Yar tallah 6

*YAR TALLA*

                 CHAPTER6

*Mun tsaya a*
inda  yayi mata dukan bala,I ya farfasa mata jiki sannan kuma ya tabbar da ko motsi batayi sannan ya kyaleta harya wuce ya dawo ganin alamun kamar ta suma yasa ya janyo ruwa cikin guga ya sheqa mata ta sauke nannauyen numfashi yace sannan ki tashi maza ki dora tuwon siyarwan don lokacin sahur ya gabato
*Zamu tashi a*
Rabiu ya miqe ya rarrafa wajenta gamida jawota jikinsa yana sharar hawaye baisan sanda wani irin kuka maiban tausayi ya kubce masa ba saida yai mai isarsa sannan
Ya janyeta ya tafi hura wutan tuwon don daman ya iya tuwon duk da ba sosai ba don tun yana yaronsa inna laure ke sanyashi kafin saude tayi kwari amman abinda ba aikinkaba har saude data girma daga baya taxo ta fishi iyawa
Saidai yau haka ya zage bakin kokarinsa yayi tuwon da miya laure ta murmula musu naira biyar biyar ta zuba tuwon a baho miyar a bokiti gamida basu fitila
Rabiu ya dauki kwanon tuwon akai kana ya dauki na miyan a hannu yace saude ta koma ta kwanta shi zaije ya siyar har bakin tasha yaje dukda rashin kyan hanyar ya samu wuri ya zauna inda yan garuwa direbobi da matasa ke zama
Acan yayi sahur dinsa saida akai sallar asuba sannan ya dawo saidai bai saida duka ba
Laure tahau fada tsohon munafuki ai daman don mugunta kaqi tafiya da sauden don kaje ka dawomin dashi
Inda kun tafi tare ganinta ai wanda baiyi niyyar siyabama sai ya siya tunda yana ganin mace amman shine kai ka kwasa ka tafi
Zan gani duk uban daya daure muku gindi a garinnan yau zan ganshi don sahur din da za,ai na gobe da ita zakaje
Munafikin bazan da wofi wanda yayi gadon baqin hali insha allahu qarshenku bazaiyi kyau ba
Yaddah uwarku ta bace a wulaqance kuma haka zaku bita daya bayan daya
Rabiu ya ajiye mata bahon ya wuce zuciyarsa na faman suya da tuquqi mai ciwo
Wasu irin hawaye suka dinga zarya a saman kumatunsa
Yana isa dakin tun kafin ya zauna ta zaburo ta nufo dakin ta hankade labule saika fito munafukin Allah kaxo ka jido mana ruwa ka tashi wannan yar iskan taxo ta fara aikin gida don aiba wani kuka ajeba da zaku kwanta kuyi barci shikuma yai muku aikin gidan maza ku taso
Rabiu ya goge hawayensa sannan ya tayar da ita zazzabine fal a jikinta tausayinta ya kamashi ya kamata suka fito yana nashi aikin yana nata har suka gama basu suka zaunaba saida rana ta haske gari gaba daya
Sannan suka kwanta hakanma badon tasoba saidon babu sauran ayyukan da zasuyi matanne amman da bata barsu sun kwantan ba
Sun samu barci yakai na awa biyu kafin masifaffiyar ta tashesu ta turasu markade daganan basu  sake samun zamaba har dare
Haka rayuwa taci gaba da tafiya cikin kunci da takura har azumi yakai ashirin da tara kowa nasaran gobe sallah duk inda ka gifta anata yankan kaji
Wasu natakai markaden abincin sallah inda su rabiu da saude ke tsugunne  kan dakalin dakinsu duk sun zubawa inna laure ido wacce ke zaune a bakin murhu saman kujera sai faman suyan naman shanu take
Iklima yar baba (sunan da take kiranta dashi kenan)sai faman kaiwa da komowa take tana miqa faranti ana tsamo mata
Suna tsugunne harta kammala suyar ta zuba cikin babban langa ta juye man tayi daki tabar iklima zaune waje tana yagar nama
Malam bala yai sallama niqi niqi da laidoji a hannunsa
Rabiu ya tarbeshi da sannu da zuwa ya miqa hannu zai karbi kayan dake hannun nasa ya noqe yana fadin
A,a barshi kawai gyaramin tabirma kawai na zauna a bakin dakina
Rabiu ya kwasa da hanzari ya gyara masa tabarman ya zauna
Sannan shima ya koma wurinsa kamar daxun inna laure ta fito daga daki tana fadin
A,a malam sannu da zuwa ya amsa yauwa laure sannu da gida taja ta zauna kusa dashi
Me muka samu kuma malam?
Ya watso hakorannan waje kaman an watsa wake amiya kamin yace kayankune na amso muku daga wajen tela sannan na qara biyawa ta kasuwa na qara hado muku sauran kayayyaki wasu kudine nai sa,a wallahi akaimin biyan bashinsu yanxunnan
Inna laure taja ledar tana fadin sannunka kuwa malam bari mu gani
Ta janyo ledojin tana zazzagewa
Atamface soso yar yayi aka dinka mata ita da yarta kala bibbiyu sai takalmi danko kowa guda guda sai tsakiya ta wuya data hannu kowa da nashi sai gyale kowa da nashi
Dadi ya cika laure aiko saita rangada guda aiyiriri wallahi tallahi malam ka biyamu Allah ya qara budi kaji
Shi kuwa sai ji yake kansa na qara fashewa ji yake dada akwai saura cikin aljihunsa daya qara zazzage mata saboda yaddah ta kodashi
Laure ta yafito iklima dake zaune tanacin namanta
Iklima ta kwaso da sauri cikin doki ta zauna tsakiyarsu tana daddaga kayan
Dadi ya cikata ta miqe tana gwargwadawa tana tsallen murna
Saude dake zaune ta daga kai ta kalli yayanta idonta cike da hawaye yaya ni ina nawa kayan?
Rabiu ya kalleta cike da tausayawa yace kiyi haquri kema anjima zan siyo miki naki kinji?
Kai kawai ta daga masa hawayen da suka taru idonta suka gangaro yasa hannu yana goge mata
Inna laure ta miqe ta tattara kayan ta shige dasu daki shikuma malam ya dauki buta yai bandaki
Rabiu ya dubi saude murya qasa qasa yace bari inje in siyo miki naki kinji?
Kai kawai ta daga masa ya miqe ya shiga dakin nasu ya bude bayan kyaure ya ciro kudin da yake tarawa yan hamsin hamsin din da alhaji bashir ya dinga bar musu ta cikon koko da kosai
Tun farkon azumi har zuwa yau ya fito ya fice abinsa
Kai tsaye kasuwa ya wuce ya zaga sosai ya samo mata yan kanti doguwar riga da wandonta naira dari bakwai sannan ya siyo mata yar qaramar abayarnan mai hade da kyale waddah akema laqabi da gemun shaidan lol ya siyo mata wannan naira dari biyu da hamsin
Sannan yasai mata takalmin dari biyar
Daman kudin dubu dayane da dari hudu ya tara kuma ko naira bai dawo da itaba don saima da aka biyoshi bashin naira hamsin
Yayi sa,a daya dawo ba kowa a tsakar gidan don haka ya wuce dakinsu kai tsaye
Saude na kwance tayi rigingine tana kallon sama daka ganta zakasan tana cikin damuwa ya zauna gefenta yana fadin tashi saude ga kayan na siyo miki
Ta tashi cikin doki ya zazzage mata kayan ta daddaga tana gama gani ta fada jikinsa domin murna shima ya rungumeta yanajin wani sanyin dadi na ratsa zuciyarsa
Ganin farin cikin qanwar tasa ya fiye masa komai a duniya
Washe gari itace ta kasance ranar qaramar sallah idan ka duba jama,a sai hada hada ake kowa yana cikin murna da farin ciki yara da manya
Kowa yana cikin sababbin kaya cikin tsabta da kamshi
Haka gidan malam bala shida matarsa da yarsa suna cikin wadanda suka raya wannan rana sunsha kwalliya cikin sabuwar sutura amman banda
Rabiu da saude
Don tunda garin Allah ya waye suketa faman aiyukan gida suna gama aiyukan kuma saude tahau kai abinci gidaje yara sai tsokanarta suke qazama qazama yau abin ko kadan bai dametaba sbd itama tasan yau zatayi tsabtar kamar kowa itama zatayi kwalliyar da take ganin iklima nayi ta shafa jan baki tayi kwalliya a fuska tana gama rabon abincin ta zura guga a rijiya cikin rawar jiki don itama tayi kwalliyarta tayi yawon sallah
Yan matan unguwar tasu sukai sallama da yawansu don aqallah zasukai goma duk sunsha kwalliya ji take babu na biyunta
Saude ta amsa musu sallamar dasuketa rerawa
Yar baba nanan?suka tambaya saude tace tananan a daki suka wuceta suka shige ita kuma taci gaba dajan ruwanta  tana shirin wankane suka fito suna labarin zuwa masallaci daganan su wuce yawon barka da sallah
Saude tace dan Allah larai nima ku tsaya nayi wanka mu wuce tare
Larai ta watsa mata wani kallo tabdijam waye zaije yawo dake yar tallah duk nanma wacece qawarki? Tayi shiru tana kallonsu
Salame tace ai sunanki ta kira kinga kenan kece qawarta
Larai tayi saurin fadar Allah ya sauwaqe saidai ko yar gidansu takebi yar baba yar uwarta yar baba ta turo baki Allah ya sauwaqe niba yar uwata bace yar tallar gidanmuce yarinyama tace zata bini ba sai inci uwartaba
Lantana tace to a ware kowa ya ware muga wanda zatabi kowa ya ware ya daddaure fuska
Saude ta hadiye kukan dake neman kubce mata tace ai nima yara yanxu zanyi wankana insa sababbin kayan da yayana ya siyo min inyi kyau
Yar baba tace ke matsa can kyan gidan ubanwa zakiyi kullum sai qazanta jibeta da wani hancinta can sai kace kajeren wando duk sukasa daria harda tafawa sannan suka fice
Saude ta dauki ruwanta ta nufi ban daki tana fadin aidai Allah ne ya bani
Tayi wankanta ba soso ba sabulu don dama ta saba ta fito ta shiga dakinsu batada ko man shafawa ballentana kayan kwalliya
Don haka kayan kawai ta dauka ta sanya ta saka sabon takalminta
Da gyalenta tayita juyawa dukda ba kallon kanta takeba amman ji take tamkar babu wanda ya kaita haduwa
Rabiu ya riqe labule dariya ta kwace masa yaddah yaga tanata faman juye juye sai kace mai rawa tayi saurin juyowa
Tace yauwa shigo yaya wai don Allah nayi kyau?
Rabiu yai murmushi mai hade da daria kamin yace aike daman kyakkyawace qanwata ba kayanne zasu fito da kyankiba kyankine zai fito da kayan kisha kuruminki insha Allahu indai ina raye saina fito da boyayyen kyanki a idanun duniya dauko kusar can kixo in kwance miki kanki duk shi ya bata kwalliyar
Saude tayi saurin dauko masa ya zauna ya kwance mata tas ya sharce mata yasa tsumma ya daure mata shi ya lulluba mata gyalen ta miqe zata fita
Sai kuma ina?
Tadanyi jim kafin tace waje zani yace to bari inci abinci sai in sameki kofar me gari zan daukeki muje kiyi kallon sallar
Dadi ya kamata harda tsalle. Ta fice
Inna laure na zaune saman kujera tanacin soyayyen nama wanda ko qashi batabamasu saudenba ballentana susa ran tsoka
Cikin rudu da kidima laure ta dauki sallallami la,ila ha illallahu muhammadur rasulillahi
Mezan gani yau ni laure saude zonan dan qashin ubanki
Ta zaburo ta shaqurota ta maqureta uban waye ya baki kayannan?
Yar iska kudina kike sata a gidannan ban saniba,,,
Ta dauketa da mari da qarfinta kokuwa maza kika farabi iye?
Saude ta fara ihu tana kakari sbd shaqar da tayi mata
Laure ta hankadar da ita har kanta ya bugu da bango ta shiga kwalama
Rabiu kira wanda tundata soma dukan nata yakejin kamar ya hadiyi zuciya ya mutu sbd baqin ciki ya fito daga dakin ya nufota yana fadin gani
Laure ta daukeshi da wani mahaukacin mari wanda ya sashi dafe kunci ta nunashi da dan yatsa cikin bala,i bakinta har kumfa yakeyi
Gidan ubanwa aka samu wannan kayan sata kukemin a gidannan ban saniba?
Aiko sai laure tasa ihu yau na shiga uku na lalace abinda nakeji a waje yau ya shigo cikin gidana ashe da yan fashi nake zaune ban saniba

Hmmm
Su  laure manya

Naku har kullum
*ABDULLAHI ISMAIL SALANKE*

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *