YANKAR KAUNA CHAPTER B
Tashi tayi ta ajiye kundin sirrin a cikin wardrobe. Bata tsaya ko ina ba se sashin rufaida, tana zuwa ta rungume ta, addua take mata godiya, fadi take
+
“kin tseratar da d’a na daga hallaka, Allah ne kadai ze biyaki”.
Kuka sukai sosai sannan su ka yi shiru, hakan ya sake tayar da shauk’in son umair a zuciyarta. Barcin da batayi ba kenan ta kwanta cikin yaranta, tana addua har sulusin dare sannan ta tashi ta yi salloli da addua.
💔💔💔
Akwana a tashi shekaran Umair biyu da Rasuwa, rabon Rufaida da farinciki tun rasuwan Umair, Alh Zunnurain ya kafa mata maaikatan Zane zane , dukiyanta kuma massallatai da rijiyoyi ta gina duk d sunan Allah ya kai Rahma zuwa ga mijinta.
Zaune take ta na Zane, ba abinda ya fado mata a rai se sanda take da cikin khadija.
Ranar hana ta Zane yayi, duk motsin da tayi yana manne da ita, alkaura da kalaman soyayya da dadadan kalamai
Kuka tasaki sosai, ji takeyi kamar lokacin ne taji sak’on rasuwar Umair.
“Rufaida me ke faruwa ne, yanzu takwara na yazo min wai gaki can kina kuka”. Alhaji Usman ne ya tambaya.
A hankali ta dago kai tana kallonsu, nan taga duk sun riked’e sun zama mata Umair, murmushi ta saki tace ” Buddy dama kana raye ka barni cikin wannan hali, please ka dawo min da farinciki na”.
Hankalin Alh ya tashi, ya juya yaga wa take kira da sunan da umair kawai take kira dashi, nan shima sai yaga Umair ne ke masa murmushi. Kafin ya ankara sai jin shi yayi yace “Grand PA don Allah ka lallasan mun mummy na tayi shiru, ka bata hakuri please”.
Nan ya gano ashe Zunnurain ne ba Umair ba, rungumarshi yayi yana hawaye yace “Rufaida daina kuka ga farincikin ki nan a gabanki. Allah bai d’auke mana Umair ba se da ya bamu waninsa, wanda zai so ki fiye da Umair, jininki, ‘Danki, farincikinki, komi naki, kinga kuwa abin ki gode Allah ne”.
Ajiyan zuciya ta saki tana share hawaye. Bai bar d’akin ba se da ya sata tayi alwala ta hau kan sallaya domin yin nafiloli ko zataji sanyi.
Yana fita parlour din Haj Safiyyah ya shiga nan ya iske su biyun da yaransu mata. Haj Jamila ce mai bayani, tana ganinsa tai shiru tana dariya.
“Me kuke tattaunawa ne, ba ko gayya”. Ya fad’i yana mai karasowa ciki. Duk suka yi dariya. Yaran suka gaida shi daya bayan daya. Kasancewa ya san da zuwansu, bai tsaya tambayarsu dalilin zuwansu ba.
“Gobe inshaaAllahu zan je India, dama saura kwana hudu ne tafiyar don ganin likita, dani da takwara na zamu wannan karan”.
Sukai masa fatan dacewa da kuma k’aruwan lafiya. Wasu na mamakin zuwansa da Zunnurain.
Haj Jamila ce ta kasa boye mamakinta se da tace ” Uwar me zakaje yi da wannan yaron, ko tun yanzu zaka daura sa akan iyayensa ta hanyar fifitashi, ‘ya’ya mata ma ai rahama ne, kuma ma ai ba gadonka gareshi ba illa kai da keda na…”
“Uwarki zanje yi dashi Jamila”. Nan ya katseta a fusace.
“Uwata fa kace Alhaji?”
“Na fad’i ko zaki rama ne, ni ban san mai suka tsare miki ba, wannan kiyayya har ina. Duk abinda kikai ma Umair ina sane, amma kika gwada akan zunnurain zakisha mamaki na, angirma ba’a san an girma ba”. Mtswww tsaki yaja ya fita ya barsu nan.
Yana fita Aisha ta kalli mahaifiyarta tace “Mama na rasa me kika tsare ma Alhaji ne, se ya ta wulakanta ki, ko don yaga duk mu mata ne, wallahi zamu dauki mataki fa.”
“Gaskiyarki Indo, ai wannan wariya da ake nuna mana ya isa haka, ko ba komi se da kika k’are haihuwa sannan aka karo aure, ba dan ba danba ai da se muce mun haife su.” Cewar maimuna, babbar ‘yar Alh Usman.
“Wai meyasa bakwa son gaskiya, idan Mama ta rik’e kanta ai duk haka baze taso ba”.
Kafin ta rufe bakinta Aisha ta daka mata tsawa ” Wai Salma meyasa kike sallamammiya ne? Ana wulakanta uwarki bakya gani. Allah shirye ki.”
Haka suka cigaba da cecekuce tsakaninsu, Haj safiyyah da yaranta uffan basu ce ba.
2
💔💔💔
Karfe 8pm, agogon k’asar India, Alh Usman Gwandu da aka fi sani da Zunnurain ya isa babban asibitin birnin Bombay. Bai sha wuya ba aka sadashi da matashin likita da kusan duk duniya ake alfahari dashi.
Ya nufo Alhaji yana mai murmushi. Bayan sun gaisa Alh ya kalle shi ya ce
” Dr Ridwan Bagudo dafatan ka gane ni?” Yayi shiru yana sauraran amsarsa.
“Ko a mafarki bazan manta fuskarka ba, tunda har na baku abu mai mahimmanci a rayuwata. Kunzo lafiya?” Cewan Dr Ridwan.
“Lafiya lau, ga d’anka Uthman, Zunnurain” Alhaji ya ce yana mai nuna masa zunnurain.
Rungumarsa yayi yana fitar da hawaye, wannan saurayi dan shekara (10) yafito daga jikin little angel d’insa.
“Ya mamanka? Tayi k’iba yanzu ko? Naga kaima ka fini k’iba”.
Dariya kawai Zunnurain yai. Alhaji ne ma yai magana;
“Tayi k’iba ta k’ara kyau sosai. Cikin shekaru takwas da rabi da aurensu ta haifa masa yara hudu. ‘Yan biyu Safiyyah da Uthman, Khadija da Zainab (mamienka). Cikin shekarun nan ban tsammaci akwai ranar da Rufaida tayi minti ashirin na bak’inciki. Muna godiya ga Allah Umair ya cika alkawari”.
Dariya Dr yayi, kana yace ” Alh nayi farinciki kwarai,amma nasan k’anwata matar alfahari ce, suruka ta gari sannan uwa ta gari ko my son?”
“She is the best mum ever, amma yanzu kullum se tayi kuka, bata dariya, in tana koya mana karatu tana kuka”.
“Whaaaat!!! Alh yanzu kace min tana cikin farinciki?”. Ridwan ya fadi a firgice yana duban Alhaji
“Rufaida na cikin tashin hankali, shine dalilin zuwa na ma. Rufaida ba suruka ta bace, ‘ya ce da nake so fiye da wa’inda na haifa, shine nazo a matsayina na ubanta in sama mata farinciki ta wajenka. Kaine kadai zaka dawo mata da farincikinta. Allah yayi ma Umair rasuwa shekara biyu da suka wuce, duk wani tawakkali da ake son d’an musulmi dashi an samu Rufaida dashi. Amma daga bayan nan duk ta firgice, ta kasa kwantar da hankalinta. Ka taimake ni Ridwan, banson hawayen Rufaida.”Alhaji ya k’arasa yana mai sheshek’a.
8
“Innalillahi wa inna ilaihir rajiun. Allah ya jikan Umair, Ya kai rahma zuwa ga makwancinsa. Zan zo in bata baki, inshaAllah zata maida farincikinta.”
2
“Aurenta nake so kayi ba kazo ka bata baki ba”.
Dr ya dauke kansa yana mai daure fuska
“A iya sanina kasan uwarmu d’aya ubanmu d’aya, kaga kenan babu aure tsakaninmu.”Kallonsa Alhaji yayi na d’an dak’ik’u kana yace “Haka dai kace Ridwan. Amma kaje kayi tunani zan sake dawowa nan ba da jimawa ba”.
4
Jan hannun zunnurain yayi suka tafi.
Kwanansu bakwai (7) a India suka dawo gida Nigeria, basu tsaya ko’ina ba sai garin Malisa gidansu Rufaida. Sun samu tarba na musanmman duk da ba’a san da zuwansu ba, bayan sun gaisa Alh ya kalli mahaifin Rufaida yace;
“Alhaji Nuruddeen”
Baban Rufaida yai saurin d’agowa ya kalle shi don a iya saninsa bai ta’ba jin ya ambaci sunansa ba se sannan.
“Nazo ne ina son sanin alak’arku da Ridwan”
Mahaifin Rufaida yai murmushi yace “Labari ne mai tsawo, amma bari muyi sallan la’asar sai na fada maka tarihin mu”
💔💔💔
“Sunana Nuruddeen, ni asalin garin Bagudo ne, dagani sai kanwata muka rage mai suna Fadila, iyayenmu sun rasu sakamakon gobara da ya kama bukkan mu, inda suka rasu da kanninmu biyu.
Mun fuskanci wahalhalu bayan rasuwan iyayenmu a lokacin ina da shekara tara, Fadila nada (7).
Wata shida bayan rasuwan mahaifanmu aka tura ni almajiranci a kauyen Kwasara, inda na k’arasa karatun Muhammadiyya a garin.
Sanda na cika shekara ashirin a duniya, malaminmu Alaranma Bello ya bani auran ‘yarsa Zainabu. Yarinya kyakyawa da kyawun hali
Watanmu uku da aure na shirya mana zuwa Bagudo dan gaida Baffa na da sauran dangi don rabona dasu tun zuwa na almajiranci.
Munje mun iske kowa lafiya, anan na taradda Fadila ta auri d’an sarkin garin har sun haifi dansu Ridwan tana kuma da tsohon ciki
Nayi farincikin ganin Fadila domin ta k’ara kyau da wayewa, mun dad’e muna hira anan take fada min ba’a k’asar suke ba, kuma mijin na sonta har yasa ta makarantar boko.
Cikin kwana (6) mun zazzaga ‘yan uwa da abokan arziki, a kwana na bakwai muka dauki hanya muka koma Kwasara.
Aurena da shekara goma sha biyu (12) muka sami Rufaida. Zainabu ta haifi yara (8) duk sun rasu, (abinda hausawa kece ma waabi).
Na aika ma mutanen Bagudo haihuwan kamar yanda na saba aika musu duk ta haihu. Ranar suna se ga su Fadila don sun zo daga k’asar da suke wato Moscow.
Nayi farincikin ganinsu don rabon da mu hadu shekaru (10) kenan. Ridwan ya girma da k’anninsa biyu Hibbatullah da Aamatullah.
Abu d’aya ya tsaya min a rai, sauyin da nagani a fuskan k’anwata da yaranta mata, sun nuna k’yamanmu suke ko ruwa bata sha ba. Ridwan ne ma ya dame ta cikin halshen fullanci akan wanene ni, tace Yayanta ne.
Bud’an bakin Hibbatullah se cewa tayi “Amma bakiyi sa’ar Yaya ba don kuwa k’azami ne talaka”.
Na zuba ido inga ta kwa’be ta se naga ta rungumo ta. Da haka suka fice.
2
Tun daga ranar ban sake ganinta ba se da auren Hibbatullah, lokacin Rufaida nada shekara (9), na samu na halarci d’aurin auren, amma ba mu je taron bikin ba.
Bayan bikin da kwana biyu, Ridwan yazo ya same ni har gida da takardun gidan nan da muke ciki, ya rok’e ni Allah da Annabi in baro Kwasara in dawo Malisa da zama saboda ya fi ku sa da babban birnin jihar.
Da k’yar ya shawo kaina, bacin gidan nan ya sama min sana’ar yi, shi ya dauki nauyin karatun Rufaida tun daga primary, har kwalejin ‘yan mata na tarayya da ke garin gwandu (FGGC GWANDU), ya sama mata jami’ar kimiyya da fasaha ta jihar Kebbi.
Duk wani hidima da uba ze ma ‘yarsa Ridwan yayi ma Rufaida, akwai sanda ya ce min don Allah in bashi dama wajen zab’awa Rufaida miji, ni kuma nayi masa alkawarin shi zai bada aurenta. Nayi tunanin ko sonta yake sai kuma banji komi dangane da haka daga garesu ba.
“Dafatan ka gamsu” Ya k’arasa yana mai dariya.
Alhaji yayi dariya yace “Na gamsu kwarai. Dama a matsayi na na uban Rufaida ne nake so na aurar da ita, zamanta haka nan bai da amfani.”
“Haka ne kam ni ma naso inyi magana sai nayi tunani kar nayi muku shishshigi.”
{27}
Alh Usman bai bar jihar Kebbi ba sai da ya zaga aminan Rufaida wato Firyal da Naseera ya tambaye su alak’ar Rufaida da Ridwan.
Amsar duk d’aya ne “Yayanta ne bacin haka babu komi.”
Ko da ya koma Kaduna baice ma kowa uffan ba akan zancen, Zunnurain ne ma yace ma Rufaida sunga wani uncle mai kama da ita, dariya kawai tayi ba tare da ta maida hankali ga zancensa ba.Akwana a tashi ba wuya, yau wata (5) kenan da Alhaji Usman ya sami Dr Ridwan.
3
Yau ma karfe 3:30pm agogon India tayi ma Alh Usman a babban asibitin garin Bombay. Bai sha wahala ba ya isa gaban Dr Ridwan. Bayan gaisuwa da sukayi a mutunce Alhaji yace
“Ridwan na zo gareka karo na biyu kuma na k’arshe, ba don Rufaida wata sashi ce ta jiki na da nake jin damuwanta kamar nawa ba da ba abinda ze dawo dani wajenka.
Rufaida mace ce da turawa ke kira (marriage material) bazaka ta’ba da na sanin aurenta ba.
Ba neman kai nake da ita ba, nayi amfani da kalamanka ga Umair ranar aurensu idan zaka iya tunawa. Lokaci yayi da zamu ga kwanjinka wajen dawo ma Rufaida da farincikinta.” Yana kaiwa nan ya tashi zai tafi.
Da sauri Ridwan ya tare shi “Baba ka tsaya Don Allah kada kayi fushi”.
Alhaji ya dawo ya zauna.
“Baba ina son Rufaida fiye da tunanin mutum. Na fara sonta tun tana shekara takwas. Kasancewar ba a k’asar muke ba bai hanani kula da ita ba, na kuma bayyana mata so tana aji shida a sakandire.
Baba munyi soyayya wanda duk ta yanar gizo ne da waya, sai ta hannun abokina kuma yayan matata in ze zo nijeriya se ya zo mata dasu.2
Baba na wahala kafin na shawo kan iyayena in aureta sai de ranar da nazo ranar na iskeku kunzo neman aurenta, Baba me ake da mace maras alkawari?”2
Ridwan ya sunkuyar da kansa ya cigaba da magana
“Zan aureta yanda kake so ba wai don ina son aurenta ba kuma. Albarkanku muke so, da fatan rabuwa daku lafiya, Allah ya jik’an umair.”
“Aameen, amma banso katse maka hanzari ba, lambar wayar da adireshin yanar gizon (email) dinta ita ta baka ko amso maka akayi?”. Alh Usman ya fadi yana mai murmushi.
“Baba aminana ya amso min, ga Facebook da Twitter duk hotunanta ne da sunanta rad’au akai”
“Ina ji maka sharrin AMINAN ZAMANI Ridwan.”
“Hmmmmn Baba ba de kason aga aibun Rufaida” Ridwan ya fadi yana dariya.
Kwanan Alhaji biyu a India,wanda duk ya yi su a bisa kulawan Ridwan ne, suka dauko hanya se k’asarmu ta gado. Kebbi suka sauka, Alh bai bar ta ba se da aka tsaida lokacin auren sati uku masu zuwa.
Shirye shirye sosai Alhaji yake yi batare da yace ma kowa komi ba.
Labaran karfe (9) ake a tashar talabijin na tarayyan Nigeria. Se aka sako talla, ga hotunansu kamar tare suka dauka.
‘Daukacin jamaar k’asar Nigeria da wasu yankunan duniya da ke kallon labaran sun gani ciki kuwa har da Firyal, Naseera, Hajiya Jamila, da sauransu. Basu gaskata hoton ba har sai da suka ji ance ;
“Iyalan Yarima Murtala Bagudo da na Alhaji Usman Zunnurain Gwandu na gayyatar ‘yan uwa da abokan arziki zuwa d’aurin auren ‘ya’yansu,
Dr Ridwan Murtala Bagudo
Da amaryarsa
Arch Rufaida Othman Gwandu
Wanda za’ayi…..”
Haj Jamila bata jira taji k’arshen ba d’akin Haj Safiyyah taje a guje kamar yarinya tana haki ta kunna mata TV
“Sanarwa daga Zunnurain Group of companies” Kawai suka ji. Se gani sukai an chanza hoto anyi sanarwan da yarbanci, inyamuranci da kuma turanci.
“Kuttumar….(ashariya) bafa zata sa’bu ba, wato ta cinye gado se aure ko, tana son yin auren ne bata koma gidan ubanta ba. Safiyyah yaushe yaushe umair din ma ya rasu da zata jajibo aure don jaraba, toh wallahi baa gidan nan ba”. Haj Jamila ke fad’i tana haki, hankalinta duk a tashe.
2
A bangarensu Firyal kuwa kiran Rufaida sukai suka had’a kiran (conference call) suna mata tsiyan amarya. Dariya tayi,bata kawo komai a ranta ba tace “Ai ni har abada amarya ce don aure na da Umair yanzu na fara…” Katsewa tayi don ganin wanda batai tunanin zai shigo d’akinta a wannan lokacin.
💔💔💔
Alhaji Uthman ne ya shigo yana mai sallama. Ta amsa ta sauko daga kujeran da take zaune.
“Barka da dare DADY” ta fad’a tana mai durk’usawa.
“Barkanmu de matar auta”Ya fad’a yana murmushi, alamun ya ji zancenta.
Durk’usar da kanta ta sakeyi se hawaye. Shirun da tayi yasa Alhaji ya cigaba da cewa;
“Allah ya miki Albarka Rufaida, ban ta’ba kallonki a matsayin suruka ba tun ranar da na fara saninki a matsayin wacce Umair ke so face na d’auke ki a matsayin ‘Ya.
Rufaida na miki shishshigi a rayuwa matuk’ar baki dauke ni Uba ba, amma in har ni uba ne agareki toh nai miki gata ne. Ba k’aramin gata ba kuwa”.
Shiru ya sakeyi na ‘yan mintoci kafin ya cigaba
“Aure, mutuwa da haihuwa duk lokaci ne, ba wanda ya isa ya hana in lokacin yinsu yayi, haka ba wanda ya isa yasa su auku in lokacinsu bai yi ba, kinga kenan da za’a iya hanawa da ni, ke, da yawan wasun da bamu ma sansu ba zasu hana mutuwan Umair. Kinga kenan hakuri ya zama dole, kuma bazamu ce zamu tsaida rayuwarmu ba”
“Rufaida!!!”
“Naam Dady”
“A matsayina na uba a gareki na tsaida miki miji, yanzu haka ranar asabar za’a d’aura miki aure”
“Aure kuma Dady” Ta fadi a firgice tare da rusa sabon kuka.
“Dady in ka gaji dani ne ka barni in tafi Malisa, Dady kar kayi ma Umair haka, (please don’t let any one come inbtwn us, I so much luv Him)” wani gunjin kuka ta saki kuma.
“Haba Rufaida, kin manta cewa Qur’an yace LIKULLI AJALIN KITAAB (Kowani Abu (kaddara) a rubuce take) kuma kin manta Allah yayi ma masu hakuri bushara daban daban a Alkur’ani?
Aure shine mutuncinki da na yaranki, darajanki nake shirin d’agawa, don Allah kiyi hakuri ban sanar dake ba amma nasan Ridwan ze kula dake fiye da tunani. Please kar ki bani kunya”
“Ridwan fa kace Dady”
“Eh shi fa, ko bakya sonshi ne? Nayi imani yana sonki fiye da son da Umair yayi miki, yafara sonki tun kina k’ank’anuwarki, ya gyara ki har Umair ya ganki ya so”
“Dady bai ta’ba cewa yana so na ba, sannan fushi yake dani, ranar aure na ya fad’amin maganganu masu d’aci kuma tun sannan ban k’ara ganinshi ba”.
“Kiyi fatan alkhairi a zamanku, da ace ina da wani ‘Da da babu yanda za’ayi in aurar dake ga wanda ba jini na ba. Allah ya miki albarka, sannan duk matsalan da zaki shiga wanda ba fata ake ba, baki da uban da yafi ni matsawar ina raye”.
“Nago….”
“Munafuka, algunguma, kin kashe mana ‘Da kin kwashe gado zaki koma ki auri dan uwanki ko”. Hajiya Jamila ce ta katse mata zancenta, bata ko kula da zaman Alhaji a d’akin ba, zagin Rufaida take tana aibata ta.
3
“Sannu uwar Umair, dad’in abin ba ke kika haifamini shi ba, tun d’azu ban tanka ki bane don ban son rigima amma bazan d’aukan miki ki taba min ‘ya ba” cewar Safiyya a fusace.
“Safiyyah ni kike ma gorin haihuwan Umair?”.
“Anyi d’in, tambayata shin ya tab’a kwanciya a cikinki ko na dak’ik’a d’aya ko kin taba shayar dashi nononki? Aure kuwa babu fashi nice nan uwar amarya.”
Ai sai Jamila ta rikice,tamkar wata zararriya take fad’in
“Wallahi ko zanyi yawo zindir ne Rufaida bazata auru ba! Hasalima se na wulakanta rayuwarta”
2
“Sannu Allanmusuru, kina bani mamaki Jamila. Wanda kike don shi fa ya rasu, kiyayyar har yanzu?”. Alhaji da duk masifa yasa basu kula da zamansa a d’akin ba ya fadi.
Duk sukai mutuwan tsaye tun ba Haj Jamila da ke shirin shirya karya da gaskiya don fada ma Alhaji.Sum sum sum duk suka fita, wani kuka mai tsuma rai Rufaida ta saki, Alhaji ne ma ya daure yana bata baki, nasiha sosai yayi mata a k’arshe ya shi mata albarka da adduan dacewa.
+
Duk yanda Haj Jamila taso ta kawo rigima a auren bata kai ga nasara ba don kuwa Alh Othman da Haj Safiyyah sun toshe kunnuwansu da kalamanta.
2
💔💔💔💔
A yau asabar aka d’aura auren Rufaida da Ridwan, a masallacin Sultan Bello. ‘Daurin Aure ne da dubban mutane suka halarta.
Rufaida tayi kuka sosai sanda Zunnurain ya zo yana cewa “Mummy an d’aura aurenki, a masallacin da akai ma dadyna sallah” Kasancewan tun bayan rasuwan Umair haka yake kwatancen masallacin.
2
Kuka sosai take yi, ta rungumo Zunnurain sosai jikinta. Hibbatullah k’anwar Ridwan ce tayi k’arfin halin lallashinta. Kasancewa tun da Ridwan yaje musu da zancen aurensa da Rufaida suke murna, ganin tafisu ilimi, wayewa uwa uba arziki yanzu ( da yake na lashe monis ne).
5
Batai shiru ba har ‘yan matanta suka shigo, nan duk suka hadu suna kuka, sun ba duk wanda ke sauraransu tausayi, nan mutuwan Umair ya dawo Sabo ga d’aukacin ahalinsa.
“Munafuka, meye na kuka, kin kashe mana ‘Da don kiyi gado ki koma gun d’an uwanki, toh meye na kukan munafurci tunda hak’anki ya cimma ruwa?”. Haj Jamila ce da zancen nan tunda labari ya iske su akan kukan Rufaida tayi maza tazo ta isko ta kafin Haj Safiyyah ta iso.
“Jamila wallahi kika kuskura kika kuma zagin ‘yata gidan nan baze dauke mu ba, ke kika haifamin Umair ko tayani nak’uda kikai? Kina son muzguna ma matan ‘ya’ya ne kika gagara haifan d’a namiji. Ba abin da ya had’a ki da Rufaida ki fita hanyarta”. Cewan Haj Safiyyah. Hannun Rufaida ta ja sukai hanyar d’akinta da su.
Kuka Haj Jamila ta saki har da kururuwa an mata gorin haihuwan d’a namiji. Babbar ‘yarta Maimuna ce ta ja ta suka fita kana tace;
2
“Hajiya wai meye aikin bokan kan tsauni ne? Kinsan shi ya mana maganin wannan tsinannen yaron nan. In ma kawar da ita zeyi gara yayi”
“Naje fa, yace in kwantar da hankali na, ajalinta na gidan auren, baza ta ta’ba haihuwa ba, don tana samun ciki zai tura mata aljanu, kin santa jarababbiya ce kwanan nan zata margaya.” Sukayi dariya gaba daya.
13
💔💔💔
Bayan sallan la’asar Alh Zunnurain da Haj Safiyyah suka sa Rufaida a gaba, fada suke mata da nasihohi akan rayuwan da zata iske, sun nusar da ita mahimmancin hakuri tare da ja mata kunni akan kada taje tana nuna son Umair a gaban mijinta. Sun mata addua sosai.
Tana tare dasu har akai kiran mangariba, Haj Jamila da yaranta sunyi bak’incikin zaman nan, sun so samun masaniya akan abinda aka tattauna amma basu samu ba.
2
Wajajen k’arfe takwas aka kawo motoci don zuwa Dinner, dakyar Haj Safiyyah ta sa Rufaida ta shirya cikin wani lallausan leshi mai ruwan madara, da gwagwaro kalan bunsuru, haka ma takalminta da jaka, yaranta mata an musu shigan doguwan riga (flower gals) Zunnurain kuwa suit yaci baki, ya sa tabarau bak’i kuma.
5
Iyalan Haj Jamila ne kan gaba wajen zuwa dinner duk da zage zage da sukayi tayi.
2
Basu tsinke ba se da suka isa hall din, tsayawa kwatanta had’uwan wajen bata lokaci ne don se ya cinye mana shafika hamsin (lolz).
Se da kowa ya zauna sannan amarya da ango suka shigo, yaranta mata ne a gaba suna masu fesa masu turaren amare (bridal spray) ta baya kuma Zunnurain ne da bak’in tabaran sa kamar irin jami’an farin kaya (SSS).
Ko mak’iyansu sunsan sunyi kyau ainun. Dinner ya k’ayatar k’warai da gaske, duk da idon amarya bai bar zubarda k’walla ba har aka tashi. Su Haj Jamila basu tsinke ba se da Alh Zunnurain ya shigo yai ma amarya kyautar kamfaninsa guda a matsayin godiya akan biyayyan da tai Masa. Hakan ya hana musu jira a tashi. Suka koma gida suka cigaba da k’ulle k’ullensu.
1
An watse taro lafiya, Rufaida raba dare tayi tana nema ma Umair gafara, ta kuma yi alkawarin baza ta taba yarda Ridwan yashi ga hurumin Umair ba, ita tashi ce ta har abada.
4
Washe gari Alhaji Usman da Haj Safiyyah da yaranta suka kaita har Abuja gidan iyayen Ridwan suka damk’a amanarta a wajensu. Nan kan Haj Fadila yai k’ato ita ce Zunnnurain Gwandu ya ba suruka, (ta manta cewa ‘Yar Dan uwanta ne da ta watsar oh su Fady lashe moni😜).
6
Da k’arfe 12 na tsakar dare jirgin su ya tashi zuwa India.
Tun a jirgi Rufaida ta tsinke da lamuran Ridwan, domin k’uda yafi ta daraja. Rufe idonta tayi tana tunano rayuwanta da Umair. Farkon shiganta jirgi a duniya suna tare, yana mak’ale da ita duk k’auyancin da takeyi ya kare ta. Ko da suka isa tun a tashan jirgin sama wata mata da yara biyu kyawawa suka tarbe su, da gani ba tambaya matar Ridwan ce da yaransa.
Rungume su yayi yana mai sumbatarsu a goshi. ‘Dagowa tayi tana murmushi ta kalli Rufaida tace;
“Amarya sannu da zuwa, kun sha hanya ko, Allah Ya sanya alkhairi”.3
Murmushi Rufaida tayi ba tare da tace musu komi ba.
Sun isa gidan da aka tanadar ma likitocin asibitin garin Bombay. Ba tare da b’ata lokaci ba aka mik’a Rufaida ga d’akinta wanda ya sha gyara. Wanka tayi kana ta kira Alh Zunnurain, Haj Safiyyah da kuma iyayenta ta sanar musu sun isa lafiya.
Bayan sallan isha’i, Rufaida ta shirya ma kwanciya, ta na shirin rufe k’ofanta sai gashi ya shigo had’e da sallama.
Kallonta ya fara tun daga tafin k’afarta har zuwa tsakiyan kanta yace “Mutum dai yaji haushi, ace ba abinda ka3 maida aure sai kasuwanci, kurwa ta kur,wallahi bazaki ta’ba samun nasara a nan ba, in kin ga dama ki fito ina son ganinku.” Yana kaiwa nan ya juya ya wuce.4
Ranta idan yayi dubu toh ya baci saidai sanin ko wanene Ridwan a wajenta yanzu ya sanya ta juya ta koma dakin a sanyaye,zani ta d’aura akan rigan barcin, ta daura hijab akai kafin ta fita wajen kiransa.
Ta isko su suna kallo a falon. Ta shiga da sallamanta, fuskanta ba yabo ba fallasa.
Bayan sun gaisa ta ja jiki ta zauna shiru. Ridwan ne ya kore shirun ya fara da addua yace;
“Ina mai godiya ga Allah da ya azurtani daku. Ina kara gode maSa don ba dabara na ko wayau na bane yasa hakan. Allah Ubangiji ya muku albarka ya azurtamu da zuria nagari.”
“Aameen” cewar Hanna,ita kuwa gwanar a zuci a ciki ciki ta amsa.
Ya dubi uwargidansa
“Hannah kece babba, bazan d’auki cin fuska ko tozarci daga gefenki ba, a shekaru kin girme ta, haka a gidana. Kinfi kowa sanin ko a dangi banda kamar Rufaida don haka ki kula…”
Ya juya ga Rufaida fuska a had’e2
“Ke kuma in baki dauki Hannah babba a gidan aure ba zaki dauke ta a matsayin matar yayanki, bazan dauki raini ba, ina son matata fiye da tunanin ki.
Idan kun kula na tabbatar da zaku fini jin dad’i, zancen kwana kuma kwana dai dai za’a dingayi.”
3
Bai nemi ji daga garesu ba ya rufe zaman da addu’a. Jiki a sanyaye Rufaida ta koma d’akinta, ta kwanta kenan ya shigo had’e da sallama.
Bin dakin yayi da kallo, yana duba ko wani lungu da sak’o, k’amshi ke tashi ta ko’ina a d’akin. Can ya sami waje ya zauna. “Mstwwwww!!” Yaja dogon tsaki kafin ya d’ora da cewa
“Wai mutum don tsabar jaraba, kayi haihuwa yara har hud’u amma sai an nemi namiji. Ki sani duk kwadayinki da jarabanki bazaki samu abinda kike so daga gare ni ba. Mayaudariya kawai, Annabi a fuska shed’an a zuci”.8
Ko ni ba don kunnin maciji gareni ba na aza kalaman soyayya yake fada mata, kuma sai naga ya kwanta ya ja bargo ya rufe su tare da kashe wutan gefen gado(bedside lamp) da ke kunne.
Da gudu Hannah ta karasa d’akinta tana kuka don tadan kashinta ya k’are, Ridwan ya auri wacce ya keso, idanunta sai hasko mata gasu can suna soyewa yake, kuka ta saki mai karfi, fadi take
“Kai it can’t be so, duk wahalan da nasha sai da yarinyan nan ta shigo gidan nan?Kai da sake”2
Waya ta dauka ta nemo wani number, ringing biyu aka daga.
“Kika ce cinna masa ita akayi, kinga soyayya kuwa? Ni ban san yanda za’ayi ba, ni de so nake ta bar gidan nan”4
“Kwantar da hankalinki, ni JAMILA na daukar miki alkawarin ajalin Rufaida na kusa, jiya na je wajen mutumin fa, ya k’ara tabbatar min da Ridwan ya kusance ta zata dauki ciki, sai ya tura mata aljanu. Yanzu de kiyi kokari ki turo kud’in sallamarsa, don yaji dad’in yin aiki.”9
“An gama Haj Jamila uwargida a wajen Alhaji Zunnurain.”
Suka kyakyata dariyar mugunta daga haka sukai sallama kowaccensu da abinda take raya ma ranta.Rayuwa tayi ma Rufaida k’unci, bata samun sassauci daga Ridwan matuk’ar sun keb’e su biyu.
A b’angaren su Hannah kuwa hankalinsu duk a tashe yake, duk boka ko malamin da suka samu yana tabbatar masu da ta sami ciki rayuwarta ya kawo k’arshe kenan.
Amai take kwararawa kamar zata fitar da hanjin cikinta, kallo d’aya zaka mata bazakaso kai mata na biyu ba. Tayi baki ta rame, ta fita kamanninta.
Watanta shida kenan da auren da ta kira auren kaddara, auren da kullum kwanan duniya ake zaginta da cin mutuncinta, kalamai ake jingina mata wadanda sam basuyi kama da halinta ba. “Oh ni Rufaida me na tsare ma Hamma Ridwan? Me nayi masa ne haka?” Kalaman da ke fitowa bakinta kenan.
Wayarta ta d’auko, ta nemo layin dadinta, uba gareta mai sonta mai share mata hawayenta. Ringing biyu ya dauka “Rufyn Ridwan ya kuke”.
Kuka ta sakar masa har da gunjinta. “Dady zan mutu, banda lafiya, daga kai se Umair kawai ke so na”.
“Subhanallah, me ke damunki, Rufaida kinki kwantar da hankalinki, jiya Abbanki yace Ridwan ya kai karanki sau biyu kina barci rungume da hoton Umair kuma kin ki bashi had’in kai, shin kina son rahaman Ubangiji kuwa? Mijinki da mahaifanki suna fushi dake, ni bazan taba fushi da ke ba don ni na ja miki. Please my dearest kiyi min biyayya kar mak’iya suyi mana dariya.”2
Bakinciki da damuwa suka mata yawa, wato kiyayyar da Ridwan yake mata har ya kai ya shiga tsakaninta da iyayenta.
“Nagode Dady in sha Allah zan gyara, Please ka dinga min addua”.
“Shike nan ‘yar albarka, zan turo miki sak’o idan Ridwan zai dawo.”
Anan tasan baya nan, wato jiya da ya gaggaya mata magana tafiya yayi.
Hannah da ke labe ta ja jikinta cike da murna da fargaba ta tafi dakinta, lambar hajiya Jamila tayi kira, bayan sun gaisa ta gyara tace
“Haj hak’onmu ya kusa kaiga ruwa fa, don k’asan da ake kwasowa da lema a jikinsa.”4
“Kai don Allah”
“Wallahi yanzu na jiyo amanta, na labe naji tana cewa bata da lafiya ayi mata addua, kamar da Alhajinki suke wayar.”
“Wayyo dad’i bara nai maza na aika kud’in yanka kinga don ayi aiki shaf shaf”.
Dariya tayi kana tace “Allah kashe ta tare da Haj Safiyyah”
“Hahhhh Hannah baki da kyau. Bara nai sauri kafin mutumin ya dawo
💔💔💔💔
“Ridwan naji sak’onka wajen Alhajin Malisa, banji dad’i ba, na rasa meyasa Rufaida take haka, amma zanzo har Gida in sha Allah in mata fad’a,don Allah ka kara hakuri kuma ka dinga hakuri da ita, ka k’ara kyautata mata. Kasan zuciyan mace nada rauni da taimakonka komi ze zama mata tarihi”.
Sunkuyar da kai yayi kamar ze masa sujjada kana yace “Nagode kwarai Dady, zan kiyaye, Allah kara girma da d’aukaka”.
“Ga sak’on baby ka kaimata, kayan kwalama ne, da kayansu na mata, muna gaisheta da kyau, se munzo”
Godiya sosai yayi masa kana sukai sallama,ya dau hanya.
💔💔💔💔
“Ashe ke banza ce, wawuya, dak’ik’iya ce ban sani ba!! Kin maida kanki jaka! Kwad’ayayya! Ban baki abinci ne da zaki je rok’on abinci?! Da yake ma talaka bai iya samun waje ba, tir da halinki Rufaida baki cancanci zama uwa ba wallahi”. Ridwan kenan yana shigowa ya tare ta da kalaman nan yana mai watsa mata tsarabanta a fuska.
Binshi tayi da kallo har ya fita. Kuka ma gagaranta yayi don tsabagen bakinciki da yai mata yawa. Tashi tayi ta shiga bayi tayi alwala ta fara karatun Alk’ur’ani.
Duk wannan akan idon Hannah akayi, tashi tayi da murnanta ta sanar ma Haj Jamila.
Bayan sallar isha’i Ridwan ya jawo na’ura mai kwakwalwansa ya jona abinda ze sada shi ga yanar gizo (modem) ya fara lalube.
Akwatin sak’onninsa (email) ya bud’e, sak’onnin murya ya gani wanda kamfanin sadarwar kasar ta aiko masa na dukkan wayan da Rufaida tayi ya fara budewa.
Mafi akasarin wayanta da yaranta ne, inda ya fahimci tsantsan soyayya da shak’uwan da ke tsakaninta da yaranta.
Se kuma kira tsakaninta da Alh Zunnurain, nan kuma nasihohi ne da kalamai da zasu kwantar mata da hankali da shawara akan biyayyan aure.
Saura duk da kawaye da yan uwa da abokan arziki. Har ze kashe se ya kula da bai bude guda ba, yana budewa yaji Rufaida na zata mutu, ba mai sonta sai Alh da Umair.3
Nan bakin ciki da kishin da baisan da yana dasu ba ya taso masa. Ido rufe ya koma d’akin Rufaida.
Jawota yayi daidai tana waya da Alh. Fisge wayar yai ya naka a k’asa kafin ya watsa mata wani kallo da hajinta saida ya murd’a. Rufe ido tayi tana jiran saukar marinsa da naushinsa shirun da taji ne yasa ta bude ido.
Zaune yake idonsa na fitar da k’walla, “Why Rufaida? Why! Why!! Why?”. Sai kawai ya tashi ya fice daga d’akin.
Bayan kwana biyu ya isko ta a d’aki ya zauna. Kallonta yayi cikin ido yace “Zan ara miki waya ki kira yaranki da Alh kiyi musu sallama akan zan tafi karatu kasar portugal na wata shida kuma dake zani, sannan tafiyan gobe ne”.
Shiru tayi tana mamaki wai da ita zashi, kashe ta kawai zeyi. Ta karbi wayar ta kira su duka har kawayenta da iyayenta sukai sallama suna mata fatan alkhairi.
Bayan ta mik’a masa wayar ya kalleta yaja tsaki kana yace “Jarababbiya wato murna kike zaki bi miji ko?Toh ba inda zamu asalima hutu na dauka. Bana buk’atan bak’i daga ko ina naji wanda yake ikirarin sonki na wani azarbabi ze zo ganinki to ya sha zamansa. In kin gaji da zaman kwaraka (kwad’ayi) kin san hanyar fita…. Mayaudariya kawai”. Yasa kai ya fita.”In bacin mutuwa mai YANKAR K’AUNA mai ze kawo ni gidan nan har na fuskanci wulakancin nan? Ya Allah kawo min mafita na alkhairi ka bani ikon cin jarabawan nan.” Rufaida ke fadin haka a zuciyarta. Bak’in cikin da take ji yafi karfin tayi kuka.+
Yanda yai ma Rufaida, haka yai ma Hannah. Amma ita kwace wayarta yayi da sunan se bayan hutunshi don yana tsoro kar Hannah ta tona mai asiri.
Zaman hutun nan zama ne da Rufaida ta kira zaman gidan yari, Hannah ta fara ciwo wai ita mai ciki, aikin gidan gaba d’aya ya dawo wuyanta.
Sau da yawa zatayi girki mai daukan lokaci kamar Fankasau, waina (masa), etc amma se ta gama Hannah tace bazata iya ci ba, haka zata koma tayi wani.
Yau ma kamar kullum Hannah tace fate take jin sha, tagama shiryawa a teburin cin abinci (dinning) tayi maza taje tayi wanka don suna fitowa ba yi zatayi ba.
Kiran da taji ya kwala mata yasa ta fitowa da towel a rud’e. Ta iso da saurinta don yanzu gudun abinda zatayi ya wulakanta ta take. Tun ranar da ya zage ta a gaban Hannah ta kama kanta.
Saukan marin da taji ya dawo da ita duniyar da ta shiga, “Rufaida zuciyarki ta bushe da za’ace ke da kanki kike shirin kisan kai, mai ta tsare miki da zaki zuba kanwa da alif cikin abincinta, wato ya narke kan taci kenan? Ko tausayinta baki ji ba duk shekarunnan bata aje kwai ko daya ba amma kike bak’inciki?! Wallahi wani abu ya sami ciki na kotu zata raba mu, sakarya azzaluma kawai!”
“Ai baby ba sonka take da zuri’a ba, kwanaki fa da kai tafiya ka barta da shigan ciki, ta kod’e ga uban amai da takeyi, kawai bayan kwana biyu na tsinci kwalin maganin nan a bola, bara na dauko.”
Tashi tayi ta barshi da tunani, ciki kuma? Magani..?!! Hmmmn bari tazo ya gani. Tana mik’o masa ya bi kwalin maganin ya karance tsaf, karkad’a kai yayi yace “Aiko zata ci ubanta Zunnurain da ya tsaya mata.”
Acan k’asan ranshi kuwa mamakin Hannah yake, ya ga kwanan watan da aka buga maganin (manufacture date) kwata kwata sati uku kenan kuma yana cikin gidan. Anya wannan ma ba shirinta bane? Meyasa yake saurin daukan laifi da aka jingina ma Rufaida ba tare da bincike ba?
A daddafe ya gama cin abincin, ya tashi ya wuce d’aki, hankalinshi ya gaza kwanciya, meyasa kishi ya masa yawa har ya kasa hakura da abinda ya faru da chan ya rungumi kanwarsa kuma wacce yafi so a duniya? Ga kamala ga hakuri kuma. Tashi yayi don ya je yaga halin da take ciki.
Isarsa keda wuya ya iske d’akin a rufe, ya jijjiga yaji shiru yai tsaki ya koma d’aki.
Rufaida kuwa tana isa daki kamar ance ta d’aga kai, sai ta hango envilop din da Dadynta ya aiko mata dashi. Ta bude kudi tagani dollars, natsuwa tayi ta kirga tasan tabbas ze kaita k’asarta. Batayi kasa a guiwa ba ta fice daga gidan ba tare da ta rike komi ba, jallabiya kawai ta saka ta yane kanta da mayafi se ‘yar wallet dinta da ya kunshi dukkan muhimman kayanta da zata buk’ata wajen fita.
STORY CONTINUES BELOW

Tana fita mota ta dauka da zai kaita Delhi, ta kama d’aki a wani hotel da hankali bazai taba kawowa tana wajen ba. Ta hannun manajar otal din Rufaida ta nemi biza (Visa) zuwa k’asar turkiyya (Turkey).
A bangaren Ridwan kuwa, ya je dakin fiye da sau goma amma a rufe, tsoronshi kar ta kashe kanta a dakin dan ko motsi ba’a ji, can yayi tunanin amfani da makullinshi ya bude. Batare da bata lokaci ba ya koma ya dauko.
Ya bude a tsanmaninsa ze ganta a sume ko a mace a wajen se ya ga akasin haka, d’akin wayam, ba alamun an fita da wani abu balle yayi tunanin ina taje. Nan ya fara zagaye gidan lungu da sak’o duk bata nan.
Fita yayi yana tambayar masu zaman waje ko sun ganta, nan wani dattijo mai siyarda kayan marmari yace tabbas yaga fitowanta ta shiga taxi, amma baisan ina taje ba. Saidai hanyar tashan jirgin sama (airport ) sukayi.
Ba shiri ya dauko mota cikin matsanancin tashin hankali, fad’i yake “Rufaida kar ki min haka!” Cikin ikon Allah ya isa tashan jirgin sama, duk inda yasan zai ganta babu ita, asalima jirgin da zai tashi zuwa naijeriya saura mintuna kadan su daga kuma bata a ciki.
Chaji ofis din yan sanda yaje ya bada rahoton b’atan ta, an duba kowani otal da ke cikin Bombay babu labari. Me zatayi a Otal ma, wacce bata ko sile biyar, saidai tayi neman gidan aiki in haka ne bazata wuce anguwansu ba.
{37}
Washegari jirginsu Rufaida ya tashi zuwa Turkiyya, anan ma daki ta kama tasa aka nema mata tikitin jirgin zuwa Naijeriya, cikin sa’a an samu mai tashi karfe sha biyun rana.
Ko da ta sauka a filin jirgin Aminu kano, shatan mota ta dauka bai direta a ko’ina ba sai Kaduna.
Hajiya Safiyyah ta fara karo da, kallonta tayi a firgice tace “Rufaida!! Tare da wa kike tafe? Kece din kuwa?! Ciwo kikayi kika koma haka?”
Murmushi tayi mai kona zuciyarta,Safiyya ta jata suka k’arasa cikin daki. Waya ta dauka ta kira Alhaji, ko minti biyar bata cika ba se gashi ya dawo. Ganin Rufaida shima yasha jinin jikinsa
“Rufaida lafiya? Me ya same ki haka? Ya kika dawo?”. Alhaji kenan ya fadi cikin tashin hankali.
Bata boye musu komi ba, ta fada musu irin zaman da takeyi. Da abinda ya hada su. Har ta kamo hanya.
“Alh wallahi aikin asiri ne, ai ni shaida ce irin son da Ridwan ke mata, kila ma aikinsu Jamie ne”
“Kul!! Kar ki kuskura ki fara zato, Manzo SAW ya hane mu da zato. A gabanki akayi? “
“Ba wani zato ko zargi ai sanin hali ne”
“Wai safiyyah bazaki min shiru ba?!”
Shiru tayi amma raya rigimar da zatayi take a ranta.
“Rufaida yanzun nan za’a wuce da ke Gwandu, akwai komi a gidan, make sure ba wanda yasan da zuwanki. Shi kuma Ridwan zan nuna masa shi karamin alhaki ne.”
” Haba amarsu, in baka iya kama barawo ba se ya kama ka” Ya juya akalar maganarsa zuwa ga Haj Safiyyah.
Abinci kawai Rufaida taci yasa aka wuce da ita, sun isa gwandu a gajiye, tayi zamanta a dakin da suke sauka da Umair.
💔💔💔
Duk inda hankalin Ridwan ya kai ya gama tashi, kwana bakwai kenan ba alamun za’aga Rufaida.
Ba shiri ya sauka a Naijeriya, gidan baffansa ya je, bayan sun gaisa ya fara.
“Baffa yau kwana tara kenan na kama Rufaida da laifin neman zubar min da cikin jikin matata, rai na ya baci har nayi danyan hukunci ta hanyar dukanta, tun daga ranar ban kara saka ta a ido ba, duk inda zan ganta naje bata nan,don Allah Baffa kai min aikin gafara”
“Gafaran me? Ai kai akayi ma laifi, ina bak’incikin aurenta da Umair ba don komi ba se don kudi sun sa ta zama wata daban. Ta bani mamaki kwarao da gaske.” Ya karashe cikin tsananin fushi da bacin rai.2
“Yoh Baban Rufaida ina kuke tunanin zata in ba gidan ubanta ba, ni tun da hajiya Jamila tazo ta ke fada min halayen yarinyar nan na sure da lamuranta. Kai ma likita kamar dole ne auren, ka saketa taje tai ta auren mamaci.” Mamien Rufaida ce ta fadi haka cikin bacin rai.2
“Baffa da Mamie hakuri zakuyi, baffa don Allah ka shirya muje Kadunan. Ba don halinmu ba, in kuka tsame hannunku a kanmu rayuwarmu bazatayi kyau ba”.
Haka yai ta basu baki da kyar ya shawo kan baffan nasa suka dau hanyar Kaduna.
Sun isa ana mangariba, se da suka idar suka isa wajen Alhaji Zunnurain.
Yanda ya tarbe su yasa gaban Ridwan fadi, don da murnansa ya kira matansa suka gaisa kowacce na tambayar Rufaida.
Yaranta suka zo da gudu, “Dady sannu da zuwa, Jabbama grand PA”
Dariya akai, Baban Rufaida yace “Bakinku ne jabbama, kuzo muje ruga kunk’i”.
Nan sukai kane kane jikin Ridwan, suna tambayar mummynsu, auta Mamie ce tace “Mummy na tayi kiba, ta daina kuka ko? Kullum se tace min na dinga cin abinci na daina kuka inyi kiba kamar ita, I want to see her please zaka je dani?”
“Ja’ira tashi ki ba mutane waje, kaud’i kamar uwarta, fitinar uwarki ai sai ya sata rama ba k’iba ba.”‘
Hannun kanninshi zunnurain yaja suka fita, bayan ya harari Haj Jamie da ta gwasale kanwarshi.
“Fitinannun yara marasa tarbiyya, zo ka duke in nasan kaji haushi. Dayake barewa bata gudu danta yai rarrafe, waye gara cikin Rufaida da Umair din. Mts! Allah kyauta taron yuyuyu.”
Ba wanda yace da ita uffan se ma chanza topic da Alh yayi. Can ya kalli matan yace “Mun tafi sallar ishai, se mun dawo.” Suka sa kai suka fita.
Bayan sun dawo sunci abinci, Baban Rufaida ya fada masa abinda ke tafe dasu. Shiru yayi amma daga ganin yanda fuskansa ta sauya kasan ba farinciki.
“Ridwan”
“Naam Dady”
“Kace a ina ne abin ya faru “
“A gida ne Dady, nine har inda ba’a tunanin zaa ganta a Bombay naje”
“A iya sanina yau wata daya da kwana ashiri(20) kenan rabon da nayi waya da Rufaida, kuma da wayarka lambar India, inda kuke min sallama zaka karatu na wata shida, ko ba haka bane?”
“Ha-hak-hakane Dady”
Ya fada cikin in ina.
“Good! Kun dawo ne ko kuwa tafiyance ba’ayi ba, da har Rufaida ta bace a Bombay India maimakon Portugal da kace min zaku?”
Shiru yayi ba amsa, ji yayi kamar kasa ta tsage ya shige ya huta.2
“Tunda baka son bayyana sirrin gidanka, nasan ‘yata mai laifi ce, amma hakan baze hana ni yanke hukunci ba, na baka sa’o’i ashirin da hudu (24hrs) ka fito min da ‘yata ko in maka ka ga hukuma. Mu kwana lafiya.” Ya tashi ya barsu nan zaune.3
“Kunsan Allah yasan inda take, ko jiya naji suna waya, ai kawai ku kai k’ararsa ga hukuma ai bashi ya haifanmuku ita ba.* Haj Jamila kenan ta sand’o ta fada musu bayan ta ga fitan Alh.”Ridwan kaji zancen matan nan ko, ni wallahi na fara jin haushin mutumin nan, hankaka kai (mai da d’an wani naka). Toh wallahi ya fito da ita ta koma d’akinta tun kafin na sauke fushi na. Haba!!”+
“Baffa baza’ayi haka ba, ita wannan matar itace ta same ni tace nayi hankali da Rufaida itace ta kashe Umair don gado”
“Innalillahi wa inna ilaihir rajiun! Ni kuma tazo tace min zaa ma ‘yata auren dole nayi shiru wai ai bakinku guda da Alh, gadon da yayi karyan bata ne ze kwace, ni wallahi da ban yarda ba yanzu ne na fara yarda”.2
“Hmmmn Baffa matar nan abin tsoro ce, muyi hakuri zuwa gobe in amsa laifi na tukun muga me zai ce.”
“Allah kaimana rai”.
Wannan kenan…..
💔💔💔
Washe gari bayan karin safe, suka sake zama da Alhaji, sun bashi hakuri iya hakuri kafin da kyar yace zasu hadu a gidansa na Gwandu, bayan kwana biyu.
Tare sukayi shiri zuwa Kebbi, har da Haj Jamila da yaran Rufaida wanda suke hutun tsakiyan zango (Mid term break).
Ko da suka isa yaran sunyi murnan ganin mamansu wacce tayi kyau, ta k’ara fresh, a iyakan zamanta bata da abinci se madaran shanu da ‘ya’yan itace. Hakan yasa kyawunta ya fito, sannan ta kara cikowa ta zama wata abinda bature ke kira da take away.
Taro ne da ya kunshi iyayen Rufaida wato babanta da mamienta, Alh Zunnurain da iyalansa, se kuma Rufaida da Ridwan.
Baban Rufaida ya bud’e taro da addua, sannan ya fara da tambayan Rufaida dalilin dawowanta gida ba tare da izinin mijinta ba.
Bata boye musu ba ta fada musu komi tun daga ranar farkonta a gidan har zuwa barinta gidan.
Nan fa Hajiya Jamila ta fara murna, bata iya boye murnanta ba dan duk an fahimce ta, tasan wannan aikin bokanta ne. “Amma kuma bata fadi cikin da take dashi ba bacin ga alamu duk sun nuna, shegiya kwananki ya kawo karshe, amma Hannah fa tace soyewa suke…” acikin zuciyanta take zancen nan.
“Madallah kin tabbata duk abinda kika fadi gaskiya ne, ba ragi ba kari?” Zancen Alh ya katse mata tunaninta
“Iyakan gaskiyar kenan Dady”
“Toh kai Ridwan kaji abinda tace, ko zaka fada mana dalili?”.
“A gaskiya Dady ba rashin So yasa nake mata haka ba, bakincikin yaudarata da tayi nake, kullum gani nake kud’i ya rud’a ta ta manta alk’awuran da taimin har ta amince da Marigayi, se kuma aka tabbatar min inda aka fada min ita ta kashe shi…. Toh tsoro da fargaba da bakincikin sabbin halayenta yasa nake mata haka nan”.
“Subhanallah.. A iya sanina Allah kad’ai ke kashewa da rayawa. Dalilin hakan yasa malam balarabe yakecewa (LAU SABARAL QAATILU LA MAATAL MAQTUL) wato da mai kisa zeyi hakuri da Wanda ya kashe ya mutu.
Umair hatsari yayi, duk da in ma kisan ne ya bar mana shedu kala kala da ya nuna sanadin mutuwansa, amma mun bar kowanene duniya ya koyamasa hankali. Tun yana jariri ake attempting kashe shi amma se da kwanansa ya kare ya mutu”.
“Mstwwww aikin banza, nasha fadi Rufaida ta kashe Umair kunk’i yarda yanzu gashi wanda tai kisan dominshi ya fadi.”
“Ah ah Haj ke kika fada min”. Nan take Ridwan ya tari Haj Jamila. Ita kuwa batai tunanin zai tona ta ba.
“Ni ba wannan ya tara mu ba.” Alh Zunnurain ya katse su.
“Rufaida ko zaki iya fada mana dalilinki na yaudaran yayanki da yafi kowa sonki da kula dake?” Ya maida akalan zancensa zuwa ga Rufaida yana mai daure fuska.
“Dady a iya sanina babu wani zancen soyayya tsakani na da Yaya Ridwan, nima se dawowansa ya fara jifana da mugayen kalamai, haka ranar aurena da Umair ya fada min kalamai da bansan kansu ba se yau da yai bayani, wallahi ni bansani ba.”
“Yaushe zaki sani kin sa kwadayi a ranki, ai da ganinta Alh kaga maras gaskiya…”
“Jamila kika sake magana wallahi zan bata miki rai!” Alh ya sake katse ta.
“Ridwan kaji me tace ko zaka fidda mu daga duhu?”
“Zancen gaskiya naso Rufaida tun tana karamarta. Haka nayi ta rainon sonta har ta kai matakin aji hudu (4) na secondary.
Lokacin ina tsaka da karatu hakan yasa ban dawo ba amma aboki na kuma aminina wanda nake turo sak’onni ta hannunshi, Sanusi ya zo India.
Na fada masa abinda ke damu na ya bani goyon baya akan na fada mata. Haka na tura mata katin soyayya, da wasiku da turare.
Dawowan da yayi kuwa na sami amsar sak’ona inda ta amince da tayin soyayyata. Tun daga ranar ba’a sati biyu ban aika mata da wasika da katinan sak’on soyayya ba
Hotunanta kuwa kala kala take aikomin nima ina aika mata, har ta gama secondary. Anan take cemin tana son karanta fannin zane zane duk da buri na ta karanci likitanci (medicine) ko aikin jinya (nursing).
Da taimakon Sanusi tasami gurbin karatu a jamiar jihar Kebbi”Anan soyayyata da Rufaida ta bunk’asa, don na bada waya an kai mata, ga hotuna da muke turawa ta hanyar yanar gizo (email).
Munyi ma juna alk’awura duk da muna nesa da juna amma hankali na akwance yake, don nasan irin tarbiyyan baffa bazebari Rufaida taci amanata ba.
Yan mata da dama sun so ni ciki kuwa har da Hannah. Wacce take kanwa ga Sanusi.
Hannah yarinya ce mai natsuwa da kamun kai, ga kyawawan halaye don sukan zo India hutu. A shekaru zata girmi Rufaida. Kyawawan halayenta yasa na so ta.
Yayanta ya fara dakatar da soyayyan ta hanyar nusar damu baza’a ci amanar Rufaida ba. Amma hakan bai shafi shirinmu ba.
Na dawo da murna ta, don Rufaida ta sanar min ta kammala karatunta, na dawo da burin zamuyi aurenmu na tafi da ita India kawai na zo na iske ana zancen Umair, ba abinda ya fi dagamin hankali kamar yanda tayi biris dani kamar bamu taba maganar ba.
Da na fada ma Sanusi yayi ta ban hakuri, kalamai na nasiha yana tunatar dani kullum adduan zabin alkhairi muke, donme zanyi fushi dan hakan ya faru.
Ba tare da nayi shawara da kowa ba naje wajen babansu na roki auren Hannah. Yayi murna kwarai. Bakincikin rashin Rufaida yasa ban sake waiwayar gida ba har zuwanka.
Munyi aure da Hannah har yau Allah bai bamu rabon haihuwa ba.
Dady, baffa, mamie, mummy da Haj kunji abinda ya faru, duk sadda na kalleta bakinciki da kishi ke sawa nayi mata abinda nake mata. Amma kuyi hakuri hakan baze sake faruwa ba.”
“Hmmm!! Maza kenan. Ina kai ina kishin bayan rai ( gaisuwa ta musamman gareki, bazan taba manta shawaranki gareni ba mawallafiyan Kishi Bayan Bai, Mumy Haj Baidau Gada). Gaskiya baka kyauta mana ba, duk da Rufy tayi laifi hukuncin ka ya fiye tsauri.” Haj Safiyyah kenan.
Yankar Kauna
{41}
“Ni wallahi bansan komi akan zancen nan b…”
“Zaki mana shiru ko sai na taso na yi kwallo da ke, ko kunyar abinda kika aikata bakiyi ba karyata shi zakiyi. Kai wannan duniya ka haifa baka haifin halin ba, Allah wadaranki Rufaida kin…”
“A’ah Alhaji Nurudden kar ka bita da baki. Ai dole aji daga gareta. In kabi ta b’arawo abi ta mabi sawo. Rufaida fadi muji” Alh Usman kenan yai saurin taron baban Rufaida wanda yake cike da fushi.
“Dady wallahi abinda na sani ban taba cin karo da sakon soyayyan Ridwan ba, sakonshi katin Allah bada saa ne sai hotonshi guda biyu. Hotuna na kuwa wasu Sanusi ke tambaya wasu ganin dama ta kesawa in bada akai masa amma wallahi ban sani ba.”
“Dady ga sheda ta.” Ridwan ya fadi bayan ya bude na’urarsa ma kwakwalwa na tafida gidanka (palmtop).
Bude musu akwatin sakonninsa yayi, ba karamin firgita Rufaida tayi ba, yace “Wa keda wannan adreshin ko shima baki sani ba?.”
Tabbas nata ne amma iyakanta rajistan makaranta dashi, saidai kuma batasan ma ko lambobin sirrin (password) da ake budewa dashi ba. Ganin shiru bazai fishsheta ba tace.
“Duk wani rajistan makaranta na a jami’a da wannan adreshin email din aka bude, amma ni tsakanina da Allah ban san ko password din budewa ba, Yaya Sanusi ke min komi, bayan aurenmu ne Umair ya bude mun wanda nake amfani dashi domin tafiyar da kasuwanci na”
“Yi mun shiru, wadderejo, sunojon banza, (wato jaira kwadayayya da fulatanci). Kin maida kowa marainin wayonki, wa zaki raina ma hankali mtswww gara tun wuri ki koma d’akinki tun kafin bakin duniya ta kama ki”. Baban Rufaida ya fadi cikin bacin rai, fada yake mata da Hausa da fulatanci.
Babu Wanda ya katse shi, har ya gaji yayi shiru, ya tashi tsaye se sannan Alh Zunnurain ya tsaida shi, ya ce matansa da Rufaida su fita, sannan yace,
“Haba Alh Nuruddeen, ina ce kai mai bada shedan Rufaida ne a duk inda take bata K’arya, bata sharri. Ni ba ina goyon bayanta bane Amma wannan abin sharrin AMININ ZAMANI ne. Don haka a matsayi na na uban Rufaida da ya bashi auren ‘yarsa ya je yai bincike akan gaskiyan lamarin kafin yazo muyi maganar komawanta”.
“Amma Alhaji …”
“Alh Nuruddeen in zaka nuna min yau ba ni na haifi Rufaida ba toh se..”
“Wallahi ba haka bane, kayi hakuri yanda ka shirya daidai ne. Allah ya saka maka da mafificin Alkhairi”.
Se bayan sallan laasar sannan su Ridwan suka bar gidan Alh Usman Gwandu. Duk yanda yaso ya ga Rufaida ya kasa, a karshe wayarshi guda ya aika mata don ya samu hanyar magana da ita.
Suna isa Malisa ya sa kai ya wuce birnin kebbi, bai zame koina ba se gidan amininsa Sanusi.
Ya sami tarba mai kyau, ya fara taba motsa baki da kayan marmarin da aka tarbeshi dashi. Suna yi suna hira.
“Na rasa ta ina zan fara, wani Karin imani na samu, domin kuwa na kara yarda cewa, duk Auren da Allah ya k’ulla ba Wanda ya isa ya hana”
“Haka ne Sanusi, Allah ya kara datar damu”.
“Wallahi Dr na maka wani babban cin amana da ban fara danasani ba se yan kwanakin nan bayan aurenka da Rufaida”.
“Cin amana kuma anini (kasancewa hakan suke kiran junansu)”
” Wallahi set up na shirya maka don ka auri kanwata. Hannah ta kasance cikin tashin hankali tun ranar da ta fara daura idanunta akanka.
Nayi zaton zaka so ta se kawai ka kawo zancen Rufaida. Ranar na zaunar da ita nayi mata nasiha da ban hakuri.
Ta amince da hakan nan amma ta fara ciwo sosai Wanda hakan ya tada hankalin iyayenmu. Gwajin farko ya nuna tana fama da hawan jini Wanda ya kai (280) ga alamun ciwon zuciya (Myocardial infarction).
Kai sheda na duk cikin yan uwa na banda kamar Hannah, nan take shedan ya kintsa min yanda zanyi. Wallahi duk wani chats da kukeyi da musayar wasik’u da kakeyi dani kakeyi. Waya kuma da Hannah kakeyi.
Banyi da nasanin aikin nan ba se da ka auri Rufaida, naje na sami baba na fada masa duk abinda ya faru, shi ya umurce ni da na bayyana maka gaskiya.
Don Allah anini ka gafarta min, nayi NADAMA,a shirye nake na amshi ko wani irin hukunci daga gare ka” ya karasa zancensa yana mai gurfanawa a gaban Ridwan.”Anini ya wuce, fatan de wannan NADAMA ya sa kayi tuba Taubatan Nasuha. Dalilin zuwa na kenan..” Nan ya kwashe komi ya fada masa.
“Innalillahi wa inna ilaihir Rajiun. Ridwan ka tafka babban kuskure, yanzu ace dagaske Rufaida tayi maka wannan laifin haka zaka cigaba da mata. Wallahi da ka tsinci kanka wuta. Kasan illan tauye hakkin mata kuwa. Tabdi”
“Ya zanyi Sanusi? Naso Rufaida fiye da tunanin mutum sannan ace ta guje ni ta auri wani”
“Hmmm toh in ka aureta ko ka hanata aurenta ya zakayi da rabon ‘ya’yan da ke tsakaninsu, kuma aure tsakaninku se yanzu ne Allah yaso ya faru. Wai kamanta karshen ayata 38 na suratul Ra’ad LIKULLI AJALIN KITAAB. Ka manta me kace min ranar da akayi mana tafsirn wajen?”
Ganin Ridwan nai da niyyar amsawa se ya cigaba
“Cewa kake babu kai ba damuwa domin komi a rubuce yake (wato dukkan abinda ke faruwa (qaddara mai kyau da akasinsa) a duniyar nan kayyadadde ne daga Allah. (Tafsir At-Tabari) ~ummu abdoul)8
Akan me zaka damu da abinda ya faru har ka dinga daukan Alhakin baiwar Allah. Yanzu dai in Allah ya kaimu gobe se muje mu nemi biko.
Amma don Allah kar ka kuskura ka sake maimata wannan. Ko ga waye, ka bar mutum da Allah kawai, shi yafi ko wa adalci”.
“Nagode Anini, samun amini kuma dan uwa irinka se an tona.
2
💔💔💔
Karfe taran safe ya musu a malisa, bayan sun gaisa ne suka maida ma Baban Rufaida abinda ya faru. Nan yai musu nasiha sannan ya ce su wuce garin Gwandu su kara bashi hakuri.
Da isansu Gwandu basu tsaya ko ina ba se gidan Alhaji Zunnurain. Ba laifi fuskanshi a sake ya tarbe su, an kawo musu abin motsa baki.
Bayan sun gama gaisawa. Nan suka kara maida Masa abinda yake tafe dasu. Bai katse su ba har suka gama sannan ya musu nasiha sosai akan cin amana da rashin bincike akan rahoto, daga karshe ya musu addua.
Sunso ya kira Rufaida Amma yai mirsisi abinshi, se kame kame Ridwan yake, don shifa matarsa ce.
“Dady don Allah zamu iya ganin Rufaida?” Sanusi ya tmby yana mai dar dar.
“Me zai Hana, bara na kirata” daukan wayarshi yayi ya kirata.
Tasha kyau abinta ta shigo falon da sallamanta gabanta na fadi.
“Dady gani”
“Su Dr keson ganinki”
Kuka ta fara kafin tace “Ni Dady bazan koma ba, na yafe masa zali na da yaci Amma na gama aurensa.
“Shike nan koma Gida. Kunji de abinda tace ko? Ni na hada da fari amma yanzu duk abinda ta zaba daidai ne. Ku samu Ku shawo kanta amma in ta nace toh sede kayi hakuri”.
Duk yanda suka so shawo kan Alh be yiyu ba, don Alh ya kafe akan abinda Rufaida keso zaayi. Haka suka bar Gwandu jiki a sanyayye.
Duk yanda Ridwan ya dauki abin ya wuce tunaninsa. Da Rufaida taga ze takura mata gidan Salma ta wuce, don duk cikin yaran Haj Jamila ba mai kyan halin Salma, ga ta da gaskiya da son cigaban mutum
Haka nan ya koma India ba wani cigaba, duk yaje se ace batanan. Ransa ya baci kwarai, ya YANKE KAUNAR samunta.
Ko da ya koma India, kwata kwata Hannah bata gane masa ba.
💔💔💔
Akwana a tashi ba wuya, watan Rufaida (6) a gida, tun Ridwan na daukan abin wasa har ya fara damunshi. Ga wani matsanancin sonta da me fizgarshi wanda ya kara masa tashin hankali
5
STORY CONTINUES BELOW

Duk inda yasan ze kama kafa yabi amma Rufaida bata saurare shi ba
Yau ma saukanshi kenan a filin jirgin Aminu kano, be Masan ina ze nufa ba, don bai da masaniya akan takamamman inda Rufaida take.
Kafin ya baro India se da yai azumin kwana bakwai don Neman taimakon Allah. Tunawa da hakan yasa ya tsaya na yan wasu dakiku yana son yaga ina zuciyarshi zata kwanta masa akan yaje.
Taxi ya dauka bai tsaya ko ina ba se gidan abokinsa Jamil, bayan sun gaisa be boye masa komi ba, ya kuma rok’e shi arziki da ya rakashi suje rok’on Rufaida, saninsa tana kunyar Jamilu gaya.
Basu bata lokaci ba suka dauki hanyar Kaduna. Don kuwa Jamil Nada tafiya washegari in basu je a lokacin ba baze sami zuwa ba.
Sun isa Kaduna da laasar, kamar kullum sun sami tarbo na gwaninta da karamci. Yaran Rufaida dun kanainayeshi se hira yake musu kasancewar su kawai yafi gani.
“Assalamu Alaikum”. Sallaman Rufaida ne ya katse musu hiransu.
Tunda ta gaisa da Jamil ta mike zata fita.
“Uhmm jjjji mana” Ridwan ya fadi yana d’ar d’ar.
“Ka shirya bani takarda tace da ka tsaidani”
“Angel please am sorry..”
“Kaga ban son wani sorry ka, in an ganka kamar mutumin kwarai Ashe macuci ne azzalumi wanda bai san darajan zumunci ba”.
“Jamil kaji ni Rufaida ke kira Macuci azzalumi ko darajan kasancewa na yayanta bata duba ba”.
“Haj Arch Rufaida kiyi hakuri Don Allah kinsan Allah yace WASSULHU KHAIR..”
“Dr Jamil kake ko wa, bana bukatan waazinka, sanda Ridwan ya tashi kashe ni baka kusa saboda haka ka masa waazi ya sake ni”. Tana kaiwa ban tai gaba.
Kowannensu baki bud’e suka bita da kallo. Basu jira sun kara minti daya ba sukayi gaba, ba direct kebbi suka nufa.
Ganin yanayin Ridwan yasa Jamil binsa. Sun isa malisa karfe 11 na dare duk da gudun da sukayi.
Bayan an bude musu sun shiga, Ridwan ya kama kafan baban Rufaida yana kuka.
“Baffa ka taimake ni Rufaida bata so na, ka taimake ni ka bata hakuri ta dawo hannuna wallahi ina sonta.”
“Shine kake kuka kamar ba jinin fulani ba, ka kwantar da hankalinka ka manta da wata Rufaida. Ka barta zatai da na sani. Ni de Nuruddeen na tsame hannu na akanta”
“A’a baba bazaayi haka ba, Ridwan fa mai laifi ne”.
“Ai Dan nan nagama magana, yanzu ina so ya nuna min shi Da ne, ya manta da ita”. Yana kaiwa nan ya shige daki.
Mamie ce ta hada musu abinci shap shap sannan ta zauna gabansu tana danna waya.
“Mamie kuna lafiya de ko” abinda sukaji daga daya bangaren wayan kenan.
“Baruwanki da wannan sallamamma. Idan baki hada kayanki nan da kwana bakwai kin koma d’akin Aurenki ba ni babu ke, ki nemi wata uwar. Allah ma an masa laifi ya yafe ballantana ke da asalinki maniyyi ne kazantar da ke hana ibada.”
“Maammmiee..”. Katse wayar tayi ta kalle su tace
“Ka shirya muku tafiya ku biyu”. Bata jira zancensu ba ta wuce.
Murna zeyi ko damuwa. Hawayen da basu dena fita daga idanta ba kenan.
💔💔💔
Barcin kirki Rufaida batayi ba, tunani take anya kuwa iyayenta su suka haife ta da zasu zabi Ridwan akanta. Basa ko duba irin wuyan da tasha amma suke so ta koma.
STORY CONTINUES BELOW

Haka de ta sak’a wannan ta kwance, ta k’ulla wannan ta warware.
Kiran sallan asuba ya tayar da ita, nan ta lura da lokutan da ta bata inama sallah da adduoi tayi ba damuwa ba da tasan tabbas zata kaiga matsaya domin kasancewan Allah maji rok’on bayinsa.
Bayan ta idar da sallah tayi azkar dinta na safe, taje ta gaida surukanta da sukai mata rikon ‘ya kamar kullum daga Alh take farawa, se Haj Jamie sannan Haj Safiyyah.
Bayan ta gaida Haj Safiyyah ta zauna gefenta tace
“Mummy nazo Neman shawara ne”
“Haba matar Auta kike fa just say it”
3
“Mummy akan zancen Ridwan ne, mumy su mamie sunfi son in koma, ga Dady ma naga kamar yafi son komawata shine nazo ki fada min me zanyi”
“Zancen gaskiya ki koma d’akinki. Zan shirya in maida ki da kaina. Kinga bin iyaye shi ke kaimu ga nasara. Ki bar komi a hannu na zan gyara komi. Nan da sati biyu (2) zaki koma.”
Kuka sosai Rufaida take, “Akan sami mutani irin mummy da dady kuwa. Mutuwa mai YANKAR KAUNA da yanzu na sake haihuwa, Allah ya jikan Umair”. Zancen zuci take hawayen na k’aruwa.
“Haba Rufaida kukan me kikeye, ki bar komi a hannu na nace ai se ya raina kanshi, se yazama miki bawa babu boka babu malam. Tashi ki shiga d’aki ki kwanta”.
Haj Safiyyah ta kira mamie, bayan sun gaisa se tace “Mamien Rufaida ko de kun kai min ‘ya ruga ne, yarinya yau ta tashi min wai tana son mjinta zata bishi. Nace ni kuwa nace se na shirya nan da sati biyu. Wallahi har da kukanta”
“Anya zan kama zancen nan naki mummyn Rufaida?” Mamie tafadi tana dariya.
“Wallahi da asuban nan tazo min da zancen komawa. Ai nan da sati biyu ya isa in gama gyara ta, Ethiopia zamu je kinsan matan kasar badaga baya ba”.
“Hmmmn lallai abin naku nayi ne”.
Suka cigaba da hiransu kafin daga baya sukai Sallama.
“Ana zaune kalau ku sa min ‘ya a gaba, ai na rufe zancen” Haj safiyyah ta fad’i tana aje wayar a gefe2
💔💔💔
A bangaren Mamie kuwa tana aje waya da sauri ta iske Baban Rufaida ta fad’a masa yanda sukai da Haj Safiyyah.
“Dama iyayi ke damunta, nasan tana son Ridwan. Allah shirye yaran Zamani”
“Ameen yai mata Albarka, baka ji farincikin da nake ba”.
“Yar fari ce fa”
3
“Kai megida wanga farinciki da ta saka ni yau ai dole na aje kunya gefe”
Sukai dariya gaba daya
💔💔💔
BAYAN SATI BIYU
Saukansu kenan garin Bombay, Alhaji Uthman, Haj Safiyyah, Rufaida da yaranta. Kowannensu na cikin farinciki in ka cire Rufaida da ke tuno zamanta gidan Ridwan.
Dereban Alh Zunnurain da ke garin ya kwashe su se gidan shi. Rufaida bata taba sanin suna da gida garin ba se wannan zuwan. Abinda yafara daukan idonta shine ‘Umair’s Villa’ kuma tsarin gidan ita ta zana, bata taba sanin an gine gidan ba se a lokacin.
Sunci sunsha yara se shiga da fita d’akunan sukeyi. Da filin wasannin yara da sauran kewayen gidan.
Mumy kuwa a nata bangaren k’ara gyara Rufaida take duk kuwa da gyaran da tasha a kasar Ethiopia. Ta mata nasiha mai ratsa jiki sannan ta kara da bata adduoin tsari.
STORY CONTINUES BELOW

Bayan Sallan isha’i suka raka ta gidanta. Tayi mamakin gyaran da akaima sashinta. Sun iske Ridwan da abokansa. Da mummy ta nemi ganin Hannah se yace ai ta tafi Nigeria da safe. (Su Hannah an cillara 9jA don kishi).
4
Nasiha sosai akai musu kafin daga karshe aka rufe da addua. Rufaida tayi kuka sosai don tsoronta kar a maimaita abinda ya faru a baya.
Bayan tafiyansu Ridwan ya roketa gafara tare da zuba Alkawura, tun tana basarwa har se da ta dara. Domin mumy se da ta nanata mata kar ta wani hukuntashi kuma haka kar ta zubar da ajinta.
A Nijeriya kuwa Hannah da Haj jamila ne gaban boka. Bayan yai rubutu a jikin wani Allo ya shafe da kasa kana yace “Gaskiya Raba su bazeyiwu ba haka kashe ta ma, se de zaa sa mata kyamar shi, shi kuma zaa sa masa matsanancin shaawarta. Duk ya kalleta se ya nemi biyan bukata, kunga anan in har ta danne zuciyarta ta amince dashi ma wata daya batare da fad’a ba toh aiki ze karye kuma asirinku ze tonu”
Ya shigaba da kiran Aljanunsa se ga hayaki ya tashi. Aljani ya fito a firgice yace “Wallahi bazan iyaba, na je sau uku amma sunyi wani addua bazan iya taba su ba”
2
Su Hannah sun firgita da jin muryan Aljani domin kuwa murya ba dadin sauraro kuma wai kuka yake.
“Kun dai ji, amma zan tura musu shuuma, zata dinga yaudaransu har su dena addua. Duk mai fadin LAA ILAHA ILLA ALLAHU WAHDAHU LAA SHARIKALAHU LAHUL MULK WA LAHUL HAMDU WA HUWA ALA KULLI SHAI’IN KADEER sau Dari (100) a rana aikinmu baze masa tasiri ba ko da kuwa tsafi ne. (Ni kuma nace ga tarin lada kuma da mutum ze tashi dashi.)”
2
“Toh mai komi, zamu sake dawowa”. Haj Jamila ta fadi tana mai ajiye masa bundle na kudi
💔💔💔
“Angel anya daga jikinki yaran nan suka fito, kai ni ban yarda ba, Allah ya miki Albarka yasa kifi haka, yasa Aljanna ne makoma. Ashe da nayi sake, wai (hmmmn You are such a blessing). Please ki so ni kar ki guje ni”. Ridwan ke surutan nan, in mai karatu ya tanka toh Rufaida ta tanka masa. A zuciyarta addua take ma Haj Safiyyah domin ta siya mata mutunci da daraja da daukaka a idon Ridwan.2
Hutun wata guda ya dauka inda suka dirji soyayya kamar zasu k’one. A watannan ta samu ta fahimce mijinta duk abinda ze kawo bacin ransa gudunsa take.
A NIJERIYA
Haj Jamila ne tare da Hannah agaban boka me Komi. Kiran gaggawa yai musu suka zo.
“Aiki yayi, amma ga mahadinsa nan, zaki shafa shi a gabanki sannan ki tabbatar da kin sadu dashi. Amma fa se kin tabbatar da baa karanta suratul Bakara a gidan ba.” Ya karasa zance sa yana mai kallon Hannah..
Bata kara sati daya ba ta had’a yanata yanata ta koma Bombay da shirinta. Ko Ridwan bai san da komawanta ba, suna zaune a falo ta shigo.
Gabanta yai mummunar fadi ganinsu zaune a tare, da alama Rufaida na yanke ma Ridwan Farce ne. Ko sannu bata ce ba ta wuce dakinta.
“Rafiq tashi kaje ga matarka kaga tasha hanya”
“Kinga angel d’an mammatse min kafafuna, naji suna zugi ne ma”
“Tab ai baka isa ba, uwargida ta dawo kace in matse maka kafa, ni nayi. Nan”. Tashi tayi ta wuce dakinta ta rufo da makulli ta ciki.
Anan tayi magrib da ishai tai kwanciyarta. Ranta taji ya baci, “dama haka masu kishiya keji, se da ta saba dashi zata. Wani dawo”. Abinda ta fadi a ranta kenan.
Tsakanin mata da miji se Allah, gari bai waye ba se da Ridwan ya biya bukatarsa da Hannah. Farinciki take har ta gaza boyewa har se da ya tanka.
“Uwargida wannan murna haka, kinyi kewana ne haka”
“Kai Ridwan banda sharri, kasan ai kai din na daban ne. Allah barmin kai”
STORY CONTINUES BELOW

“Barmuku de”
“Kanka ake ji”. Ta juya mai baya, minsharinta kawai yaji.
💔💔💔
Tashin Rufaida daga barci kenan, ji tayi duk ranta ya jagule, jikinta yai mata nauyi kuma. Da kyar ta ja jiki tayo Alwala, tayi sallah.
Ta jawo littafin Hisnul muslim dinta don tayi azkar din safe se wayarta tayi kara, dauka tayi da duba kafin nan ya tsinke, ganin lambar ya kulle yake yasa ta aje wayar.
Nan ta tuna jiya Naseera tace zata turo mata hotunan baby don ta haihu kwana uku (3) da suka wuce. Daga duba hotuna se ta cigaba da chating azkar din da batayi ba kenan.
2
Karfe takwas dai dai ya shigo dakin cikin shirinsa, ta gaishe shi kamar ana mata dole.
“Kai amma ba abinda ya kai namiji mai mata biyu ko fiye kazanta, yasaka anan ya saka a chan ba ko kunya” duk aranta ta ke fadi.
5
“Mtsswwww” bata San lokacin da ta saki tsaki ba.
“Angel lafiya kike kuwa yau”. Ridwan ya fadi yana mai rungumo ta.
“Kiyi hakuri angel kinsan ina sonki da yawa, minti goma kawai bazan zarce haka ba ki taimake ni”.
“Minti goma mene, fadi abinda zaka fadi inada abinyi”.
“Matata nake so kiyi mun rai”
“Badaga wajenta….”
“Shhhhhhhhh”
Bata iya masa gardama ba, haka kawai zuciyarta tai baki kirin, bakinciki da kyamar kanta take, idonta na auno mata Ridwan da Hannah suna abinda sukeyi.
Albarka yake shi mata haka kawai yaji dama ya kara. Ya lallaba ya tafi wajen aiki. Abin mamaki kuma yana barin gidan ya dena jin wata shaawa kuma.
💔💔💔
Abinda ke faruwa kenan a rana se ya nemeta sau takwas zuwa goma (8-10) ko fiye. Gashi kwata kwata bata jin dadin, tsanarshi se yaduwa yake a ranta, ibadan kirki bata natsuwa tayi.
Shima a nashi bangaren ya rasa me ke damunshi, da ya ji muryan Rufaida se ya biya bukatanshi da ita yake samun natsuwa, adalilinshi tayi bari, meye dalilin Hannah na cewa ta yafe musu kwanakinta? Ga ibadanshi ya ja baya sosai.
2
“Mummy ina cikin matsala, ki taimake ni” Rufaida kenan bayan sun gaisa da haj Safiyyah da ta kirata.
“Matsalan me kuma rufy, wannan karan bazan laminta bafa”.
Nan ta kwashe komi ta fada mata, bata boye mata komi ba.
“Kikace wata hudu amma se yau zaki fadi, wai wani irin zurfin cikin nan namene haka?”
“Mummy tun Abun baiyi wata ba muka taba fada akai, shike nan se yayi”
“Kina azkar dinki kuwa”
“Nakanyi wani lokacin, wani sa’in kuma se in kasa”
“Yaushe rabonki da karanta Suratul bakara a gidanki”.
“Mummy kusan wata (5)”
“Amma kema kinyi sakaci, kina sane baa so mutum yai kwana (3) bai karanta bakara a gidanshi ba, yoh ai kin bar shedanun aljanu a muhallinki maza kunna yanzu inaji”.
Tashi Rufaida tayi ta kunna Digital Quran dinta ta kunna Suratul Baqara kiran sheikh Abdul basit.
“Mummy na kunna”.
“Oya yanzu ba se anjima ba ki tashi kiyi kwaleman dakin nan, ance miki rayuwarki da dayanzu daya ne, kishiya fa gareki. Zan kira Ridwan din yanzu”.
STORY CONTINUES BELOW

Tashi tayi ta fara, yayin da achan bangaren Haj Safiyyah ta kira Ridwan. Inda ta umurce shi da ya koma gida.
Kira’an da Hannah taji ya tada hankalinta, tashi tayi ta kunna waka ta k’ura volume. Hakan yasa bata ji shigowan Ridwan ba har se da yaje wajen kashewa. Shima karatun yasa suratul Bakara.
Hankalinta ya tashi, nan ta tuna da bokan da kawarta Mohini ta kaita. Bata bata lokaci ba tadauko zinarinta ta fita, fadi take “gara na tsiyace da mutanen nan su tsiyatar dani”
2
{50}
Bata tsaya koina ba se gidan kawarta Mohini, Yar kabilar Hindi ce, kuma addinin Hindu. suna bautar Radha. Mijinta Dr charlie likita ne a asibitin su Ridwan.
Bayan sun gaisa basu tsaya ko ina ba se wajen bokan. Akai musu iso suka shiga.
Kafin ya fara aikin se da sadu da Hannah kafin ya ji bukatunta wanda hakan ne ka’idansa.
9
Nan take ya tura aljanu gidan domin su shanye ma Rufaida barin jikinta, ko haraban gidan basu isa ba su ka dawo a firgice, gurnanin da sukeyi ya firgita Hannah amma ta dake.
Boka bai bata lokaci ba ya kora ta, don yana son lafiyanshi fiye da komi. Bakincikinta se da ya gama amfani da ita sannan yace aiki baze yiwu ba.
Ko da ta isa Gida ta iske suna kone abu, taji tsoro don kamar layunta ne. Dakewa tayi ta wuce su ganin ba Wanda ya ce mata uffan yasa tadan sami kwanciyar hankali.
A Nijeriya kuwa rumfar boka mai komi ne ya kama da wuta, ba abinda ya tsira dashi, gudu yakeyi yana neman inda ze buya har ya iso bakin titi bai sani ba.
Kiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiit!!! Karar da ta ankarar da jamaa kenan. Wata mota ce ta kade shi.
“Ku kama minshi don Allah in sashi a mota Asibiti zan kaishi”.
“Alhaji mahaukaci ne fa”
“Mahaukaci ba mutum bane?”.
Sannan suka kama masa ya sashi a mota ya tafi.
“Shide mutumin nan ya huta wallahi, baya da wulakanci kuma ga kirki, da haka mutane suke ai da duniyar ta zauna lafiya”
“Wallahi kuwa baabaa, gidanshi na anguwan sarki, mutanen da ya ba jari da yawa suke, baka ganin keke napep masu ZUNNURAIN da lambobi a jiki”.
2
“Har da Yar kumbula ya bada masu zuwa Rigacikun da Maraba, ai ya ba Faisal din gidan malam Zubairu”
5
“Allah sa masu kud’in Kasan nan suyi koyi dashi su sama ma matasa aikinyi, hakan ze rage barna”
“Aameen, mu matasa kuma mu rage cin amana da yaudara”..2
Samarin da suka taya Alhaji Usman saka boka mai komi cikin mota ke zancen nan.
💔💔💔
Se bayan kwana (2) Boka mai komi ya farfado a asibitin Giwa da ke cikin garin Kaduna. Firgici ya sumar dashi dama babu wani ciwo da yaji, hakan yasa aka basu sallama
Gidanshi ya kaishi, bayan yaci yasha ya umurci matansa su zo su gaishe shi.
“Me ya kawoka gidana” Haj Jamila ta fadi tana shigowa taga mara lafiyan.
“Kin sanshi ne” inji Alhaji
“Alh ai ita ta jamin duk abinda ya same ni”
“Ta yaya? Matatace fa”
Haj Safiyyah de yar kallo ta zama.
“Nasanta shekaru ashirin da suka wuce ta hannun wata kwastama ta Haj Hadiza, sunzo akan in kashe Dan mijinta.
STORY CONTINUES BELOW

Duk aikin da nai baya ci saboda takan kuskure a wani wajen, se shekara biyar da suka wuce sannan nayi nasara. Shima wani ifiritu ne ya fito a siffan mota ya fado masa.
Alhaji Don Allah ka yafe min, sanaa tace bokanci. Kayi mun rai Alhaji”.
Fadin Haj Jamila yasa yai shiru, Haj Safiyyah CE ta taro ta da sauri, tana “Alh kamota mu kaita asibiti kar ta mutu”.
Amma ina ko motsi baiyi ba, hakan yasa ta kwara mata ruwa se ta fara motsi, shi kuwa boka yana ganin haka ya fita gidan a guje, wuk’a rik’e a hannunsa. Gudu yake se da ya isa kasuwan anguwan shanu yai kururuwa ya daba ma kansa wuk’an. Kafin mutane su karaso ya cika. Nan aka mika sa asibitin Dan tsoho da ke tudunwada kaduna.
Bombay
Rayuwa yai ma Hannah tsauri, ita ta rasa me ke damunta tunda ta ankara duk kayan da boka ya bata basa gidan, kuma Ridwan ya fita batunta se ta sameshi da tanason komawa Nijeriya da zama, bai musa mata ba. Cikin kwana biyu ta hada kayanta se kasarmu ta gado
BAYAN SHEKARU ASHIRIN (20)
Abubuwa sun faru, an haihu kuma an rasa rayuka kamar na dattijan kwarai Alh Zunnurain da Haj Safiyyah. Mutuwan da ya taba kowa kuma kullum kwanan duniya adduan bayin Allah isa garesu.
Haka anyi auren Safiyyah, Zainab da Khadija yaran Rufaida da Umair wanda se da sukai karatunsu na boko daidai gwargwado amma dukkansu mahaddata Al’qurani ne.
Ridwan ya zaman musu waliyyi, Alh Zunnurain ya rakasu dakunansu yana mai shi musu Albarka.
Soyayyan Rufaida a gun mijinta kullum sabo yake kara zama. Kyakykyawan halinta yasa ta siye zukatan dukkan dangin mijinta, hakan ya dawo da zumuncin da aka watsar shekara da shekaru.
2
Rufaida ce da tawagar yaranta samari yan shekaru sha tara (19) da ka gansu kaga yan uku ne, Abubakar, Umar da Aliyu kenan, se kuma budurwa yar shekara (14) mai suna Fadila. Yaran da Rufaida ta haifa ma Ridwan kenan a cikin shekaru (20) da aurensu.
1
Isansu kebbi kenan suka wuce asibitin FMC don gaida maras lafiya, kwace suka ganta a fannin masu fama da ciwon cida/ kanjamau.
Sun isa gareta bayan sun gaisa, ta kara lalacewa ta jeme se tari take.
“Hannah wai bakya shan magungunanki ne, kina Neman kashe kanki a banza”
“Inasha Rufaida, kwanaki na dena sha shiyasa duk ciwon ya kwantar dani. Don son Maiki ki yafe mun”
“Haba in baki min komi ba, fata Allah tashi kafadun ki”.
“Ameen”.
“Zamu wuce isowanmu kenan zamu lek’a su Nasira daga nan gwandu zamuje”
“Toh Allah bada lada”
Hannah kenan, bayan dawowanta Nijeriya da shekara daya ciwon kanjamau ya bayyana a jikinta, wanda ta kwasa a jikin boka baindiye. Tun sannan ta tsorata da duniya, ta nemi gafaransu Ridwan. Rufaida ta hana shi sakinta kuma tun lokacin suke daukan nauyin jinyarta.
💔💔💔💔
“Assalamu Alaikum”. Matashi Dan shekekara 30 ya shigo cikin shiga na kamala, firgigit tsohuwan da ke zaune ta tashi.
“Wayyo! Wayyo Umair kai min aikin gafara kar ka kashe ni na tuba”.
“Hahhhh baki tuba ba wolla, se mijinki da ya mutu ya dawo toh babana ma ze dawo”.
“Oh ni Jamila mai sunan Alhaji Kaine haka, Allah mai iko” nan ta sa kuka, kallon ta yake ya rasa ya zeyi da ita.
Sallamansu Rufaida ya tsaida ta, itama kyam ta tsaya tana kallon Zunnurain take yana rik’id’e wa zuwa Umair. Hawayen da ya fito idonta ta share tana ma Umair addua a ranta
Shigowa ake da kayan marmari. Bayan duk sun shigo sun gaisa se ta kuma sa kuka,
“Kaico na ni Jamila da nasami ikon kashe Umair kafin yai aure wa ze kula dani, dama ance baka san wa ze jik’anka ba, yanzu ji zuriansa bacin yara Hudu ga jikoki 5 kuma. Duk kwan da Allah ya nufa ze fito duniyar nan se ya fito” ta share majina sannan ta cigaba2
“Rufaida ki yafe min, Ridwan ka yafe min, duk yanda naso kuntata muku Amma Allah ya nuna min ba ni keyi ba, se gashi yanda nake cin moriyanku bancin na kowa.”
“Albarkanku muke nema Haj”
“Allah muku Albarka”
“Aameen” duk suka fadi a tare.
Rayuwa ta cigaba, Islamiyyan da Rufaida ta bude da gidan marayu duk da fatan Allah ya kai ladan zuwa ga Umair ya habaka, bacin wanda aka bude a Gwandu sun bude a Kaduna da zamfara. Talakawa da marayu suna ta Mora.
Allah ya bamu zuciyar taimakon Marayu da mabukata.
Alhamdulillah!!!!!
KARSHE