YAR SHUGABA CHAPTER 11

YAR SHUGABA
 CHAPTER 11
Yaya Ahmad yace “Basma auren ki da Shureym dole za’ayi shi, tunda iyaye sun riga sunyi magana, kuma da an d’aura shikenan zai daina wannan iskancin nashi” hawaye ne ya sauka a kuncinta tace “Yaya Ahmad bana fatan auren Yaya Shureym ni ina da wanda nake so, kuma in ba a bani shiba wlh Yaya zaku rasani, domin zan mutu” a razane ya kalleta yace 
“Basma kina da hankali kuwa? waye kike So haka? waye shi kuma d’an gidan waye?” Cikin kuka tace “ni Yaya Aryan nake so, kuma in ban aureshi ba zan iya mutuwa” a razane Yaya Ahmad ya mik’e tsaye yace cikin kad’uwa, “a’a Basma, a’a Basma, karki ce za kiyi sanadin rabuwar family d’inmu, kinsan yanda Shureym yake a wajenmu, yaron Yayan Ammi ne, karki ce za kiyiwa Ammi haka, plss ki d’auka mafarki kike da sanin Aryan, ki gaggauta cire Aryan a ranki” a razane ta d’ago ta mik’e tsaye tace 
“Yaya Ahmad bazan iya ba, wlh Yaya Aryan nake so” da gudu ta flta daga d‘akin tana kuka, lanbun gidan ta nufa taje ta zauna, kuka take kamar ranta zai fita ba ‘tare da sauti sosai ba, Yaya Ahmad cikin sauri ya isketa a gun, dan yasan tabbas ba zata koma part d’in Ammi ba a haka, zama yayi gefenta ya kama hannunta shima a zuciyarsa yana gasgata lallai Basma da Aryan ta dace, domin Mutumin kirki ne ga Addini da sanin yakamata, a d’an zaman da yayi dashi baiga wani aibu a gunsa ba, sai dai matsala d’aya ne, su Ammi ba zasu yarda Basma ta kawo wani Mijin ba, sai Shureym, sannan kuma Aryan ba d’an kowa bane shi, baya tunanin su Ammi zasu yarda ta auri talaka. Yace 
“Basma nima ina son ki auri Aryan, amma kin san hakan bazai yuwuba a wurin su Ammi” cikin kuka tace “Yaya zai wuyu tunda ina sonsa, kai zaka taimaka na aureshi kamar yanda zan taimaka maka ka auri Deeja” nisawa yayi yace “karki damu zanyi wani Abu a kai, ki bani lokaci” sassauta kukan tayi ta share hawayenta tace “Nagode Yaya Ahmad, Allah ya mana jagora” Ameen” yace, kana ya rakata part d’in Ammi ya koma d’akinsu cike da tunani barkatai, da damuwa fal zuciyansa. Lallai yana tausayin Basma kuma yana sonta flye da kansa. dole yayi k’ok’arin sama mata mafita, da wannan tunanin har barci ya kwashe shi. 
‘Bayan kwana biyu“ Basma sun cigaba da soyayyansu, wanda a yanzu basa b’oyeta ko a gaban waye, Umma ta kad’u sosai data fahimci haka, kiran Yaya Aryan tayi, ta masa fad’a akan yabi a hankali Basma ba tsaran aurensa bane, dole ya iya takunsa, hankalin Aryan ya tashi yace “Umma wlh ina son Basma ki mana addua, domin Addu’anki yana da matuk‘ar tasiri a garemu” Umma tayi ajiyar zuciya, ta sanya musu Albarka, can kasan zuciyarta tana tausayawa yaranta, domin tasan iyayansu Basma ba zasu yarda da auren su Deeja ba, saboda su d’in ba kowa bane, talaka ne futuk. Haka Yaya Shureym ya k’araci zama a gidansu Basma bai samu fuska a gunta ba, ko ya kirata bata d’agawa, haka ya tattara ya koma Kano. 
‘To bari na waiwayi wajensu Leema da Meena.‘ Leema tana kano a takure take, domin bata samun sakewa sosai kullun tana gida, in zata fita saida kuyangi da dogarai, hakan yasa taji duk zaman Kano ya gundureta, ta fara tunanin komawa Abuja, in sha’awarta ta motsa kamar za tayi hauka, wataran a sace take fita tayi b’adda kama taje su had’u da Jalal, su gama shek’e ayarsu ta dawo gida a gaugauce. A daddafe ta iya kaiwa har wata hud’u a Kano, yanzu ta gama shirya kayanta da yawa domin komawa Abuja, in kuma ta koma bata tunanin dawowa, sai dai ta rik’a zuwa tana gaishe da iyayenta. 
Haka ma b’angaren Meena, Alhaji Ibrahim mahaifinta mutum ne mai sanya ido sosai kan yaransa, hakan ne yasa Meena bata fita saida dalili sannan, Yaya Jamal ya sanya mata ido shima domin yaga take-takenta akwai rawar kai, Meena in son shan syrup ya motsa mata, rufe kanta take yi a d’aki taita kuka tana buk’atar abinda zata sha, dakyar barci ke d’aukanta, in ta farka shikenan ta dawo dai-dai, hakan yasa ta samu wani shed’ani d’an unguwarsu, suka tsadance yana siyo mata syrup a sace ya kawo mata, sai ta bashi kud’i mai yawa, haka zatai ta maneji dashi harya k’are, gaba d’aya zaman Kaduna ya gundureta, saita soma had’a kaya dan komawa Abuja gaba d’aya, itama sam ba zata zauna a Kaduna ba, waya sukayi da Leema, suka gayawa juna matsalansu, nan take suka yanke shawaran barin gidan iyayensu a gobe in Allah ya kaimu, domin ci gaba da rayuwan freedom da suka fara a England. ‘ 
Washe gari” 
Da safe Meena tayi sallama da iyayenta, dama ta riga ta sanar musu zata koma Abuja,jirgin k’asa tabi, daga gidan president aka aiko mota ya d’auke ta. Leema ma haka ta sauka a airport, mota daga gidan President yazo ya d’auketa. 
Dukansu suna zaune a falon Ammi suna shan farfesu, Ammi ne ta flto tace 
“Leema wai ku baza ku zauna guri d’aya bane, baku nan baku can, ni dai naga alama aure kuke so, bari anjima zan samu president in sanar masa, sai a sanya rana mu fara shiri kowa ya huta” bata rufe baki ba Leema tace “taf wlh Ammi aure ba yanzu ba, munyi k’anana” Meena tace 
“gaskiya kuwa aure sai mun kai 30yrs” Basma dai murmushi tayi kawai domin ita a yanzu auren take so amma fa da Aryan d’inta, Momy ce tace 
“lallai yaran nan da sauranku, wlh baku isa mu zuba muku ido ba har kukai lokacin da kuke so, aure kam kuma fara shiri” tana gama fad’a ta mik’e ta wuce d’aki, turo baki su Meena sukayi, su a dole basa so, Basma ce ta kallesu tace “dama dai kun bar wannan shirman, domin dai aure shine riban ko wace mace” tana gama 
fad’a ta mik’e ta wuce d’aki tana murmushi, kallon mamaki suka bita dashi, daga bisa ni suka tafa hannu Leema tace 
“nifa Basma ta sauya, ko ke baki ga a lama ba? Sam ba ji da kai, ba shan k’amshi, duk wani mulki ta aje, anya babu wani abu a k’asa kuwa?” Meena tace “ita ta sani dai, dan ni ba zanyi aure yanzu ba” haka suka mik‘e tare, d‘akin Basma suka Shiga sun sameta bisa gado tana chart, ba wanda ya kulata suka haye gadon suka fara hiran yanda suka yi missing zuwa club, yau sunyi masa shiri na musamman, Basma na 
jinsu bata ce musu k’ala ba. Bayan sallan la’asar suka shirya sai gidan hutun Basma, Basma bata bisu ba, sun wuce tare da escot, ita kuma ta wuce wurin masoyinta, suka had’u a inda suka saba had’uwa, suka wuce wurin hutawa domin su samu yin hira mai dad’i. Sai misalin k’arfe shiga na yamma suka yi sallama da Yaya Aryan ta wuce gidan hutun da sauri, domin tana son yin wanka a swimming pool, dan ta kwana biyu bata yi ba. ‘ Tana isa ta samu su Meena a wajen, haka itama ta shiga ta soma wankanta, Leema ce tace “Besty wai yane naga duk kin sauya ne, ko akwai abinda ke damunki ne?” murumushi tayi a ranta tace “soyayyan Aryan ne ya sauya ni” a zahiri kuma tace 
“Me kika gani besty, ina nan a Queen Basma kamar yanda kuka sanni” Meena ce tayi caraf tace “ba wani nan, da akwai abinda ke going wanda bakya so ki gaya mana, sam ban gane sauya wanki akan zancen aure ba, ko kuma soyayyar Yaya Shureym ke fizgarki” nan take Basma ta b‘ata rai, bata ce komai ba, ta cigaba da wankanta, Leema da Meena suka had’a ido sai suka kwashe da dariya, hiransu suke bata tanka musu ba, harta gama ta bar su ta nufi d’akinta. Magrib ya gabato ba halin yin rawa, shiyasa ta wuce d’aki dan gabatar da Sallah akan lokaci. 
Bayan k’arfe takwas na dare kamar yanda suka saba fita, yau ma cikin shirin doguwar riga masu fidda tsiraici su Leema suka sanya, Basma harta d’auko wata yalolon riga wanda duk rabin cinyarta a waje yake, sai zuciyarta ya karaya saboda tunawa da tayi da Yaya Aryan, dole yasa ta maida ta d’auko wata doguwar riga mara tsagu, kuma mai kauri ta sanya, duk da haka tana jin wani iri, zuciyarta na gaya mata kamar taci amanar Yaya Aryan, haka dai ta shirya, ta taje sumanta ta sakeshi a bayanta, ta d’aura hular Queen, sai ta flto a Queen Basma tamkaryanda take a da, tayi kyau sosai, haka sukaita d’aukar photo kafln nan suka wuce. 
Kamaryanda suka saba, Leema dama Jalal yana Abuja, cikin k’ank’anin lokaci ya bayyana, yazo suka tafi cikin hotel, Leema kuwa cikin group d’in su na mashaya ta nufa, nan suka soma ihu da kalamai masu dad’i, da irin missing d’inta da suka yi, Basma dai yau a d’arare take ta kasa sakin jikinta, duk hankalinta yaki kwanciya gani take kamar Yaya Aryan zai bayyana a gurin, dakewa tayi ta mik’e ta nufi saman step da abokan rawarta, suka fara cashewa cikin salo mai ban sha’awa. 
A can gida kuma, Momy ta shiga part d’in Ammi domin ta kira su Meena, zata sanya su aiki a system d’inta, koda ta shiga wayam, da yake Ammi yau ita ke da girki tana part d’in president, mamaki ne ya cikata, sam bata san sun flta ba, kiran wayansu tayi amma duk a 
kashe, girgiza kai tayi tace a flli 
“wato Basma bata tashi rashin da’a sai su Meena sunzo, yau kenan a gidan Hutu zasu kwana, anya yaran nan suka aikata Alkhairi kuwa? amma zan d’auki mataki” sai taja tsaki ta fice rai b’ace. 
Sai misalin k’arfe sha d’aya na dare Basma ta dawo hayyacinta, tunda ta soma rawa saita manta da duniyar da take ciki, Aryan ya fad’o mata a rai a zabure ta flta daga hall d’in ta shiga mota ta rufe, wayarta ta ciro ta kunna, sak’oninsa ne suka fara shigowa har kusan biyar, kan ta kaiga bud’ewa kiransa ya shigo, a tsorace ta d’auka tamkar mara gaskiya tace “My Aryan lol, afwan wayana ta rnutu ba chrgy ne” murmushi yayi tare da ajiyar zuciya yace “Alhamdulillah tunda lafiya kike, amma Basma baki tab’a min k’arya ba sai yau” damm gaban Basma ya buga, a tsorace tace “k‘aryan me nayi baby lol?” yace “saboda tunda nake dake wayoyinki basu tab’a mutuwa babu chrgy ba sai yau, domin wayoyinki uku ne kuma layi daban-daban” jikinta ne ya d’auki rawa cikin rawar murya tace “am am dama” tsawa ya daka mata “yimin shuru karki b‘atamin rai, ina kika je?” nan take fitsari ya kamata tace “naje gidan Hutuna ne ni da su Meena” murmushi yayi yace 
“good, to kinga abinda ya sa kika kashe waya, saboda yau su Meena sunzo har kin fara mantawa dani, haba Basma kinsan kuwa halin da kika sani danaji wayarki a kashe” marairaice murya tayi ta shiga bashi hak’uri, ajiyar zuciya yayi yace 
“Basma babu komai banyi fushi ba, sai dai zan rubuta wannan ranar a cikin tarihin rayuwana, ranarda Basma ta fara min k’arya, amma ki kiyaye, kuma ki tabbatar kin ware min lokacina, domin na lura sai na dage miki akan su Meena, dan naga zasu rage soyayyar mu” murmushi tayi ta kuma bashi hak’uri da kalamai masu dad’i har ya sakko, sukayi hira mai dad’i, hakan ya d’auke su har kusan k’arfe d’aya, kana suka yiwajuna sallama. Sai misalin k’arfe uku na dare suka koma gida, ko wacce d’akinta ta nufa ba ko tub’e kaya duk suka fad’a gado sai barci. Yau kusan kwana biyar kenan su Basma basa kwana a gida, kullun sai sunje club, Basma tana k’ok’arin ki yayewa Yaya Aryan, domin time d’in wayansu na dare nayi take fita a hall din taje susha hira a waya. Ta b’angaren Momy kuwa abin yana matuk’ar damunta, in suka fita da yamma sai da safe suke dawowa gida, sam bata nuna musu ta sani ba, kuma bata gayawa kowa ba, yau tayi shirin bin diddiginsu, Yaya Ahmad ta kira yazo sameta a d’aki, suka gaisa, bayani ta shiga yi masa akan su Basma, mamaki k’arara ya bayyana a idonsa, domin bai tab’a tunanin hakan zai faru ba, duk yawan security dake gidan, Momy ta gama gaya masa tsaf, tace 
“ina so yau kaje gidan hutun Basma, ka gano min meke faruwa” ajiyar zuciya yayi yace “insha Allah Momy zanje, domin ni abin nasu ma mamaki ya bani, a ce wai harda Basma, duk yanda akayi su Meena ne suka sauya ta” murmushin takaici Momy tayi tace “ba ruwansu duk halinsu d’aya, ko da can ma haka suke yi” 
“To Allah ya shiryesu, bari mu gani zuwa dare in basu dawo ba, sai na d’auki Naufal muje tare dashi”. 
Hmm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *