YAR LEKEN ASIRI CHAPTER 7 BY ANUP JANYAU (_SPY_šŸŽ„)

YAR LEKEN ASIRI CHAPTER 7 BY ANUP JANYAU

(_SPY_šŸŽ„)

               Www.bankinhausanovels.com.ng 

*_RADDAL State_*

9:40am jirgin ya sauka a cikin *S.I* airport, dama  tafiyar 40 minutes ne tsakanin FUNADE zuwa RADDAL a jirgi, saboda akwai ā€˜yar tazara kad’an tsakaninsu.  

Cikin natsuwa Kuzeem ke saukowa daga kan matakalan jirgin daga ita sai hand bag da wayarta, don tuni aka sauko musu da kayansu a field d’in jirgin, bayan ta sauk’o k’asa ne ta isa wurin kayanta, tayi tsaye tana k’arema airport d’in kallo, saurin mayar da dubonta tayi kan wayarta da kira ya shigo, sai taga Abba ne ke kiran.

ā€œBarka da zuwa Ranki shi dad’e, sunana Ahmad Sani, ni ne zan kaiki masaukinkiā€.

Tana k’ok’arin amsa kiran Abba muryar wani mutum ta ratsa kunnuwanta,  a hankali ta d’ago ta kallesa na ā€˜yan seconds, sannan ta d’auke kanta tace;

ā€œOkayā€.

Cikin sauri Mutumin ya d’auki trolley da laptop bag d’inta, sannan yace;

ā€œRanki shi dad’e, Motar tana can gabaā€.

Yana gama fad’in haka ya fara tafiya, hakan yasa Kuzeem tabi bayansa calmly, tare da kiran Abba back don nashi kiran ya katse, tana tafe tana wayar da Abba har suka iso wurin wata rantsattsar Veler black color sabuwa fil da ita, don har wani d’aukar ido take.  Da hanzari ya bud’e mata back seat, wanda tak’i shiga har saida ta gama waya da Abban, kana ta shiga, laptop bag d’inta ya aje mata a gefenta, sannan ya mayar da k’ofar ya rufe, tare da saurin zagayawa bayan boot d’in motar yasa trolleyn a ciki, daga haka ya shige motar ya tada suka bar cikin airport d’in, inda yake driving a hankali, cike da taka tsantsan.

D’an jingina ga jikin kujera Kuzeem tayi, tare da lumshe idanuwanta tana sauraren hayaniyar garin na RADDAL kama daga ta ababen hawa har zuwa ta al’ummar dake ta hada-hadarsu a kan hanyoyi. K’arar wayarta da ta cika motar ne ya sanyata bud’e kyawawan sleeping eyes d’inta masu d’aukar hankali, ta saukesu a kan screen d’in wayar. *Fav cousin* abinda ke rubuce kenan a jikin wayar, saurin d’aga kiran tayi tare da karawa a kunnenta.

ā€œDr Saimah!ā€.

Kuzeem ta fad’a tana d’an murmushin gefen baki. Daga chan b’angaren cikin tsiwa wacce ta kira da Dr Saimah d’in tace;

ā€œNa bita da gudu na mara, kikace zaki zo gani tun d’azun cikin airport sai zuba idanuwan ganinki nake amma ko mai kama da ke ban gani ba, har an fara watsewaā€.

ā€œWanne airport d’in?ā€.

ā€œInternational airport RADDAL manahā€.

ā€œAyya a S.I jirgin ya saukaā€.

ā€œS.I?, hala kam bakida gaskiya?ā€.

ā€˜Yar dariya Kuzeem tayi wacce bata shirya ba, sannan tace;

ā€œKusan hakanā€.

ā€œChapp tou nidai ban zuwa S.I saboda uniforms ne jikina, saidai ki tari Cabā€.

ā€œOkayā€.

Kuzeem na fad’in haka bata jira jin abinda Saimah zata ce ba, ta katse kiran tare da maida idanuwanta ta lumshe kamar mai bacci. Tafiyar 15 minutes ta kawo su cikin wani layi.

ā€œChiiir!ā€.

Cewar d’aya daga cikin wasu matasan samari biyu dake zaune kan wani benci a gefen babban titin layin, yana bin bayan motar da kallo. Saurin d’agowa d’ayan yayi daga dannar wayarsa da yake ya kallesa yace;

ā€œHisham lafiya kuwa?ā€.

ā€œ*Miswar* kalli canā€.

Ya fad’a yana nuna bayan motar su Kuzeem, sannan ya d’ora da fad’in,

ā€œWallahi banyi tinanin wannan motar ta iso k’asar SARBIK ba, balle har ta shigo RADDALā€.

ā€œMtssw!ā€.

Miswar d’in ya ja dogon tsaki tare da maida hankalinsa kan wayarsa k’irar kamfanin Techno spark 4, sannan yace;

ā€œKaidai kanada matsala wallahi, ni na d’auka wani abun kirki ne zaka nunamin, ashe wani shirmen banza ne kawai irin nakaā€.

Baki Hisham d’in ya bud’e yana kallonsa, yana k’ok’arin magana kenan, muryar wani mutum ta ziyarcesu.

ā€œInnalillahi gyaran kenan?, amma yaran nan kun iya shegantaka wallahi, kunsan da sanin anjima kad’an mai motar nan zaizo karb’a amma kuka zauna kuna danna wayoyi tare da firar banza, waiku wad’anne irin sakarkarun yara ne?ā€.

A tare suka mik’e suna mazurai, Hisham ne yace;

ā€œAyyi Baba mun fara gyaran fa, zaunawa mukayi mu d’an huta sai mu cigabaā€.

Dak’uwa d’an dattijon yayi masa yace;

ā€œKaci gidanku Hashimu, ni kake yiwa k’arya?ā€.

ā€˜Yar dariya Hisham yayi tare da bin bayan Miswar da tuni ya isa wurin wata mota da ke cikin d’an garejin nasu wanda yake a filin Allah, ba tare da an killace sa ba, babu wanda ya sake magana a cikinsu suka duk’ufa duba gaban motar.

A gaban wani k’aton get da aka rubutama *Nagarta Estate* ya tsayar da motar tare da danna horn, kamar abinda ake jira kenan, aka wangale musu rafkeken get d’in, a tsiyace ya cilla kan motar cikin tafkeken had’ad’d’en Estate d’in mai d’auke da manyan gidaje na alfarma kusan goma duk gininsu da tsarinsu iri d’aya, saidai kowane gidan da akwai ā€˜yar tazara tsakaninsa da wani gidan. Tsit Estate d’in yake tamkar babu ā€˜yan adam dake rayuwa a cikin wurin. 

Perking yayi cikin wani k’aramin canopy dake gaban d’aya daga cikin jerin gidajen wanda aka  rubutama House no.6, sannan ya d’an saci kallon Kuzeem ta cikin mirrow wacce har lokacin idanuwanta suke a lumshe sai ka rantse da Allah kace bacci take saidai kar take jin komai.

ā€œRanki shi dad’e mun isoā€.

Ya fad’a mata, yana bud’e murfin motar ya fita, tare da saurin bud’e mata k’ofa sannan ya d’auki laptop bag d’inta ya d’an matsa baya yana jiran fitowarta. Bud’e lumsassun idanuwanta tayi a hankali, sannan ta kai hannunta ta d’an gyara zaman veil d’in kanta, kana ta d’au hand bag d’inta ta fito daga cikin motar tare da kai dubonta kan  tsadadden watch dake d’aure a hannunta.

Da sauri ya isa bayan motar ya ciro mata trolleyn ta tare da nufar hanyar shiga gidan, hakan yasa Kuzeem tabi bayansa tana danna wayarta, ba tare da ta damu da tsayawa k’arema gidan kallo ba, balle taga yanda yake.  Saidai taku kad’an tayi taji an rungumeta ta baya, ba shiri tayi saurin kai dubonta ga marik’in nata.  Wani d’an k’aramin yaro ne da bazai wuci shekaru hud’u ba, kyakkyawane ba kad’an ba wanda kallo d’aya zaka masa ka tabbatar da buzu ne, saboda janshi har yayi yawa, gashin kan nan nashi yasha gyara yayi kwance luf a kansa, jikinsa sanye da wata farar shadda mai d’auke da tsafta ta musamman sai k’amshi yake zubawa.

ā€œMomy zata dake niā€.

Yaron ya fad’ama Kuzeem yana k’ara shigewa cikin jikinta, jin abinda ya fad’a ya sanyata d’an kalle-kallen gefenta nan idanuwanta suka sauka kan wata farar mace dake nufo wurinsu fuskarta tamke, hannunta d’auke da wata ā€˜yar k’aramar hula wacce take ta yaron ce, janyo yaron Kuzeem tayi a gabanta, tare da d’an rage tsayinta tana kallon kyakkyawar fuskarsa, shoulder d’insa ta d’an dafa sannan tayi mishi wani sassanyan murmushi  tace;

ā€œBa zan bari ta dake ka ba, kaji kou?ā€.

ā€œWacece ke?, da har zaki d’ora k’azamin hannunki akan yaronaā€.

Macen ta fad’a tana yima Kuzeem wani kallon banza, sannan ta nufi wurin da sauri, tare da fisgo yaron ta dungure masa k’eya tace;

ā€œDan ubanka wuce muje gida, shege mai kama da k’osaiā€.

Murmushi Kuzeem tayi tare da mik’ewa tsaye tace;

ā€œAyyi kiyi masa a hankali manah, kinga yaro neā€.

Saurin kallon Kuzeem macen tayi tare da jan wani dogon tsaki, sannan ta rik’e k’ugunta tace;

ā€œToufah! kaji wani sabon kicihi sa sarakkuwa university, tou idan ban bisa a hankalin ba fa?ā€.

D’an kallonta Kuzeem tayi na ā€˜yan seconds sannan ta juya ta nufi k’ofar shiga gidan ba tare da ta sake furta wata kalma ba,  hakan yasa macen ta d’aga murya tace;

ā€œKaruwa kawai anzo za’a dasa muna sabon bariki, to billahil azim mu nan matan Nagarta Estate munci uwar duk iskancin da kike tak’ama da shi yarinya, dama kin kama kanki kinyi abinda ke gabankiā€.

Tana gama fad’in haka ta fisgi hannun yaron nata da k’arfi har saida ya kusa fad’uwa k’asa tsabar fisgar da tayi masa. Kuzeem kuwa da ranta ya kai k’ololuwar b’aci bata san sanda ta saki hand bag d’inta ba a wurin tayi saurin shigewa k’ofar da  mutumin ya bud’e mata tun d’azun, cikin sauri ya d’auki hand bag d’in tare da bin bayanta, ganin ta zauna kan d’aya daga cikin kujerun palorn ne ya sanyashi fad’in,

ā€œDan Allah kiyi hak’uri Ranki shi dad’e, kinsan halin wasu mutanen sai a hankaliā€.

Kuzeem bata ce masa k’ala ba, hakan yasa ya tsuke bakinsa sannan yasa hannu a aljihun rigarsa ya ciro car key tare da wani d’an kati ya ajiye kan wani k’aramin table dake palorn, sannan ya juya ya nufi hanyar fita.

ā€œNagodeā€.

Ya tsinkayo muryar Kuzeem tana fad’a masa, juyowa yayi tare da sakar mata murmushi wanda batama san yayi ba, sannan ya fice daga gidan. Wata nannauyar ajiyar zuciya Kuzeem ta sauke tana sake nazartar kalaman wannna macen, kana ta girgiza kanta a ranta tace;

ā€œZan saita muku notin kanku da ya kwance kuwaā€.

ā€˜Yan danne-danne tayi a wayarta, tare da karawa a kunne alamar kira ne tayi.

ā€œBilalā€.

Abinda ta fad’a kenan, tare da yin shiru tana sauraren Bilal d’in dake magana, sannan tace;

ā€œZan turo ma da copy biyu, inaga ai zaiyi kou?ā€.

Sai kuma ta d’an gyad’a kanta kamar tana gabanshi tace;

ā€œOkay bani nan da 5 minutesā€.

Tana gama fad’in haka ta katse kiran, daidai lokacin kiran Saimah ya sake shigowa wayar,  saidai bata d’aga kiran ba har ya katse, a hankali ta mik’e tsaye tana k’arema palorn kallo ta ko’ina kamar mai neman wani abu, sannan ta taka ta nufi gaban wata k’atuwar Tv plasma dake manne a jikin bangon palorn, hannunta ta tura a k’asan tv tana d’an lalube can ta danna wani abu, nan take taji wata ā€˜yar tsuwa daga ta gefen damanta, hakan yasa tayi saurin juyawa wurin, idanuwanta suka sauka kan wani agogon bango mai kyau, k’arasawa tayi wurin agogon sannan ta d’anyi tsalle kad’an ta cirosa daga mazauninshi ta zuba idanuwanta akan agogon.

D’an murmushi tayi tare da kai hannu jikin wani mab’alli dake bayan agogon ta danneshi nan take agogon ya tsaya cik daga barin aikin da yake, hakan ya bata damar ganin ā€˜yar k’aramar cctv camera da ke can cikin tsakiyar agogon, daga haka ta mayar da shi mazauninshi sannan ta bar wurin ta nufi inda laptop bag d’inta ke ajiye, da d’an hanzari ta cirota daga cikin bag d’in kana ta zauna kan kujera tare da d’ora laptop d’in a saman laps d’inta, ta fara ā€˜yan danne-danne nan take wani dogon rubutu ya bayyana a cikin laptop d’in, da sauri tayi 2 copy d’inshi sannan tayi search email d’in Bilal ta tura masa copyn rubutun, fitowa tayi ta shiga cikin d’aya daga cikin folders d’inta, nan hotunan wasu manyan mutane uku maza suka bayyana, a jikin hoton mutum na biyu ta tsaida arrow sannan tayi wani murmushi tare da mik’ewa, veil d’in jikinta ta cire ta d’aura a saman kanta, sannan ta nufi hanyar ficewa daga d’akin, tayi tsaye a wurin balcony dake jikin ginin tana k’arema tsari da yanayin gidan kallo.

ā€œMom Arif lafiya dai?, naga ranki kamar a b’aceā€.

Inji wata siririyar mace dake zaune cikin wani had’ad’d’en palor tana kallon macen da ke gefenta.

ā€œBarni kawai Mom Eshmal, wallahi wata shigiya ce ta b’atan raiā€.

Gyara zama Mom Eshmal d’in tayi tana kallonta, sannan tace;

ā€œAmma dai ba ā€˜yar cikin Nagarta Estate ba kou?ā€.

ā€Ai kema kinsan ba shigiyar da ta isa duk fad’in gidan nan, bak’uwar da aka ce muna zamuyi a house no. 6 ce, in fad’a miki koda na fito ta kama Arif ta rik’e tamkar ita ta haifamun shi, ke dana dunguresa harda fad’a mun wai inyi masa a hankaliā€.

ā€œIyye samun wuri d’an kuturu da rawar dambe, kaji shegiya to sai kika ce mata me?ā€.

D’aukar Arif d’in tayi ta d’ora akan cinyoyinta sannan ta fad’a mata yanda tace ma Kuzeem, kwashewa sukayi da dariya tare da tab’ewa sannan Mom Arif tace;

ā€œAkwai meeting d’in cin uwarta wallahi, don nasan tunda ta fara kula yaranmu tou mazan mu ma bazasu tsira ba, ke kinma san wani abu?, billahil azim shegen kyau ne da ita kamar ita tayi kanta, duk yanda nake jin kaina ni kyakkyawa ce da na ganta saida na raina kaina don ta fini kyau saidai in nuna mata jan fata, kinko san akwai bala’i idan mijin Surayya ya ganta kinsan halinsa da mugun son mataā€.

ā€˜Yar dariya Mom Eshmal tayi tace;

ā€œHar na hango Surayya da dogon wando tana caskale akan babyn ta..heeā€.

Maganarta ta sark’ene jiyo kukan ā€˜yarta Eshmal daga cikin wani d’aki, da sauri ta mik’e ta nufi cikin d’akin inda ta tarar da wata yarinya da bazata wuce shekaru sha uku ba, hannunta d’auke da Eshmal d’in mai shekaru uku, sai kuka take.

ā€œKe Binta uwar me kikai mata ne?, take kuka hakaā€.

Saurin girgiza kai yarinyar tayi, fuskarta bayyane da tsoro tace;

ā€œWallai babu komai Aunty, bacci ta tashi..ā€.

Tun kafin ta k’arasa maganar taji saukar wani lafiyayyen mari a kuncinta wanda saida taga wasu taurari sun gilma mata a idanuwa.

ā€œDan kan uwarki tun daga palor in jiyo ihun yarinya kice babu abinda kikai mata?ā€.

Ta fad’a tana fisgar Eshmal d’in, da sauri Binta taja baya tana dafe kuncinta tace;

ā€œWallahi babu abinda nayi mataā€.

Ta k’arashe maganar wasu zafafan k’wallah na gangaro mata a kunci, wani banzan kallo ta watsa mata tace;

ā€œDilla banza, wuce maza ki d’auko kayan tea kizo ki had’a mataā€.

Cikin sauri Bintar ta fice daga d’akin, yayinda Mom Eshmal d’in ta bar d’akin itama, tana zama Mom Arif tace;

ā€œMe Eshmal d’in kema kuka?ā€.

ā€œHala kam yunwa ce take jiā€.

Mom Eshmal d’in ta fad’a tana shafa lallausar sumar kan yarinyar tata. Daidai lokacin Binta ta iso wurin da kayan had’a tea, kallo d’aya zaka yimata ka san natsuwarta bata tare da ita, don jikinta sai faman rawa yake, gabanta na fad’uwa ta shiga had’a tea d’in.  Baki Mom Eshmal ta saki tana kallon Binta, sannan ta saki wani uban ashar tace;

ā€œKutmarr…. keeee kashemin Eshmal zakiyi?ā€.

A firgice Binta ta dakata daga had’a tea ta d’ago ta kalleta jikinta na cigaba da rawa, wani azababben marin da taji ya ziyarci kuncinta ne ya sanyata saurin mik’ewa tsaye ta fashe da kuka, itama Mom Eshmal mik’ewa tayi tana zaro idanuwa waje tace;

ā€œNace kasheta zakiyi?, madarar da kikayi mata amfani da ita jiya shine zaki sake had’a mata tea da ita yanzu?ā€.

Ta k’arashe maganar tana dire Eshmal a kan kujera tare da cafko Binta ta sake wanka mata wani marin, a gigice Binta ta sake sakin wata k’arar tana fad’in,

ā€œDan Allah kiyi hak’uri Auntyā€.

Amma ina ko jinta batayi ta rufeta da duka cike da rashin imani, dak’yar Binta ta samu ta fice daga gidan tana kuka sosai, hakan yasa Mom Eshmal rufa mata baya a guje tana fad’in,

ā€œWallahi yau saikin yabama aya zak’inta, dan uban da ya haifekiā€.

Binta na gudu tana biye da ita har suka kusa isowa ta wurin da Kuzeem ke tsaye, cikin mamaki Kuzeem ke kallon abinda ke gudana, bata gama cika da mamaki ba saida taga Mom Eshmal tasa k’afa ta sharb’e k’afafun Binta ta zube a k’asa, nan ta sameta tana jibga, harda su had’awa da harbi tamkar dai ka samu wani k’aton gardi. Cikin sauri Kuzeem ta nufo wurin ranta a matuk’ar b’ace, tana gaf da kawowa Binta ta samu ta mik’e ko gani batayi ta nufi wurin Kuzeem tare da fad’awa jikinta ta fashe da wani sabon kukan wahala.  Tun daga kan tsafatattun fararen yatsun k’afar Kuzeem, Mom Eshmal ta fara k’arema kallo har ta iso kan kyakkyawar fuskarta wacce b’acin rai maras misiltuwa ya bayyana k’arara a kanta.

ā€œMalama miye haka?, zaki wani zo ki tare muna hanyaā€.

Mom Eshmal ta fad’a cike da masifa, tana watsama Kuzeem wani kallon banza don ta tabbatar da itace bak’uwar da sukayi a Estate d’in, wacce Mom Arif ke bata labari. Jin Kuzeem tak’i kulata ya sanyata tunkaro ta da niyar fisgo Binta da ta lahe a jikinta tana kuka sosai.  Cikin sauri Kuzeem ta maida Binta a bayanta, tare da kawar da b’acin ran da take ciki ta hanyar sauya yanayin fuskarta zuwa fara’a, kana ta watsa idanuwanta cikin na Mom Eshmal da suke cike taf da zallar rashin mutunci da tijara, a hankali Kuzeem ta furta.

ā€œDan Allah kiyi mata hak’uriā€.

A mugun k’ufule Mom Eshmal ta d’aga mata hannu tare da fad’in,

ā€œDilla malama dakata min, kinsan laifin da tayimin ne?, zaki wani tsomo bakinki kice in mata hak’uri. Ha’aan wallahi na rasa dalilin da yasa wasu mutanen suka fiye shisshigin tsiya akan abinda bai shafesu ba, koda yake tsantsar jahilci ne ke d’awainiya da su, don kuwa masu ilimi sun dad’e da sanin akwai hadisi da yace ka daina shiga abinda bai shafeka baā€.

ā€œKiyi hak’uri amma bazan baki ita ba har saikin fad’amin laifin me tayi miki?ā€.

Kuzeem ta fad’a cike da k’arfin hali, don wani irin tafarfasa ranta keyi mata. Rik’e k’ugu Mom Eshmal tayi tana yimata wani d’an iskan kallo sannan tace;

ā€œSai naji shak’a da mak’ura kana zan sanar miki da laifin da tayiminā€.

Wani murmushi Kuzeem tayi saurin gayyatowa akan fuskarta, cike da taku ta d’an rausayar da kanta kad’an tana yima Mom Eshmal kallon k’asan idanuwa sannan tace;

ā€œHaba ā€˜yar uwa me yayi zafi shi ba wuta ba?, a matsayina na malamar makaranta na dad’e da sanin kalolin halayyar yara na rashin jin magana da yawan sanya bari-bari wanda har sai kanka ya d’au chaji, hakan yasa na tambayeki domin ganin ko zan iya taimaka miki da wasu shawarwari akan yanda zaki rik’a hukunta yaran naki idan sukayi maki laifi, cikin hanya mafi sauk’i ba tare da kin wahalar da kanki baā€.

Sai a lokacin Mom Eshmal ta d’an saki fuskarta jin abinda Kuzeem ta fad’a mata, sannan ta gyara tsayuwarta tace;

ā€œOhh yanzu na fahimce ki, wallahi yarinyar nan bata da hankali ko kad’an, kiga fa madarar gwongwonin da ta fasa jiya ta had’ama Eshmal tea, to shine fa zata sake yimata amfani da sauran ragowar madarar don kawai tsabar jahilci da dabbanci irin nata, ko uban waye ya fad’a mata mu d’in matsiyata ne?ā€.

Fuska d’auke da tsantsar mamaki Kuzeem ke cigaba da kallon Mom Eshmal, tana sake tariyoma k’wak’walwarta maganganun da take, lokaci k’alilan ta gama tabbatar ma kanta ba ā€˜yar ta ba ce wannan yarinyar, don da fari tayi tunanin ā€˜yar ta ce. D’an lumshe idanuwanta tayi tana jin tamkar ta shak’o wuyan Mom Eshmal har sai taga tana k’ok’arin mutuwa ta saketa.  A hankali ta b’amb’are hannuwan Binta da ke rungume da ita ta bayanta, sannan ta bud’e idanuwanta da suka sanja launi daga fari zuwa ja ta sauke su akan Mom Eshmal da hankalinta ke kan Binta tana b’alla mata harara da kallon zaki sani ne. 

ā€œBari kiga irin hukuncin da ya dace kiyi mataā€.

Kuzeem ta fad’a cikin wata kalar murya mai wuyar tantancewa, hakan yasa Mom Eshmal tayi saurin maido dubonta akan Kuzeem d’in fuskarta d’auke da murmushin jin dad’i, saidai batayi aune ba taji saukar wani lafiyayyen mari mai d’auke da nau’o’in azaba a kuncinta, wanda yayi sanadiyar d’aukewar ji da ganinta na wucin gadi.  Yayinda Kuzeem taja hannun Binta suka bar wurin. 

Mom Eshmal kuwa tsaye tayi a wurin tamkar an dasa ta, don ko motsin kirki bata iyawa, hasalima bata cikin hayyacinta a lokacin saboda marin ya shigeta sosai yanda bakuyi tsammani ba. (*Wa zai d’an taro fuskarsa Kuzeem ta mara don ya tantance kalar azabar da Mom Eshmal ta ji?*)😹

Cikin sauri Mom Arif da fitowarta kenan daga gidan Mom Eshmal d’in don duba ko lafiya bata ga ta dawo ba tunda ta biyo Binta,  ta iso wurin don akan idanuwanta Kuzeem ta wanke Mom Eshmal da mari.

ā€œInnalillahi Mom Eshmal garin ya kika bari waccen yarinyar ta mareki?, gaskiya kin bani kunya wallahiā€.

Inji Mom Arif tana kallon gefen bakin Mom Eshmal da ya fashe yana zubda jini, ga kuma kuncinta da ya kumbura nan take, ganin bata tankata ba ya sanyata girgizata da k’arfi tana kiran sunanta, sai a lokacin ta d’an dawo hayyacinta, suna had’a ido da Mom Arif tayi saurin rintse idanuwanta tare da kai hannunta a kuncinta daidai inda Kuzeem ta wanka mata marin, sannan ta fashe da wani kuka wanda ya firgita Mom Arif ba kad’an ba, dak’yar ta samu ta jata suka bar wurin don kar kukan ya janyo hankalin sauran matan Estate d’in.

Kuzeem kuwa suna isa gidanta ta mayar da k’ofa ta rufe tare da kallon Binta cike da tausayi, kana ta nuna mata kujera alamar ta zauna,  ita kuwa ta nufi wurin da wayarta ke ajiye tare da d’aukar wayar tana dubawa, nan taga kusan 15 missed call, 5 na Ammah sai 10 da suke na Saimah. Duk da b’acin ran da take ciki saida ta d’an murmusa kana ta zauna kan kujera tare da kai hannunta kan center table ta d’auki card d’in da Ahmad ya ajiye mata, wanda yake address na layin ne a jikin card d’in, tana gama duba address d’in ta turama Saimah tare da wani guntun sak’o.  sannan ta kira number Ammah, saida ta shafe kusan 15 minutes tana waya da Ammah kana sukayi sallama, bayan ta ajiye wayar ne ta janyo laptop d’inta ta kashe tare da rufeta. Mik’ewa tayi ta nufi hanyar zuwa wurin wasu k’ofofi uku da ke cikin tangamemen palorn. 

Cikin sanyin jiki ta murd’a handle d’in k’ofar tsakiya tare da kutsa kanta a cikin d’akin, tsaye tayi tana k’arema d’akin kallo wanda yake d’auke da wani makeken gado sai closet tare da mirrow.  Kai tsaye wurin closet d’in ta nufa ta bud’e taga babu komai a ciki, hakan yasa ta rufe sannan ta nufi wata k’ofa da ke cikin d’akin wacce nake tunanin bathroom ne, tana bud’ewa kuwa shi d’in ne, nan ma maida k’ofar tayi ta rufe kana ta nufi hanyar fita ta koma palor.  Gefen Binta da ke kuka har lokacin ta zauna tare da d’an dafa kafad’arta sannan a hankali tace;

ā€œKi daina kuka kinjiā€.

A hankali Binta ta gyad’a mata kai tana jan majina. Hannu Kuzeem ta kai ta share mata k’wallan da ke kuncinta kana tace;

ā€œYa sunanki?ā€.

ā€œBintaā€.

Ta bata amsa cikin dasasshiyar murya. D’an murmushi Kuzeem tayi tare da fad’in,

ā€œInyee ashe takwara ta ce, tou yanzu kinsan me?ā€.

Saurin girgiza kai Binta tayi alamar a’ah.

ā€œIna so ki fad’a min menene alak’arki da waccen matar, da kuma duk wani abu da take miki, bana son ki b’oye min komai kinji kou?ā€.

Ba k’aramin tsoro ne ya bayyana a idanuwan Binta ba, ganin haka ya sanya Kuzeem rik’o hannuwanta tace;

ā€œKarki ji tsoro ki fad’amin, babu abinda zatayi miki, bazan bari ta sake dukanki ba. Idan kuma kika k’i fad’amin to kuwa zan maidake wurinta yanzun nanā€.

ā€œNi bazan koma wurinta baā€.

Binta ta fad’a tana fashewa da wani sabon kukan, don babu abinda take hangowa sai yanda Mom Eshmal zatah kusa kasheta idan ta rik’ata. Kuzeem na k’ok’arin magana aka fara knocking k’ofar palorn, ai batayi aune ba taji Binta ta zabura ta fad’o jikinta tana fad’in,

ā€œKarki bud’e k’ofa Aunty, ita ce tazo ta dake niā€.

ā€œBa zan bari ta dakeki baā€.

Kuzeem ta fad’a mata sannan ta janyeta daga jikinta, daidai lokacin aka sake knocking, sai kuma kira ya shigo wayar Kuzeem. Mik’ewa tayi ba tare da tabi ta kan kiran da ya shigo wayarta ba, ta nufi k’ofar tana fatan Allah yasa Mom Eshmal d’in ce, fuska a murtuk’e ta bud’e k’ofar sai kawai taci karo da Saimah tsaye a bakin k’ofar tana danna wayarta, jikinta sanye da wasu maroon uniform da d’an k’aramin white hijab a kanta.

ā€œYou’re welcome Drā€.

Kuzeem ta fad’a fuskarta ba yabo ba fallasa, d’agowa daga dannar waya Saimah tayi tare da b’alla mata wata uwar harara kana ta nufi hanyar shiga palorn ta bangajeta ta shige ciki, hakan yasa Kuzeem sakin murmushi kana ta bi bayanta.  Kan kujera Saimah ta cilla kanta tana fad’in,

ā€œWallahi Kuzeem kin gama da ni, ko ma ince kin cuceni, tunda safe kinsa na bar wurin aikina na tafi airport zaman jiranki, nayi wahalar banza ba can kika sauka ba, sannan naje airport d’in da kika ce kin sauka can ma ban sameki ba, na d’auki waya na kiraki har sau goma amma baki d’auka ba, billahi yau idan hawan jini ya kamani kece silaā€.

               ******************

ā€œMom Arif dan Allah ina so kimin alfarmar karki sanar da kowa wannan abin da ya faruā€.

Inji Mom Eshmal tana kallonta fuskarta d’auke da tsantsar damuwa, kwashewa da dariya Mom Arif tayi tace;

ā€œAmma wallahi yarinyar nan ta bala’in gamawa da ke Mom Eshmal, ta mareki baki rama ba, ta kuma kumbura miki fuska, kai Innalillahi wallahi abun tamkar a film haka na gansaā€.

Had’e rai Mom Eshmal tayi tace;

ā€œHaba Mom Arif yanzu fa nace karki sanar da kowa don gujewa dariya, shine ke zaki sakani gaba kina min dariyar?, tou bari kiga abinda zanyi ma yarinyar nan wallahi saita raina kanta, kuma yau idan Binta ta dawo gidan nan billahil azim saina kusa halakata don sai na sumar da itaā€.

Zaro idanuwa Mom Arif tayi tace;

ā€œA’ah Mom Eshmal ki k’yale yarinyar nan haka, haba ai ta daku a hannunki wallahi karki je ki karairaya ā€˜yar mutaneā€.

ā€œMtsswww ke kika san wannan, nidai yanzu bari kiji kalar cin uwar da na shirya ma wannan ā€˜yar iskar, wallahi na rantse miki da Allah ba zata sake kwashe kwana uku ba a gidan nan, zata had’a komatsanta ta k’ara gabaā€.

Tana gama fad’in haka ta rad’a ma Mom Arif wata magana a kunnenta, kusan a tare suka kwashe da dariya tare da tab’a hannuwa, sannan Mom Arif ta mik’e tace;

ā€œYanzu fita zanyi K’awata, zan tab’oki a waya mu k’arasa zancen ko kuma idan na dawo in shigo anjimaā€.

               **************

Sai yanzu su Miswar suka gama gyaran motar da suke, wurin bencin da suke zama suka zauna, sai kuma Hisham ya mik’e yace;

ā€œAbokina dan Allah idan Baba ya tambayeka ina na tafi kace masa nayi shagon askiā€.

Da mamaki Miswar ya kallesa yace;

ā€œTou amma dai ka san zaka kwance tayoyin waccen motar kou?ā€.

Ya k’arashe maganar yana nuna mishi wata babbar mota da ke ajiye cikin garejin, d’an tsaki Hisham yayi yace;

ā€œIdan na dawo zan cire, bazan dad’e baā€.

Miswar bai sake cemasa komai ba ya maida hankalinsa akan wayarsa, Hisham kuwa wurin wani tsohon Scooter ya nufa tare da hawa ya bar wurin.

                ************

Kuzeem na dariya tace;

ā€œAyya Dr kiyi hak’uri, akasi aka samuā€.

Saimah da ta bud’e baki da niyyar magana idanuwanta suka sauka kan Binta da ta rakub’e kan kujera tana kallonsu.

#AnupšŸ’‹ā¶ā¶ ⁷⁰

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *