YAR TALLA
CHAPTER23
Saudat na kife a katifarta tana rusar kuka, Iyah ta shigo, “Saude tashi maza mu tafi” ,, Saudat ta dago da sauri tana kallon Iyar da jajayen idanuwanta, ji take tamkar zolayarta take Iyah ta mika hannu ta kamo hannun Saude tana fadar, “Tashi. maza mu tafi, yau mu ai mun ga ikon Allah”.
‘ Saudat ba ta iya yin musu‘ba ta mike tabi Iyah suka fito, inda suka iske har hare ta kai qofar gida don haka suka rufa mata baya suka rankaya, Saudat jin abin take tamkar cikin mafarkinta, to meke faruwa ne? “‘ Hmm oho
“””””””””””. ‘””””””””
Tunda Dr Ahmad yayiwa motarsa key ya dauki hanya tafiya kawai yake amma ba tareda yasan irin tunaninda yakeyiba gudu yake saman titi bana wasa ba, tamkar wanda ke dambe da iske,, Allah dai ya kawo sa garin Abuja.l fy
. ~ Babu inda ya yi wa tsinka sai gidan iyayensa; yana faka motar tasa ya kulle murfin , motar yasa qafa ya shiga tamkar’wani mara lakka‘
ya na cikin gidan nasu, da ‘yar siririyar sallamar dashi kadai ya san yayi ta. ‘ Babu kowa a falon shiru babu komai
sai kukan AC,kamar wanda aka
hankada ya fada saman doguwar kujera ya rungume fitan kujerar ‘ tare da lumsha ,idanuwansa tamkar wanda ya sha wani abin maye, yana shakar sanyayyen qamshin turaren wutar dake tashi,sannu ahankali yana falon tsawon mintunan da suka haura talatin babu wanda ya fito falon , sai can Hajiyarsa ta fito daga falonta da alama ma fita za tayi don’ sanye ta ke da atamfa super Holland wadda . aka yi wa dinkin riga da siket, da wani qaton mayafi wanda tsadarsa ta tasar wa dubu talatin. Hannunta na riqe dana riqe dana qaramar jaka bazaka taba cewa ta haura shekaru arba”ba, amma nan sittin ne harda‘yan kai. < Kodayake k0 shi uban gayyar a yanzu talatin da shida ne ke kanshi Ganin Dr a falon ya bawa Hajiyar mamaki Dr. ya bude idanuWansa da kyar yana . kallonta tamkar wanda yayi cutar shekara guda
tace “Lafiyarka kuwa Ahmad? Me ke damunka ne ”
Dr. ya dago hanunsa da kyar ya dafa kansa .kafin yace “Momy kaina kamar zai rabe biyu, zuciyata fashewa za tayi”.
Hajiya ta dimauce ta soma kiran sunan
Allah tana fadar, “Yau nina shiga uku Ahmad tashi mu je in kai ka Maitama District Hospital a duba min kai”.
Dr. ya girgiza mata kai, “No Momy ki kyale ni don Allah, ciwona bana asibiti bane, bugun zuciya ne idan na dan samu relive zai daidai
Ta ce“Kamar ya zai daina Ahmad? wacce irin damuwa ce wannan da ta ke qokarin kai ka kabari?”
Dr. yaja dogon numfashi kafin yace “Momy sun hana ni Saudat, wallahi Momy ina sonta, taBa zuciyata ki ji yadda ciwo ke‘ nuqur kusar zuciyata”.
Momy ta dan zuba wa dan nata ido, kafin tace “To ita Saudat din sukace bazasu baka ita baka ita ba sai kace wani mai
mugun hali? Duk duniyar nan da ma akwai inda zakaje neman aure ahana ka?”
Dr. ya girgiza kai “Wallahi Momy baza su barni na auretaba don Allah Momy ki bani shawara, ya zan yi?” .. Hajiya ta sauke wata nannauyar ajiyar zuciya kafin ta raBa kusa da shi ta zauna, ta cusa hannunta ‘cikin sumar kansa tana sosa . masa cikin Sigar rarrashi taci gaba da fadar. “Don Allah ku zamo mai tawakkali Ahmad, ka zamo mai juriya da rungumar abin da Allah ya qaddara maka, ka sani bai hana ka Saudat don baya sonka’ ba, sai don kawai ya jarrabe ka Ya gwada imaninka, haba dana kai _ din fa mai kwarin zuciya ne, ina kwanjin dana ’ Sanka da shi? Haba dana ka zamo mai juriya kaji?” ‘ ‘ Kai kawai ya iya daga mata tace ’ “Yauwa nawan daure ka tashi mu tafi aSibitin ’ Doctor ya duba ka yanzu mu dawo” , Baimusa ba yayunkura dakyar tana riqe da hannunsa suka fice ta sa direba ya jasu ‘cikin babbar Jeep dinta suka nufi asibitin.
⬆️⬇️⬆️⬇️⬆️⬇️⬆️⬇️
Iyah na”riqe da hannun Saudat har suka isa gidan, ita dai tafiya kawai take, amma ba ta san inda take jefa Kafarta ba, sunsa qafa cikin zauren gidan taji gabanta yayi wata mummunan faduwa, irin wadda kesa mutum ya yanke jiki ya fadi.
Suna shiga tsakar gidan suka yi karo da Inna Laure, wadda ke qoqarin hada hankalin gidan kasancewar duk ‘yan bikin sun watse tunda har isha ta karato ga shi kuma hadari ya gangamo a garin. Suna shiga tsakar gidan Inna Laure ta zabura ta mike tana fadar, “Me nake gani haka kuma ni-Laure, ba ku kai ta gidan nata bane k0 ya ya aka yi?”
Iyah ta ja hannun Inna Laure ta damqa mata Saudat.
“Ga amananku nan mun maido, yarinya mijinta yace ya mata saki uku saiku nemi dalili a wajensa, mu kuwa mun tafi Allah ya bamu alheri”.
Suka juya suka yi gaba abinsu.
Inna Laure ta hankade Saude dake
hannunta tana kwalla wa Malam Bala kira, wanda ke qoKarin fitowa daga dakinsa yana
zuba sallallami, kira yake“Me kunnena ke jiye min Laure?”
Inna Laure ta taBe baki.
“Abin da kaji Malam nima shi na ji”.
Malam Bala ya nufi Saude ya nuna ta, “Ke kuwa wannan yarinya banji dadin haihuwarki ba, uwarki ta haifa min jaraba da alaqaKai, kalu’inna lillahi wa”inna ilaihi raji’un, aiko yau sai kin bar gidanan na gaji ba zan iya ba wallahi na gaji. . .”
Saude ta fashe da wani dan marayan kuka na rashin sanin madafa, ta dora hannuwa biyu a kai, ta rasa abin dake mata dadi, tashin hankalin data gani Kiri-Kiri a idanuwan mahaifin nata shi yafi firgitar da ita, ta zuba wa Malam Bala ido wanda ke jin zuciyarsa tamkar zata tarwatse saboda tashin hankali, wasu irin hawaye masu zafi suka biyo kuncinsa, cikin tsananin takaici da bacin rai yace. ; “Ai dole ya sake ki Saude, don idan ba dan iska irinki ba babu namijin da zai iya zaman aure dake, amma ina so ki sani ni na riga na sauke nauyin da Ubangiji Ya dora min a kanki, don haka sai dai ki nemi inda zaki
amma ba dai gidana ba, yadda kika taho haka ‘zaki juya ki tafi duk gidan uban da zaki, kuma tsakanina dake Allah ya isa ban yafe miki ba” Saude ta ji kalamansa tamkar saukar . ruwan zafi a jikinta ta durkushe a gurin tana wani gunjin kuka. ‘ “ Malam Bala ya dube ta a fusace, “Eh ’zamama kikayi kenan kina kukan rashin kunya ko ai ko zaki bar gidan nan a nakashe”. Ya juya ya rarumo muciyar Inna Laure‘kafin tayi yinkuri ya muka mata a baya .Saude ta fasa wata uwar Kara ta sheme a qasa Malam Bala ya hau maka mata muciyar ‘ ‘ iya Karfinsa, ya hau fadar, “Ni za ki dauka dan iska? Ni zaki kawo wa shakiyanci a cikin gida? ‘
‘ Ganin yana shirin kisan kai yasa Inna Laure ta riqeshi, ta soma ba shi haquri, sai data yi da gaske sannan tasamuya ya. kyaletaya ta nufi dakinsa dashi yana sharar gumi, duk da kuwa ba ’
«lokacin zafi bane a lokacin. ~ , .
Saude kuwa ko kwakkwaran motsi ba tayi, saboda doguwar sumar da tayi. Haka duk suka shige ciki suka barta ayashe tsakar gida kamar ba dan mutum ba.
Tsawon lokaci wani irin iska mai hade da. guguwa yataso tare dasaukar wasu ruwan sama masu qarfi tsawon lokaci ruwan na dukan Saude kafin ta fara motsawa sannu a hankali ta bude idanuwanta a hankali abubuwan da suka faru suka rinka dawo mata tamkar bidiyo. Ta runtse idanuwanta da sauri tanajin tamkar zuciyarta zata tarwatse, ta yunqura ta mike da kyar wata irin tsanar
’mahaifin natane maitsanani tarinqaji zuciyarta batada wata bukatar data wuce barmasa akurkin gidansa dukda wani irin
masifaffen ciwon da jikinta ke mata amma
hakata takarkare ta fito daga gidan dukda
juwar dake faman rufe mata idanuwa. ga
kuma tsananin ruwan saman, ga-tafiyar tata tamkar: ta ‘yan kayo saboda tsamin da jikinta yayi Cantaji andanno mata oda abayanta da qarfin- gaske Saude taji har cikin dodon kunneta tamkar zai rabe biyu gashi kuma an
danne odar anki saki. Saude taji tamkar ta zuba da gudu saboda yadda ta kejin hatta ‘yan ‘ cikinta na amsa kuwwar odar sai dai ba qarfin jikin da zata iya yin gudun, don haka ta durkushe a gurin.
Cikin takaici Hamid ya Balle murfin motar ya leko da kansa cikin ruwan cike da masifa yana fadar, “Ke k0 wacce irin mace ce ‘ ana miki oda ba kiji, kawai ki zauna saman
hanya k0 aljana ce ke ai kin kauce daga saman hanya donvkar waniyazo ya takaki cikin rashin sani”.
Saukar muryarsa a dodon kunnen Saude ya sata saurin waiwayowa don tabbatar wa cikin wata rikitacciyar murya Hamid ya kira sunanta tare da zabura ya fito daga cikin motar ya nufo ta yana fadar, “Saude kece kuwa, ko dai gizo ki ke min?”
Ya durkusa a ‘gabanta, “Lafiya Saude me ya fito dake daga gidanku cikin wannan damunan?”
Cikin kuka Saude ta some fadar. “Sakina yayi Hamid, ya sake ni”.
Hamid ya dafe kai, “Innalillahi wa’inna ilaihirrajiun
Wayaji miki wannan ciwon a jiki haka? Dubi yadda jini ke zuba a jikinki”.‘ ‘ Sai a lokacin ma ta lura da wani irin kwasheshen ciwo da taji a gwiwar hannunta. . Hamid yace “Tashi maza mu tafi asibiti kada jininki ya Kare”. ‘
Ganin tana ta KaKaniyar tashi yasa ya sure ta da kuzarinsa ya sata a mota ya maida ya rufe, ya zagaya gidan direba ya shiga yaja, kai tsaye ya nufi medical center da ita.
Cikin .ikon Allah yana zuwa ya samu likita Dr. Mariya ta karBe ta aka wuce Emergency room da ita, abu kamar wasa sai da ‘ aka shafe fiye da awa guda Hamid na nan’ zaune babu wanda ya fito, tsoro ya cika masa zuciya tun yana addu’a a zuciya har ta fara fitowa fili. . .
Can cikin ikon Allah sai ga Dr. Mariya , ta fito,Hamid ya zabura ya miKe ya nufe ta yana fadar,“Lafiya dai k0 likita?” Dr: Mariya ta yi murmushi kafin tace
Ka kwantar da hankalinka Malam Hamid insha Allahu ‘yar uwarka zata samu sauKi ‘ amma yanzu ka biyo ni ofis akwai wasu yan ; tambayoyi dazan maka
Cikin karyayyar zuciya hamid ya amsa da, “To”. Sannan yabi ta ofis din
Sai data zagaya ta zauna ta cire gilashin fuskarta sannan ta nuna masa wurin zama, Hamid yaja kujera ya zauna yana kallon magidanciyar matar, wadda a qallah ba zata wuce shekaru arba‘in. Ba
Dr. Mariya ta gyara zamanta tare da tattaro duk wata nutsuwa, kafin tace “Malam Hamid don Allah akwai wasu ‘yan tambayoyi da nake so in maka, da fatan za kayi min. uzuri, ka kuma fada min gaskiya, amma fa kayi hakuri”.
Hamid ya qara tattara nutsuwarsa sosai yana kallonta, kafin yace “lnsha Allahu”
Doctor Mariya tayi wani murmushi kafin tace “Tona gode kwarai“.
Ta dan ja numfashi taci gaba da cewa, “Dama ba wata magana bace kan maganar ‘yar uwarka ce Saudat a katinta naga ka
. rubuta sunan unguwarku wadda ke cikin Dandagoro haka ne? ‘ Ya daga mata kai alamar eh
~ Ta girgiza kai, “To amma Hamid kace. Saude Kanwarka ce, don Allah kayi haquri ka
fada min gaskiya, ya kake da Saudat tsakaninka da Allah?”
Hamid ya dan zuba mata idanuwa yana mamakin tambayar tata, kafin lokaci guda ya sauke numfashi; “Duk cikin magarta babu wadda na fada miki ba daidai ba, Saudat Kanwata ce wani abu ne likita?”
Dr. Mariya ta koma ta jingina da bayan kujerarta cikin sanyin jiki ta girgiza masa kai alamar a’a kafin ta buda baki, “Saudat ta samu tsagewar qashi a hannunta na dama
sannan a qafarta ma ta goce, sannan akwai buguwa a qashin bayanta duk da dai buguwar
ba ta cossing din wata matsala ba, amma nayi . ‘
mamakin irin wannan manyan ciwuka haka a . jikin mace, kuma qaramar yarinya gashi kace ba hadari tayi ba, ba komai ba”.
Hamid yace “Wallahi ba hadari bane, duka ne kawai”.
Dr. Mariya taja wani tsaki-kafin tace “A gaskiya akwai marasa tausayi a duniya, yanzu ko dabba ai ba a yi mata irin wannan dukan ba”,
Ta qara jan wani siririn tsaki sannan ta ja dan siririn gilas dinta ta sanya a idonta, tare
da janyo biro tayi wasu rubuce-rubuce ta yage ta mika masa, ya sa hannu ya karBa tare da miqewa ya yi mata godiya ya fice. Dr. Mariya ta kwantar da kanta saman makarin kujerar tana kallonsa har ya fice daga ofis din nata. Hamid bai bar asibitin ba har garin Allah ya waye yana ta faman zurga-zurga siyo wannan auno wannan, karbo wancan har sai da aka kira assalatu sannan ya tafi masallaci ya yi sallah, a lokacin an daura mata karin ruwa, yana gama sallar ya dauki mota ya fice don hado mata‘ abin karyawa, sannan ya wuce gida, kai tsaye restaurants ya nufa yayo take away sannan ya fito ya siyi fruit da kayan tea da duk abin da yasan zata iya bukata sannan ya dawo asibitin a lokacin kuma ya iske Doctor nata nemanshi aka bashi wani list din abubuwan da zai siyo, kuma sai ya fita asibitin, Hamid ya sauke numfashi don yasan yana zuwa yanzu Dad dinsa ya gama Kuluwa don tun cikin daren jiya ya keta faman kiran wayarsa yana fada masa gashi nan gashi nan, daga qarshe ma saiya
kashe wayar gabadaya tabbas ya san kuwa sunada rigima a gidan yau.
Ya zura hannu cikin aljihunsa ya ciro wayoyin tare da kunna su sannan yayi gaba yana ta faman sauri kamar mai shirin “tashi sama, ba shi ya samu yayi saitin din komai ba sai wurin daya saura na rana, shima kuma yana kokarin tafiya Dr. Mariya ta tsayar dashi zata rubuta masu sallama.
Hamid dake zaune bakin gadon na Saudat yaji wani farin ciki ya kama shi, ya dafa gadon da Saude take zaune a kai, wadda ta sha ledojin ruwa biyu, tayi fayau kuma tana nan kamar an kulle biredi, muryarsa a sanyaye _ yace, “To yanzu idan aka sallame ki ina kike ’ ganin zan kaiki Saudat kafin in nemo mana mafita?”
Saude ta lumshe idanuwanta wanda .damuwa take cike fal a cikinsu, Hamid ya sake kiran sunanta, “Kiyi hakuri Saudat ki manta, insha Allahu lokaci yayi da zaki dandani zaqin rayuwa kema kin ji?”
‘ Saude ta bude idonta da kyar tana kallonsa, aka turo Kofar dakin aka shigo daga ita har shi suka zuba wa mai shigowar idanuwa, ba kowa bane sai mahaifin Hamid, fuskarsa ba yabo ba fallasa ya shigo ‘
Dr. Mariya na bayansa da takardu riqe a hannunta. Yana qarasowa tun kafin Hamid yayi wata magana ya cire hannu ya zabga masa wani mari wanda ya sashi saurin dafe kunci, Alhaji Bashir ya nuna shi da dan yatsa, ni zaka dauka mutumin banza ka nuna wa duniya ban isa da kai ba? Wato har wannan
‘ yarinyar ta fiye maka mu k0 Hamid?
Kai yanzu in bacin ma ba ka da zuciya har ka sake kallon yarinyar nan wadda ubanta ya nuna bai sonka, bai Kaunar tarayyarka da ita, amma shine kake like ka nace har kake bibiyarta da aure? To wallahi ba zaka zubar min da mutunci ba, cikiri satin nan zan daura ‘ maka aure da duk wadda tayimin tunda na lura auren ka keso, wuce muje mutumin banza kawai, na san babu abin da ke dibarka
~ sai wannan kyan fuskar”
. Hamid ya zaro ido tare juyawa baya, muryarsa a sarKake yace“Dad ka tafi zan zo don Allah ‘ka dubi halin da yarinyar nan take
. ciki, bata da kowa sai ni sai Allah idan na tafi ‘ na barta zata iya shiga kowane irin hali, don Allah Dad kayi haKuri ka bani awa daya”,
Alhaji Bashir ya zuba masa idanuwansa cike da mamaki, kafin yace, “Ka san kuwa abin da kake fada Hamid? Wato har wannan abin yafi ni kenan k0? Yanzu kai har kana da ~ hujjojin kare kanka idan iyayenta suka samu labari, yanzu har ka manta cin mutuncin da mahaifinta ya zoyayi mana har gida ke nan? To wallahi tallahi ka Kara minti biyar a nan ban yafe maka ba, mutumin banza kawai”.
Ya juya a fusace ya bar dakin, Dr. Mariya ta matso daf da Hamid muryarta a sanyaye tace“Hamid kayi .hakuri kabi mahaifinka kada fushin Allah ya tabbata a kanka”. ‘
Idon Hamid ya kawo Kwalla cikin sarqewar murya yace, “Doctor bata da kowa baiwar Allah ce idan na tafi na barta ban san halin da zata samu rayuwarta ba, na tabbatar tafiya in barta ita ce silar da rayuwarta‘ za ta salwanta”.
Dr. Mariya tasa hannu ta dafa kafadarsa tana fadar, “Kaje Hamid nayi maka
alqawarin rike Saudat a hannuna’ daga yau har zuwa lokacin da zaku daidaita da mahaifinka, nayi maka wannan alkawarin”.
_ Dadi ya kama Hamid ya soma zuba mata godiya, ya zaro wasu sauran kudin da suka rage masa ya mika mata, wadanda bai
san ko nawa bane. “Ga wannan don Allah ki fara rikewa a
hannunki kafin in dawo”. Dr. Mariya ta girgiza masa kai. “A’a, kai dai kawai kaje, ga Katina muyi magana”. Hamid ya karBa yana godiya, sannan ya zuba da gudu ya fice don tsoron cikar lokacin. Yana fita Dr. Mariya ta wuce ta nufi qofar, ta maida ta kulle sannan ta juyo ta dawo inda Saude take, wadda tunda mahaifin Hamid ya shigo ta lumshe idanuwanta tana maimaita innaIiIIahi saboda yadda ta kejin zuciyarta na barazanar tarwatsewa. Dr. Mariya ta dawo cikin dakin ta ja kujera ta ‘zauna tana fadar, “Bude idonki
kalle ni nan Saudat”.
Sosai Saudat ta bude idanuwanta wadanda sukayi jajawur tana kallonta, kafin tace, “Saudat waye mahaifinki?”
Saude taji tamkar ta caka mata wuqa a kirji cikin dusasshiyar muryarta tace Malam bala. . Dr. Mariya tace, “Mahaifiyarki fa?” Saude ta danyi shiru tamkar ba zatayi magana ba, kafin ta bude baki cikin muryar kuka,tace “Ban santa ba, banma taba ganinta ba tunda na tashi na ganni da Yayana Rabi’u da matar mahaifina Inna Laure, tunda na tashi ban san dadin uwa ba, ban san wani ‘ gata ba wanda da ke samu wurin mahaifansa ba saboda ni. . .” .
Saude ta saurara daga bayanin da take saboda hawayen data gani suna zubowa daga idanuwan matar, idanuwan Saude suka yo warwaje muryarta a sarqaqe ta soma fadar, “Lafiya dai Doctor, me ya faru?”
Dr. Mari’ya ta riko hannunta gam ta rike tana motsowa cikin kuka tace; “Saudat nice mahaifiyarku, nina haife ku da cikina tun… ” ‘
Kuka yaci qarfunta ta soma wani kuka
mai cin zuciya.
Saude kuwa dif ta tsaya da kukan nata tana kallon matar muryarta na sarkewa tace “Kece mahaifiyarmu? Idan kece
‘ mahaifiyarmu me ya sa kika tafi ki ka barmu? Me yasa baki sake waiwayarmuba kika manta damu kika watsar da rayuwarmu kika wofintar damu, kika bari aka tarwatsa mu, muka sha wahala muka rasa mataimaki a duniya, kowa ya tsane mun . Dr. Mariya tayi saurin rufe mata baki cikin kuka tana fadar, “Ya isa! Ya isa haka Saudat wallahi ban barku ba sai don hakan shi ne mafita, ban watsar da kuba sai don ina jiye muku tsoron wahalar da zaku iya fuskanta ne idan nace zan tafi daku alhalin nima ban san inda zan nufa ba, kuyi hakuri Saudat ina .yayanki?” ‘ Saude ta runtse idanuwanta wasu hawaye suka ziraro mata, cikin kuka tace
“Sun raba mu tun shekarun da suka wuce Baba ya kore shi ban sake ganinsa ba, ban san halin
da yake ciki ba. Nan ta labarta mata labarin rayuwarsu
tun farko har izuwa yau.
‘ Dr. Mariya kuka ta ke sosai ta rungume Saudat a jikinta suna jin dumin juna, soyayya tsakanin uwa da da ta rinka shigarsu tsawon lokaci kafin. su saki juna, Dr. Mariya tace,
“Taso muje gida Saudat ki huta in baki tarihin .mahaifinku da irin taskun da na shiga a lokacin aurena dashi”. -. . Ta riqo Saudat ta taimaka mata ta miqe, ta dauki makullin motarta suka fita har zuwa
harabar asibitin inda aka tanada don ajiye motoci.
Hmmm to Saude dai ta hadu da mahaifiyarta Mu tara gobe daidai wannan lokacin donjin yaddah rayuwar Dr Maria da malam bala ya kasance abaya zamanin aurensu
*ABDULLAHI ISMAIL SALANKE*
KE cewa GOBEMAAA da LABARIII