Y’AR MAULAH CHAPTER 3 BY MAMAN TEDDY

Y’AR MAULAH CHAPTER 3 BY MAMAN TEDDY 

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Tun da ta tun kari, Office din takejin Kirjin ta na bugawa,wanda itah kanta Sectary nashi,a tsorace take dashi”. Amma a haka tasa hannu hadi dayin knocking a jikin Kofan”. Sai da suka kusa minti Sha biyar a tsaye,sannan sukaji Muryan sa yana masu Umarnin su shigo daga ciki”.

Jiki a salube suka shiga,sectaryn nashi a gaba. Safiyyatu na Bin ta a baya!!.  Ko Umarnin Zama bai basu ba,wanda Itakam Safiyyatu sabd tsaban kauyanci bin wurin take da kallo,tana tunanin Abubuwa da Yawa a xuciyarta”. Sai asannan ya dago hadi da xiba mawa Sectary nashi shnyayyun idanuwan shi”. Wanda yasata saurin kasa da kanta tana Fadin Good morning sir”. Bai bata amsa ba ya juya ga Safiyyatu da sai a yanxu ta dawo hanyaccinta”. Hada ido sukayi wanda sai da takara fito da dakwa²n Idon ta waje…Shima din ita yake kallo,don komai ya dawo masa yanxu.itace yarinyar Da kan ya taho nan Ya kusakadewa”. Ya mutsa baki yayi kan ya kauda kai yana zaman jiran Jin ta gaisar dashi amma sai  yaji shiru”. Juyowan da zaiyi ne yaga itama ta juya kanta gyefe tana kallon Gyefen windown Office din nasa”. Mamaki ne yayi matukar kamashi,Haushin yarinyar ya kara rufesa”. Tuno da Abun da tayi masa A akan kwalta yasa shi karajin Wani Haushi,ga kuma mulkin da take shirin nuna masa,taxo har Office din sa wai zata juya shi”. A ranshi yace” Kina kaskantacciya??? Waye ke???.sai ya dake yana cigaba da duba takardun gaban shi”. Itakam Safiyyatu Haushin sane itama anata bangaren duk ya gama cikata”. Takaici duk ya isheta,Tuno da Garirogon Oumman ta da yasa ta xubar,sai dai Tasha mai kasa,sabd mugune shi.abun da take cewa kanan a Zuciyarta”

Hmmm Nan ya kalli sectaryn shi yana sauke ajiyar zuciya da cewa” Okay wannan Yarinyan Ce??. Ehh Sir. Okay ki bata komai na Uniform ki kaita wurin Endrew kice basai an mata Enterview ba”. Abarta ta fara xuwa gobe. Miss Gwandu ta mata bayanin Salaryn ta Fah day,da kuma Duk Wata”. Cike da mmikn yanda Ya amince da Safiyyatu lokaci guda Sectaryn tace” Okay sir”.Anan bangaren namu Zata ring aikin Cleaning din?…. Kaman baiji mai tace ba” ya cigaba da rubuce²n sa,kan yace,Office dina zata ringa gyraww da komai na”. I dont like too much Talk. Go Out!!. Ya fadi cike da Dan tsawa!!! Wanda yasa Sectary da Safiyyatu saurin ficewa” A ranta Safiyyatu tana cewa” Wai Lallai masu kudi suna baxa mulki,Wannan wulakanci haka??. Shikam da fitan sane ya tsaya yana bin Safiyyatu da kallon zaki San koni Waye. Don yasa ma ransa cewa” Sai yayi maganin Wannan Mummunar yarinyar mai Hanci dagagge”.😂

Itakam Safiyyatu da Fitan tane tabi bayan Sectary hadi da nufa da itah Office din Miss Nagwandu,wanda ta kasance itace” Shugabar Masu cleaning din Company”.

Bayan Isansu ne,matan cike da mutuntawa ta amshi safiyyah,hadi da bata Uniform wanda suke farare kal,sai hijab karami iyah Wuya guntu,Mai launin Brown. Har ta kalmin su cover ne,kuma anan NaGwandu ta bata”. 

Kan takoma ga Mr.Andrew ta masa godiya hadi da nufar Wajen Compyn,ranta far I kal. Don Farin ciki yasa bakin ta yaki Rufuwa”.

Napep ta Tara hadi da kaita unguwar su,sannnan ya sauketa ta gangara,layin su”.

Tun da Baba Jume ya hangota ya nufota yana kirarta,tsayawa tayi tana murmushi hadi da Nina masa Uniform din da suka bata Kala uku,Aiko nan Baba Jume yakara wangale bakinsa. Yana aikin godiya ga Allah”. 

Da suka shiga daga ciki ne,Oumma taji labari haka take ta murna da Saka mawa Diyartata Addu”a.

A washe gari kam,da Sassafe Safiyyatu ta shirya tsaf da itah, cikin Uniform din da yy mata azabar kyau,duk da Bakace sosai ya haskata,don fatan ta irin BB colaour ne”.

Tun da ta shiga Company kowa ta gani zata gayshesa cike da mutuntawa suke amsata,wanda abunka ga mai suna Safiyyah dason mutane ga Farin jini,tini kowa yake  nan nan da itah,duk da itace Yar Talakawa,kaskantattu”. Miss Ngwandu kuwa,sosai ta kara koya mata Abubuwan da akeyi a Office din Sir Omar Maccido,wanda tun kan yaxo ta kalkale ko inah,har Privacyn shi”. Sai da ta gyara ta saka Room freshener,sannan ta rufo masa Office din”.

Kusan karfe 11am ne tana,zaune hadi da Tata Miss Ngwandu wasu aiyukan,ne kirar Sir Omar yaxo mata”.

A sanyaye ta nufi bangaren sa,hadi da knocking,jin shiru yasata Tura kofan hadi da Shiga kai tsaye Abunta”. Ba tare da tunanin wani Abuba”. 

Zaune ta ganshi da  Layla tana saman cinyar sa,suna aikin kissing din junan su,sam basu san da shigowanta ba. Sai karar Yarda flask din da Sectary tabata tana cemata,Is part of her duty”. Don haka ta kara kiyayewa”.

Babu abun da takeji sai Tsuuu….tsuuuu kaman wasu mayu…..Ganin Abun da bata taba gani ba yasata Yarda Flask din,tana cewa’Innalillihi…..Subhanalllh”. 

Sai asannan Suka juyo hadi da kallonta,Itakam jikin ta sai Bari yake yana karkarwa”. Cikin Xafi Hjy. Layla ta jubeta cike dajin tsanarta a zafafe ta Ce mata” Are you mad??? See Stupid.  Ta fadi tana Nuna nata da Hannu”………………

Jikin Safiyyatu ne ya hau Rawa kaman mazari,Rasa Abunyi kawai yasata saurin juyawa Tana Dad’a Zubar da Kwallah,Cikin Wani irin mugun Tsawan Hjy.Layla tace”Keee”. Tsayaawa tayi cak, Tana Bin su duka da Kallo,Kwallah na cikah idon ta,Bayan Wanda yake Zubo wa a kuncin ta”. Kallon Omar Hajiya Tayi da ya Kauda kansa gyefen kamaan Bai Masan Allah yayi Ruwar Su a wurin ba”. Husby waye ya kawo wannan yarinyar Nan Wurin???.Kallon ta yayi kan ya Kauda kai yana Fadin” tambayeta”. Ba tare da Ta kuma Maimata mata tambayar ba,Safiyyatu tace”Bokowa Hajiya”. Okay tom Waye ya dauke ki aiki a masana’antan nan?”. Kan tace” Wani Abu ne Omar ya Kalli,Safiyyatu da take ta xubar Da kwallah,tom dama hakan yakeson gani,shine Dalilin da yasa Yace” ya dauketa aikin,tom gashi Layla tayi maganin ta,Don haka Wannan ma ya ishesa”. Fuskar sa a Dan Hade,wanda dama tuntuni a hakan yake ne yace” mai yasa kk ta wannan Tambayoyin ne?. Hmmm Keehhh daga yau kar nakara Ganin ki a wannan Companyn,fita kibani,Kazamiyar Yarinya kawai”. Da Sauri Safiyyatu ta fice tana Dada Zubar da Hawaye,Wannan Wani Irin Rashin mutunci ne?,Mai tayi mawa Wannan Baiwar Allah ta tsaneta haka??. Tana Kuka ne ta ke wannan maganar a xuciyar ta,wanda da fitowan ta bata nufi kowa ba,face Sectary da take Tambayar ta Lafiya???. Anan ne Wasu sababbin Hawayen ya cigaba da Sauka a kan Fuskan ta,kan daga bisani tace” An kore ni ne!!!”. Kirjin Sectary ne ya bada damm”. Tuni tausayin Safiyyatu ya kamata matuka,don Tabbas Tasan Da Wannan,Duk wanda Zatayi aiki a Office din Sir Omar Maccido,Bata Rufah Satin yake Sallamarta,Ai kinshi kenan,Yace Find another Cleaner P.A.  nisawa tayi a ranta,tana cewa” Tom Shikam P.A aiki ya sameshi,yanxu ma sai yakara cewa” Anemo masa Cleaner. Daga wani File tayi tana Fiddo,wasu kudi wanda a kallah sun kai Dubu Hudu ne,ta mika mawa Safiyyatu,da cewa” Kiyi Hakuri Safiyyah,Mai Hakuri shikeda Riba,Ga wannan Kiyi na Transport. Hannu Safiyyah ta saka ta amsah Kudin tana mawa Sectaryn Godiya”. Wanda Cikin Sauri S
ectaryn tace” Muje na Rakaki!!. Da tom Safiyyatu ta bata Amsah,kan su fice xuwa farfajiyar Masana’antan”. 

Wata Shimfudediyar moto Ce kirar Accury,Ta shigo xuwa Cikin masana’antar,Wanda yasa Sectaryn da katawa tana cewa” Ohhh ni Jiddah,Safiyyah tsaya Oumma na ce taxo gani na!!”. Tsayawa Safiyyah tayi,wanda tuni Security sun bai baiye Moton Hajiyan Suna mata sannu da Zuwa,Abun ka da Wurin Aikwai Kudi,shiyasa duk kallo ya koma Idon ta”. Fitowa matan tayi,wanda Ganin Ta yasaka Safiyyatu Fiddo da Idon ta waje, A xuciyar ta ne ta ambaci Sunan ta Da Lami??!. Sai kuma tayi saurin juyawa tana nufar gate naa fita  Company don Sam batason suyi ido Biyu da wannan baiwar Allah. Da fitan tane ta tare Napep,tana shiga,wanda a sarari take cewa” Wannan Shine an gudu ba’a tsiraba,tom tayaya Matan Dana Santa a Bauchi ta taho Adamawa”. Tambayar da tayi ta Watso ma kanta kenan,har ta sauka a napep din”. 

Koda Ta koma gida,bata sanar mawa Oumma cewa” An koreta ba,sai Baba Jume da yaga ta dawo da wiri sosai”. Wanda bata boye masa Komai ba,ta fadesa duk Abun da Yafaru. Sam bai nuna mata ya damuba,sabd ya kwantar da Hankalin ta,kawai sai yace” Okay tom Safiyyatu,Kar ki samawa Ranki,Allah yasa haka shine Mafi Alheri”. Ameen tace” Sannan ta nufi Dakin Oumman ta”.

A haka tayi kwana biyu a cikin gidan,Oumma dai Tuni ta fahimci da Matsala,ammma Safiyyatun bata Fadeta ba sabd Damuwa kar tasamawa Ranta”. Ganin Abun yaki ci,yaki cinyewa ne yasa Oumma da kanta tayi mata magana”.Wanda Yanda ta fadimawa Baban Nata,haka itama ta fadeta”. Itama Oumma Addu”a tayi,hadi da Rarrashin Safiyyatun”. Wanda Tun daga nan ta Saki ranta,tama manta Da wani batun company”.

Bayan Kwana Uku ne suka cigaba da Barar Maularsu tana mawa Oumma Jagora,Dama shine masu Dahir”.

********************

Zaune Hajiya Latifah akan Dinning wanda da”alama Break sukeyi da Mai gidan Nata,Alh. maloniya”. Bayan takai Kai Spoon din Couscous Bakin tane ta kalleshi tana cewa” Alh. ya kamata a Yanxu ace mun manta da Bul-bul,Ba dauki Hakuri,da juriyar Rashin ta garemu,komai Kaddara Ce”. Ta fadi maganar cike dason Kwantar mawa Da Alh. Maloniya da Hankali”. Wani irin murmushin su ta manya yayi,kana yace da itah’ Baxan taba iyah cire Soyayyar Bul-bul a xuciyata ba”. Gudan jini na?,  Ita Ce daya fah da na rike a Yar Gareni”. Tayaya Zan manta da wacece Bul-bul. Hawaye ne ya ciko Idon Hajiya Latifah a sanyaye tace” Haka ne Alh. Tun da Hakanne,Mai Zaisa ka karo Wata matan,a matsayin  Abokiyar Zama ta”. Tunda kasan ni Dai an Riga da Anciremun Mahaifah baxan Taba kara Haihuwa ba”. Kaga Xamuyi ta xama ne a cikin gidannan babu ma gaji,babu wanda Zamu kallah muji sanyi??”. Ya isah Hjy. Latifah,ya isah,Alkawari ne nayi,har Abada Bazan yi maki kishiya ba”. Koba komai kin bani Bul-bul,kuma nasan Rashin Haihuwar ki ciwone daga indallah”.Shiru Hajiya Latifah tayi,tana Kara matsar Kwallah,Tabbas Alh.Maloniya miji ne,kuma Uba,ga duk Macen da tasameshi tayi dace matuka”. A haka suka cigaba da Break din,yana kokarin ganin Ya kwantar da Hankalin Matar nashi’. Wanda bai samu natsuwa ba sai da Yaga ta Saki,suna fira da Dariya”.

**********************

Bazan Mantaki ba har Abada,Kanwata kuma matata,Kece kk fara sani cikin Farin ciki,Wanda nake maki Addu’ar Rahama a duk inda kk ya kaimaki”. Yana maganar ne Hawaye nabin saman Kuncin sa,Hannun sa daya Dauke da Hoton Bul-bul,wanda shine yazama masa Abun kallo,a ko inah nansa”. A bedroom din sa hoton tane,har A moton sa yasaka Hoton ta,da Office din sa,Haka Safwan yake,sam bashi da aiki kullum sai ganin Hoton ta yana kallo,Maryam dake Kwance tsawon Daren takasa Bacci ne,duk Abun da yake a idonta,wanda itama duk dauriyar ta batasan Lokacin da Takaici yasata fara kuka kasa² ba”.  Shikam ban da kallon Fuskan Bul-bul babu Abun da yakeyi”. Wanda anan ne ya tuno da Maganan ta yana masa Ansa kuwa a kunnen sa”. Yah Safwan”. Ya Safwan Zan tafi,Amma ni nasan inshaallh xan dawo gareka,wannan mafarkin dakayi,duk sharrin shaidan ne,Ka koma Dakin ka kayi Addu’a,inshaalh xan dawo gareka. Zama yayi a gyefen Bed side drower Nata yana cewa” Kin tabbata??. Daga masa kai tayi da cewa” Inshaalh Yah Safwan!!”. Komai ne yafara masa Yawo,har ta xubewar da yayi gaban Gawan Nata tana mace” Cike da Firgici ya ambaci sunan ta da Karfi”. bul- Bul….”

Saurin mikewa yayi daga kwancen dayake,wanda sai a sannan ya Lura Ashe mafarki yakeyi”. Waigawa yayi Bangaren da Maryam take,anan yaga tana makale dashi tana ta sharar Baccin ta hankslin ta kwance”. Tausayin ta ne ya kamashi,nan ya kai bakin sa,saman Goshin ta yana manna mata kiss,kan ya rabata da jikin sa a hankali ya mike yana Dada rufa mata Bargo,ya nufi Toilet”. Alwala ya dauro,wanda Da futowan sa ya shimfida Sallaya,sannan ya fara sallah don Addu’ar Rahama yakai mawa Bul-bul din tasa”.

Bangaren Omar kam,tun ranar nan da Layla ta kori Safiyyatu,hankalin sa yaki Kwanciya sam,kuma ya rasa Dalilin hakan. Sam da ya kwanta bacci otah yake gani tana Zubar masa Kwallah…wanda yanxu Haushi duk ya ishesa,na mai Ruwar sa da,Yarinya da,har yake mafarkin ta haka”. Yarinyan dako sunan ta baima sani ba”. A haka yayi watsi da Itah a xuciyar sa”. Da cewa kilah ma Maiyace itah”.

Safiyyatu ne da Oumman ta Akan hanyan su ta dawo gida,suna tafe suna Barar Maulah,wanda yaga dama ya basu wanda bai ga damaba,ya hantaresu da cimasu mutunci…jingina yayi da Jikin moton sa yana kare masu kallo,wanda sam bata ma Lura dashi ba”. Har sai da suka xo gabanshi suna Maular”. Hada ido sukayi Itah da Omar,ko wannan su yana mawa Dan Uwan sa Kallon²…Wanda Kwakwalwar Sir Maccido ya tsaya cak da aikidon ya raasa Ma Abunyi…….

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *