YAR MAHAUKACIYA CHAPTER A BY SAJIDA

YAR MAHAUKACIYA CHAPTER A BY SAJIDA

Www.bankinhausanovels.com.ng 

                 Labari

Kakarin amai take tana jan nunfashinta , ita kuwa ta daneta ta matse mata baki ala Dole sai ta dura mata danyen misan da ta tsinto a cikin bola , MAhaukaciya ce na hango ta dane wata yar budurwa tana kokarin dura mata mushe a bakinta ita kuwa ta gumtse bakin taki budewa , tana tsaka da kokowa da ita sai naga ta dakata , ta ja da baya kuma sai naga ta saka ihu ta shiga shure shure tana dafa cikinta da alama nakuda ce ta taso mata , yarinyar nan naga ta taso da gudu tana ta bibiyar wanan mahaukaciyar tana fadin , sanu haihuwar ce ?

Ita dai Mahaukaciya ba bakin magana banda juya kai ba abinda take hakan yasa yarinyarnan fita da gudu daga cikin tsumakoran da suka saka suka dadaure sukayi dan dakinsu inda zapi , sanyi , damana ke riskarsu , tana FIta tayi ta gudu tana haki da kyar ta samu ta fito cikin layin domin a can cikin bola ne suke can karshen anguwa , tana fitowa ta tsaya tana waige waige ta rasa ina zata dosa domin neman taimako , wani gida ta hango tamkar kango ta nufa domin wani lokacin sunkan sakata kai shara gidansu wato bola , su bata dan kanzo da ruwan daurayarsu na kayan wankin su wani lokacin har barinta suke ta debi na rijiya taje su sha dadinsu ita da Mahaukaciya ,

Tana shiga ta rafka salama ta ja gefe ta rakube , wasu yara naga sun fito su kansu daudar jikinsu ta ishe su suna ta wasa suna ganin wanan yar budurwar saï naji sun fara wake suna fadin *Ke mai suna Yar Mahaukaciya yaya haukan ki Yar Mahaukaciya , shin ina babarki Mahaukaciya tana ta zuba haukan? Yar mahaukaciya* ita kuwa sai murmushi take aika musu bata ce komai ba , har suka gama daukar maganar su suka tafi abinsu , ta kusan rabin awa a tsaye sai ga uwar gidan ta fito ta sha damara da niyar yin surfe tana ganin Yar mahaukaciya tayi hamdallah ta yafitota

Yar mahaukaciya ta matsa da Sauri ta zuguna a gabanta ,

Larai ta ce ” idan abinci kike so zan baki da ruwan rijiya ke harma da zanin daurawata aman sai kin surfe min wanan dawar gaba dayanta

Yar mahaukaciya ta juya inda aka nuna mata dawa ta hadiyi wani yawu mai daci ta ce ” To uwar gida ran gida zan surfa yanzu kuwa

Larai ta washe hakora ta kama mata buhun dawar suka tsayar da tirmin da tabaryar ta gyara yagegen zanin dake daure a jikinta ta shiga daka ba kakautawa , tun da rana ba ita ta gama ba sai yama lilis , Larai ta aiketa tayo mata cefane taje har cikin kasuwa a kafarta ita dai fama take ta gama ta koma wajen Mahaukaciya tasan yanzu ta dena iface ifacen domin takanyi hakan ,

Ba ita ta gama bautar gidan yawa ba sai da wajen shigar magariba ,

Larai ta harhado mata abinci harda na shekaran jiya ya gama yin tsami ta turo mata harda kanzo ta sauye mata shi a cikin wani bokici da ya gama yin tsatsa sanan ta ce ta jawo guga biyu ta isa gudun kar ruwan rijiyar ya kare ta je ta jawo guga biyun ta sauye a tsohuwar jarkarta ta dauka gaba daya tana tafe tana Sauri yara kuwa sai binta suke suna fadin yar Mahaukaciya ita kuwa bata kulasu famarta ta isa bola

Tana zuwa ta hango dan karton da ta kara ta rufe an janye shi ta kara Sauri ta shige cikin kewayen nasu , jini jini ta fara gani a dashe a ko’ina ta yaye rufar da tayi da ledodi tana yayewa gabanta na faduwa don abinda idanuwanta suka gani bata san sanda ta saki bokicin abincin da ta wuni tana aiki dalilinsa ya zube a nan ba ta dauki hanunta ta dora saman kanta saman bakar ledar da tayi dan kwali da ita ta kurma ihu domin jariri ta gani konce cikin jini yashe a nan gashi ba Mahaukaciya ba alamarta da gudu ta karasa ta shiga dage dage da alama neman Mahaukaciyar take

Shin ina mahaukaciya? Yaron nan wa ya haife shi? Su waye Mahaukaciya da Yar Mahaukaciya? Taku har kulun Sajida

*’YAR 👧🏻*    

         *MAHAUKACIYA👹*

*_Na SAJIDA_*

*♻EXCLUSIVE WRITER’S FORUM*

                    2

Dadaga tarin tarikicen su take tana ihun kuka tana Kiran Mahaukaciyata ina kike ? Da kyar ta dena dage dagen ta matso kusa da jaririn nan ta tsura masa ido yaron sai kuka yake tun karfinsa wani tausayinsa ya kama ta ta Mika hanu a nitse ta dauko shi ta jawo ruwan nan ta wanke masa fuskarsa ta dorashi a bayanta ta dauki zanin nan da Larai ta bata ta goya shi ta fito ta fantsama neman Mahaukaciya ,

    Wai shin wacece Yar mahaukaciya?

Yar mahaukaciya ita kanta bata san sunanta ba bata san na mahaifiyarta ba , ita dai ta fara wayo ta ganta a gidansu bola kuma taji yara na kiranta da *Yar Mahaukaciya* ana kiran mahaifiyarta da *Mahaukaciya* duk da irin tarin daudar da suke ciki da cin abinci marar kyau da kwana a waje marar kyau idan ka kalesu zaka gane cewar fararen mutane ne rayuwa ce kawai ta mayar da su masu duhu , Yar Mahaukaciya ba arabi bale boko , bata da kowa sai Mahaukaciya , tarbiyarta tarbiyar Allah ce domin tanada nutsuwa tana masifar son Mahaifiyarta Mahaukaciya , bata son komai ya rabeta kulun cikin shan dukanta take domin idan ta kawo mata abu mushe taki ci sai kawai ta daneta wataran ta dura mata wataran kuwa ta samu ta gudu ,

Abincinsu gida gida take bi tayi aikace aikacen ragwayen mata ta samu abinda ta samu ta kai musu su ci abinsu kuma ruwa na kwata ne kadai basa sha domin tana yin iya kokarinta don ganin mahaukaciya ta kwana da ruwa a dakin , tun tana karama suke cikin bolar nan wataran ta wayi gari taga Mahaukaciya na dauke da ciki bata san KO na waye ba hasalima sai da taji yara na fada ta gane inda suka dosa tayi mamakin inda mahaukaciya ta samu cikin nan harma tayi tunanin KO hakan kawai ake wayar gari da shi , ita dai bata da mai bata amsa hakan yasa ta yi shiru abinta take lalaba mahaifiyarta cikin tsananin so da kauna iya labarin tarihin mahaukaciya Kenan

Tafe take da dan yaro a bayanta tana girgizashi tana fadin kayi shiru dan Mahaukaciya muje mû nemo Mahaukaciyarmu mu kawota gidan mu ta goya sabon dan mu , kayi shiru Dan mahaukaciyana tana ta yawo gaba daya ta jigata sai jiri take na tsananin yunwa ga Dan mahaukaciya sai dai ta bashi ruwa yara kuwa banda tsokanarta ba abinda suke duk inda ta zaga sai an biyota ana fadin lah Yar mahaukaciya ta sato beby har ta ISO wajen wani police zata huce taji yace ” ke yar mahaukaciya dan wa kika sato haka?

Tayi narai narai gabanta na mugun faduwa ta ce ” Mahaukaciya ta haife shi kuma ta gudu

Ya zabga mata mari har sai da ta dan fara sakin fitsari ya damketa sai police station , suna zuwa ya Nuna cewar ta sato yaro ne suka shiga tambayarta amsar dai data ce Dan Mahaukaciya ne hakan yasa suka kunce yaron suka shiga nadarta Dole sai ta fadi inda ta sato yaro banda kuka ba abinda take suna tsaka da dukanta sai ga tsohon daraja shima police din
ne aman ya fisu mukami , yana zuwa ya tambayi mai tayi

Ilyasu yayi masa bayanin ai ga abinda aka kamata da shi

Tsohon daraja ya ce ” tabas kwanakin baya naga Mahaukaciya da ciki a jikinta kuma yau na ganta wajen kasuwa ba cikin sanan saninta duk jini ne tabas wanan yaro *Dan Mahaukaciya ne* dan haka ku saki baiwar Allahn nan tayi tafiyarta

Haka suka saketa ba dan ransu ya so ba domin sun so ta kwana a nan suyi anfani da ita ,sai dai kash tsoho ya kawo cikas

Da kyar take takawa domin ta daku ta dauko dan Mahaukaciyar tayi wajen kasuwar don neman Mahaukaciya tana tafe tana kuka yaron na kuka tayi kasuwa neman duniyarnan ba Wanda bata yi ba ta juyo ta nufi wani layi tana tafe ‘tana kugin sunan Mahaukaciya har ta isa wata makaranta ta zauna tayi tagumi almajirai sai shigi da fici suke suna ta sha’aninsu har akayi sallar isha’i bayan an gama sallah Malan ya fito daga masalaci ya hangi yatinyar nan zaune tana ta jijiga yaro a hanunta kawai sai wani tausayinta ya kama shi ya matso yayi mata salama

Ta dago jajayan idanuwanta masy shige da na misa ta sauke su saman fuskar wanan Malan mai cike da Haiba ta amsa salamarsa

Ya ce ” Baiwar Allah lafiya kike zaune a nan? Ga yaronki da alama yunwa yake ji to ki bashi ya sha mana

Yar Mahaulaciya ta kale shi tace ” Malan ai ruwan ya kare babu kuma abincinsa

Malan sai yaji tausayinta ya ce tashi mû shiga gidana a tatsa miki nonon akuya tayi sabuwar haihuwa sai ki bashi ya sha , ta mike har tana harde kafafuwanta ta bi bayansa suka shiga gidansa

Matansa biyu dayar mai kirkin gaske DAyar kuwa tadi dafi zafi hakan yasa ya nufi dakin saratu ya fada mata ta fito ta taimaki yarinyar nan da danta ,

Saratu ta fito suka gaisa da yar Mahaukaciya tace miko yaron a bashi nonon akuya kema kije ga ruwan dumi kiyi wanka domin da alama sabuwar haihuwace

Yar Mahaukaciya ta ce ” nayi wanka? Da gaske?

Saratu ta ce ” eh man ga bokici ki dauka ki zuba ruwan sai ki dan sirka da na rijiyar ki je kiyi wanka shima bara nayi masa sai a bashi nonon

Sai washe hakora take domin itadai da wayonta har ta manta rabonta da tayi wanka ta jawo isashen ruwa ta kai bayi ta aje saratu ta bata soda ta dauko mata jacen kayanta ta mika mata har tana fadin ki wanka ruwan zafin da kyau fa saboda jego ita dai har lumshe ido take tana zuba ruwa a jikinta kafin ta fito Saratu ta wanke dan mahaukaciya ta bashi nonon akuya ya sha sosai har ya samu wani ni’imtacen baci mai dadi

Wanka take tun karfinta wani bakin ruwa na zuba daga jikinta yana bin magudadar ruwan nan da nan sai gâta ta fara haske tamtar mai , ta cire ledar dake rufe a kanta ta dauki sodar nan ta ringa kwabata a cikin gashin kanta nan da nan naga wata irin dauda mai yauki tana zuba daga kanta ta kama kwarara ruwa gaba dayanta ta darwaye jikinta dagowar da zata yi na zaro ido domin gashin kanta ba baki bane kalar 🙍🏼 masara ne yelow gaba dayansa aman yalow mai haske ga shegen tsayi da gareshi na tambayi kaina wai Yar Mahaukaciya yar hausawa ce kuwa? Ta dauko ledarta ta daure kanta ta saka kayan da Saratu ta bata sai ajiyar zuciya take domin ta rabu da kashi 80 na daudar dake jikinta tana fitowa gaban Saratu ya fadi , duk irin kirkin saratu matsalarta daya ce kishi Allah yayi mata kishin mijinta tamkar mai , hakan yasa da Sauri ta daukowa Yar Mahaukaciya yan tsumakoron da ta dadauko mata ta bata ta hada mata da tuwon lamshi mai yawa ta ce ” to yar uwa rufe gidan zamu yi kinsan Malan ba a nan yake kwana ba hakan yasa Mike rufe gida da wuri

Yar Mahaukaciya ta kama godiya harda tsugunawa saratu ta ce ba komai ta dora mata dan Mahaukaciya ta goya ta dauki sauran kayan tayi gaba tana yiwa Allah godiya taci GABA da Neman Mahaukaciya

                😌

.[8/11, 06:27] ‪+234 816 681 0364‬: *’YAR 👧🏻*    

         *MAHAUKACIYA👹*

*_Na SAJIDA_*

                    3

Tafiya take har karfe biyu na dare yayi mata ta gaji tamkar ta kife idanuwanta sai zugi suke yi mata na baci dan mahaukaciya kuwa sai bacinsa yake shekawa hankalinsa konce domin ya sha nonon akuyar nan ya koshi , wata bishiya ta hango a hankali ta isa ta samu ta rakube ta shinfide dan Mahaukaciya tayi konce a gefensa ta shiga tunanin duniya tana tunani tana share hawayenta ta mike da ruwan na yar jarkar ta zauna ta daura wata kalar alwalah gaba daya ba daidai bace ta juya Gabas tayi sallah Wace bata karanta komai sai dai tayi ta musmus da baki shima wajen Larai ta jiyo idan tana sallah tamkar koton kurciya nan da nan ta gama tana salamcewa ta konta kusa da dan kaninta tana adu’ar Allah ya jikanta ya ya fito mata da Mahaukaciya ,

Haka rayuwa tayi ta tafiyarwa yar mahaukaciya tun bata iya raino ba har ta kware ta iya goya yaron da zuwa wanki , shara a bata nera ashirin nera goma ta je ta siyowa Dan Mahaukaciya koko ta zo ta bashi ya sha , idan ya koshi itama ta samu ta sha , a tanzu yara sun koma tsokanar Yar Mahaukaciya da Dan shege ita dai ta kanta take tana nema musu dan abunda zasu saka a bakarsu har yanzu tana zuba ido ne taga ta inda Mahaukaciya zata bilo duk fitar da zata yi kuwa sai ta nemi Mahaukaciya har yanzu bata fida rai da ita ba ,

Konce take ta samu da kyar barci ya dauke Dan Mahaukaciya ita kuwa sai hama take ga wani uban sauro na damunta inuwa inuwar mutun ta fara gani ta mike zumbur ta fara kalon kofar wani katon mutun ne bakikirin mai murdaden jiki ya shigo kafin ta ankara tayi wani abu har ya watsa mata wata hoda a fuskarta ya kwasheta ya sakata cikin wata bakar mota ya dauko jaririn shima ya saka shi cikin motar wa’inda suke cikin motar suka figi motar ,

Tafiya suke tun karfinsu sai da sukayi tafiyar awa hudu sai gasu a garin jos suka karkata suka nufi wani tankamemen gida mai shegen kyau suna isa aka wangale musu porte din suka dana kai ciki , wata hanya naga sun dauka a cikin gidan sun nufi wani gate din aka kuma bude musu , suna isa ya diro ya bude ya dauko Yar Mahaukaciya a kafadarsa ya nufi wani daki da ita ya dauko yaron shima ya Mika shi wajen wata tsohuwa naga ta nufi ciki da shi ,

Dishi dishi ta fara gani sanan a gankali ta buda idanuwanta , wajen da ta ganta konce saman wani makeken gado Wanda tunda uwarta ta haifeta bata taba sanin akoyshi a nan cikin duniya ba ta Mike tsaye da Sauri ta fara dubedube can ta koma ta zauna ta tare fuskarta da hanayenta ta shiga tinani , watarana taji kishiyoyin Larai suna fadin idan aka mutu akoy wuta akoy aljana , ance a aljanar akoy manyan gadaje da manyan TV da komai da komai a wutar kuwa wutace kawai sunce ai idan Larai ta mutu tace ita aljanar zata zaba su kuwa a kaisu wuta dan sun aure mata miji ( to kaji Larai shawara Kenan za’ayi miki?) , ta kuma daga kanta ta hango babar TV din ta kali gadon da take zaune saman kansa a fili ta furta ” Au Kenan mutuwa nayi aka kawoni aljana? To ina dan Mahaukaciya da Mahaukaciya ? Ku zo ku ga aljana ku zo muyi zaman mû a nan aljanar tafi duniyar dadi , tana tsaka da maganarta aka bude dakin wata mata ce ta  shigo rusheshiyarta ta ja ta tsaya da Sauri yar Mahaukaciya ta mike tana soshe soshe tana kalonta

Matar nan ta ce ” ke yarinya ki tashi nayi miki wanka na shirya ki na kaiki wajen hajiya

Yar Mahaukaciya ta ce” baiwar Allah nan ina ne? Duniya ce KO lahira?

Matar nan ta ce ” ke karki kawo min maganar banza ta kama Yar Mahaukaciya kiiii sai cikin bayi tana ji tana gani matar nan ta tube ta tamkar wata beby ta zirata cikin bahon wanka ta kama dirzarta  da wani soso mai shegen zafi , tun tana nonokewa
har ta hakura matar nan dan rashin imani ta dauko wani tirare da detol ta zuba a ruwan har kanta ta kuma darje jikin Yar Mahaukaciya jikin har wani sulbi yake na wahala ruwan ya kuwa shigar mata ido ta rufe ruf tayi ta murzawa aman matar nan bata damu ba , tana gamawa ta jawo tawul ta nade jikin yar Mahaukaciya ta jawota tsakar dakin nan Yar mahaukaciya ji take tamkar sabuwa har wata iska ke daukan ta tayi fayau da ita farinta yayi mugun fitowa ,

Matar nan mai suna Mesi wato ba musulma bace ta dauko kayan bushe gashi da wani mahaukacin kaya doguwar riga mai daukan hankali ta jawo hanun Yar Mahaukaciya ta zaunar da ita ta shiga bushe mata gashin kanta ta dauko man shafawa ta shafa mata nan da nan kan nan mai kalar blonde ya fara sheki ta saka ribom ta daure aman har gadon bayanta ya zubo , ta mika mata sabon pant da breziya ta saka gaba daya aikin nan da take yi mata bata yi mata magana itama tayi shiru tana kikifta manyan idanuwanta ta rasa wanan wani irin Abu ne? Wanan wata irin masifa ce? Meye za’ayi mata ne? Ina za’a kaita? Ina Dan Mahaukaciya? Nan din ina ne?

     Ni ma ban sani ba yar mahaukaciya sai dai mu bisu mu gani

[8/11, 06:28] ‪+234 816 681 0364‬: *’YAR 👧🏻*    

         *MAHAUKACIYA👹*

*_Na SAJIDA_*

                    4

Tana tsaka da sakar zuci taji Mesi cikin wata uwar muryarta tamkar namiji tace ” ke tashi mu tapi

Cikin Sauri Yar Mahaukaciya ta mike ta bi bayan Mesi suka ratsa wani falo baba , suna ratsa na biyu ta hango wata tsohuwa tana ta jijiga yaro a hanunta ,

Tsohuwar ta matso ta mika mata yaron ta ce ” bashi ya sha

Yar Mahaukaciya tayi shiru ta amshi Dan Mahaukaciya ta rungume shi yana ta bacinsa kawai sai taki cewa komai

Mesi ta ce ” yaronta ne kuma mahaulaciyar ce dan Haka kawai mû kaisu wajen Hajiya

Tsohuwa ta washe hakoranta jajaye ta ce ” kai aman hauka shi kadai yake wanan yarinyar mai kyau haka ya kamata? ( tsohuwa shin haukan ba kadarar Allah bane? Akoy Wanda ya isa ya kaucewa kadara ne? )

Messi ta ce ” baki ma ga gashin kanta ba wani mai shegen kyau sai tambayar masifa ke malama mu je KO na ci ubanki a nan

Yar Mahaukaciya tayi gaba da gudugudu suna biye a bayanta sunyi tafiya mai nisa sai gasu sun bilo dakin wata mata tana zaune bakin gadonta ta hakimce Matar zatayi shekara arba’in da biyar a duniya ,

Suna shigowa su duka suka tsuguna suna gaishe da ita banda yar Mahaukaciya

Hajiya Falmata ta ce ” ya zaku kwaso min yarinya karama haka nayi yaya da ita?

Mesi ta ce ” ai hajiya wanan ta dade cikin hauka yanzu haka da kokowa da komai muka samu muka fito da ita kinga sai da na sharara mata mari hudu sanan ta dena buge buge kuma kinga yaron nan danta ne ita ta haife shi bashida uba shege ne kuma ita din ma shegiyar

Hajiya Falmata tayi shiru ta ce to ku zaunar da ita

Suka zaunar da Yar Mahaukaciya ita dai binsu take da kalo bata ce komai ba , sai da suka zaunar da ita suka fice

Hajiya falmata ta taso ta zauna nesa da yar Mahaukaciya ta kura mata ido ta ce ” ba laifi kina da kyanki , kuma kinfi wancen Wanda nayi da ita kuma na kasheta da alama ke zaki fita iyawa kuma aikina zai fi ci sosai

Gaban yar Mahaukaciya banda faduwa ba abinda yake tayi shiru tana ta kifta ido , ita dai har yanzu bata gane inda Hajiya Falmata ta dosa ba , wani aiki ? Mai zata yi da ita? Tana tsaka da tinani taga hajiya ta Mike tana famar tube kayan jikinta Yar Mahaukaciya ta sada kanta kasa taki dagowa , duk da mahaukaciya ta reneta bata ganin tsiraicin Babar mace haka ,  gabanta sai faduwa yake

Hajiya falmata ta mika hanu ta dauke dan Mahaukaciya ta ja hanun Yar mahaukaciya ta kontar da ita saman bed din dakin ta yar mahaukaciya tayi zumbur ta Mike tana kalon kasa

Hajiya falmata ta ce ‘ ke dan ubanki konta min ke badan boka yace na konta da mahaulaciya mai da ai da baki isa na konta dake ba sai manyan hajiyoyi to dan dai kawai ina gudun kar asirin da nayi shekara goma sha hudu da suka fice ne ya karye dan uwarki konta min KO na saka a daure min ke

Yar Mahaukaciya ta zaro ido ta ce ” Ni fa ba dana bane dan Mahaukaciya ne

Hajiya Falmata ta zabura ta ce ” kutumar ubancan to wacece mahaukaciyar ke kuwa wacece ?

Yar Mahaukaciya ta ce ” Ni Yar Mahaukaciya ce Kuma wanan ma dan Mahaukaciya ne Mahaukaciya ta tafi yawo bata dawo ba

Hajiya falmata ta zaburo ta ce ” ai kuwa yau sai na kasheki tsinaniya shine kika sakani a gaba har na tube miki ?  Yau sai na galabaitaki sanan nayi anfani da ke kuma na kashe ki tayo kan Yar Mahaukaciya ta shaketa

    Wayo yar Mahaukaciya

🇳🇪 BElles écrivaines du Niger

*’YAR 👧🏻*    

         *MAHAUKACIYA👹*

*_Na SAJIDA_*

                    5

Wayo Kano ba wuta sai ingi 🙆🙆🙆🙆🙆🙆

Famar sumewa take domin Hajiya Falmata ta mugun shake mata wuya ta gaza tabuka komai domin karfin ba daya ba , tana kokarin ganin bayan Yar Mahaukaciya wayarta dake aje a gefen bed din ta shiga ringin kuma karar wayar wakar da ta sakawa mijinta ne hakan yasa cikin Sauri ta cikata ta dauki wayar

Daga dayan bangaren Elhaj biloniya ya ce ” Hajiya na fasa tafiyar gani na dawo bangarenki bakya nan shin kina ina ne?

Hajiya Falmata ta ce ” what? Kana gida?

Elhaj biloniya ya ce” eh lafiya nake jin muryar taki a tsaitsaye?

Hajiya Falmata ta ce ” no ba komai dear gani nan zuwa yanzu yanzu

Ta datse Kiran ta danawa Mesi kira tana kokarin mayar da kayanta , Mesi ta shigo da gudu tana amsawa

Hajiya Falmata ta ce ” ke sakaran banza da wofi zo ki san yanda zaki fitar min da wanan dabar domin honorable ya dawo gidan nan idan kika yarda aka kama ki da ita ke zaki kwana a ciki , bata samu damar fada mata cewar yarinyar ba mahaukaciya bace hakan yasa Mesi bata tsaya tambayar a kasheta KO kar a kasheta ba kawai ta jata ta bi ta hanyar baya da ita ta tura ta ta wata karamar kofa ta ingiza keyarta sai waje ita kuma ta juyo ta koma cikin gidan tana ta tsinewa halayar Falmata ta samu babar yarinya haka aman tana aikin mita ,

Yar Mahaukaciya da take rungume da Dan Mahaukaciya tana zabga Sauri bata ma san ina zata dosa ba gashi kafarta KO takalmi babu tana godewa Allah da ya kubutar da su daga hanun wa’inan bayahudan

Tafiya take zabgawa tana haki ta rasa ina zata nufa hankalinta duk a tashe ta rasa mai zata yi , ina zasu kwana ga garin bata san shi ba tafe take tana  tunani idanuwanta sai zubar da hawaye suke , karar taka birki taji kiiiiiiiii aman ina duk da haka sai da ya buge kafafuwanta ta fadi dabas a kasa aman Dan Mahaukaciya na rike a hanunta , mutumin da ya kadeta ya fito daga cikin motarsa dan matsakaici ne , bashida kiba aman yanada dogon hanci yana cikin jalabiya fara da alama ba nesa zai je ba

Ya ce ” Malama lafiya kike tafiya bakya kalon gabanki?

Yar Mahaukaciya ta dago kant
a ta sauke idanuwanta a saman fuskarsa bata ce komai ba ta mike taci gaba da tafiya , yayi sororo yana kalonta kawai sai yaji a ransa wanan yarinyar da danta duk inda zata tafi tana cikin damuwa ne gashi kuma ya bigeta da mota kuma bata ce masa komai ba , cikin Sauri ya tayar da motar ya bi bayanta

A hankali yake binta da motarsa yana fadin baiwar Allah lafiya? Mai yake damun ki? Ina zaki tafi? Ina takalman ki? Aman shiru bata bashi amsa ba hakan yasa ya ce to ki shigo na kaiki inda zaki tafi mana?

Tana jin haka ta waigo tana kalonsa ta ce ” zaka kaini?

Wanan bawon Allah mai suna Idrissa ya ce ” eh ki shigo na kaiki inda zaki je

Ya Buda mata motar ta shiga tana jijiga Dan Mahaukaciya , shi kuwa ya koma ya shiga tuki ,

Tafiya suke ba mai yiwa dan uwansa magana shi jira yake ta fada masa ga kwanar da zai sha KO ga unguwar da zai kaita aman tayi masa shiru hakan yasa ya ce” baiwar Allah ina zamu nufa ne?

Cikin sarkakiyar murya Yar Magaukaciya ta ce ” Bawon Allah ina ne nan?

Idrisse ya ce ” Jos ne baki san sunan garin ba? Mai yake damunki ne?

Yar Mahaukaciya maimakun ta bashi amsa sai ta jefe shi da wata tambayar ta ce ” menene jos? Sunan anguwa ne?

Idrisse yayi tsai yanzu fa ya dan fara tsorata KO dai ya kwaso ruwan dafa kansa ne? Ya nisa ya ce ” Dan Allah ya sunan ki?

Yar Mahaukaciya tayi tsam ta ce ” ana kirana da sunan *YAR MAHAUKACIYA*

Idrisse ya taka birki ya juyo yana kalonta rigar jikinta duk ta dame mata jiki tamkar karuwa (  yar bariki ) gashi batada dan kwali gashin kanta tamkar ba na bahaushiya ba kai fatar jikinta kanta tamkar na mai Jan kune nasara sai dai kwayar idanuwanta bakake ne sidik shine banbancinta da nasaru ,

Ya ce ” ban gane ana kiranki da Yar Mahaukaciya ba , meye ainahin sunan ki na kirki? Wanda aka rada miki? Wanda dadynki ND momynki ke kiranki da shi?

A ranta tana mamakin yaransa meye dadynki ND momynki? Meye sunan da za’a kirayeta da shi wanda ya dara Yar Mahaukaciya? Ta juyo suka hada ido hudu da shi ta ce ” haka ne suna na , haka suke kirana da shi kuma wanan sunan sa Dan mahaukaciya

Idriss ya girgiza kai a ransa ya ce bazan iya barin wanan haka ba da alama ta gaji shi yasa take sakin zance ba tsari hakan yasa ya ce ” zan kaiki gidan abokina yana da ma’aikata mata ki kwana a can gobe da safe idan Allah ya tashe mu lafiya zan zo muyi maganar abinda ke damun ki da kuma sunan ki aman ki sani bazan yarda cewar sunan ki Yar Mahaukaciya ba because ke din da alamar nutsuwa a tatare da ke so ki yarda da ni bazan cutar da ke tomorrow sai na kaiki gidan ku tunda yanzu kin gaji

Ita dai kalon bakinsa take yanda yake magana ba tun karfi ba daman akoy maza masu magana a hankali? Sai kuma da taji yace tanada wani suna bayan yar Mahaulaciya tana son sanin sunan , sai kuma da yace zai mayar da ita gidansu wato bola hakan yasa hankalinta ya konta harma ta gyara konciyarta tana kalon titi ya tayar da motar ya harbata kan titi ,

Sun dan yi tafiya mai dan nisa suka isa wani gate shima tankamemen sa lokacin Yar Mahaukaciya tayi baci shi dai haka kawai yaji matar nan yana tausaya mata ya dana horm aka wangale masa gate din yana shiga daidai Umar abokinsa ya fito da computer sa zai je jardin ya huta yayi tsai yana kalon Idrisse , Idrisse yayi parking da motar har lokacin bata farka ba , ya fito ya nufi Umar yana isa suka tafa

Umar ya ce ” kai mutumina wanan bebyn fa?

Idrisse ya ce ” kai karka yi min zakarancin naka wanan wata baiwar Allah ce na hadu da ita na kawota nan tunda kana da masu aiki mata ta kwana a wajen su tomorrow sai na kaita gidan su yeah?

Umar ya ce ” wayo baiwar Allahn harda danku kai na tayaku murna abokina Allah ya raya bara na matsa na ga bebyn tamu

Idrisse ya girgiza kai suka matsa tare shi da Umar , Umar ya Mika hanunsa a hankali yana konkwasa gilashin motar

Yar Mahaukaciya dake barcinta ta Buda idanuwanta a hankali ta dago kanta suka yi ido hudu da Umar gabansa ya yanke ya fadi yayi Saurin ja da baya nan da nan jikinsa yayi wata muguwar mutuwa ya saki computer hanun NASA ,   ,,,,,,,,,     ,,,,,,,,,,

To jama’a mai ya baiwa Umar tsoro? I don’t know 🤷🏻‍♀🤷🏻‍♀🤷🏻‍♀🤷🏻‍♀🤷🏻‍♀🤷🏻‍♀🤷🏻‍♀🤷🏻‍♀🤷🏻‍♀🤷🏻‍♀🤷🏻‍♀🤷🏻‍♀

I’m sorry ba wuta ba nepa 😭😭😭😭😭😭

  *’YAR 👧🏻*    

         *MAHAUKACIYA👹*

*_Na SAJIDA_*

                    6

Na sadaukar da wanan shapin gareki masoyiyar asali AMINA AMINU ina godiya da adu’o’in ki

Umar ya saki computer hanunsa ji yayi duka gabobin jikinsa sunyi wata irin mutuwa

Idrisse da Sauri ya matso ya dafa kafadar Umar ya ce ” yayadai abokina lafiya mai ya faru? KO ka Santa ne?

Umar ya ce ” abokina yarinyar nan na taba ganinta a turkey naje wani aiki na ganta ana tuka ta ita da kanta aman wanan tafi wacen fari kuma gashin wacen baki ne yarinyar nan aljana ce domin da nayi mata magana gurds dinta sai da suka kusan kashe ni , gaskiya bazan sauketa a gidana ba 😡

Idriss ya zuba masa ido yana sauraron sa ya ce ” to aman mai zai kawo mutumin dake turkey saman titin jos ba KO takalmi? Kuma tafiyar nan taka duka duka yaushe ne ai bai kai har ta haihu ba KO? KO da tsohon ciki ka BArTA ne?

Umar ya daga kafada irin bai shafe shi ba ya ce ” ni dai banga ciki a jikinta ba may be ta ajiye shi a gida ne  kafin ta fito na fada maka wly aljana ce ka rabu da ita tun wuri ,

Idris ya juya yana kalon Yar MaHaukaciya Wace itama su take kalo tana son fahimtar yaren su , abinda suke fada , Idris ya nufo motar jikinsa ba kwari ya Bude mazaunin direba ya tayar da motar ya kama hanyar fita yana tafe yana sakar zuci shi dai Allah baiyi masa tsoro ba kuma ya sani idan har Aljana ce wanan tofa zata bace ne koda tsakar dare ne hakan yasa yayi imani da Allah ya dauki hanyar gidansa da ita , a hanya ya tsaya wani butique ya siyo mata hijabai uku da dogayen riguna ya fito ya sayi kaji ya shigo motar ta koma barcinta hankalinta konce ya tada motar , sai da yayi tafiyar minti ashirin ya isa gidansa mai gadi ya bude masa ya zagaya ya shiga ta baya da ita gudun kar a kai tsegumin ya zo da mace harda yaro gidansa momynsa kuwa mai zafi ce

Bayan ya gama daidaita tsayuwar motar ya rasa taya zai tayar da ita yayi tsai yana kalon fuskarta verry inoscente wanan yasan bazata fice wata shekara 15 a duniya ba , gashin idanuwanta ya tsurawa ido sai yaji sha’awar tabawa yaji KO nata ne domin bakinsu yayi over ga kuma tsayi ga sheki ya Mika hanu a hankali zai taba wani abu yace masa kai Idris matar aurece fa hakan yasa da Sauri ya janye hanunsa ya dan bubuga kujerar da take konce

Firgigit ta farka ta tsura masa idanuwan nan nata masu matukar firgitar da mutun , ya kawar da kansa ya ce ” ki fito mu tafi


Ya bude motar ya fita ita dai da kalo take binsa ta rasa ina ne wajen bude motar ganin taki fitowa yasa ya bude mata ya kwashi kayan ta fito ta tura motar irin yanda taga yayi ta bi bayansa cikin gidan suna shiga ya Mika mata leda baka

Ya ce ” ga abincin ki da kuma hijabi ga daki can ki kwana ciki da safe idan Allah ya kaimu zamuyi magana kinji?

Yar Mahaukaciya ta gyada kanta tayi hanyar dakin da ya nuna mata , tana turawa taga dakin masha Allah ya sha kwaliya tayi tsai tana tunanin to wai daman haka suke gidajensu ko’ina ka shiga da shegen kyau haka? Ta samu nan kasa saman kafet din ta shinfide Dan Mahaukaciya ta rungume shi sai baci , KO abincin bata ci ba , baci yayi awon gaba da ita ( baiwar Allah )

Da sasafe taji ana dukan kofar tata ta farka ba shiri taje ta bude kofar tana budewa yayi saurin sunkuyar da kansa domin rigar ta jikinta ta dan yaye daga sama ya juya ya ce ” Baba gatanan zan tafi kwana uku zanyi kinsan halin oga idan yana gari dan Allah ki kular min da lamarinta idan na dawo zan mayar da ita gidan su

Baba ta ce ” to yaron kirki Allah yasa a dace Allah ya bada sa’a ,

Yar Mahaukaciya dai kalonsu take bata ce komai ba , ya dan kalota ya ce ” na tafi ogana ne ya dawo wajen aiki kuma yanada bukatana wajen aiki duk da cikin gari ne ya saba ya rike mu har sati , so kiyi zaman ki idan bukatar wani abin ya tashi ayi kirana Insha Allah zan samu yanda zanyi na fito

Yar Mahaukaciya ta ce ” zaka kaini bolar?

Yayi tsai yana kalonta can yace” sunan unguwarku bola?

Yar Mahaukaciya ta ce ” aa gidan mu ne can bolar

Idris yayi shiru a ransa ya ce ” KO dai ta haukace ne yarinyar nan ?

Yar Mahaukaciya ta ce ” kuma kaga ina neman Mahaukaciyata ban ganta ba

Har zaiyi magana wayarsa ta hau ringin da Sauri ya daga yana furta ai na shigoma sir , ya kashe da Sauri ya juya yana fadin eh ki zauna idan na dawo zan kaiki bolar kinji?

Ta gyada kanta baba ta ce ” Allah ya kiyaye hanya dan nan

Yana amsawa ya tafi ya Buda motar sa ya tafi

Baba ta juyo wajen Yar Mahaukaciya ta ce ” Yarinya muje ki canja kayan nan KO? Ya sunan ki ne?

Yar Mahaukaciya ta ce ” *Yar Mahaukaciya* sunana

Baba ta zaro ido ta ce,,,,,,,,,,

Sorry masoyan yar mahaukaciya ina kara baku hakurin kadan in da nake yi hakan ya faru ne da 🏌🏼‍♀ nepa🏌🏼‍♀

🇳🇪 Belles écrivaines du Niger

*’YAR 👧🏻*    

         *MAHAUKACIYA👹*

*_Na SAJIDA_*

                    7

Na sadaukar da wanan gareki yar uwa masoyiya Maman manal matar oga lolz Allah ya barmin ke

Baba ta zaro ido tace”  yar nan bana son neman magana wani irin yar mahaukaciya kuma? Ina babarki take ne?

Yar mahaukaciya tayi tsai ta tuna lokacin idan tana daka a gidan su Larai yayansu suna cewa babata babata nan ta gane Babar mutun tamkar uwa Wace ta haifi mutun hakan yasa ta watsa hanayanta irin bata sani ba

Baba ta ce ” mu je kiyi wanka ki ci abinci sai ki bani labari ,

Baba ta shige gaba yar Mahaukaciya na biye a bayanta ta buda bayin ta tara mata ruwa sai da ta nununa mata komai domin a yanda tayi mata tsaye da alama bata iya ba , ta juya ta dauki yaron harda pampos dinsa tun na jiya da suka saka masa ba’a cire ba , hasalima ita bata san menene ba tana tsaka da yiwa yaron wanka yana tsala kukansa Yar Mahaukaciya ta fito ta dauki rigar da Baba ta Nuna mata ta saka tayi tsaye tana kalon yanda Baba ke juya Dan Mahaukaciya tana yi masa wanka , a hankali ta zauna tana kalon fatar hanunta ta zama wata kala wai daman haka take?  Tana tsaka da tunanin irin rayuwar nan mai dadi ta ji baba tsohuwa na cewa to bude ki bashi ya sha

Yar Mahaukaciya a ranta ta ce ” wai meye ake cewa ta bude ta bashi ya sha ne? Ita fa bata san mai ake nufi da hakan,

Baba ta ce ” ke yarinya ki dena yawon tunani kar ciwon nan mai suna totion ya kama ki , ai ina fada miki haka mukayi da sale ya shirishiri ya dankara min saki uku bayan ya dala min mari a gaban sabuwar amaryar sa kuma ya tunkudo ni waje aka yi mana taro jama’a na tambayar mai ya hadamu wai kinsan mai yace?

Yar Mahaukaciya ta girgiza kai tana sauraron baba

Baba ta ci gaba da cewa wai wani cewa yayi fa na saci kudinsa murtala fa

Yar Mahaukaciya ta ce ” kai har Murtala ? To wa ya dauka ?

Baba ta karkace ta gyara zama tace” yar nan nera sha biyar ne na dauka aradu ni ba duka na dauka ba kuma wata hudu yayi bai bani kudin cefane ba shine fa na dauka kuma ai ba sata bace KO?

Yar Mahaukaciya ta gyada kanta tana mamakin wai dauka ne tayi ba sata bane tayi murmushi

Baba ta ce ” ke yarnan ai dukan da yayi min da kuma sakin ya saka na kumbure uwa hulawa ni kadai nake kara girma babar uban gidana ta kaini ganin likita a can ne yace min wai totion ( tension ) ce ta kamani kuma har kisa take kinga ki dena tunani dan miji ya sakeki kiyi hakuri Allah zai baki wani cikin ruwan sanyi balatana ke din nan mai kyan aljanu

Yar Mahaukaciya tayi murmushi ta ce ” toh , domin ta lura Babar nan ba dai surutu ba

Baba ta kama rigar Yar Mahaukaciya ta zuge zup din , ita dai kalonta take tana son ganin abinda zata aikata tana zugewa Yar Mahaukaciya ta saka hanayenta biyu ta rufe mamarta

Baba ta ce ” ke kuji mini yarinya da iyayi kunyar shayar da yaron ne kike a gaban idona na FITA?

Yar mahaukaciya ta ce ” kunu yake sha

Baba tayi tsai ta ce ” dadina da yan gayu Kenan wai baza’a shayar da yaro ba kar nono ya fadi ,hum to Allah shi kyauta ta dauki yaron tayi kicin da shi sai wake take rera masa ta dora kunu ta kada domin shima mai gidan ma’abotin shan kunu ne hakan yasa ta hada ta baiwa yaron ya sha ya koshi sai baci ( bawon Allah )

Wasa wasa yau har sun cika kwana uku a gidan Idriss bata aikin fari bale na baki aman duk da hakan tana fitowa tana kalon yanda baba ke kula da harkokin gidan da irin kulawar da take basu ita da Dan Mahaukaciya , har mamaki take wani abin ,

Zaune take tana kalon TV baba ta zo ta zauna kusa da ita ta ce ” yarinya baki fada min inda babarki take da kuma abanki ba fa abun da mamaki har yanzu basu neme ki ba lafiya kuwa?

Yar Mahaukaciya ta juyo tana kalon baba a hankali ta furta nima nemanta nake , Mahaukaciya ta bata ban san inda ta nufa ba , na rasa inda ta tafi ta barmu da Dan Mahaukaciya

Baba ta gyara zama ta ce ” ban gane ba

Yar mahaukaciya ta gyara zamanta ta baiwa baba labarin rayuwarta har Wanda bata san sunanta ba bata san kowa ba hasalima bata san sunan garin nan ba wai jos ita kuwa a tinaninta a kano take domin tana ji a bakin mutane

Mai baba zatayi in ba kuka ba harda face majina tana karkata kai ta ce ” kai duniya kai duniya ina zaki da mu ? Oh ni habiba ya ga murja jikar saude wayo duniya kana tunanin a kunci kake sai ka tsinci Wanda ya fika oh Allahna , ta juyo ta kali Yar Mahaukaciya ta ce ” yarinya Ashe shi yasa da na tambayeki sunan ki kika ce min Yar Mahaukaciya?

Yar Mahaukaciya ta gyada kanta

Baba ta ce ” to ni zan ringa kiranki da Rahamu sunan yayi miki?

Yar Mahaukaciya tayi dariya ta ce ” eh yayi min baba

Suna tsaka da zance sai ji suka yi an banko kofar dakin an shigo , Baba ta mike tana dafe kirji ta ce ” salalahu alaihi wasalam Ta
wa ta sameni ,

Kafin Yar Mahaukaciya ta fahimci inda baba ta dosa sai jin saukan duka tayi ta ko’ina dukanta ake ba kakautawa , mai dukan ta warto Dan Mahaukaciya ta jefa shi kasa ya rufe da kukan jarirai da gudu Yar Mahaukaciya ta nufi wajen da yake yashe ta rungume shi suna rusa kuka a tatare , 

Mai dukan ta nuna su da yatsa ta ce ”  “”””‘ “””””””” “””””

Love u

🇳🇪 Belles écrivaines du Niger

*’YAR 👧🏻*    

         *MAHAUKACIYA👹*

*_Na SAJIDA_*

                    8

Mai dukan ta nuna su da yatsa tana kunfar baki tace” ke karamar yar bariki shegiya mai shige da zabaya ( albinos ) a gidan ubanwa ma ya hadu da ke har ya dirka miki cikin nan kika haifo yaro mai kama da ke? Kaga yayan shegu sai dai suyi kama da uwar su to bara kiji na fada miki Idriss nawa ne ni kadai babu ubanda ya isa ya hada shi da wata matar sai dai bayan raina dan haka ki dauki shegen danki da ke ku bace min a gidan mijin da zan aura tun kafin na kontar da ku nayi muku yankan rago

Yar Mahaukaciya dake goge jinin dake zuba a kan Dan Mahaukaciya ta dago idanuwanta ta sauke su a fuskar wanan matar wada da gani ta girmi idriss nesa ba kusa ba kuma tana ambatan mijin da zata aura cikin rashin kuzari ta dauki dan Mahaukaciya ta juya tana share hawayenta daidai zata bude kofa Idriss ya turo ya shigo ta dan ja da baya da sauri ya matso yana tambayar lafiya?

Hajiya Mariya ta taso tana fadin : my man ai na koreta ne kana ganin irin yanda ake zaginka a cikin family dina ana fadin ka ajiye karuwa yar bariki harda danku a cikin gidan ka ?

Idriss yayi gagawar daga mata hanu cikin daga murya yace ubanwa ya baki izinin korar a gidana? KO gidanki ne? An fada miki itama irinki ce? An fada miki itama ta samu yayane a waje irinki?

Hajiya Mariya tace” kai dakata Malan yayan ba da kai na samesu ba? KO an fada maka KO wani jaki nake mu’amala da shi ne? To wly KO ka kori yarinyar nan KO na kirayi mahaifiyarka na fada mata sanan na yada ka har a wajen uban gidan naka na samu na ganshi na fada masa irin abinda kake aikatawa ya koreka banza kawai , ta ficeshi ta ja rigar yar Mahaukaciya tayi waje da ita ta baiwa mudi mai tebur kudin mashin tace ya kaita inda yaga dama ,

Baba tsohuwa ta zauna tana ta hawaye ta fadawa idriss gaba daya abinda Yarinyar nan ta fada mata , harda sunan da tayi mata wato Rahamu ,

Idriss ya nisa ya ce” ban taba tinanin cewar watarana zan hadu da mace lokaci guda naji ta shige min a rai irin wanan yarinyar ya lumshe idanuwansa ya ce na kamu da sonta baba kuma insha Allah KO ina take zan nemota na aureta koda kuwa zan rabu da aikina ne , aman gaskiya ni bazan raka mata sunan Rahamu ba , bakya ganin yanayinta yanayin yayan larabawa ne ina wa laifin sunan Manal?

Baba tsohuwa ta washe hakora tace ai kuwa kaga sunan yayi min dadi sosai wato Manil

Yace aa Manal take baba ya Mike yayi dakinsa yana neman layin yaronsa ya kwatanta masa kamaninta da nufin maza ya zo anguwar su zai ganta da beby a hanunta ya dauketa kafin ya fito ( baka sans cewar a mashin aka dauketa ba ?)

Tafe suke yana papara gudu tun karfinsa ya ce ” ke wace unguwa zan kaiki?

Yar Mahaukaciya tayi shiru can tace ” Dan Allah ka kaini wajen magani kaga dan Mahaukaciya duk yayi wani iri

Mudi ya juyo kadan yaga yaron duk ya wani banbankare a ransa ya ce ” kan uba kar aje ya mace min a rufe ni hakan yasa ya ja ya tsaya daidai wata katuwar asibitin kudi ta Yaron nan mai tashe wato Ibrahim Y Nazir ya ce ” ke sauka ki shiga nan zasu warkar da ke kinji?

Yar Mahaukaciya ta sauka da sauri mayafinta har yana dan zamewa ta shige asibitin , tana zuwa ta nufi wajen da taga kamar nan ne wajen maganin , ta shiga layi , tun abin karfe goma sha daya har karfe 12 da yan mintuna sanan layinta ya ISO tana zuwa sai taga wata taga taji ance katin yan me kike so?

Ta dago dan Mahaukaciya ta nuna ta ce ” dan Allah kiyi masa magani kina ganin jikinsa?

Matar ta dan bude windows din ta leko ta ce ” ke dauke min jini mana karki bata min wajen aiki ki bayar da kudi a yanka miki katin ganin likitan yara

Yar mahaukaciya ta ce ” nawa ne kudin?

Matar ta ce ” dubu hudu

Yar Mahaukaciya ta ce ” dan Allah ki yanka min a bashi zan kawo miki

Matar nan na jin haka ta dana Kiran securitie yana zuwa ta ce masa yayi waje da wanan tana neman tsayar musu da aiki

Sécuriti din ya ce ” madame mu je

Haka tana ji tana gani yayi kokarin tura keyarta tana ta magiyar su saurareta , har ya kusan turota waje wata mata da wani a gefenta da alama sun zo dubiya ne ta tsayar da direban dake Jan su ta fito tana tambayar lafiya?

Securitie din ya fada mata abinda yake faruwa ,

Ta girgiza kai ta bude motar ta zaro kudi ta mikawa Yar Mahaukaciya tana fadin take kiyi maza ki kewaya urgence domin wanan ai urgence ne daga baya kwayi katin Allah ya bashi lafiya

Yar Mahaukaciya tayi Saurin tsugunawa da dan Mahaukaciya a hanunta tana hawaye ta shiga godewa wanan mata har ta shige mota direba ya jasu sai cikin asibitin ita kuwa da gudu ta mike tayi inda aka nuna mata , tana isa aka tarota aka dorashi saman wani gado na yara suka tura shi

Suna shiga akace wanan ai tamkar accident dan haka a kirawo Wanda ya kawoshi idan ba haka ba baza’a taba shi ba ( kuji fa )

Wata nurse da gudu ta fito ta yafito Yar Mahaukaciya ta biyo bayanta cikin Sauri

Suna zuwa

Docter mai sunan Abdallah ya ce ” mai ya samu yaron ?

Yar Mahaukaciya ta ce ” ban sani ba

Ya dan dago idanuwansa ya sauke a samanta domin muryarta mai dadin gaske , a ransa ya ce yarinya ce hakan yasa yace” ina Mahaifiyar sa?

Yar Mahaukaciya ta nuna kanta ta ce ” nice Mahaifiyar sa faduwa yayi dan Allah Malan kayi masa magani kar ya mutu

Docter Abdallah ya ce ” Malan ? Sai kuma ya basar ya mike domin gaba daya ji yayi ya kasa musa mata , ya nufi dakin da aka shinfidar da yaron ya ce a shiga dakin tiyata da shi ,

Nan da nan aka shirya shi akayi dakin tiyata da shi cikin gagawa domin yaron har wani shidewa yake , suna shiga docter Abdallah da sauran ma’aikatan suka dukufa don ceto rayuwar Dan Mahaukaciya Bawan Allah

Gani nayi Docter Abdallah da Sauri ya cewa nurse ta bashi irin abin nan da idan mutun yayi doguwar suma ake dana masa a kirjinsa ,  da gudu ta dauko ta daidaita ya kara yage rigar Dan Mahaukaciya ya murza abin ya dora masa saman kirjin sa , aman shiru kake gani ya kara murzawa ya dora masa cikin karaji ya ce ” no ,no  boy ka tashi mana kar ka yi min haka please ba’a taba mutuwa a hanuna ba ya kara murzawa ya dora masa yana kokarin kara murzawar da Sauri wata nurse ta rike hanunsa suka kama suka duba lokacin mutuwarsa 12h da minti 47

Docter Abdallah ya yi shiru gaba daya jikinsa ya mutu maganar matar nan wato yar mahaukaciya ta fado masa a rai inda take cewa dan Allah ka yi masa magani kar ya mutu , a hankali ya furta i’m sorry ,

Ya fito yana layi yana fitowa Yar Mahaukaciya tayi kuri tana kalon kofar dakin tiyatar sai da gabansa ya fadi ta iso da Sauri tana fadin ” Likita ya jikin Dan Mahaukaciya ?

Da kyar ya tataro nutsuwar sa ya ce ” Madame i’m sorry Allah ya amshi abinsa

Yar Mahaukaciya ta ce ” ban gane ba mai kake nufi?

Docter ya hadiyi wani yawu ya ce ” ya rasu ,

Yar Magaukaciya gaba daya taji tana kokowa da nunfashinta da kyar ta iya furta ya mu
tu? Sai luuuuuuuu ta tafiiiiiiiii

     😭😭😭😭😭😭😭😭😭

🇳🇪Belles écrivaines du Niger

*’YAR 👧🏻*    

         *MAHAUKACIYA👹*

*_Na SAJIDA_*

                         9

Luuuuuuuu ta tafi kafin ta fadi Docter Abdallah ya tarota ya dagata cimak yayi wani daki da ita ya shiga bata taimakon gagawa cikin kankanin lokaci ta dawo hayacinta tana farkawa ta shiga rusa kuka har muryarta na dishewa , shi kuwa yana zaune yana kalonta yana share zufa domin ji yayi kwatakwata baya iya wata magana ,

Tana tsakar kukanta ta daga kanta sama tana kalon pankar dake juyawa a dakin asibitin tana tunanin ya zatayi da rayuwarta ? Tana kalon Dan Mahaukaciya tamkar Tana tare da mahaukaciyarta , Yanzu ta sanadiyarta aka kashe mata dan Mahaukaciyarta? Ta nisa bata san cewar a fili taci gaba da fadin ” shin ya zanyi? Wa gareni? Ina zan kai Dan Mahaukaciyana ayi masa sitira? Wayo Allah gani gareka

Docter Abdallah ya dago kansa yana kalonta ga dukan alamu zancen zuci ne ya fito fili ya lura tana boye wani abu a ranta da alama ta fiya zurfin ciki, to aman mai take nufi da ina zata kai Dan Mahaukaciya? Mai yiwuwa yaron nata ne mai suna hakanan domin da ya tambayeta sunan yaron hakan ta fada, to aman ina babansa?

Cikin karfin hali ya ce ” ina babansa yake ne?

Ta juyo idanuwanta wa’inda suka koma kalar ja tana kikifta ido ta ce ” babansa ya mutu , bamu da kowa a garin nan kuma ban san hanyar bola ba

Ya budi baki zaiyi magana sai yaji karar bude kofa yana juyawa yaga kakarsa ta shigo cikin shigarta ta alfarma ta sha glas na karin gani tana shigowa ta juya ta cewa direban da ya kawota ” yaro Kagan shi a nan ai ka juya kawai idan na gama yi masa fadan ya maidani gida KO ya dorani mashin 😌

Shi dai dan ladi direba ya juya yana dariya domin lamarin hajiya Hawaou sai ita , ta shigo cikin nutsuwa ta tsaya ta ce” kai Abdallah ka kiyayeni yanzu dan nayi maka maganar aure shine zaka fice yau baka gaisheni ba? Ai Allah ya taimakeni nasan wajen aikin naka , to ka sani aure ba fashi au ka kawo KO na zabo maka yaro 😏

Docter Abdallah ya taso da sauri a ransa yana fadin wani dan duniyan ya gaya mata yau ga asibitin da yake ? A ransa ya ja dan karamin tsaki haka kawai iyayensa basu takura shi kan yayi aure ba ita tana faman shiga rayuwarsa , ya kamo hanunta ya zaunar saman kujerar da ya tashi sai a sanan taga Yar Mahaukaciya na kuka ta zaro ido ta ce ” Ikon Allah yarinya mai akayi miki? KO alurar ce bakya so? Ko dai yaci zalin dinki yayi miki biyu irin yanda yayi min?

Docter Abdallah ya ce ” iya dan Allah ki saurara kadan kinga nan fa asibiti ne yama akayi suka barki kika shigo?

Hajiya Hawaou ta ce ” gidanku akayi suka barni na shigo, kuma na fada maka ka dena kirana da iya sai kace uwar kaji

Ya girgiza kai ya ce ” kinga wanan yarinyar marainiya ce batada kowa kuma yanzu ta kawo yaronta nan ya rasu shine take kuka domin bata san kowa a garin nan ba ,

Ai hajiya Hawaou na jin haka ta shiga salalami tana kuka ta Mike ta rungume Yar Mahaukaciya tana fadin” kiyi hakuri yarinya dukan mai rai mamacine , ai nima dan makociyata tana haihuwar shi ya rasu kai nayi kukan mutuwar yaron nan domin suna mugun neman haihuwa Allah ya basu kuma ya amshe abinsa kiyi hakuri Allah ya jikansa muje gidana ayi masa sitira idan kin huce sai asan yanda za’ayi aman bazan barki haka ba , kawai ta shiga tatara mayafin yar Mahaukaciya ta dagota KO takalmi babu a kafar Yar Mahaukaciya ta kamo hanunta tana kuka itama tana kukan suka shiga cikin mota Shi kuwa ya koma ciki dan ya dauko gawar dan Mahaukaciya

Cikin mutunci aka yiwa dan Mahaukaciya sitira harda taro domin Hajiya Hawau mutuniyar mutane ce sosai aka yiwa dan Mahaukaciya adu’a inda mata ke shiga suna ta’aziya domin Hajiya Hawau tayi ruwa tayi tsaki tace jikanta ne daga kauye suka zo Allah yayi masa rasuwa ,

Ita dai Yar Mahaukaciya tana Zaune da zunbulelen hijabin Iya da tazbaha a hanunta tana ja astagfari kawai take ja itama Iya ta fada mata tace ki ringa hailala kina maimaita astagfrullah Allah ya jikansa ke kuwa ya sanyaya miki zuciyarki ya baki dangana, hakan yasa ta koma gefe daya irin yanda ta saba zamanta tayi shiru tana ta jan carbinta tana astgfari hawaye wani na korar wani ,

Konci tashi har an yi cikon satin Dan Mahaukaciya , aman har yanzu sakewa ta gagari Yar Mahaukaciya domin jira take a koreta ta kara gaba dan tasan hakan rayuwarta take KO an Nuna mata so to fa za’a kyamaceta ,

Dawowarsa Kenan daga asibiti ya nufi can cikin gidan su domin mahaifiyarsa tayi kiransa cewar tana son ganinsa , yana shiga ya tarar da ita zaune ta harde kafafuwanta ya karasa ya zauna yana kokarin gaisheta kamar yanda ya saba , cikin sauri ta katse shi ta ce ” abdul wai wacece yarinyar nan? Ni dai a sanina dangin ku duk yawancinsu yan camaru ne ya akayi ita wanan na ganta a nan ? Wa ya kawota ne? Meye halakar kakarnan taka masifafiya da ita?

Abdallah ya rasa amsar da zai baiwa umansa domin ita a rayuwarta ta tsani taga an rabe su idan dai mutun ba mai arziki bane tofah ranta baya so , ya ce ” am haba mom kinga nima tare na gansu bansan KO wacece bâ fa ,

Hajiya Marhaba tayi shiru can ta ce ” naji can ita da jarabarta aman na haneka da shiga sabgar yarinyar nan idan kuwa ba haka ba wly sai na saba maka , kuma karka manta nayi maka mata dan haka ka mayar da hankalinka kanta kaji KO?

Abdallah ya dan Sosa keya ya ce ” an gama mom please ki dena rayar da hankalinki ai itafa bazawara ce kingani ai sai bazawari KO?

Hajiya Marhaba ta daga kafadarta irin su ya shafa din nan ta Mike tana tafiya ciki gadara ,

Bayan ta tafi docter Abdallah ya kontar da kansa jikin baban kujerar dake tsakar dakin su ya lumshe idanuwansa ya ce” ina son sanin labarinki beauty ( wato Yar Mahaukaciya ina ruwanka da labarinta inji ni sajida 😏 )

Zaune take ta saka kwanon furar da Hajiya Hawau ta dama mata a gaba tana ta tunani , Hajiya Hawau ta dauko karamar kujera tayani tsegumi ta zauna ta ce ” to yarinya bani labarinki kuma ki fada mini sunan ki

Hankalin yar Mahaukaciya ya tashi a ranta ta ce ” Nasan idan kema na fada miki sunana Yar Mahaukaciya zau gujeni ne, ni kuwa wani suna zan fadawa iya?

To jama’a ku taya Yar Mahaukaciya zabar sunanta don gujewa tsanar sabuwar family dinta 🤝🤝🤝🤝🤝

🇳🇪Belles écrivaines du Niger

*’YAR 👧🏻*    

         *MAHAUKACIYA👹*

*_Na SAJIDA_*

                       10

Yar Mahaukaciya ta gama yanke hukuncin ba Wanda zai kuma sanin labarinta domin idan ta fada kyamarta ake gwara ta boye sirinta ta nemi Mahaukaciyarta a boye daga baya idan ta ganta sai ta gudu da ita ,

Ta dago kanta ta kali hajiya Hawau ta ce ” Ni dai Marainiya ce bani da kowa sai Allah ,

Hajiya Hawau ta ce ” to shi mijinkin rabuwa kuka yi KO mutuwa yayi?

Yar Mahaukaciya ta ce ” mutuwa yayi hajiya , domin tasan idan ta ce rabuwa suka yi za’a nemi sanin KO shi waye dan a nemi yan uwanta ,

Hajiya hawau ta ce ” eyah Allah ya jikansa kar ki damu yata kinga daman ni dana daya a duniya Allah ya ba
ni ya aure mata marar mutunci kinga tana can ciki ba ruwanta da ni , yaron ma da yake kulani bakin ciki take kinga kuwa ohon mata Allah ya bani nima yar KO?

Yar Mahaukaciya tayi murmushi a ranta ta ce ki gafarceni hajiya ki gafarceni ,

Hajiya hawau ta Mika mata furar da ta dama ta sha nono mai kauri da cukui sai abin mai take ga siga ta ce ” kinga damun Dan Aljana ne wanan kwana biyu bai shigo ba mahaifiyarsa ce bata da lafiya ai har Idrissu ya kamata a gadon asibiti yaki sakinta sai da akayi da gaske

Yar mahaukaciya tayi murmushi ta ce ” kai gaskiya bai kyauta ba sam

Hajiya ta kara karkata daurin dan kwalinta tace ” kyaji mai yi dan Allah kinga ai ke kinsan abinda kike yi aman sauran gaba dayan su sun goyi da bayan a BArta ta samu lafiya ji suke asibitin ci ce , ai sai sun ga uwar bari kafin su yarda da magana ta ,

Yar Mahaukaciya tayi dariya domin du yanda kaso kaucewa lamarin hajiya to fa sai ta saka ka dariyar ,

Hajiya ta ce ” KO ke fa to baki fada min sunan naki ba ,

Yar Mahaukaciya ta ce ” sunana RAHAMU domin bata manta sunan da Baba tayi mata ba

Hajiya hawau ta ce ” Rahama suna mai dadi To ni dai zan ringa kiranki da Ramatu domin Rahama haka sunan sirikata yake a gaban baban idrisu bazan iya fada ba

Yar Mahaukaciya ta ce ” to hajiya ba damuwa na gode , haka suka wuni suna dan tataunawa Yar Mahaukaciya ta dan fara sakewa da hajiya Hawau domin tana kara janta a jiki

Washe gari da safe Hajiya Hawau ta shirya tacewa Yar Mahaukaciya ta tashi su je gidan su Dan Aljana su ga jikin babarsa an sakota daga asibitin,

Haka kawai Yar Mahaukaciya taji bata ra’ayin fitan ta kali Hajiya ta ce ” Hajiya ki je ni na karasa aikin mu KO?

Hajiya ta ce ” kai Ramatu bakya son yawo kema ga son aiki to ni dai kinga tafiyata sai na dawo

Yar Mahaukaciya ta ce ” a dawo lafiya Allah ya tsare

Hajiya ta ce ” Amin tayi gaba abinta ,

Bayan tafiyarta Yar Mahaukaciya ta zage damtse ta shiga sharar gidan ta share tsaf ta dawo ta zuba cleam ta wanke da ruwa da tsintsiya ta koma ta harhada kayan wanke wanke ta dawo ta zauna ta cire  hijabinta ta kara gyara daurin zaninta ta zauna saman tayani tsegumi ta shiga wanke wankenta

Ya jima tsaye yana kalonta tana ta wanke wanke yana mamakin kalar fatarta har wani yelow yelow yake sakawa faratunan kafarta dogaye ba kananuwan yatsutsai bane da ita a hankali yayi salama ya shiga

Ta razana da jin salamarsa ta dago da Sauri tana konce hijab dinta daga kanta ta saka tana amsa salamar sa ,

Idriss ya karaso ya jawo kujera ya zauna kusa da tata , yana fadin sanu da aiki madame wanan aiki haka?

Yar Mahaukaciya tayi murmushi tana kara gyara zaman hijabinta

Ya ce ” ina masu aikin gidan ne?

Ta ce ” ai an aiki biyun kasuwa dayar kuwa tana baya tana wanki

Ya ce ” ai kuwa sai an karo muku masu aiki KO?

Yar Mahaukaciya ta dago da Sauri suka yi ido hudu kuwa ta kawar da kanta ta ce ” ina ma aikin gidan yake ai ni kadai ma na isa nayi shi

Docter ya girgiza kansa ya ce ” tap ikon Allah ai bazai taba yiwuwa ba hutawa kawai zakiyi

Yar Mahaukaciya ta ce ” hum , a ranta ta ce hutu fa lale KO a mafarki

Ya lura bata cika magana ba aman tana da girmama mutane yana son yi mata tambayoyi sosai aman sosai yake jin nauyin hakan bai san dalili ba haka yayi ta zama har ta gama wanke wanken ya dauke kondon kwanonin yayi kicin da su ita kuwa tayi murmushi ta dauko tabarma katuwa ta shinfida masa ta dauko kwarya da ludayi ta zauna ta a saman yar kujerar nan ta shiga dama furar , shima waje ya nema ya zauna yana kalon yanda take aiki bata da alamun gajiya tana gama damawar sai ga Hajiya hawau ta shigo gidan da salamarta

Yar Mahaukaciya taje da Sauri ta amshi ledar dake hanunta tayi daki da ita fruits ne ta sauye ta wanke ta jera rabin a frij ta debo wasu saman tire da wuta ta fito tana fitowa taga Hajiyar na zaune saman kujerar tana kara dama wata furar a hanunta , gefenta Idriss ne zaune yana shan wada ta dama masa idanuwanta suka ga wata kafa fara kar cikin wani bakin takalmi mai shegen kyau takalmin uwa na sarakai domin kalar adon sa ji tayi bazata iya kalon mai takalmin nan ba hakan yasa a hankali ta ajiye fruits din a kusan Hajiya Hawau ta Mika hanu tana fadin Hajiya kawo na dama miki mana

Hajiya hawau ta ce ” aa yar gidana wanan damun sai ni da kaina kowa ya dama baya sha sai ni din nan da kike gani ai ta Dan aljana ce da nake baki labari , ta kuma kalon dan Aljana ta ce ” Dan Aljana kaga yartawa da nake fada maka

Bai dago ba bai kuma ce kanzil ba itama haka kawai ta kasa koda dago kanta bare ta kale shi , jin takun tafiyar hils da wani kalar tiraren yasa ta bada hankalinta kan kofar shigowa

Wata budurwa ce ta shigo ta sha mahaukacin hils mai shegen kyau kai ita kanta abin kalon ce domin haduwa iya haduwa ta hadu ga kamshi tana zubawa batayi  salama ba kawai shigowa tayi sai da taga idriss na zaune sai naga ta saki murmushi ta ce ” Brother daman kana nan har momys take neman ka?

Idriss ya dago kansa daga kwaryar furarsa ya dan kaleta yace ” sauran kice mata ina nan

Tayi murmushi bata gaida hajiya Hawau ba bare ta gaisar da Yar Mahaukaciya Wace take kalon takalmin kafarta tana mamakin yanda akayi ta hau saman sa , ta nufi wajen wanan mutumin mai cike da korjini tana zuwa ta saki murmushi ta ce ” Honorable barka da warhaka

Sai yanzu Wanda aka kira da honorable ya dago kansa ya zabga mata harara , da Sauri na furta ya Salam na fadi ba shiri ba ni kadai ba Yar Mahaukaciya kanta gani nayi ta zaro idanuwanta tana kalon wanan bawon Allahn

Shin wanene Dan Aljanar da Hajiya Hawau ke fada tana karawa? Wacece wanan budurwar da ta shigo meye halakarta da Irdriss? Mai yasa bata gaishe da Iya ba? Muje zuwa daga Yar mutan niger

🇳🇪Belles écrivaines du NigerDagowar kan da yayi , yayi daidai da kalonsa da Yar Mahaukaciya tayi gabanta ne ya yanke ya fadi da Sauri ta sada kanta kasa a ranta ta ce ” to shi kuwa wanan mutun ne KO aljan? Daman akoy mutane kalar haka? Shi kuwa wanene?

Muryarsa ta tsinto ya furta kalma uku Wace bata san mai yake nufi da ita ba

Yana kalon budurwar da ta shigo ya ce ” are u crazy?

Ta girgiza kai gwuiwa a sace ta juyo wajen Hajia Hawau ta ce ” hi grandma

Idriss ya ja tsaki ya mike da furar sa ya kali Yar Mahaukaciya Wace take ta al’ajabin maganar dan Aljanah  kamar yanda Hajiya ke kiransa da shi ya ce ” sister taso ki ga sakon nawa na shige ance mom na kirana

Yayi ciki Yar Mahaukaciya ta bi bayan sa

Hajiya Hawau ta gama dama furar kai KO ni sai da ta ban sha’awa irin yanda take daukan ido ta mikowa Dan Aljanah ta kakabe zaninta sai tura baki take tayi cikin dakinta ,

A hankali wanan budurwa ta ja kujera tana fuskantar Dan Aljannah cikin raunananiyar murya ta ce ” Mubasshir please manan kayi hakuri ai na gaisheta

Sai da ya gama jujuya furar yana ta tinanin wanan sabuwar mai aikin ta Hajiya ce ta dauko kwaryar da aka dama masa furar a ciki shi fa yaki jinin yan aiki yana kyankyamin harkokinsu baya son KO kadan su rabi abincinsa gashi kuma furar sai fizgarsa take , maganar Budurwar nan ta maido shi daga tunanin da ya tafi ta ce ” *Mubasshir* ka amsa min please  nace kayi hakuri

A hankali ya dago idanuwansa ya sauke su a saman fuskarta suka yi ido cikin ido da Sauri ta kawar da kanta domin duk tsatsauran halinta bata san ya akayi take shakar hada ido da Mubasshir ba ,

Cikin fadafada ya ce ” *Sahla* ki gane ni fa ba zan kwashi marar tarbiya ba , a kulun ina fada miki
ki kiyayi rashin kunya , idan baki girmama macen da ta haifi mahaifin ki ba fada min zaki girmama tawa kakar kuwa? Da da ranta nasan har sai kin taka ta domin kince kina kyankyamin tsofafi, ki gane darajar tsohuwar nan da kika raina yasa har nake iya kalonki har nake kula ki kin fi kowa sanin KO wanene ni nafi karfin ajin ki aman ina jin kunyar wanan tsohuwa da nake kalo tamkar kakata ke kuwa Allah yayi miki rahama kina kaucewa , so bara kiji ni bazan lamunci shashancin nan naki ba idan har bakya mutunta manyan ki to fa tsakanina da ke horo ne kawai ba wani Abu

Cikin tsoro da kalamansa ta ce ” I’m sorry honorable nayi alkawarin mutunta ta kayi hakuri please karkayi fushi da ni

Ya dago kansa yana kalonta gaskiya shima ya san yana son Sahla domin kyakyawa ce ajin karshe , sai dai abinda baya so a tatare da ita raina mutun sam ita ta raina mutane ta tsani ta shiga lamarin mutun indai ba ta yarda da shi ba hakan kuwa harda kakarta Wace ta haifi mahaifinta ,

    Wacece Sahla?????

Sahla itace auta a wajen hajiya Marhaba wato kanwar Idriss , Hajiya Marhaba tayi ta samun ciki tunda yarintarta sai dai cikin ikon Allah cikin yana barewa cikin haka Allah ya bata cikin idriss ta haifi abinta cikin koshin lafiya , bayan sa ma sai da tayi barin biyu kafin ta samu cikin Sahla , tun bayan haihuwar Sahla shikenan tamkar anyi ruwa an dauke Hajiya Marhaba bata kuma samun wani cikin ba hakan yasa suka dauki son duniya suka dorawa matar manya lakabin da Sahla tayiwa kanta Kenan , tarbiyar Sahla ba kwaba ba tsangwama , makarantar sai taga dama take zuwa , kawayenta duka yayan manya ne , Sahla ta kasance Doguwwar mace fara ga shegen kyau masHa Allah ga iya Jan aji ga yanga kai Sahla da ba dan halayenta ba sai nace goma ce cifffffff sai dai kashhh irin wanan gata da ta samu ya saka bata ganin kan kowa da gashi , baba KO karami zata takaka san ranta domin tasan abinda ta taka

Abinda ke hadasu fada da Hajiya Hawau irin yanayin shigarta da kuma sangartar ta idan fa hanya ta hado su sai dai ita ta rakube ta fice sanan ita ta fice hakan yasa sam basa jituwa suke yar tsama , hakan nayiwa Hajiya Marhaba dadi domin taki jinin sirikar tata abu ya hana tayi maganin ta Elahj domin yana matukar kaunar jangom lakabin da take kiranta da shi Kenan ( ya Allah ka tsare mu amin )

Abu daya yake saka Sahla dan sadakawa soyayar Mubasshir da ta wayi gari ta tsinci kanta a ciki tsundum hakan yasa take dan rage wasu abubuwan a cikin halayenta domin shi bazai lamunci rashin mutuncinta ba idan kuwa ta rasa shi tasan ta tafka asara ( tofah )

      Ci gaban  Labari

A hankali ya aje furar domin sai ya deba da niyar kaiwa bakinsa sai ya mayar da ludayin yana matukar son ya sha furar nan kyankyaminsa ya hana shi ya sauke ajiyar zuciya ya mike yana saita agogon hanunsa ya dan dubi Sahla kasa kasa ya ce ” ki kaiwa hajaju furar nan ki fada mata na koshi , sai tomorrow ya juya ya saka kansa gaba yana tafiya cike da isa tamkar dan Sarki

A hankali tana kalonsa har ya fice daga harabar gidan ta sauke nanauyar ajiyar zuciya ta lumshe idanuwanta ta ce ” i love you My man i  really love u  ta kuma lumshe idanuwanta ta ce ” zaka soni ne a hankali domin nasan dan ni kadai aka yi ka , ta Mike ta saka kafa ta shure furar harda hararan kwaryar tayi waje ta nufi motarta dan tasan a yanzu ya bar unguwar tana iya fita

😌😌😌😌😌😌😌😌😌

🇳🇪Belles écrivaines du Niger

*’YAR 👧🏻*    

         *MAHAUKACIYA👹*

*_Na SAJIDA_*

                       13

Karfe biyar da rabi Mai gadi yayi salama ya gaida Hajiya Hawau ya sheda mata ga Mutumin da Idriss yace a bari ya shigo idan ya zo ,

Hajiya hawau ta amsa masa ya juya inda aka yiwa Malan yunus shinfida a banban falon dakin Hajiya Hawau a nan za su ringa yin karatun kulun har ita hajiyar ,

Cikin ikon Allah kulun sai Malan Yunus Ya zo da yama sunyi karatun arabi da Yar Mahaukaciya yau har sati uku Kenan sosai take fahimtar hukunce hukunce na musulunci gaba daya , domin kowace rana akoy abinda zasu karanta sanan a kulun sai yayi mata wa’azi sosai sosai , sai yanzu ta san cewar itama mutun ce mai daraja domin an haliceta a jinsin bil’adama , idan yana bata tarihin manzanin mu da irin yanda suka sha gwogwormaya dan yada adinin musulunci sai taji wani irin shaukin adininta taji wata irin soyayar adininta taji haushin shekarun da ta shafe a bola bata zuwa ta saurari karatu koda yaran na tsokanar ta , 

Bangaren Malan Yunus yana matukar jin dadin karatu da Yar Mahaukaciya domin idan yana koya mata karatu tana bada hankalinta gaba daya ga saukin daukan harda domin akoy tambayoyi sosai kan du abinda ya koyar da ita

Yau ta kama alhamis tun da safe Yar Mahaukaciya tayi aikace aikacenta ta gama ta dora girkin su karfe biyu ta sauke komai har jus jus dinsu da suke hadawa ta gama ta saka a frij Hajiya Hawau sai aikin sanu take jera mata , sai da ta gama taje tayi wanka ta fito ta daura zaninta ta zira rigarta na atampa ta fito ta nufi falo wajen hajiya Hawau

Tana shiga ta zauna kasa , saman kapet wanan na daya daga cikin al’adunta sam bazaka ganta saman kujera idan baban mutun na sama ita sai dai tayi zamanta a kasa koda kuwa ka tashi tana matukar jin kunyar hawa wajen da ka tashi

Hajiya Hawau ta dago kanta daga kalon da take tace : taso maza yau na kunce miki kitson nan da na yi miki uwa mai takaba

Yar Mahaukaciya tayi murmushi ta matsa kusan Hajiya Hawau ta kunce daurin dan kwalin kanta Hajiya Hawau ta kama tsifa

Suna tsaka da tsifar Docter Idriss yayi salama ya shigo cikin falon da Sauri Yar Mahaukaciya ta shiga kiciniyar kwace kanta don ta rufe domin KO hijab babu a jikinta gashi rigarma ba zumbuleliya bace

Hajiya Hawau ta kama baki ta ce ” ke zauna min kaji min yarinya to dan wanan dan neman ya shigo shine zakina kokarin ganin kin kwacen kanki? To ba yayanki bane shi din?

Idriss ya zauna ya ajiye jakarsa baka da alama daga office yake , ya dago kansa ya ce ” Iyancy mitar mai kike yi ne?

Hajiya Hawau ta turo daurin dan kwalinta gaba ta kankance idanuwa ta nuna masa yatsarta ta ce ” Kai wanan yaro ka kiyayeni , ka FITA a idona na rufe aradu zan kai kararka wajen ubanka dan ni din nan da kake gani daidai nake da kai

Idriss ya bushe da dariya har yana rike ciki ya ce ” haba Madame haba madame mai yayi zafi kiyi hakuri kin sani sarai ke din ta kudin ce KO?

Ta kuma turo bakinta , Yar Mahaukaciya tayi murmushin diramar Hajiya da jikanta ta dan juyo fuskarta ta ce ” Yaya ina yini ya aiki

Idriss da sai yanzu ya lura da ita domin da ya shigo ya ji dai hajiya Hawau na mita aman bai san mitar mai take yi ba , ya amsa salamarta idanuwansa a saman tarin gashin kanta da ake kuncewa

Ya ce ” Hajiya wai atach ne yar taki tayi?

Hajiya Hawau ta ce ” Allah ya kiyashemu da Karin gashi, ai gashinta ne ba wani atach

Idriss ya zaro ido ya ce ” Aman ya naga uwa na nasaru wanan kalar gashin ai ba na hausawa bane kinga fa ja ne ga tsayi aman kina yi masa shampo KO ?

Yar Mahaukaciya ta dago kanta idanuwanta yana mage ta saukesu a fusfar idriss ta ce ” YAYANA kuma mainene shampo?

Idriss ya hadiyi wani yau da ya tsaye masa a makogoronsa a ransa ya kara yarda tabas Ramat ba bahaushiya bace to aman wai ita wace yare ce?

Ya ce ” haja
ju ki bar kan nata mana na kaita saloon a wanke mata idan mun dawo sai ki dadaure mata

Hajiya hawau da daman hanayenta sun gaji sosai ta ce ” to dan Albarka Ramatutu tashi ki dauko hijabinki ku tafi a wanke miki da abin wankewa kinji ?

Yar Mahaukaciya ta mike tana dan jan rigarta dan ta rufe mata jikinta aman ina da Sauri Idriss ya kawar da kansa daga dubanta yana fadin a’uzubilah yana kawar da kansa ,

Ta dauko zumbulelen hijabinta ta zira Idriss ya bar jakar Ma’aikatan NASA a nan suka shiga mota

Daidai zasu FITA daga harabar gidan sai ga Sahla da kawarta Alisha sun shigo suna shan kidan su ran Sahla ya gama baci domin wanan ai zubar mata da mutunci ne Idriss yayi niyar yi ya zai dauko wanan bagidajiyar a motarsa kuma gashi kawarta Alisha ta gani ga irin yanda Alishan ke maseefar son Idriss din

Alisha ta waigo ranta a bace ta ce “”””””””””

           Love u

🇳🇪Belles écrivaines du Niger

*’YAR 👧🏻*    

         *MAHAUKACIYA👹*

*_Na SAJIDA_*

                       15

hajiya hawau cikin bacin rai ta nuna Sahla da hanu ta ce ” ke yarinyar nan kin fiya neman magana , shin yaushe zaki fara mutuntani ne? Ki tuna ni fa na haufi mahaifinki aman kashinki yafini daraja , ta girgiza tana kama hanun Yar Mahaukaciya ta juya ta ce ” Idrissu karka ce mata komai ka barta duniya ce , ta kuma juyawa wajen Mubasshir da ita ya kurawa ido bai taba ganinta a irin wanan halin ba tabas KO wacece wanan tanada baban mukami a wajen Hajiya ,

Hajiya ta hade hanayenta biyu tana kalon sa tace” Yarona dan Allah karka hukuntata dan ta batamin ka barta ta hukunta kanta da kanta , ka BArTA ta gane cewar mutun yafi kudin nan nasu daraja , ta ja hanun Yar Mahaukaciya suka nufi kicin

Gaba daya jikin Sahla yayi sanyi aman fa batayi nadamar abinda ta aikata ba

Idriss da tunda ya tare Yar Mahaukaciya ya shiga wani yanayi Wanda eh lale bazai ce bai taba shiga ba aman wanan kam yafi na kulun yana bukatar yin nesa da mutane dan ya dandance abinda ke kokarin damunsa ya mikawa Mubasshir Hanu ya ce ” friend sai mun hadu nayi ciki

Mubasshir ma ya mike ya ce ” muje tare kasan inada abun yi

Haka suka tafi suka bar Sahla nan zaune duk irin kwaliyar da ta sha da kanshin da take zubawa duka suka tashi a banza domin Wanda tayi dominsa KO kalon banza bata ishe shi ba , ranta ya kuma baci ta kara kudurtawa ranta sai tasan wacece wanan yarinyar mai kama da aljanu sai ta binciki lamarinta

Shigar su Hajiya Hawau kicin Yar Mahaukaciya ta dakata

Hajiya Hawau ta juyo tana kalonta , Yar Mahaukaciya ta duka gwuiwoyinta a kasa cikin shashekar kuka ta ce ” Dan Allah kiyi Hakuri Hajiyata ki dena fushi dan an bata min ki sani fushinki na Konan raina kakata bani da kowa sai Allah sai ke kiyi hakuri ki yafe mata

Hajiya hawau ta tsura mata ido ba komai ya birgeta ba sai kalmar kakarta da Yar Mahaukaciya ta furta a hankali ta saka hanayenta biyu ta dagota daga tsugunin da tayi ta ce ” ba komai jikata na hakura na daina fushi , ki tayani da adu’a Allah ya karkato min da hankalin dana kaina

Yar Mahaukaciya cikin fuskar tausayi ta ce ” nayi alkawarin saka aban gidan nan a adu’a Allah ya ganar da shi

Hajiya tayi murmushi ta ce ” mû je kinga Dan Aljannah naji tashin motarsa bai sha fura ba , karbi ki saka min a frij nasan zai dawo gobe sai na dama masa

Yau tunda safe gogo Fatima kawar Hajiya Hawau ta turo yaro a fada mata jikanta mai wata shida ya rasu , Hajiya Hawau harda kuka ta dauko hijabinta zumbulele ta zumbula ta dauko goronta da carbinta ta yiwa Yar Mahaukaciya salama tana fadin sai dare idan tana son ganinta mai gadi ya kaita , ta kama hanya ta shiga adaidaita sahu tayi tafiyarta

  

Zaune yake a office yayi shiru yana nazari ya zama wajibi ya koyawa yarinyar nan hankali yana matukar sonta yana so ta san darajar mutane domin shi mutumin mutane ne , tabas zai kai kudin aurenta aman fa zaiyi iya yinsa dan ta gane cewar mutun rahama ne , yayi murmushi da ya tuna irin abinda zai hadata da shi abinda tafi tsana ne wato tsofafi , yayi nisa da tsare tsarensa a cikin zuciyar sa kawai fuskarsa ta hasko masa furar Hajaju ba shiri ya hadiyi yau ya mike ya shiga tatare wayoyinsa dan kuwa yayi missing din furar nan yau har kwana 24 bai sha ba da jiya ya sha aka bata masa rai yayi tafiyarsa ,

Tunda Hajiya Hawau ta tafi Yar Mahaukaciya bata zauna ba sai da ta wanke gaba daya kayansu masu dauda ta kai bayan gidan ta shanya , ta dawo ta dauki tsintsiya ta wanke tsakar gidan ta koma wajen shukar mangoron gidan ta share tas ta kwashe ta dawo ta kuna tiraren wuta mai dadin kanshi sanan ta shiga bayi ta kuma yin wani wankan ta dauko zani na sabuwar atamparta ta daura ta dauko jar Riga ta saka ta daura dan kwalin zanin ga Jan kunshinta da ta kunsa ya fito yayi shar da shi batayi wata kwaliya ba KO mai bata murza ba domin yanayin garin da dan zapi zapi ta fito ta saka silifas dinta ta shige kicin ta shiga kiciniyar hada dan jus a Kofi dan kuwa yau baza tayi girki ita kadai ba , ,, bayan ta hada ta dawo wajen da ta wanke ta shinfida tabarma baba ta zauna ta saka cokali a cikin kofin ta fara shan fruits salat dinta ,

Cikin takun kasaita ya shigo cikin gidan da salamarsa cikiciki yanda ya saba , Yar Mahaukaciya kam bata ji ba hakan yasa bata dago kanta ba aman hancinta ya jiyo mata kanshin Dan Aljannahn Hajiya , kasa kasa ta kali kafarsa ta ga cikin takalmi kafa ciki ne yake tafe gabanta ya fadi domin Hajiyar bata nan yanzu budurwar sa zata zo ta shifka mata rashin mutunci ,

Karasowa yayi yana dan kalonta a ransa ya ce ” Ashe kunshi nayiwa wasu matan kyau , shi bai taba ganin kunshin da ya birge shi kamar wanan ba , Yar Mahaukaciya ta dago kanta da tsoro tsoro ta tsura masa ido , ita kawai mamakin gashin kansa take uwa mace

Cikin fada fada ya ce ” Meye

Yar Mahaukaciya tayi gagawar sada kanta kasa kunya ta rufeta a ranta ta ce ” baki iya kalo ba , Yar Mahaukaciya baki iya kalo ba , aman a fili ta ce ” Bata nan Hajiyar

Ya yatsina fuska ya ja kujera nesa da ita ya zauna , a ransa yana fadin melodius , kuma wani bangaren na zuciyarsa ya ce , ina ruwanki da ni 😌

Ya kusan minti ashirin a zaune bai ce mata ufan ba itama ta kama bawan Allahnta tayi shiru , can dai ta mike ta shige cikin falon ta dauko furar ta debo kindirmon mai zaki ta dauko cikui uku masu shegen laushi ta hado da yar madarar ta fito inda ta shinfida tabarmarta ta nemi waje ta zauna ta jera kayan a gabanta tayi zaman makaranta ta dauko kwaryar ta zuba furar da nonon ta maida hankali ta dameta sai da ta damu gaba dayanta ta zuba madarar nan sanan ta saka hanunta a ruwa da sabulun dake gefe ta wanke hanunta ta dauki cikui din nan gaba daya ta cicira shi a ciki ta zuba dan siga ta motsa , nan da nan man ya hayo sama furar ta fara sheki ,

Tunda ta fara dama furar ya kura ido yana kalonta kwarai ya gamsu da tsaftar yanda aka dama furar ganin ta mike yasa ya kawar da kansa , a hankali ta rufe kwaryar furar ta shiga kicin ta dauko karamar kujera ta fito tana taku cike da tsoro ta kawo kujerar gabansa ta ajiye ta juya ta dauko furar da wani ludayi wankake ta dora saman murfin furar ta karasa gabanta na faduwa ta ajiye saman kujerar sanan ta shige falo tana sauke ajiyar zuciya a ranta ta furta tasan ba sha zaiyi ba

Tofah Mubasshir ya zubawa kwar
yar furar ido abinka da idan Abu na birge mutun har kanshinta yake ji shawara yake da zuciyarsa shin zai iya sha kuwa?

Ni zan sha 😋😋

🇳🇪Belles écrivaines du Niger

*’YAR 👧🏻*    

         *MAHAUKACIYA👹*

*_Na SAJIDA_*

*This Page Dedicated to Aunty QUEEN MERMUE, Aunty NAFEE ANKER and AUNTY HALILOSS*

                   16

Ya jima yana kallon kwaryar furar sai ya mika hannu zai dauka sai ya maido hannun nasa , ganin dai ta shige d’akin bata fito ba yasa ya Mika hannu ya bude furar ya saka ludayin cikin nutsuwa ya kara motsata ya debo a cikin ludayin yayi bismillah ya kai bakinsa , bai san sanda  ya lumshe idanuwansa ba , ya d’auko k’waryar gaba d’aya Kamar Wanda wani zai warce masa ya maida

   

  Wanene *MUBASshir* ?

D’a d’aya tilo ga Marigayi Elhaj Mubarak Balarabe Mai farin gida , Elhaj Mubarak bai ta6a siyasa ba babban d’an kasuwa ne yana harkar kayan larabawa abayoyi , siga kantu, tiraruka , zamzam inda ya gaji wanan sana’ar wajen mahaifinshi , Matarsa da’ya tilo Hajiya Fad’imatu ya ga sarkin chadi , sun kai shekara goma sha biyu da aure har ta kusa shiga ménopause Allah ya azirtasu da cikin Mubasshir , abin nema ya samu sarkin chadi gaba daya ya nemi alfarmar su koma kasar su har ta haihu irin ganin girman su da Elhaj Mubarak yake yasa bai musa ba suka tatara suka koma , cikin ikon Allah tana rainon cikinta cikin kulawa da d’umbin kauna ga mahaifinta da kuma mijinta harma da al’umar garin , cikinta ya kai wata tara da kwana bakwai ta haihu ta sami da namiji cikin tsananin murna da godiya ga Allah subahanahu wata’ala Elhaj Mubarak yayiwa Yaron huduba da sunan Mubasshir , sosai aka sha shagalin bikin haihuwar Mubashir inda Mahaifin Hajiya Fad’imatu yayi Kiran Elhaj Mubarak ya bashi wata akwati mai dan girma da wani katon kwad’o a jikinta yace masa wanan a bari sai Mubasshir ya girma a bashi sako ne daga kakansa ,

Cikin girmamawa Elhaj mubarak yayi godiya da fatan Alkhairi suka juya Nigeria yaci gaba da harkokinsa na neman kud’i da gine gine na gidaje da sunan D’ansa tilo Mubasshir ,

Mubashir nada shekara shida suka shirya da mahaifansa suka d’aga saudiya sukayi Sallah daga kasar saudiya Mahaifin Hajiya Fad’imatu tsoho mai ran karfe da mijin Hajiya Fadimatu wato Elhaj Mubarak suka shirya tafiya Chine daga nan su komo Nigeria ,

Ranar da zasu tafi sai da suka raba dare suna hira duk rabin hirar jawabi ne Mahaifin hajiya Fad’imatu ke yi musu ita da mijinta , haka kawai take jin wata irin kaunar mahaifin nata Wace bata taba ji ba , har lokacin tafiyarsu yayi , a filin jirgi ma sai yayi gaba sai ya dawo ya kuma d’ora hanunsa a saman kanta ya ce ” Allah yayi miki albarka

Itama tayi murmushi ta ce ” amin Abu , haka mijinta ya d’auki yaronsa yayi ta sumbatar goshinsa yana saka masa albarka hardai aka fara Kiran sunaye ya ajiye shi yayi mata bankwana ,

Jirgin ya fara shawagin tashi sun dan daga sai ji kake bam wani irin kara Wanda duk jama’ar wajen suka tsorata wato jirgin da su Elhaj Mubarak ke ciki ne ya kama da wuta inda pilot din yayi yayi ya tsayar da jirgin abin ya faskara , gaba daya mutanen cikin jirgin Allah ya amshi ransu ,

Mutuwar nan ta girgiza Hajiya Fad’imatu ba ita kadai bama ta girgiza mutanen lagos da chad da kuma makah , Allah ya sa sun huta

Bayan rasuwar su sarkin Makka ya rike Hajiya Fad’imatu sai da yaga ta zama normal ya gamsu da ta hakuran sanan ya yarje mata ta koma lagos domin chadin bata da kowa mahaifiyarta ta dade da rasuwa yan uwa ba wani jituwa suke ba haka kuwa mijinta maraya ne GABA da baya ita kuwa bazata iya rayuwa a kasar makah ba tafi son tazo ziyara , kuma tana son ta koma gida KO don ta kula da dukiyar dan Marayanta Mubasshir , Sarkin Makah yasa akayi kiranta ya shaida mata bai hanata tafiya ba aman ta bar Mubasshir ya sauke alkur’ani domin yayi nisa a karatun hakan yasa ta barshi a wajen uwar gidan sarki Abdulrahman ita kuwa ta juya gida

Mubasshir nada shekara tara ya sauke alkur’ani mai girma , a shekara goma ya rubutashi da hanunsa , sanan litatafen musulunci ba wanda baya kokarin ganin ya hadace , kuma ga karatun boko sosai yana samun ci gaba

Mubasshir nada shekara ashirin da hudu har ya kamala karatunsa na boko idan ka Ganshi sak sufar larabawa ce da shi ga yalwar gashi baki sidik ga tsayi gaskiya Mubasshir Allah yayi masa tsararen kyau

Yar gidan sarki abdulrahmane ta mugun kamu da kaunar Mubasshir wato Mubinah Aman ina shi a yanzu yafi son ya koma gida domin Mahaifiyarsa yanzun ta fara gajiyawa kuma ga aboki da yayi Idriss yana mugun kwadaita masa rayuwa a Nigeria duk da Makah karshe Kenan aman garin mahaifiya yafi komai dadi hakan yasa ya tada Bali dole sai da aka shirya kaurowarsa Lagos unguwar dolar sunan unguwar tasa domin gaba daya gidajen unguwar gidajensa ne sai daya daya irin tsafin ginin nan na wasu aman sauran duk nasa ne inda gwomnati ke hayar su .

Dawowarsa Nigeria sosai yaji dadinsa domin yanayin kasar ya birge shi Mahaifiyarsa tayi murna sosai inda ya kama kasuwancinsa yaci gaba da yi , sanan yayi kaka wato Hajiya Hawau domin a rayuwa daga Hajiya Fadimatu sai wanan tsohuwa domin yana jinta sosai a ransa kuma a wajenta ya idasa kwarewa da hausa sanan dalilin girmanta da idanuwansa ke gani yasa yake kula jikarta Sahla don ba dan ita ba sam bazai saurari Sahlan ba don kuwa ita din bata cikin tsarin kalar matan da yake so , sam bata birgeshi sai dai dan dole don kuwa KO mubina da ta tafi tsere ta dan fita cikowa ( to fa 😳 )

           Ci gaban labarin

Taku har kulun ……….sajidah

🇳🇪Belles écrivaines du Niger

*’YAR 👧🏻*    

         *MAHAUKACIYA👹*

*_Na SAJIDA_*

  

                     17

Dedicated to ♻ *EXCLUSIVE  Forum* ku gane ina yinku irin da yawa din nan ,

*Ummy xeey*

*Aishan umma*

*Ruksad*

*Nabilancy*

*Bébé’arth*

*Phertimer Umar Abdallah*

*Aishat À muhd*

*Réal khady*

*Meelart Ahk*

*Sardy bash*

*Ummu khady*

*Billy Ladan*  da da da ,,,,……..,,,,,, da duk sauran da ban zano ba jinjina gareku *Muah*

              Ci gaba

Yana tsaka da shan furarsa yaji takun takalmin Sahla ta nufo cikin gidan a ransa ya ce ” oh Ashe taga zuwana KO wa ya fada mata , ? Wata zuciyar ta ce masa kanshin tiraranka manan tace ta shi take gane idan kazo ,, yana tsaka da tinanin yaji salamarta ya dago kansa a hankali ya ce ” Amin wa’alaiki salam warahamatulah Sahla

Tana mugun jin dadin idan ya kama sunanta domin ji take duk duniya ba Wanda ya kaishi iya furta *Sahla* har wani sanyi sanyi take ji idan ya furta , cikin nutsuwa ta dauko farar kujera ta aje kusan sa ta zauna , kasa kasa yake kalon shigarta doguwar Riga ce ta atampa da wani zungureren takalmi mai kyau a kafarta sai dai ta tafi zumbal ba kibar komai ba inda ya dan ciko ya sauke ajiyar zuciya da yayi arba da jagirar da ta ja baka a goshinta domin harga Allah sai da ya tsorata

Cikin wata murya mai dadin sauraro ya ce ” ki dena wanan abin a goshinki yayi yawa

Sahla tayi murmushi ta ce ” huby a saloon fa akayi min


Cikin basarwa ya ce ” basu iya ba

Ta kuma yin wani murmushin a ranta tace mutun sai shegen kushe mutane aman a fili tace ” to zan dena 

Yayi murmushi da yasa ta kuma narkewa ya ce ” Masha Allah Allah yayi miki albarka

Tayi far da ido ta ce ” Amin , aman a ranta tana fadin sai kace ubana ka ringa saka min albarka duk sai na rabaka da wanan shegiyar akidar ta mahaifiyarka ta saka albarka duk motsin da za’ayi

Mubasshir ya ce ” ina son muyi magana da ke mai mahinmanci

Sahla ta ce ” toh muje cikin gidan mom mana ai yafi siri KO?

Mubasshir ya ce ” no muje cikin falon Hajiya hankalina yafi konciya da nan din

Ta mike cikin yanga tayi gaba har ta kusan shiga ta waigo ta Ganshi a zaunan ta juyo domin tasan abinda ya hana shi tashi ta dauki kwaryar furar tasa ta yi ciki , yayi bismillah ya mike yayi cikin shima

Suna shiga ta kara kakabe masa wajen da zai zauna ya karaso ya zauna ta juya ta nufi dakin Yar Mahaukaciya Wace ta gama sallah kenan da zumbulelen hijabinta mai hanu kalar blue mai duhu fuskarta ta kara haskawa a cikin hijabin , tana shiga ta ja tayi tsaye tana yatsina , taso taga wani abin fada sai dai bata ga komai ba domin dakin tas a gyare ga kanshin turaren wuta da yake ta ja tsaki ta ce ” Ke yar talakawa tashi maza ki kawowa mijina abin motsa baki domin shi baya kyankyanin tsohuwar nan kiyi maza ina jira , ta juya kwas kwas ta koma falon bata cire takalmin kafartata ba

Yar Mahaukaciya ta mike tana fadin daman na sani yau tawace ta sameni , ta fito cikin nutsuwa ta nufi kicin din falon inda suke ajiye jus jus kalakala ta bude frij din ta ja ta tsaya , ita dai bata san wani kala yake sha ba ta rasa wane zata dauka kawai ta rintse ido ta dauko guda exotic karami dan naira dari uku ta dora saman faranti ta dauko abin zubawa ta juyo tana tafe tana adu’ar Allah ya taimaketa kar tayi laifi , ta kusan isowa cikin falon taji Sahla ta kwala wani ihu ta shiga rawa tana ta kakaba dariya Yar Mahaukaciya ta ja daidai kapet din ta tsaya ita bata karasa ba ita bata koma ba

Sahla cikin murna ta ce ” wai dan Allah da gaske kake zaka aure ni? Dan Allah yaushe ? Wayo dadi kasheni Ashe daman kana son nawa?

Mubasshir ya girgiza kai yana kalonta uwa zautata sai ihu take wai na murna ne 

Tana tsaka da murnar tata ta waigo ta ga Yar Mahaukaciya ta zuba mata manyen idanuwan nan nata ya na mage tana kalonta saida gabanta ya fadi dan kuwa ba karamin kyau taga tayi ba cikin bacin rai na ganin jus din da ta dauko ta nufeta ta kifeta da mari cikin fada ta ce ” ke jakar ina ce? Ki rasa jus din da zaki daukowa Honorable sai wanan? To yayi mai da jus din dari uku? Ke dan kin saba shan sa sai ki kawowa mijina? To bari ki ji KO karena yafi karfin ya sha kalar jus din nan bale Honorable

Yar Mahaukaciya da tunda ta mareta ta saki farantin gaba daya kayan saman suka zube kasa tayi Saurin tsugunawa tana kwashewa gaba daya jikinta na kyarma

Muryar Mubashir ta sakata dago da kanta cikin gagawa domin bata taba jin muryarsa a haka ba

Mubasshir ya ce “””””””

😟😟😟😟😟😟😟😟😟😟

[9/20, 13:53] Umar Dalha: 🇳🇪Belles écrivaines du Niger

*’YAR 👧🏻*    

         *MAHAUKACIYA👹*

*_Na SAJIDA_*

            18

Mubashir ya ce ” ki guji batawa mutun rai a duk inda kike kiyi kokarin ganin kun wanye lafiya da mutun , ya juya wajen Sahla ya ce” ki je ki kawo min kalar Wanda kike si na sha din , Sahla ta juya tana matukar mamakin canjinsa na lokaci daya da  da ne Hasan sai yayi mata fada tayi murmushi ta ciro wayarta dan tayiwa kawarta albishir mai dadi

Bayan tafiyarta ya dan kali wajen Yar Mahaukaciya Wace ta sala hanunta cikin kwalbar nan tana tsincewa tana ta hawaye domin ta tsorata da  fadan da Sahla da mijinta suka yi mata a fada mana wanan ai shine a dakeka a hana ka kuka yanzu da hajiya tana nan ai da bata bari sun yi mata wanan wulakancin ba , aman ba komai zata kara hakuri har Allah ya bayana mata Yar Mahaukaciyarta su tatars su nemi wata bolar su domin kuwa konciyar hankali yafi kudi ,

Mubashir ya sauke ajiyar zuciya ya danyi murmushin abinda yake sakawa a ransa daidai nan muryar Malan yana salama Yar Mahaukaciya tayi Saurin dago kanta tana kalon kofar ta amsa salamar tare da yin kicin da sauri ta fito tana goge hanunta da tsuma ta nufi kofar falon ta bude sai ga Malan yunus yana murmushin sa

Yar Mahaukaciya cikin murnar ganinsa ta duka har kasa ta ce” Marhababika Malan ina yini an zo lafiya? Ya hanya?

Malan yunus yayi Murmushi ya ce” Lafiya lau Rahama ya na sameki ya kuma gida?

Ta ce” lafiya Alhamdulilah

Ya ce Masha Allah , Masha Allah , daman nazo na shaida miki zamu mayar da karatun mu da dare domin mai gidan yayi kirana ya fada min ya sama miki wata makaranta ta boko ita kuwa wuni ake a can , kin san kowane yana da anfani dan haka sai a maida hankali Allah ya kama mana

Yar Mahaukaciya cikin jin dadi domin harta manta marin da aka gaura mata ta ce” Alhamdulilah Allah abin godiya

Suka yi salama da Malan Yunus ya juya KO cikin dakin bai shiga ba dan kuwa sunyi da idriss sai na dare kuma daga gobe zasu fara ,

Ta Mike ta rufo daki sai murmushi take dokawa kuncinta na lobawa suka yi ido hudu da Mubasshir Wanda tunda ta bude dakin ya tsura mata ido , suna hada ido ya kawar da kansa a ransa ya ce” who is she??????? (Entouka i don’t know)

Cikin nutsuwarta ta raba ta gefensa tayi shigewarta dakin hajiya ta rufo tana adu’ar Allah ya kawo hajiya lafiya tayi mata albishir

Sun jima shi da Sahla suna zance ba laifi yana observing dinta idan tayi tayi sai ta tambaye shi ya fahimceta? Shi kuwa sai ya gyada mata hakan kuwa sam baya damunta domin ta saba da rashin maganarsa ita dai ba aikin bokan mamarta ya ci bâ; maganar ma zai koya gaba gaba ( to fa )

Karfe shida da rabi ya mike domin yaga alamar Hajiya ba dawowa zata yi ba suka fito tayi masa rakiya har wajen motarsa ya shige ya tafi ita kuwa ta nufi wajen mahaifiyarta dake jiranta su tatauna

[9/20, 13:53] Umar Dalha: 🇳🇪Belles écrivaines du Niger

*’YAR 👧🏻*    

         *MAHAUKACIYA👹*

*_Na SAJIDA_*

                19

Tana shiga Hajiya Marhaba ta ce ” tun dazu ina zaune ina zuba idon ganin kin dawo fada min nawa ya ce za’a kawo kudin tambayar

Sahla ta ce ” Momy bamu yi wanan maganar ba kin sani sarai tuwon girma miyarsa nama kin san abin mamaki za’a kawo mana ya ce fa a cikin satin nan yake so a kawo komai tunda na fada masa Dad zai dawo gobe kinga kawai sai ayi ayi a amshi kudin muma mu shiga shirye shiryen mu

hajiya Marhaba ta ce” Ohk tohm ai ba damuwa sai muyi jiran dawowar Elhajn

Ba Hajiya Hawau ta dawo ba sai karfe Takwas Idriss ya biya ya daukota suna tafe yana mitar ta bar yarinya ita kadai a gida tun tana kyale shi har tace” yo to kaji ubana ai sai ka kawo min duka , yanzu ayi mana mutuwar ka hana ni zaman makoki dan kin Allah? To KO ubanka bai isa ya hanani balatana kai ehe , nan da jikana ya rasu har kwana tayi a gidana tana tayani jaje dan ita ta isa da iyalanta ba Wanda ya bi sayunta ya titsiyota a gaba ya korota gida sai ni da aka raina , ni dai Idrissu ka fita a idona na rufe Aradu tohm

Idriss yayi gum da bakinsa sai a lokacin yayi mata  maganar ya samawa Yar tata makaranta
har an gama uniform dinta da komai sai dai direct secondry ya kaita aman da masu yi mata lesson dan dai kawai ta kara wayewa ne ta san wani abin

Hajiya ta washe baki kamar ba itace yanzu take fadan an dameta ba ta ce” Allah yasa ka gama da duniya lafiya yanda kake kokarin faranta min ni da yata Allah ya baka mai faranta maka Allah ya jikan kakanka kuma sai hawaye aka ci gaba da fadin sak irin halayensa ne ka dauko Allah ya sa ya huta

Idriss ya gumtse dariyarsa don kuwa lamarin na Hajiya yanzu dariya yanzu kuka kai Allah ya sa muyi tsufa mai anfani , ya Mike yayi mata salama ta rufo dakin nata ta kashe komai itama ta yasu sai barcin gajiya .

Tunda asuba bayan sunyi sallah Yar Mahaukaciya tati wanka Hajiya ta miko mata kayanta dogon wando ne da riga daidai gwuiwa da fararen safa kayan ma farare  ne tas sai bakin hijabi mai hanu da kuma bakin takalmi mai dan tudu mai igiya , makarantar ta yayan manya ce shima ta kan Mubasshir ya bi aka dauketa sanan aka daukar mata malaman da zasu kula da harkar karatun ta ya kasance tayi gagawar iya turanci KO test baza’ayi mata ba dan ya fadi gaskiya bata iya komai ba .

Cikin minti talatin ta gama shiryawa ta daure gashin kanta da kyar ta saka hijabin Wanda yake da tsayi sosai domin har ya fi rigar tsayi ta juyo cikin nutsuwa ta fito wajen Hajiya Hawau da ta gama mata abin kari da kuma zuba mata wani a kwano ta saka mata a jakar da kudin abinci idan ta cinye wanan abincin , tana fitowa ta gaisar da Hajiya

Hajiya ta ce” kai kayan nan sun karbeki Ramatutu wly sunyi miki kyau nasan duka sai kinfi yaran kyau

Yar Mahaukaciya tayi murmushi ta ce” Hajiyata kings hijabin harda wajen fitar da hanu

Hajiya ta ce ” kema kya fada zamani , tashi mu je muyi jiransa kar ya tafi ya barki ga abincinki komai da komai harda kayan hada shayi idan kinje ki zauna ki karya sanan ki shiga ajin kinji KO?

Ta ce ” toh suka fito kofa wajen mai gadi suka zauna suna jiran fitowar Idriss Wanda KO daga baci bai farka ba

Sai karfe bakwai da rabi ya fito shima dan kar aje bata shirya ba suyi lati ranar zuwanta ta farko bai dace ba , yana fitowa ya hangosu Hajiya a zaune a yar tayani tsegumi ita kuwa a tsugune a gefenta ai besan sanda dariya ta kufce masa ba ya ce ” aiki ga mai kare ka

Haka ta Mike ta shiga ya tayar suka haura titi suna tafe yana yi mata bayanin yanda zata yi dan karta sha wahala sosai, ya ciro wani kati mai walwali ya Mika mata ya ce” wanan katin cin abincin ki ne na biya na shekarar gaba daya sanan na zabi na biya idan kinje kinada damar duk lokacin da kika ji yunwa ki shiga restaurant ne part VIP ki shiga can ki zabi kalar abinda kike sha’awar ci a kawo miki ki ci ki dan huta kiyi sallah sai ki huce wajen karatun ki , karkiyi wasa da karatun nan naki domin kafin ki fahimci lesson sai kin sha fama tunda baki iya rubutawa da karantawa ba aman da yardar Allah zaki iya harma ki koya min , ya karasa yana murmushi ‘

Tayi murmushin itama ta miko hanu ta karba tana godiya ta ce” ai kuwa kaga Hajiya har ta zuba min kayan abincina a jaka

Ya kwalalo ido ya ce” to kaji yo ai baza’a barki ki shiga da wani abinci ba gudun karki zo da abinda zai bata miki ciki kuma a tsayar da karatun KO wani ya ci ya bata masa ciki a samu matsala , makarantar nan akoy shegen tsaro dan haka ki kiyaye ki dena zuwa da komai wanan din ma ki juye shi a nan idan kin shiga kya karya  , hakan kuwa akayi ta juye komai ya rakata har kofar shiga daidai nan aka tsayar da shi ita kuwa aka caje Jakarta aka rage litatafan aka ware na ranar abinda zasu yi sai  wani litafin aka saka mata dan saboda karatun da zata ringa dauka da wasu malaman bayan aji .

                   ❤

🇳🇪Belles écrivaines du Niger

*’YAR 👧🏻*    

         *MAHAUKACIYA👹*

*_Na SAJIDA_*

                    20

Haka Yar Mahaukaciya ta shiga cikin makarantar ta nufi office din da aka nuna mata taje ta ja ta tsaya ta shiga rapka salama ta kai wajen minti biyar a nan a tsaye sai da wani dalibi ya zo ya dana wani jan abu sai taga kofar ta bude ya shige ta kwalalo ido tana nan tsaye ya fito yayi tafiyarsa ta lumshe ido tayi bismillah hanunta na karkarwa ta dana jan abun kofar ta ce wani guiui ta bude ai uwa an hankadata ta fada sai zazare ido take tana kifkif da ido

Mutumin dake zaune ya hakimce da shigar manyan kaya a jikinsa gefensa kuwa da wasu mutane sai dadana computer suke gaba kadan da shi kuma jerin wasu mutanen ne suna observing dalibai a computer ita dai tayi tsai tana kalon su yayi gyaran murya ya mika mata hanu da nufin ta bashi takardarta Wace idan tazo zata gabatar a kaita aji a nuna mata komai

Ai gaba daya takardun hanun nata da litatafen da jakar ta ajiye masa saman table din nasa na glass ta ce” wly sun caje ni kosan ma yaya ya juya da shi KO karyawa banyi ba

Nan da nan suka shiga kalon juna , banban na zaune Wanda ke hakimce ya ce” ur name?

Yar Mahaukaciya tayi Kifkif da ido tana kalonsa fuskarta bayane da tsoro kafin tayi magana téléphone din saman table din yayi ringin ya Mika hanu ya daga

Daga dayan bangaren ya ce ” tazo KO?

Abdallah mai kula da makarantar ya ce” aa dalibai dai suna ta shigowa har yanzu bamu ga mai sunanta ba aman ga wata tsaye inajin bata iya turanci ba ma

Mubasshir ya ce” what? Na fada maka yar gidana ce kuma akoy abinda ya tsayar da ita ba’a kula da karatunta ba kayi mata hausa idan tazo shine zakana cewa baka sani ba ? Look idan kaga bazaku kula kan karatunta ba na tura a dauko mini ita , karatu KO a Wace kasa take so sai na kaita kuma KO wani kalar malami sai na sama mata ya koyar da ita

Abdallah ya ce ” kayi hakuri abin du bai kai nan ba yaya sunanta ne?

Mubasshir ya zaro ido yayi Saurin rufe kan wayar ya kali idriss da ya saka shi a gaba kan a kula kar su banzatar da ita ya ce” kai sunanta fa?

Idriss ya dane dariyarsa ya ce” *RAHAMA IDRISS*

Mubasshir ya yatsina fuska ya kara a kunan sa ya ce” Rahama idriss

Abdallah ya tambayi Yar Mahaukaciya dake tsaye da hausa ya ce” kece Rahama Idriss?

Da Sauri ta gyada kanta ta ce ” eh Nice

Abdallah ya ce” sir itace a kara hakuri zata samu kyakyawar kulawa

Mubasshir ya ce ” ohk thx ya datse Kiran

Abdallah da kansa ya mike ya raka Yar Mahaukaciya aji Sanan yayiwa malamin bayanin idan ya gama ya nuna mata office din hajiya Amina , ya juya ita kuma ta samu waje ta zauna ta shiga kalon Malan yana ta gwaranci toh gwaranci mana domin ita dai ba abinda take ganewa a cikin abubuwan da yake fada tana dai kalonsa har ya gama ya kaita wajen Hajiya Amina inda ta kwashe awa uku tana koya mata A B C D ……Z, sanan taje wajen cin abinci inda ta sha mamaki kamar ba a cikin makarantar yake ba kuma gaba daya sai daukan ido wajen yake nan taga manya manyan yan mata da samari kowa yana harkokinsa wasu suna ta selfi wasu suna buga gem , wasu suna ta labari, wasu suna zance, wasu kuwa suna jiran abincin su kai wajen ba dai tsaruwa ba , 

Cikin tsoro ta nufi wani table mai shegen kyau Wanda taga ba kowa samansa sanan harda wani rubutu a farar takarda ta nemi waje tayi zamanta da bismillah tana dan yarfe hanunta domin ba komai a hanun ta mugun gaji ne da rubuta A B C din nan , tana zama bata ma gama hutawa ba taji muryar wata cikin turanci na fadin tayi ta tashi ga princess nan zuwa table dinta ne ,

Abinka da Wanda bata san mai take cewa ba kawai sai ta dan sakin mata murmushi ta waiga dan taga inda zata kai katin ta a zuba mata abinci ta
ci ta koma masalaci ,

Bata Ankara ba sai ji tayi an daki table din ta dago kanta da sauri tana kalon wace ta buga table din , wangalau tayi da idanuwanta tana kalonta batada KO dan kwali a kanta ta sha kananan kitso na atash sun mugun yi mata kyau , ta kara girar ido sunyi zako zako ta sha lips dinta mai sheki gwanin kyau gata fara kar ta budi baki cikin turanci ta ce ” ke yar gidan uban waye harda zaki zo ki dora tsumakaran duwaiwanki a saman kujerarr da ni nake zama?

Yar Mahaukaciya bata kauce idanuwanta daga kalonta da take ba ita mamaki take Kenan ana zuwa makarantar babu hijabi KO dan kwali?

Ita kuwa ganin kalon da take yi mata da idanuwanta kamar na mage kuma ta ki yi mata magana yasa cikin zafin rai ta saka hanu ta ja hijabin Yar Mahaukaciya tana fadin shegiya mai acuci bari na tona miki asirin abinda kike boyewa a hijabin yanzu haka wani kurji ne da ke daidai lokacin gaba daya daliban wajen sunyi ca suna kalonta dan kowa yasanta da rashin mutunci yar gidan embasader ce table dinta ba mai zama mutun daya take shayi shi kuwa yayi kwana uku bai zo makarantar ba shi yasa take taka rawarta yanda take so a makarantar, kuma taga bakuwar fuskar nan tana kokarin kawo mata raini dole tayi maganinta

Da karfi ta idasa Jan hijabin Yar Mahaukaciya harda ribom din da ta daure kanta da shi ya biyo hijabin gaba daya gashinta ya barbazu har gadon bayanta cikin gigita ta Mike tsaye ai kaf wajen suka kwashi waouh domin sai da ta Mike dirinta ya fito ita kuwa baiwar Allah kokarin ganin ta kame kanta take suna tsaka da wanan rigimar chef din cafetariar ta fito itama ta sha ado da masarar Riga a daure a tsatsonta ta fito cikin turanci tana tambayar mai yake faruwa?

Princess da gaba daya jikinta yayi sanyi domin sai da ta raina kanta duk irin tarin adon nan da ta sha kuwa sai taga tamkar wata banza a  Yar Mahaukaciya ga kalar gashinta kalar blonde kuma gashinta ne ba atash bane ga tsahi da gareshi ga shegen santsi ga yanayin jikinta da ka ganta ka san daga gidan hutu ta fito ,

Wani daga cikin daliban ya ce” aunty wanan mai kyau ce ta zauna a table din princesses shine princesses take fada

Aunty ta kali Yar Mahaukaciya ta ce” ina katin ki yarinya ?

Yar Mahaukaciya jin an ce kati ta gane na cin abincinta ake tambaya ta juya nan kasa inda ya fadi ta dauko ta mikawa Auntyn ,

Aunty ta zaro ido ta ce” kai princesses kin san da wa kike magana kuwa? Kinsan du wanan gyaran da muke tunda safe na tarbanta ne ? Kinsan KO yar gidan wacece?

Gaba daya suka bada hankalinsu wajenta har Yar Mahaukaciya domin yanzun da Hausa tayi magana don kuwa ta tsorata kar wanan yar masefar princesses din ta ja musu asara dan an hau shegen table dinta , ita kuwa yar mahaukaciya tambayar kanta take to ita kuwa Yar gidan waye harda za’a yiwa yar gidan ambasader fada dan ta taka ta ???

Nima ina son sanin amsar wanan tambayar???????????????????????????????????

🇳🇪Belles écrivaines du NigerTunda garin Allah ya waye jama’a ke kai kawo manya manyan mata masu ji da kansu kawayen Hajiya Marhaba , tayi wanan gayar ne dan kawai a tsayar da shagulgulan da za’ayi mawakan da za’a dauko har na wajen diner , da sauransu

Sahla ce ta fito daga dakinta tana waya , Hajiya Marhaba ta ce” beby ina kuma zaki je haka?

Sahla ta juyo ta ce” mom zan je na zabo kalar Wanda zan dora , tayi kirana ta ce ta kawo su jiya

Hajiya Marhaba ta ce ” Ohk karfa ki yarda ki jima, sanan ki san da kinyi lulubi saboda kin san ya hane ki fita so ki kula

Sahla ta amsa mata tayi gaba abinta

Idriss ya dago kansa ya kali mahaifinsa ya ce” ina yaro ban taba ganin mutun mai biyayar iyaye kamar ka ba abanah, aman tunda na kawo shekara goma sha uku a duniya sai naga ka fara janyewa da Hajiya , Abanah karka manta Hajiya kai kadai gareta danginku duk babu, Abanah yar uwarta daya ba mai aure a nan bace bata da labarinta ma , shin Abanah idan ka samu dan lokaci na ka zauna kadan da kakata bazaka je ka gaisheta ba ? Tana matukar nisa rashinka a cikin zuciyarta kuma nasan bata barci Haba Babana karka manta fadar Allah ce mu maza mu bi iyayenmu matayenmu kuwa su bimu dan samun tsira a gobe kiyama, a kulun idan muka zauna da ita sai na bata hakuri sai tayi murmushi ta ce ba komai ,  ya hade hanayensa ya ce” kayi min rai Abanah ka gyara koma meye tsakaninka da Hajiya ka koyar da mu kulawa da tamu mahaifiyar 😌

Mahaifin Idriss , Ilyas ya kare masa kalo gaba daya jikinsa ba kwari ya ce ” Idriss please tashi ka bani guri ina bukatar tinani

Idriss ya mike yana adu’ar Allah ya sa mahaifin sa ya gane

Bayan fitar Idriss Elhaj Ilyas ya mike ya har wani juwa yake yana mamakin kansa, mai yake sha’afar da shi da mahaifiyarsa? Yaushe rabonsa da ya kai mata abinci ya zauna ya bata ta ci yana yi mata hira? Mai ke damunsa? Cikin Sauri ya juya daga office dinsa ya shiga motarsa ya nufi gida , yana zuwa ya bar motar a kofar gida gudun kar Marhaba ta Ganshi ya dawo yanzu

Cikin Sauri ya fada bangaren Mahaifiyar sa , sai da ya lumshe ido domin Hajiya ba dai kanshi ba , kulun cikin zambada tiraren huta take na hayaki kalakala , ga tsakar gidanta sai ka yarda Abu ka dauka ka cinye, kai ba dai tsafta ba Allah ya bata abinta ,

Cikin faduwar gaba yake takawa a hankali yana dosar dakin bugun zuciyarsa na tsananta , kuma wani bangare na zuciyarsa na korarsa ya rasa meye wanan, aman a yau kaunar ya ga Hajiya ta rinjayi kin ya ganta,

Sautin dariyarta ya tsinkaya tana fadin” kai aman akoy aiki kwabin fulawa wajen yan mata kadai ta isa ta saka bawa ciwon ciki dan dariya

Yar Mahaukaciya da ta takarkare zaune a saman tabarma ta saka Roba baba tana kwaba fulawar da zasu yi fanke na mutanen hajiya tunda Hajiya ta zuba mata kilo biyu ta kasa kwabeta sai nishi take ita kuwa Hajiya ta ce ai kuwa sai ta koya

Salama yayi inda cikin zabura Hajiya ta dago kanta ta zubawa fuskar gudan jininta ido , kasa amsa salamar tasa tayi dan tsananin mamaki ,

Suna yin ido hudu ya dauki sauki ya je da Sauri ya tsuguna ya dora kansa saman ciyoyinta ya rike kafafuwanta daga kasa ya saki kuka kamar karamin yaro

Yar Mahaukaciya dake zaune ta waigo ta zaro ido , tunda tazo gidan nan yau kadai Allah ya taba hadata da mahaifin Idriss daga kamar ta gane cewar mahaifinsa ne , da Sauri ta Mike ta basu waje

Ya kusan minti goma yana ta kuka a saman cinyar Hajiya Hawau , Wanda kukan ke ratsa duk wata gaba ta jikinta , ta rasa ya zata yi sai ta daga hanunta zata shafa kansa sai ta kasa , ji tayi an daga hanunta an dora saman kan Elhaj Ilyas ta dago kanta tayi ido hudu da *Mubasshir* ya sakar mata wani lalausan murmushi sanan yayi mata nuni da ta kula baban, baiyi magana ba gudun kar ya ganshi a haka ya shige a hankali dakin Hajiyar .

Cikin nutsuwa Hajiya ta ce” mai yake damunka Dan gidan Hajiya?

Da sauri ya dago kansa ya kuma rushewa da kuka yana fadin dan Allah ki yafe min , wly ban san abinda yake damuna ba , na rasa nutsuwata na rasa abinda ke damuna , na rasa farin cikina Hajiya ki yafe min

Hajiya Hawau ta share hawayenta ta ce” kulun cikin yi maka adu’a nake Dan gidan Hajiya , ka sani Allah yana tare da mai gaskiya kuma ka kara riko da adininka Allah ya baka lafiya

Elhaj Ilyas ya ce” Amin na gode Allah ya kara tsawon kwana da lafiya , nan fa tsakani uwa da Da suka shiga hirar su

Mubasshir na shiga ya tarda Yar Mahaukaciya zaune saman wata kujera mai tsayi tana kalon madubi da macaji ( masarci) a ganunta tana caje gashin kanta da kyar sai nishi take dan kuwa daga ta caje sai ya koma ya nanade kansa haushi ya kamata ta wurgar da macajin tana fadin wly sai na askeka gaba daya ma na huta , haka kawai

Mubasshir dake tsaye yana kalonta yau dai yay
i niyar sai ya san wai atach ne take sakawa KO kuwa haka kalar gashinta yake ,

Yayi gyaran murya ,

Da Sauri Yar Mahaukaciya ta kale shi , sam bata ji karar shigowarsa ba , kuma tirarensa da ya zama KO da yaushe yana gidan sai ya kasance kanshin tiraren KO yaushema jinsa take a hancinta hakan yasa KO yanzun da tana caje kanta ta dan ji kanshin bata wani kula ba , tana ganinsa ta shiga neman hijabinta da a tinaninta saman bed din Hajiya ta ajiye shi , da Sauri ta bude akwatinta ta dauko na makarantarta ta zumbula Sanan ta shiga kikifta ido,

Mubasshir shi abin nata dariya ma ya bashi wai kariya bayan bugu , aman sam bai daran ba  ya ce” menene kike kokarin rufewa tamkar naki bayan kin loda gashin doki KO na matacen mutun a kanki ?

Yar Mahaukaciya jin an ambaci ta loda gashin matacen mutun a kanta ya saka ta kwalalo ido waje ta ce” karde aje gashin nan na matacen mutun din ne?

Mubasshir ya kaleta a ransa ya ce zata raina min hankali , a fili ya ce” ya zanyi miki tambaya kiyi min ni ma?

Yar Mahaukaciya tayi kalar tausayi ta ce” wly kaga gashin mutane duk baki ne, gashin Fati ma baki ne, haka na princess da su Tina su Mariam duka baki ne, kaga kuma ance idan mutun ya mutu gashinsa fari yake zama, kuma ni tun ina yarinya yara idan suna bina sai suna cewa Yar Mahaukaciya mai farin gashi matata,      ……     Maganar ta tsaye mata a makogwaro lokacin da ta ambaci sunanta a gaban Dan Aljannah da Sauri ta rufe bakinta ta tura bayi tayi shigewarta

Mubasshir dake tsaye yana sauraronta gaba daya zancen ya shige masa duhu mai take nufi da yara na kiranta da *Yar Mahaukaciya*? Mai hakan ke nufi?

Sahla dake labe tana sauraron su ta jiyo gaba daya abinda suke fada ranta ya gama baci ya mijin da zata aura ya zo yana magana da wanan banzar? Kuma taji Ashe ma ita din *Yar Mahaukaciya ce*, ai kuwa zata fadawa momy tun wuri ayi maganin wanan abin tun kafin a jaza mata bala’i

Wayo Yar Mahaukaciyata

🇳🇪Belles écrivaines du Niger

*’YAR 👧🏻*    

         *MAHAUKACIYA👹*

*_Na SAJIDA_*

                    24

Sahla na fita ta ficewarta ta nufi cikin gidan su, tana zuwa ta shige dakin mahaifiyarta tana haki,

Hajiya Marhaba na ganin yanayin yar Tata ta Mike ta nufi dakinta tana fadin tana zuwa, tana shiga ta tarar da Sahla tana ta haki ta ce” Beby lafiya?

Sahla na ganin mamarta ta fashe da kuka har tana  buga hanayenta jikin bed tun karfi

Hajiya Marhaba ta je da gudu ta rike hanunta tana fadin Beby wa ya taba miki zuciya haka? Fada min uban wa ya taba min ke? Idriss ne KO?

Sahla ta shiga sauke ajiyar zuciya ta ce” mom ni fa kawai a kori yarinyar nan daga gidan mu , gaskiya ta fara fice Gona da iri ,

Marhaba ta ce” wace yarinyar?

Sahla ta ce ” wanan mai kalar fatar zabaya mana,

Hajiya Marhaba ta ce” toh mai tayi ?

Sahla ta dago kanta ta ce” kinga irin yanda Yaya Idriss ke kashe mata kudi kuwa? Sanan yarinyar uwarta Mahaukaciya ce , tana nan tana hauka kina son samun sirika Yar Mahaukaciya ne? Kuma duk da Mubasshir ya tsaneta hakan baya hana shi zama inda take, kinga tun wuri kiyi maganinsu dan kuwa yau naga dad a wajen Hajiya .

Hajiya Marhaba ta zabura tana dafe kirji ta ce” what? Dadyn naki ne ya tafi wajen Hajiya? To mai yasa bai fada min ba? Mai yaje yi wajenta ? KO dai asirin nawa ya karye? Kam akoy matsala ,

Ta juya ta dauko wayarta ta dana kira tayi ciki ta bar Sahla zaune tana dariyar cin galaba , sanan tayi kwafa tace” da naso na barki ki dan gana da danki aman tunda kika fifita wata bare a kaina ni da ke sai dai sheri ba dai khairi ba ( Allah ya shirya mana yayanmu )

Mubasshir ya jima tsaye bata fito ba kuma yaji tafiyar Aban Sahla hakan yasa ya juyo ya fito ya yiwa Hajiya salama ya nufi gidansu zuciyarsa cunkushe da abubuwa kala daban daban,

Yana shiga yaji sautin wakar larabawa hakan yasa cikin farin ciki ya dan kara Sauri ya isa baban falon mahaifiyarsa , ai kamar jira ake yana saka kafa yaji gaba daya an shiga watsa masa tirare , ta ko’ina wasu na fesawa sai hamdallah suke , daga gefe kuwa Ashe mawakiyar ce suka zo da ita takanas sai yi take tana juyin nan na larabawa,

Mubasshir ya sada kansa kasa da kyar yake iya cira kafarsa yana dana sanin zuwansa a wanan lokacin gashi suna kokarin rikita masa lisafi ,

Hajiya Fareedah ce ta taso ta kama hanunsa ta karaso da shi kusa da mahaifiyarsa ta ce” yarona an girma, Alhamdulilah yau har zan wankeka , Allah mai kyauta da kari ,Mubasshir ya zama ango

Mahaifiyar Mubasshir tayi murmushi da taga sai kawar da kai take , tasan baya son kida yayi yawa , baya son yawon hayaniya, inda ya sha banban da ita domin ita tana mugun son mutane tana son KO wani motsi zata yi ta jita kusa da mutane ,

Ta ce” nurul’ayne mai yake damunka?

Hajiya fareeda tayi caraf ta ce” ku shiga daga ciki mana sai ya fada miki aman a nan bazai yiwu ba tunda kinga akoy mutane da yawa

Mubasshir na jin an bashi damar tashi ya Mike yayi sama , ya nufi dakin mahaifiyarsa ya konta ya lumshe idanuwansa yana fadin wacece ita? ( wai mai ya shafeka malan 😏 )

Cikin nutsuwa ta turo kofar ta shiga da salama aman bai ma san ta shigo ba , ya lula duniyar tinani ,

A nitse ta ISO ta tsaya a kansa tana mamakin abinda yake saka Mubasshir cikin tashin hankali haka tana mamakin abinda ke saka shi tinani haka , KO yana tina mahaifinsa ne? KO taron nan da yayi yawa ne yake damunsa?

Ta kai minti ashirin a tsayen nan bai san tana wajen ba hakan yasa ta matsa ta zauna kusan sa ta dago kansa ta dora saman cinyarta ta ce” mai yake damun Mubasshir da har ya kasa fadawa mama?

Mubasshir ya dago kansa ya ce” maman Mubasshir al’amuranta na mugun daure min kai

Mahaifiyarsa ta ce” Al’amiran wa fa?

Sai a sanan ya Ankara da abinda yake fada ya dago idanuwansa da suka rine ya ce””””””””,,,,,,,,,,,””””””””””

[10/3, 13:50] Umar Dalha: 🇳🇪Belles écrivaines du Niger

*’YAR 👧🏻*    

         *MAHAUKACIYA👹*

*_Na SAJIDA_*

                      28

Wani ma yayi rawa balatana dan makadi, sisterna rabin jikina , ke din ta daban ce , wanan babin gaba daya naki ne Madame Abdul Kader *Maman Imran* love u so much

                 Labari

Ya dade yana wanka dan saboda sai da ya shiga ruwan zapi sosai ya wanke harda kansa ya dauro banban towel ya fito ,   yana fitowa ya ga Maman sa ta ajiye masa kayan da zai saka da komai saman bed

A nitse ya zauna ya busar da gashin kansa uwa na mace dan santsi da shekin baki ,ya dauki mayukan gashi ya shafa

Shi da kansa yake nanade kansa ya saka macaji ya daidaita shi yana jin haushin saurin taruwar gashin kansa kawai sai ya aske ya huta, kuma sai ya fito

Cikin nutsuwa yayi shirinsa ya gama ya dauko kayan , yana dagawa yaga manyan kaya ne gari da yar ciki da hula sun sha wani mahaukacin zubi a jikinsu hular kanta wani irin aiki ne aka yi mata sosai ta hadu , abinka da mai son manyan kaya , yayi murmushi a fili ya ce ” Maman Mubasshir Kenan

Su Idriss na  suna ta labari suna dariya
su uku daidai suma sun sha manyan kayan su sai anuri suke abinka da ranar fito na fito

Mubasshir ya sauko cikin takun kasaita tamkar dan Sarki daidai da takalmin kafarsa na shadar nan ne haka agogonsa mai zubi ya sha hularsa , yana ganin su ya saki murmushi

Nura ya ce ” waouh , waouh , waouh , wata miyar sai a makota , wai dan Allah kaine kuwa?

Mubasshir ya Mika musu hanu daya bayan daya suna gaisawa sanan cikin murmushi ya ce ” angoncewa ce

Idriss ya sha kunu ya ce ” kai kasan gaban manya fa kake

Mubasshir ya ce ” meye manya? Yana wata yatsina

Ramadan ya ce ” ya ilahi sirikinka ne fa

Mubasshir ya mike yana fadin ” kunga mu yanzu mun zama masu iyali ku tashi mu nufi gidan iyayena na gaisar da kakata sai iyayen matata a al’adar chadi

Suka Mike suna murmushi , fitowarsu keda wuya wanan mawakiyar ta larabawa ta kwasa sai koda Mubasshir take , dago kansa da zai yi ya hango gimbiya Mubinah yar gidan sarkin Makah cikin shiga ta alfarma ta zuba zinari da wani mahaukacin lesh fari gata fara sai daukan ido take ,

Suna fitowa ta mike ta nufo Mubasshir Wanda sai da gabansa ya fadi a ransa ya ce ” ya akayi mai martaba ya BArTA ta biyo su mai girma Barhan?

Tana isowa ta rungume shi irin gaisuwar larabawan nan sanan daidai kunan sa ta rada masa ” na zo na raka mijina gidan amaryarsa da tayi min shigar wuri kafin na shigo

Mubasshir ya dan saketa ya lakaci habarta yayi murmushi sanan ya juya wajen iyayensa yayi Saurin tsugunawa yana gaisar da su

Hajiya ta taso ta kama hanunsa ta daidaita masa hularsa ta ce ” Alhamdulilah yarona ya girma , Allah ya kade baki ( kunsan larabawa suna mugun gudun baki shi yasa daga sunyi magana sai kaji sun ce Masha Allah , 😁 )

Haka sukayi ta saka masa Albarka sanan suka juya inda wasu motoci kwaya hudu a jere farare tas sai sheki suke , yau yau aka fitar da su da ka gani ka san an cashi kudi a nan ,

Karar tafiyar doki naji na waiga wani ne ya taho da dokina biyu  yana jaye da su da irin runfar nan ana jaye da su , sai karar kacaukacau suke sun mahaukacin sha ado na zinari sai kara suke

Mubasshir ya juya ya sauke idanuwansa saman Mubinah dan kuwa ya san wanan aikinta ne ya gala mata harara dan ta sani sarai ya tsani hawa doki KO a can su biyu suke hawa KO da ita KO da wani a gefen sa ,

Tayi murmushi cikin harshen larabci ta ce” kar a yada al’ada ka sani sarai da a can ka yarda kayi aurenka da sai ka zaga gari a saman doki dan haka ya sa na shirya wanan KO ba komai ka girmama al’adar mai martaba uba a wajenka

Da haushi haushi ya taka ya hau itama aka kama mata ta dare tamkar itace amaryar ,motocin nan suka saka su a tsakiya , mai girma Barhan ya karaso ya rufa masa alkyaba aka cire masa hular aka rufa masa ta alkyabar nan dan kuwa haka al’adarsu take

Cikin nutsuwa suka kama hanyar gidan su Sahla

Hajiya Hawau ta sha dinkinta na shada ta hade harda kafa daurin dan kwalinta sun malaya manyan tabarmi a tsakar gidansu da kawayenta tsofafi sai labari ake ana shan fura mai cukui sai kanshi take ga dadi abinka da tsohuwar da ta san darajar baki duk Wanda ya shigo Yar Mahaukaciya da kawarta Fati sai su zuba furar a cikin kwarya da ludayi su Mika masa , suma sun sha dinkinsu na shada duk da ba wata kwaliya suka yi ba dalilin ainkin da suke yi

Suna tsaka da shan dariyarsu suka jiyo karar ganga da kuma muryar mace tana ta ISO da larabci tana wakarta , ga Wanda ya iya ya san dan gata ake wakewa ga Wanda bai iya ba kuwa sai dai ya gyada kai dan dadin wakar

Fati  ta kama hanun Yar Mahaukaciya ta ce” kawata ai angwaye ne

Yar mahaukaciya ta ce” mai ya kawo angwaye nan kuma a yanzu?

Fati ta ce ” oho o mu dai mu shirya tarban su

Hajiya Hawau ta fado kincin din ta ce” Ramatutu ai ga Dan Aljannah nan ya ISO da tawagarsa kinga wa’incan kwaryoyin masu zane su za’a dauko a zuba musu furar , aman ai ke kinsan yanda ake dama ta dan Aljannah dan haka a dauko duka cukuii din da nonon a dame musu yi maza yar Aljannah

Yar Magaukaciya tayi murmushi Ganin irin yanda Hajiya ta rikice ta ce ” Hajiya ai na dame ta tun dazu Idriss ya ce a aa zuwan su duk da nayi zaton ko wasa yake mun dai dame kuma yanda kike sonta , aman ciki zasu shigo kinga baza a bar Dan Aljannahn ki a wajeba KO?

Hajiya ta sauke ajiyar zuciya ta ce” Allah yayi miki Albarka bara na sauke su a baban falon , ku kuwa ku jera furar ku kawo musu

Ta juya tana kara daure dunkunkumin dan kwalin da ta dunkuma

Yar Mahaukaciya haka kawai ta tsinci kanta da tsoron hada ido da Dan Aljannah a wanan ranar , mutun a ranar da ba ta aurensa ba ma yana mugun daukan ido bare a yau?

Fati ta ce” Malama Hajiya garin kidima har kofina take ambato 😁

Yar Mahaukaciya ta ce” Dole Hajiya ta rikice dan kuwa dan gatanta ne

Haka suka dauko kwaryoyin suka kara darwaye su , gasu kananuwa masu shegen kyau da ludayinsu masu kyan gaske suka jere a saman wani baban faranti na silba mai  shekin gaske , sanan suka ringa zuba furar nan suna saka ludayin a ciki , sai da suka gama

Yar Mahaukaciya ta ce ” plz my kawali ki dauko na Dan Aljannah dan Allah

Fati ta zaro ido ta ce ” mai kike nufi da hakan? Yayanki ne fa kuma kin sani sarai kar na fita na zubar garin kalonsa

Yar Mahaukaciya ta san sarai zata aika hakan yasa ta dauko wani farantin dan madaidaici ta zuba furar a wata kwaryar mai murfi sanan ta dauko ludayi ta dora a gefe ta dauko mushoir ( hankici ) sabo fil fari kar ta dora shima a gefe ta gyara komai

Fati dake kalonta ta ce” gaskiya al’adar Hajiyar gidan nan na mugun birgeni , koman ta daban ne sanan ta koyawa yar Jikanlen ta

Yar Mahaukaciya tayi dariya tana dora farantin Dan aljannah a gefen sauran furar ta ce ” kama mu tafi malama kar suyi tafiyarsu

Suka kamo suka fito suna tafiya cikin nutsuwarsu suna fitowa kanshin ya daki hancinsu daga fatin Har Yar Mahaukaciya suka dago suka zubawa bakin dakin kalo

Idriss da dan Aljannah sun saka Hajiya a tsakiya ita kuwa sai washe hakora take daga gefe guda kuwa Mubinnah ce sai fifitu ake yi mata ta sha kyau har ta gaji, sai su Ramadan da Nurah a wata kujerar abin gwanin ban sha’awa

Fati ta juyo ta kali Yar Mahaukaciya Wace itama kamar ta fadi dan yanayin Mubasshir ya kidimata harda Idriss abin ya mugun haduwa kawai sai taji eh lale tana iya yin soyaya da shi dan kuwa ya mugun birgeta a yau

Fati kuwa ta kidime ta haukace ta ce” kawata kina ganin zinaria ce fa a jikinsu dan Allah ki duba ki ga irin yanda AA ya zama uwa Kwaï dan daukan ido

Yar Mahaukaciya cikin rada ta ce ” ki nutsu mu basu juya tun kafin na kife a nan

Su duka suka dan saki murmushi sanan sukayi salama

Hajiya Hawau ta dago kanta ta amsa haka sauran jama’ar wajen

Cikin nutsuwa su Yar Mahaukaciya suka ajiye wanan farantin a saman table din dake ajiye a tsakar dakin sanan suka shiga dauka suna mikawa mutanen dakin , har sai sun duka har kasa su Mika musu hakan ba karamin birge hajiya Hawau da kuma su idriss yayi ba

                   🙆🏿

[10/3, 13:50] Umar Dalha: 🇳🇪Belles écrivaines du Niger

*’YAR 👧🏻*    

         *MAHAUKACIYA👹*

*_Na SAJIDA_*

                      29

Fati ta d
auko ta nufi Mubinnah tana isowa ta dan risina ta Mika mata da Sauri mai yi mata fifitar nan zata karba Mubasshir ya daka mata tsawa ” cikin harshen larabci ya ce” idan anzo waje ana anfani da al’adar su ce sanan nan gidan sirikai na kuma iyayena ne dan haka kar a kawo min batanci kin gane ?

Da sauri ta risina tana fadin Allah ya huci ran Dan Gattahn Mai Martaba mafi soyuwa ga gimbiya Mubinnah

Mubinnah duk da bata ji dadin yanda ya sacewa kuyangarta gwuiwa aman bacin ransa yafi komai daga mata hankali hakan yasa ta mika hanu ta karbin wanan kwabin da bata san KO na menene ba ta dan gyara zamanta tana shawara da zuciyarta shin zata sha ne KO aa

Su dai KO a ransu , Yar Mahaukaciya ta dauko farantin Mubasshir har a lokacin bata gama yi masa kalo ba tayi niyar bazata yarda tayi masa kalon kurula ba ,

A nitse ta nufi wajen da tafi jin kanshin sa , itama Fati ta dauko na Idriss ta nufe shi

Yar Mahaukaciya na isawa ta tsuguna har Kasa ta dago hanayenta ta mikawa Mubasshir dan farantin mai kyan gaske

Mubasshir ya zuba mata ido dan gashinta daga gaba ya dan leko kadan sanan bakinta sai sheki yake na mai mai maski da ta dan goga ,

Maganar idriss ya dawo da shi inda yake fadin” Malan kaga Karka wahalarmin da mata mana ka karba plz karka rama a kanta

Firgogit yayi dan kuwa ya fada wata duniyar tinani ya Mika hanunsa wajen karba sai da hanayensu suka gogi juna , ita kuwa Allah Allah take ta bar wajen dan jikinta har karkarwa yake jin baranbaramar da Idriss ya afka mata a gaban Hajiya harda bakin kunya sai ma da taji Muryar Ramadan na fadin” au kace kaima taka a gidan take , gaskiya kunyi mana wayo , wanan wayo har ina ? Gaskiya muma a san yanda za’ayi da mu

Da Sauri Yar Mahaukaciya ta janye hanunta ta Mike da gudu tayi dakinta tana haki

Mubasshir da Idriss gaba dayansu da ido suka bita , Mubasshir yayi dan daman bai rike hanunta ba , ji irin yanda take gudu ana kalonta ( inada tambaya , ina ruwanka hon)

Shi kuwa Idriss wata irin faduwar gaba ce ta ziyarce shi ta haka kawai a ransa ya ce ” wai a nan a cikin zulumbuwar riga take lale akoy aiki a gabana ( to kaji 😏 )

Hajiya ta katse dan shirun da ya gilma ta hanyar fadin ” tayi maka kyau idrissu , nace tayi maka kyau ka firgita min ya

Yayi murmushi ya ce ” haba kakus ya zamu zo ki hada mû da fura ?

Ta ce ” to dan nema ita ce da ni ehe 😏

Mubasshir ya ce ” kyale shi hajiyata ni kadai na san darajar wanan dan haka kowama kar ya sha idan yana so

Haka sukayi ta barkoncinsu har dai Sahla ta gaji da Kiran mamanta tana fadan sun shiga wajen tsohuwar nan sun makale kar ayi mata abinda ba shi ba

Sahla ta ce ” mom kiyi Kiran Yaya Idriss plz

Hakan kuwa akayi ta dana kiransa daidai zasu shigo falon nata ,

Salamarsu ta saka ta katse kiran jama’ar dakin na amsawa

Marokiyar ta rangada guda ta kwashi kirari da kuma isowar angon auta wato Sahla

Cikin nutsuwa suka tsuguna gaba dayansu kasa suka shiga gaisar da Su Hajiya Marhaba da kawayenta

Hajiya Marhaba murna kamar mai ,

Suna tsaka da gaisawa wayarta ta fara ringin

Ta dauka sai taga sunan bokanta ne inda ta rubuta hajiya bokatu ,

Tayi murmushi ta Mike ta dan matsa kadan ta daga

Daga dayan bangaran ya ce ” na gama aikinki na aikawa mijinki yanzu yanzu zai aikata abinda na saka shi tunda kince kina so a cikin jama’a yanda kowa zai ganta a rana yanda ba Wanda zai so ta rabe shi KO?

Hajiya Sahla ta ce ” kwarai kuwa boka yanzu ne daidai dan kuwa gaba dayan mutanen da nake so su ganta a tozarce suna wajen nan so kawai ayi aiki na cika

Boka ya ce ” karfa ki manta kudin ki mai yawa ne

Ta ce ” kar ka manta aikinka mai kyau ne idan har yayi kyau din ai kuwa abinda zaka samu har sai ya fi wanan

Ya bushe da wata mahaukaciyar dariya ya e ” to bunsura sai na jiki , ya datse Kiran

To fa , kaka kara kaka , shin waye za’a tozarta a cikin mutane? Waye za’a wulakanta har ma kowa ya gujeta? 🤷🏿‍♀🤷🏿‍♀🤷🏿‍♀🤷🏿‍♀🤷🏿‍♀🤷🏿‍♀ taku har kulun yar mutan Niger 😘😘😘😘

🇳🇪Belles écrivaines du Niger

*’YAR 👧🏻*    

         *MAHAUKACIYA👹*

*_Na SAJIDA_*

                      30

*Jiki Alhamdulilah sisters na gode da adu’ar ku gareni love u*

          Cikin takunta tamkar ba ita ce ta gama wayar ba ta juyo ta zauna , tana zama idanuwanta suka sauka kan Mubinnah Wace ita har ga Allah da farko bata ganta ba , gabanta taji ya fadi abinka da mai sakin magana idan ta raya mata ta kali Mubasshir wanda ya kagauta su tashi su bar dakin irin yanda matan nan kowace ta zuba musu ido ga uban surutu an cika su da shi ga wasu hotuna uwa Wanda aka gayace su gidan TV shi kam duk a takure yake

Hajiya Marhaba ta ce” Mubasshir wanan fa? Ban Santa ba

Mubasshir ya kara sada kansa kasa dan kuwa KO bai dago ba ya san da Wace ake magana

Idriss ya kaleta ya ce” Mom Wanan fa itace Mubinnah daya daga cikin yayan sarki

Hajiya Marhabah ta ce” wani sarkin?

Idriss ya ce” na Makkah mana mom

Hajiya Marhaba ta washe hakora ta shiga yiwa Mubinnah barka da zuwa jama’ar dakin ma haka , sanan kasa kasa sai surutu suke suna tambayar Kenan harda iyalan sarkin sun zo? Gaskiya Hajiya Marhaba ita tayi dace ,

Wani irin ihu suka jiyo , gaba dayansu suka yi tsit , suka kuma jiyo wani ihun da Sauri suka Mike Idriss ya ce ” a nan ne

Mubasshirr ya kama hanyar fita shi da Idriss inda matan suka yi cirko cirko suna raraba ido dan kuwa kowanen su tsoron FITA yake ayi ba shi

Suna fitowa suke jin ihun daga wajen bangaren Hajiya Hawau ne Harda Alamar koke koke

Idriss ya sha gaban Mubasshir ya ce cikin haki” Malan dakata , mu fara Kiran yan sanda kafin mu shiga cikin gidan nan wa ya san Abinda ke faruwa a ciki, idan fa yan boko haram ne?

Mubasshir ya gala masa harara ya ture hanunsa ya ce” KO yan a rayu haram ne Allah ya jikana ya juya ya nufi cikin gidan

Da shigarsa abin mamaki ya tarar Wanda ya kasa gaskatawa idanuwansa abinda suke gani , haka kunuwansa suka kasa yarje masa abinda suke jiyowa, nan da nan wata nadama da dana sani suka darsu a zuciyarsa domin wanan ba halin datako bane, sam wanan abin datijon kirki ba zai aikata shi ba

Cikin sauri ya FITA ya saka akayi gida da Mubinnah domin idan ta ga wanan abin shi aka tonawa asiri ba kowa ba ,

Cikin mutuwar jiki ya juyo ya dawo inda wajen ya zamana tamkar ana kida dan kuwa har dan gewaye su aka yi ana kalo , ba kowa bane face *Elhaj Ilyass* sai Jan kafar *Yar Mahaukaciya* yake yana mugayen kalamai a kanta kamar haka

    *Ashe Hajiya Mahaukaciya ce kika tare min a gida? Ashe kortuwa ce yarinyar nan ? Idan ka ganta luplup tamkar mutunuyar arziki ashe ita kuwa munafuka ce?*

Hajiya hawau cikin tashin hankali da kuka tana Jan Yar Mahaukaciya , Elhaj Ilyas na jan ta ta ce” Haba , haba Ilyasu dan girman Allah ka cika min yarinya ka
cikata mu bar maka gidan ka domin wanan yarinyar ni shaida ce kan mutuniyar kirki ce , KO wa ya fada maka abinda ya fada maka karya ne domin wanan yarinyar marainiya ce sanan ni ni na daukota lokacin da danta ya rasu harma akayi masa sitira a nan , Haba Ilyasu wanan wulakanci har ina, ya kake so nayi da raina ne?

Elhaj Ilyass ya ce” Hajiya wly kinji na rantse ba inda zaki sanan yarinyar nan a yau yau din nan zata bar min gidana domin ni ba mazinaci bane sanan ba zan lamunci ta bata min suna ba da sunan iyalina , ke kuwa ni kika Haïfa ba ita ba dan haka ita kadai zata bar min gidana

Hajiya Hawau ta juya wajen kawayenta tsofafin dake tsaye suna al’ajabin wanan lamarin da hanu daya ta fara rokon a taimaketa a tafin mata da Yar Mahaukaciya kafin danta ya gane yayi kuskure ta maidota

Aman ina kowa sai ya silale domin da ace ma jinin hajiyar ce aman haka kawai haduwar rana tsaka a zo da wanan zancen gashi daga an ganta bata shigen yayan hausa ga ido irin na kyanwa aje tsakar dare ta farka ta cinye mutun,? Gaba daya kowa tsoron Yar Mahaukaciya ya darsu a zuciyarsa

Mubasshir na rakube jikin garu yana kalon yanda da daya daya jama’ar suka fara fashewa suna tafiyarsu sai yan tsirirai su hajiya Marhaba da sauransu , muryar Idriss ta dawo da shi inda ya ce” Aba ka kontar da hankalinka ka cikata haka ni zan fitar da ita

Da hajiya da Mubasshir a tare suka kali Idriss jin furucin bakinsa

Elhaj Ilyass ya ce” Yawa yaron kirki fitar min da anoba daga gida

Yar Mahaukaciya da ta zamto tamkar mutun mutuni , a da da farko tayi tinanin zuwan wanan ranar , aman ganin irin yanda ta samu zama sai tinanin ya kau daga ranta, tabas ta saba da wulakanci, da cin zarafi aman bata taba zaton a wanan ranar haka zata faru da ita ba , furutin Idriss shi ya fi komai daga mata hankali bata san lokacin da wani karfi ya zo mata ba ta Mike daga yashen da take cikin karaji ta ce ” Ya isa ,

Ta juyo da idanuwanta da sauran farin ya koma ja, tsakiyar kuwa yake haske haske cikin dakakiyar murya ta ce” *Idriss ba sai ka fitar da ni ba , zan FITA da kaina, ta juya wajen Hajiya ta tsuguna ta kama kafafuwanta ta ce” Ni ba mazinaciya bace , aman kuma ban san ba KO ni mayiya ce KO aljana ce, abu daya na sani nima mutun ce, sanan ni YAR MAHAUKACIYA CE, kiyi hakurin rashina , karki damu da inda zan kwana na saba da wahala, kar kiyi fushi da danki haka Allah ya so , na gode sosai da tarbiyar da kika bani harma kika nuna min nima inada daraja*

Tana gama fadar haka ta jawo hijabinta na makaranta dake rataye saman igiya ta juya cikin nutsuwa ta fito daga gidan su Idriss inda take yi masa kalon karshe

To jama’a ina Yar Mahaukaciya zata nufa? Muje zuwa😁😁😁😁

🇳🇪Belles écrivaines du Niger

*’YAR 👧🏻*    

         *MAHAUKACIYA👹*

*_Na SAJIDA_*

                    31

Tafe take bata san inda take jefa kafarta ba , gata dai da ganinta ka san yar banban gida ce KO yanayin jikinta da yanda take haske sai dai fuskarta a mugun hade tamkar hadarin gabas

Mutane sai kalonta suke suna al’ajabin wanan mai ke damunta? Wasun kuwa har tambayarta suke , aman ina ita ba ta tasu take ba

Tun da ta fito yake biye da bayanta a hankali yana son sanin inda zata je , tafiyar yaga ba mai karewa bace hakan yasa ya samu ya shiga gabanta da motarsa daidai wani dan karamin gida na laka

Kasa take kalo ganin mota ta shiga gabanta ya saka ta juya ta fada cikin kofar gidan nan ita duk a tunaninta hanya ce

Da Sauri ya sauko yana kokarin cire Babar rigarsa domin ji yayi kwatakwata tayi masa nauyi , cikin nutsuwa ya kutsa cikin gidan nan inda ya tarar da Yar Mahaukaciya da wata mata tana yi mata tambayar wa take nema , ita kuwa kawai ta tsura mata ido tamkar sabuwar halita

Cikin nutsuwa ya karasa yana fadin ” salam kiyi hakuri kanwata ce bata tayi ne

Matar nan ta ce” oyo sanu kinji kiyi hakuri ga yayanki

Yar Mahaukaciya ta dago idanuwanta ta sauke su a fuskar *MUBASSHIR* Wanda shima a lokacin ita yake kalo , suka yi ido hudu da shi

A hankali ya furta ” mu tafi yana nuna mata kofa

Tamkar wata karamar yarinya Yar Mahaukaciya ta make kafada tana nufin ba inda zata je

Mubasshir ya hade rai yayi iya yinsa aman firr ta kafe ita fa ba inda zata tafi

Matar nan ta fito itama ta saka baki ake baiwa Yar Mahaukaciya hakuri kan ta shige su tafi aman kamar da kurma suke magana

Mubasshir ya hade rai tamkar bai taba yin dariya ba ya umarci Yar Mahaukaciya da ta fice su tafi , aman ina abinka da Wanda bai iya fushi ba , ita duk gani take idan fa ta bishi za’a koma ne a kuma ci mata mutunci kamar yanda akayi mata yanzu KO ma fin hakan , shi yasa sam ta kasa daga kafarta kuma bata ga abinda zai Sakata daga kafar tata

Mubzsshir ya lumshe ido a ransa ya ce” Ya Allahna ka yafe min taimako zanyi ka fini sanin ba dan wani abin zan tabata ba ,

Kawai sai gani nayi yana tatare hanun rigarsa ya CIRA Yar Mahaukaciya sama ya nufi motarsa da ita , Wace ta zaro ido tana wutsil wutsil din ya sauketa tana yakushinsa tamkar sabon kamu

Tunda ya sakata cikin motar ya zagaya ya shiga ya dauki hanya ita kuwa tsananin tsoro ya hanata dagowa ta kale shi balatana ta tambaye shi inda zai kaita dan haka kawai sai ta hade kanta da gwuiwar ta tana ta sheshekar kuka

Tafiyar da sukayi ta kai ta minti talatin gaba dayanta ta hada zufa domin du ta dababaye jikin nata da katon hijab dinta na makaranta ,

Ji tayi ya ja ya tsaya ta kasa dago fuskarta kawai jiran jin duka take KO wulakanci dan tasan gidan su Idriss din ne kawai ya maidota , ta kai kamar minti biyar a zaune bayan tsayuwar motar tana ta sheshekar kukanta , wani sanyi kamar na busawar iskar Allah du da hijabinta sanan taji wani lalausan hanu wanda da ba dan taji yatsitsai ba da KO ya za’ayi da ita ba zata yarda cewar hanu ne ba , cikin Sauri ta dago kanta dan ganin wanda ya dora hanunsa saman kafadunta

Hajiya Fatimatu Mahaifiyar Mubasshir ce tsaye sai kyali take , ga kwaliya ta sha ga sarka mai kyanli, ga farar fata ga kuma hasken gari hakan ya hadu ya haska fuskarta a idanuwan Yar Mahaukaciya Wace nan take ta gane wanan mata KO ya take ta hada alaka da Dan Aljannah da tsabar kamar da suka yi har ta baci , aman sam bata kawowa ranta cewar ta haife shi ba saboda ita bata da banban jiki sanan du da daga fuskarta zaka gane ta manyanta aman hutu ya hana a gane shekarunta ,

Hajiya Fadimatu ta katsewa Yar Mahaukaciya tinaninta ta hanyar sakar mata murmushi sanan ta kamo hanayenta cikin nutsuwa ta ce ” Marhababiki yata , ta juya fuskarta cike da fara’ar da Mubasshir har ya fara kishi ta ce ” Son kaga Adu’ata ta karbu KO Allah ya bani ya daidai lokacin da na aurar da dana ,

Mubasshir yayi Murmushin shima ya ce” Maman Mubasshir aure fa kika yiwa Mubasshir ba mutuwa yayi ba , dan haka kar a maye gurbin Mubasshir a zuciyar Maman Mubasshir dan kuwa ba zai taba yarda ba

Mahaifiyar Mubasshir tayi murmushi ta lakaci Hancin Mubasshir ta ce ” Kishi? Au kishi kake? To ka zage dantse dan kuwa aiki ya sameka jan aiki kuwa , ta kama Hanun Yar Mahaukaciya wace KO takalmi babu a kafarta sanan jikinta yayi busu busu da kura ta bi wani lungu da ita saboda taron jama’ar gidan ta nufi dakin Mubasshir da ita dan kuwa ita bangarenta jama’ar sunyi yawa sosai

Suna shiga wayar dakin ta fara ringin ta daga tayi salama

Mubasshir ya ce ” Maman Mubasshir hajiya ce tayi kira na hadaku kuyi magana tace tana son sanin idan har da gaske kin
karbi sha lelenta

Hajiya Fadimatu tayi murmushi jin yanda ya karasa maganar sanan ta amsa Kiran Hajiya Hawau  ,   sun jima suna zantawa sanan hajiya Fadimatu cikin wani irin farin ciki ta ce” Haba , haba Hajiya ai yarda daya ce , da kuma na kowa , sanan tunda ta zamto musulma koda yayanta ashirin ai bai haramta ba , dan haka ina so insha Allah kiyi kokari nan da kwana uku ki zo mu hadu da shi Aban tun kafin ya juya sai ayi KO?

Hajiya Hawau cikin Hamdallah da godiyar ubangiji ta ce ” Allah ya saka miki da mafificin alkhairin dake nan gidan duniya da kuma na kiyama, Allah ya sa ki gama da duniya lafiya, Yanda kika kudurci aikata Alkhairi a kan marainiya Allah ya jibanci lamuranki

Hajiya Fadimatu tayi saurin fadin” Amin hajiya aman plz ki dena Gode min na fada miki yiwa kai ne na yarda da ke da zuciya daya , haka suka datse Kiran su dukansu suna farin cikin abinda suka yanke Wanda a tinaninsu hakan shine banban gudumuwar da zasu yi dan taimakon marainiyar Allah wato Yar Mahaukaciya

Cikin nutsuwa ta juyo wajen Yar Mahaukaciya Wace gaba dayanta take tsorace da wanan dakin, ita tunda ta wayi gari ta ganta a gidan duniya  bata taba , no bata taba kawowa kusan ranta cewar wai a nan gidan duniya za’a iya tsantsara wanan tsarin haka , Dakin ciki daya ne wani wawakeke sanan du madubi ne ya gewaye dakin sai gadon dake tsakiyar dakin kasan ba kafet jikin tils din kasan hoton Mubasshir ne aka zana da sajensa yana murmushi gaba daya wata kunya ta kamata gani take kawai kalonta ne yake ta kuwa tatare siket dinta ta matse ita kar yaga jikinta ( lol ) aman kuma mamakin da take Wai ina bayi? Sanan ina wajen kaya? Ita tsoroma ya mugun kamata da ace ita kadaice da ba abinda zai hanata ta zare a dakin nan

Hajiya Fadimatu ta kamo hanunta cikin nutsuwa ta jata saman gadon Mubasshir suka zauna a gefen gadon sanan cikin sanyinta da kwarewa wajen kontarwa da mutun hankali ta ce” Rahma, Rahmatullah, mai yayi zafi da aka manta Kiran inalilahi wa’ina ilaihi raj’une ake kukan nan? Shin kin manta fadar Ma’aiki idan ka ga abinda ya kayar maka da gaba KO ya bata maka rai kayi ta maimaita sunayen Allah kana tazbihi kana kusanta da ubangijinka dan samun saukin zuciyar ka ? Domin kinsan ita zuciya a jikin dan Adam Mugun nama ce idan har zuciyar Dan Adam ta baci to fa ba mutun, sai ki ga mutun yana aikata abubuwa irin Wanda KO daba ba zai aikata ba dan kuwa cikin aikinsa tsabar kin Allah zaiyi yawa a ciki , shi kuwa wanan Halaka ne Rahma Tabas Halaka ne

Cikin nutsuwa Yar Mahaukaciya ke kalon Bakin Mahaifiyar Mubasshir wata irin nutsuwa taji tana ratsata wace bata taba jinta cikinta ba hadi da kunya Wace ta rasa ta maicece, da sauri ta sada kanta kasa tana dan murza yatsuntsanta tana raurau da ido

Hajiya Fadimatu tayi murmushi ganin Yar Mahaukaciya tana da kunya ta dago kanta ta ce” Ni sunana Nana Fadimatu sanan ni Mahaifiyar Mubasshir ce kuma ina son zama mahaifiyarki , shin zaki bani wanan damar?

Idanuwan Yar Mahaukaciya suka ciciko da kwallah tana kokarin zubar da hawayen shaukin wanan kalma ta Mahaifiyar Mubasshir

Hajiya Fadimatu tayi Saurin girgiza mata kai ta ce ” AF sanan idan abu ya faranta ranta kayi hamdallah ba kayi kuka ba

Ta cire hijabin Yar Mahaukaciya ta dora kanta saman cinyarta a hankali tana yi mata labari har barci mai dadi yayi awon gaba da Yar Mahaukaciya cike da farin cikin wanan rayuwa sabuwa tare da adu’ar Allah ya  sa mai dorewa ce

To fa shin mainene abinda su Hajiya Hawau suka yanke ne? Muje zuwa 😘

🇳🇪Belles écrivaines du Niger

*’YAR 👧🏻*    

         *MAHAUKACIYA👹*

*_Na SAJIDA_*

                    33

Sosai take bacin ta hankali konce harda ajiyar zuciya, Hajiya Fadimatu ta gyara mata konciya ta Mike a hankali gudun kar ta tashe ta ta koma wajen bakin ta

Bayan wanan tarzomar kowa ya watse aka bar Hajiya Hawau ita kadai domin gaba daya bakin nata sunyi tafiyar su gudun kar a makala musu Yar Mahaukaciya

A boye ta samu wayarta har tayi magana da mahaifiyar Mubasshir , bayan ta gama ne ta fito dan ta tatare tabarmin da ta shinfidawa bakin ta , tana fitowa ta tarar da Fati kawar Yar Mahaukaciya rakube kanta a kasa tana ta tinane tinane

Hajiya Hawau ta karaso a hankali ta zauna kusa da ita ta ce” Fati tinanin mai kike?

Fati ta dago kanta ta kali hajiya sanan cikin gargadar murya ta ce” shin Hajiya ina sister ne? Hajiya dan Allah ki cireni daga cikin duhu cos ina cikin duhu ta karashe zancen da kuka

A hankali hajiya Hawau ta dafa kafadarta ta ce” RAHMA ba mazinaciya bace , sanan mafaifiyarta ba mahaukaciya ba ce, kuma ita marainiya ce sanan ni kakarta ce, Kuma Dan Aljannah yayanta ne , wanene baki fahimta ba a ciki?

Fati ta ce” Kenan AA jikanki ne shima?

Hajiya Hawau kawai ta daga kanta alamar eh

Fati ta sauke nanauyar ajiyar zuciya sanan ta ce” yanzu tana ina Ita din?

Hajiya Hawau ta ce” Tana gidan su Mubasshir dan haka ki mike kiyi wanka zan saka a rakaki wajenta , ki tafiyan mata da kayanta gaba daya kin ji?

Fati ta daga kanta tana farin cikin jin Rahma na gidan su AA Mubasshir ,

Hakan kuwa akayi Hajiya Hawau tayi kira ta shaidawa Mubasshir yayi Kiran securites ya shaida idan za’a kawo wata budurwa baka mai dan tsayi da kaya a shiga da ita ta baya , sanan ya shaidawa Mahaifiyarsa , ita kuwa sai murna ta karu dan Hajiya Fadimatu akoy son yaya mata shi yasa kulun adu’arta Allah ya bata kafin rasuwar mahaifin Mubasshir to bayan  rasuwar tasa ma bata daina ba tana fatan Allah ya baiwa Mubasshir sai a bata ta rike sai gashi yau Allah ya bata ya mai kyau haka tayi murmushi tana adu’ar Allah ya tayata riko

Cikin bacinta taji an kankame mata  jiki firgigit ta farka tana zare ido domin bata san tayi baci har haka ba , idanuwanta ta shiga murzawa dan gaskatawa kanta Wanda take gani

Fati tayi dariya ta ce” ni ce sis

Yar Mahaukaciya tayi musrmushi ta ce” wa ya kawoki? Ya akayi kika zo ? Kinga abinda ya sameni ko ? A ina……….cikin sauri Fati ta ce” ke ki dan huta da tambayoyin mana , Hajiya ta fada min komai dena daga hankalinki haka kinji

Yar mahaukaciya tayi shiru tana tinanin mai Hajiyar ta fada mata , aman sai ta share bata ce mata komai ba ,

Suna nan zaune Mahaifiyar Mubasshir ta kuma shigowa ta ce” Yar Fadimatu kin farka? A taso  ayi wanka domin yama tayi

Yar Mahaukaciya ta ce ” ohk mamana tana murmushi

A hankali Mahaifiyar Mubasshir ta nufi daidai wani madubi ta mika hanunta a nitse ta dan shafa wani farin abu , abin mamaki kofa ta bude daga Yar Mahaukaciya har Fati da kalo suka bi Hajiya Fadimatu baki sake uwa zararu sanan ta kuma taba wani bayi biyu suka bude a cikin dakin cikin nutsuwa ta taho ta kuma taba wani abin sai dirowa ta bude ta zaro tapi ta nufi wajen tiraruka ta dauko kala uku du ta zube musu ta ce” kuyi wankan ga salaya, ga kuma wanan kafin ku gama kimtsawa za’a kawo muku kayanku ku saka

Su duka suka amsa mata

Har ta kusa FITA ta dawo ta ce” zaku tafi diner ne?

Fati ta ce” Eh

Yar Mahaukaciya ta ce” aa

Suka kali juna a tare

Hajiya Fadimatu tayi murmushi ta ce” Kuyi shawara idan kun yanke shawarar sai na turo mai shirya ku

Suka amsa mata da to ta juya ta fita

Tana fita Fati ta zarowa Yar Mahaukaciya ido ta ce ” hey😳, for what zaki ce ba zamu tafi ba?

Yar Mahaukaciya ta ce” k
i gane sisi idan na tafi kinga abinda ya faru da safe bana so ya kuma faruwa

Fati ta ce” auren yayanki ne , auren gidanku ne, dan kawai wata nonsence bata sonki a wajen sai ki ki tafiya? Sis harda mai shiryamu fa waouh har ina tinanin yanda zamu dawo idan aka shiryamu plz ki amince mu je muma

Haka dai suka zauna suna ta musanyar yawu kan su je KO kar su je

Eyah fans shin Su je din ne KO kar su je??????🤷🏿‍♀

🇳🇪Belles écrivaines du Niger

*’YAR 👧🏻*    

         *MAHAUKACIYA👹*

*_Na SAJIDA_*

                    34

Wanka suka shiga kowace ta dau lokacinta , ita dai Fati tana gamawa ta dauro alwalah ta zo ta gabatar da salar Magarib, tana nan zaune tana lazumi Yar Mahaukaciya ta fito ta nufi Jakarta ta buda ta dauki pad ta juya cikin bayin ta saka ta kuma fitowa kanta daure da tawul karami ta lulube jikinta da hijabinta

Sai da Fati tayi sallar Isha sanan ta mike daga saman dardumar ta ninke ta ta tsaya ta zubawa hoton Mubasshir dake zane saman terrace din

Yar Mahaukaciya ta ce” mai kike kalo?

Fati ta ce” sis kinsan Allah gaskiya banga laifin matan da suka yanyanka hanayensu lokacin annabi yusuf , ki duba ki ga irin kyan AA fa sis ni KO da AA kadai aka barni sai nayanyanke hanuna

Yar Mahaukaciya ta bushe da dariya ganin yanda Fati tsakaninta da Allah take bayaninta har cikin zuciyarta yanayin yanda take fitar da zancen

Ta ce” sisi kinsan wani Abu? Ni sam kyan mutun baya rudata wly ke wani lokacin nafi son mutun mai bakar fata cos yafi kyau

Fati tayi mata kalon kin raina ni sanan ta ce” to tayaya kyau zai rude ki ? Ai dan kinsan kina da shi shi yasa , da baki da kyan nan da garin kalon mai kyau har sai kin fadi , sis dan AA yayanki ne shi yasa kyansa baya baki tsoro

Yar Mahaukaciya a ranta ta ce na fiki tsoron kyan bawan Allahn nan domin ina daya daga cikin wa’inda suka Ganshi yana zubawa mahaifiyarsa shagwaba , da a lokacin kika Ganshi da sai kin suma ma ina jin , aman a fili ta ce” idan kin gama ki zo mu kimtsa plz

Suna tsaka da kimtsawa Fati ta dage ta gyara zama tana tsantsarawa Yar Mahaukaciya kwaliya mai shegen kyau da tsari ta caje mata girar ta domin girar kalar gashin kanta , ta dauko tana kokarin zabar mata jan bakin da zata shafa Hajiya Fadimatu ta shigo fuskarta dauke da murmushi

Tayi musu salama

Suka amsa suna gaishe da ita

Ta amsa su tana ta zuba murmushi ta ce” kuyi hakuri yayana na barku ku kadai, kunsan bakin ne da yawa sai yanzu na samu na kufce

Yar Mahaukaciya ta ce” lah ba komai mama

Hajiya Fadimatu ta karasa tana fadin zaku tafi ne wajen dîner?

Fati ta ce” No mama ba zamu je ba

Hajiya fadimatu ta ce ohk ba damuwa , daidai nan wata mata tayi salama da wata jaka a hanunta ta tsuguna har kasa tana gaishe da su fati , suka amsa suna kalonta

Ta juya cikin murmushi ta ce” ma’am wacece kanwar ogan?

Hajiya Fadimatu ta nuna Yar Mahaukaciya ta ce” kin ganta nan baki ga kama ba?

Wace aka nunawa mai aikin bangaren Hajiya Fadimatu ce ta ce” kai masha Allah , Ashe ta warware ma , Allah ya raya mana ita ( uwa wata beby? )

Hajiya Fadimatu ta amsa da Amin Ya Allah sanan ta karbi jakar ita kuwa ta juya ta bar dakin

Hajiya Fadimatu ta bude jakar  wasu abayoyi ne a ciki da kuma wasu mahaukatan less farare tas anyi dogayen riguna da su gwanin ban sha’awa da ribon na less  din ta ce” kunga wajen ango ga abinda zasu saka nan wanan less din , tunda bazaku tafi ba sai kuyi shigan arabian ku fito dan saboda hotuna da za’ayi mana da ango kafin ya tafi diner

Yar Mahaukaciya ta ce” An gode mama,,,,,…..kafin ta karasa Hajiya Fadimatu ta rufe mata bakinta tana fadin no kar naji godiyar nan , dan mamanki tayi miki kyauta sai ki kama gode mata? No kiyi hamdallah ya wadatas sanan ta Mika hanu ta dauko wani Jan baki kalar pink ta Mika mata ta ce” wanan shine daidai da kwaliyarki

Yar Mahaukaciya tana murmushi ta karba ta dan goga pink ne Wanda bai ciza ba sanan bashida man lebe a hade da shi ta fito tsaf da ita

Hajiya Fadimatu a ranta ta ce” Allah yayi halita a nan , Allah ya kade hau da bakin duniya , a fili kuwa ta ce” Yar Fadimatu kinyi kyau har kin gaji masha Allah

Yar Mahaukaciya tayi murmushi sanan ta sada kanta , Hajiya Fadimatu ta kali Fati ta ce” takwara kuyi Sauri ku fito fa kunsan al’adar mu da banbanci

Fati ta ce ” toh mama i’a gamu nan fitowa

Ta juya ta fita ,  tana FITA Yar Mahaukaciya ta cire tawul din dake nanade da gashinta ta saka macaji baba ta caje kanta sanan ta dauko ribom ta daidaita gashin tsakiyar kanta ta daure ta warware abayar bata san lokacin da ta furta masha Allah ba ta juyo dan nunawa Fati sai taga ita har ta saka

Fati ta ce” kawai ki rage mamaki yan Mata dan kuwa haduwa mun hadu saka nayi miki roling mu tafi ,

Yar Mahaukaciya ta saka tata Fati ta nada mata mayafin Abayar ta fito tamkar balaraba ga hasken da idanuwanta ke bayarwa idan ta kaleka abin ba’a cewa komai ,suka dauki takalmansu mai shegen kyau suka saka , Fati ta dauko wayarta ita kuwa ta kama hanyar fita cikin takunta na nutsuwa da daukan hankali

Fitowa suka yi suka tarar da matar nan ta dazu tana tsaye tana jiran su , ta ce ” Hajiya mu je na kaiku falon da ake salamar angon

Yar Mahaukaciya ta ce” salamar ango kamar yaya?

Amina ta waigo ta ce” Eh ai haka al’adarsu take yanzu angon ya fito tun dazu ana ta hotuna tamkar baza’a daina ba , idan aka gama sai a barku ku uku tunda Hajiya ce yar uwarsa ta jini da Mahaifiyarsa , Mahaifiyarsa tayi masa nasiha sosai da sosai shi Kenan sai ya tafi daga wajen dinern gidansa zai fice da matarsa shi Kenan sai jibi da auren zamu ganshi shima gasuwa zata kawo shi idan ya koma sai bayan sati guda kuma shikenan ya zama magidanci shima

Fati ta ce ” waouh wanan tsarin ya tsaru ya birge ni sosai tsarin nan , ta juya kan Yar Mahaukaciya ta ce ” sister al’adar ku tana birge ni

Yar Mahaukaciya tayi murmushi tamkar wata sakara ta dan juya kanta a ranta ta ce ” nima yanzu na ji ,

Daidai nan suka karaso wani falo Wanda fadin haduwarsa bata lokaci ne , ya hadu ya hadu yayi karshen haduwa , cikin nutsuwa Yar Mahaukaciya ta saka hanunta ta bude tana kalon Fati dake yi mata magana , sai gani tayi Fati ta zama tamkar robo kikam tana kalon ciki

Cikin faduwar gaba ta juyo a hankali idanuwanta sukayi arba da jama’ar dakin ta furta ya salam ta lumshe idanuwanta dan faduwar da gabanta yayi

Hajiya Fadimatu ta mike cike da murmushi ta tarota ta kamo hanun Yar Mahaukaciya da Fati ta ISO har tsakiyar jama’ar dake hahakimce ana ta daukan hoto domin Mubasshir a zaune yake saman wata kujera mai ruwan ash da baki baba gaba daya idanu aka zuba mata ganin wanan yarinyar mai shegen kyau a tare da ita ,

Hajiya Fadimatu cikin Murmushi ta ce” Asalamu alaikum

Gaba dayansu suka amsa mata salamarta kanan ta ce ” Ina mai gabatar muku da Yarinyata Rahma , da kuma kawarta mai sunana , Kanwar Mubasshir ce she is my daughter my lovely Girl ta karashe tana sakarwa Yar Mahaukaciya Murmushi

Gaba daya dakin suka kwashi dan surutu suna fadin waouh,

Hajiya Halima ta taso ta karaso gaban kawarta tana murmushi ta Mika hanayenta ta kamo na Yar Mahaukaciya tana murmushi ta jata jikinta suka yi irin gaisuwar nan ta larabawa sanan ta ja
ta gaban sauran kawayen Hajiya Fadimatu suna gaisawa cikin raha kowa yana mamakin daman yayanta biyu?

Bangaren Mubasshir Hajiya Fadimatu ta nufa tana nazartar yanayinsa , lokaci guda du ya wani dan daburce yana kalon kasa gashi Mubinna ta rumgume shi ana daukan su hoto aman sam hankalinsa baya kan daukan hoton

Hajiya Fadimatu na isa ita ma ta shiga aka dauke su da Mubinnat sanan ta yafito Yar Mahaukaciya , sai da gabanta ya fadi ta mike kamar wace Kwaï ya fashewa kaza a ciki ta nufe su , Allah ya taimaketa kafin ta isa Mubinnat ta daga waya tayi waje ,

Cikin nutsuwa ta isa abin mamaki kanshin tiraren da ta fesa shi ne a jikin Mubasshir , shima yana jin kanshin ya dago suka hada ido daidai ta ISO kusa da shi

Cikin Sauri ya kawar da kansa yana ajiyar zuciyar da bai san KO na mainene ba ,

Hajiya Fadimatu ta kara matsota sosai jikin kujerar kamar yanda itama take ta ce ” Yar Fadimatu ki saki jikinki mana sanan kiyi murmushi ayi mana hotunan mu

Mubasshir ya dago kansa ya kali Mahaifiyarsa da alamar shagwaba a fuskarsa ya ce” Yar ?????🙁

Hajiya Fadimatu tayi murmushi ta ce ” yes

Mai hoton ya dauke su ya kai kala biyar sanan Hajiya Fadimatu ta ja Yar Mahaukaciya ta zaunar da ita a gefen kujerar sanan ta dora hanunta na dama saman kafadarsa kasa kasa ta ce” wai ba zaku saki jikinku ba ana kalonku fa

Mubasshir da yayi sumar zaune ya kuma dago da kansa da cikin muguwar kasala ya bi dayan hanun nata da kalo Wanda ya sha kunshi yayi mugun kyau a ransa ya ce Au Ashe sai da tayi kunshin , a fili kuwa ya sakar mata murmushi itama ta mayar masa inda mai hoto ya dauki abinsa tamkar itace amaryar yanda take wani annuri

Haka dai akayi ta hotunan nan har lokacin nasiha yayi , gaba daya mutanen suka bar dakin harda Fati kawar Yar Mahaukaciya ,

Hajiya Fatima ta nemi waje ta zauna ta kali Yar Mahaukaciya dake kalon kofa tana son fita kuma ta rasa ya zata yi

Hajiya Fadimatu ta ce” Yar Fadimatu zo nan ki zauna mu yiwa Yayanki gargadi KO?

Mubasshir ya zaro ido Yar Mahaukaciya ma ta zaro ido nima haka cos wanan gargadi harda abinda yaro ba zai ji ba , ita kuwa Mahaifiyar Mubasshir an fada mata Yar Mahaukaciya bazawara ce , shi yasa zatayi maganar ta a gabanta , shi kuwa gani yake sam bai dace ba karta raina shi dan kuwa KO da ta taba aure har ta haihu hakan ba yana nufin za’a yi masa galgadi a gabanta ba dan yarinya ce , ita kuwa mugun tsoron sa ne ya Sakata firgici jin za’a yi masa gargadi a gabanta

Hajiya Fadimatu ta ce””””””””””””””””'”””””””””””””””‘

           Muah

🇳🇪Belles écrivaines du Niger

*’YAR 👧🏻*    

         *MAHAUKACIYA👹*

*_Na SAJIDA_*

                    35

Hajiya Fadimatu ta kare musu kalo sunyi wani cirko cirko suna kalon ta ta ce ” yar Fadimatu matso kusa da ni ki zauna KO kema kina jure tsayuwa ne?

Yar Mahaukaciya ta kifta ido tamkar ta juya ta fice take ji aman kuma bazata iya yin hakan ba , cikin nutsuwa ta karasa ta zauna a kasa daidai kafar Hajiya Fadimatu , inda shima ya karaso ya zaunan

Gyaran murya tayi sanan ta fara da adu’a , wato haka al’adar su take idan kayiwa yaron ka aure sai ka zaunar da shi ka tinatar da shi cewar da da yanzu ba daya bane , ka kara jadada masa irin nauyin dake kansa a yanzu Wanda idan yayi wasa da su tabas gobe kiyama yana cikin garari tsirar sa sai wani ikon Allah , hakan Hajiya Fadimatu ta dage wajen kawowa danta kwaya daya misalai da ayoyin da suka zo mana da mahinmancin iyali da yanda zaka kula da su , tana tsaka da yi masa wanan jawabin gaba daya ya nutsu maganganunta na ratsashi duk da ya san duk abinda take fada masa kamar ana kara yi masa bita ne aman kwarai yana ratsa shi kuma yana ji a jikinsa cewar dole ne ya kula da iyalinsa, jin mahaigiyarsa tayi shiru ne ya saka shi dago da kansa , aman mai zai gani *Hawaye* take sharewa daga idanuwanta

Cikin kidima ya mike tsaye ya dare saman kujerar da take zaune har hanunsa na rawa ya dan karkato fuskarta , kwarai hawaye Mamanda ke zubarwa , cikin wata irin murya ya ce ” Kuka? Hawaye daga idanuwan Maman Mubasshir? Shin mai ya batawa Maman Mubsshir rai haka? Mai ya daga mata hankali haka?

Hajiya Fadimatu tayi lalausan murmushi a ranta ta ce’ ina kaico da rashin sa’ar mata da kayi shi ya saka ni kuka aman a fili ta ce” Ina mamakin girman Mubasshir ne , yau da gobe sai Allah

Yar Mahaukaciya ma da ta mike tana kalonta sai taji hawayen maman Mubasshir na shigar mata zuciya tamkar Mahaukaciyarta , haka kawai taji zuciyarta ta tsinke wani irin kuka yana kokarin zuwar mata tayi iya yinta ta dane shi aman sai da hawaye ya zubo mata tayi saurin sharewa

Hajiya Fadimatu ta Mika mata hanu ta matso itama ta zauna suka Sakata a tsakiya a hankali taci gaba da jawabinta Wanda wani har kunya yake baiwa Yar Mahaukaciya , wasu abubuwan sai yau ta taba jin wai a aure akoy su kuma Dole a kiyaye , ita kam tata ta sameta koda yake Wanda ya nuna yana son nata ya fasa son nata kenan bata da wata damuwar tinanin idan fa bata yi biyaya ba itama zata hadu da fushin ubangijinta

Sosai ta kwashe lokaci tana ta kara jadadawa har abokan Mubasshir suka fara dana masa kira ba kakautawa domin can wajen diner an taru sosai har amarya ta zo tana jiran karasowar ango su shige tare , nan Mahaifiyarsa ta salame shi ya mike suma suka mike dan su yi masa rakiya ta kama hanun Yar Mahaukaciya da hanunta na dama shima ta kama hanunsa da na hagu suka Sakata a tsakiya suna dan taba hira suna dan murmushi idan har ba saninsu kayi ba to lale zaka rantse cewar su duka yayanta

Sai da suka rakoshi har daidai motar da tarin mutanen gidan da jama’ar sa suka cicika , daidai wata yar madaidaiciya fara mai shegen kyau Hajiya Fadimatu ta Bude masa gidan baya dan kuwa a yau ta hane shi tuki da kansa ,

Ya rungume ta suka yi irin gaisuwar larabawa ya juyo kan Yar Mahaukaciya suka kali juna tayi dan murmushi ta daga masa hanu alamar byby ya juya ya shige cikin motar tare da faduwar gabar da baisan KO ta meye ba

Wajen diner ,casu ake sosai kowa yana kwasar gara inda Mubasshir yayi shiru yana kalon mutane hankalinsa a rabe yake wajen gida da yawa daman shi ba ma’abocin son kida ba ga kuma abinda ke nukurkusar sa Wanda yake matukar jin haushin kansa da kuma kunyar kansa dan kuwa wanan tabas abin kunya ne a gareshi ( to kaji )

Sahla ta juyo tana kalonsa taga hankalinsa a wani wajen cikin kisa ta matso daidai kunansa ta ce” Mijina tunanin mai kake?

Mubasshir yayi murmushi ya kaleta ya ce” ba komai wifey

Ta ce ” taso muyi rawa manan

Yayi dan murmushi ya ce” kinsan su Maman Mubasshir suna kalo daga can fa

Tayi far da ido ta dora kanta a kafadarsa ta wani lumshe ido , su kuwa masu daukan hoto da yan uwa sai yi suke

Mubinnat dake hakimce tana kalo a ranta ta ce , wai a kan wanan skelet din ce zaka kasa zama a can , lale zaku dandana kudarku , tayi murmushi

Zaune suke su uku da dan abin ciye ciye a gefen su suna kalon abinda ke faruwa sai suna ta yabawa haskowar da za’ayi aka hasko Sahla ta manawa Mubasshir kis a kuncinsa  su Yar Mahaukaciya suka zaro ido a tare nan da nan wata kunya ta kama Yar Mahaukaciya ta rufe idanuwanta

Hajiya Fadimatu dake zaune   itama ta lura da yanayin Yar Mahaukaciya a ranta ta ce ” BIYU Kenan domin tana wani wasi wasi a ranta aman ba komai lokaci 

[11/7, 07:51] Umar Dalha: 🇳🇪Belles écrivaines du Niger

*’YAR 👧🏻*    

         *MAHAUKACIYA👹*

*_Na SAJIDA_*

                    36

Haka dai ta kawar da tinanin suka ci gaba da kalonsu har wani lokacin inda baci ya fara kama idanuwan su

Hajiya Fadimatu ta ce ” Baci KO?

Yar Mahaukaciya tayi murmushi tana murza ido

Hajiya Fadimatu ta ce ” ai sun gyara miki dakin naki ( wato dakin na wajen Mubasshir ita ta zaune shi dan kuwa yafi kusa da dakin Hajiya Fafimatun )

Yar Mahaukaciya a ranta ta ce ” dakina? Waouh , a fili kuwa ta ce ” an gode mamana

Hajiya Fadimatu na matukar jin dadin sunan da Yar Mahaukaciya ke kiranta da shi wato *Mamana*

Suka mike da niyar zuwa yin bacin suka yi mata sai da safe suka haura saman benen

Suna shiga suka tarar an canza zanin gadon , an saka tirare mai kanshi an gogoge ko’ina sanan kayansu an jere su tsaf

Fati ta kali Yar Mahaukaciya ta ce ” ke princess ce ashe shi yasa kike luwai luwai da ke

Yar mahaukaciya tayi murmushi tana cire kayanta ta zaro na baci ta saka tayi konciyarta

Fati ma ta saka ta haura saman gadon ta lumshe ido can ta ce ” yau za’a kwashi gara , duk da kashi ce Zala

Yar Mahaukaciya ta bude idanuwanta ta ce ” gara ? Ta me fa?

Fati ta karkato ta ce ” ta angoncewa mana yau su AA za’a fada wata duniyar

Yar Mahaukaciya ta zaro ido ta cije lebenta ta daga filo ta kwalawa Fati suka shiga kokowa uwa wasu kananun yara sai kyakyata dariya suke , can Yar Mahaukaciya ta nisa ta ce ” Allah ya shirye ki

Fati ta ce ” ya shirye mu baki daya

Washe gari tunda asuba Yar Mahaukaciya ta farka , ta saba gidan Hajiya Hawau idan suka Farka sai aikace aikacen su Hakan Yasa ta kasa hantsewa tana baci sanan zaman dakin ya ishe ta , cikin nutsuwa ta bude dakin ta fito daure da Zani na atampa da rigarta daidai ita da dan kwalin atampar ta sauko kasa ba kowa a falon duk da ba wata dauda gare shi ba ta zage ta shiga aiki kakabe can goge nan share can gaba daya har inda Yan Aikin basa tabawa dan wani abin sai mutun da kansa dan kuwa dan aiki bazai tsaya ya yi maka aikinka yanda ya kamata ba , kafin karfe takwas Yar Mahaukaciya ta gama gyare falon nan , sanan ta je bangaren masu aikin ta tambaye su ina tiraren gidan

Cikin rawar jiki hanne ta fito tana mamakin Hajiyar ce da kanta take shara , lale wanan ta daban ce , ta fito ta buda wani dan daki Yar Mahaukaciya ta shiga , haba zo laga kalo tamkar dan shago ne aka Buda na tiraruka kanshi ta ko’ina tashi yake kai kace kasuwar tiraruka ta shiga , wangalau tayi da baki tana kama sunayen Allah tana mamakin rayuwa , bolarsu ta fado mata a rai da Mahaifiyarta ta lumshe ido tana adu’ar Allah ya sa bata cikin wata bolar , ganin zata fara sana’ar tata yasa ta shiga bubudawa can wani mai sikari ya mugun birge ta , kanshinsa yayi mata sosai hakan yasa ta dauko shi ta dauki abin kunawar ta fito ta rufo ta je ta kuna sanan tayi kicin wajen masu aiki

Da salama ta shiga cikin kicin din gaba dayansu su hudu suka shiga gaishe da ita da harshen turanci , sarai hausawa ne aman kowace da iliminta kuma sunyi karatun girki , su duk a tinaninsu Yar Mahaukaciya bata iya hausa ba dan yanayin tsarin halitarta ,

Tayi murmushi sanan cikin kwarariyar hausarta ta ce ” kun tashi lafiya? Ya aiki ?

Gaba dayansu mamaki ne ya kama su har hada baki suke wajen fadin ” hajiya ashe kin iya hausa?

Yar Mahaukaciya ta kuma yin wani murmushin ta ce” plz ku dena kirana da hajiya , ya Za’a kira mamana da Hajiya Kuma nima a kiraye ni da Hajiya ? No ku ringa kirana da Rahma

Daya daga cikin su mai suna Aisha ta ce” kiyi Hakuri Hajiya ai ita Hajiya Baba ta gidan nan muna kiranta da Maman Rahma da can sunanta Maman Mubasshir to a jiya ta canza kinga ke sai dai mu ce aunty

Yar Mahaukaciya tayi murmushi a ranta tana matukar kaunar Maman Mubasshir Wace ta dawo Maman Rahma wato ita sosai take girmama darajar matar , ta ce” to naji, yanzu mai kuke dafa mana yau?

Nan suka bubuda mata gaba daya abincin na yan gayu ne , wanin na larabawa ne ma mai yiwuwa na al’walin Mubasshir ne dan kuwa shi kadai ya dan dakata sai daga baya zai koma

Yar Mahaukaciya ta ce ” fanin jus fa?

Suka amsa mata da ai na kwali kawai suke sha

Yar Mahaukaciya ta ce” am , fura zan hada da kuma jus na gargajiya

Kalon kalo suka shiga yiwa juna Mariam ta ce” Fura? Fura ma tamu?

Yar Mahaukaciya ta ce ” Yes KO babu kayan hadata ne?

Aisha ta ce” akoy sosai akoy komai da komai dan kuwa elhaj ma muna hada masa aman sai yace bata da taushi aman har hatsin a surfe Yake

Yar Mahaukaciya ta ce ” baya son Wace ba ta hanu ba shi yasa , dauko min komai harda baban turmi

Mamakinsu dada karuwa yake balatana da suka ga Yar Mahaukaciya ta dage tana kirbar fura a turmi , sai da tayi mata lilis ta kuma maida ta a tukunya sosai furar ta hade kanta tayi wani irin taushi ga uban cikui ga kayan daka , Yar Mahaukaciya ta kwashe ta cicibra kayanta sanan ta raba gida biyu ta bar musu rabi , ta shiga hada jus na hausa sai da ta hada na gyada , da zobo, da kuma na abarba ta markadeta

Su dai kalonta suke suna mamakin yanda yarinya mai gata haka har ta iya daka

Karfe tara ta gama komai ta kwashe tayi frij da su sanan ta haura sama dan yin wanka

Daidai lokacin Hajiya Fadimatu ta sauko ,

Tunda ta sauko falonta take mamakin gyaran dakin tayi murmushi ta ce” Lale yau Hanne tayi abin kanta , itace da tashi da wuri haka KO dai wani wajen zata tafi?

Tana zama ta dana Kiran dakin su nan da nan sai ga hanen ta duka har kasa tana gaisar da hajiya Fadimatu

Hajiya Fadimatu ta amsa mata da fara’a sanan ta ce ” yau su hanne anyi abin kai anyi aiki da wuri

Hanne ta Sosa kai cike da kunya ta ce ” Maman Rahma ai aunty Rahma ce tayi gaba daya aikin nan

Hajiya Fadimatu ta zaro ido ta ce ” Wace rahamr ? Tawa?

Hanne da tsoro ya  kamata ta ce” eh ita Maman Rahma ai harda fura tayi a kicin

Mamakin Hajiya Fadimatu ya kasa boyuwa sai ga su Yar Mahaukaciya suna saukowa. Fati Harda akwatinta

Suka tsuguna suna gaisar da Hajiya Fadimatu

Ta amsa fuskarta cike da Murmushi ta ce” Fati ya haka kardai ki ce min sai tafiya

Fati ta sada kanta tana murmushi ta ce ” wly mama yanzu yayana yayi kirana ya ce ya kwana a Lagos nayi masa kwatance ya biyo ya dauke ni dan yanzu zai fice gida

Hajiya Fadimatu ta ce ” Eyah to ai sai kin karya KO?

Fati ta ce” Mama ai ya dade da isowa tana dan Murmushi

Hajiya Fadimatu ta Mike tana fadin maza a hada mata kayan kari a kwano ita kuwa ta haura sama ta hadawa Fati sha tara ta arziki ma’aikatan gidan suka kwasa suka yi waje da  su

Yar Mahaukaciya  tayi mata rakiya har waje suna yiwa juna byby cike da kewar juna ,

Ta juyo zata shiga falo Kenan taga wata mota mai mahaukacin kyau ta shigo da wani irin gudu tamkar za’a tashi sama

Gabanta ne yayi mugun faduwa ganin Wanda ke cikin motar

,,,           morning ,,,,,,,,,,,😘

[11/7, 07:51] Umar Dalha: 🇳🇪Belles écrivaines du Niger

*’YAR 👧🏻*    

         *MAHAUKACIYA👹*

*_Na SAJIDA_*

                &nbs
p;   37

Gabanta ne ya fadi ganin wanda ke kokarin fitowa daga cikin motar , ta kara maida hankalinta tana kalonsa , shadar jiya ce a jikinsa a dan yamutse kadan daga sama ,sanan fuskar nan a mugun hade tamkar ba shine jiya yake son kin murmushi ba , bata Ankara ba sai gani tayi ya kifta ta ya shige falo , haka kawai ta tsinci kanta da kasa komawa dan kuwa yanayinsa zai nuna maka cewar yana cikin bacin rai sanan yana yana bukatar ganawa da Mahaifiyarsa *Mubasshir* Kenan

Yana shiga sanyin kanshin falon da dadadan tiraran da aka kuna suka daki hancinsa ya lumshe idanuwansa ya saki ajiyar zuciya

Hajiya Fadimatu dake zaune ta baiwa kofa baya ta ji alamar an shigo aman bata waigo ba ta ce” Yar Fadimatu kin dawo daga rakiyar? Sai ki zo ki fada min a ina kika iya daka fura mai kyau haka

Cikin nutsuwa da karayar zuciya yake takawa har kusan mahaifiyarsa , a hankali ya zagaya gabanta ya tsuguna ya dora kansa a saman cinyarta

Hajiya Fadimatu da tayi mutuwar zaune ganin Mubasshir a wanan rana shi da ya kamata sai a gobe a ganshi , gashi yau ya zo karfe goma na safe sanan ba a cikin hayacinsa ba , a hankali ta dora hanunta na dama tana shafar sumar kansa wace da dan ruwa ruwa a cikinta shaidar yayi ta wanke kansa dan yaji saukin abinda ke damun sa

A hankali yake samun nutsuwa yana sakin ajiyar zuciya sanan yana godewa Allah da jama’ar gidan duk sun juya sun bi jirgin karfe biyu na dare zuwa kasa mai tsarki wasun kuwa yan chadi na karfe biyar suka bi ,

Hajiya Fadimatu ta dan dakata da adu’ar da take tofa masa ta ce ” Mai ya fito da angon jiya yau? Mai ya fito da saurayi yau? Shin ya yarda al’adar mu ne KO yaya?

Mubasshir ya dago da kansa bayan ya daidaita muryar sa ya kali mahaifiyarsa sanan cikin raunin murya ya ce ” Maman mubasshir KO daya Mubasshir bai yarda al’adar sa ba , no ina matukar jin kunya maman Mubasshir cos nayi alkawarin bin al’adata shi yasa dole na dawo gidan nan a yau dan nayi biyaya , Mamana i’m sorry

Rintse ido Hajiya Fadimatu tayi domin sarai ta gane inda zancen ya nufa wato Sahla ba cikakiyar budurwa bace shi yasa ya dawo a yau , wata kunya ce ta kama ta da kuma godiyar Allah da ya Sanya duk basa nan , sai tausayin danta a ranta ta ce mai yiwuwa zuwa gaba ya samu cikakiyar , a fili kuwa tayi gagawar kawar da zancen ta mike ta kama hanunsa tayi wajen table da shi tana fadin albishirinka

Ya ce ” goro yana biye da ita

Ta ce ” Yau sistern ka tayi maka mutuniyar taka tun da safe ta farka ta daka ta da kanta , ta KO yi laushi sosai da gani zata birge ka

Mubasshir ya dan yatsina fuska duk da horon Hajiya Hawau ce aman tata ta daban ce sam bazata iya hada furar Hajiya ba

Zaunar da shi tayi sanan ta leka dan ganin rakiyar tayi ni sa da yawa

Tana lekawa ta ganta zaune tana kalon fulawowin gidan , a hankali ta ce ” Yar Fadimatu

Firgigit ta waigo tana amsawa ta mike a nitse ta karaso

Hajiya Fadimatu ta ce ” yayanki ne ya zo , ki zo ki bashi mutuniyar tasa , kinga kuwa kamar kinsan zai zo ta karashe tana yi mata murmushi

Yar Mahaukaciya ta shige itama tana murmushin , direct kicin din ta shige ta shiga dama furar da harhada komai da komai , ta dauko katon faranti ta jera kayan a saman sa harda jus jus din da ta hada ta dauko gabanta na faduwa tana tsoron kar aje har yanzu yana yanayin da ya shigo wato cikin bacin rai

Tana tunkarar table din taji Hajiya Fadimatu na aikin nata wato gargadi da ban baki , nitse tayi salama saï da ta ajiye farantin tsakiyar table din sanan ta tsuguna har kasa ta ce ” barka da safiya , an tashi lafiya?

Ciki ciki ya amsa mata da lafiya lau sanan ta Mike da niyar juyawa , Hajiya Fadimatu ta ce” yaya dai , a zo a karya KO?

Yar Mahaukaciya ta juyo a nitse ta ce ” No mama ai bana jin yunwa na sha jus din nan ta nuna jus na ayabar

Hajiya Fadimatu tayi murmushi dan a zaman da Yar Mahaukaciya tayi a gabanta jiya zuwa yau ta lura bata son hayewa abinci ta ce ” ai fa jiya ma abinda kika sha Kenan jus , aman yau da rana ni da kaina zan baki abinci ki ci

Yar Mahaukaciya tayi gaba tana dan murmushi , Mubasshir yayatsina fuska a ransa ya ce” iya yi duk haka suke shegen kin son abinci ga shegen boyayen mugun hali a tatare da su ya mika hanu ya bude furar bayan tafiyarta

Sahla ce konce tana kuka dan kuwa zuwa tayi aka yi mata dinki aka kara matseta sosai har doctern na fadin KO Aljani ne shi bazai gane cewar a bude take ba , sai dai kash bata san cewar duk inda take tunanin Mubasshir to ya zarce tinaninta sai gashi tun kafin ya idasa manufarsa ya gane cewar a bude fa take wani ya rigaye shi

Wayarta dake ajiye saman bed din ta dauki tsuwa ta Mika hanu ta dauko sunan mahaifiyarta ne ke yawo a Saman screen din ta dana ta kara tare da fadin hello cikin shakakiyar muryarta

Hajiya Marhaba ta ce” beby ya kika kwana? Ina fatan dai lafiya lau

Sahla ta ce” lafiya lau mama

Hajiya Marhaba taji muryar tata wata iri ta ce” kin tabata? Muryar taki nake ji wata iri

Sahla ta fashe da kuka tana fadin na shiga ukuna Mama wly yayi tafiyarsa , shin yaya zanyi?

Hajiya Marhaba ta kwashi di kira da salamewa ta ce” ya tafi gidan uban wa? Taya zai FITA ya barki a haka? Ba cewa akayi su ga yanda al’adar su take ba ? Kardai aje irin mazan nan ne an mori ganga an yar da sauran , ? Can tana tsakar fadanta wani Abu ya fado mata a rai ta dan dakata

Ta ce ” Sahla

Sahla ta amsa

Ta ce” ki fada min gaskiya u’r NT Virgin?

Gaban Sahla ya fadi ta shiga kame kame da inda inda

Hajiya Marhaba ta ce” Dan ubanki ki fada min gaskiya idan kin san a bude kika je masa gida ki fada min tun da wuri mu nemi mafita mu gayawa boka tun kafin ya dankara miki saki dan ubanki

Sahla cikin tashin hankali ta ce ” eh a bude

Hajiya Marhaba ta datse Kiran tana babalawa Sahla zagi da sakacin da tayi tun wuri bata sanar mata ba ayiwa bakin zaren tufka nan da nan tayi Kiran bokanta ta sanar masa komai abinda yake faruwa harda fadin a daure shi sai yanda suka yi da shi

Bokan ya bata amanar za’a fara aiki a lokacin ma aman Dole ta je da kanta

Hajiya Marhaba ta ce ” ba damuwa gatanan zuwa

To fah shin wanan boka zai iya kara daure AA Mubasshir??????? Muje zuwa😘😘😘😘😘

[11/19, 9:34 AM] ‪+234 909 534 8504‬: 🇳🇪Belles écrivaines du Niger

*’YAR 👧🏻*    

         *MAHAUKACIYA👹*

*_Na SAJIDA_*

                    38

*I’m sorry please ayuka ne sunyi yawa aman bi’izinillah zanyi kokarin ganin na gama shi love u*

Hakan kuwa akayi ta shirya da kanta ta je gidan bokan ya gama tsafe tsafen sa ya bata magungun nan da Sahla zatayi aiki da su dan ganin Mubasshir ya haukace a kanta

Daga gidan bokan ma direct gidan sahlan ta zarce tana isa aka tsare ta da tambayoyin Wace ita , sai da suka yi Kiran Sahla cikin fada ta ce” Mahaifiyar tawa zaku tsare a kofa?

Cikin Sauri ya bata hakuri ya bude mata

Hajiya Marhaba baki ta wangale tana kalon wanan gida , ita mamaki take da Mubasshir ke tuka kansa da kansa alhalin ya malaki arzikin da koda a jirgi ne sai ayi yawo da shi a tsakar garin Lagos aman may be bai yarda da kowa ba ne , su dai ta fado masu gasasa , haka har ta samu ta karasa cikin falon S
ahlan inda take tsaye tana jiranta

Sahla da kyar ta mike ta daukowa Mahaifiyarta jus dan bata son mai aiki ta gani aje Mubasshir ya sani

Hajiya Marhaba ta bita da kalo har ta dawo , abinka da uwar zamani kuma sam kunya ba a tsarinta yake ba ta ce ” ke da kika ce ga a yanda kika zo kuma wanan tafiyar fa ?

Sahla ta tabe baki ta ce” hm momy ba’a cewa komai ni fa gaskiya du na Sare, na tsorata gaskiya momy wly tsoronsa nake kamar raina

Hajiya Marhaba ta zaro ido ta ce ” tap to bara kiji abinda zan fada miki , haka zakiyi ta hakuri har ki saba , sanan ga sakon Boka nan kiyi tayi har mu kule masa bakin gaba daya kawai sai yanda muka yi da shi,  dan kuwa KO da wasa bana ra’ayi jin makamancin cewar ba zaki iya ba dan KO wanan gidan kadai ya malaka miki to fa mun haye balatana ina hango mana nesa

Sahla ta amsa tana kara yatsina suka ci gaba da hirarsu ba ita ta bar gidan ba sai da ta ci abincin rana karfe uku tayi sanan ta fito ta shiga motarta ta ficewarta ( to kaji )

Bayan tafiyarta Sahla ta Mike ta shiga aikata gaba daya abinda mahaifiyarta ta saka ta sanan ta darmi aniyar shiga ta daga hankali dan ta lura da mutumin ya FIya fadawa hanu

Tunda ta haura sama tayi konciyarta ta lumshe ido ta fada duniyar tinanin mai ya kawoshi gidan a yau shi da akace sai gobe? Aman mai yiwuwa yazo ganin mama ne dan a irin yanda ya shaku da ita daman da wuya ya iya kwanaki ba tare da ya ganta ba , tana cikin tinaninta baci yayi awon GABA da ita , ba ita ta farka ba sai da salar la’asar ta mike a firgice tana salati tana mamakin bacin da tayi a nitse ta nufi bayi ta sakarwa jikinta ruwa tayi wankanta tsaf Sanan ta fito daure da tawul dinta ta zauna ta bude Jakarta ta makaranta ta kama karatunta tamkar suna tsaka da karatun, sai da taji ta gaji sanan tana dan jin yunwa sanan ta mike ta bude Jakarta mai kayanta na sakawa , abin mamaki Hajiya Hawau sabin kayanta kawai ta zubo mata a jakar tayi shiru tana kalon wa’inda ta cire har wani dan wari suke dan kuwa da su tayi bacinta ta farka bayan ta ci aikace aikacen nan da su , ta kara dadagawa a zuciyarta ta ce , gaskiya bazan iya saka sabin kayan nan ba uwa wata amarya , to naje ina da su , gaskiya aa , ta koma ta dauko zaninta da rigarta ta mayar da kayanta hankalinta konce ta daure kanta da dan kwalinta ta nufi waje daidai ana kiran magarib ,

Mubasshir ne zaune suna ta kara tataunawa da mahaifiyarsa bayan adu’o’in da ta kara masa sanan ta bashi hakuri harda neman alfarmar ya zauna lafiya da matarsa kar ya nuna mata komai , yayi hakuri tunda ga abinda yasa ya aure ta to kawai ya jure kar ya goge aikin ladan da yayi niya

Mubasshir kansa a kasa ya ce ” Insha Allah maman Mubasshir zanyi biyaya sanan zanyi kokarin ganin na bi abinda kika ce i promise ,

Tayi murmushi ta ce ” Allah yayi maka albarka , Allah ya baka yaya masu biyaya

Ya ce ” Amin yana murmushi domin a rayuwarsa yana matukar kaunar yaya , yana son yaya sosai duk da yanzu wani tinanin ya fara darsuwa a zuciyarsa

Mikewa yayi ya rungume mahaifiyarsa yayi mata salama da niyar tafiya gidansa daidai nan Yar Mahaukaciya ta sauko ta tsuguna har kasa tana gaishe su

Hajiya Fadimatu ta kamo hanunta ta ce” kin sha baci sau uku ina shiga sai na tarar baki farka ba , yunwa bata tayar da ke ba ?

Yar Mahaukaciya tayi murmushi ta ce” Ai mama ni ma yau nayi mamakin bacin nan nawa ya jima sosai

Mubasshir dake tsaye yana kalonsu suna birgeshi tamkar Mamanshi ta haifeta dan dai farin wanan aljanar ya fi na mamanshi , a hankali ya ce ” zan fice sai na dawo maman mubasshir

Hajiya Fadimatu ta ce ” am Yarona nace ba , ina son saka yata makarantar islamiya kasan karatu da jama’a yafi shiga , kuma ina son ka fadawa kaf masu tsaron gidan nan cewar idan akayi baki da sunan ita suke nema to a barsu su shigo dan kaga akoy yan makarantarsu sanan yarinyata ta isa aure idan nayi siriki kar a tsayar min da shi a waje

Da Sauri mubasshir ya kaleta harda zaro ido gabansa yayi wani mugun faduwa idanuwansa suka wani firfito waje , ita kuwa wata irin kunya ta rufeta ta mike da sauri har tana hade kafafuwa wajen sauri ta shige kicin

Ya bita da kalo gabansa ya kara faduwa

Hajiya Fadimatu dake kalonsa tana nazarinsa ta ce ” kana ji ?

Mubasshir ya juyo da Sauri ya ce ” ohk toh zzzzan fada harda wata sabuwar inda inda da ta same shi , ya juya da Sauri ya fita ya nufi motarsa still gabansa bai dena faduwa ba

Hajiya Fadimatu tayi murmushi ta lumshe idanuwanta ita kadai ta san abinda take tinani sanan ta kuma yin wani murmushin ta mike ta nufi kicin dan ta dawo da yarta da taji kunyarta ta tsere

.

.

……………………… . . . . . . . . . . . . . . . . . .  . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . .

[11/19, 9:35 AM] ‪+234 909 534 8504‬: 🇳🇪Belles écrivaines du Niger

*’YAR 👧🏻*    

         *MAHAUKACIYA👹*

*_Na SAJIDA_*

                    39

Yana fita ya fada motarsa ya tayar ya kama hanya tafe yake kwakwaluwarsa tana cikin caji sai maimaita kalmar inalilahi wa’ina ilaihi raj’une yake ya rasa wanan wani irin tashin hankali ne ke tunkarar sa

Tun kafin ya isa kofar gidansa yake horn da gudu aka bude masa ya fada gidansa ya ajiye motar a nan ba tare da ya daidaita ta ba ya fito ya bar wayoyinsa a nan cikin motar ya nufi cikin gidan

Sahla dake zaune ta sha kananan kaya Wanda ilahirin jikinta a waje yake tana jin karar motarsa domin daman hankalinta gaba daya a wajen yake ,

Cikin yanga da karairaya ta Mike ta nufo kofar dan ta taro sa , kafin ta karasa har ya bude ya fado falon ja tayi ta tsaya gabanta na faduwa tana tinanin ta karasa ne KO ta juya ,balatana a irin yanda ya shigo

Tsayuwa Mubasshir yayi yana karewa Sahla kalo tun daga kitson atach din da aka yarfa mata kananuwa masu shegen kyau da yanayin tsarin halitarta da Allah yayi mata , sam Sahla a shafe take tun daga saman har kasan sanan abin haushin mamarta har sun dan fara faduwa daman gasu kananuwa hakan na nufin au haka halitarta take KO kuwa an zubar da su ne , yayi saurin rintse ido da ya Tina wai yayi taraya da matar da wani ya fara taraya da ita ,

Cikin bacin rai ya raba ta gefenta wani tirare mai karfin tsiya ya bige masa hanci take ya furta a’uzubilahi minan shaidanin rajim , yaci gaba da tafiyars ya nufi dakinsa

Da gudu Sahla ta bi bayan sa tana rungume shi ta baya ta saki wani irin kuka mai tsuma zuciyar duk wani mai saurare ,

Ta kai wajen minti biyar a haka sanan ya juyo da ita a gabansa cikin kakausar murya ya ce ” Kuka? Sahla kina kukan jin kunyar halayenki ne, kina kukan irin dabi’unki ne, kina kukan kin banzatar da kanki ne KO kukan na share ki kike?

Cikin shashekar kuka Sahla ta ce ” Haba Yaya Mubasshir mai yasa zaka yanke min irin hukuncin nan ba tare da kayi bincike ba ? Ka sani wly ba laifina bane kadara ce Wace ba Wanda yafi karfin ta afka masa, Haba Yaya Mubasshir dan Allah kai fa musulmi ne taya zaka yanke hukunci haka ba tare da bincike ba?

Mubasshir yayi tsai yana kalonta a ransa ya ce lale KO shekarunta nawa? Yarinyar da har tasan ita ba budurwa bace har ta san ta je wajen wani katon ya kara wangaleta yayi mata aiki dan ya mayar mata da abinda ta kau a titi wai itace zata yi tsaye ta kirayi kanta da kadara ? Tabas akoy na kadara kuma akoy na ra’ayi, ya lumshe idanuwansa a fili ya ce ” Kadara? To Allah ya kare mu da mumunar kadara ya juya dan kwata kwata baya son wanan yawan dumin

Sahla ta kara shan gabansa ta ce ” Dan Girman Allah , Dan Soyayarka da fiyayen Halita, Dan Darajar mahaifanka ka yafe min ka manta da komai muyi rayuwar mu cikin aminci dan Allah

Gaba daya ji yayi tamkar an dadaure masa gabobin jikinsa irin yanda ta hada shi da Allah , cikin kasalaliyar murya ya ce ” Tabas ni musulmi ne , bazan so na kwana da haushin ki a raina ba , sanan du mai yafiya Allah yana yafe masa kurakuransa shi ma , ya dafa daidai zuciyarsa ya ce ” Na Yafe miki , sanan zan ci gaba da rayuwar aure da ke aman fa bisa sharadi biyu zuwa uku idan kin amince

Cikin sauri Sahla ta ce ” na amince koma mainene

Ya danyi murmushi ya ce ” a yanzu na farko ina son ki dan nisanta kanki da ni na dan lokaci kadan dan na samu nutsuwa kafin na dawo gareki , a cikin gidan nake ba wani waje zan je ba , aman ina son nayi rayuwa da ibada har naji na ware da wanan , sai dai idan kin san kina da muguwar sha’awar da zata hanaki yin hakan

Wata irin kunya ta kama Sahla da dana sanin tarboshi a haka cikin sine kai ta ce” no aa ba komai Insha Allah zanyi iya yina dan ganin na kiyaye , mainene sauran sharadin?

Ya dan cije lebensa ya ce ” idan lokacin ki san su yayi zan sanar da ke , sanan ya juya cikin nutsuwa ya fada tankememen dakinsa yana sakin ajiyar zuciya

Sahla ta bishi da kalo tana cije lebe domin ta dirki magunguna gudun yau ma kar ta sha wahalar da ta sha jiya sai dai a banza  ga kuma maganin da aagaifiyarta ta ce shi kadai ma dubu ashirin ta baiwa boka sunansa malaka idan ya sadu da ita shikenan ta saye shi , haka ta juya tana mutsumutsutu ta nufi dakinta itama

Yana shiga dakin nasa ya nufi bayi ya dauro alwala ya fito ya kama nafillah yana karawa duk idan ya kai sujada sai yayi ta adu’a yana rokon sasaucin abinda ke damunsa , da ya gama ma ya mike ya cire kayansa ya saka na baci ya juya ya konta

Lumshe idanuwansa yayi yana adu’ar baci aman ina hotonta ya fado masa a idanuwansa ya mike tsaye ba shiri ya shiga zirga zirga a fili ya ce ” anya kuwa Mubasshir baka sayarwa kanka tashin hankali ba?

Ya koma ya fada ya jawo filo ya rukumkume yana sakin ajiyar zuciya aman sam bacin ya kauracewa idanuwansa banda juyi ba abinda yake yana kokarin cire hotonta daga idanuwansa dan kuwa sam basu dace ba , wanan zancen idan ya fito ai kowa ma sai ya debe masa albarka dan wanan ai cin amana ne

To fah mai ya hana honorable baci? Hoton wacece yake kokarin cirewa daga zuciyarsa????????????????????????????????????????????????????????????????????

🇳🇪Belles écrivaines du Niger

*’YAR 👧🏻*    

         *MAHAUKACIYA👹*

*_Na SAJIDA_*

                      40

Da kyar baci barawo yayi awon gaba da shi , baci marar dadi dan kuwa cike yake da mafarkai marasa dadi , a ganinsa domin mafarkinta ya kwana yi Wanda har wani zazabi ya zubo masa dalilin hakan dan kuwa damuwa bata daga cikin abinda ya sani , ba dai irin wanan damuwar ba

Konci tashi yau har kwana uku daidai da auren Mubasshir Da Sahla inda rabonsa da gidan mamarsa tun washe garin auren sa bai koma ba yana gidansa sanan shi da kansa ya cire dokar da ya dorawa Sahla KO ya rage tinanin abinda bazai fishe shi ba,

Kamar yanda ta saba ta farka da wuri tayi aikace aikacenta Wanda Hajiya Fadimatu tayi tayi ta rabata da su aman ina sai ta farka ta ga ta gama komai hakan yasa ta kawo ido ta zuba mata sanan tana matukar farin cikin irin yanda sam Yar mahaukaciya bata da ragonta sanan ga biyaya sosai take jin dadin yanda take kafakafa da duk abinda ya shafeta ,

Bayan ta gama aikinta ta koma dakinta ta tsala wankanta tana fitowa Hajiya Fadimatu ta fito cikin bakar abayarta ta sha nadinta tsaf masha Allah

Yar Mahaukaciya ta duka ta ce” barka da safiya mama

Hajiya Fadimatu ta amsa tana mikar da ita ta ce” yata zan fita , may be na dan jima , daga nan zan biya makarantar ku dan hutu kinga ya kusa karewa na ga abinda ya dace ayi KO?

Yar Mahaukaciya ta ce” to mama Allah ya kaiki lafiya ya maido ki lafiya

Hajiya Fadimatu ta amsa da amin ya Allah sanan ta juya tana mai adu’ar Allah ya sa wanan hadi da sukayi niyar yi alkhairi ne

Hajiya Hawau na hango cikin mota tana zaune da hijabinta zumbulele Hajiya Fadimatu ta karasa direba ya bude mata ta shiga sanan ta ce” unguwar yan baiwa zaka kaimu inda wakili ya sauka

Direba ya ce ” toh Hajiya sanan ya harba motar bakin titi ya kama hanyar gidan wakili Elhaj Muhammad

Hajiya Fadimatu ta gaisar da Hajiya Hawau cikin mutunci sanan ta ce ” tabas nima na yarda da tarbiyar yarinyar nan domin camera na laka a dakinta duk abinda take aikatawa ina kalonta sanan ina saurare , sai dai abu guda dake daure min kai ,

Hajiya Hawau ta ce ” mai yake daure miki kai?

Hajiya Fadimatu ta ce ” am akoy abinda ke damun Rahma domin ta fiya tinani KO haka Allah ya halice ta?

Hajiya Hawau ta ce ” tabas nima na sha ritsata da tambayar shin tinanin mai take saï tace ba komai , sai nafi mayar da hakan kan KO dan yaronta ya rasu ne ?

Hajiya Fadimatu tayi shiru sanan ta nisa ta ce” hakane , Allah ya sa abinda zamu aikata alkhairi ne dan ni kam nayi ta rokon Allah kan isan har ba alkhairi bane to ya cire min wanan tinanin daga zuciyata aman cikin ikonsa a kulum kara sha’awar hakan nake

Hajiya Hawau ta ce” tabas alkhairin Kenan Allah ya biya mana burin mu sanan ya kade shetan

Daidai nan direban ya bubude musu kofa suka fito suka nufi falon inda wakili Elhaj Muhammad ke zaune yana jiran karasowar su

Bayan sun gaisa Elhaj Muhammad ya dago kansa ya gama nazartar Hajiya Hawau tabas daga ganinta ka ga tsohuwa mai kamala , sai dai ba a nan gizo ke sakar ba , shin da gaske ne abinda ta fada ?

A nitse ya ce ” baba tabas na gamsu da bayananki sai dai wani hanzari ba gudu ba ,mai zai nunan shedar eh lale yarinyar nan mutuniyar kirki ce? Sanan shi yaron nan baba jininki ne kuwa?

Hajiya Fadimatu ta dauko wayarta ta ciro wata memori ta jona jikin TV daram sai ga vidion Yar Mahaukaciya tun zuwanta gidan da yawancin maganarta harda idan tana tare da kawarta Fati , da komai sanan ta ce ” Yaya ka yarda da maganata ka jagoranci daurin auren nan domin yarinyar nan yar Amana ce ceton rai zamu yi , Allah shi zai bamu ladan mu

Elhaj Muhammad ya aa numfashi ya sauke Sanan ya ce ” toh babu damuwa Allah ya sa alkhairi ne , yanzu su liman din suna can dakin bakin KO?

Hajiya Hawau ta amsa da eh suna can

Ya ce ” sunan yarinyar Rahma wa?

Hajiya Hawau ta ce ” lokacin da tazo daidai da sunanta ta manta hakan ya sa mukayi duk yanda ya dace a musulunce muka saka mata Rahma

Elhaj Muhammad ya kuma kalonta shi dai yana dan kokonto aman bashi da wani iko a nan Dole ya aiwatar da umarnin hajiya fadimatu haka ya mike ya tafi wajen su liman din da niyar daura auren Rahma da agonta ……………………………………………………………………….🤷🏻‍♀🤷🏻‍♀🤷🏻‍♀🤷🏻‍♀🤷🏻‍♀🤷🏻‍♀🤷🏻‍♀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *