YAR MAKIYAYA CHAPTER 10

YAR MAKIYAYA




CHAPTER 10




Duk de yadda akayi akwai dalilin restlessness na Ummin Habeeb, a shafi na baya tayi magana a kan idanuwan Laila ko miye dalili? Bari mu garzaya muji yadda dinner zai fara…..

“Sapna!”
“Na’am Ummi!” Fitowa Sapna tayi daga d’aki tana kallon Ummi.

“Ummi gani ” Murmushi Ummi tayi tace
” na tabbata Yayan ki Suraj ya baki labarin Laila ko ba haka ba?”
“Eh Mom , meyasa kike tambaya? Ita da tak’i ta zo nan? ” Murmushi Mom tayi ta shafa kan Sapna tace

“Idan kuma nace miki ta zo fa? Kuma tana tare da mu a cikin Wannan gidan? ” zaro ido Sapna tayi tace
“Wait Mom! Na sanki you are not good at zolaya “
“Ba zolaya bane tana nan d’akin yanzu dare yayi amma gobe in Allah ya kaimu ina so ki kaita domin makeover, ina so ta chanja ki tabbata Suraj bai had’u da ita ba har se komai ya kammala it’s going to be a surprise ina fata kin gane?”

Tsalle Sapna tayi ta mak’ale wuyan Ummi tace “wow! Ummi Yaya akayi kuka iya taho da ita? Nai miki alk’awari se Yaya Suraj ya kasa gane ta ma, Mom ni barin je wajen ta in yaso zan sauk’o tare da ita mu ci abincin. Kai Mom ta jinjina tana dariya “Toh ni kar ki ka da ni maza ki je”. Da sauri Sapna ta nufi d’akin Laila ta kutsa kai gami da yin sallama.

Amsa Sallamar Laila tayi tana ta faman gyara doguwar vintage gown d’in da ta kasa d’aure igiyar ,Murmushi Sapna tayi ta k’arasa ta gyara mata rigar. D’ago wa Laila tayi tana kallon Sapna ganin hakan yasa Sapna tayi Murmushi tace

“Oh yi hak’uri babbar Yaya! Nice Sapna K’anwar Habeeb, gaskiya Yaya Suraj ya fad’i gaskiya, komai da ya fad’a ba k’arya kin kai mak’ura wajen had’uwa, Yaya Suraj ba k’aramin sa’a yayi ba I must say.
Yawwa na zo mu tafi k’asa don cin abinci nasan kina jin yunwa zo mu tafi”. Sapna ta kama hannun Laila suka fita…

Wak’ar ta take tana gyara zaman plates dake dining table saboda lokacin dinner ne hankali kwance take aikin ta cikin rawar kai.

Da fito yake sauk’o wa daga bene sanye da 3quater wando brown da bak’ar shirt button duk a bud’e hakan ya bayyana farin vest d’in ciki ,zubewa yayi kan lallausan kujera setin ta yake kallo yana yamutsa fuska ita kuwa Zainab se k’ara sautin wak’ar ta take yi

Da k’arfi yayi ihu yace “Allah ya bada sa’a”!!!
Tsayawa Zainab tayi tana kallon shi yayinda yayi saurin maida kallonshi ga k’ofa. A hankali ya juyo suka had’a ido ya tab’e baki yace “ke malama kiyi abinda ya shafe ki ,kin wani sa min ido anga d’an handsome ,Toh kwalelen ki aradu.”

Tab’e baki tayi taci gaba da wak’ar ta tana gyare gyare.
Tsalle Habeeb yayi daga kujerar da yake
Yace “Wayyo Allah! Wai daman ba almajirai ne ke bara ba kece kike wak’a? Tab Allah kuwa na zaci bara ake yi irin na marok’an nan shiyasa nace Allah ya bada sa’a Ashe kece. Murya sekace gogen tsumma!!”

Had’e rai Zainab tayi tace “wai ni Toh ina ruwan ka da ni ne? Dube ka kamar tsohon inyamuri wai ka sa kaya yo kai har wani kyau ne da kai da har kake wani burga? Wanda ko a kyauta aka ban kai zan ce Albarka ”
Wani takaici ne ya rufe Habeeb ya bud’e baki zai maida Martani ya hango Ummi da Mom suna zuwa saboda haka ya ja balance kan kujera ya zauna yana d’an humming wak’a, kamar babu abunda ya faru ita ma Zainab taci gaba da harkar gabanta , ba’a jima ba Sapna suka sauk’o tare da Laila , ita Sapna Uwar surutu ce Laila kuwa shiru se Murmushi. Su ma dining suka nufa Sapna ta ja ma Laila kujera ta zauna sannan ta ja na gefen ta ita ma ta zauna zainab ta fara taya su zuba wa duk abunda ke faruwa Habeeb na kwance cikin kujera yana wani shu’umin Murmushi

“Bro Habeeb kai bazaka zo mu ci abincin ba?” Sapna ta tambaya , zaro ido yayi yace
“Wa !? Wai ni? Allah sauwwak’e in ci jagwalgwalen wannan k’azamar ku de da kuka saba ci bisimillah *aci dad’i lafiya*
Komawa yayi ya kwanta ganin yadda Ummi ke galla masa harara.

Kusan a tare suka kai loma , Zainab ta shiga kitchen se jin ihun Sapna ta jiyo ai kuwa ta runtumo a guje se gani take kowa yana faman tofar da abincin bakin shi da kyar Ummi ta bud’e baki tace

“Zainab!!! Me kika aikata wa abincin nan? Sapna da yanzu ta gama k’urban ruwa tace “Toh wai wannan ma abinci ne?”. Zainab da jiki ke rawa ta d’auki cokali tayi loma d’aya ko gama gauraye bakinta abincin bai yi ba ta Furzar tana goge bakin , yayinda lokaci guda ta zube tana kuka.

Habeeb tuni ya mik’e yana dariya harda rik’e ciki ya ce “wuhuhu Wayyo Allah! Ina fata yanzu kun fahimci dalilin da yasa nake gudun cin jagwalgwalen wannan k’azamar? Gashi yanzu kun shiga tarkon ta.

Ummi ta bud’e baki zatayi fad’a wa Zainab kwatsam ta hango Habeeb yana tsalle irin na victory a bakin k’ofa hakan yasa ta fara zargin wani abu

D’ago Zainab tayi tace “it’s alright ya isa hakanan kukan, nasan ba laifin ki bane an d’an samu matsala ne ,ina ga kawai d’auko min mayafi na da Makullin mota ,se mu fita ko a nearest eatery se mu ci abinci “. Tana fad’in haka Habeeb ya ji haushi ya cije leb’e ya fice ,Mom ma ta lura da hakan ,Murmushi kawai tayi ta mik’e yayinda Sapna tayi kicin kicin ta b’ata rai tana Hararar Zainab..Tun bayan sun dawo daga motsa jiki da safe tare da Habeeb ya yi wanka sannan ya dawo falo ya zauna, manta wayar sa yayi a d’aki dan haka ya koma upstairs don ya d’auko,

K’ofar d’akin ta bud’e ta fito se kalle kalle take tana k’ok’arin neman hanyar da zata bi ,karo suka ci da juna ba shiri ya rik’o ta saida ya tabbatar ta daidaita tsayuwar ta sannan ya sake ta, se lokacin ya d’ago kai baki a sake ya zaro idanuwa waje cike da mamaki
“Laila?”
Ya fad’a yana kallon ta ,Murmushi kawai tayi.

Sapna dake tsaye a bayan su ta dafe goshin ta da hannu ta buga k’afa kafin tace
“Oh my gosh! Komai ya birkice yanzun haka! “

Cikin rashin fahimta Suraj ya saki baki yana kallon Sapna wanda yanzu ta k’araso kusa da su yace “wait a second! Wai daman kina sane Laila ta zo? So dake aka had’a baki a mayar da ni wawa ko?”

Nad’e hannu tayi a kafad’a tace “waye ya maida ka wawa? Kawai de muna so mu baka surprise ne kuma gashi ka riga ka ganta, tunda haka ne ga shawara! “
Gyara tsayuwa Suraj yayi yace “miye shawarar?”
Sapna tace “how about ka raka mu shopping ma Laila,abun da yawa ga makeover ga dinkuna da sauran su nasan zaka taimaka, in yaso se muyi breakfast mu fita”

Hi five suka yi yace “Shawara me kyau ! Come on!! Let’s have something to eat! Sapna ta ja hannun Laila suka nufi downstairs, Mom da Umma har ma sun fara karya wa ,Ummi na hango Laila ta kalli Suraj sannan ta kalli Sapna tace
“Ai daman na sani, dole se kin b’ata mana shiri,ni da na so y’ar fillo ta bashi wahala kuma kika bada gari tun wuri haka? Kai da kayi fishi ka bar gida ma?”
Murmushi kawai Suraj yayi ya ja tea mug ya fara had’a wa ko a jikin sa yana yi yana kallon Laila da ko k’ok’arin had’a tea d’in bata yi.

Habeeb ne ya fad’o cikin kujerar da ke tsakanin Laila da Suraj dan haka Suraj sai ya lek’a kafin ya gan ta ita kuwa duk abunda take yana sane se b’uya take yi kar ya ganta.

“Malam ka bar y’ar mutane ta ci abinci hankali kwance mana! Gaba d’aya ka sa ta kasa yin ko loma d’aya, in ta k’oshi in kaga dama ka maida ta TV na bango flat screen ka yi ta kalla” Habeeb ne ke magana, duk wajen ya d’auki dariya ,Zainab ta ji komai da ya fad’a hannun ta d’auke da. Fresh juice a jug , tana ajiye wa tace,

“Dube shi! Wani wai TV na bango, yo ai gwara shi Suraj ya fito da tasa kai ko daidai da kwaila baka tab’a kawo wa Mun gani ba a matsayin suruka.
A fusace Habeeb ya mik’e zai bi Zainab amma ta ruga yayinda Suraj ya chafke hannun sa yana dariya Sapna ma dariyar take.

“Ai gaskiya ta fad’a!” Cewar wata murya da ta fito daga wani b’angaren gidan.
Dariya Sapna tayi ta zaro ido waje cike da fara’a tace “Dad! Amma gaskiya ka shammace mu! Yaushe ne ka dawo?”

Dad kamar yadda Sapna ta k’ira sunan sa , Murmushi yayi sannan ya k’arasa inda suke ya ja kujera next to Sapna ya shafa kan ta kafin yace “jiya na iso late at night kun yi bacci duk” Habeeb ya duba kafin Habeeb d’in yace “barka da Safiya Dad “,

“Barka ka dea! Ai ni da na yanke shawara tunda ga ita Zainab d’in me zai hana ayi y’ar gida kawai? Tunda kaga yanzu ai Zainab y’ar mu ce, kuma fa kun dace Habeeb”.

Kafin dad ya gama magana Habeeb ya Furzar da Shayin da ke bakin sa , cikin tashin hankali da har Laila saida ya bata dariya yace 
“Wayyo Allah ! Dad na tabbata barci ne bai ishe ka ba watak’il ba Zainab d’in nan kake fad’i ba ko? Wa zai iya fama da K’azama? ” mik’e wa yayi kamar me hauka ya bar wajen su Ummi se dariya suke mishi.
Kai Dad ya girgiza da Murmushi ya dubi Suraj da sai lokacin ya d’ago kai yace “morning Dad” 
“Morning son ,kana lpya?” 
“Lpya lau Dad” Suraj ya fad’a a tak’aice.
Haka ma Laila ta gaida shi ya kuma amsa cike da fara’a, don mutum ne mai son wasa, haka suka kammala break fast cikin nutsuwa dan Habeeb baya nan.

*Three weeks later*

     Laila kam ta saba yanzu da mutanen gida  saboda Sapna tana nan , sannan ga Zainab komai normal sannan kullum tana waya da baba kamar yadda aka mata alk’awari, babu wani takura a zaman gidan su Habeeb ,b’angaren Junaid ma haka domin ga Suraj ga kuma Habeeb. Sedai har yanzu suna shan dariya domin Laila tafi Junaid d’aukar abu da wuri, kafin kace me ta koyi abu banda Junaid se ya sa shirme amma sam hakan baya damun su Ummi don kam ana shan dariya.

Kwanaki biyar ya rage bikin Sapna gida ya fara amsa k’iran bak’i , kullum Laila tana tare da Sapna ta yi kyau da ita yanzu kam kana ganin ta kaga baturiya.

Suna hira a falo Dad yayi sallama suka shigo tare da Dad d’in Suraj, 
Suraj dake zaune saida gaban sa ya fad’i dim! Tuni ya mik’e ya nufi upstairs zuwa d’akin sa, Dad d’in Habeeb ya d’an saki Murmushi yace “mu shiga ko?”.
K’arasa wa sukayi falon suka suka zauna yayinda duk su Habeeb suka kwashi gaisuwa, kafin Laila.

Ido Dad ya k’ura mata na d’an wasu lokuta kafin yace “she must be Laila ko?” Da Murmushi Abban Habeeb yace “eh ita ce ,y’ar k’ani na Rasheed, shima da yau zai zo amma se suka yi bak’i a wajen aiki kuma dole ya tsaya , “. Murmushi Dad yayi ya sake kallon Laila yace

“Ba komai Allah ya kawo shi lafiya, ni yanzu duk a gajiye nake I need to freshen up , take some rest sannan na iya zaman hira.” Dariya Abban Habeeb yayi ya mik’e yace “gaskiya kam don ka sha hanya”. Haka suka wuce ciki suka bar yaran a wajen, Sapna ta dubi Laila suka yi dariya kafin suka mik’e suka nufi d’akin Suraj tare da Junaid da Habeeb….

   K’ofar ya turo yana k’are wa falon kallo fuskar shi d’auke da shu’umin Murmushi hannun sa d’aya jacket ne ya rik’e d’ayan kuma jakar kayan sa ya d’aura ta kafad’ar sa , cikin takun k’asaita ya shigo tsakiyar falon ya tsaya, ya cigaba da kalle kalle kafin ya jefar da jakar a k’asa ya kama kunkumi.

  Tsaye take rik’e da bowl na salad tana kallon sa don bata tab’a ganin sa ba, “yanzu wannan bai wuce abokin wancan Goggon birin ba mtsew”.
Ajiye bowl d’in tayi ta haura stairs duk bai ma sani ba yana tsaye rik’e da kunkumi, ba’a jima ba ta dawo tare da Ummi daidai lokacin Mom ta shigo don tun d’azu tana garden ,baki a sake Mom ta ce 
“Innalillahi wa inna-ilaihirraji’un! Me kuma wannan yake yi a nan? Why is it that duk lokacin da Suraj ke k’ok’arin samun kwanciyar hankali Ameer se ya shigo lamarin? ” ba tare da ta nuna damuwa ba ta k’araso da y’ar Murmushi wanda bata kai zuci ba tace 
“Ameer my son! Ashe kaima zaka zo? ” Murmushi kawai yayi mata wanda shi kad’ai ma ya bata amsar tambayar ta , gaida ta yayi sannan ya gaida Ummi da ke tsaye ita kam ji tayi kamar tayi masa korar kare, ko amsa shi bata yi ba ta dubi Zainab tace

“Ki kai shi d’akin gefen Habeeb nasan zai ji dad’in zama a chan sannan kuma ki tambayi me yake buk’ata ki girka masa nasan da yunwar sa yazo ki kuma sanar da Omar Yariman Belel Ameer yana gidan ,duk abunda yake buk’ata Umar yayi masa.” Toh Ummi” Cewar Zainab kafin ta sa hannu ta d’auki jakar da Ameer d’in ya jefar ta wuce idon ta cikin nasa yana mata kallon sa na munafurci ita ma kuwa tana masa na rashin mutunci kafin ta murgud’a masa baki ta wuce ya bi bayan ta.

Zubewa Mom tayi kan kujera ta dafe goshin ta da hannu Ummi ta ma rasa yadda zata yi don babu halin Ameer da bata sani ba Tun ma bai kai haka ba.
” kar ki damu y’ar uwa komai zai tafi yadda ake so In shaa Allah”
Kai kawai Mom ta jinjina kafin ta mik’e tayi d’akin ta tabar Ummi zaune tayi jugum da ita.What the jahannam!😱 Ameer again? Me Dad yake tunani da zai taho da Ameer Kaduna! Beware ! Ameer can never be trusted. +

      “Kai Suraj! Me yake damun ka ne wai? Abunda kayi fa ba daidai bane you can’t just ignore him that way” Habeeb ne ke magana.
D’ago wa Suraj yayi ya rufe laptop d’in gaban shi yace “look! Ni ba ignoring Dad nayi ba, It’s just that ko na masa magana ma bazai kula ni ba saboda d’azu Mun yi waya yace yana hanya kuma tare da Ameer wai don na nuna banji dad’i ba shine yace ko ya zo bai buk’atar gani na and he mean it, Habeeb wai don Allah wannan wacce irin rayuwa ce haka? Dad bai gane halin Ameer bane, Ameer can never be trusted saboda munafuki ne! Kawai yana shiga tsakani na ne da Dad”

Zama Habeeb yayi bakin gado yace ” wai nikam me yasa yake maka haka? Ameer yayi nisa fa! This has to be stopped! Someone’s got to put an end to this! ” Laila de na zaune kan bedside drawer Sapna na jingine a bango ta nad’e hannu a kirji kafin tayi tsaki tace

“Mtsk! Ni fa gaskiya kar ya kawo mana cikas don nasan ba tsakani da Allah ya. Zo nan ba” cike da b’acin rai ta ja hannun Laila suka fita zasu tafi d’akin Sapna

    Tafe yake hannayen shi duk cikin aljihu se kalle kalle yake ,karo suka ci da Laila Sapna na biye da ita, 
D’ago kai tayi suka had’a ido Ameer ya tsaya kallon ta cike da mamaki kafin ya shafa gefen fuskar yayi ya na tuna inda yasan fuskar ita kuwa se neman hanyar wuce wa take yi daidai lokacin Suraj  ya fito daga d’aki yana waya ,turus yayi ganin yadda Ameer ya k’ura wa Laila ido da alama yana so ya gano wani abun Sapna dake bayan Laila ta galla masa harara kafin ta kama hannun Laila zasu bi d’ayan gefen su wuce 
   Gaban su ya sha duk suka yi turus suna kallon sa ,bai d’auke ido a kan Laila ba ita ma bata fasa k’ok’arin tsere masa da kallon sa ba

“Kamar na tab’a ganin fuskar nan?” Ya fad’a yana shu’umin Murmushi.
  Dake wa Sapna tayi tace “Wai wannan fuskar? Eh to ba mamaki zai yiwu ka tab’a gani d’in domin ita a Turkey take da zama birnin Istanbul.” Naji ance a chan kayi makaranta.

“Wani Murmushi ya sake yi kafin yace ” Hmmm ko?”

Bai sake magana ba saboda Suraj ya k’araso wajen ,dubansa ya mayar kan Suraj tuni ya had’e rai , ganin hankalin sa na kan Suraj su Sapna suka yi saurin wuce wa suka bar su a wajen.

   Zagaye Suraj yayi da kallo kafin ya dawo ya tsaya a gaban shi yace “Seems like baka ji dad’in gani na ba a nan!  Ko? Don’t worry ba don kai na zo ba, y’an mintina basu fi hud’u ba da suka wuce na fahimci Cewar kai ma ba tayar baya bane wajen iya rainin hankali , amma ni bazaka raina min hankali ba, wasan ka yayi kyau but yanzu asalin wasan zai fara”

Suraj da ya tsaya kallon shi bai iya furta komai ba tsabar takaici har ya gama maganar da zai yi ya wuce zuwa d’akin sa.

Kafad’ar shi yaji an dafa juyawan da zai yi yaga Mom tsaye fuskar ta d’auke da damuwa , Murmushi yayi mata kawai ya bar wajen ba tare da yace ko k’ala ba , Mom bata matsa ba har saida ta daina hango shi sannan ta yi nata hanyar.

  Ranar duk cikin su babu wani me walwala, Sapna da Laila suna chan suna ta y’an shirye shirye gida se k’ara bunk’asa yake yi ,duk abunda ya dace Amarya tayi duk Sapna tana yi, gyaran jiki da sauran su. 
Laila kuwa kowanne yini yinsa take cike da fargaba kar Ameer ya gano ta, yayinda Suraj ko da wasa baya bari ya shiga harkar Ameer ,amma duk da haka komai na gidan Ameer yana sane ,kuma ya sa ido sosai, Dad kuwa tun isowar sa da yaga Suraj basu sake had’uwa ba se yau da ya kasance babban rana ce gare su a  masallacin juma’a suka jame ,ko da Suraj ya gaida shi da kyar ya amsa, bayan sallar juma’a aka d’aura auren Abdullah Ali da Sapna Abdur-ra’uf Ali , ba sai na tsaya kiyasta adadin jama’ar wajen ba da kuma shagulgula da aka yi ,haka ma cikin gida , biki yayi biki Sapna kuwa Washegari aka kai Amarya gidanta dake garin Kano .

Laila sam taji ba dad’i Amma babu yadda zata yi, Ummi ma ta ga Lailar ta chanja shiyasa take ta k’ok’arin taga an d’ebe mata kewa.

   Dad yana zaune a falo su Mom suka shigo , nan suka shiga hirar su ta manya, 
A hankali ta ke tafiya kamar wata mara lafiya se dube dube take yi , Mom ne ta kalle ta kafin tace “Laila Yaya dai nagan ki wata iri yau d’in? Kina buk’atar wani abu ne?” 
Murmushi Laila tayi kafin tace

“A’a kawai na gaji da zaman ne ni kad’ai shine nake neman Zainab muyi hira.”

Dad ya kwantar da kanshi jikin kujera yana kallon Laila Kame yana suspecting wani Abu yace
“Why is she acting as if she  were a stranger? ?”
Ummi ce ta yi saurin katse shi da fad’in
” Laila kawai damuwa ce ke damun ta ,kasan sabo da mutum in anyi rabuwa ba dad’i she just missed Sapna suna tare since childhood” kai Dad ya jinjina yace 
“Suraj yace tana Istanbul kuma se bayan watanni hud’u zata dawo am surprised da na ganta a nan.
Abban Habeeb ya yi saurin katse shi da fad’in

“Ohh you shouldn’t be ! Mamaki ba naka bane saboda kasani cewa Laila da Sapna zasu yi koma miye to see each other happy” 
Kai Dad ya girgiza yace “yes haka ne .”

Mom kam nannauyar ajiyar zuciya ta sauk’e a ranta tace “wannan mijin nawa ko lawyer iyakaci”

Laila kuwa tuni tayi kitchen inda ta iske Zainab tana aiki ,itama tayata tayi suna hira suna aikin……

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *