YAR NAJERIYA CHAPTER 5 BY SUMAYYAH ABDULKADIR

YAR NAJERIYA CHAPTER 5 BY SUMAYYAH ABDULKADIR 

                  Www.bankinhausanovels.com.ng 

Saheeb, yana falon su a zaune yana jiran fitowar Hasna’u cikin tsananin bacin rai bayan shigewar Nusaiba dakin Mama.  Ya ji shiru-shiru har wajen mintuna talatin ba Hasna’u, sai yayi tunanin ko ta canza shawara tana wankan ne don haka ya cigaba da jiran ta yana yi yana duba agogon hannun sa yana tsaki, don ba karamin bata masa rai Nusaibah ta yi ba har bai san sanda yayi furucin da ya yi ba, kuma an ce Magana Zarar Bunu ce… ta riga ta fita, bashi da ikon mayar da ita.1

Tsoron shi Allah tsoron shi kada ta je ta hada shi da Mama, don haka yayi maza ya bi ta dakin Maman, ilai kuwa yana gab da shiga ya ji ta tana waya ya kuma tabbatar ba da kowa bane da Mama ne “…..wannan zabiyar ta Unity ya kawo mana gida har yana neman duka na don nace bazan bata soso na da sabulu na tayi wanka ba har da cewa……”. Saheeb ya yi maza ya doke wayar daga hannun ta ta fadi kasa, ya bi ta ya take da takalmin sa ta wargaje. Nusaiba ta kwalalo ido tace .

“Yaya Saheeb! My phone?”

“An fasa din, bakin ki ma ina gab da fasa shi in kika fada mata abinda kikai niyya. Wallahi Nusaiba ki fita harka ta na ga alama raini ya fara giftawa a tsakanin mu” ta zumburo baki ta sunkuya tana tattare fasashshiyar wayar ta, sai yasa takalmi ya take mata hannu sai da ta saki kara don azaba. Ya ce “wallahi Allah na kara jin zancen zabiya a bakin ki ko a kunnen Mama sai na  fyato ki. Ni sa’an ki ne ko abokin wasan ki? Ina ruwan ki da duk wanda zan kawo gidan nan? Gidan ki ne ko na Uba na ne?”

Nusaiba ta soma hawaye. Tace “tun kan ka auri zabiyar kenan? Ranar da ka aure ta ashe raba ni zata yi da kai. You never talk to me in this manner Yaya Saheeb sai akan Zabiya, don haka kasa a ranka wallahi (I hate her with passion) kuma ta yi kadan ta aure ka.

Na ji bazan gayawa Mama abinda ka fada ba amma kasa a ran ka bazan taba son Zabiyar ka ba.

I want my darling brother back to me….this is not my Yaya Saheeb…”. Ta fashe da kuka sosai.

Saheeb sai ya ji jikin sa yayi sanyi, wai meke da Zabiya ne da al’umma ke kyama haka? Ya dauka digon maniyyi ne ya samar da kowanne dan adam kuma shi ya samar da Zabiya? In haka ne kenan ashe duk daya muke (irrespect of skin colour) sai wanda ya fi tsoron Allah? Kanwar sa Nusaiba needs a counseling on disability ba fada duka ba.

Ya zauna a kusa da ita yace “Nusaiba-Nusy, you are my only sister da bani da kamar ta ya kamata ko me na zo da shi ki fahimce ni, ni ban ce auren ta zan yi ba, tausayin ta nake ji. Na yi alkawarin kulawa da rayuwar ta a matsayin ta na marainiya ba uwa ba uba ga nakasa. Ina son ganin rayuwar ta yi kyau kamar ta kowa despite her abnormality.

Kin san yawan ladan dake cikin hakan? Ita din miskiniya ce dake bukatar tausayi da jin kai daga al’umma, amma irin abinda kike yi a kan ta jahilci ne, mai ilmin addini in ya san farkon sa bai san karshen sa ba, kada ki manta kema mace ce, kuma haihuwa zaki yi nan gaba kadan, kin san irin halittar da zaki haifo?

Zaki so al’ummar duniya su taru su juya mata baya don tafito ba irin sauran mutane ba?

Nusaiba yanzu haka Maman ta ta mutu, yau sati biyu ba tare da ta sani ba!”

Ya karasa fada yana kifa kansa a kafadar ta, Nusaiba could not believe it, da taga hawaye cikin idanun sa.

“This is serious!” ta fada a fili, “Yaya Saheeb da gaske son yarinyar nan ka ke yi?”

Kai ya shiga girgizawa har yanzu kan sa a kafadar ta. Yace.

“Nusaiba I don’t know, son ta nake ko ba son ta nake ba. All I know shine zan sadaukar da rayuwa ta don ganin tata ta yi kyau. Zan iya batawa da duk wanda ya tozarta ta” Nusy ta ture shi daga kusa daga ita tace “Har Mama, har ni?”

Ya dago a hankali ya dube ta idanun sa sun kada, a hankali yace “I tried my best to make you understand amma kina komawa wani direction din daban. Now, face your business and leave me”.

STORY CONTINUES BELOW

“I will not leave you Yaya Saheeb, I must get my brother back, yarinyar nan ba haka ta barka ba”.

“Me kike nufi da ba haka ta bar ni ba?” “It’s possible charming din ka tayi, in ba haka ba meye hadin zabiya da Yaya na Saheeb duk ‘yammatan da ke fadin duniya da irin matar da Allah ya baka mahaifiyar ka ta zaba maka? Sai ka kare a disease?”.

In bai kai zuciyar sa nesa ba zai kare ne da yiwa Nusaibah dan banzan duka, haka take da kafiya da taurin kai kamar Mama, shikuma as softhearted as their father late Alh. Wamakko. Kullum yayi gabas, Nusaiba da Mama sun yi arewa.

Fita yayi ya bar ta a dakin zuciyar kowannen su na tafasa, ya nufi dakin Nusy ganin har zuwa lokacin Hasna bata fito ba.

Ya duba cikin dakin bai gan ta ba, ya karasa kofar toilet din yana kwankwasawa, shiru ka ke ji, babu Hasna’u babu alamar ta.

Da sauri ya fito waje yana tambayar mai aikin su Tani dake shanya ko ta ga wata farar yarinya da uniform? Tace ta fice tun dazu. Da sassarfa ya karasa wajen maigadi yana tambayar sa mintuna nawa da fitar yarinyar? Maigadi yace tafi minti biyar da ficewa.

Sai ya koma ya fada mota ya kunna yayi reverse ya durfafi get da mugun gudu, tuni maigadi ya wangale get din don bai taba ganin Saheeb cikin gaggawa haka ba tunda aka haife shi. Domin kuwa a kan idon sa aka haife shi a gidan.

Tafiya yake a gefen titi yana mamakin meyasa Hasna’u zata yi masa haka? Daga ki yi sallah ki fito? Sai ki kama hanya alhalin baki san kowa ba cikin gari irin Kano? Ba mamaki bacin ran abinda Nusaiba ta yi mata ne yasa ta ga gara tayi tafiyar ta.

Gumi ya shiga barko masa da ya tuna ya karbo amanarta ne wajen Kawun ta, in bai ganta ba me zai ce masa? Ko daure shi aka yi bashi da hujjar kare kan sa, tunda har principal ta san suna tare.

Bai kai karshen fita daga layin su ba ya hange ta tana tafiya a gefen titi tana ta zuba sauri kamar zata tashi sama, yayi maza ya sha gaban ta da motar ya sauke glass daga ciki yace.

“Hasna’u”.

Yadda ya kira sunan ta da rauni, sai zuciyar ta ta idasa karyewa, dama idon ta jike yake da hawaye.

“In kin yarda ni Yayan ki ne Saheeb kuma bazan cutar da ke ba, taimakamin ki shigo motar nan in maidawa Kawu Sama’ila amanar sa dana dauko, daga nan ki yanke hukuncin duk da kike so akan alaqar mu, ni dai ta fanni na ba gudu ba ja da baya wajen zamowa bango abin jinginar Hasna’u, kiyi hakuri ko me ya faru ni na jawo miki, saida ki ka ce min bazaki je ba sabida gudun hakan, ni kuma ba don komai na takura kije ba sai don ina so ki saba da karbar kalubale kowanne iri daga mutane mai dadi ne ko mara dadi? Rayuwa bata taba yiwuwa without challenges from people koda kuwa a ce ke kika fi kowa kyau a duniya sai an samu wanda zai ce kyan nan naki ba alkhairi bane, shaidan zaki zamewa mijin ki.

I want you to Open your heart and mind and learn how to accept critcsm no matter how bitter, shigo mu tafi kin ji Hasna’u?”.

Idan ta ce zuciyar ta bata ragargaje da dadin kalaman sa ba ta yi karya, haka idan tace bata yarda da duk abinda yace ba ta cika butulu. Amma abinda bai sani ba shine ba abinda Nusaiba ta yi mata ne yasa ta barin gidan su ba wutsiya a zage ba tare da ta jira shi ba, sai don tana so ta kawo karshen wannan alaqar, alaqar da ta fara lura bazata haifar mata da Da mai ido ba kuma karshen ta nadama zai zama.

“Ki nemo majanyi da zanin goyo kifara shirin goya ALBINOS domin wannan zabiyar itace uwar ‘ya’ya na, Insha Allahu”.1

Wadannan  sune kalaman da suka fiddo ta daga gidan Wamakko helter-skelter, ba tareda second thought ba. Domin bai yi kalaman da sigar da za’a ce wasa yake ba, haka intonation na muryarsa a lokacin da yake furta su kaifin sa yafi na takobi, domin maganar ta fito ne kai tsaye daga karkashin zuciyar sa ba tareda shi kansa ya san ya yi ba.

STORY CONTINUES BELOW

Amma a maganar sa ta yanzu yace zai bata zabi akan alaqar su, fatan sa kawai tayi masa alfarma ya maida amanar da ya dauko. In har zaya bata wannan damar, to yau ce rana ta karshe da alaqar tasu zata kare. Allah ya kai su gida lafiya.

Da kansa ya fito ya bude mata kofa ta shiga, ya maida ya rufe silently sannan ya koma nasa mazaunin.  A yadda yake tukin motar tamkar tayoyin ta sun yi faci, kuma a gefen titi don ma kada ya sha zagi daga motocin gaban sa da bayan sa.

Ji yake kamar kada ya maida ita wannan gidan nasu da ba abinda zata fuskanta a cikin sa sai wahala, tunda babu sanyin idaniyar ta Inna, to in bai kaita nasu gidan ba wanne zai kai ta? Ko dai kawai ya gudu da ita ne ya nema mata shelter? Anya in yayi hakan Kawu Sama’ila zai taba yafe masa? Ya yarda da shi ya amince masa bari ya tabbatar da wannan yardar, ya tabbatar masa har yanzu cikin ‘yan adam akwai masu amana.

Sai da suka hau babban titi dodar ya tuna bata son A|C sai ya kashe, ya kunna mata sautin Khusairi cikin Suratul-Al-Imran. Kamar ya san surar da take matukar so kenan kuma a ita suke a islamiyyar su ta cikin UNITY wato daga ita sai Baqarah sai saukar su, wanda zai zo daidai da kammala SSCE din su.

Sai ta hau bin karatun a zuciyar ta wata irin nutsuwa na shigar ta, tsoron Allah na kara samun gurbi a ran ta. Ta ji dama su dawwama suna wannan tafiyar ita da Saheeb, watakila daga yau bazata kara ganin sa ba, don ta riga ta yankewa kanta kawo karshen alaqar su, kada tausayi da jin kai irin nasa su sa ya saki layi ya hau kan turbar wanda su duka ba zai bulle dasu ba.

Suka tsaya a Wudil ya je ya sayo mata soyayyen kifi ragon ruwa da ruwan sha, daga shi har ita an rasa mai Magana, zukata kadai ke kiyasi, kowanne kuma da abinda yake kiyastawa daban da na dan uwan sa. Ita tana tunanin hanyar kawo karshen alaqa, Saheeb yana tunanin hanya mafi dacewa ta maida alaqa infinite. Sai a lokacin da ya ajiye mata kifin ne ta ji kamshin sa ta dan motsa kadan tace .

“Bana cin kifi, inada allergy da cin kifi”.

Ya dube ta a hankali da lumsassun idanun sa yace.

“Dama shi yasa na so tafiyar nan, don in san likes and dislikes din ki, and I know a lot in one day, ga tsoro kamar farar kura”.

Murmushi ta dan yi ta juya kan ta ga taga, bata ce komai ba.

Ya cigaba da tuki har suka kusa albasu, lokacin shidda na yamma ta yi, ya tsaya a garin albasu ya saya mata lemun La-Casera mai sanyi guda biyu sannan ya shiga wani shago ya dinga sayayya.

Sabulun wanka dana wanki, omo, maclean, brush, deospray, hypo, Dettol soap, Vaseline da sababbin panties, always pad, indomie, kayan tea da kuma slippers ya sayo cikin katuwar bagi ya zo yasa a kujerar baya. 

Ya je ya bi jam’in sallahr magriba a kofar shagon sannan ya zo ya tadda Hasna’u ya tada motar.

“I’m sorry for keeping you waiting Yayan naki akwai kailula”

“Sallah fa ka yi, to ai dole in jira ka don Inna ta ce it ace sama da komai”. Saheeb ya juyar da kai kamar bai ji ta ba, zuciyar san a kokawa da hawayen idon sa.

Daga nan basu kara Magana ba har suka shiga Kachako, kawai ta ga yana daukar hanya babu tambaya domin tuni ya rike gidan Kawu Samaila.

Kugin karshe da motar ta yi a kofar gidan Kawu Samaila ne. Ga yara suna ta wasan dare an kunna aci bal-bal wasu kuma na gefe suna sayar da soyayyar gyada marau-marau. Hasken motar yasa duk suka dare suna ihu. Duhun dare da ya shigo yasa basu san su waye a cikin motar ba don Saheeb ya kasha fitilar.

Ta juya da zummar yi masa godiya ta fita sai ta hango idanun sa cikin hasken farin wata suna wani irin sheki da maiko kamar na hawaye amma dai basu gangaro kan kundukin sa ba. Tace.

“Yaya Saheeb bani da bakin gode maka, sai dai in ce Allah ya yi maka sakayya da aljannah madaukakiya ya ji kan ka kamar yadda ka ji kai na. Allah ya shige maka gaba a kan dukkan al’amuran ka ya baka duka binda kake nema a rayuwar duniya”.

STORY CONTINUES BELOW

Ta murda handle din kofar da zummar ficewa, amm sai ta ji shi gadagau (a kulle). Ta juyo tana duban sa da idanun bidar dalili? Sai y langabar da kai yace mata.

“Abu daya nake nema yanzu a rayuwa ta, ki taya ni rokon Allah to make it easy for me wurin mallakar sa, ta ko’ina na juya na hanga na hango it is not easy, duk da haka ban fidda rai ba kuma ban ja da baya ba, sannan gaba na bai fadi ba. Tunda Allah ya ce “La taqnadou min rahmatullah…”.

Hasna’u tayi murshi, he’s always bold, kuma dama ita ta tsani ragwan ta, tana son mutum mai yarda da kan sa da jajircewa bisa ra’ayin sa.

“Idan alkhairi ne a gare ka Allah ya baka, idan ba alkhairi bane Allah ya musanya maka da mafi alkhairi sa. Ka dinga sanya tagociya a addu’ar ka sabida ba duka abinda muke so bane yake zame mana alkhairi ba”.

Ta sake kokarin bude mota amma ko gezau. Da ta juya saida tayi nadamar juyawar a karo na biyu.

His eyes are sparkling tamkar hasken wata dan daren goma sha hudu. A cikin su wani yanayi ne mai wuyar fassarawa wanda bata taba gani cikin kwayar idon kowa ba.

Muryar ta na dan rawa tace “ka bude min in fita Yaya Saheeb, nan kauye ne, bai kamata muyi ta zama cikin mota ba”.

Da wata irin murya kasa-kasa yace.

“Idan kuma na fito na tsaya a zaure a ce na zo zance ko?”

“ZANCE?”

Hasna’u ta maimaita Kalmar cikin sigar tambaya don kuwa da gaske bata gane mata ba.

“Eh mana, idan na fito zauren ku muka tsaya muna Magana ya zama zance irin na saurayi da budurwa”.

Da sauri Hasna’u ta lullube fuskar ta da hijabin ta tana fadin ‘’ka bude min kofa Yaya Saheeb”. “An ki a bude, sai kin gaya min sunan saurayin ki?” “Ya ilahi!” Hasna’u ta fada a fili amma ta kasa sauke mayafin da ta rufe ido da shi, shi kuma yace bai bude kofa sai ta gaya masa sunan saurayin ta.

Da ta ga lokaci yana ta ja, sannan yaran gidan su sun fara taruwa suna shafa  motar sai tace masa a hankali kamar cikin rada.

“Banda abun ka waye zai so zabiya ne?  Ni fa ka san Allah ban taba yin Magana da wani namiji ba bayan malamai na a class ko staff room. This is out of my vocab-bank (vocabulary Bank)”.

“And it must be included in your vocabulary bank, because at this stage da kike ciki na gab da kamala makaranta its either ki zabi miji ki gabatarwa Kawu, ko ya aura miki duk wanda ya ga dama”.

Hasna’u a ran ta tace “ashe kuwa zamu shata babban layi ni da Kawun, nan kusa ban ga ranar aure na ba, daga ni har Inna karatu muke so na yi”.

Murmushi Saheeb yayi, domin shi mutum ne mai karfin ji, abinda take zaton a zuciyar ta ta fada ya gama shigewa kunnen sa. Ya kuma gamsu da abinda tace din na bazata bari a yi mata aure yanzu ba, kafin nan zai tunanin mafita ga rayuwar su, koda kuwa hakan na nufin….

Ya dauke ta ne ya gudu da ita inda basu da kowa a daura musu aure. Idan Mama ta ki.

“Ka yi wa Allah Yaya Saheeb ka bude min kofa in fita”.

Ta fada kamar zata yi kuka.

“Sai na gama kallon mata ta!”.

Hasna’u bata san lokacin da ta bude light blue eyes din ta tana kallon shi ba, kallon mamaki da tsoro, hadi da firgici.

Wadannan sune kalaman da har abada bazata manta ba, domin sune mabudin littafin kaddarorin ta masu dadi da marassa dadi. Sune kuma suka maida zarar bunu…. ta zama babbar maganar da ta kai ta har matakin da take kai a yanzu.1

Ya lura da irin kallon da ta ke yi masa na firgici da tsoro, sai ya lumshe mata lumsassun idanun sa tare da daga girar sa guda daya. Ya saki lock din motar ya fita ya zagaya ya bude mata, amma sai ta kasa fitowa tamkar an sa glue an manne ta a  kujerar.

Bai takura mata ba, ya koma booth yana sauke kayan ta yana baiwa yaran suna shiga dasu gida.  Suna ta ihu “ga zabiya ga zabiya ta dawo”.

Wani bakin ciki yazo ya tokare Saheeb a kahon zucci. Why not al’umma bazasu kira mai nakasa da sunan yankan sa ba? Sai dai a kira shi da inkiyar sunan nakasar sa?”

Suna gama shiga da kayan sai ga Kawu Sama’ila ya fito da sauri da far’a yana “maraba lale da mutanen Kano, ya bashi hannu amma Saheeb sai ya tsugunna akan gwiwowyin sa bai bashi hannun ba yana gaishe shi with due respect.

“Ayi hakuri kawu mun yi dare, hakan ya faru ne a bisa layin ganin likita” Kawu yace “babu komai Sahabi, ai na san yadda ake ganin likita a Kano, kwanaki da ido ya matsa min ai can naje, Murtala, kada ka so ka ga wahalar da na sha sai I yanzu na dawo gida”.

Ya maida duban sa ga Hasna’u tana fitowa daga mota jiki a mace kmar wadda ta sha duka. Ya ce “ka gaya mata ne?” Da sauri Saheeb ya girgiza kai “a’ah Kawu, gara kai ka gaya mata da kan ka” “to babu laifi ka je, Allah ya kiyaye hanya nagode Allah yayi maka albarka. An yi gilashin?” “Eh an yi, ji bi zan karbo in kawo maka, insha Allah”.

Babbabn abinda yake burgeshi da yaron kenan, komai zai ce sai ya hada ta da Kalmar “insha Allahu”.

Daidai lokacin da Hasna’u ta karaso tana gaida Kawu, ya dube ta da tausayawa yace “shiga gida gani nan, kicewa Hajjo ta baki abincin ki”.

“Ai ya saya min abinci na ci Kawu, Sallah dai zan yi in kwanta in huta” Kawu y ace “to maza ‘yar albarka, shi din kun yi sallama ne?” Hasna tayi maza ta shige gida bata tankawa Kawu ba. Ya yi murmushi yace “ai Hasna’u bata son Magana Kawu, in ma nayi mata sai ta ga dama take tanka ni” Kawu yace “haka take fa, uwarta ma Allah ya jikan rai haka take, sai su wuni basu kula kowa cikin gidan nan shiyasa sam basu da abokin fada, basu da abin yi sai sana’ar sayar da abinci da surfen su”.

“Kawu a gaya mata ta lallashi, ta kyakkyawar siga, a nuna mata dukkan mu na haka ne Inna bata yi gaggawa ba muma duk jiran tamu muke”.

Kawu yace “je ka kada kayi dare da yawa, na san yadda zan bi da ita, gashi ba iya kwanan zaure zaka yi ba da ka kwana dakin su Hassan in ya so da sassafe ka tafi”.

Murmushi yayi ya juya yan fadin “ba kwanan ne bazan iya a nan ba, watarana zan zo na kwanan, yanzun ina kan uzuri Kawu”. Kawu ya ji dadin abinda yace masa yayi ta saka masa albarka.

Kawu Samaila bai koma gida ba sai da Saheeb ya ja motar sa ‘kia-picanto’ a hankali ya bar harabar gidan sa.

Sannan ya juya ya nufi gida, zuciyar sa cike da kaunar yaron da kuma alhinin abinda zai gayawa Hasna’u.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *