YAR NAJERIYA CHAPTER 7 BY SUMAYYAH ABDULKADIR

YAR NAJERIYA CHAPTER 7 BY SUMAYYAH ABDULKADIR 

                 Www.bankinhausanovels.com.ng 

Tana kudundune cikin zanin Inna a can karshen gadon bonon ta, rabin gashin kan ta ya fito, wanda ba baki bane gabadaya, a kwana biyu kacal tayi mugun ramewa, ‘yan idanun sun kara kankancewa daga ‘light-blue’ sun koma ‘ash colour’. Ba zaton ta ba tsammani, kawai sai ganin Uncle Saheeb ta yi a gaban ta.

Ya tsaya hannayen sa biyu zube cikin aljihu staring at her straight in to her eyes with so much sympathy and pity, bai zauna ba daga tsaye motsa baki yace

“HASNAH!”

Saukar muryar sa ke da wuya cikin kunnen ta da gangar jikin ta, sai ta ji duk wani rauni na duniya da maraicin duniya  ya rufto mata….. ‘this is indeed a shoulder to lie on’, zata so ta kwanta a wannan kafadar… tayi kukan ta mai isar ta a inda ta san za’a lallashe ta a gaya mata mai dadi, amma babu dama tunda ta san ba muharramin ta ba ne ba. Kawu sai ya kasa tsayawa tare dasu ganin sai kallon juna suke bakin sun a motsi idanu fal hawaye, ya juya ya fita.

Saheeb ya tsugunna a gaban gadon bonon Inna yasa gwiwoyin sa a kasa, cikin raunin murya yace “pls accept my heartfelt condolence, Allah ya jikan Innar mu da Rahma….”. Ai kamar jira take sai ta kifa kai a jikin bango, ta bude sabon shafin kuka.

“Hasna’u come and cry on my shoulder…..idan kukan zai sa ki ji sanyi? Amma mafi a’ala, mafi fa’ida, mafi dacewa ba kukan bane, addu’a ce a gare ta.

Hasna’u da gaske yau kwana biyu baki ci abinci ba?” 

Ta soma share hawaye da zanin Inna, tana sheshsheka irin ta wanda ya ci kuka ya koshi. Gashin kanta yake kallo mai kama da na tsofaffi amma sai yaji bazai taba cewa da ita tayi dying ba koda Allah ya cika masa burin sa na auren ta, zai zauna da ita (against all odds in her natural defect and abnormality) kuma zai gaya mata bakin gashin mata ba komai bane face irin nata watarana, suma duka fading zai yi, amma akwai lokacin da zai gaya mata hakan ba yanzu ba.

Bagcon da yayi mata sayayya ya janyo sai ya tarar ko tabawa bata yi ba, ya dauko ‘juice’ din ‘exotic’ da madarar ‘hollandia’ ya dauko kofi cikin kwanukan dake gefe a wanke, Inna sarkin tsafta ta wanke ta kife abin ta, babu ko ledar tsakar daki a dakin sai karauni, amma ko’ina kalkal yake sannan gadon su babu shirgi sam sai wani kodadden zanin gado, sun shirya kayan sawar su su cikin kwandon roba mai murfi.

Ya zuba jus din cikin kofi ya bata sannan yace cikin lallashi “akwai risho in dafa miki indomie?” ta bude idanu tana kallon sa kawai, yace “Hasna bazaki yimin magana ba?” Ta juyar da kai bata ce komai ba, mikewa yayi yana duba kayan wajen don duk wani kayan amfanin su Inna bata barin shi a waje, ilai kuwa rishon ta na nan, harda ashana a kasan shi, ya dau karamar tukunya ya zuba ruwan swan a ciki ya kunna, tun ruwan bai yi zafi ba ya zuba indomin da maggin ta, shi dai burin sa ta ci wani abu koda danye ne in dai zai shiga hanjin ta.

Kan minti goma indomie ta dahu ya juye a plate ya kuma kasha rishon ya kawo mata.

“Ki karba ki ci, in kin ki ki zan yi miki dura wallahi” ya aje plate din a gabanta yana kuma nade hanun riga.

Ba shiri ta karba ta soma ci kamar mai cin dussa, loma uku tayi ta ture don daci yake mata a baki, Saheeb ya ce “Hasna ko sai na baki a baki ne?” Ta daga ‘light-blue eyes’ din ta ta kalle shi, sai aka yi sa’a shima ya dago yana kallon ta. Murmushi ya sakar mata, murmushin da ya kusa narka zuciya da ruhin HASNA’U, ya haifar da wani ‘chemistry’  mai karfi a tsakanin su, ya kuma debo abinci akan spoon ya nufi bakin ta da shi.

Sai ta kasa wofantar da wannan kulawar a karo na biyu ta bude dan jan bakin ta ya saka mata abincin. A haka sai ga Hasna ta tashi da plate din indomie tsaf batare da ta san lokacin da ta tashi da shi ba.

Ya zuba mata ruwa ta sha. Sai taji gardin ruwan hannun Saheeb ya fi na kowanne ruwa da ta taba sha a rayuwar ta.

Yasa hannu a aljihun sa ya dauko galasses guda biyu a cikin akwatin su ya ce, “ga su na karbo, will you do me a favour ta wear it for you?” (Zaki yi min alfarma in saka miki?) Ya fada yana ciro kyakkyawan glass din daga gidan sa. Yace “in rana tayi zai yi duhu, in dare yayi ya yi haske, ki kula da su sosai su zama ‘companions’ din ki, barci kadai zai raba ku, sai ko wanka. Kin dai ji abinda Dr. Turaki yace in kika kula da sanya su kina girma ganin ki na kara gyaruwa”.

Ya sa mata glass din, kada kiso ki ga yadda yayi  wa karamar fuskar Hasna kyau, kuma da yake rana ce yayi duhu sosai sai ya boye kalar kwayar idanun ta, ta zama kamar baturiya, banda gashin girar da yake fari.

STORY CONTINUES BELOW

“Lallai kin iya zabin gilashi, inye!” Inji Saheeb, a kokarin sa na son kawo murmushi fuskar ta.

Bai yi nasarar hakan ba amma ta mike kafar ta daga tankwashetan data yi. Kafar sumul da ita fara sal kamar ta jarirai, babu kaushi ko kadan.

Yace “Hasna’u yanzu har in tafi bazan ji muryar ki ba? Kina so in kasa nutsuwa gobe ma in kamo hanya in dawo?”

A yadda ya marairace mata sai ya bata tausayi, bata taba ganin mutum irin sa ba, saukin kansa ya yi yawa, abinda bata sani ba ita kadai yake wa saukin kan, kuma in yana gaban ta ji yake bashi da komai, ba shi da kowa sai ita.

A hankali ya ji siririyar muryar Hasna’u na fadin;

“Na gode Uncle Saheeb, Na gode for all the assistance, care, and concern showed to me. My world has never meet a person like you. You are an ANGEL. I must say thank you!

Amma don Allah don Annabi na roke ka daga yau kada ka sake dawowa in dai waje na zaka zo. Ina nufin alaqar mu ta kare daga yau”.

Ta fada tana mai sunkuyar da kan ta kasa, wasu hawayen masu zafi na kwararowa.

Saheeb ya bude baki yana kallon ta with astonishment, sannan ya girgiza kai ya ce “ko zan iya sanin hujjar ki?”

“Hujjata itace our relationship has no meaning, has no direction, has no focus….” Da sauri ya katse ta da cewa “a wurin ki ba? Amma a wuri na yana da shi, haka a wurin Ubangiji yana da shi. Annabi SAW ya hore mu da mu kalli matar da zamu aura kafin a daura mana aure.

Ni Saheeb kuma neman aure nake yi, kamar yadda kowa ke yi, yau din nan ba sai gobe ba zan gayawa Mamana a zo nema min auren ki”.

Hasna’u ta dube shi da idanun tausayi, cikin ran ta tana fadin tausayi na ya sa Uncle Saheeb ya zare! Ko in ce yana gab da zarewa! Kamar ya san me take fadi a ranta yace “ki yi min kallon zararre da kyau, dama gobe zan je Zaria wajen aminin mahaifi na, in gaya masa ya zo shi wajen Kawu ya kawo sadaqi na. ana kamala SSCE a shafa mana fatiha”.

Da fadin haka ya mike tsaye, hannayen sa cikin aljihu. Hasna’u ta bi shi da kallo da ‘light blue eyes’ din ta tana tausaya masa cikin ran ta, something is really-really fishy in his brain don mutum mai hankali bazai ce zai auri zabiya ba!

Zabiya ai sai zabiya dan uwanta ba wannan sardidin lafiyayyen matashin ba, wanda ko a masu lafiya shi ajin farko ne. Tana tausaya masa don ta san ya dauko hanyar da su duka bazata bulle da su ba, ya dauko rigimar da ba zai iya ba, ya dauko fadan da yafi karfin sa….. tsakanin sa da Kawu, da tsakanin sa da Mama. Watakila har da sauran al’ummar dake zagaye da shi. Ciki har da kanwar sa ciki daya.

Har ya fita bai bar sakar mata murmushi ba, murmushin da bazai taba gushewa daga zuciyar ta ba, murmushin da ta tabbatar shine na karshe da zata gani daga kyakkyawar fuskar sa don ta san tabbas in har ya fadi abinda yake niyya ga Maman nasa, to kuwa zata taka masa katoton birki ne, watakila har daga yin aiki a ‘Unity Kachako’.

Fitar Saheeb ba jimawa Kawu ya shigo, daka gan shi ka ga wanda ke cikin rudani, yace “Hansai, saura wata nawa ki gama makaranta?” A hankali ta ce “uku” “daga ukun an gama ko?”  “Eh an gama Kawu sai kuma shiga Jami’a” yace “akwai jami’a a Kachako ne? Ko ke ce zaki bude University of Kachako?” Tace “a’ah babu, dama mun yi da Inna Kano zani in yi” ya kama baki cikin mamaki “kije Kano fa kika ce, da wane muharramin?”

Hasna’u tayi shiru, ya e “to Hansai ni ba zan takura miki ba, amma dole in miki aure yanzu, auren da hankali na zai kwanta da shi.

Don haka tun kafin Sahabi ya furta neman auren ki gara in miki aure, don bazai iya neman wata alfarma  a gareni in hana shi ba, har ga Allah ina son yaron nan, kuma ina miki sha’awar aure sa, domin kika aure shi kin gama samun soyayyar miji.

Amma ki sani, muddin kika aure shi to fa shi kadai kika aura jinin sa da dangin sa har abada baza su so ki ba.

Sannan bazaki taba yin daraja a idanun su ba, ba zasu taba son abinda kika Haifa ba, musamman in ya zo a ZABIYA, ban kuma isa in tsawatar ba in wani cikin su zai taba mutuncin ki.

A bisa hakan, da wasu dalilai da dama, na yanke shawarar aurar dake ga dan uwan ki HASSAN gobe-goben nan ba sai jibi ba, kafin Sahbi ya sake dawowa da kokon alfarmar da bazan iya maida masa alkhairin sa ba, kin ga hakan ya fi dan dama-dama tunda yana dan zuwa makaranta yanzu, kuma yana dan jin Magana ta ba kamar da ba.

Idan kika auri Hassan dukkan ku kuna karkashin iko na komai zai zo da sauki, sanna ‘ya’yan ki suna tare da jinin su iya wuya iya zabiya ana tare.

 

Amma me kika gani? Don ko shi Hassan din ban gaya masa ba sai na fara neman amincewar ki tukunna. Ba zan yi miki auren dole ba, ‘yan zuqe-zuqen nan da yake yi duk dainawa zai yi da zarar nauyin aure ya hau kan sa”.

Hasna’u ko motsi ta kasa. Mutuwa mai tonon asiri!” Anya Kawu da gaske yake kaunar ta yake yi ko son kan sa? Da sanin sa zai aurawa dan wiwi ita? (MARIJUANA)? Kawai don Allah ya yo ta ZABIYA ana neman yadda za’ayi da ita? Ba gara-gara Hussaini ba shi da baya shan komai kuma yana zuwa makaranta?

Amma ai ya fi ta sanin akwai Hussainin ya zubar mata lalataccen don su taru su rufawa juna asiri.

Ta yarda da duk abinda ya fada akan Saheeb gaskiya ne, ta yarda bazata iya zuwa jami’a ba tunda babu Inna, wannan burin ya zagwanye! Ta san da Inna na raye koda jan gindi sai ta kai ta Kano jami’a ba tareda ta ji koda darr ba kuma ba tare da ta nemi taimakon kowa ba sai aikin karfi da lafiyar ta.

Wasu hawaye suka gangaro daga idanun Hasna’u. Hawayen da ta tabbatar har abada bazata daina zubar da suba har zuwa karshen rayuwar ta, idan ba har Inna ce ta dawo duniya ba.

A wannan gabar da Kawu ke son jin ra’ayin ta na eh ko a’ah zata auri lalataccen dan sa Hassan bata da zabi, bata da wani hope, bata da wani sauran buri a rayuwa bayan na fatan cikawa da imani.

Dama karatun karatun shine kadai burin ta, Kawu ya ce bazai taba yiwuwa ba tunda ba’a Kachako bane. Bai san cewa Annabi SAW y ace ku nemi ilmi ko da a birnin Sin ba, kuma bai iyakance mace ko namiji a wajen neman ilmi ba.

Ta dubi Kawu, da rinannun idanun ta, wadanda ke cike taf da hawaye, yayi zuruuu! Yana jiran hukuncin ta…… Kawun ta mai fada da kowa har da ‘ya’yan cikin sa a kan ta, Kawun ta da baya bari a nuna mata yatsa bai karya shi ba, Kawun ta daya da ya rage mata a duniya don an ce Kakar ta ta Kabo ma ta rasu da jimawa, shi da bai kyamaci hada jinni da ita ba bai kira haihuwar ta mummunar haihuwa ba, so yake ma ta haifo Zabiyun shi ta kawo masa.

Kawunta shakikin Innarta guda daya a duniya ya kyautu tace masa bazata iya auren dan sa ba don yana shan wiwi? Ai ana barin halas ko don kunya. Masu iya Magana suka ce “Naka sai naka…. sannan in ta saki Kawu da iyalin sa wa za ta kama???

Abu daya ta iya tambayar Kawu a wannan lokacin da yake zake da jin amsar bakin ta. “Kawu karatu na fa na Unity saura wata uku in gama shi?” Yace in don wannan ne da auren ki ki je ki karasa ki dawo ki tare a dakin ki. Hassan bazai hana ki ba, in ya hana zan saka kafar wando guda da shi”.

Bayan wannan bata kara tambayar shi komai ba. Sai da yace.

“Kin amince ko Hansai? Ki duba hujjoji na da idon basira, bana nufin son kai ko yi miki dole cikin lamarin nan sai don an ce ko me zaka yi kayi shi da tsinkaye”.

Hasna’u ta ce “Kawu   duk hukuncin da ka yi a kaina, daidai ne”.

Tana gama fadin hakan ta rufe ido kamar mai barci, Kawu yayi ta sanya mata albarka.  Ya ce gobe ta tashi da wuri tayi wanka karfe goma za’a daura aure.

Yana bada baya taji cikin ta ya hautsine, da gudu ta sakko daga gadon, ta amayar da girkin SAHEEB tsaf, sannan ta samu sa’ida.

Ta kwanta a dandaryar kasa tana maida numfashi a hankali, tana rokon ubangiji da ya dauki ranta kafin wayewar garin.

Domin ta tabbata Hassan dan uwan ta ne amma bai dauke ta a mutum ba, balle akai ga zancen kauna ta aure, Kawu kadai ke son ta cikin gidan nan, daga Hassan har babar shi Hajjo da kannen sa babu mai kaunar ta.

In comparison to SAHEEB BELLO WAMAKKO wanda ke son ta da dukkan zuciya da ruhi soyayya ta fisabilillahi daga indallahi,  ‘yan Uwan shi ne kawai da Maman shi baza su so ta ba, in haka ne ‘challenges’ na auren Hassan da ‘challenges’ na auren SAHEEB duk daya ne babu banbanci, so it was da duk wani miji da zata aura.  Gara ma na SAHEEB akwai soyayya da gatan miji (wanda shi ya fi komai dadi da muhimmanci ga mace) idan babu na wadanda ke zagaye da shi. 

Duka wannan tunanin ta na yi ne kawai ba don tayi wata hobbasa ta ceton kai a kai ba. Ta tattara komai ta mikawa sarki Allah, amma zabi ko jayayya da Kawu Samaila ba nata bane, ta bar wa Allah komai yayi duk yadda ya ga dama da rayuwar ta………

SUMAYYAH ABDULKADIR.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *