Yar tallah13

               *YAR TALLAH*

               

                *CHAPTER13*

         *ASHA KARATU LAFIYA*

a cunkushe take saboda duk abin da ake, tana jin ‘Yar Baba ta tabe baki ta wucc soron gidan, Saude ta tsaya da hura wutar tana kallonta idonta ya ciko da hawayce
Hamid yana zaune a barin tabarma yana karkada kafafuwansa yayi irin zaman nan na masu cin tuwo, ‘Yar Baba ta jingina da bangon soro ta kafe shi da ido cikin ido tana wani murmurtsa idanun
Hamid ya tsaya yana qare mata kallo cike da mamamki yace, “Ke kuma fa wace ce?”
‘Yar Baba tayi wani qasaitaccen murmushi irin na gogaggun yan duniya kafin tace “Ai nice  iKilima wadda akafi kira da ‘Yar Baba, da alama baka gane niba ko?” Ta Kara jan wani munafukin murmushi tana fadar.
“Kowa ma idan nasa kayan nan haka yake fade: be ganeni ashe dama haka nake da kyau hummm Kayan suna mini kyau sosai.”
Wani takaici da haushi suka kama Hamid cikin takaici yace, “Ke da Allah saurara kinji bana san shirme da sakarci kinji, Saudat nace a kira mini ita nake nema ba wai keba kin gane? ’
‘Yar Baba taji tamkar ya watsa mata ruwan zafi a zuciya cikin Bacin rai tace, “Ai ba ita Baba yace kana nema ba ni ya ce kana nema
Hamid ya dan sassauta murya, “Kin ga kiyi hakuri don Allah ki je ki kira mini ita ta sanda zuwana please ban san ku biyu bane a gidan.”
‘Yar Baba ta waro ido tana kallon shi bakinta na fadar, “Kutumar… wallahi ba zan je ba har ma ta isa in kula ta ‘yar tallan gidan namu ba zan jeba wallahi, sai dai ka daskare a nan.’
Ta juya za ta tafi Hamid yayi wani murmushin takaici ya zura hannu cikin aljihu ya ciro kudi‘ yan dari biyar biyar sababbi dal guda hudu ya miqa mata.
‘Amshi ga wannan ladan kiran nata idan ba zaki kira ta don Allah ba. ”
‘Yar Baba tasa hannu ta fizge kudin tana fadar, “Ai raba mugu da makami ibada ne” Ta juya ta yi cikin gida.
Laure ta tarye ta tana fadar, ‘Ya akai ne?”
‘Yar Baba ta fashe da kuka tana fadar, “Wai Laure wai ba ni yake so ba, wai SAUDE yakeso.’
Laure ta ja wata ashariya ‘Kan babbam…. Bake yake soba to uwar wa yake so?”
‘ “Yar Baba ta nuna’ mata kudin da ya ‘ba ta, “Kin gama waiyabani inkiramasa ita
Laure tace daukomin mayafina naje na sameshi ‘Yar Baba ta kwasa da gudunta ta dauko mata mayafinta ta baza saman kafada ta nufi soron kamar an hankada ta.
Hamid yana zaune hmnunsa riqe da qatuwar
wayarsa yana charts da ita, yana ganinta ya fadada fuskarsa da fara’a.
“Sannu da fitowa Umma barka da rana.’ Inna Laure ta amsa fuskarta ba yabo ba fallasa
sannan ta gyara tsayuwarta tana fadar, “Kai ne bakon Saude?”
Ya dan sunkuyar da kai qasa alamun kunya kafin
ya ce “Eh nine Umma.”
Laure ta kuma gyara mayafinta mai kama da an kwato shi daga bakin kura ta ce “To Saude dai da kake ganinta shegiya ce ‘yar gaba da Fatiha, ce yarnan da ka gani kuwa ni ce mahaifiyarta nina haife ta da cikina, kuma ka san ana cewa shi dan gado sai yar gado sannan wurin gantali da yawon bariki gari gari babu inda Saude bata zaga’ ba. Kai in taqaice maka har cikin shege sai da ta yi.’
Wani irin abu ya dakarwa Hamid zuciya mai zafin gaske ya samu da kyar Ya iya hadiye shi kafin ya iya fadar, “Amma Umma da mamaki a gaskiya ba zan Boye miki ba Saude bata yiwa rayuwarta adalci ba sululu kenan macijin  sari ka noqe
Ki yi hakuri Umma insha Allahu ba zan guje mataba don wannan qaddarar ta fada  nayi
miki aIqawarin  auranta  a hakan in ceto rayuwarta.”
Laure ta ce, “A’a ahir!.Dinka karka fara don ba zaka taba iya ceto Saude ba saboda kin Allah irinna yarinyarnan ya wuce tunanin ka” Laure ta sa kukan munafurci har da su fyace majina.
Hamid yana kallonta saidata gaji dankanta ta dan sassauta ta ci gaba da fadar, ‘Dan nan shu’umancin Saude yana ci min zuciya wai yarinyar  hartasan tanemi mace ‘yar uwarta,bacin mazan datakebi yandakasan karyar maza haka take.
Na zubarwa Saude ciki yakai biyar a asibiti har sun haddace mu, sun gaji dan har cewa sukai damu idan muka a qara zuwa kararmu sukace zasuyi wai saboda zubdawa Saude cikin da muke yakai iyaka.”
Hamid ya ce“Duk wannan ba matsala ba ce Umma, wallahi ahakan insha Allahu indai saude mai shiryuwa ce sai na shiryar da ita.”
Inna Laure tace, “Kai malam,Saude bazata taba shiryuwa ba saboda ba ta tsoron Allah k0 kadan babu Allah a ranta.”
Hamid ya ce “Ai Umma Islamiyya zan sanya ta insha Allahu kekanki saikinyi mamakin yanda zata shiryu ta nutsu.”
Inna Laure tace“Dannan kenan bakasan Saude ba har yanzu, ai kwakwalwarta a dode take ba
ta daukar komai babu abinda kwakwalwar ke iya dauka ballentana harta iya haddace shi.’
Yace, “Ai Umma babu abin da yafi qarfin addu’a, sai mu taya ta da addu’a insha Allahu za muyi nasara amma ni ina son ta kuma wallahi aurenta zanyu
Inna Laure ta harzuka cikin haushi tace “To baza,a aura maka itadinba ‘yata daice to nayi mata miji koka tashi kabarnan yanzunnan wallahi k0 in maka ihu kwarto, dan iska kai ana gwada maka Annabi kana rintse ido.”
Hamid ya mike ya ajiye mata bandir din yan dari bibbiyu na dubu ashirin ya ce, “Zan tafi Umma ga wannan a sai sabulu zan dawo sati mai zuwa da fatan za ki sauko daga dokin qiyayyar da kika hau, na gode
Ya juya ya fice daga soron ya bar Laure tsaye dakam tamkar wadda aka kafe sai zazzare na mujiya take a kan kudin, wani abu na yi mata zarya a zuciya ta duqa ta suri kudin tayi cikin gidan tana kwalawa Saude .kira Saude da take duke gaban murhu ta yunkura da niyar tatashi, amma ina dukanda Laure ta soma
kai mata yasa ta duke babu shiri, Laure ta janyo
bakin wuta tana faman dukanta sai kace yaqi fadi
take. “Yau sai na kashe ki har lahira inga ta
soyayya, ke nan har kin isa wani yace yana sonki a hakan. To idan ma farar fatar ce ta janyo shi yau
sai na lalata ta.” Tun Saude na ihu har ta soma Kokarin kwatar
kanta, ‘Yar Baba ta tare ta tana fadar, ‘Laure fuskar za ki toya ki lalata mata ita muga ta kyau da iyayi.”
Saude .tasa wata irin kururuwa, ta kwace daga hannun ‘Yar Baba ta yi dakinta ta maida qofa ta rufe, tana jin Laure na fadar k0 ta bude ko ta cin nawa dakin wuta amma ba ta motsa ba.
Kuka take sosai kamar ranta zai flta, dan Laure duk ta tattaye mata jiki da bakin wuta abin ka ga jar fata duk jikinta ya yi jawur. Ai kuwa nan ta sulale Kasa ta zauna tana faman kukanta.
Tabbas ya zame mata wajibi ta cirewa zuciyarta kwadayin wata rayuwa mai dadi, dan ta tabbatarwa kanta Inna Laure ba za ta taBa barinta ba, tasa hannu tana sharar kwalla. Inna Laure ta sake bubbuga qofar tana fadar,
“Sai ki fito ki daukar mini talla ta in ba haka ba in karya kyauran in shigo.”
Yadda take dukan kyauren da Karfinta ya tabbatarwa Saude za ta iya ma abin da ya fi hakan, ta   miKe tana kallon kayan jikinta, tun   leshin da ta saka ne ta je gidan Garba Gurgu ne a jikinta, har yanzu ga shi Laure duk ta qona shi. Ta dauki hijabinta ta sanya ta bude kofar ta fito, Laure ta kai mata wani duka tana fadar.
“’Yar iska munafuka!”
Ta watsa mata kayan hannunta, ‘Karbi maza ki canza kayan jikin ki duk wani abu da ki ka san na kwalliya ne a cikin dakin nan toki  miqo mini shi yau sai na ga qaryar soyayya ai dai sai da kyan ake soyayyar ko to zan gani.”
Saude ta amsa ta koma dakin, wata kodaddiyar atamfa ce riga da zani ba dankwali, rigar sai a hada irinta mutum hudu su shiga ciki ga ta duk ta yage saboda tsufa. Sai zanin Jaka tsaye yayi matukar shan jiki ya sha gamun baki har wuri hudu, ga shi babu dankwali ‘sai wata abaya, hawaye suka ciko a idanuwan ta tausayin kanta ya kamata ta cire kayan jikinta ta sanya wadanda ta ba tan, sannan ta tattara komai na cikin dakin ta fito da shi.
Laure ta kwashe tana fadar “Munafukar banza, kuma wallahi ki sake in ji labarin kin tsaya kin saurari matsiyacin yaron nan na rantse da Allah sai
na lahira ya fiki jin dadi, ‘yar iska tambadaddiya.’ Ta sa qafa ta haure ta sannan ta wuce
Saude ta dauki bokitin tallarta tasa kai ta fita, tana faman sharar kwalla. Rayuwa kenan ita dai ta san ba ta daga cikin wadanda sukai sa’ar rayuwa a duniya.
Tana tafe tana sharar kwalla tana zancen zuci, ba ta ankara ba sai dai ta ga mutum a gabanta, wani irin kallo yake mata mai cike da mamaki muryarsa a sarkake ya ce Lafiya Saudat, wace irin shiga ce wannan laflyarki qalau kuwa?”
‘ Saude tasa hannunta guda tana goge hawayenta, ta soma magana cikin kuka.
“Lafiyata lau don Allah kayi hakuri ka fita daga rayuwata na roqeka.”
Hamid ya girgiza kai yana fadar, “Impossible, wallahi abin da ba zai taBa yiwuwa ba kenan, sai dai idan har son ki zunubi neto na ratayawa kaina alhakinsa, amma ba zan taBa barin ki ba.”
Saude ta tsaya da kukanta tana kallon shi kafin
ta ce, ‘Me yasa ba xaka rabu da ni ba, k0 kana san jefa zuciyata ne cikin bala’in da ba zan iya fita ba? . Wannan kukan da ka ga ina yi duk ta dalilinka ne.” Hamid yace “Na ji na dauka, amma don. Allah ki yi hakuri ki bani kadan daga cikin labarin ki ni
nayi miki alkawarin taimaka miki da duk wata gudunmawar da kike buqata.”
Hawayen da suka tsaya da zuba daga idanuwan saude suka Ci gaba da zubowa tana sharBar majina kana ta fara magana.
“Kamar yanda ka sani sunana Saude, tunda na . tasona bude idanuwana na ganni tare da Yayana,shine uwata shi ne ubana shine komai nawa. Bai  barin nayi kuka , kullum burin shi ya samamin farin ciki da gatan da na rasa a rayuwa,
Ni kuwa burina kullum in matsa masa in sanya shi yimin abinda baidai ikonyinsa
Hamid ya ce, “To yanzu yana ina shi Yayan naki?
‘ Saude ta Kara rushewa da kuka kafin ta ce . an raba ni da shi, su suka raba ni da Yayana.”
Ya ce, ‘Su waye?’
Muryarta na rawa cikin kuka ta ce, “Baba da inna Laure.”
Hamid ya ja wani numfashi mai nauyi yana jin yanda take ta faman kuka da shashsheka tausayinta mai tsanani ya shige shi, muryar shi a sanyaye yake magana.
“Ina mahaifiyarki da mahaifinki su ke?”
Saude ta ce, “Ban san inda mahaifiyata take ba,
Ban taBa ganinta ba, wannan kuma da ka gani shi
ne mahaifina, Inna Laure kuma matarsa ce ‘yar Baba ita kuma qanwata ce
Hamid ya sake sauke wani nannauyan numfashi ya fahimci yarinyar tana cikin matsala, ya zuba mata idanuwansa farare tas cikin sanyin muryarsa ya ce, “Ki yi hakuri Saudat na fahimci irin abin da ki keji a zuciyarki, ki kwantar da hankalin ki insha Allahu na yi miki alqawarin taimaka miki da dukkanin karfina in dai ina raye sai na daga darajarki a duniya, sai kuma na wanzar da murmushi a idanuwan da Yaya ya bari cikin hawaye.”
Ya dan qara numfasawa kafin ya ce “Ki je
” ‘lallar ki dawo, zan zo da daddare in same ki wurin tallarki za muyi magana, amma don Allah ki daina kukan nan haka nan kin ji?”
Saude ta daga masa kai tana goge hawayen da
ke fuskarta, ya dan tsura mata ido da murmushi a kumatunsa ya ce, “To dan yi murmushi mana beauty
*Dukda batasan abindayace ba,ammatayi murmushin kuma kalmar beauty din ta yi mata’ dadin sauraro a kunne. Sai da ya ga tafiyarta
sannan shima ya juya ya tafi zuciyarsa na raya masa abubuwa masu yawa.
Da yamma likis Saude ta dawo daga wurin tallarta Laure ta jibgo uban wanki, sannan tace ta ‘ dora sanwar tuwan dare. Saude ta duka a gun ta yi kukanta har ta gaji sannan ta ja ruwa ta dora sanwar ta dawo ta ci gaba da wankin.
Ana gama sallar Magariba Malam Bala ya dawo gidan, Laure ta shimfida masa tabarma a
tsakar gida ta kawo masa fura da mafici ta zauna gefensa.
Malam Bala ya bude furar ya soma sha, sannan
ya dubi Laure yana fadar, “Wai ya suka yi da yaron nan ne Laure?”
Ta taBe baki tare da furta, “Uhmm! Malam kenan, ai yaron dan iska ne takadari kana ganinsa kamar na kirki suna hira da ‘Yar Baba ya nemi taushe ta cikin zaure Allah ya rufa asiri yarinyar nan ta yi ihu, na kwaso da gudu na raka shi da bakin wuta har waje, mutane na ta bani hakuri suna fadar in kyale shi ai ni’wannan abu ya cimin zuciya wallahi har kuka na yi.
Yanzu dan kawai an gan mu talakawa matsiyata shine za a shigo har cikin gida a ci zarafin mu. Kai Malam wannan abu da me ya yi kama?” .
Tunda ta fara zancen ‘ya’yan cikin Saude suka fara juyawa wani irin gumi ya shiga tsatstsafo
mata, take juwa ta kwashe ta, sai dai ta ganta zaune a gefen bokiti.
Malam da tunda ta fara zancen ya hau sallallami, ai sai ya rufe furar yana fadar, “Wai harni za a ciwa mutunci a garin nan Laure na rantse miki da Allah sai na yi kararsa kotu, kuma ta addinin Musulunci.”
Laure ta ce ‘Aa, Malam abin ai duk bai kai na kotu ba wurin mahaifinsa za ka gobe tunda sassafe ka kai qararsa ka ce ya jawa dansa kunne ga abin da ya yi maka in ba haka ba za kasa hukuma ta
shiga tsakaninku.”
Bakin ciki ya cika malam Bala ya zabura ya
mike ya suri buta ya nufi bandaki.
Laure ta tabe baki ta raka shi da harara a zuciyarta tana fadar sauna kawai. Ta yunkura ta mike ta dubi Saude da ke ‘zaune tace, “Toke kuma tsohuwar munafuka kin zauna kin kasa kunne kina sauraran jama‘a sai ki tashi ki dauki tallar gyadar ki tafi idan kin dawo kin qarasa wankin tunda cinikin na yanzu ne.”
Saude ta lallaba ta mike tana jin tamkar za ta
fadi ta dauki tallar ta fice, kukama ya gagareta idanuwanta sun yashe babu komai cikin zuciyarta sai duhu. ‘ ‘K0 minti goma bata yi da zama ba ta hango shi ya nufo inda take; yau sanye yake cikin manyan kaya, ‘na wani lallausan yadi milk colouz; mai hasken gaske dukda a’cikin duhu ne amma bata kasa ganin shekin yadin ba, kansa yana sanye da hula baka yasa bakin takalmi a Kafafuwansa, tun kafin ya Karaso kamshin turarensa ya daki hancin Saude ta lumshe idanuwanta, sai a lokacin wasu
hawaye suka tarar mata ’ Hamid ya yi mata sallama tare da durKusawa gabanta, muryarsa a sanyaye ya ce “Sannunki yan matana barka da Kokari.” ‘
Saude ta bude idanuwanta tana kallonsa. hawayen da suka taru a kwarin idanuwanta suka ziraro ‘ ‘ Hamid ya mike tsaye ya ciro farin hankicif
Dinsa daga cikin aljihu ya miqa mata, Saude ta girgiza masa kai don ta san k0 rike hankicif dinma kadai tayi sai ya yi dauda, to balle ta goge fuska dashi wai sunan wani   wai shi
Danduwala.
. Hamid ya sake mika mata hankicif. din yana fadar :‘Wallahi sai kin goge garama ki karBa kawai” ‘
‘ Jim yanda ya yi saurin rantsuwar ne yasa Saude
ta amsa ta goge hawayen, ya ce, “To bani abuna”
Ta yi wani dan taqaitaccen murmushin da bai  , wuce kan labbanta ba ta  ya qara goge fuskar shi da shi sannan ya saka a aljihu yana fadar.
“Wannan tafiyar yau ba taki ba ce wurin Baba nazo don haka ni kin ga tafiyata.”
Bai jira abin da za ta ceba ya juya ya tafi abinsa zuciyar Saude ta qarasa karyewa ta kifa kanta saman kayan tallar tana rera wani irin kuka mai cin zuciya. .
Hamid ya karasa Kofar gidan da qarfin zuciyarsa ya aiki yaro ya yi masa sallama da Malam Bala. Yaron bai jima da fitowa ba ya ce ga ‘ shi nan zuwa, sai ga Malam Bala ya fito da alama masallaci za shi saboda an fara kiran sallar Isha’i, yana ganin Hamid a qofar gidansa ya ja ya tsaya yana fadar.
“Malam laflya?”
Hamid ya durKusa har qasa yana gaishe shi. Malam Bala ya ce“Kai dakata ban san rashin kunya ka ji har ni za ka dauka mutumin banza da WOfl, to ka je komai ka yi dan kanka kuma, Allah ya isa tsakanina da kai, duk da ka ganni talaka ina da wadatar zuci.”
Mamaki ya kashe Hamid ya dago yana kallon
Malam muryar shi cike da rudani ya ce Don girman Allah ka yi hakuri Baba wallahi ban san abin
da nayi ba wanda kake fadarsa a yanzuba Malam Bala yace ‘Ai dama ba zaka san abin da kake; fada a kansa ba, tunda kaci idon dan akuya ‘ amma abin da nake so da kai anan shi ne ka tashi ka bani Wuri kar in sake ganin ka gifta k0 qofar gidan nan, kuma zanje in samu mahaifin naka ya yi maka tsakani da‘ ya yana mutumin banza kawai’ Yana gama fada ya juya zai tafi, Hamid na kiransa‘ Baba don Allah ka saurare ni, amma bai kula shi ba , ya yi gaba Wani  abu ya tsaya zuciyar Hamid, ya lallaba . ‘ ‘ya mike jikinsa ya yi masa masifar sanyi ya nufi ’ inda Saude take zaune tana faman rera kukanta. ‘ ‘ « Tausayinta ya lullube shi ya kura mata ido ‘ na wani dan lokaci kafin ya soma magana muryarsa a ‘ sanyaye yace“Ba zan hana ki kiyi kuka ba Saudat, « dan zubar hawayenki ya zama dole na fahimci abin da aka shirya mana, amma don Allah kiyi haquri kamar yadda na dauki alkawarin taimaka miki ba . zan fasa ba Saudat da yardar Allah sai naga rayuwarki ta inganta, kar ma Wannan abun ya dame ki ki yi hakuri kinji share hawayen ki karma  ki Jawa kan ki
. ciwon kai” ‘ Ya samu ya lallasheta ta yi shiru sannan ya tafi zuciyarsa na faman saqe-sake ‘
Washe gari da sanyin safiya Malam Bala ya shirya ya nufi gidan Alhaji Bashir saboda yanda Laure ke ta faman ingiza shi. A kofar gidansa ya same shi zaune saman mota da News paper a hannunsa yana dubawa.
Malam ya yi masa sallama, Alhaji Bashir ya dago tare da amsa masa cikin sakin fuska ya miqa
. masa hannu su kai musabaha. Malam Bala ya ce
‘Dama Alhaji wajen ka nazo.”
Alhaji Bashir ya ce, ‘To mu shiga daga ciki k0?”
“A’a daga nan ma ya isa, Kara na kawo maka.”
Alhaji Bashir ya ce, ‘Kara kuma tawa?”
Ya ce ‘Danka Hamid na kawo maka qararsane ka ja masa kunne dan kuwa ya shiga har cikin gidana zai keta mini haddin‘ ya shi yasa na zo wurinka na kawo maka kashedinsa, don kar naje in dauki mataki kaga anatare babu dadi,don haka nazowurinka kai masa kashedi da iyalina.”
Alhaji Bashir da ya nutsu yana kallonsa mamaki ya dabaibayeshi muryar shi a sanyaye ya ce, “Lallai ka haifi yaro ba ka haifl halinsa ba, don Allah ka yi haquri Malam in dai nina haifi Hamid ya gama bi k0 ta gefen gidanka kayi haKuri don Allah, don Annabi.’
Malam ya ce, “To ni dai kashedi na kawo maka
kaja masa kunne.’
Alhaji Bashir ya ce, ‘Insha Allahu.” Sannan ya juya ya Lafi buzun-buzun.
Alhaji Bashir ya sauke wani gwauron numfashi, sannan ya yunqura ya nufl cikin gidan zuciyarsa a cunkushe ya shiga falon gidan, babu kowa a falon sai Hajiya Hanifa tana tsaye tana goge-gogenta a falon, yana shigowa ta tsaya da aikin da take tana kallon maigidan nata bakinta na fadar.
“Lafiya dai k0 Alhaji?”
Muryarshi ba dadi ya ce, “Ina yaron nan yake?”
Hajiya Hanifa ta ce, “Yana dakinsa ka san ai bai farka ba yanzu.” Alhaji Bashir ya ce tado mini shi maza-maza.
Jikin Hajiya Hanifa na rawa ta nufi kofar dakin Hamid din. ta kwankwasa masa yana kwance nannade cikin bargo yana Sheqa barcinsa, saboda rashin baccin da ya samu jiya.
Ya bude idanuwansa tare da yunkurawa ya mike, yazo ya bude kofar, Hajiya ta dube shi kafin ta ce “Ka je Abbanka na falo yana jiran ka Ya amsa dato, sannan ya juya ya koma ciki ya nufi bandaki ya wanko bakinsa da fuskarsa sannan ya fito ya dauko jallabiyarsa ya sanya ya fito
Alhaji Bashir yana tsaye inda yake har Hamid ya qaraso yana qokarin dukawa ya gaishe da mahaifin nasa, ya ji saukar wani gigitaccen mari ya ratsa .
Kunnensa ya dago da sauri yana kallon sa, cikin Bacin rai Alhaji Bashir ya soma fada“Ni zaka dauka dan iska k0 Hamid dama abinda. ka koyo kenan a qasar wajen dana tura ka. Ni zaka jawa; abin fada a cikin garin nan. To baka isaba., maza ka tattara yanaka-yanaka ka koma Kaduna, yau
ba sai gobe ba ka je ka kula da kamfanina tunda aikin gwamnatin bai zama dole ba, ba zaka zauna nan kaja mini abun kunya ba, dama shi yasa da aka ce ka je ka nemi yarinyar nan Zainab kaqi saboda ba ka gaji da barbada ba, ka yi daidai gwargwado amma ka kyauta tashi ka bani wuri.’ Jikin Hamid ya yi matukar yin sanyi  ya miqe a sanyaye tare da fadar, “kayi hakuri.” Ya juya ya koma dakinsa ya kwanta, tunani ya addabi zuciyarsa ‘ya rasa hanyar da zai bi ya taimaki yarinyar nan, ya ‘ lusmhe idanuwansa yana jin wani abu na masa
yawo.
Ya san fushin mahaifinsa  yana fushi da shi yayi kwana uku, tabbas kuma dole ya tafi Kaduna tunda ran mahaifin nasa ya Baci, ya lallaBa ya mike ya cire jallabiyar dake jikinsa ya fada bandakin dake cikin dakinsa.
Saude ta dawo daga tallan safenta ta iske Laure Zaune itada Malam Bala suna tattauna maganar
Hamid, ta a jiye bokitin wainar ta ‘bama Laure kudin, ta karba tana kirgawa sannan ta ,dubeta tana fadar.
“Jeki ga wake can ki kai markaden alala.”
Saude ta amsa da to, sannan ta wuce Malam Bala ya dubi Laure yana fadar, “Kin ga nama mance, Malam Garba ya fada min za”a kawo kayan sa ranar yarinyar nan gobe
Laure tace “Ai garama a gaggauta Malam mu kawar da yaran nan mu huta.” ‘
Iya abin da Saude ’ta ji kenan ’ta fice tana jin tamkar za ta kifa saboda tashin hankali da fargaba. Haka ta je ta kai markadan ta dawo ta dafa alalar duk Laure na zaune tana kallonta, ta gama ta zauna ta Kirga mata a bokiti, sannan ta dauka ta tafi
Hamid da ke kokarun sanya jakarsa a mota ya hango ta ya rufe motar da sauri ’ ya nufo ta da murmushi a fuskarsa ya ce, “Ranki shi dade barka da
fitowa.” Saude ta waigo tana kallonsa kafin ta gaishe shi
da dakusasshiyar muryarta. Hamid yargyara tsayuwa yana fadar. “Dama ke nake jira ki taho mu yi magana  tun dazu   Hamid ya ce ‘Kinga wannan fitowar wallahi Kaduna zan tafi yanzu yanzun nan mahaifina ya tura ni amma karki damu kwana uku kaWai zan yi in
dawo saboda maganar ki, akwai wata hukumar kula da haqkin mata zanje ofiss din su a kan maganar ki
Saude ta daga masa kai alamar eh yasa hannu cikin aljihu ya Ciro kudi masu yawa ‘yan naira dari biyar biyar guda ashirin ya miqa mata yana fadar ‘Ga wannan ki riqe ki yi amfani da su kafin in dawo.”
Saude ta zaro idonta wadanda suka ciko da hawaye, ta girgiza masa kai alamar a’a, Hamid ya hade fuska yana kallonta yace “Karbi na ce mana meye haka?” ‘
Ganin yanda ya hade fuska yasa Saude ta sa hannu ta karBa tana fadar, “Na gode.’ Ya zaro wata waya cikin aljihunsa ‘yar qarama mai kyau ya mika mata.
“Ga wannan ki riqe ta hannun ki zan rinka kiran ki mu yi magana.”
Saude ta karBa ya juya yana fadar, “Sai na dawo.” Saude ta juya da niyar taflya su kai ido hudu
da ‘Yar Baba tana tsaye tana kallon su, suna hada ido ‘Yar Baba ta ja kwafa tana kada kai ta wuce ‘Hankalin Saude ya yi masifar tashi wasu zafafan hawaye suka biyo kuncinta ta ji tamkar ta zubar da kudin saboda firgita, cikin tsoro ta je tallar yau ta dawo cike da tsoron irin hukuncin da za ai mata. Haka ta shigo gidan ‘tana faman sanda kamar munafuka a tsakar gida ta samu Laure da dillaliya
suna zaune. Ita lauren tana kan tabarma, inda ita kuwa dillaliya tana kan kujera ‘yar tsugunne. Saude ta durkusa tana gaishe da dillaliyar sannan ta mikawa Laure kudin tallar nata, ta karBa ta sake mika mata hannu.
“Bani sauran wanda kwarton naki ya baki
Jikin Saude na rawa ta ciro kudin da wayar ta mika mata, Laure ta shiga jujjuya wayar a hannunta da kudin tana taBe baki ta dubi dillaliya tana fadar.
“Duba ki ga fa.”
Dillaliya ta karba tana gani, ta dago tana kallon Laure tana fadar, “Amma ni sai nake ganin kamar wata banza ce ta sauko muku daga sama, kawai ki yi kwance-kwance kinada abun duniya idan ma yaudara ce ta kawo sa ke dai me ya dame ki ita ta jiyo.”
Laure ta ce, “Hmm! Dillaliya kenan ba zaki gane bane yaron fa da gaske aurenta zai yi ba wai da wasa yakeba.”
Dillaliya ta dan yi shiru kafin ta ce, “To yanzu ya ki ke ganin za a yi?”
Laure ta ce, “Gaskiya na fara tsora ta da lamarin nan karfa danhakin dakaraina yazo yatsone maka ido. Shi yasa na kira ki kawai ki dauke ta ki tafi da ita AIKATAU cikin gidaje har zuwa lokacin bikinta shekara guda za a sanya ranar daurin aurenta sai ki taho da ita kawai kin ga na yi maganin takadarancin k0ba haka ba?” Dillaliya ta ce, “AI ko kin kawo shawara Laure, Abuja ma zan tafi da ita gidan wani sabon dan Majalisa, mai tashen kudi, wata kawata ce ta yi min maganar  kai masu ma’aikata gidan, don haka ta shirya gobe zan zo in dauke ta da sassafe mu tafl, duk wata
kina da dubunki biyar zan rinka karBo miki na albashinta.”
Dadi ya kama Laure ta ce “Allah ya kai mu Kawata, tun Asuba ma zan tasheta.”
Dillaliya ta ce, “Amma kina ganin ba za mu samu matsala da mahaifinta ba?”
Laure ta ja wani gajeran tsaki tana fadar, “Ke kuma da sonkawa zance wannan hoton wake sanya shi a lissafi ai sai yanda na yi da shi.”
Dillaliya ta ce “To shi kenan babu matsala ‘yar
uwa. ‘ . Duk labarinsu Saude tana jiyo su daga daki tana zaune saman simintin dakin kanta na jingine da bango, wasu irin hawaye ne masu zafin gaske kebin kuncinta. Wayyo duniya ita dai ta san ta zo duniya a rashin sa’a. Haka ta ci gaba da rera kukanta babu mai‘lallashinta.
Washe gari Karfe takwas kamar yanda dillaliya ta
fada ta zo cikin shirinta Laure ta tiso qeyar Saude a
gaba, ta hada ta da dilla’liyar tana faman zuba mata kashedi.
‘Ki kulada aikin da za,a baki kuma banda dan hali, dan wallahi kika sake ki ka yo abin da za a koroki kika dawo min lokacin dawowarki bai yi ba wallahi saina shaqe ki kin mutu kinji na fada miki, kuma kinsan zan  iya
Ta zaro naira dubu cikin kudin da Hamid ya ba ta, “wanda ta kwace, ta mikawa dillaliya tana fadar.
“Ga wannan kiyi kudin mota.” Dillaliya ta karBa ta tisa Saude gaba suka tafi.
Sai a lokacin wasu hawaye masu zafi suka samu damar zirarowa daga idanuwanta, tana ji tana gani suka nufa tasha cikin‘ yar qaramar motar nan Kurkura.
Suna sauka dillaliya ta kama masu motar Abuja suka “ hau, dama. saura mutum uku, aka samu wani namiji
yakarasa cikon na ukun direbaya dau hanyar Abuja.
ALHAMDULILLAHI MASHA ALLAH _
Sai mucewa matafiya Allah ya kaisu lafiya. .

Mu badu  a LITTAFIN Na biyu  gobe daidai wannan lokacin
Donjin yaddah wannan lbrn zaici gaba da kayawa Naku har KULLUM
*ABDULLAHI ISMAIL SALANKE*
ke cewa GOBEMAAA DA LABARIII

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *