YAR LEKEN ASIRI CHAPTER 7 BY ANUP JANYAU
(_SPY_🎥)
Www.bankinhausanovels.com.ng
*_RADDAL State_*
9:40am jirgin ya sauka a cikin *S.I* airport, dama tafiyar 40 minutes ne tsakanin FUNADE zuwa RADDAL a jirgi, saboda akwai āyar tazara kadāan tsakaninsu.
Cikin natsuwa Kuzeem ke saukowa daga kan matakalan jirgin daga ita sai hand bag da wayarta, don tuni aka sauko musu da kayansu a field dāin jirgin, bayan ta saukāo kāasa ne ta isa wurin kayanta, tayi tsaye tana kāarema airport dāin kallo, saurin mayar da dubonta tayi kan wayarta da kira ya shigo, sai taga Abba ne ke kiran.
āBarka da zuwa Ranki shi dadāe, sunana Ahmad Sani, ni ne zan kaiki masaukinkiā.
Tana kāokāarin amsa kiran Abba muryar wani mutum ta ratsa kunnuwanta, a hankali ta dāago ta kallesa na āyan seconds, sannan ta dāauke kanta tace;
āOkayā.
Cikin sauri Mutumin ya dāauki trolley da laptop bag dāinta, sannan yace;
āRanki shi dadāe, Motar tana can gabaā.
Yana gama fadāin haka ya fara tafiya, hakan yasa Kuzeem tabi bayansa calmly, tare da kiran Abba back don nashi kiran ya katse, tana tafe tana wayar da Abba har suka iso wurin wata rantsattsar Veler black color sabuwa fil da ita, don har wani dāaukar ido take. Da hanzari ya budāe mata back seat, wanda takāi shiga har saida ta gama waya da Abban, kana ta shiga, laptop bag dāinta ya aje mata a gefenta, sannan ya mayar da kāofar ya rufe, tare da saurin zagayawa bayan boot dāin motar yasa trolleyn a ciki, daga haka ya shige motar ya tada suka bar cikin airport dāin, inda yake driving a hankali, cike da taka tsantsan.
Dāan jingina ga jikin kujera Kuzeem tayi, tare da lumshe idanuwanta tana sauraren hayaniyar garin na RADDAL kama daga ta ababen hawa har zuwa ta alāummar dake ta hada-hadarsu a kan hanyoyi. Kāarar wayarta da ta cika motar ne ya sanyata budāe kyawawan sleeping eyes dāinta masu dāaukar hankali, ta saukesu a kan screen dāin wayar. *Fav cousin* abinda ke rubuce kenan a jikin wayar, saurin dāaga kiran tayi tare da karawa a kunnenta.
āDr Saimah!ā.
Kuzeem ta fadāa tana dāan murmushin gefen baki. Daga chan bāangaren cikin tsiwa wacce ta kira da Dr Saimah dāin tace;
āNa bita da gudu na mara, kikace zaki zo gani tun dāazun cikin airport sai zuba idanuwan ganinki nake amma ko mai kama da ke ban gani ba, har an fara watsewaā.
āWanne airport dāin?ā.
āInternational airport RADDAL manahā.
āAyya a S.I jirgin ya saukaā.
āS.I?, hala kam bakida gaskiya?ā.
āYar dariya Kuzeem tayi wacce bata shirya ba, sannan tace;
āKusan hakanā.
āChapp tou nidai ban zuwa S.I saboda uniforms ne jikina, saidai ki tari Cabā.
āOkayā.
Kuzeem na fadāin haka bata jira jin abinda Saimah zata ce ba, ta katse kiran tare da maida idanuwanta ta lumshe kamar mai bacci. Tafiyar 15 minutes ta kawo su cikin wani layi.
āChiiir!ā.
Cewar dāaya daga cikin wasu matasan samari biyu dake zaune kan wani benci a gefen babban titin layin, yana bin bayan motar da kallo. Saurin dāagowa dāayan yayi daga dannar wayarsa da yake ya kallesa yace;
āHisham lafiya kuwa?ā.
ā*Miswar* kalli canā.
Ya fadāa yana nuna bayan motar su Kuzeem, sannan ya dāora da fadāin,
āWallahi banyi tinanin wannan motar ta iso kāasar SARBIK ba, balle har ta shigo RADDALā.
āMtssw!ā.
Miswar dāin ya ja dogon tsaki tare da maida hankalinsa kan wayarsa kāirar kamfanin Techno spark 4, sannan yace;
āKaidai kanada matsala wallahi, ni na dāauka wani abun kirki ne zaka nunamin, ashe wani shirmen banza ne kawai irin nakaā.
Baki Hisham dāin ya budāe yana kallonsa, yana kāokāarin magana kenan, muryar wani mutum ta ziyarcesu.
āInnalillahi gyaran kenan?, amma yaran nan kun iya shegantaka wallahi, kunsan da sanin anjima kadāan mai motar nan zaizo karbāa amma kuka zauna kuna danna wayoyi tare da firar banza, waiku wadāanne irin sakarkarun yara ne?ā.
A tare suka mikāe suna mazurai, Hisham ne yace;
āAyyi Baba mun fara gyaran fa, zaunawa mukayi mu dāan huta sai mu cigabaā.
Dakāuwa dāan dattijon yayi masa yace;
āKaci gidanku Hashimu, ni kake yiwa kāarya?ā.
āYar dariya Hisham yayi tare da bin bayan Miswar da tuni ya isa wurin wata mota da ke cikin dāan garejin nasu wanda yake a filin Allah, ba tare da an killace sa ba, babu wanda ya sake magana a cikinsu suka dukāufa duba gaban motar.
A gaban wani kāaton get da aka rubutama *Nagarta Estate* ya tsayar da motar tare da danna horn, kamar abinda ake jira kenan, aka wangale musu rafkeken get dāin, a tsiyace ya cilla kan motar cikin tafkeken hadāadādāen Estate dāin mai dāauke da manyan gidaje na alfarma kusan goma duk gininsu da tsarinsu iri dāaya, saidai kowane gidan da akwai āyar tazara tsakaninsa da wani gidan. Tsit Estate dāin yake tamkar babu āyan adam dake rayuwa a cikin wurin.
Perking yayi cikin wani kāaramin canopy dake gaban dāaya daga cikin jerin gidajen wanda aka rubutama House no.6, sannan ya dāan saci kallon Kuzeem ta cikin mirrow wacce har lokacin idanuwanta suke a lumshe sai ka rantse da Allah kace bacci take saidai kar take jin komai.
āRanki shi dadāe mun isoā.
Ya fadāa mata, yana budāe murfin motar ya fita, tare da saurin budāe mata kāofa sannan ya dāauki laptop bag dāinta ya dāan matsa baya yana jiran fitowarta. Budāe lumsassun idanuwanta tayi a hankali, sannan ta kai hannunta ta dāan gyara zaman veil dāin kanta, kana ta dāau hand bag dāinta ta fito daga cikin motar tare da kai dubonta kan tsadadden watch dake dāaure a hannunta.
Da sauri ya isa bayan motar ya ciro mata trolleyn ta tare da nufar hanyar shiga gidan, hakan yasa Kuzeem tabi bayansa tana danna wayarta, ba tare da ta damu da tsayawa kāarema gidan kallo ba, balle taga yanda yake. Saidai taku kadāan tayi taji an rungumeta ta baya, ba shiri tayi saurin kai dubonta ga marikāin nata. Wani dāan kāaramin yaro ne da bazai wuci shekaru hudāu ba, kyakkyawane ba kadāan ba wanda kallo dāaya zaka masa ka tabbatar da buzu ne, saboda janshi har yayi yawa, gashin kan nan nashi yasha gyara yayi kwance luf a kansa, jikinsa sanye da wata farar shadda mai dāauke da tsafta ta musamman sai kāamshi yake zubawa.
āMomy zata dake niā.
Yaron ya fadāama Kuzeem yana kāara shigewa cikin jikinta, jin abinda ya fadāa ya sanyata dāan kalle-kallen gefenta nan idanuwanta suka sauka kan wata farar mace dake nufo wurinsu fuskarta tamke, hannunta dāauke da wata āyar kāaramar hula wacce take ta yaron ce, janyo yaron Kuzeem tayi a gabanta, tare da dāan rage tsayinta tana kallon kyakkyawar fuskarsa, shoulder dāinsa ta dāan dafa sannan tayi mishi wani sassanyan murmushi tace;
āBa zan bari ta dake ka ba, kaji kou?ā.
āWacece ke?, da har zaki dāora kāazamin hannunki akan yaronaā.
Macen ta fadāa tana yima Kuzeem wani kallon banza, sannan ta nufi wurin da sauri, tare da fisgo yaron ta dungure masa kāeya tace;
āDan ubanka wuce muje gida, shege mai kama da kāosaiā.
Murmushi Kuzeem tayi tare da mikāewa tsaye tace;
āAyyi kiyi masa a hankali manah, kinga yaro neā.
Saurin kallon Kuzeem macen tayi tare da jan wani dogon tsaki, sannan ta rikāe kāugunta tace;
āToufah! kaji wani sabon kicihi sa sarakkuwa university, tou idan ban bisa a hankalin ba fa?ā.
Dāan kallonta Kuzeem tayi na āyan seconds sannan ta juya ta nufi kāofar shiga gidan ba tare da ta sake furta wata kalma ba, hakan yasa macen ta dāaga murya tace;
āKaruwa kawai anzo zaāa dasa muna sabon bariki, to billahil azim mu nan matan Nagarta Estate munci uwar duk iskancin da kike takāama da shi yarinya, dama kin kama kanki kinyi abinda ke gabankiā.
Tana gama fadāin haka ta fisgi hannun yaron nata da kāarfi har saida ya kusa fadāuwa kāasa tsabar fisgar da tayi masa. Kuzeem kuwa da ranta ya kai kāololuwar bāaci bata san sanda ta saki hand bag dāinta ba a wurin tayi saurin shigewa kāofar da mutumin ya budāe mata tun dāazun, cikin sauri ya dāauki hand bag dāin tare da bin bayanta, ganin ta zauna kan dāaya daga cikin kujerun palorn ne ya sanyashi fadāin,
āDan Allah kiyi hakāuri Ranki shi dadāe, kinsan halin wasu mutanen sai a hankaliā.
Kuzeem bata ce masa kāala ba, hakan yasa ya tsuke bakinsa sannan yasa hannu a aljihun rigarsa ya ciro car key tare da wani dāan kati ya ajiye kan wani kāaramin table dake palorn, sannan ya juya ya nufi hanyar fita.
āNagodeā.
Ya tsinkayo muryar Kuzeem tana fadāa masa, juyowa yayi tare da sakar mata murmushi wanda batama san yayi ba, sannan ya fice daga gidan. Wata nannauyar ajiyar zuciya Kuzeem ta sauke tana sake nazartar kalaman wannna macen, kana ta girgiza kanta a ranta tace;
āZan saita muku notin kanku da ya kwance kuwaā.
āYan danne-danne tayi a wayarta, tare da karawa a kunne alamar kira ne tayi.
āBilalā.
Abinda ta fadāa kenan, tare da yin shiru tana sauraren Bilal dāin dake magana, sannan tace;
āZan turo ma da copy biyu, inaga ai zaiyi kou?ā.
Sai kuma ta dāan gyadāa kanta kamar tana gabanshi tace;
āOkay bani nan da 5 minutesā.
Tana gama fadāin haka ta katse kiran, daidai lokacin kiran Saimah ya sake shigowa wayar, saidai bata dāaga kiran ba har ya katse, a hankali ta mikāe tsaye tana kāarema palorn kallo ta koāina kamar mai neman wani abu, sannan ta taka ta nufi gaban wata kāatuwar Tv plasma dake manne a jikin bangon palorn, hannunta ta tura a kāasan tv tana dāan lalube can ta danna wani abu, nan take taji wata āyar tsuwa daga ta gefen damanta, hakan yasa tayi saurin juyawa wurin, idanuwanta suka sauka kan wani agogon bango mai kyau, kāarasawa tayi wurin agogon sannan ta dāanyi tsalle kadāan ta cirosa daga mazauninshi ta zuba idanuwanta akan agogon.
Dāan murmushi tayi tare da kai hannu jikin wani mabāalli dake bayan agogon ta danneshi nan take agogon ya tsaya cik daga barin aikin da yake, hakan ya bata damar ganin āyar kāaramar cctv camera da ke can cikin tsakiyar agogon, daga haka ta mayar da shi mazauninshi sannan ta bar wurin ta nufi inda laptop bag dāinta ke ajiye, da dāan hanzari ta cirota daga cikin bag dāin kana ta zauna kan kujera tare da dāora laptop dāin a saman laps dāinta, ta fara āyan danne-danne nan take wani dogon rubutu ya bayyana a cikin laptop dāin, da sauri tayi 2 copy dāinshi sannan tayi search email dāin Bilal ta tura masa copyn rubutun, fitowa tayi ta shiga cikin dāaya daga cikin folders dāinta, nan hotunan wasu manyan mutane uku maza suka bayyana, a jikin hoton mutum na biyu ta tsaida arrow sannan tayi wani murmushi tare da mikāewa, veil dāin jikinta ta cire ta dāaura a saman kanta, sannan ta nufi hanyar ficewa daga dāakin, tayi tsaye a wurin balcony dake jikin ginin tana kāarema tsari da yanayin gidan kallo.
āMom Arif lafiya dai?, naga ranki kamar a bāaceā.
Inji wata siririyar mace dake zaune cikin wani hadāadādāen palor tana kallon macen da ke gefenta.
āBarni kawai Mom Eshmal, wallahi wata shigiya ce ta bāatan raiā.
Gyara zama Mom Eshmal dāin tayi tana kallonta, sannan tace;
āAmma dai ba āyar cikin Nagarta Estate ba kou?ā.
āAi kema kinsan ba shigiyar da ta isa duk fadāin gidan nan, bakāuwar da aka ce muna zamuyi a house no. 6 ce, in fadāa miki koda na fito ta kama Arif ta rikāe tamkar ita ta haifamun shi, ke dana dunguresa harda fadāa mun wai inyi masa a hankaliā.
āIyye samun wuri dāan kuturu da rawar dambe, kaji shegiya to sai kika ce mata me?ā.
Dāaukar Arif dāin tayi ta dāora akan cinyoyinta sannan ta fadāa mata yanda tace ma Kuzeem, kwashewa sukayi da dariya tare da tabāewa sannan Mom Arif tace;
āAkwai meeting dāin cin uwarta wallahi, don nasan tunda ta fara kula yaranmu tou mazan mu ma bazasu tsira ba, ke kinma san wani abu?, billahil azim shegen kyau ne da ita kamar ita tayi kanta, duk yanda nake jin kaina ni kyakkyawa ce da na ganta saida na raina kaina don ta fini kyau saidai in nuna mata jan fata, kinko san akwai balaāi idan mijin Surayya ya ganta kinsan halinsa da mugun son mataā.
āYar dariya Mom Eshmal tayi tace;
āHar na hango Surayya da dogon wando tana caskale akan babyn ta..heeā.
Maganarta ta sarkāene jiyo kukan āyarta Eshmal daga cikin wani dāaki, da sauri ta mikāe ta nufi cikin dāakin inda ta tarar da wata yarinya da bazata wuce shekaru sha uku ba, hannunta dāauke da Eshmal dāin mai shekaru uku, sai kuka take.
āKe Binta uwar me kikai mata ne?, take kuka hakaā.
Saurin girgiza kai yarinyar tayi, fuskarta bayyane da tsoro tace;
āWallai babu komai Aunty, bacci ta tashi..ā.
Tun kafin ta kāarasa maganar taji saukar wani lafiyayyen mari a kuncinta wanda saida taga wasu taurari sun gilma mata a idanuwa.
āDan kan uwarki tun daga palor in jiyo ihun yarinya kice babu abinda kikai mata?ā.
Ta fadāa tana fisgar Eshmal dāin, da sauri Binta taja baya tana dafe kuncinta tace;
āWallahi babu abinda nayi mataā.
Ta kāarashe maganar wasu zafafan kāwallah na gangaro mata a kunci, wani banzan kallo ta watsa mata tace;
āDilla banza, wuce maza ki dāauko kayan tea kizo ki hadāa mataā.
Cikin sauri Bintar ta fice daga dāakin, yayinda Mom Eshmal dāin ta bar dāakin itama, tana zama Mom Arif tace;
āMe Eshmal dāin kema kuka?ā.
āHala kam yunwa ce take jiā.
Mom Eshmal dāin ta fadāa tana shafa lallausar sumar kan yarinyar tata. Daidai lokacin Binta ta iso wurin da kayan hadāa tea, kallo dāaya zaka yimata ka san natsuwarta bata tare da ita, don jikinta sai faman rawa yake, gabanta na fadāuwa ta shiga hadāa tea dāin. Baki Mom Eshmal ta saki tana kallon Binta, sannan ta saki wani uban ashar tace;
āKutmarr…. keeee kashemin Eshmal zakiyi?ā.
A firgice Binta ta dakata daga hadāa tea ta dāago ta kalleta jikinta na cigaba da rawa, wani azababben marin da taji ya ziyarci kuncinta ne ya sanyata saurin mikāewa tsaye ta fashe da kuka, itama Mom Eshmal mikāewa tayi tana zaro idanuwa waje tace;
āNace kasheta zakiyi?, madarar da kikayi mata amfani da ita jiya shine zaki sake hadāa mata tea da ita yanzu?ā.
Ta kāarashe maganar tana dire Eshmal a kan kujera tare da cafko Binta ta sake wanka mata wani marin, a gigice Binta ta sake sakin wata kāarar tana fadāin,
āDan Allah kiyi hakāuri Auntyā.
Amma ina ko jinta batayi ta rufeta da duka cike da rashin imani, dakāyar Binta ta samu ta fice daga gidan tana kuka sosai, hakan yasa Mom Eshmal rufa mata baya a guje tana fadāin,
āWallahi yau saikin yabama aya zakāinta, dan uban da ya haifekiā.
Binta na gudu tana biye da ita har suka kusa isowa ta wurin da Kuzeem ke tsaye, cikin mamaki Kuzeem ke kallon abinda ke gudana, bata gama cika da mamaki ba saida taga Mom Eshmal tasa kāafa ta sharbāe kāafafun Binta ta zube a kāasa, nan ta sameta tana jibga, harda su hadāawa da harbi tamkar dai ka samu wani kāaton gardi. Cikin sauri Kuzeem ta nufo wurin ranta a matukāar bāace, tana gaf da kawowa Binta ta samu ta mikāe ko gani batayi ta nufi wurin Kuzeem tare da fadāawa jikinta ta fashe da wani sabon kukan wahala. Tun daga kan tsafatattun fararen yatsun kāafar Kuzeem, Mom Eshmal ta fara kāarema kallo har ta iso kan kyakkyawar fuskarta wacce bāacin rai maras misiltuwa ya bayyana kāarara a kanta.
āMalama miye haka?, zaki wani zo ki tare muna hanyaā.
Mom Eshmal ta fadāa cike da masifa, tana watsama Kuzeem wani kallon banza don ta tabbatar da itace bakāuwar da sukayi a Estate dāin, wacce Mom Arif ke bata labari. Jin Kuzeem takāi kulata ya sanyata tunkaro ta da niyar fisgo Binta da ta lahe a jikinta tana kuka sosai. Cikin sauri Kuzeem ta maida Binta a bayanta, tare da kawar da bāacin ran da take ciki ta hanyar sauya yanayin fuskarta zuwa faraāa, kana ta watsa idanuwanta cikin na Mom Eshmal da suke cike taf da zallar rashin mutunci da tijara, a hankali Kuzeem ta furta.
āDan Allah kiyi mata hakāuriā.
A mugun kāufule Mom Eshmal ta dāaga mata hannu tare da fadāin,
āDilla malama dakata min, kinsan laifin da tayimin ne?, zaki wani tsomo bakinki kice in mata hakāuri. Haāaan wallahi na rasa dalilin da yasa wasu mutanen suka fiye shisshigin tsiya akan abinda bai shafesu ba, koda yake tsantsar jahilci ne ke dāawainiya da su, don kuwa masu ilimi sun dadāe da sanin akwai hadisi da yace ka daina shiga abinda bai shafeka baā.
āKiyi hakāuri amma bazan baki ita ba har saikin fadāamin laifin me tayi miki?ā.
Kuzeem ta fadāa cike da kāarfin hali, don wani irin tafarfasa ranta keyi mata. Rikāe kāugu Mom Eshmal tayi tana yimata wani dāan iskan kallo sannan tace;
āSai naji shakāa da makāura kana zan sanar miki da laifin da tayiminā.
Wani murmushi Kuzeem tayi saurin gayyatowa akan fuskarta, cike da taku ta dāan rausayar da kanta kadāan tana yima Mom Eshmal kallon kāasan idanuwa sannan tace;
āHaba āyar uwa me yayi zafi shi ba wuta ba?, a matsayina na malamar makaranta na dadāe da sanin kalolin halayyar yara na rashin jin magana da yawan sanya bari-bari wanda har sai kanka ya dāau chaji, hakan yasa na tambayeki domin ganin ko zan iya taimaka miki da wasu shawarwari akan yanda zaki rikāa hukunta yaran naki idan sukayi maki laifi, cikin hanya mafi saukāi ba tare da kin wahalar da kanki baā.
Sai a lokacin Mom Eshmal ta dāan saki fuskarta jin abinda Kuzeem ta fadāa mata, sannan ta gyara tsayuwarta tace;
āOhh yanzu na fahimce ki, wallahi yarinyar nan bata da hankali ko kadāan, kiga fa madarar gwongwonin da ta fasa jiya ta hadāama Eshmal tea, to shine fa zata sake yimata amfani da sauran ragowar madarar don kawai tsabar jahilci da dabbanci irin nata, ko uban waye ya fadāa mata mu dāin matsiyata ne?ā.
Fuska dāauke da tsantsar mamaki Kuzeem ke cigaba da kallon Mom Eshmal, tana sake tariyoma kāwakāwalwarta maganganun da take, lokaci kāalilan ta gama tabbatar ma kanta ba āyar ta ba ce wannan yarinyar, don da fari tayi tunanin āyar ta ce. Dāan lumshe idanuwanta tayi tana jin tamkar ta shakāo wuyan Mom Eshmal har sai taga tana kāokāarin mutuwa ta saketa. A hankali ta bāambāare hannuwan Binta da ke rungume da ita ta bayanta, sannan ta budāe idanuwanta da suka sanja launi daga fari zuwa ja ta sauke su akan Mom Eshmal da hankalinta ke kan Binta tana bāalla mata harara da kallon zaki sani ne.
āBari kiga irin hukuncin da ya dace kiyi mataā.
Kuzeem ta fadāa cikin wata kalar murya mai wuyar tantancewa, hakan yasa Mom Eshmal tayi saurin maido dubonta akan Kuzeem dāin fuskarta dāauke da murmushin jin dadāi, saidai batayi aune ba taji saukar wani lafiyayyen mari mai dāauke da nauāoāin azaba a kuncinta, wanda yayi sanadiyar dāaukewar ji da ganinta na wucin gadi. Yayinda Kuzeem taja hannun Binta suka bar wurin.
Mom Eshmal kuwa tsaye tayi a wurin tamkar an dasa ta, don ko motsin kirki bata iyawa, hasalima bata cikin hayyacinta a lokacin saboda marin ya shigeta sosai yanda bakuyi tsammani ba. (*Wa zai dāan taro fuskarsa Kuzeem ta mara don ya tantance kalar azabar da Mom Eshmal ta ji?*)😹
Cikin sauri Mom Arif da fitowarta kenan daga gidan Mom Eshmal dāin don duba ko lafiya bata ga ta dawo ba tunda ta biyo Binta, ta iso wurin don akan idanuwanta Kuzeem ta wanke Mom Eshmal da mari.
āInnalillahi Mom Eshmal garin ya kika bari waccen yarinyar ta mareki?, gaskiya kin bani kunya wallahiā.
Inji Mom Arif tana kallon gefen bakin Mom Eshmal da ya fashe yana zubda jini, ga kuma kuncinta da ya kumbura nan take, ganin bata tankata ba ya sanyata girgizata da kāarfi tana kiran sunanta, sai a lokacin ta dāan dawo hayyacinta, suna hadāa ido da Mom Arif tayi saurin rintse idanuwanta tare da kai hannunta a kuncinta daidai inda Kuzeem ta wanka mata marin, sannan ta fashe da wani kuka wanda ya firgita Mom Arif ba kadāan ba, dakāyar ta samu ta jata suka bar wurin don kar kukan ya janyo hankalin sauran matan Estate dāin.
Kuzeem kuwa suna isa gidanta ta mayar da kāofa ta rufe tare da kallon Binta cike da tausayi, kana ta nuna mata kujera alamar ta zauna, ita kuwa ta nufi wurin da wayarta ke ajiye tare da dāaukar wayar tana dubawa, nan taga kusan 15 missed call, 5 na Ammah sai 10 da suke na Saimah. Duk da bāacin ran da take ciki saida ta dāan murmusa kana ta zauna kan kujera tare da kai hannunta kan center table ta dāauki card dāin da Ahmad ya ajiye mata, wanda yake address na layin ne a jikin card dāin, tana gama duba address dāin ta turama Saimah tare da wani guntun sakāo. sannan ta kira number Ammah, saida ta shafe kusan 15 minutes tana waya da Ammah kana sukayi sallama, bayan ta ajiye wayar ne ta janyo laptop dāinta ta kashe tare da rufeta. Mikāewa tayi ta nufi hanyar zuwa wurin wasu kāofofi uku da ke cikin tangamemen palorn.
Cikin sanyin jiki ta murdāa handle dāin kāofar tsakiya tare da kutsa kanta a cikin dāakin, tsaye tayi tana kāarema dāakin kallo wanda yake dāauke da wani makeken gado sai closet tare da mirrow. Kai tsaye wurin closet dāin ta nufa ta budāe taga babu komai a ciki, hakan yasa ta rufe sannan ta nufi wata kāofa da ke cikin dāakin wacce nake tunanin bathroom ne, tana budāewa kuwa shi dāin ne, nan ma maida kāofar tayi ta rufe kana ta nufi hanyar fita ta koma palor. Gefen Binta da ke kuka har lokacin ta zauna tare da dāan dafa kafadāarta sannan a hankali tace;
āKi daina kuka kinjiā.
A hankali Binta ta gyadāa mata kai tana jan majina. Hannu Kuzeem ta kai ta share mata kāwallan da ke kuncinta kana tace;
āYa sunanki?ā.
āBintaā.
Ta bata amsa cikin dasasshiyar murya. Dāan murmushi Kuzeem tayi tare da fadāin,
āInyee ashe takwara ta ce, tou yanzu kinsan me?ā.
Saurin girgiza kai Binta tayi alamar aāah.
āIna so ki fadāa min menene alakāarki da waccen matar, da kuma duk wani abu da take miki, bana son ki bāoye min komai kinji kou?ā.
Ba kāaramin tsoro ne ya bayyana a idanuwan Binta ba, ganin haka ya sanya Kuzeem rikāo hannuwanta tace;
āKarki ji tsoro ki fadāamin, babu abinda zatayi miki, bazan bari ta sake dukanki ba. Idan kuma kika kāi fadāamin to kuwa zan maidake wurinta yanzun nanā.
āNi bazan koma wurinta baā.
Binta ta fadāa tana fashewa da wani sabon kukan, don babu abinda take hangowa sai yanda Mom Eshmal zatah kusa kasheta idan ta rikāata. Kuzeem na kāokāarin magana aka fara knocking kāofar palorn, ai batayi aune ba taji Binta ta zabura ta fadāo jikinta tana fadāin,
āKarki budāe kāofa Aunty, ita ce tazo ta dake niā.
āBa zan bari ta dakeki baā.
Kuzeem ta fadāa mata sannan ta janyeta daga jikinta, daidai lokacin aka sake knocking, sai kuma kira ya shigo wayar Kuzeem. Mikāewa tayi ba tare da tabi ta kan kiran da ya shigo wayarta ba, ta nufi kāofar tana fatan Allah yasa Mom Eshmal dāin ce, fuska a murtukāe ta budāe kāofar sai kawai taci karo da Saimah tsaye a bakin kāofar tana danna wayarta, jikinta sanye da wasu maroon uniform da dāan kāaramin white hijab a kanta.
āYouāre welcome Drā.
Kuzeem ta fadāa fuskarta ba yabo ba fallasa, dāagowa daga dannar waya Saimah tayi tare da bāalla mata wata uwar harara kana ta nufi hanyar shiga palorn ta bangajeta ta shige ciki, hakan yasa Kuzeem sakin murmushi kana ta bi bayanta. Kan kujera Saimah ta cilla kanta tana fadāin,
āWallahi Kuzeem kin gama da ni, ko ma ince kin cuceni, tunda safe kinsa na bar wurin aikina na tafi airport zaman jiranki, nayi wahalar banza ba can kika sauka ba, sannan naje airport dāin da kika ce kin sauka can ma ban sameki ba, na dāauki waya na kiraki har sau goma amma baki dāauka ba, billahi yau idan hawan jini ya kamani kece silaā.
******************
āMom Arif dan Allah ina so kimin alfarmar karki sanar da kowa wannan abin da ya faruā.
Inji Mom Eshmal tana kallonta fuskarta dāauke da tsantsar damuwa, kwashewa da dariya Mom Arif tayi tace;
āAmma wallahi yarinyar nan ta balaāin gamawa da ke Mom Eshmal, ta mareki baki rama ba, ta kuma kumbura miki fuska, kai Innalillahi wallahi abun tamkar a film haka na gansaā.
Hadāe rai Mom Eshmal tayi tace;
āHaba Mom Arif yanzu fa nace karki sanar da kowa don gujewa dariya, shine ke zaki sakani gaba kina min dariyar?, tou bari kiga abinda zanyi ma yarinyar nan wallahi saita raina kanta, kuma yau idan Binta ta dawo gidan nan billahil azim saina kusa halakata don sai na sumar da itaā.
Zaro idanuwa Mom Arif tayi tace;
āAāah Mom Eshmal ki kāyale yarinyar nan haka, haba ai ta daku a hannunki wallahi karki je ki karairaya āyar mutaneā.
āMtsswww ke kika san wannan, nidai yanzu bari kiji kalar cin uwar da na shirya ma wannan āyar iskar, wallahi na rantse miki da Allah ba zata sake kwashe kwana uku ba a gidan nan, zata hadāa komatsanta ta kāara gabaā.
Tana gama fadāin haka ta radāa ma Mom Arif wata magana a kunnenta, kusan a tare suka kwashe da dariya tare da tabāa hannuwa, sannan Mom Arif ta mikāe tace;
āYanzu fita zanyi Kāawata, zan tabāoki a waya mu kāarasa zancen ko kuma idan na dawo in shigo anjimaā.
**************
Sai yanzu su Miswar suka gama gyaran motar da suke, wurin bencin da suke zama suka zauna, sai kuma Hisham ya mikāe yace;
āAbokina dan Allah idan Baba ya tambayeka ina na tafi kace masa nayi shagon askiā.
Da mamaki Miswar ya kallesa yace;
āTou amma dai ka san zaka kwance tayoyin waccen motar kou?ā.
Ya kāarashe maganar yana nuna mishi wata babbar mota da ke ajiye cikin garejin, dāan tsaki Hisham yayi yace;
āIdan na dawo zan cire, bazan dadāe baā.
Miswar bai sake cemasa komai ba ya maida hankalinsa akan wayarsa, Hisham kuwa wurin wani tsohon Scooter ya nufa tare da hawa ya bar wurin.
************
Kuzeem na dariya tace;
āAyya Dr kiyi hakāuri, akasi aka samuā.
Saimah da ta budāe baki da niyyar magana idanuwanta suka sauka kan Binta da ta rakubāe kan kujera tana kallonsu.
#Anup💋ā¶ā¶ ā·ā°