YAR LEKEN ASIRI CHAPTER 5 BY ANUP JANYAU (_SPY_🎥)

YAR LEKEN ASIRI CHAPTER 5 BY ANUP JANYAU

(_SPY_🎥)

                  Www.bankinhausanovels.com.ng 

     Cikin takunta mai tattare da jarumta ta tako har zuwa wurin da yake tsaye, tare da hard’e hannayenta a k’irji tana jifarshi da wani irin kallon raini. Saurin had’e rai yayi, don baya son ta fahimci yanayin tsoron da yake ciki, saidai ya makaro don tun kafin ta iso office d’in ta san halin da yake ciki. 

“Da izinin wa kika shigo cikin office d’in nan?, tun wuri kiyi gaugawar ficewa kafin inyi mummunan sab’a miki, don baki kai matsayi tare da darajar da zaki kwaso k’azaman k’afafuwanki ki shigo min cikin office ba. Oya get out of my office!”.

Major Khalil ya fad’a mata a d’an daburce, don ba k’aramin rikita shi Kuzeem tayi da kallonta ba.  Wani murmushin gefen baki tayi sannan tace;

“Kwantar da hankalinka zan fita ba ma sai ka koreni ba. Saidai kafin nan ina so in gargad’eka akan kada ka sake kuskuren yin abinda ka aikata. Banada wata mummunar manufa a kanka, da tuni na tona maka asiri saboda inada k’wak’k’warar hujja a kanka.  Amma idan kere na yawo zabo na yawo dole wata rana za’a had’u!”.

Kuzeem na gama fad’in haka ta juya tare da nufar hanyar ficewa daga office d’in, ba tare da ta jira jin abinda zai fad’a ba.  Yayinda Major Khalil ya bi bayanta da kallo har ta fice daga office d’in. Sai a lokacin ya kai hannu a goshinsa, ya sharce uban gumin da ya keto mai duk da sanyin A/C dake wadace a office d’in kuwa,  ya san yau da Kuzeem ta tonashi ya kad’e saboda baisan ta inda zai kare kansa ba, don yasan Kuzeem manya ce ta k’arshe indai ta sa abu a gaba dole saita gano mafari da k’arshenshi, ta k’ware wurin biyar diddigin abu duk girmansa, hakan yasa ko kad’an baiyi mamakin yanda akayi tayi saurin ganosa ba.

*1 week later*

A yau Alhaji Yusuf (Abba) ya dawo daga Dubai, bayan wasu satukka da ya shafe a can wurin wani meeting da sukayi na manyan ‘yan siyasar k’asar SARBIK.  Farin cikin da su Kuzeem ke ciki baya misiltuwa, musamman ma ita da take ‘Yar lelensa, saisa duk tafi kowa murnar dawowarsa.

 Around 8:30pm Kuzeem ta nufi part d’in Abba sakamakon kiranta a waya da yayi akan yana son ganinta. Bakinta d’auke da sallama ta shigo cikin k’ayataccen palorn shi, wanda ya gaji da tsaruwa.  Abba dake zaune yana kallon news ya amsa mata sallamar cikin fara’a, zuciyarshi cike fal da k’aunar ‘yar tashi, don yana matuk’ar k’aunar Kuzeem. Zama tayi kan lallausan rug d’in palorn tare da tank’washe k’afafuwanta tana kallonshi sannan tace;

“Barka da dare Abba!. Ina yini, ya gajiya?”.

“Lafiya Alhamdulillahi ‘Yar lelenah”.

Abba ya fad’a fuskarshi d’auke da annuri.  Wani tsadadden murmushi Kuzeem tayi, ba tare da ta sake furta wani abu ba, hakan yasa Abba gyaran murya yace;

“‘Yar lelenah na kira ki ne saboda zamuyi wata muhimmiyar magana”.

A hankali ta gyad’a kanta tace;

“Tou Abba”.

“Fatima! ke yarinya ce mai biyayya a gareni, a koda yaushe kina bin duk wani umurni da nake baki,  Allah yayi miki albarka”.

“Ameen Ameen”.

“Ina fatan a wannan karon ma ba zaki bani kunya ba?”

“Insha Allahu Abbah”.

Kuzeem ta fad’a mishi kai tsaye ba tare da ta kawo komai a ranta ba. Fuska d’auke da farin ciki Abba yake fad’in,

“Shigowar Mu’az Salame a cikin rayuwata babban alkhairi ne a gare ni, saboda nasan likkafata zata cigaba, sunana zai zagaye ko ina a fad’in k’asar nan, yayinda mahassada zasuyi ta cizon yatsa don ba haka suka so ba”.

Cike da rashin fahimtar kalaman Abba take maimaita sunan Mu’az Salame a ranta, sannan a hankali tace;

“Abba na kasa fahimtar inda zancenka  ya dosa?”.

D’an murmushin manya ya saki yace;

“Nasan sarai kin fahimceni kawai dai kina so ki nunamin halinku ne na jami’ai, to bari dai inyi miki kwatta hilla yanda zaki fahimta dakyau. Mu’az Salame gwamnan bankin NBS na k’asar nan dai da kika sani, kuma mai jiran kujerar shugabancin k’asar SARBIK nan da shekaru biyu masu zuwa, shine ya ganki yace yana sonki da aure, sannan kuma yana son a tsaida maganar aurenku cikin abinda bai gaza wata d’aya ba. Tabbas ‘yar lelenah ke d’in daban kike a cikin yaranah da har kikayi wannan babban kamu, dama kullum ina ji a raina duk sai kinfi sauran ‘yan uwanki dacen miji mai arziki. Ina fatan zaki bani had’in kanki ayi komai cikin dattako, kinji ‘Yar lelenah, idan kikayi hakan wallahi kin gama min komai a duniyar nan”.

Kallonshi kawai Kuzeem keyi har ya kammala maganar.

“Abba da kanka kake cewa in auri Mr Salame?”.

Kuzeem ta fad’a fuskarta d’auke da tsantsar mamaki. Saurin had’e rai Abba yayi yace;

“Bana son shirme Fatima, hala kam Mu’az Salame d’in Aljani ne?”.

“Kayi hak’uri Abba, amma bazan iya auren Mr Salame ba.  A tak’aice ma dai banada ra’ayin aure a yanzu ka fi kowa sanin haka Abba”.

Abba baisan sanda ya cire glass d’in idonshi yana kallonta ba, tsabar dirar mikiya da kalamanta suka yimishi a kunnuwa, nan take yaji wani uban gumi na tsattsafo mishi ta kowace kusurwa dake jikinshi, ganin asarar da take k’ok’arin yimishi, kuma yasan halin Kuzeem sarai da shegen kafuwa, tare da ra’ayin rik’au wanda ta gada daga gareshi. Muryarshi na rawa yace;

“Kinsan me kike fad’a kuwa?, kina nufin….bazaki bi umurni..na ba?”.

“Ba haka nake nufi ba Abba..”.

“Shut up my friend!!!”.

Abba ya daka mata wata irin tsawa, yana kafeta da idanuwanshi da tuni suka sanja launi tsabar b’acin rai, sannan yace;

“Dan ubanki baki isa ki kunyata ni a idon duniya ba, baki isa ba Fatima!!!”.

Yana gama fad’in haka ya nuna mata hanyar waje, muryar shi har wani shaking take yace;

“Get out….of my..room!”.

Cikin tashin hankali maras misiltuwa tayi saurin kneeling a gabanshi, ganin yanda ranshi ya b’aci ba kad’an ba. 

“Dan Allah Abba kayi hak’uri, banyi haka don niyar b’ata ranka ba”.

“I said get lost!!!”.

Ya sake fad’a mata da k’arfi yana mik’ewa tsaye, hakan yasa Kuzeem ta mik’e ta fice daga d’akin cikin sanyin jiki, kai tsaye hanyar zuwa d’akinta ta wuce bata ko bi ta kan su Ammah dake zaune palor ba. Tana isa d’akinta ta fad’a kan bed tare da lumshe idanuwanta tana jin zuciyarta na yimata wata irin suya. 

“Subhanallah Kuzeem lafiya kuwa?, meya faru tsakaninki da Abban naki?”.

Ammah da ta biyo bayanta ta fad’a tana zama bakin gadon.  A hankali Kuzeem ta bud’e idanuwanta da sukayi jawur sannan tace;

“Abba yayi fushi dani, dan Allah Ammah ki bashi hak’uri.  Duk duniyar nan zan iya jurar komai amma banda fushin ku keda Abba”.

“Tou naji zan bashi hak’urin, amma ki fara yimin bayanin abinda ke faruwa tukuna, sai insan ta inda zan fara bashi hak’urin”.

Ammah ta fad’a cike da tausayawa, don ta san duk abunda ya shiga tsakanin Abba da Kuzeem to kuwa ba k’aramin lamari ba ne. Ba musu Kuzeem tayi mata bayanin komai. Mik’ewa Ammah tayi ba tare da tace wani abu ba, ta fice daga d’akin, kai tsaye part d’in Abba ta nufa. Inda ta tarar dashi a tsaye hannuwanshi goye a bayanshi sai kai kawo yake a tsakiyar palorn. Kallo d’aya zaka yimishi ka tabbatar yana cikin tashin hankali. Zama tayi akan d’aya daga cikin kujerun palorn sannan tace;

“Alhaji shin dagaske ne abinda Kuzeem take fad’amin?”.

A mugun fusace ya juyo ya kalleta yace;

“Tambaya kike?, ko neman sani?”.

“Duka biyun”.

Ammah ta bashi amsa cike da takaici. Cikin wata irin murya mai d’auke da zallar b’acin rai,  Abba yake fad’in,

“Wanne irin abu ne banyi ma Fatima ba a duniyar nan?, wacce irin k’auna ce ban nuna mata ba?, da har zata sakamin da wannan butulcin. Na fifita soyayyarta a kan komai da kowa a duniyar nan, duk cikin ‘ya’yana babu wacce nake yima k’aunar da nake yimata, ko kad’an ban tab’a tsammanin zan cancanchi haka a wurinta ba. Don haka ki iya fad’a mata na riga na gama yanke hukunci ko tana so ko bata so sai ta auri Mu’az Salame, don ba zan yarda ta maidani k’aramin mutum ba”.

“Haba Alhaji!, wai me yake damunka ne?,  wallahi ka cire wannan dogon buri a ranka domin kuwa babu inda zai kaika sai dana sani, saboda duk wanda ya hau motar kwad’ayi to tabbas zai sauka a tashar wulak’anci. Kuma ni bazan tab’a bari hakan ya kasance ba indai ina raye”.

Da wani irin kallo Abba ya bita, sannan yace;

“Au haka kika ce?”.

Kasa bashi amsa Ammah tayi sai binshi take da idanunta da suka fara tara k’wallah, ta rasa sai yaushe mijin nata zai sanja ya cire son abin duniya a ranshi, gwargwadon hali shima yanada arzikin nan na azo a gani, a kuma yi kwatance, amma duk bai isheshi ba sai ya hangi na wani.  Abba kam hanyar bedroom d’insa ya nufa kamar zai tashi sama yana fad’in,

“Zanga tsakanin ni da ke waye keda k’arfin iko a kanta”.

A wannan dare bacci k’auracewa idanuwan Kuzeem yayi, ba wai zancen Mr Salame ba ne ke damunta don ta san ko k’asar SARBIK zata koma bangon duniya bazata tab’a aurenshi ba. Fushin da Abban ta yayi ne ke mugun d’aga mata hankali, saboda wannan shine karo na farko a rayuwarta da suka tab’a samun matsala da Abban nata,  kuma ta lura yayi fushi mai yawa da ita, wanda duk sanadin Mr Salame ne hakan ya faru, bata tab’a jin tsanar wani mahaluk’i a duniyar nan ba kamar Mr Salame, lallai zata nuna mishi iyakarshi. Haka ta cigaba da sak’e-sak’en abubuwa da dama a ranta, sai daga baya ta mik’e tare da fad’awa bathroom ta d’auro alwala ta fara gabatar da sallar nafila ko zata samu sukuni a ranta.

_Washe gari_

Koda Kuzeem taje gaida Abba kafin ta wuce aiki har ya fice daga gidan, dole ta wuce wurin aiki ranta duk a jagule. Bata wani jima da isa ba suka shiga meeting, wanda ya d’aukesu tsawon 1 hour. Bayan an kammala meeting d’in ne aka tsayar da Kuzeem, Bilal da wasu maza hud’u. Yayinda sauran suka watse ciki harda Khalil dake ta mamakin meyasa aka tsaida su Kuzeem?, tou ko dai wani laifi sukayi?, yana fatan hakan ya zamo gaskiya, don yasan ba dalilin da zaisa a tsaida su indai ba wani laifi sukayi ba.

Wani babban mutum ne da ke sanye da wasu fararen suit ya mik’e.  Hakan yasa su Kuzeem saurin mik’ewa tare da k’amewa wuri d’aya, alamar bashi girma, saboda kasancewarshi mai babban matsayi a garesu nesa ba kusa ba, don shine *Brigadier General* na hukumar. B.G Atiku Tanko kenan, wanda kallo d’aya zaka yimishi ka san baida wargi.

“Nasan zakuyi mamakin dalilin da ya sanya muka tsaida ku kou?”.

Ya fad’a yana binsu da kallo d’aya bayan d’aya, fuskar nan tashi ba fara’a.  A tare suka girgiza mashi kai alamar eh, kowannensu na tambayar kansa dalilin da yasa aka tsaida su.

“Da akwai wata muhimmiyar tattaunawa ta sirri da muke son muyi da ku”.

Cikin sauri suka ce;

“Okay Sir!”.

D’an jinjina kai yayi sannan ya koma ya zauna, tare da yimusu alama da hannu akan su zauna, sai a lokacin suma suka zauna. Daidai lokacin wani farin mutum dogo, daga cikin manyan mutane biyar da ke hall d’in ya mik’e, ya fara magana a tsanake.

“Sanin kanku ne a halin yanzu muna fuskantar manyan matsaloli a cikin wannan k’asa ta SARBIK. Wannan dalilin ne yasa hukumarmu ta d’aura aniyarta wurin ganin ta taka muhimmiyar rawarta kamar yanda ta saba domin ganin ta shawo kan wasu ‘yan matsaloli da ke addabar k’asar nan, saidai kuma a wannan karon tunkarar wad’annan matsalolin yanada matuk’ar hatsarin gaske. Hakan yasa zan baku dama ku fad’i ra’ayoyinku tare da kawo muna shawarwari akan hanyoyin da kuka ga ya dace muyi amfani da su wurin ganin munyi nasarar magance matsalolin”

Yana gama fad’in haka yayi shiru yana kallonsu domin jin ta bakinsu. Kuzeem ce ta fara mik’ewa, tare da k’amewa, kana tace;

“Dukkaninmu bamu fara gudanar da aiki wa k’asar mu ba, har saida mukayi rantsuwa tare da alk’awarin zamuyi aiki tuk’uru ba gudu ba ja da baya, duk tsanani duk wahala. jajircewa, juriya, sadaukar da lafiyarmu tare da rayukanmu, domin ganin mun kare martaba, dukiya, lafiya tare da rayukan Al’ummar k’asar nan.  Sir! shin haka ne?”.

Ta k’arashe maganar tana kallonshi. Kai yayi saurin girgiza mata yace;

“K’warai dagaske haka ne”.

D’an murmushin k’arfin hali ta saki sannan ta cigaba da fad’in,

“Inaga tunda munsan har munyi wannan alk’awarin bai kamata ace muna d’arsama zukatanmu tsoron tunkarar ko wace iriyar matsala ba, komai muninta da hatsarinta kuwa. Kawai abunda ya dace muyi shine mu zama hadari sa gabanka inda ka dosa, koda ace hakan zai zamo silar rasa rayukanmu. Inada yak’inin koda bama raye, wata rana k’asarmu da mutanen cikinta zasuyi alfahri damu..”.

_*Raf! Raf!! Raf!!! Raf!!!! Raf!!!!!*_

Tun kafin ta gama rufe baki suka shiga tab’a mata cike da yabama jarumtarta, domin kuwa kai tsaye take fad’in abinda ke ranta ba tare da fargabar komai ba, balle tsoro, tabbas kowa yasan Kuzeem jaruma ce ta gaban kwatance, hakan yasa suke matuk’ar alfahri da ita, gata dai mace kuma yarinya amma sai tsagwaron jarumta da rashin tsoro.

“Mun gode!, mun gode!! mun gode!!! Kuzeem Yusuf Garba!, abinda kika fad’a ma kawai ya wadatar da mu, don haka yanzu zamu tsunduma cikin abinda ya taramu”.

Yana gama fad’in haka yayi saurin kai hannu a goshinsa yayi mata salute fuskarshi d’auke da murmushi. ✍️

Cikin sauri itama Kuzeem tayi masa salute d’in, tare da gayyato murmushi akan kyakkyawar fuskarta, wanda iyakacinsa a bakin leb’e, sannan ta zauna. Inda ya cigaba da fad’in,

“Mun zab’oku ne, a matsayinku na zak’wark’warun ma’aikatan mu, wad’anda muka aminta da su, muka kuma yabama k’wazonsu wurin aiki da gaskiya tare da jajircewa, domin ku gudanar da wani gagarumin aiki, wanda muke sa ran samun nasara a cikinsa da yardar Allah. So insha Allahu zuwa gobe zamu sanar muku ko wanne irin aikine wannan, da kuma yanda yanayin

aikin zai kasance, saboda ba k’aramin shiri muke buk’ata ba. Bayan haka muna so ku sani, wannan sirri ne wanda bayan ku da ahalinku wad’anda suke dole a gareku, bamu lamunta wani ya jisa ba, koda a cikin hukumar nan ne kuwa, domin kuwa bayyanarsa zai iya janyo muna barazana a kan k’udurin mu, da fatan kun fahimce ni?, kuma zaku kiyaye?”.

Kusan a tare suka gyad’a kawunansu alamar gamsuwa. Murmushi yayi sannan yace;

“Daga k’arshe ina rok’on Allah ya samar muna da zaman lafiya mai d’orewa a cikin wannan k’asa tamu ta SARBIK mai albarka, ya kawo muna cigaba tare da bunk’asar tattalin arziki da kuma had’in kai”.

 “Ameen!”.

Suka amsa su dukkansu, daga haka meeting d’in ya kammalu.

Kuzeem na shigowa office d’inta, ta cire rigar saman suit d’in jikinta, ta bar ‘yar cikin kalar ligt blue, wacce tayi matuk’ar dacewa da farar fatar jikinta, dama Suit sune kayan manyan jami’an hukumar, sai idan zasu fita operation ne suke saka monkey jarket.   Wurin wani k’aramin fridge dake cikin office d’in ta isa, tare da ciro robar ruwan swan, kana ta dawo ta zauna ta fara shan ruwan, saida ta kwankwad’esu tass sannan ta aje robar, tare da lumshe idanuwanta da take jin sunyi mata mugun nauyi, ga kuma sarawar da kanta keyi mata, saboda rashin baccin da bata samu ba a daren jiya, ga kuma meeting d’in da sukayi.

A hankali ta bud’e idanuwanta tare da janyo wasu files da ke kan table d’inta ta fara dubawa, saida ta kai tsawon 15 minutes tana duba files d’in sannan ta mik’e ta fice daga office d’in.  Tana tafe Security’s na sara mata alamar bata girma, ita dai hannu kawai take d’aga musu har ta iso d’aya daga cikin buildings d’in wurin.  Cikin sauri Security’s dake bakin k’ofar shiga wurin sukayi saurin bud’e mata k’ofa tare da sara mata suka k’ame wuri d’aya, suma hannun kawai ta d’aga musu ta shige ciki.  

Kai tsaye wurin da ta hango Meerah zaune da wasu mata su biyar ta nufa, suna ganin isowarta wurin suka fara k’ok’arin mik’ewa don su sara mata, da sauri ta dakatar da su da hannunta tare da fad’in,

“Dan Allah ku barshi, na hutar da ku”.

Kusan a tare suka sakar mata murmushi suna jinjina kyawawan halayenta, tana sama dasu nesa ba kusa ba a hukumar, amma sam bata nuna musu d’agawa balle ta nuna ta fisu. Musamman Meerah da suke tamkar ‘yan uwa da Kuzeem d’in, kasancewar Meerah nada kirki matuk’a tare da hankali da nutsuwa ya sanya Kuzeem ta jata a jikinta, wanda tun Meerah bata sakin jikinta da ita don gani take ko kad’an bata kai matsayin da zatayi mu’amala da Kuzeem d’in ba, saboda ta fita komai a cikin rayuwar nan.  Amma Kuzeem bata tab’a nuna mata ta fita wani abu ba, hakan yasa Meerah ta saki jiki da ita, tana kuma bata girmanta saidai Kuzeem d’in ce ta hanata, don da fari bata kiran sunanta saidai tace *Ranki shi dad’e* kamar yanda na k’asa da ita ke kiranta, amma fafur Kuzeem ta hanata tace ta rik’a kiran sunanta kai tsaye, duk cikin jami’ai mata da ke hukumar da Meerah kawai Kuzeem ke huld’a saboda ta yarda da ita sosai. Bilal ma yana k’asa da ita amma ta hanashi bata girma saboda ya d’an girmeta, shima suna mutunci da Kuzeem, wanda tuni zuciyarsa ta kamu da zazzafar k’aunarta saidai ya san ko giyar wake ya sha bazai iya tunkarar Kuzeem da kalmar So ba, saboda ya san tafi k’arfinsa gaba da baya, kuma ya san waye ubanta, wato Alhaji Yusuf (Abba) namu na mutunci.🙇‍♀️😂

“Shine yau ko lek’ani bakiyi ba kou?”.

Kuzeem ta fad’a tana zama gefen Meerah.  D’an murmushi Meerah tayi tace;

“Ki gafarce ni Ranki shi dad’e aik……”.

Shiru tayi ganin kallon da Kuzeem keyi mata. 

5:00pm Kuzeem ta wuce gida, saboda zazzab’in  da take ji yana neman rufeta. Bata tarar da kowa a palorn gidan ba hakan yasa ta wuce part d’in Ammah, nan ta tarar da ita zaune kan kujera cikin wani irin yanayi. Sakin bag d’in hannunta tayi tare k’arasowa da sauri wurin Ammah da numfashinta ke zuwa yana dawowa. 

“Ammah!”.

Kuzeem ta fad’a tana rik’ota cikin tashin hankali. kwantar da ita tayi akan kujerar, sannan ta nufi bedroom d’inta  ta bud’e wata locker ta ciro Inheler sannan ta dawo wurin Ammah.  Saurin tallabota tayi a jikinta tare da sanya mata Inheler a baki, cikin sauri Ammah taja da k’arfi, sai a lokacin numfashinta ya d’an fara daidaita, tsawon 5 minutes ta d’auka sannan numfashinta ya dawo normal.

“Sannu Ammah”.

Inji Kuzeem da idanuwanta ke zubar da k’wallan tausayin mahaifiyar tata. Kai Ammah ta girgiza mata tace;

“Ki daina kuka, ko wane bawa da tashi kalar jarabawa a rayuwa saidai ta wani tafi ta wani”.

“Hakane Ammah. Inaga ya kamata mu tafi k’asar Japan d’in kamar yanda Dr ya bamu shawara mu gani ko Allah zaisa a dace”.

D’an murmushi Ammah tayi tace;

“Kuzeem da zan rabu da wannan Asthma da baki zo duniya kin sameni da ita ba. Saboda anyi magani har an gode Allah, ko Abban ku ya kashi mak’uddan k’ud’ad’e amma duk a banza, lamarin kamar harda iska fa”.

Cike da damuwa tace;

“Duk wata cuta da Allah ya halitta a duniyar nan, saida yayo maganinta, don haka kisa a ranki komai daren dad’ewa zaki rabu da wannan Asthma da yardar Allah.”.

Murmushi kawai Ammah tayi bata ce komai ba, hakan yasa Kuzeem tace;

“Ina su Raudah?”.

“Sunje Saloon tun d’azun”.

“Okay”.

Kuzeem ta fad’a, ta d’an jima d’akin Ammah sannan ta wuce room d’inta, bayan ta cire suit d’in jikinta ta d’aura towel kana ta shiga wanka ko zata ji d’ad’in jikinta. Tana fitowa daga wankan ta nufi gaban mirrow tare da jan stool ta zauna ta fara taje himilin bak’ar sumar kanta da ta sauko mata har a kafad’u. Turo k’ofar d’akin da akayi ne ya sanyata d’an d’ago kanta ta kalli cikin mirrow da yake yana saiti da k’ofa ne, d’an murmushi tayi tare da juyowa tace;

“Ammah”.

Itama Ammah murmushin tayi mata, sannan tace;

“Idan kin shirya ki fito ga mutuminki can (Dambu) nayi miki tun d’azun”.

Mik’ewa Kuzeem tayi ta nufi wurin Ammah tare da rungumeta, fuskarta d’auke da tsantsar farin ciki tace;

“Nagode Ammah tah”.

Allah ya sani tana mugun son dambu a rayuwarta, musamman ma na Ammah don ta iya had’ashi ba k’arya. Kanta Ammah ta shafa har lokacin fuskarta d’auke da murmushi, kana ta fice daga d’akin.  Kuzeem kuwa cikin sauri ta d’aure sumar kan nata tare da zura hijab a saman towel d’in jikinta ta nufi hanyar fita. Kai tsaye dining area ta nufa, nan masu aikinsu sukayi serving d’inta had’ad’d’en dambun, daketa k’amshin had’uwa, sannan ta fara ci duk da batada wani apatite a bakinta, amma haka nan take turashi saidai bata wani ci da yawa ba ta mik’e. Tana isowa cikin main palor ta ci karo da Abba, wanda rabonta da shi tun jiya.  Cike da girmamawa tayi saurin durk’usa tace;

“Abba ina yini”.

Banza yayi da ita tamkar ma bai san da wanzuwarta a wurin ba, ya wuce part d’in Ammah yana d’aga wayarshi da aka kira. Rai a jagule Kuzeem ta koma d’akinta, a gurguje ta zura wata bak’ar abaya a jikinta, kana ta zauna kan gado tana sak’a abubuwa a ranta. Lokaci d’aya ta saki wani murmushi mai tarin ma’anoni, tare da d’aukar wayarta ta lalubo wata number ta kira, tana jin an d’aga tace;

“Muyi magana yanzu a Skype”.

Tana gama fad’in haka ta ciro wayar daga kunnenta sannan ta katse kiran, kana ta mik’e ta d’auko macbook d’inta ta dawo kan gadon ta shiga skype.

*Har na gyara zaman d’auko muku rahoto Kuzeem ta watsomin firgitattun idanuwanta hakan yasa na gudo, karta d’auke ni da alburushi*.😹🚴‍♀️

*The following day*

Around 9:00am suka fara gudanar da Meeting d’in, inda aka fara yi musu bayanin yanda yanayin aikin yake. Saida aka shafe kusan 2 hours ana tsara musu yanda zasu gudanar da aikin, sannan suma aka nemi jin ra’ayoyinsu. Shiri na ban mamaki hukumar tayi game da wannan gagarumin aiki na *LEKEN ASIRI* da su Kuzeem zasu je.

“Kuzeem Yusuf Garba!.

B.G Atiku Tanko ya fad’a fuskar nan tashi a tamke. Saurin mik’ewa Kuzeem tayi tare da sara mishi sannan ta k’ame, tace;

“Yes Sir!”.

D’aya daga cikin wasu manyan Envelopes da ke ajiye a gabanshi ya mik’o mata, da sauri ta nufi wurinshi ta karb’a sannan ta koma ta zauna, nan ya kira Bilal shima ya bashi kana ya ba sauran mutane hud’un. Ko wannensu shiru yayi ya maida hankali wurin bud’e envelope d’in da aka bashi, sannan suka ciro takardun da ke ciki suka fara dubawa, bayan wasu mintuna suka d’ago kusan a tare da alama duk sun gama duba abinda takardun suka k’unsa. Sai a lokacin B.G Atiku Tanko yayi murmushi sannan yace;

“A halin yanzu kun tashi daga jami’an hukumar nan  kun koma a matsayin korarrin ma’aikata, don har mun riga mun lik’a notice”.

Kai sukayi saurin girgiza mishi a tare, alamar gamsuwa. 

“Ina yimuku fatan nasara a kan wannan gagarumin aiki”.

Yana gama fad’in haka ya zauna, nan wani babban mutum da ke gefenshi ya mik’e yace;

“Karku ji komai a ranku, duk wani motsi naku zai dinga gudana ne a k’ar’ashin kulawarmu. Insha Allahu zakuyi nasara”.

Yana zaunawa L.G Aliyu Iko ya mik’e fuskarshi d’auke da murmushi yace;

“Nikam banada haufi a kanku yaranah, dukkan wata yardata tana a gareku, don har ji nake a raina kunyi nasarar ma”.

Dukansu dariya sukayi jin abinda ya fad’a wai har sunyi nasara, Kuzeem kuwa d’an murmushin dole kawai ta k’irk’iro sannan ta cigaba da nazarin da take yi a ranta. Daga haka aka cigaba da yimusu sauran bayanai akan yanda aikin zai gudana cikin lumana da kuma lokacin da ko wannensu zai tafi inda aka tura shi. Sai daga bisani aka tashi meeting d’in.

                      

Kuzeem na tsaka da harhad’a wasu files da zata kai office d’in L.G Aliyu Iko.  Major Khalil ya fad’o cikin office d’in yana wani shu’umin murmushi. Ba k’aramar dariya ya bata ba amma sai ta maze ta cigaba da abinda take, tamkar bata san da wanzuwarshi a cikin office d’in ba.

“Ke kuwa wanne irin mugun laifi ne kika aikata haka?, da za’a yimiki wannan wulak’antacciyar kora ba zato babu tsammani, tamkar yanda ake korar karnuka har da security’s”.

Ya k’arashe maganar yana kallon Security’s d’in da ke tsaye bakin k’ofa suna jiran Kuzeem. Mik’ewa tayi tana kallonshi fuskarta ba yabo ba falla sa tace;

“Zaka iya komawa wurin da ka jiyo mafarin labarin ka sake tambayar laifin da na aikata na san bazaka rasa samun amsa a can ba”.

Cikin wani irin yanayi na farin ciki ya gyara tsayuwarshi yana kallonta sannan yace;

“Tou ai wak’a a bakin mai ita tafi dad’i kou?, zanfi jin dad’inta idan har kika rairamin da kanki”.

Kuzeem bata sake kulasa ba, ta d’au laptop bag d’inta tare da files d’in. Daidai lokacin Meerah ta shigo office d’in idonta cike da k’wallah ta rungume Kuzeem.  Kwashewa da wata shegiyar dariya Major Khalil yayi yace;

“Anayi da kai yafi ba’ayi da kai, wai gwamna ya koma mai unguwa!”.

Kuzeem da ke bubbuga bayan Meerah, wani murmushi tayi, sannan tace;

“Kaga ko ba komai ya d’an rage zafi, saidai kuma kama da wane bata wane!”.

Tana gama fad’in haka tayi mishi wani kallo mai wuyar tantancewa, sannan ta ja hannun Meerah da ke kuka har lokacin suka bar office d’in, yayinda Security’s dake d’auke da bindigogi suka rufa musu baya.  Suka bar Major Khalil a cikin office d’in, sai kwasar dariya yake tamkar wani zararre.

#Anup💋ā“ā¶ āµā°

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *