaira, yace ” Ok naji dadi sosai,yayah ka se mu hanzar ta mune mi liman da sauran da shedu a daura koh.” Se lkc dad ya iyyayen magana yace ” Hmmm! Ibrahim je kakiramin mai gadi.” Da hanzari khalil yaje yakira mai gadi,suka shigo tare. Dad yace mai ” Baba inna sone kuje da khalil gidan liman kukirashi yazu inna neman shi,kuma inkuna zuwa kuje gun mlm hamidu koce mai yazo,kuhan zarta Dan Allah.” Mai gadi yace ” too.” Fita sukayi da khalil kaman yanda dad yace, zali kam dajin an ambaci akakira liman kuma taga dagaske ne zaa aurar da itta ga ya Umar saurin dago kanta tayi ta kalli mom. ” Shiiiit.” Mom tayi mata alaman tayi shiru dun taga fiskan ta da alamun magana take so tayi, yayan ta tajuya ta kalla da haryan zu idon sa ceke yake da kolla, sun kuyar da kanta tayi kasa. Wasu zafafan hawaye ne suka sauko kan kuncin ta, tarasa meke mata dadi,wai itta yaushe ne zata bar kuka,duk dalilin mamane ai dabata mata zalunci ba da baza amata aure ba. Haka suka cigaba da zaman shiru. ✨✨✨✨✨✨✨ Sallama sukaji anyi ba shakka su khalil ne, amsa wa sukayi tare da musu izinin su shiga,guri suka samo suka zauna. Gaisuwa sukayi saka nin su inda dad yace da mai gadi yazauna. Gyran murya dad yayi yace ” Am malam daman nakira kone badun kune sabuda kuzo kuzama shedu,zan hada Dana Umar da yar yayanah zulaihat aure,ga sadaki.” Yamika ma liman shaddan, amsa liman yayi, kafun yace ” To waye wakilin Amarya , waye na ango.” Bane yace ” nine wakilin Amarya,ango kuma ga wakilin shi. ” Yafada yana nuna dad. Shiken ikon Allah a ka daura auren, Umar Ahmad baba Da Zulaihatu Umar baba Farin ciki gun mom, baba,dad,ya Usman,da ya Umar har dasu aunty hapsat,maryam,khalil. Amma banda zali dun tunda akafara daura auren zuciyan ta kemata wani irin kuna ga hawayen da yaki kare wa a idonta. Liman ne ya dauki shaddan ya bama baba,baba ko yami kawa mom tarike ma zali. Ahaka aka rufe da addua da fatan Allah yabasu zaman lfy da zuria dayyiba. Mom ce taja zali suka wuce dakin ta inda shikuma Umar da ya Usman suka wuce bangarin su. Dad yaraka baba harkun dayayi parking motan sa,yatafi gida. Zaunar da itta mom tayi a bakin bed din, ittama ta zauna ta kama hannun zali tace. ” Zaliha kiyi hkr da abunda yafaru nasan farko kindauka mgn wasane, munyi hakanne saboda muraba ki da gidan mama ko zaki samo farin ciki, kuma batun ya Umar yanzu shi mijin kine kuma yayanki, kina da zabi dan kika girma kika samo wanda kike so se yasake ki ki auri wanda kike so. ” Zali kam bata iyya cewa kumai ba se kuka,mom ta ringa lallashin ta harta samo tayi shiru. Wayanta taja takira Umar tace masa yazu shida Usman,ba bata lkc suka zo,guri suka samo suka zauna, Umar yace ” Gamu mom .” Nan mom takwashe yanda sukayi da Umar ta gayama Usman ,ya jidadi sosai yama mom godiya. Tace ” Umar kai kuma yanzu masayin ka ya chanza daga yaro zuwa babba, wani dauyi ne akanka yanzu kuma dole kasauke shi,dun kar Allah yakama ka da hakkin ta akan ka, kuma ka kula da lamuran ta, kuma inna rukun ka da ka reke Amana da Allah yabaka, kaji tsoron rannan da Allah ze tambaye ka game da Amanan daya baka,kuna kaga itta marainiya ce, fatana Allah baka ikon rike Amana, fatan kafahim ce ni. ” “Ameen”suka amsa, tace ” zaku iyya tafiya.” Tashi sukayi suka bar dakin Usman kam farin ciki kaman yaka she shi,suna fita mom taba ma zali shaddan. Tace ” wannan sadakin kine.” Karba tayi, ta juya shaddan se alukacin takarama shaddan kallon, sky blue ne yayi kyw sosai gaskiya shaddan ya shiga ranta sosai, rungume wa tayi a kirjinta wani murmushi tayi wanda har tasa mom tayi murmushi ba shiri. Mika ma mom tayi tace ” Mom ki ajeyi min.” Karba mom tayi, tace ” To uwar masu gida.” By halimatusadiya saleh.❤️ 😔 YANAYIN RAYUWA😱😭 🌸🌷💐💐💐🌷🌷. By halimatusadiya Saleh❤️ Babane zaune a falo shida mama, su zainab suna daki, mama takalli ba tace ” Ya naga kadawu kai kadai?” Murmushi yayi yace ” Eh! Ai yanzu kam matan wanine kuma seda izzinin shi zata zo nan.” Damamaki mama ta kalle shi tace ” Bangane ba,zalin ce matan wani ko wa?” Murmusawa yayi yace ” eh itta man.” Mama tace ” plxx yimin bayani yanda zan gane.” Nan yakwashe abunda yafaru ya gaya mata, a take annurin fiskan mama yatafi, yanzu kenan zali baza ta dawu gidan nan ba,kuma Umar ta aura tabb ai zata gani kuma da itta take. Tashi tayi zata wuce daki, baba yace ” Inna kuma zaki, kuma naga kaman bakiyi farin ciki ba, to innaso ingaya miki ko kiyi ko karkiyi, baze hanasu zaman lfy ba, kuma inkina ga hali mai kyw ne kike yi to kiciga da sannu zaki ga a kuryan towun ki.” Yana gama fadan haka yatashi yayi gaba abunsa,binsa tayi da ido tace ” Kune de zaku gani, mtwssss.” Taja saki tayi daki. ✨✨✨✨✨✨✨ ” Kuyi kugama shiri kafun su ya Usman sudawo.” Mom ce ta fadawa su maryam da zali, tana gama fada tayi dakin ta. Zali tafito rike da veil orange a hannun ta zata wuce dakin mom. Atamfa ce riga da skirt tasa tayi daurin Aisha buhari ta sake kitson ta abaya, kwalliya tayi tasa pink lips tick,ata kaice de tayi kyw, chacolate skin nata yadada haskawa, tafiya take cikin kasaita bazaka ce yarinya bace dayake tanada sayi amma ba sosai ba. ” Yammatan yayah ?” Ya Umar ne yakirata, juyowa tayi ta yamusa fiska tace ” Me?” Kallon ta yayi da kyw yace ” Inna zakije haka?” Tace ” gidan kaka zamu man.” Yace ” amm! Shine kikayi kwalliya haka, to oya je kiguge kuma ki ajiye gellen nan kisa hijabi, daga yau kuma baza kisake sa gelle ba, kingane ko.” Tura bakinta tayi zatayi kuka yace ” Kika kuskura kikamin kuka se in hanaki zuwa ma gaba daya.” Kama bakinta tayi tawuce daki dun mom ta garga deta akan haka. Bude kofan tayi da karfi tashiga, tanashiga tapashe da kuka, tajuyo da dasauri tace ” Lfy, meyasame ki?” Zali tayi magana cikin muryan kuka tace ” Ba ya Umar bane yace kar inkara sa gelle kuma in guge kwalliya na.” Murmushi mom tayi taka mu hannun ta tace ” Kiyi hkr kinji, kukin manta da abunda nagaya miki ne.” Girgiza kanta tayi alaman a’a Mom tace ” Yauwa Allah miki albarka,yanzu tashi kisa hijabin ki, inna shiga kasuwa zan saya miki wasu.” Share hawayen ta tayi tanufi wool drop ta dauko hijab din ta orange ta sa ka tadau jakan ta zata fita mom tace kikiramin aunty hapsat. ” Ok se mun dawo.” Inji zali, mom tace ” adawo lfy, kugaida kakan ku.” Tace ” yauwa.” Fita tayi tanufi dakin su, tace ” Aunty hapsat mom nakira.” Daman sun gama shiri , fita aunty hapsat tayi ta nufi dakin mom, tana shiga da sallama mom ta amsa tace ” Gani mom.” Wani Polly bag mom ta dauko tace ” Ku kaima kakan ku kuce mai inji dad dinko .” ” Ok” inji hapsat,fita tayi hade dama mom bye bye. Gidan kaka sukaje rannan kusan agun suka inni tun 11 se 4 suka dawo gida. Akwana atashi yau 3 yrs da auren zali da Umar

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *