YAR SHUGABA CHAPTER 8

YAR SHIGABA
CHAPTER 8
‘Bayan mako guda‘ 
Yaya Aryan yanata zuba ido yaga zuwan Basma amma shuru, wani lokacin har tashi yake a kasuwa da wuri domin yazo ko zasu had’u, cikin dabara yake tambayan su Umma akan Basma tazo? sai suce bata zoba, wasa-wasa har aka shafe sati d’aya, sai rashin zuwan nata ya fara sa shi damuwa, Addu’a yake Allah yasa laflya. Ta b’angaren Basma kuwa kalau take, domin a cikin satin Yaya Shureym yazo, sun sha soyayya shiyasa bata samun lokaci sosai  na zuwa gidansu Deeja, domin kullun yamma suna flta da Yaya Shureym dasu Na‘im, sai Magrib suke dawowa. Hakan yasa bata samu damar zuwa ba, amma fa tana tunaninsu da kewar Umma sosai, ta 
d’auki aniyar siyan musu waya, in bata samu zuwa ba ta rik’a kirasu. Yau ya kama ranar Juma’a, bayan Sallan La’asar Basma da Yaya Ahmad suka shirya zuwa gidansu Deeja, Basma tayi shigan lafaya mai kalan fari da green, Yaya Ahmad kuma ya sanya sky blue na shadda hula bak’i dara da takalmi bak’i, sunyi kyau sosai. suka kama hanya suka tafi a mota ba tare da escot ba, hira suke cikin nishad’i tare da kwanciyar hankali, a haka suka isa gidan. 
Bayan sun isa Basma, ta fito tace “Yaya bari na gaya musu tukunna saika shigo” ya kalle ta da murmushi yace “ba damuwa inajira”. Cikin natsuwa ta Shiga gidan, duk kan su suka amsa, cike da fara’a Umma ta tarbeta, Deeja kuwa tasowa tayi ta amshi jakan hannunta tana mata sannu, Yaya Aryan kuwa basar da ita yayi tamkar bai ganeta ba, Amma fa a zuciyarsa yana yaba kyawun da tayi, dauriya kawai yayi ya matse, zama tayi a kan tabarma sai da suka gaisa da Umma kana suka gaisa da Deeja, ta kai kallonta wajen Yaya Aryan tace “ina yini Yaya Aryan?” farin cikin ne ya mamaye zuciyansa jin yanda ta kira sunansa yayi masa matuk‘ar dad’i, amma kuma saiya amsa fuska ba yabo ba fallasa a dak’ile, daga nan bata k’ara cewa komai ba domin jikinta yayi sanyi yanda taga ya amsa mata, sai duk tajita a takure, Waigawa tayi wurin Umma tace da Yaya Ahmad muke yana waje, nace bari na sanar muku kafin ya shigo” Umma ta fad’ad’a fara’an fuskanta tace “Allah Sarki kice dashi ya shigo tunda duk gida ne, Kai Aryan tashi ka shigo dashi” da sauri ya mik’e ya flta, cikin minti uku saiga su sun shigo, ya zauna a tabarman da Yaya Aryan ke zaune shima ya zauna gefensa, cikin natsuwa ya gaida Umma, ta amsa cike da farin ciki, Deeja ne ta fito daga d’aki sanye da gyale ta kawo masa ruwan pure water a cikin plet ta aje a gabansa, sannan ta gaishe shi, cikin kulawa ya amsa, Basma na satan kallonshi, taga sai wani kallon Deeja yake kamar zai had’iyeta, ita ko Deeja batasan yana yiba, nan ya shiga 
yiwa su Umma bayanin zuwansa, yace 
“Umma kan zancen makarantar Deeja ce, insha Allah ranar Monday zasuje tare da Basma tayi mata registration, saboda yanzu ana farkon fara d’aukan sabbin dalibai, sannan kuma na d’auki Aryan zai yi aiki a company Abbanmu, In ba damuwa” Aryan cikin natsuwa yace “Ayi haka kuwa? wannan dawai niya ai zata yi yawa, ga Deeja ga kuma ni” murmushi Yaya 
Ahmad yayi yace “d’an uwa karka damu dukyiwa kaine” Aryan yace 
mun gode Allah ya saka da Alkhairi” Umma ma godiya tayi harda yar kwallanta, Deeja ko murna ne kan murna, itama godiya tayi. 
Nan fa hira ya b’arke sunata zan tawa, Amma fa banda Basma data takure, saboda irin nuna ko in kula da Yaya Aryan yayi mata, bayan minti talatin da zuwansu, Yaya Ahmad yace zai je wani wuri inya dawo zaizo ya d’auki Basma, nan yayi musu sallama Yaya Aryan ya rakashi waje, Basma ne ta juyo wurin Deeja tace “saiki shirya ranar Monday da wuri zanzo domin mu tafi makarantan, ina so mu gama registration a ranar ne” cikin farin ciki tace 
“insha Allah tun Asuba zan tashi na shirya da wuri” Umma tace “da dai ya fi miki da wannan shegen barcin asaran da kike yi, to yanzu ga makaranta nan saiki cigaba da barcin mu gani” duk suka sanya dariya,Yaya Aryan ne ya shigo yace “Umma wai ina furan ne? wallahi yunwa nakeji” da sauri tace “af kaga na manta, da an dama Ahmad yasha kan ya tafl, ke Deeja d’auko min kwanan furan nan da kuma kindirmo had’e da sugar” taje ta d’auko, nan Umma ta dama fura da 
Nono da yawa, ta fara zubawa Basma a cup ta aje a gabanta, sannan sauran ta zuba musu. Deeja ta mik’awa Yaya Aryan nashi yace “mik’o min sugar na k’ara” ta mik’a masa ya k’ara, ya juya da kyau ya fara sha, duk suka fara sha banda Basma, Umma tace “ya dai Basma yau na ganki wani iri ko lafiya?” dariya tayi tace “Umma laflya lau zan sha” Yaya Aryan ya mik’e ya shiga d’aki d’auko wani abu ya bar furan a wurin, yana shiga Basma tayi sauri ta d’auko furansa ta fara sha, Umma da Deeja suka sanya dariya ba tare da sunce komai ba, sun zuba ido suga drama ya Aryan zaiyi, yana fitowa yaga wurin wayam ba cup d’in furansa; D’ago kan da zai yi, ya hango Basma tana sha hankalinta kwance, murmushi kawai yayi ya matsa kusa da ita yace, “bani furana ai ba naki bane wannan” k0 d’agowa bata yi ba, ta cigaba da sha, Khadija ce ta kwashe da dariya tace 
“kai Yaya tunda ta d’auka naka sai kayi hak’uri ka d’auki nata kasha” d’aura fuska yayi ya harareta, sai ta gimtse dariyan da takeyi, Umma dai uffan ba tace ba, k‘arshe ma tashi tayi ta shiga kicin dan ta duba tukunyarta, aiko tana shiga kicin ya saka hannu ya wafce kofIn 
furansa, sai Basma ta sa kuka harda shagwab’a, ga hawaye na malala, mamaki ma ta bashi, Amma saiya dake ya koma ya zauna, murza gyad’a mai gishiri yayi, ya zuba a furan ya cigaba da sha, Umma ce ta fitO taga abin mamaki, d’aure fuska tayi tace Tace”Aryan ba dai amsa kayi ba?” da murmushi fuskansa yace “Umma ai ba nata bane nawa ne fa, shiyasa na amsa” d’aure fuska ta kuma yi tace “banson shirme ita ma ba k’anwarka bace, shine baka barmata ba” aiko Basma ta samu goyon baya, sai ta kuma narkewa cike da shagwab’a tace Umma ni nashi zan sha ki ce masa ya bani” Umma taso tayi dariya Amma sai ta dake tace “Aryan bata naka kayi hak’uri kasha nata” shima cikin yana yi na shagwab’a yace “Umma nawa nake so na sha” Umma ganin zasu sa mata hauka sai ta shige d’aki ta basu guri, domin tasan da gan-gan Aryan yayi haka, zuciyarta ne ya fara mata zargin wani abu. Deeja ta dinga dariya a b‘oye, haka Yaya Aryan ya shanye furan, harda lashe kofin, Basma na gefe sai kumbure-kumbure take yi. 
‘Nace ohhh su Basma ko ina akaje sai an raba hali lol.”Deeja ta mik’e ta shige bayi, Yaya Aryan ya mik’e ya matsa kusa da ita ya d’auki furanta yace a hankali yanda Umma ba zataji ba, “Ga naki kisha kar kuda ya shanye miki, domin nima ban koshi ba, in baza ki shaba sai na shanye” hawaye cike a narkakkun idonta ta d’ago, sai suka had’a ido, ai gaba d’aya saita saukar masa da kasala, sun d’auki tsawon minti biyar suna kallon juna, ita tana masa kallon tuhuma “meyasa baka yafemin ba” shi kuma yana mata kallon “da sauranki ban hak’ura ba” Shine ya katse kallon ya limshe idonsa, kana ya bud’e ya sakar mata wani shu’umin murmushi, da sauri ta sunkuyar da kai domin tabbas duk gangar jikinta ya amsa, bai kuma cewa komai ba, ya aje cup d’in a gabanta, ya sanya takalmi yace da k‘arfl “Umma na flta saina dawo” a cikin d’aki ta amsa masa “adawo laflya”. 
Yana fita Basma itama ta sanya takami ta bi bayan sa. Shi dai yaji ajikinsa Basma zata biyo shi, sai ya d’aure fuska ya cigaba da taflya, sai da ya d’anyi nisa da gida kana ya juyo fuska d’aure, yace “lafiya kike bina?” Cike da damuwa tace “ba kaga sak’ona bane” yayi guntun murmushi yace 
“inna gani me zan miki” marai raice fuska tayi tamkar zatayi kuka tace “Yaya Aryan na baka hak’uri Amma kayi burus, kamar ma na k’ara zuga ka ne” ya kuma d’aure fuska yace “da yake kin raina min hankali da, zaki wani rubuta min a takarda, to ki sani bai min ba, kaya kuma suna nan na aje, duk lokacin da kika ga dama zaki zo ki d’auka” Cikin rashin jin dad’in abin da ya ce mata tace cikin tsiwa, “dan ma na baka hak’uri, wlh banda kaci darajan su Umma ba abinda zaisa na baka hak’uri, tunda wancen bada hak’urin bai maka ba, yanzu nace Yaya Aryan kayi hak‘uri komai ya wuce” dariya ya kwashe dashi yace a ransa “wannan Yarinya ba tad’a kunya zanyi maganinta” yace “a haka zaki bani hak‘uri kina min masifa? malama banda lokacin ki yanzu, sai anjima” ya 
juya zai tafi da sauri ta sha gabansa tace cikin marai raice fuska “Yaya Aryan kaine kake hasalani, to naji zan baka hak’uri,Yaya Aryan kayi hak’uri bazan sake ba” sai tayi shuru, murmushi yayi yace “to naji na hak’ura Amma, ki wuce gida sai anjima” baijira me zata ce ba ya wuce da sauri, ita kuma murmushi tayi, tace a fili “Aiko zanyi maganinka”. Bayan sallan Magrib Yaya Ahmad ya dawo, kai tsaye ya shigo gidan, ya same su duka a tsakar gidan, ya kuma gaishe da Umma, ya kalli Basma yace “kin shirya mu wuce k0?” tace na shirya” Umma tace ka tsaya kaci tuwo mana, itama yanzu ta gama ci” da sauri ya dubi Basma yace 
“da gaske kinci?” dariya tayi tace “eh mana na ci” yace “tafdi, aiko yau za ayi ruwa da k’ank’ara, keda bakya kaunar tuwo” dariya duk suka yi tace “eh yau dai naci na Umma na mai dadi yaya Ahmad ya mik’e yace 
“Umma wallahi a k’oshe nake, sai dai wani lokacin inna zo” Umma tace “Ba komai Allah ya kaimu” Basma ma mik’ewa tayi ta d’auki jakanta, suka yi wa Umma saida safe, Deeja tayi musu rakiya har mota. 
Basma ta ciro waya Android mai kyau ta bawa Deeja tace ki rik‘e a hannun ki, zan dinga kiranku da shi, inajin laflyanku” ta amsa tayi godiya sosai. Yaya Ahmad ne ya kalli Deeja yace “Hajiya ba magana ne” murmushi tayi tace “akwai, ai d’azu mun gaisa” yace “hakane Amma ai gaisuwa bata yawa” “eh hakane, to ina wuni Yaya Ahmad” yace “bazan amsa ba tunda saida na rok’a d’ago kai tayi suka had’a ido sai ya kanne mata ido d’aya, da sauri ta sunkuyar da kai k‘asa tana murmushi tace “ayi hak’uri Yaya Ahmad bazan sake ba” dariya yayi yace “karki damu, masu suna Deeja basa laifa dama, amma a wurina” murmushi kawai tayi bata ce komai ba, a yanzu dai ta fara gane ina Yaya Ahmad ya dosa, domin duk had‘uwansu saiya tsokaneta. Nan suka yi sallama ya ciro kud’i bandir d’in dubu d’ai-d’ai ya mik’a mata yace “ga wannan ki sha sweet” sai tak’i karb’a, sai da Basma ta sa baki, kana ta amsa tayi godiya, sannan su ka wuce. 
Yaya Aryan sai bayan sallan isha’i ya dawo, bai samu Basma ba, sai hakan bai masa dad’i ba, domin yana son fad’ansu dan yana masa dad’i. Bayan ya gama komai ya shiga d’aki da nufln kwanciya, sai ya ga d’akinsa a gyare, murmushi yayi domin yasan wacce ta gyasa masa, sauya kayan jikinsa yayi ya sanya na barci, ya kwanta akan katifansa, yayi d’ai-d’ai akan filo, ya d’aura kansa baifi minti goma ba yaji baburetin k’ark’ashin filO, da sauri ya mik’e cike da tsoro yana tunanin menene haka, Sam tunaninsa bai kawo masa waya bane, saboda shi baida ita, da sauri ya fmciko filon yaga ko miye, waya ce android babba mai kyau a kirar 
SAMSUNG GALAXY S9 PLUS  ya gani, mamaki ya cika shi, Yace “wannan yarinyar ko mayya ce sai haka, kullun sai ta barni da mamaki, nasan ba kowa ba ne sai Basma” Wayan ne yaga yana haske da alama kira ne ya shigo, da sauri ya matsa kusa ya d’auka ganin Basma a zanen kan wayan ne, yasa shi murmushi yace 
“mayyar k’anwata” d’agawa yayi ya kara a kunne bai ce komai ba, itama bata ce komai ba har tsayin minti uku, ganin ba zaiyi magana ba yasa tace “Yaya Aryaaan” tsigan jikinsa yaji ya tashi, irin yanda ta kira sunansa taja k’arshe, a kasale 
yayi murmushi wanda sai da taji sautinsa, itama murmushi tayi tace “dama zance maka ne kayan d‘akinka sunyi datti, zanin gadonka yana bukatar wanki da labule, kayi k‘ok’ari ka bayar a wanke maka ko kai ka wanke, domin tsafta cikon addini ne, dan d’azun dakyar nake shak’ar numfashi, saboda yanda kayan ke tashi ya kuma had’e da k’amshin turare” 
Tsananin fushi Yaya Aryan yayi, cike da b’acin rai yace “wai ke ni sa’anki ne? wallahi inda kina kusa sai na miki marin dayafi na rannan, mara kunya kawai” 
kwashewa tayi da dariya tace “haba Yayana Aryannny, daga gyara kayanka ai ba zai zama sauke mu raba ba,Allah dan ni 
ban iya wanki bane, dana wanke maka, shiyasa nace bari na gaya maka Ka wanke” Murmushin takaici yayi yace 
“ko kin wanke saina sake wankewa” murmushi kawai tayi bata ce komai ba, yace “kuma wannan wayar ta miye zaki aje min a d’aki?” tace “dan na rik’a jin muryan Yayana, shiyasa na aje a gun” a wannan lokacin gyara kwanciyansa yayi gaba d’aya Iamarin Basma ya daina bashi mamaki, tana da saurin hasala mutum, tanada saurin sakko da mutum in yayi fushi, Yarinya kamar mai Aljanu, a nushe yace 
“to Yayan naki yace bai so, kizo ki d’auki kayanki” cike da shgwab’a tace 
“uhum ni ban yarda ba, ina son jin muryan Yayana ne, ba zan amsa ba” murmushi ne ya sub’uce masa yace “shi kuma Yayan naki baya buk’atar jin muryanki, dan haka ba zai yi amfani da wayan ki ba, 
ni saida safe barci nakeji” sai ya gimtse kiran. Saiya rungume wayar a k’irjinsa, haka nan ya tsinci kanshi cikin nishad’i. 
Basma sam bata ji dad’in gimtse kiran da yayi ba, hakanan ta tsinci kanta da k’ara son jin muryansa, sake kiransa tayi, baburetin d’in wayar ce ya dawo dashi daga duniyar tunanin da ya shiga, sai ya d’aga kiran, cikin kasalan murya yace “Basmaaa, ki barni nayi barci mana” sai taji wani yarrrr, tsigan jikinta ya tashi, gaba d’aya sai taji wani irin nutsuwa ya shigeta, tace cikin irin yanayin muryan da yayi magana tace “eh bazan bari ba sai munyi hira” cikin tsokana yace “ke wai mayya ce” tace cikin tsiwa “eh mayya ce Amma a gunka kai kad’ai” dariya yayi sosai yace 
“to nama na d’aci gareshi yarinya dan yafi k’arfln ki” itama dariya tayi tace “namanka dai zak’i zaiyi kanma a ce hancinka zai d’auki romo sosai” dariya duk suka kwashe dashi a tare, kana cikin dariya yace 
“kwalelen ki Yarinya” itama cikin yana yin farin cikin tace “ba wani kwalele Yaya Aryany” nan dai sukai ta hira cikin nishad’i nishad’i da fad’a~fad’a. Sai misalin sha biyun dare suka yi sallama, sun rabu cike da kewarjuna, da rashin jin dadin rabuwansu. Aryan da kyar barci ya d’auke shi, yanata tunani bar katai a kan Basma. itama ta bangaranta da tunaninsa ta kwanta, cike da farin cikin duk suka kwana. 
Tofa anya kuwa? muje dai zuwaaa….” 
Hmmmm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *