YANCIN MATA CHAPTER A
* Tafiya take tana cikin sauri tana duba agogon dake d’aure a tsintsiyar hannun ta , yarinya ce y’ar kimanin shekara goma sha biyar tana sanye da dogon hijjabi da alama daga islamiyya ta dawo , titin tas babu kowa gashi magariba ta gabato hakan yasa take ta sauri dan tasan halin unguwar tasu yanzu sai a sace mutum .
+
Wata mota ce bak’a k’ira Benz tazo ta gifta yarinyar a guje , cike da tsoro yarinyar ta cigaba da sauri kamar zata tashi sama , cak motar ta tsaya tare dayin reverse har ta dawo inda yarinyar take
Wasu maza ne suka fito daga motar basu tsaya wani tunani ba suka fesawa yarinyar wata hoda a fuska , nan dake tayi baya zata fad’i suka taro ta suka saka ta a mota suka cigaba da gudu.
Sabon sirinji suka d’auko suku dibi jinin yarinyar sannan suka rife sirinjin , basu tsaya a ko ina ba sai a bakin wani asibiti d’aya daga cikin mazan ya d’auki wannan jinin ya shiga cikin asibitin .
Direct lab ya nufa yana zuwa ya mik’a musu kamar yadda suka saba , gwajin cutar k’anjamau akayi akaga babu , sannan akayi na ciwon hanta shima akaga babu , result din ya karb’a ya juyo a guje ya koma cikin motar suka cigaba da tafiya.
Basu tsaya a ko ina ba sai a bakin wani k’aton gida mai bala’in kyau ,horn suka danna mai gadi ya bud’e suka shiga cikin gidan , parking suka yi cikin sauri suka d’auko yarinyar suka shiga da ita parlourn gidan.
Bedroom suka shiga da yarinyar suka kwantar da ita suka fito suka tsaya suna jiran ogan nasu yazo .
Basu wani dade ba ya fito daga d’aya d’akin ya tafiya dak’yar kamar Wanda baya San taka k’asa , zama yayi a kan d’aya daga cikin yace “Aikin Ku yayi kyau zaku iya tafiya”
Cikin rawar jiki suka amsa da “An gama ranka ya dad’e a ji dad’i lafiya” suna gama fad’ar hakan suka juya suka fita daga parlourn.
Mik’ewa yayi ya shiga d’akin da yarinyar take , murmushi yayi yace “Babu laifi tayi” k’arasawa kan bed d’in yayi tare da kwanciya kusa da yarinyar, a hankali ya zame mata hijjabin daga jikin ta ya Zuba mata ido yana kallon ta , tab’e baki yayi kamar yaga kashi haka ya zuge zip d’in rigar ta ya fara sha’anin sa .
Bai bar yarinyar nan ba sai ya tabbatar yayi mata kaca-kaca sannan ya kyale ta , wani bakin Abu ya d’auko ya kama hannun yarinyar ya rubuta _BAD MAN_ da manyan bak’i tare da yin singing a gaba , kayan ta ya d’auko ya saka mata sannan ya fito daga d’akin.
Kallon agogo yayi a yaga har sha d’ayan dare tayi tsaki yayi ya dau waya ya kira yaran sa yace ” Dalla malamai kuzo Ku d’auke min wannan bazawarar a gida na”
Jin ya ambaci bazawara yasa suka gane ya yiwa yarinyar fyade ,cikin rawar jiki suka dawo gidan suka d’auke ta suka shiga mota suka jefar da ita a inda suka d’auke ta.
Bad man kuwa shiryawa yayi cikin k’ananan kaya ya shiga mota ya nufi club.
Washe gari
*****
“Umme na shirya zan tafi wajan aiki” wata kyakykyawar budurwa ta fad’a tana rataya jaka
Wacce aka kira da Ummen tace “To Hazifa Allah ya kikaye hanya Allah ya bada sa’a”
Hafiza tace “Ameen Ummee na , ina Hanifa?”
Ummee tace “kema kinsan tunda suka samu hutun makaranta bata da aiki sai bacci”
Hafiza tayi dariya tace “To in ta tashi ki gashe ta na tafi ” ta fad’a tana fita daga gidan.
Sauri take ta Dan ta isa titi sabida ta kusa makara a wajan aiki, mutane ta gani a kan titi an cika a waje d’aya da alama akwai abinda ya faru a wajan , da sauri ta k’arasa wajan tana fad’in “lafiya jama’a meya faru?”
Wani mutumi yace “wani Mara imanin aka samu yayiwa k’aramar yarinya fyad’e kalli kiga halin da take ciki” ya fad’a yana nuna inda yarinyar take
Cikin tashin hankali Hafiza ta k’arasa wajan ta durk’usa a gaban yarinyar , ganin halin da take ciki yasa Hafiza ta fara hawaye tana fad’in ” wannan ai Iman ce y’ar mak’otan mu , Dan Allah Ku samo mota mu kaita asibiti “
Adaidaita sahu aka tsayar aka saka yarinyar da take sume bata numfashi ,
Suna zuwa aka shiga da yarinyar d’akin taimakon gaggawa likitoci suka rufu akan ta Dan ganin Dan ceto rayuwar ta ,
Zama Hafiza tayi tana tunanin halin da yarinyar take ciki , wajan minti talatin wani likita ya fito ya kalli Hafiza yace “muje office”
Bin bayan sa tayi suka shiga ta zauna yace “Fyad’e aka yiwa yarinyar nan na rashin imani dan Yanzu haka sai da aka yi mata dinki kuma itama akwai wannan tambarin a hannun ta”
Dukan table Hafiza tayi tace “Bad man again”
Dr Amin yace “Eh tabbas abinda yake jikin hannun ta kenan”
Cikin b’acin rai Hafiza tace “Wai waye wannan Bad man din ?”
Dr Amin yace “Allah ne ya sani Dan har yanzu ko full name dinsa ba’a sani ba balle kuma a san fuskar sa , kuma duk wacce yayiwa fyad’e sai yayi mata wannan tambarin a hannu, lauyoyi , y’an sanda har yanzu basu gano waye wannan mutumin ba”
Hafiza ta mik’e tace “Ni BARRIER HAFIZA nayi alk’awarin ganin bayan wannan mutumin , nayi alk’awari sai na gurfanar dashi a gaban kotu”.
📖* mik’ewa Dr Amin yayi yace “Ina bayan ki Barrister nima zanyi k’ok’ari wajan ganin an kamo wannan Bad man din”
+
Juyowa Hafiza tayi tace “Nagode sosai , dani da kai zamu had’a k’arfi da k’arfe wajan ganin bayan wannan mutumin, yanzu mu koma wajan Iman d’in”
Fita suka yi daga office d’in suka koma d’akin da aka kwantar da Iman , basu dad’e da shiga ba ta farka tana bud’e ido a hankali , nan take abinda ya faru ya shiga yi mata yawo a kwakwalwar ta ,
Juyowa tayi ta kalli Hafiza da ta Zuba mata ido tana kallon ta, cikin kuka Iman tace “Aunty Hafiza meye ya faru dani bayan wannan mutanen sun zuba min Abu a fuska?”
Cikin Tausayi Hafiza tace “ki kwantar da hankalin ki Iman ki daina kuka kinji”
Bud’e k’ofa akayi aka shigo ko ba’a fad’a ba ansan dangin Iman ne suka k’araso , Maman ta ta k’arasa wajan tana goge hawaye ta zauna kusa da Iman d’in tace “kiyi Hak’uri Allah yana bayan mai gaskiya, Allah ya tona asirin nan mutumin” ta fad’a cikin dashewar murya
Mik’ewa Hafiza tayi ta isa kusa da Iman ta dafa ta tace ” Iman a cikin Wanda suka Zuba miki Abu a fuska babu Wanda zaka iya ganewa?”
Iman tace “bazan iya gane su ba tunda ta baya na suka biyo daga nan kuma ban kuma sanin inda kaina yake ba sai yanzu”
Numfashi Hafiza ta sauke tace “Mama zan tafi wajan aiki amma insha Allah zan iya bakin k’ok’ari na wajan ganin na binciko wannan mutumin”
Mama tace “Allah ya baki sa’a Hafiza , Nagode sosai Allah yasa kiyi nasara akan sa”
Murmushi Hafiza tayi tace “Ameen Mama daman addu’ar Ku make nema , ni na tafi Allah ya k’ara lafiya” ta fad’a tana fita daga d’akin.
Sallama tayiwa Dr Amin ta fita daga asibitin.
Da kallo Dr ya bita yana wani irin murmushi dashi kad’ai yasan ma’anar sa .
Hafiza kuwa bata wuce ko ina ba sai cikin babbar kotun dake garin Kaduna , bayan an gama shari’ar y’an uwanta lauyoyi ta kira maza da mata ta had’a meeting bayan su zauna Hafiza ta kalle su tace ,
“Na had’a wannan meeting ne badan komai ba sai dan mu had’a kai mu kama wannan Bad man d’in da yake cutar y’ay’a mata a banza , yanzu maganar da nake muku y’ar mak’otan mu Iman tana can a asibiti a kwance , meye amfanin mu in banu binkico wannan azzamulin ba , sabida na taimakawa mata nayi karatun lauya kuma har yanzu ina kan baka ta , ya kuke ganin za’a b’ollowa abin?”
Mik’ewa barrister Hidaya tayi tace “Sam bada ni za’ayi wannan aikin ba haka kawai ina zaune lafiya , ai nasan kin San Barrister Hadiza itama irin halin kine da ita ta nace sai ta gano wannan mutumin in takaice miki labari karshe sawa yayi aka d’auko ta yayi mata fyad’e na rashin mutunci kuma d’auki hotunan ta tsirara ya watsa su a social media, tsabar bakin ciki sai da ta kusa mutuwa wallahi, Dan haka Hafizatu Allah ya baki sa’a nayi nan” ta fad’a tana fita daga wajan.
Jin haka yasa sauran matan suka tsorata suka dinga barin wajan sai da ya zama daga Hafiza sai maza guda biyu a zaune , Hafiza tace ” to ko kuma zaku gudun ne?”
D’aya daga ciki ya mik’e yace “wacce Hidaya ta baki labari tare suka had’a kai da Barrister Buhari shima bai kyale shi ba sai da yayiwa matar sa da k’anwar sa fyad’e kuma ya turo masa hotunnan yace masa in bar aiki a kansa ba wallahi sai ya yad’a su a media, nima bazan iya ba Allah ya baki sa’a”
D’ayan yace “A’a nima tsaya ni mu tafi bazan iya ba wallahi inason matata da y’an uwana ” ya fad’a suna fita tare daga wajan.
Dukan table tayi tace “wai waye wannan Bad man d’in? Su kuma matsorata kowa ya gudu sun barni ni kad’ai , to ni da Allah na dogara babu abinda ya isa yayi min indai Allah bai tsara hakan ba, ” mik’ewa tayi ta rataya jaka tace “ina nan akan baka ta na ganin bayan mutumin nan” ta fad’a tana fita daga wajan.
******
Sauke wayar yayi daga kunne yayi murmushi mai baiyanar da sirrin kyaun sa yace “Barrister Hafiza sabuwar customer ta kenan , ina yi miki barka da shigowa rayuwar Bad man , da kinsan waye ni da bakiyi gangancin k’ok’arin shiga rayuwa ta ba amma babu komai nasan ta yarda zan b’ullo miki sai kinyi Dana sananin sanin sunana a rayuwar ki”
Waya ya d’auka ya kira yaran sa suna d’auka yace “another baby” kawai ya kashewar wayar ya cigaba da murmushi.
*Tofa ya akayi yasan shirin Hafiza a kansa*🤔
Hafiz ya katse mata tunani da fad’in “Lafiyar kuwa ?”.
+
Bata yi magana ta mik’a masa wayar , bai karb’a yace ” rik’e kinsan bana so ina tuk’i ina danna waya kawai ki fad’a min abinda faru.”
Tace “Message akayi min aka ce min wai sai an takura rayuwa ta , kuma yana gab da baiyana kansa a gare ni amma wai ko ya baiyana ban isa na kama shi ba .”
Tsaki yayi yace “wai Wannan mutumin kike nufi? Shi har ya isa da zaice baza ki iya kama shi ba , ya baiyana kan nasa daman haka muke so ai , nidai buri na ki cire damuwa a ranki .”
Shiru tayi bata kuma magana ba .
Gab da azahar suka shiga garin Kano mai tarin albarka , tunda suka shigo Hafiza take faman baza ido tana santin garin kana ganin ta kaga y’ar k’auyen garin Kd.😜
Basu wuce ko ina ba sai Sakkoto road , a bakin wani tank’amemen gida suka tsaya Hafiz ya fara danna horn .
Da yake an ba’a San da zuwan su ba sai mai gadi ya lek’o ai yana arba da Hafiz ya bud’e k’ofar yana washe baki , ko da suka yi parking Hafiz suka gaisa da mai gadin sannan ya Bud’ewa Hafiza ta fito ya rik’e hannu suka shiga cikin gidan.
Tun a parlour ya fara k’wallawa Janan kira , jin muryar Yayan ta yasa ta fito da sauri tana murnar zuwan sa.
Turus ganin Hafiza tsaye tana sakar mata murmushi ai sa ta fasa zuwa wajan Hafiz ta rungume Hafiza tana kwallawa Mama kira .
Mama ta fito tana fad’in “Haba Janan Wannan kira haka , lafiya?”.
Tace ” Mama Yaya Hafiz ne yazo tare da Aunty Hafiza. “
Sai kuwa Mama ta washe baki tace “Kai sannun ku da zuwa , kunsha hanya Ku zauna mana .”
Zama Hafiza tayi tana sunkuyar da kai , Mama ta harari Hafiz tace “meyasa baka fad’a min zaku zo ba ai Dana shiryawa y’ata Abinci .”
Dariya yayi yace “mamaki muke son Baku shiyasa.”
Janan tace “Ai kuwa kun bamu mamakin , kash gashi Aunty Salima bata nan jiya suka yi tafiya da mijin ta , amma nasan zata ji haushi wallahi. “
Rik’e baki Hafiz yayi yace “kice na shiga uku da mita , Mama ina Uncle d’in?”.
Mama tace ” Yana masallaci amma yanzu zaka ganshi.”
Hafiz yace “muma bara muyi sallah sai muzo asha hira ” ya fad’a yana rik’e hannun Hafiza alamun ta Mik’e.
Bige hannun sa Mama tayi tace “kai kam Hafiz baka da ta ido wallahi, to babu inda zata kaje ka dawo , D’iya ta tashi muje ciki” ta fad’a tana Jan hannun Hafiza suka shiga d’aki.
Bayan an idar da sallah Hafiz da Uncle tare suka shigo suna hira , a parlour suka yada zango uncle yace “Wai ina Hafizan ne?”.
Mama da ta fito yanzu tace ” Yanzu zata fito ” ta fad’a tana shiga kitchen.
STORY CONTINUES BELOW

Hafiza ta fito tana sunkuyar da kai ta zauna a k’asa tace “Barka da Rana”.
Murmushi Uncle yayi yace ” Haba tashi ki koma kan kujera , sai kace wata bak’uwa maza tashi.”
Mik’ewa tayi ta zauna a kan kujera tana wasa da zoben hannun ta , Uncle yace “Ya aikin naki?”.
Tace ” Alhamdulilah “.
Uncle yace ” Masha Allah , ina fatan dai lafiya kuke zaune ko?”.
D’agowa tayi ta kalli Hafiz aikuwa suka had’a ido ya kashe mata ido d’aya yana d’aga mata gira , sunkuyar kai tayi tace “Babu komai “.
Uncle yace ” Masha Allah haka ake so.”
Hafiz ya kalli uncle yace “Uncle wai kuwa su Mu’azzam suna zuwa kuwa?”.
Uncle yace ” A’a basa zuwa , ai idan kaga Mu’azzam a gidan nan to wata babbar matsalar ce ta kawo shi , to gwara ma Humaira ta kan zo wajan Janan amma shi da Mahaifiyar sa ko lek’e , kuma ko da wasa uwar taji labarin Humaira tazo gidan nan ta shiga uku inta dinga zagin ta wani lokacin ma har da duka , da bakin ta Humairan ta fad’a min dan ita tana son y’an uwan ta.”
Ajiyar zuciya Hafiz yayi yace “Na rasa abinda nayiwa Aunty gabad’aya bata k’auna ta , kuma ni a matsayin uwa na d’auke ta ba kishiyar uwa ba , da ace Umma tana raye yadda zan yi mata biyayya haka zan yiwa Aunty , ta hana y’an Uwana zuwa inda nake kofa zuwa gaishe ta nayi banda harara da tsaki babu abinda take min , ni inason y’an uwa na kuma zamu je gidan dan Hafiza ta sansu su Santa.”
Uncle yace “Hakan yayi kyau Allah ya baka ladan zumunci.”
Hafiz yace “Ameen”.
Haka aka dinga hira ana wasa ana dariya .
Bayan sallar i’sha an gama cin Abinci kowa ya mik’e ya tafi d’akin sa aka bar Hafiza da Hafiz a zaune .
Mik’ewa Hafiza tayi cikin Tsokana tace “to nima dai zan kwanta sai da safe ” ta fad’a tana niyar barin wajan.
Rik’e hannun ta yayi yace “ok bara muje mu kwanta a d’akin da zaki kwana d’in” ya fad’a yana mik’ewa.
Zaro ido tayi tace “ka Yanzu in akace kazo mu kwana a d’akin Janan sai ka kwana?”.
D’aga kafad’a yayi yace ” to sai me ba wajan Matata nazo ba.”
Hafiza tace “to kuwa baza ayi Wannan abin kunyar dani ba.”
Matsowa yayi kusa da ita sosai har tana jin saukar numfashin sa , ya zuba mata ido yana yi mata wani irin kallo cikin wata irin murya yace “Meye Dan na kwana kusa Matata ? Ni bana jin kunyar kowa a ko ina zan nuna ke Matata ce .”
Yanayin da yayi maganar da kuma yadda yake kallon ta yasa jikin Hafiza yayi sanyi tana jin wani Abu nayi mata yawo a jikin ta , kasa magana tayi ta kau da kai Dan bata so su had’a ido .
Murmushi yayi ganin yanayin da ta shiga sai rik’e hannun ta yana matsawa a hankali yace “Baki ce komai ba kinyi shiru”.
Nan ma tayi shiru bata amsa ba , bakin sa yakai satin kunnen ta yace ” Kina wani basarwa bayan kema kinyi kewar mijin ki .” bai tsaya ta bashi amsa ba ya ja hannun ta suka d’akin sa.
Washe gari a gajiye Hafiza ta tashi dan ba k’aramar wahala tasha ba a hannun Hafiz , ganin yana wanka yasa ta gyara parlourn sannan tayi wanka ta fito ta nufi d’akin Mama.
Suna zaune an gama karyawa ana hira ana dariya Hafiza ta shigo.
Har k’asa ta durk’usa ta gaida Mama da Uncle sannan ta zauna tana sunkuyar da kai.
Janan ta kalli Hafiza tayi murmushi tace “Aunty na an tashi lafiya?.”
Hafiza tayi murmushi Dan har cikin zuciyar ta tana k’aunar Janan tace “lafiya lau “.
STORY CONTINUES BELOW

Kafin Janan tayi magana Hafiz ya shigo parlourn , kallo d’aya Hafiza tayi masa ta d’auke kai Dan yadda taji gaban ta na fad’uwa tsabar kyaun da taga yayi.
Janan ta saki baki tana kallon sa tace ” Yaya nah Wannan kyau haka kamar zaka je gasar kyauwawa na duniya gabad’aya. “
Murmushi yayi yace “kin cika surutu Janan , ya na ganki a gida ina makarantar?.”
Janan tace “ai mun sami Hutu Dan da Baku zo ba mana da cikin satin nan zan sauka a Kaduna.”
Hafiza yace “yayi kyau.”
Janan ta shagwab’e fuska tace “Dan Allah Yaya ka dawo nan da zama ina so na dinga ganin ka kusa dani Dan Allah ka dawo nan.”
Kallan ta yayi yaji tausayin ta har cikin rainsa amma sabida ya nunawa Uncle da Mama kara sai yace “haba Janan to anan d’in me zai ciki? Ga Abban ki ga Maman ki to meye abin damuwa kuma? Kedai kawai yau shagwab’ar ce ta tashi.”
Uncle yace “duk da haka dai da zaka dawo nan d’in sai yafi , ko ba’a gidan nan ka zauna ba sai ka sami gida daga cikin gidajen ka ka zauna muma muna so mu ganka kusa da mu ba iya Janan ba kawai.”
Murmushi Hafiz yayi yace “To Uncle za’a duba a gani.”
Mama tace “ai gwara a duba d’in”.
Hafiz yace ” Mama wai ni ina su Fadil ne badai har Yanzu bai samu Hutu ba ?”.
Mama tace “Hmm kaima dai ka fad’a Hafiz har yanzu yace basu samu Hutu ba kasan karatun likitanci akwai wahala shiyasa ba kasafai suke yin Hutu ba.”
Janan tace “Allah sarki Yaya Fadil yana can England ana karatu , nayi kewar sa sosai wallahi ji nake kamar na tashi na bishi.”
Uncle yace “ko zaki yi tsuntsuwa ki bishi?.”
Gabad’aya parlourn aka sa dariya.
Mama tace “Hafiza baki ci komai bafa kike zaune , haba Hafiza bak’unta zaki yi mana a gidan nan tashi ki had’a abinda zaki ci.”
Hafiz ya shagwab’e fuska yace ” Nifa Mama?. “
Tab’e baki tayi tace “ai na daina yi da kai tunda na samu d’iya .”
Akayi dariya gabad’aya .
Bayan sun gama cin Abinci Hafiz ya kalli Hafiza yace “idan kin gama ki same ni a mota.”
Ya kalli Mama yace “Mama gidan Aunty Zamu je .”
Mama tace “ai hakan yana da kyau gwara kuje d’in.”
Uncle ya Mike yace “to nima dai na wuce wajan Sana’a ta” ya fad’a yana fita daga parlourn.
Janan tace “Yaya Dan Allah nazo na raka Ku ? Kaga gidan babu kowa saura mu kad’ai .”
Kafin yayi magana Hafiza tace “d’auko mayafin ki muje.”
Ai kam da sauri ta mik’e tayi d’aki tana murna.
Shi kuwa Hafiz mota ya shiga yana jiran fitowar su .
Tare suka fito Hafiza ta bud’e gaba ta shiga Janan kuma ta shiga baya.
Baice komai ba suka fara tafiya sai sautin karatun alkur’ani da yake tashi a motar , ta mudubi ya kalli Janan da take ta washe baki Dan yasan farin ciki take sun fita tare dashi .
Murmushi shima yayi yana jin k’aunar kanwar tasa har zuciyar sa .
Janan ta katse masa tunani da fad’in “Aunty Hafiza wai kwana nawa zaku yi?”.
Hafiza tace ” Kwana biyar munci d’aya yanzu saura hud’u. “
B’ata rai Janan tayi tace “Haba Aunty ina laifin wata d’aya.”
STORY CONTINUES BELOW

Hafiza tayi dariya tace “lallai ma Janan wata fa kika ce.”
Janan tace “eh mana , Yaya nah Dan Allah ku bari sai kunyi wata d’aya sai Ku tafi.”
Banza yayi mata bai kula ta ba , nan take ta tsuke bakin ta dan tasan hali .
Bata k’ara magana ba har suka k’arasa gidan da zasu je.
Sai a sannan Hafiz yayi magana yace “Janan duk abinda zasu ce miki kar ki tanka musu kiyi musu shiru.”
Janan tace “to “.
Bud’e motar suka yi suka shiga cikin gidan.
Da sallama suka shiga parlourn.
Wata hamshak’iyar mata ce a zaune a parlourn dak’yar ta amsa sallamar tasu.
Tunda taga Janan da Hafiz ta b’ata rai kamar taga mutuwar ta , Hafiza tace ” Barka da rana “.
Wani banzan kallo tayiwa Hafiza sannan tace ” barkan ki.”
Hafiz ya kalle ta yace “Aunty mun same Ku lafiya?”.
Cikin masifa tace ” da baka same mu lafiya ba zaka ganni a zaune anan ? Nifa bana son shishshigi a cikin lamura na.”
Janan kuwa daman ita Tsoro Auntyn take bata sai tayi shiru bata ce komai ba.
Humaira ta fito da gudu tana fad’in “oyoyo Yaya Hafiz da Janan “.
Wata banzar harara Aunty tayiwa Janan amma tayi mata banza kamar bata ganta ba Dan ita tana son y’an uwanta.
Kusa da Janan ta zauna tace ” Sis kwana biyu.”
Janan tayi murmushi tace “kedai bari sis exams ta sani a gaba amma yanzu na gama har munyi Hutu.”
Humaira ta tace “nifa daman na daina kula Yaya Hafiz , baya nema na gabad’aya ya manta dani.”
Murmushi Hafiz yayi yace “haba kin tab’a ganin inda Yaya ya manta da k’anwar sa ? Ban manta dake ba kawai dai aiki ne yayi min yawa.”
Murmushi Humaira tayi tace “kuma fa haka ne big bro shiyasa nake ji da kai.”
Ta kalli Janna tana nuna Hafiza tace “Aunty Hafiza ko?.”
Janan tayi dariya tace “Ashe dai zaki gane ta.”
Wani tsale tayi taje ta rungume Hafiza tana fad’in “kai masha Allah gaskiya Yaya Hafiz ka iya aure Wannan zankad’ed’iyar mata haka , Aunty Hafiza sannu da zuwa .”
Y’ar dariya Hafiza tayi tace “yauwa Humaira mun same Ku lafiya?”.
Tace ” Lafiya lau wallahi bara na kawo muku ruwa.”
Ai tana juyowa taji saukar mari a fuskar ta , cike da mamaki Humaira ta kalli Aunty tace “Aunty lafiya kika mare ni?.”
Aunty tace “ban sani ba, da yake y’ar iska ce bara mutunci wacce bata San ciwon kanta ba shine zaki dinga kula wad’annan gadon tsiyar , bara kiji daga yau na kuma ganin kin kula d’aya daga cikin su sai na yi miki tsinanne duka , ko uwar su Aminatu ce zata dawo daga lahira Yanzu bata isa na kula taba balle kuma yaran ta , banza shashasha Mu’azzam ne kawai yake Goya min baya amma ke badan nasan ke y’ata bace cewa zanyi ke jinin tsiya ce wallahi , Ku kuma bara kuji daga yau kar na k’ara ganin k’afar Ku a cikin gidan nan tunda ba da kud’in Aminatu dana Ali na gina shi ba , daga yau sai yau kar wacce ta kuma tako k’afar ta nan gidan”.
Cikin fushi Hafiz ya mik’e yace “Dan ina yi miki biyayya a matsayin ki na kishiyar uwata ba hakan yana nufin tsoron ki nake ji ba , ke badan ina ganin idon Humaira ba da ke har kin isa kizo kina zagin iyaye na , akan iyaye na babu abinda bazan iya yi ba zan cire kallan mahaifiyar da nake miki naci miki mutunci in yaso daga baya na dawo dashi , ki kula ki kuma shiga hankalin wallahi, kuzo mu tafi” ya fad’a ya fita daga parlourn.
Bayan sa suka bi duk jikin sa a sanyaye , suna shiga motar yaja ta da gudun tsiya ya bar unguwar.
Tunda suka shiga babu Wanda yake yiwa wani magana har suka k’arasa gida.
Ko kula su baiyi ba ya bud’e motar yayi cikin gida , parlourn Mama suka shiga ita da Janan .
Mama ta kalli su tace ” daga ganin fuskar ku Maimuna tayi abinda ta saba , kai wannan mata wane irin tsana take yiwa mahaifiyar Ku haka ? Matar da take cikin kabari amma da ita take gaba ni na rasa wannan Abu wallahi. “
Janan tace “ke dai Bari Mama zagin yau yafi na ko yaushe Dan yau har sunan Umma da Abba ta ambata a cikin maganganun ta , ran Yaya Hafiz ya b’aci sosai Dan tunda muka tawo bai kula kowa daga cikin mu ba.”
Mama ta kalli Hafiza tace “Kinga fa irin kishiyar uwar da Allah ya bawa su Hafiz , Yanzu dai ki tashi kije ki bashi Hak’uri ki kwantar masa sa hankali.”
Hafiza tace “to” ta mik’e ta nufi d’akin sa.
A zaune ta ganshi ya jinginar da kansa jikin kujera ya rufe ido , a hankali ta k’arasa ta zauna a kusa dashi ta rik’e hannayen sa duka biyu tace “Dan Allah kar kasa damuwa a cikin ranka ka kwantar da hankalin ka tunda Allah yaga niyar ka kuma zai baka lada , Dan Allah ka cire damuwa a ranka.”
Bud’e ido yayi da suka koma ja yace “Zan iya jure komai a rayuwa ta amma banda zagin iyaye na , duk mutuncin ka da nake gani indai zaka bud’e baki ka zagi iyaye na to wallahi bazan kyale ka ba .”
Hafiza tace “Shiyasa nace kayi Hak’uri ka cire komai a ranka in ba haka ba zaka jawowa kanka wani ciwon , Dan Allah kar ka rik’e wannan a cikin zuciyar ka.”
Shiru yayi bai kuma cewa komai ba har akayi kiran sallah ya mik’e ya nufi masallaci.
Da daddare suka zaga dangin mahaifiyar sa , sosai yaga kauna ana nan nan dashi , Hafiza kuwa kamar a cinye ta sabida murnar ganin ta , hakan sai ya Wanke wancan b’acin ran da yake tare dashi.
Bayan kwana uku
Hafiza taji dad’in zama a gidan Uncle Dan sosai ake nuna mata kauna .
Yau suka tashi da shirin komawa garin Kaduna Dan ana tayiwa Hafiz waya akan yana da aiki sosai a company.
Bayna sun gama suka fito Janan ta ruk’unk’ume Hafiz tana kuka , ba k’aramin Tausayi ta bashi ba , ganin irin kukan da take sai uncle yace “kiyi shiru kinji Janan zuwa wani satin nayi miki alk’awarin zuwa Kaduna mu zauna har hutun ki ya k’are , sai mu zauna a gidan mu na can ki kwantar da hankalin.”
Sosai tayi farin ciki dajin wannan labari ta dinga murna , Sallama suka yi Hafiza ji take kamar kar ta rabu da Janan haka suka yi sallama suka d’au hanyar Kd.
Gab da Magariba suka shiga garin Kaduna , koda suka k’arasa mai gadi suka yi horn ya bud’e musu suka shiga cikin gidan .
Washe gari.
K’arar wayar tace ta tashe ta daga bacci , mik’a hannu tayi ta d’au wayar ganin message ne gaban ta ya fad’i Dan tasan ba alkairi bane .
_idan kina son gani na kizo unguwar rimi layi na ashirin da biyar gida mai lamba goma , ammafa kika sake kika fad’awa wani wallahi sai na kashe k’anwar ki Yanzu nake so kizo ba wai sai anjima ba , na baki nan da minti ashirin.(Bad Man)_
Cikin sauri ta mik’e ta saka hijjabi ta fita daga gidan.
Adaidaita sahu ta d’auka ta nufi inda yayi mata kwantance gaban ta na fad’uwa.
Koda suka k’arasa k’ofar gidan mai gadin ya kalle ta yace “Oga yace a fad’a miki kinyi sake lokacin da ya baki ya wuce Dan haka zaki ita komawa” yana gama fad’a mata haka ya juya ya koma wajan zaman sa.
Cikin sanyin jiki ta hau mota ta koma gida.
Tana bud’e k’ofar parlourn taga Hafiz a tsaye a parlour da alama ita yake nema .
Kafin tayi magana ya katse ta cikin tsawa yace “ina kika je da sassafen nan? Wa kika tambaya da zaki fita ? Me kika fita yi?”.
* Jikin ta banda rawa babu abinda yake , sai yanzu take dana sanin rashin fad’a masa.+
Durk’ushewa tayi a wajan zata yi magana yayi saurin katse ta da fad’in “Bana son wata magana kawai ki fad’a min ina kika je.?”
Fashewa tayi da kuka tace “D’azu ina bacci akayi min text akace nazo unguwar rimi zanga Bad man , kuma na sake na fad’awa wani sai an kashe Hanifa , na rasa yadda zan yine shiyasa naje kawai Dan Allah kayi Hak’uri ni daga yau ma na fita daga Wannan case d’in na gaji” ta fad’a tana k’ara fashewa da kuka .
Jikin sa yayi sanyi a hankali ya tako inda take ya mik’ar da ita tsaye yace ” Shikenan daina kuka , amma da kin sani kin sanar dani da wani Abu ya faru dake fa? Daga yau in irin haka ta faru kafin ki yanke hukunci ki sanar dani , Yanzu to kin ganshi d’in?”.
Girgiza kai tayi tace “Ban ganshi ba lokacin Dana k’arasa sai akace wai time d’in da ya bani ya wuce .”
Yace “Shikenan ya wuce , amma baza ki bar case d’in nan ba ki cigaba Allah yana tare dake.”
Tace “to , bara na had’a break fast” ta fad’a tana shiga kitchen.
Cike da Tausayi Hafiz ya bita da kallo yana raya wani Abu a ransa.
Bayan Sati Uku.
Hafiza ta shigo gidan da sallama , yana zaune a kan kujera yace “har kin dawo daga gidan Ummeen?”.
Tace ” Eh na dawo , Ashe jiya kaje shine baka fad’a min ba , Abbie ya fad’a min irin Alkairin da kake musu Nagode sosai Allah ya bar mu tare.”
D’agowa yayi yace “Dan na yiwa iyaye na Abu sai kinyi min godiya Dan shishshigi , to daga yau bana so kar ki k’ara.”
Murmushi tayi tace “To insha Allah bazan k’ara ba.”
Yace “Kwana biyu case d’in mutumin ki shiru.”
Tace “kaima dai ka fad’a , idan anaso aga farin ciki na a duniya bai wuce ace yau gashi na kama shi ba , zanyi murna sosai.”
Hafiz yace “Allah ya kaimu time d’in, bara naje office ana jira na.”
Tace “To sweet H a dawo lafiya, ka kular min da kanka.”
Murmushi yayi yayi mata kiss a goshi ya juya ya fita daga gidan.
Hafiza na zaune tana danna waya tana karanta sabon novel d’in da Gaskiya writers suka fara , cike da nishad’i take karantawa dan ba k’ara min dad’i littafin yake yi ba.
K’arar Abu taji kamar an bugi gate , da sauri ta mik’e ta saka hijjabi ta fita .
Cak ta tsaya ganin wasu mutane fuskar su a rufe sun ritsa mai gadi da bindiga , jikin ta ya fara rawa da sauri ta juya zata koma taji ance,
“Kin d’aga k’afar ki zan fasa miki Kai.”
Cak ta tsaya jikin ta na rawa hawaye na zuba daga idon ta .
STORY CONTINUES BELOW

K’arasawa wajan ta mutumin yayi yace “bake mai taurin kai ba kin nace sai kin San waye Bad man , to shikenan ki cigaba yace a fad’a miki Yanzu aka fara wasan ” bindiga ya d’auko ya d’aura Mata a goshi yana dariyar mugunta.
Had’e rai yayi kuma ya kalle ta yace “Kinsan Wannan hoton da yayi miki lokacin da ya sace ki ? To yace a fad’a miki zai watsa shi a media sai ya b’ata miki suna” yana gama fad’ar haka yayiwa yaran alama da su bar gidan .
Cikin sauri kowa suka bar gidan.
Kasa motsawa Hafiza tayi a wajan kawai sai durk’ushe a wajan ta saki kuka mai ban Tausayi.
Wannan yace irin rayuwa ce ? Shikenan mai laifi bazai bari a kama shi ba? Tunda haka suka nima na Hak’ura na fita daga harkar su , na Hak’ura. Hafiza ce take magana ita kad’ai tana girgiza kai .
Tana zaune a wajan motar Hafiz ta shigo gidan , cike da mamaki yake kallo ta ganin ta zaune a tsakiyar gida.
Fitowa yayi ya nufi inda take , ganin yanayin ta yasa ya gane babu lafiya , kama ta yayi yace “me kike yi anan ? Tashi maza ki koma ciki” ya fad’a yana mik’ar da ita.
Girgiza masa ka ta fara tana fad’in “na Hak’ura na rabu dashi , shima kuma ya fita daga rayuwa ta , Allah yana gani ai nayi iya bakin k’ok’ari na .”
Cikin rashin fahimta Hafiz yace “waye wai ? Meye ya faru?.”
Parlour tayi a guje tana hawaye bata tsaya bashi amsa ba.
Binta yayi a parlour ya ganta tayi tagumi tana girgiza kai kamar mahaukaciya.
Cikin tashin hankali Hafiz yace “ki nutsu ki fad’a min abinda ya faru.”
Cikin rawar murya tayi masa bayanin komai ta d’aura da cewa “Ni na Hak’ura da kama shin amma da zan samu ko ganin sane nayi nasan waye “.
Rungume ta yayi yana bubbuga bayan ta danshi Tausayi ma take bashi.
Ajiyar zuciya take saukewa a haka har bacci ya d’auke ta.
Kwantar da ita yayi yana kallon fuskar ta cike da Tausayi , a ransa yace ” Nayi miki alk’awari insha Allah komai zai zo k’arshe , zan taya ki Neman Wanda kike nema .”
Haka Hafiza ta kwana ranar kamar Mara lafiya.
Bayan kwana biyu.
Cikin kwanakin Hafiza bata da magana da ya huce ta gano waye Bad man , ta zage sosai tana bincike .
Yau ma kamar kullum tana zaune tana tuno irin singing d’in da yake yiwa yara wayar ta tayi k’ara.
Dubawa tayi taga private number , cike da fargaba ta bud’e message d’in.
_Daga Yanzu har zuwa dare zaki iya zuwa kiga waye Bad man tunda naga duk basirar ki kin kasa ganowa shiyasa na yanke hukuncin baiyana miki kaina , kizo Governor road layi na sha biyar gida mai number 2, idan kika zo yara na zasu shigo dake kar ki damu zaki ganni yau amma baki isa ki kamani ba , kuma zan cigaba da abinda nake yi bawai zan fasa ba._
Tana gama karantawa Hafiz ya sauko da sauri yana duba agogo , cikin sauri Hafiza tace “yauwa kaga” ta fad’a tana mik’a masa wayar.
Karb’a yayi ya karanta yace “Alhamdulilah haka muke so daman , yanzu kinga sauri nake zanje office ki bari sai anjima sai muje tare.”
Girgiza kai Hafiza tayi tace “Dan girman Allah ka barni naje insha Allah babu abinda zai faru , Dan darajar Kabarin iyayen ka ka barni.”
Babu yadda zaiyi dole yace “ok maza tashi ki d’auko hijjabi na sauke , amma Allah ya sani bana son zuwan ki ke kad’ai amma kin nace.”
Bata tsaya sauraran sa ba tayi ciki da sauri , hijjabi ta d’auka ta fito tace “na gama .”
Cikin rashin fara’a yace “muje” Dan baya son Fitar .
A k’ofar gidan da yayi mata kwatance ya sauke ta yace “Nama fasa zuwa office d’in ta muje tare” ya fad’a ya bud’e k’ofar motar.
Tsayar dashi tayi tace “basai ka shiga ba kila in ya ganka ya fasa baiyana kansa , a waya a hannu na duk abinda ya faru zan yi maka flashing ” bata tsaya sauraran sa ba tayi cikin gidan.
Hafiz kuwa zuciyar sa tana fad’a masa kawai yabi bayan ta , hakan yasa ya bud’e motar ya shiga cikin gidan .
Har cikin parlourn aka shigar da Hafiza Wanda suka shiga da ita duka fuskar su a rufe take.
K’arar takalmi taji hakan yasa ta juya Dan gannin waye .
Mik’ewa tayi tayiwa mutumin kallan up and down tace “daman Kaine Bad man d’in ? Mtwsss Ashe ma ba wani abun arzuki ne da kai ba , to……”
Katse ta yayi ta hanyar d’aura hannun sa akan lips dinsa yace “shihhhhhhh .”
Fuskar a rufe hakan yasa maganar sa bafa fito sosai ba yace “bani ne Bad man ba kinga Bad man can” ya fad’a yana nuna mata wata k’ofa.
Zubawa k’ofar ido tayi Dan ganni waye zai b’ullo.
K’afar sa sako kafin ya bud’e labulen fuskar sa ta fito .
Da sauri Hafiza ta mik’e tace “A…………….”
Ku canka😜
__________📖* Da sauri Hafiza ta mik’e tace “A’a Meya kawo ka nan ?.”
+
Murmushi yayi mai sauti yace “Bani kika zo nema ba hala?”.
Cikin rashin fahimta Hafiza tace ” Ni da muka rabu da kai akan ka tafi office ya akayi ka shigo nan?.”
Matowa yayi yazo kusa da ita yace ” Hafizty ba Bad man kika zo nema ba?”.
Tace “Kwarai kuwa kama ka sani ai.”
Y’ar dariya yayi yace “Bud’e idon ki da kyau kiga Bad man tsaye a kusa dake , Hafiza duk wayon Neman Bad man da kike ba wani bani ila ni!!”.
D’an tsaki tayi tace ” Dan Allah ka daina had’a kanka da wancan mutumin , in zuwa kayi ka taimaka min kawai ka fad’a min.”
Murmushi yayi yana nannad’e hannun rigar sa , nan take Wannan bak’in zanen ya baiyana .
Gaban ta ya fad’i amma bata nuna ba Dan ita gani take wasa yake.
Bai kula ta ba ya d’auko wani spray ya fesa a wajan nan take rubutun ya goge kamar babu shi a wajan.
D’ago kai yayi ya kalle ta yace “har yanzu baki yarda ba ko?”.
Itadai tana tsaye ta kasa motsawa , cikin rawar murya tace ” idan kasan wasa kake Dan Allah ka daina”.
Hafiz yace “Hafiza wallahi! Wallahi!! Nine Wanda kike nema , nine dai Bad man kuma nine Hafiz d’inki , kinsan dai bazan yi rantsuwa akan k’arya ba.”
Zuba masa ido tayi Dan duk yadda zata yi Dan taga hawaye ya zubo ta kasa , dafe kai tayi dan ji take kamar zai b’alle .
Cikin rawar murya tace “Hafizz ! ka cuce ni ka gama dani , kayi wasa da hankali na , na zauna da Wanda nake nema ido rife na zauna da mai lefi mazinaci , fasiki mai lalata y’ay’an mutane , ka cuci Hafiz” sai a sannan hawaye masu zafi suka fara zarya a idon ta.
Murmushi yayi ya tsuguna a kusa da ita ya d’age gira d’aya yace “Sauk’ak’a miki nema na fa nayi , Yanzu baga shi kinsan waye Bad man , Haba Hafizty ki daina zubar da hawayen mana” ya fad’a yana k’ok’arin share mata hawaye.
A fusace ta mik’e tace “kar ka kuskura k’azamin hannun ka ya tab’a ni , Kuma bara kaji sai na maka ka a kotu an yanke maka hukunci mai tsauri , Na tsane ka ! Kuma dole ka sake ni ko kana so ko baka so.”
Mik’ewa yayi ya zauna akan kujera ya d’aura k’afa kan d’aya yace ” Tab’a ki Yanzu na fara Hafiza domin ke Matata ce , zancen kotu kuma eh ki kaini amma baki isa kisa a kulle ni ba , baki da hujjar da zaki bawa kotu a kaina, saki kuma wallahi bazan sake ki ba domin kuwa ina mutuk’ar sonki kuma babu Wanda ya isa yace na sake ki”.
STORY CONTINUES BELOW

Fashewa tayi da kuka ta fara tafiya tana girgiza kai , wani jiri ne ya d’auke ta aikam ta fad’i sumammiya.
Cikin tashin hankali Hafiz ya mik’e ya d’auko ruwan sanyi ya shafa mata a fuska , ajiyar zuciya tayi tana bud’e ido a hankali.
Ganin ta jikin Hafiz sai ta fashe da kuka tace “Dan Allah kace min mafarki nayi ba gaskiya bane Dan Allah .”
Tausayi ta bashi sosai amma babu yadda zaiyi dole ya sanar da ita .
Rungume ta yayi yace “Ki daina damun kanki akan abinda na fad’a miki , Hafiza ba mafarki kikayi ba nine dai Hafiz dinki kuma nine Bad man , kuma…..” .
Sakar Marin da yaji a fuskar sa ya hana shi k’arasawa , mik’ewa tayi tana kuka sosai tace ” Allah ya isa tsakani na da kai Hafiz , ka cuci rayuwa ta ka raba ni da farin ciki na , Ashe duk Wannan abubuwan da suke faruwa duk kai ka shirya ? Kaine kake yo min message Kaine ka turo mutane gidan ka suka ritsani da bundiga , Kaine ka sace ni , Kane ka sace k’anwata , duk abinda yake faruwa Ashe duk cikin shirin Kane , Me nayi maka ka zab’i ka hukunta ni ta Wannan hanyar ? Na tsane ka Hafiz na tsane ka bazan k’ara zama da kai ba dolen dole ka sake ni kuma wallahi tallahi alk’awarin Dana d’auka sai na cika shi karka ga wai kana matsayin mijina sai na wulak’anta ka kamar yadda kake wulak’anta y’ay’an mutane , mazinaci , fasik’i , mayaudari , kayi wasa da hankali na nima kuma zanyi wasa sa naka , ka jira sammaci” ta fad’a tana juyawa zata bar parlourn.
Duk da yaji zafin maganganun ta amma haka ya d’aure yace “dakata mana Matata , duka Wannan abinda kika lissafa babu Wanda za’a cika shi , ki kaini kotu ban hana ki ba amma baki isa kisa alk’ali ya kama ni ba , saki kuma da kike fad’a bazan sake ki ba domin kina d’auke da cikina a jikin ki , mazinaci , fasiki , mayaudari duk naji kuma na karb’a amma ki fad’a min Yaya sunan matar mazinaci , fasiki , fad’a min Yaya sunan ta ? Tabbas nayi wasa da hankalin ki Wanda koda wanine yazo yace miki nine Wanda kike nema baza ki tab’a yarda ba , duk abinda kika fad’a nine na tsara shi kuma ya tafi dai-dai yadda nake so , nasan Yanzu babu inda zaki wuce sai gidan Ummee ko ? To kije maza ki k’arasa” bai tsaya jin abinda zata ce ba ya juya ya shiga d’akin daya fito.
Da gudu ta fita daga gidan tana kuka sosai k’afar ta ko takalmi babu , koda ta fito bata damu da mutane ba haka take kuka harda shashshek’a .
Mota ta Tara ta hau ta fad’a masa inda zai kaita , tunda ta shiga take kuka tana tuno irin rayuwar da suka yi da Hafiz , Ashe duk yaudara ce ba sonta yake ba , har suka k’arasa bata sani ba sai da mai adaidaita sahun yace ” baiwar Allah mun iso fa.”
Jikin ta na rawa ta fita , hannun ta ta duba babu komai , ganin haka sai mai adaidaitan yace “barshi kawai Allah ya baki lafiya” ya fad’a yana barin wajan Dan shi kallon mahaukaciya yake Mata.
Da gudu ta shiga gida tana kuka , Ummee tana zaune tana ninkin kaya taji shigowar Hafiza , fad’awa kan Ummee tayi tana kuka sosai.
Abbie da yake zaune shida Hanifa cikin tashin hankali yace “Lafiya Hafiza meya faru? Ina Hafiz d’in?.”
Cikin kuka tace “Abbie Hafiz ya cuce ni ya yaudare ni , Ashe daman ba sona yake ba , ni kawai kusa ya sake ni bana sonsa na tsane shi.”
Cikin fargaba Ummee tace “wai meye ya faru ne Hafiza? Me Hafiz d’in yayi miki ?”.
Tace ” Ummee shine Wanda nake nema , shine Wanda ya sace ni ya sace Hanifa yake lalata y’ay’an mutane , Ummee Ashe shine Bad man d’in da nake nema yayi wasa da hankali na ya aure ni na zauna dashi har tsahon wata guda ba tare Dana sani ba , Dole ya sake ni Ummee ” ta fad’a tana k’ara sakin kuka mai cin rai.
Kafin Abbie yayi magana Suka ji sallamar Hafiz tare da shigowa gidan.
Mik’ewa Hafiza tayi da sauri tace “ka Fitar mana daga gida nan ba gidan y’an iska bane , na fad’a maka bazan zauna da kai ba na tsane ka”.
Kallan Ummee Hafiz yayi yace ” kin gani ko Ummee gabad’aya na rasa abinda yake damun ta ,sai wasu maganganu take tun d’azu , nifa gani nake anya Wannan binciken da take bai tab’a mata kwakwalwa ba?”.
Ummee ta rik’e Hazifa tace “Na ga alamun hakan kuwa , gashi duk abinda ka fad’a a waya tazo tana yi , Allah yasa dai ba asiri yayi mata ba.”
Abbie ya dafa kafad’ar Hafiz yace “kar ka damu Hafiz zata dawo dai-dai insha Allah.”
Cikin damuwa sosai Hafiz yace “Allah yasa”.
Wata k’ara Hafiza tayi tace ” Ummee yana wasa da hankalin Ku kamar yadda yayi wasa da nawa , Abbie duk abinda yake fad’a muku k’arya yake ba gaskiya bane.”
Kallan Hanifa da take kuka Abbie yayi yace “jeki maza ki kirawo min Dr Faruk yazo yayi mata allurar bacci.”
Da sauri ya fita Dan itama gani take yayar tata ta fara zarewa.
Fusge- fusge take tana kuka tana fad’a musu Hafiz k’arya yake amma ina su Abbie gani suke Hafiza asiri aka yi mata ko kuma shafar aljanu.
Zuwan Dr yayi mata allura nan da nan bacci ya d’auke ta .
A k’asa Hafiz ya zauna yayi tagumi idon da yayi ja kamar garwashi.
Kallan sa Abbie yayi cikin Tausayi yace “kayi Hak’uri kaji yanzu gashi can ana kiran sallah tashi kaje tayi sallah.”
Mik’ewa yayi jiki a sanyaye ya fita daga gidan.