YAR ZINA CE CHAPTER A

 YAR ZINA CE CHAPTER A

*Y’ER ZINA CE*

      _(kaddarar iyayena)_

*MUNEERA*

Wattpad 👉🏻 fatimamuneera001

Alhamdullilah masoyana fatan Anyi sallah Allah maimaita mana badin dadad😄

*KIRKIRARAN LABARI NE DA NA ZAUNA NAI NAZARIN SA BANYIN SHI DAN CIN ZARAFIN KOWA BA IN KA/KI JI YAYI DAI DAI RAYUWAR KA/KA AKASI AKA SAMU*

Pg~1

Wata hadadiyar mota ce tayi parking a bakin makarantar secondary school din wace taja hankalin jama’a dake wurin da dama  sun zubawa motar ido domim ganin wanda ze fito daga cikin ta, seda yaja wasu yan mintina kafin ya sako kafar shi waje wanda specticle a idon shi wanda in mutum ua shiga rana se lense din ya canja launin kala kalon shi nayi da kyau yayinda naga kayan dake jikinsa kayan NYSC ne sunmasa kyau sosai wanda suka saje da launin fatar jikin sa, sakin baki mutanen wurin sukai suna kallonshi dan duk garin basu taba ganin me kyau haka ba duk da cewa ana turo musu irin waanan masu zuwa bautar kasa garin amma wanan nashi salon daban yake Se yamutsa fuska yake kasancewar lokaci na damuna anyi ruwa duk ya kwnta a cikin kasa cikin makarantar ya shiga kai tsaye wurin shugaban daliban (head master ) ya wuce domin gabatar da kanshi ya samu tarba me kyau a wurin shugaban daliban kafin a nuna masa masaukinshi yaji dadi kwrai dan yanzu ze samu ya huta domin kuwa ya gaji wanan gari badai nisa ba yasha tafiya Allah dai ya temake shi 3wks zeyi ya koma garin su wayar shi dake gefe ce ta hau ruri da sauri ya mika hannu ya dauka domin ganin sunan wace take kira din

   “mom ya furta cikin shagw’ba kamar wani karamin yaro Autana ka sauka ne, ta fada daga can bangaran muryarta dayaji yasashi jin sanyi a ranshi sanan yadan yamutsa fuska hadi da fadij Alhamdullilah mom na sauka lafiya sedai akwai gajiya gaskiya, toh autana Allah huta gajiya, Ameen mom ta katse wayar kayan jikinshi ya rarage kafin yaji ana kwnkwsa kofar dan karamin gidan karasawa yayi ya bude ba tare da ya kali wanda ya kwnkwsa ba ita ma ganin haka seya sa ta sakai cikin gidan, jiyowa yayi da niyyar tambayata lafiya Amma kyaun yarinya yasashi tsayawa yana kallon ta ba tare da yace komi ba gajiya datai da tsugunuu yasata cewa

    “yallabai fura ce shugaban dalibai (head master)yace akawo maka se lokacin ya dawo  daga duniya tunanin daya fada yace mene me kika ce kara maimata mishi tayi a karo na barkatai, da taga bashi da niyyar bata amsa se ta ajiye masa ta juya shi kuma yabi mazaunan ta da ido, ji yayi wata muguwar sha’awa ta kamashi dan haka dakyar ya dauki furar ya koma daki yana mukususu.

+

      Yau ta kama monday, da wuri ya shirya ya nufi cikin makarantar inda yaga tarin dalibai suna ta faman shiga makarantar wanda yawancin ajujuwan ba kujerun zama na dalibai( benches)  a kasa suke zauna wata iska ya furxar yana fadin *KASATA* kenan SS3 ya shiga domin su kadai ze dauka ya gabatar musu da kanshi inda wasu keta kokarin kulashi Amma ba fuska jiyowar da zeye suka hada ido da yarinyar nan ta jiya data kai masa fura ji yayi wani zirr ajikin sa Hada ido sukai a tare tai saurin janye nata idon dan ita a Rayuwarta ta tsani kallo dan karamin tsaki taja wanda duka yan ajin sunji ta waiwayowa yayi tare da fadin *SAKINA* ce sedai ya maimaita sunan kafin yace ki same ni a office yanzu tuni cikin ta ya duri ruwa dan a duniyar nan in akwai abinda ta tsana shine a taba lafiyar jikin ta yana fita tabi bayanshi har office din.

    sakina ya ambaci sunan ta cikin wata irin murya, dagowa tayi ta kale shi fuska cikeda tsoro shi dariya ma ta bashi, tambayoyi ya fara mata tana bashi amsa har ta saki jiki dashi lokaci guda har sun saba dama sakinah akwai saurin sabo dariya suke sosai a zuciyarta taji lalai malamin nan ya shiga ranta sosai, tsayar da dariya tayi tana cewa

   “wani abin sokwnci har yanzu bansan sunan ka ba fa dariya yayi yace mata wato baki ji bakenan lokacin danake fada muku a class, murmushi kawai tayi sanan yace sunana *HASHIM* nice name ta fada tana jujuya ido kafin ya sallame ta takoma class(aji) ranar da takoma gida har kakata seda ta gane yau sakinah tana farin ciki abinci ta dauka zata fita kaka ta tambayeta ina zuwa jiyowa tayi tace zata kaiwa malamin su ne da yaxo bautar kasa girgida kaii kawai kakar tayi ita kuma ta fice da taje daga shi se dan gajeran wando a jikin shi ko vest babu haka ta shiga shi kuma ya tura kofar ya rufe malama sakina kece kenan eh malam ga abinci noke kafada yayi yana fadin nidai baxanci ba 😳zaro manyan idanuwanta waje tayi tana tambayar shi dalili nidai seda in zaki bani a baki bata musa ba ta daurayo hanun ta ta dibi abincin ta mika mishi bakinshi wani shock sukaji duka su biyun a lokaci guda janye hanunta tayi ta dago ido tana kallon shi a kasale hanunsa yakai kan boobs dinta yana dan shafawa ita kuma batai yunkurin hanashi ba seda ta kali wandon shi taga🍌 ta mike hanun ta takai wurin tadan taba Ashh ya yafada yana cewa cigaba sakina. 🤦🏻‍♀wa’iya zubillah haka sukaita romance dinsu suna tababe har suka samu nutsuwa sanan ta tashi zata tafi sukaima toh sir ni zan tafi ta fada tana wani juya ido toh babyna se yaushe ya fada yana shafo mazaunanta seda dare ta bashi amsa, yace sena ganki.

*👉🏻me kuke gani ze faru tsakanin sakina da hashim, anya sunyiwa kansu adalci kuwa*

👉🏻👉🏻comment dinku shi ze bani karfin gwaiwar yin Typing

Fatiman ku ce*Y’ER ZINA CE*

         _(kaddarar iyayena)_

*muneera*

wattpad👉🏻fatimamuneera001

Pg~2

Tunda sakina ta fita kaka ta mike ta fara kokarin dora musu abincin da zasu da dare shuru-Shuru taji sakina bata dawo ba tana wanan tunanin ne taji sallama sakina a jiyar zuciya ta sauke kafin kakar ta fara yiwa sakina kallon tsaf kamar tana nazarin wani abu, kakalo murmushi sakina tayi tace kaka yadai, kuma zuba mata ido tayi tana kara nazarin ta.

   Sakina ya akai kika jima haka, seda ta danyi shiru sanan tace da baje baya nan seda na jira ya dawo kakata kije ki zauna nizan cigaba da girkin komawa tayi ta zauna kamar yarda sakina tace Kafin wani dan lokaci tuni Sakina ta gama girkin tana saumewa ta shige bayan gida domin yin wanka da dauro alwala ta fito a lokacin iskar La’asar har tasa kaka yin bacci har sakina ta iddar da sallah

Kaka na kwnce dan haka seta lalaba tare da daukar abincin sir hashim tai gidan a bude gidan yake dan haka kawai seta sa kai dakin nasa ta shiga kwnce ta ganshi da waya a hannu yana wayar yana lumshe ido da Alama dai yana jin dadin wayar katse wayar yayi yana fadin malama sakina sannu da zuwa Amsa masa tayi kafin ta ajiye kwnon tana cewa mlm hashim inason insan waye kai pls kallon ta yayi da murmushi sanan ya fara magana kamar haka

    “sunana dai hashim da daya tilo a wurin iyayen shi asalin mu daga mamana har babana yan kano wato haifafun kano ni kadai Allah basu daga kaina kuma basu kara samun haihuwa ba dan haka banida kanwa koo kani na taso cikin kadaici da sha’awar dama inada yan uwa musaaman ina shiga dangi naga kowa da dan uwanshi babana ma’aikacin gomnati ne mamana kuma likitace toh kinji takaitacen tarinhi na” ya fada yana sauke numfashi sanan yace ke kumafa ‘Dan murmusawa tayi kafin tace malam

    ” ni sunan sakina  Muhammad iyayena y’an asalin nan madubi ne babana fatauci yake sunyi auren soyaya kafin mamana ta samu cikina wurin haihuwata Allah ya mata rasuwa lokacin da babana labarin mutuwar mahaifiyata yaje masa shima zuciyar ta buga ya rasu  yanzu ina wurin kakata ne a zaune  a wurinta na taso komi ita take min harda ma bokon nan ita tasani duk da cewa yawancin mutanen kauyen nan basa barin yaransu suyi karatu Amma ni kakata ta sani saboda tana da burin taga nazama likita”

     “sakina” hashim ya kira sunan ta “a shirye nake na aure ki kuma a shirye nake na kalubalanci ko wace matsala akanki  murmushi tayi ta dan sukuyar da kanta tana mai jin dadin cewa yanzu kamar hashim dan gayu dan birni irinshi ze auri y’ar kauye irinta anya ba yodurar ta ze ba. Kamar yasan metake tunani yace ki cire tantama sakina bazan yodare ki ba auren ki nake son yi mu rayu tare mu kuma mutu tare tun lokacin da na ganki sakina naji ina son ki so bana wasa ba ki yarda dani bazan cutar dake ba” numfasawa tayi tana kallon kwyar idon shi tsantsar gaskiya ya hango ta cikin idon shi duk da har yanzu tana tantama zuciyarta bata gasgata abinda ya fada ba din “Sakina  inaso zanje wurin kakarki mugaisa” dago kai tayi suka hada ido sanan tace toh a sanyaye jiki ba kwri dan se yanzu ta gasgata kalaman sa da taji ya ambaci zeje wurin kakar dan girgida kai kawai tayi sanan  Tamasa sallama ta koma gida

    “sakina kaka ta fada cikin tsawa nagaji da fice-ficen nan naki kinji koo bana son shashanci da rashin kamun kai ki nutsu na fada miki” zunbura baki tayi “ai dama nasan basona kike ba ke kullum se kinyiwa mutum fada gaskiya ni kaka bana so ta fada” tana buga ‘kafaa “Sakina ai mutumin da ake masa fada dan gata ne ba kadan ba wallahi saboda a wanan zamanin wasu ma suna nan suna neman masuyi musu fadan amma basuda shi ke kuwa da ake miki har kike wanan iya shegen ki sani sakina baki da uwa bakida uba se ni nima kuma so kike na fadi na mutu ki huta shikenan ai zunbura baki tayi tana shigewa daki domin ita a ganinta kaka ta fiye masifa

+

_______________________

Shiryayen bikin hashim momy ketayi gidan duk ya taru da jama’a dan befi saura sati 3 a daura aure ba yana dawowa kenan zasu fara shagalin bikin yan uwa na nesa duk sun fara zuwa yayinda zakadidyar amaryar tashi domin kuwa auren zuminci zaa musu yar kanwarta ce sedai fuskarta ba walwala sanadiyar tunda hashim yaje garin can baya daga kiranta sosai a ranta kawai taji anya ba garin zata bishi ba(🙄nida ke gefe nace kyje ki ganowa kanki bakin ciki😂domin yana can yana holewarshi da sakina yar fulani) 

    Ana sallama da sakina yaron ya fada kaka seda taji gaban ta ya fadi tace wai injiwa ,yaron yace inji wanan dan gayun da yazo…. Kaka tace kace ya shigo ciki……….

Fatiman ku ce👌🏻*Y’ER ZINA CE*

       _(kaddarar iyayena)_

_Akwai wace takira ni jiya tana fadamin kan cewa sunan littafin be dace ba harda wanda suka min magana ta grp da pc toh gaskiya a yarda na tsara labarina haka naga sunan ya dace nasa👌🏻nayi yunkurin sa sunaye da dama amma an riga anyi toh bnson kanan maganganu naga haka ya dace da sunan bawai ban amshi gyra ba Aa haka sunan littafin yakamata_

*WANAN PAGE DIN SADAUKARWA NE GARE KI MY RAHEEMA ALLAH BAMU SA’AR EXAMS*

*TUKUICI GAREKI MY HABIBTY UMMI ONTOP*

Pg~3

koda yaron ya dawo ya sanarwa hashim haka be kawo komiba ya shiga tabarma kaka ta shimfida masa ya zauna cikin girmama juna suka gaisa sanan hashim yace

   “gaskiya kaka da gaske auren sakina zanyi domin tunda naganta naji na samu matar aure inaso ne ki lazimce min zan dinga zuwa tadi wirin ta bada wasa nazo ba inaso ina komawa zan turo iyayena ai maganar aure” kaka dan numfasawa tayi sanan tace “bana sone na yarda dakai kazo ka cutar min da sakina ta domin bana fatan abinda zai cutar da ita inaso ne tayi rayuwar me dadi wanda ko bayan ba raina bazatayi kukan rashi ba”

   “insha Allah bazan cutar da ita ba zan riketa da amana abinda kawai nake so dake kaka shine *KU YARDA DANI*  bazan cutar da ku ba “

    Duk abinda suke sakina na daki tana jinsu a zuciyarta seta ji ta kuma yarda da hashim 100% wayaga ita sakina ta auri hashim dan birni dan gayu ita bata damu da koo shi me kudi ne ba ko talaka *KADDARAR SO* (miss xerks) ne yasata fara son shi tafarar daya a kwna biyun nan sa sukai taji  kamar shekara biyu sukai  tare Hashim da ze tafi ya ajiyewa kaka raper din yan naira 200 amma taki karba da zolaya da janta da wasa irin na jikoki ya ajiye mata ya fice+

———————-__________________

momy ce ta shigo dakin da zainab take ta rafka uban tagumi tana tunanin meyasa yaya hashim baya kiranta kuma inta kirashi baya dagawa se lokaci-lokaci tabbas akwai abinda ke faruwa ta fada duniyar tunani sosai firgigit ta dawo daga tunanin data tafi momy tace *zainab* lafiya kuwa meke damun ki kuka tasa tana fadawa jikin momyn “yaya hashim ne” meya faru da shi din ” momy baya kirana kuma koo na kirashi seya ga dama yake amsawa kama hanun zainab ta zaubar da ita a gefe gado sanan cikin nutsuwa da tsantsar ilimi daya ratsa momyn take fadin”haba zainabu abu me tagwyen suna yanxu kan wanan kike kuka karki manta kefa mace ce me class akan namiji zaki kuka hakuri zakiyi yanzu haka aiki ne ya masa yawa kinji karki damu kanki kinji autana (dake zainab Yarinyar kanwar momy ce babar hashim momy ce ta riketa tun yaye sun shaku da hashim sosai daga baya iyayen su suka hada auren su gani shakuwar tasu tayi yawa) ta ji dai maganar momy amm bawai zatai amfani da maganar bane

..

“””””””””””””””””””””””””””””””””””””””””””’

Bayan sati guda soyaya me karfi da shakuwa tashiga tsakanin Sakina da hashim da sakina da har sakina take jin zata iya bawa hashim duk abinda yakeso indai daga gareta ne kullum hashim cikin zafafan kalamai yakewa sakina da tabbatar mata da baze taba yodarar ta ba yau sakina ta shirya zata kaimasa abinci kaka tace karta jima tace toh Gidan hashim ta nufa ta kwnkwsa kofa ya bude sanan ya tura kofar suka koma daki ya kwnta idoj shi yayi jajir jikin shi ya dau zafi sakina tace bakada lafiya ne kai kawai ya daga mata zame hijab din ta tayi ta karasa kusa dashi tanajin hucin zafin jikin nasa a hankali takai hanun ta kan wuyanshi zafi taji tace ynzu me zan maka niko ka samu sauki , kinada abinda zaki min sakina tace menene shi matso nan ta matsa seya rungumota kirjin su na gugar juna tace sir abin ranar nan daga mata kai yayi kafi yakai hanun shi kan boobs din masu laushi yana murzawa ita kuma har ta fara sunbatu ganin haka yasashi yin murmushi kafin yaja hanunta zuwa kan🍌 dinshi murza masa ta fara yi gaba daya suka dinga ihuu da sumbatu ita dashi kafin sakina ta farga da aika aika da hashim yake shirinyi domin kuwa idonshi ya rufe bai ji bai gani neman fadawa babar harka kawai yakeyi🙊 wata kwla me zafi sakina ta futar yayinda taji hashim ya shigeta ga wani radadi da ta faraji se yanzu ta gano wautar da tayi Shima se lokacin ya samu nutsuwa sanan ya fara rarashin sakina datake faman kuka lalabata yayi da kuma tabbatar mata ai aure zasuyi karta sa komai a ranta jin kalaman sa yasata jin sanyi a ranta da tuna ai aure zasuyi sanan ta mike taja kayanta tasa sedai da kyar take tafiya hakan yasa hashim zura doguwar rigar shi yace suje yakaita a mota har kofar gida ya ajiye ta sukai sallama ta shiga Allah ya temaketa kaka bata nan taje makota dan haka da sauri ta hada ruwa me dumi ta fada toilet danyin wanka seda ta gasa jikin ta sosai sanan ta fito ta shirya ta kwnta a tsakar gidan nasu domin zazabi takeji…….

Bacci ne mai nauyi ya dauketa har kaka tazo ta tarar da ita a wurin bata tashe ta ba saboda ganin  yarda take jin dadin baccin seda tayi me isarta sanan ta tashi tana dan dinshi tai kokarin shiga bayan gida kaka dake zaune tana kallon yanayin tafiyar jikar tata tace”sakina wace irin tafiya ce wanan kikeyi haka” gaban ta ne ya fadi zuciyar ta ta fara bugawa da sauri ji tayi tana kokarin fada da numfashin ta saboda kaka ta mata tambayar bazata, ba tare da ta jiyo ba tace tuntube nayi na fadi inaga ma targade nayi anjima zanje wurin me gyra a dubamin  “kakar kamar tana nazarin wani abu tace toh Allah ya bada lafiya Ameen ta fada kafin tai sauri ta shige bayan gidan tana sauke ajiyar zuciya.

……………………………………

Toh zan iya cewa sakina ta zama matar hashim ba tareda an daura aure ba kullum seta je sun sheka ayarsu ta dawo sedai kash sati ukun da hashim zeyi ya cika

    “sakina wanan alkawari nane ina zuwa zan turo iyayena ayi maganar aure baki san irin son da nake miki bane sakina ina  komawa zaa kawo kayan gaisuwa soo pls stop crying” dan tsagaitawa tayi da kukan tayi da kukan tana kallon hashim nan suka tsirawa juna ido kudi ya zaro yan 1k rapa guda biyu ya danka mata yana fadin ki boye kan nadawo karki nunawa kaka kinji gyda masa kai tayi shi kuma yana shigewa motar shi suna dagawa juna hannu hashim har kurewa ganin sakina bata bar wurin ba Tana kallon shi……

*KUNA GANIN HASHIM ZE DAWO GA SAKINA KAMAR YARDA YA FADA A GANIN KU ZE AURE TA KAMAR YARDA ITA TA YARDA ANYA SAKINA BATAJ WAUTA BA, KARKU MANTA BATA SAN HASHIM BA FA BATA SAN IYAYEN SA BATASAN UNGUWAR SU BA GARIN SU KAWAI YA FADA MATA*2

Hausawa sukace wasa farin girki yanzu labarin ya fara

Fatiman kuce👌🏻*Y’ER ZINA CE*

       _(kaddarar iyayena)_

*muneera*

Pg~4

Dawowa tayi ta samu kaka na dama fura karba tayi tana damawa se yamutsa fuska take saboda bata son karnin nonon daya gwraya da kamshin furar Tana gamawa ta mikawa kakar ta mike jikin ta ba kwri seta bar hakan a cewarta duk kewar hashim ne banda tunanin sa ba abinda take gaba daya ranar tunanin hashim ta wuni tanayi tana tunanin lokotan da sukai tare a hakan tunanin labaran saurayin ta daya tafi kano neman kudi dan ita tunda suka hadu da hashim ta manta dashi dukda cewa shima labaran suna dan iskancin su dashi sedai bata taba bari yakai ga yarda hashim yakai ba dan duk lokacin da labaran yazo a soro in sun tsaya ta kan bashi boobs din ta ya tsotsa yayi wasa dasu sedai batai sakacin datai kamat na hashim ba

——————————————-

Tunda hashim ya kira gida yasanar musu cewa yana hanya aketa shiryayen tarbar shi dama ga gidan ya cika da jama’a dan kuwa gobe ake shirin fara shagalin biki Momy da zainab na gama shirya masa komi a part dinsa sukaji kakani daga can waje nata tsokanar sa shi kuma yana tamke fuska ya shige part din nasa zainab ya gani tsaye bakin ta har kunne hakora sun kasa rufuwa murmushi kawai take masa shima dan murmusawa yayi ya kane mata ido rufe fuskar ta tai da tafin hannu ta masa nuni da kujerar da momy ke zaune wace be lura da cewar tana wurin ba da sauri ya karasa yana sosa keya yake fadin momy na nayj kewar ki da yawa ja masa kune tayi kafin tace momyn xa ba’a kula da ita ba mata ta rufe ma ido daga shi har Zainab seda sukaji kunya ya mike domin shiga dakin sa yana fadin wane ita ai ke nafara gani momy na fita sukai zainab da momyn domin cigaba da tarbar ba’ki da suketa shigowa momy nayin gaba zainab tace tayi mantuwa zata dauko dawowarta yao dai-dai da fitowar hashim daga dakin nashi wurin dining ya nufa yana fadin “Amarya yar shagalu” Ango kasha kamshi meka taho min dashi tsaraba dan naga kauyen ya karbe ka ka yi fresh dakai ” hmm kawai yace kafin yaksi lomar abincin bakinsa Sunyi hirar yaushe gamo kafin a kira sallah magrib ta tashi tayi cikin gida shi kuma yayi alwala ya wuce masalaci

+

Yau ta kama laraba yau ranar kawayen Amarya da abokan ango ce wato Friends day karfe 8:00 dai-dai zainab ta fito domin shiga motar da aka tanadar musu ita da angon ta hashim Bawani taro bane dan daga kawayen Amarya 10 se abokan ango 10 anci ansha an yi farin ciki

________________

Me zan gani sakina ciki kaka ta fada tana matse kwla ciki ni hafsatu na shiga uku sakina ki rasa dame zaki saka min se wanan sakina ta marasa fada tana mai nuna cikin sakina wace sakina ke durkeshe ba abinda take se rusa Uban kuka take sarkewa numfashin kaka ya fara kokarin taro shi take amma ina kuka take tana nishi da kyar

—-*—–**-*———-

.Farin ciki anyi shi hashim kuwa se rawar kai yake na zeyi sabuwar amarya dan  ya dade yana tsare zainab baya bari tun tana yarinya wani ya kula ta sun dade suna rainon soyayarsu

..

Ki fada min sakina waya miki ciki meya rude ki dashi ya miki ciki iya kokarina akan ki inayi sakina sakayar da zaki min kenan

Muje zuwa

Fatiman ku ce👌🏻[6/30, 11:11 PM] mai tuwo🍚: *Y’ER ZINA CE*

     _(kaddarar iyayena)_

*muneera*

Pg~5

Kuka ta cigaba dayi kawai tana mai girgida kai bakin ta kuwa se rawa yake tana fitar da iska me huci jin kaka ta janyo ta, tana kuma girgiza ta lokaci daya sakina ki fada min girgida kai tayi tana fadin bansani ba ban sanshi ba….. Tasss taji saukar mari a fuskar ta a ruwa kika sha kenan wallahi ki fada min tun kafin Audu ya dawo garin nan (yayan babar sakina daya tafi cirani lagos wanda shi yake kula dasu) zare ido tayi wani hawayen na zirarowa daga idon ta jin an ambachi sunan kawu Audu sakin ta kaka tayi ta koma gefe itama ta cure wuri guda tana kukan, duka su biyun kuka suke bame rarashin daya a cikin su kaka ta kuma dagowa tana

    “na zauna da uwarki lafiya harta rasu bata taba bata min ba sakina mahaifiyar ki mutuniyar kirki haka ma mahaifin ki mutanen arziki Allah yasa bazasuga wanan bakin cikin Ba Allah yasani shiyasa ya dauke su tun kan suga wanan abin kunyar sakina kin cuci kanki kin cuci iyayen ki kuma kin cuce ni sakina bazan tsine miki saboda nasan tsinuwata zata biki Amma….” se kuma tayi shiru tana goge kwla da ta kuma taho mata da bakin zani d’aki ta shige taba

+

Yau ta kama kamu daga can na hango Amarya da ango cikin yan uwa sunata yin hotuna kiran waya ne ya shigo wayar hashim ya dan matsa gefe yana dagawa kafin muryar wace yaji ne yasashi saurin kara shigewa bayan gidan su yana zare ido “hashim sakina ta fada daga can bangaren hashim yaushe zaka dawo kazo muyi aure” wani wawan tsaki yaja kafin yace “kee wace irin wawiya ce wace irin jaka ce kee iyee babza y’ar kauye ma irin ki wace bata san kanta ba toh ni bari na fada miki ma karki kara kirana domin gobe ne daurin aurena da wace nake so in kuma kika sake kika kara kirana na lahira ma seya fi ki jin dadi Sanan daga karshe Allah ya wadarai ma na aure mata irin ki da nagama sanin ki a waje in munyi auren me zaki nuna min me zan gani wanda ban gani ba bakida abinda zaki bani ma in munyi auren shashasha mtweee”

Yana gama fadin haka ya  kashe wayar yana kuma jan wani uban tsaki

Ajiye wayar tayi wace ta siya kaka bata sani ba da kudin da hashim ya bata se yanzu nadama da nasani da kuma tausayin kanta yazo mata sedai me jin sallamar da ake a tsakar gidan nasu ya sa gabanta faduwa tana dafe kirji domin kuwa muryar kawu audu taji awaje kaka na masa sannu da zuwa gabanta ne ya kuma faduwa dukan cikin nata tana fadin hashim ya cuceta can ta jiyo muryar kaka na kiran ta jiki a sukwne ta fito Hada ido sukai da kawu audu da sauri tai kasa da idonta kirjin ta na dukan 3-3 murmushi yayi yace kaka yanaga mituniyar taki yau a tsorace kaka wani murmushi tayi na gefen baki sanan tace “ciki ne da ita ai” Hajiyakaka (dake kaka ya bita tun da sakina ta sa mata kowa yake kiranta da kaka) nima wasan jika zaki mata a gabana ba wasa audu ta fada kwla na fitowa daga idonta audu ai sakina ta cuci zuri’ar mu wanan yasa idon kawu ya kuma fara sauya kala yana me tambayar kaka waya mata gata nan ai kai seta fada maka wanda ya mata tunda ni ta raina ni bata fada min audu ya kali sakina , sakina ya fada muryar ba wasa yace sakina waya miki ciki? ” bansan shi ba kawu”  tass taji mari dan uwar ki toh a ruwa kika sha ya zare belt din dake jikin sa yana tafka mata Aa kayi hakuri wayoo na shiga uku zai kashe ni kaka ki temake ni wayoo ni kaka ze kashi kawai take maimaitawa shi kuma dukan ta kawai yake yana fadin waya mata ihuu tasaa tana da karfi tace ” hashim ne” tsayawa yayi da dukan yana kallon kaka Alamar tambyar waye hashim innallilah kaka ta furta tana toshe bakin ta

fatiman ku ce👌🏻

[7/2, 1:13 PM] mai tuwo🍚: *Y’ER ZINA CE*

      _(kaddarar iyayena)_

*MUNEERA*

*DEDICATED TO*

*Suwaiba Ibrahim(mama)*

*fatima Ibrahim(Anty teema)*

*saudat ibrahim*

*hauwa Ibrahim*

*INASON KU YAN UWANA😘ALLAH BAR KAUNA TSAKANIN MU*

Pg~6

Waye hashim kaka, Alama tayi masa kan cewar su zauna yana hakki da numfarfashi ya koma kan tabarma ya zauna ya kali kaka yace”waye hashim?” numfasawa kaka tayi ta kwshe gaba daya labarin hashim tundaga zuwa garin da yayi har lokacin da head master ya aiko siyan fura sakina ta kaimasa har zuwa kan kai masa abinci da sakina ke zuwa yi da kuma zuwan da yayi ya gabatar da kansa wurin kakar jinjina kai kawai audu yake “kaka ke kika taka muhimiyar rawa a wanan abu da ya faru kin fi sakina lefi kaka meyasa zaki yarda yarinya budurwa kamar sakina ta dinga kaiwa wani abinci haba kaka wanan sakacin yayi yawa musamman yarda zamanin nan ya zama yin *ZINA* ya zama *RUWAN DARE* (ummi ontop) a zamanin nan da har sakina zatai kai masa abinci, kai abincin ma ba cikin bainar jama’a  ba Aa har cikin gidan sa kaka kinyi sakaci wallahi”

Tabbas *NAGA SAKAMAKO*(ummu nabil)  ni a ganina sakina bazata taba aikata zinna ba se gashi wai yau sakina ce zata haifa min *Y’ER ZINA KO DAN ZINA* a cikin gida yarana basu yi min haka ba se jika ni hafsatu *NAGA TAKAINA*(muneera) tabbas nayi kuskuren da bazan iya gyrashi ba audu yanzu meya kamata muyi Bayarda zamuyi kaka sedai hakuri kuma cikin nan seta haifeshi dan bazamuyi kisa ba ya zama mun aikata lefi biyu Ni kuma zan duba hashim din duk inda yake a garin nan

___________________

Yau ta kama daurin aure wanda yasa jikin zainab yin sanyi domin bata san me zata cewa hashim ba in yasan halin da take ciki dafe kanta tayi kafin ta fashe da kuka tana tunano lokacin da kabir yayi mata fyd’e kuka ta kuma fashewa dashi lokacin da momy tace kar a fadawa hashim zaa gyra ta baze gane ba ya salam ra furta tana kuma fashewa da kuka dakin aka kwnkwsa da karfi a hankali ta goge hawayen idonta kana taje ta bude kofar momy ce ta shigo tana kallon ta tare da nazarin sana tace”kukan me kikeyi” wani kukan ta fashe dashi tana mai fada wa jikin momyn tana kiran sunan ta momy bansan ya zanyi ba in yaya hashim ya gane momyn da ta dan figita da tuno abinda kabir ya mata(kabir dan kanin baban hashim ne ya lalami zainab ta soshi taki toh se ya yi mata fyde ya kuma gudu ya bar garin) karki damu zainabu abu ba abinda ze faru kinji ki kwntar da hankalin ki kuma koo hashim ya sani bayar da zeyi domin ke din yar uwarshi saboda haka ki kwntar da hankalin sedai abinda zan fada miki shine zainab “ki zama me biyaya me da’a me girmama shi me bashi kulawa yarda koda ya gane indai zaki dinga masa haka zesa ya manta da wancen ki zama me tsafta ta jikin ki da ta gidan ki, ki kula da girkin ki wato ki kula da kichen dinki ki kula da lokacin da zaki masa magana misali ki kula lokacin da yake nishadi kema seki taya shi nishadin ki kula da lokacin daya shigo rai a bace se ki kokari ki kwntar masa da hankali, banda daurin kirji banda yawo ba takalmi banda yawo ka ba dankwli ki kula da dakin mijin ki dakin miji wato turaka sirri ce karki ce kowa yazo zaki dauke shi ki shiga dashi dakin mijin ki domin sirrin ki ne sanan uwa uba ki rike sirrin mijin ki saga ke se zuciyar ki karki fadawa kowa sirrin mijin ki ki barshi a zuciyar ki sanan banda yawan kawo kara domin zaki sa yan uwanki su tsani mijin ki in ya miki lefi kiyi yajin ki a cikin gidan ki wanan itace nasihata gareki”

Kuka zainab ta fashe dashi momy ta rungometa tana bubiga bayanta sanan tace toh maza ki shiga wanka ki fito yan uwa

An daura auren hashim da zainab hashim baki yaki rufuwa se washewa yakeyi bakinsa har kunne ana mimika masa hannu suna gaisawa da jama’a masu busa kuwa na tayi hashim se raba musu kud’i yakeyi

*************

karfe takwais 8:00 motocin daukar amarya sukazo daukar Amarya kuka kam zainab tasha shi kuka bawai daya ba kukan ta dana barin gidan da kuma kukan bata san wani kallo hashim ze mata ba in ya gano ita din bata je masa da budurcin ta gidan ba har a mota duk da tsokanar da kakarta ke mata kota kansu bata biba kuka kawai take har suka isa gidan.

_______________

Audu inaso dai mubar kauyen nan kasan su da magana gwra mubar kauyen nan duk da nasan tun kakani mu a kauyen nan  a ka haife su aka bine su kuma Amma kaddar tasa zamu bar shi kane ma mana  gida a makwftan garin nan irinsu Rikadawa koo karaye hakan zesa asirin mu ya rufu

___________________

Mezan gank haka hashim ya maimaita yana jijiga zainab wace itama hawaye ne ke fitowa daga idon ta ki fada min zainab duk iya kokarina akanki amma har wani ya yodare ki, kika bashi mutuncin ki zainab bangane ba zainab ki fahimtar dani

1

*fatiman kuce**Y’ER ZINA CE*

     _(kaddarar iyayena)_

*MUNEERA*

*KINA INA NE MISS XERKS PAGE DIN YAU NAKINE KE KADAI BAN HADAKI DA KOWA BA*

Pg~7

wallahi se kin fada min uban daya fafake ki dan ubanki ya fada yana huci kamar wani zaki zainab da duk ta firgice tai saurin sauka daga kan gadon ta lalubi kayanta tana kokarin ficewa daga dakin hashim yayi wani tsale ya karaso inda take yana kuka yana fadin” zainab meyasa zaki min haka meyasa zaki saka min da wanan ha”incin zainab meya cuce ni wayoo ni hashim nashiga uku zainab why?? why!!! zainab bazan iya jurewa ba kinsan ina kishin ki zainab kin cuce ni kin cuci kanki wallahi se kin fada min wani shegen ne yayi miki wanan abin” zainab din da tunda ya fara magana banda kuka da girgiza kai tare da toshe bakin ta ba abinda takeyi Yaya hashim ka saurareni dan Allah ka saurarenj ji yayi zuciyar shi na wani irin zafi hakan yasa shi saurin bude kofar dakin ya koma palo ya zauna kan 1str yana kuka me tsuma zuciya se a lokacin ya tuna da sakina zunbur ya mike yana fadin” na cuce ki sakina Alhakin kine sakina ki yafe min sakina ina wanan halin duk a sanadin abinda na miki ne sakina ki yafe min na tuba sakina wayoo sakinaa” tabbas gobe zanxo gareki sakina ina nan tafe sakina Na cuce ki sakina haka dai ya kwna yana sumbatu zainab kuma ta kwna tana kukan rashin samun kulawa da kowace mace take samu a wurin mijinta ranar daram farko itadai zata iya cewa daren be zo mata a dadi ba tabbas ita zata bada wanan bayanin haka duka su biyun suka kwna suna alahni

+

——————————-

Sakina da kaka a tare suka fito da kayansu duka kaka nata kukan da alhinin barin garin sakina kuma na kukan tabbas tasan hashim ze dawo gareta dan tana ji ajikin ze dawo ya share mata hawayen ta a haka suka shiga motar da kawu audu ya kawo musu suka shiga yan gari nata Alhinin barin mutuniyar kirki irin kaka garin se daga musu hannu ake har suka kurewa mutan kauyen gani ba kuma tareda sun fada musu wani gari suka koma ba kawu audu ne a gaba se kaka da Sakina a baya, kaka ta jawo sakina jikin ta tana bubuga bayanta alamar rarashi kan cewa tayi shiru a hankali ta dinga sauke ajiyar zuciya kafin kaka ta dagota tana fadin “sakina sedai kiyi hakuri dan abinda ya faru ya rigada ya faru sedai kuma ayi hakuri ki dau dangana abinda zaki haifa ta hanyar Allah yaso yazo kenan haka dai kaka ta dinga kwntarwa da sakina hankali

*******************

Da sasafe hashim yayi wanka yayi kyau sosai sanan yayi yunkurin fita zainab dake gefe duk a darare take dashi tace yaya hashim dan Allah…… Saurin dakatar da ita yayi ya fice se jiyo hucin tashin motar shi taji ai kuwa ta kuma curewa wuri daya ta saki kuka me tsuma zuciyar me sauraro hashim kuwa ba inda ya nufa se madobi garin su sakina wace se hango kykywar fuskar ta yake tana masa murmushi be wani jima ba ya karasa garin sallama ya dinga kwdawa a kofar gidan amma ba wanda ya amsa masa wani mutum ne yazo wucewa ya ganshi yace malam ai mutanen gidan nan sun bar garin nan domin kuwa jiya suka bar garin gidan ma sun saida shi hashim da yake zare ido yana goge zufa tunda mutumin ya fara magana yaketa Goge zufa yana girgida kai kafin mutumin ya gama magana hashim ya koma cikin motar sa ya dafa jikin kujerar yana fadin tabbas shiyaga abinda akexewa *duk abinda kaiwa dan wani se anwa naka inba ama dan ka zaaiwa kanwarka inba aiwa kanwarka ba zaaiwa matarka yau shi ze fadi haka yayiwa sakina yana ganin ya mata bawanda ze masa se gashi zainab daya yarda da ita ya dade yana  tsaron ta ya dade yana kula ta ya dade yana tarairaiyata segashi wani ya riga shi sanin ta jiyayi kamar yana jin juwa a haka dai ya lalaba ya tada motar tashi ya fara tafiya da kyar ya karasa gida.

_____________________________

Tunda hashim ya fita zainab tai kukanta iya son ranta sanan ta shiga toilet ta kuma yin wanka sanan ta fito palo ta zauna kowa ya ganta yasan tana cikin damuwa  a haka aka turo kofar palon da take  daga ido tayi ta kali duk mutanen dake shigowa Aunty hafsa ce se auntu faty da kuma yaya saudat da gudu taje ta rugome aunty faty tana kuka Aunty faty ita dariya ma ta bata se cewa tayi Aa ya akayi ne Amarya kuka ta kuma fashewa dashi sanan tace gaskiya Aunty faty ni binku zanyi baza zauna ba ya kasheni yi hakuri Auta kinji ai hakuri akeyi kinji kowa da haka ya girma

🖐🏼🖐🏼gwgo sa’ade se kibarni nasha iska😂🤣

Fatiman kuce*YER ZINA CE*

*muneera*

_Saheeba ummu nabil ga naki base nace komai ba ana mugun tare and pls sorry😶🙂_

Pg~8

Anty faty ta rarashi zainab sosai tare da kwntar mata da hankali zainab din kuma kwntar da hankalin nata kadan nan suka ajiye mata abincin da suka kawo mata suka tafi……

Koda hashim ya dawo gida ya duba zainab a palon beganta ba hakan yasashi komawa daki kan dasuma ya ganta zaune da carbi a hannu ta rafka uban tagumi tausayi ta bashi ya karasa a sukwne ita da take gyain-gydi tuni tai azamar mikewa tana yin baya da bashi hakuri ya karasa inda take rungometa yayi duk dauriya irin ta hashim seyaji hawaye zirr a idon shi zainab kuwa kasa fuskantar shi tayi sanan ya jawo ta ya zaunar da ita yana fadin fada min zainab yanzu ina sauraren ki meyasa kika bawa wani kanki wani hawaye taji kafin ta fara magana kamar

     ” *Nasan dai kasan yaya kabir dan kanin abba, wanda yake karatu a india wata ranar asabar da yamma na dawo daga school na shigo gida a makare domin lokacin se kiran sallah Magrib akeyi  da sauri nake tafiya bana ko ganin gabana burina na karasa shiga gida ina wanan yanayin naji na bugi mutum dagowar dazan muka hada ido na bashi hakuri nayo cikin gida ba tare da na’kara waigen sa ba zainab ta kuma goge kwla dake fitowa daga idon ta shi kuma hashim ya zuba mata ido yana sauraran ta yaya hashim tun wanan ganin danaiwa bawan Allah nan senaji ban yarda dashi ba sedau kasancewar shi dan uwanku bayan da zanyi toh tundaga lokacin yake shiga sabga ta bana kulashi yayi yayi kan cewa na saki jikina dashi Amma naki yarda hakan yasashi cewa yana sona na fada masa an mana baiko seya kyle ne wata rabar asabar da yamma momy tace na shirya ta aikeni gidan kawarta hajiya salma na shirya aka aika kiran driver se aka tarda baya da lafiya hakan yasa momy cewa yaya kabir ya kaini tun lokacin naji gabana na faduwa amna hakan nan na bishi muka tafi a hanya muna tafiya yayi parkin ya sa wani dan tsuma ya shaka min wani abu a fuska cikin lomaci kankani na fara ganin dishi Dishi daga haka ban kara sanin inda kaina yake ba se tashi nayi nagani kwnce akan wani gado jikina duk ya baci kuka nasaka ina kiram sunan momy Amma banji alamun mutum ba can sega yaya kabir ya fito ya kara shaka min wanan abin ban kara sanin inda nake ba kawai seganina nayi a gida momy na ta min sannu ashe wai zuwa yayi ya yarda ni a kofar gate ya bar motar ma a wurin tun daga ranar baa kara ganin sa ba ni kuma naso a fada maka amma momy ta hana*”

+

    Hashim na gama jin haka ya rungome zainab dake ta kuka yana dan bubuga bayanta alamar tai shiru komi ya wuci

———————————————-

5mounth later

Cikin sakina ya girma ya fito yan kauyen Rikadawa sun dauka sakina matar aure ce Amma tunda ladidi dilaliya ta zo garin taga sakina da ciki ta dinga bi makota tana sanar musu ai sakina batada Aure cikin shege ne tayi shiyasa suka bar garin su suka dawo nan Aiko nan da na garin ya dauka kaka koo fita batayi hakama sakina sakina kullum cikin damuwa tana zuba idon ganin hashim Amma shiru Amma duk da haka bata fida rai kan cewa zai zo gareta ba

Hashim kullum cikin neman sakina yake Amma ina A watani biyar din nan da suka wuce abubuwa da yawa sun faru harda rabuwar auren hashim da sakina sedaga baya aka maida auren saboda wani boyayen Al’amari da aka gano amma duk da haka zainab tana gida tana rainon ciki wanda zeyi wata biyar itama Rayuwa na shudewa komai na canzawa Sakina kuwa kuka kullum cikinsa take tana adduar Allah yasa abinda zata haifa bazai yi kuka ba ko kuma danasanin zama mahaifiya a gareshi takan zauna taita tunani kala-kala harse kaka ta hana ta sanan take denawa takan yawaita tunano lokutan da sukayi itada hashim tana dama ace a  lokacin aure sukai sedai tayi sake yau gashi zata haifa yarinya bata aure ba yar gaba da fatiha ya illahi sakina iya danasani tayi shi👉🏻 *(‘kalubale gareku yan mata da zawarawa wallahi wallahi zina babar zunubi ce kuma kuma a wanan zamanin zina ta zame mana ruwan dare game duniya duk macen da tai sake namiji yasanta a waje wallahi saboda koda kunyi aure baze taba kallon ki da mutunci ba Yar komai rintsi kikai budircin ki gidan mijin ki shine kimar ki Amma kika zubada mutuncin nan a waje ko kunyi aure inba zargi to akwai cin mutunci Allah sa mu dace)*

Garin yayi sanyi se kamshin kasa ne ke tashi ni’ima ta ko’ina na sauka kowa yana cikin gidan sa saboda yayafin da akeyi yana sauka a hankali kaka da sakina na daki suna dan hira Amma sakina dauriya kawai takeyi domin wata rikewa da bayanta yayi ga kasan marar ta kamar zata fado kaka na lura da ita yau tun safe ta gane nakuda takeyi a tsatsaye Amma taki magantuwa shiyasa kaka ma ta bita da haka yanzu kam ji tayi bazata iya daurewa rumtse ido tayi tana fadin kaka ciki na washh Allah na zan mutu ta fada cikin rumtse ido kaka da sauri ta miki ta fara harhada mata abinda ta sani nasu na manya

A wanan lokacin zainab na kwnce kan ciyar momy suma suna dan taba hira zainab ta mikebta zauna momy tace lafiya dai lafiya lau momy can dai da takasa daurewa ta saki wata uwar kara tana kiran suna yaya hashim tuni momy ta rikece tai sauri riketa sukayi asibiti

*************************

Wayooo kaka ki yafe min mutuwa zanyi na shiga ukuna kaka ni sakina gwra na mutu na huta wayoo ya Allah in mutuwa ce sauki a gareni ya Allah ka dauke da sauri kaka ta toshe mata baki nan fa sakina ta saki wani uban nishi kukan yarinyar ce ya cika gidan sakina kuwa faduwa tayi jagab kamar bata motsi😟

—————*—–***********

suna karasawa momy ta kira hashim ta sanar masa gasu a asibiti basu wani jima ba zainab ta haifo yarinyata mace

Muje zuwa

fatiman ku ce😁*Y’ER ZINA CE*

     _(kaddarar iyayena)_

*BARKAN MU DA JUMA’A ALLAH YA SADA MU DA ALKHAIRAN  DAKE CIKIN WANAN RANAR*

Pg~9

Nan kaka ta fara kiciniyar gyra jajariya Dan dama ta dade da dora ruwan zafi gyra dakin tayi ta gyra sakina kanta wanda tunda kaka ta mikomata yarinya ta ‘kura mata ido hawaye se ambaliya suke a fuskarta yarinyar sak kamarsu daya da hashim hawaye ne ya kuma zubowa daga idonta a fili tana fadin Allah ya baki rayuwa mai kyau Allah ya rabaki da tsangwma ki yafe min na haifo ki ba ta…..Se tayi shiru kaka kuma bata hana ta kukan ba tadai zuba tagumi tana kallon su itama hawayen taji na zuba daga idon ta wai yau ita *HAFSATU*  ce jikar ta ta haifa mata *Y’ER ZINA* a cikin gida Kukan duka sukeyi yayinda yarinya se tsotsar hannu hannu takeyi tana dan cicila kafa suna haka Audu ya shigo kallon su yayi duka seyaji sun bashi tausayi musamman ma sakina miko hannu yayi alamar ta miko masa yarinya mima masa tayi sanan ya kale ta sakina wani suna Kike so amata huduba Dashi sunkuyar dakai tayi tana fadin Amina Kawu masha Allah ya fada ya mata huduba da Amina amma kuma ama kuma zasu dinga kiran ta da meena 

+

hashim koda yazo ya Ya karbi yarinyar kuka ya fashe shi dashi yana rungome yarinyar sonta na ratsashi tausayin kansa na kamashi lalai Allah abin duniya abin tsoro huduba anyi suna anyi shagali sosai yan uwa se mamakin saurin haihuwar zainab take

5years later

Shekaru na shudewa komai na wucewa sakina kuwa mutane da yawa in sunzo auren ta sukaji tana da yarinuar data haifa bata hanyar aure ba se mutum ya hakura ace karuwamcin ta har yakai yin ciki ta haihu meenat kuwa kullum ba dama ta fita an finga mata ihuu kenan ana kiran ta da *YAR ZINA* haka zata dawo gidan tai kuka ga yarinyar kyakyawa gashi har gadon bayanta shiyasa wasu ma ke cewa sakina da balarabe tai zina ta samu cikin yarinyar akwai wani khamis da yaji labarin sakina yace yaji ya gani ze aure ta a haka kuma ze rike mata yarinyar tata sun shaku sosai da sakina sedai sam iyayenshi suka ki yarda ya aure ta a lokacin sakina har rashin lafiya tayi meenat kuwa tunda wanan shekarun nata take kuka tana fadin Ita maman ta, ta nuna mata wane babanta tana son sanin mahaifinta..Kullum sakina cewa meenat take zezo ne meenat ko bayan ba raina zakiga babanki kinji babyna duk lokacin da sukai maganar nan se sakina ta koma daki ta sha kuka iya son ranta sanan take hucewa haka ma washe gari meenat an sata a makaranta kullum kowa babanshi ke kaishi a keke ko babir ita kuwa mamanta ke kaita yau kamar kullum sakina ta shirya meenat suna tafiya a kafa har suka karasa makaranta, meenatu na ayi karatu da kyau kinji banda wasan banza Allah bada saa duk maganar da take meenat bajin ta take ba hankalin ta na kan wani yaro da babanshi ya ajiye shi yana masa kiss mama meenat ta fada nima yaushe babana zezo in kin koma dan Allah kice masa Yazo yan ajin mu suna ce min sunana meenat Rikadawa kawai ba sunan abbana ajiki sakina ta goge kwlar idon tace meenat zezo kinji dena kuka yakusa zuwa maza tafi class kinji yarinyar kiriki

*************************

Zainab ce zaune a palo tana kallon zee world ji tayi taku dai-dai wata hadadiyar yarinya nagani da bazata wuce shekara biyar ba an baza mata gashi a baya *Nihla* naji zainab ta fada yarinyar ta taho da gudu zata rungume zainab Amma kuma baba talatu me aiki n su ta taho itama da sauri da abinci hanunta se suka bigi juna ita da nihla dagowa yarinyar tayi a fusace ta kali baba talatu sanan tace ke baki da hankali ne talatu da zaki zuba min abinci a jiki dan ubanki jikin matar se kyarma yake yana rawa ta fara yunkurin yin magana amma nihla ta dakatar da ita kinsan ni kinsan kuma yar waye shine kika min haka toh a bakin  aikin ki tuni baba talatu ta tsuguna tana bawa nihla hakuri Dan Allah ki temake ni ………. Hashim na gano yana shigowa gidan domin sun canza gida sun koma abuja sakamakon hashim yanzu senator ne  hakan yasa ya kara girma da kyau fatar shi ta kuma yin fresh ya dakatar da nihla yana fadin haba my princess ai mata afuwa mana ya fada yana daukar ta sanan yayiwa baba talatu nuni da hanun alamun taje Aa dady ni se an koreta bana son ta tunda ta bata min kaya

——————————————–

Tunda sakina ta dawo wani azababen ciwon kai ya kamata ta samu wuri ta kwnta kaka ta tambaye ta lafiya tace lafiya lau kanta ke dan mata ciwo tana kwnce har meenat ta dawo daga makaranta, sakina ta kama hannun meenat “Aminatu na kiyi hakuri kinji duk yarda zaki samu rayuwar ki kiyi hakuri ki yafe min meenatu na ” kaka dake gefe tace sakina wani irin magana kike haka”kaka mutuwa zanyi nasan na bata miki kaka amma dan Allah kaka kiyafe min ga amanar meenat nan kaka Allah ya bayana mahaifinta Allah yasa sunada rabon Haduwa” sanan ta kuma kallon meenat tace meenatu na , nasan na haife bata yarda ake haifar kowani da ba Amma dan Allah ki yafe min nasan nan gaba zaa cigaba da miki gori na rashin uba dan Allah meenat karkiyi irin rayuwar da nayi ” se kuma tayi tari ta kali kaka ra danka hanun meenat a hanun kaka, da kyar ta iya cewa kaka ga Amanata nan, maganata ta karshe meenatu ki rike mutuncin ki koo bani kika zubda mutuncin ki ban yafe miki ba se kuma idon ta ya fara sama tana shakuwa tace kaka ruwa kaka da sauri ta tafi debo mata ruwa, meenat kuwa cewa take Mamana bazaki mutu ba banida baba kema mamana zaki tafi karki tafi dan Allag bana so ki mutu kalmar shahada sakina tayi se kuma difff tayi shiru

Fatimanku ce🤝🏻*YAR ZINA CE*

_(kaddarar iyayena)_

muneera

🤕🤕i miss you my Raheema

Pg~10

Kaka na dawowa ta dago sakina tana cewa sakina ga ruwan shiru taji taga dai fuskar Sakina alamar murmushi sanan ta wani kara kyau ga farin ta daya kara fitowa, kallon ta kaka tayi taga jikin ta ya saki hannun ta, ta kamo ta ga ya fadi kasa yaraff, innalilahi wa’ina illahi raji’un sakina ki tashi badai mutuwa kimayi ba sakina na shigesu Innalilahi, meenat ta kali kaka tana murmushi tace kaka nifa mamana ba mutuwa tayi ba kalli fa kaka murmushi take min kuma ma ai tace ki kawo mata ruwa, kuka kaka ta kuma fashewa da wani kukan sanan ta jawo meenat jikinta tana rugume ta, toh dama audu yazo noma dan haka fita tayi ta sa yaro ya kiranshi ba jimawa segashi kallon sakina yayi duk juriya irin ta Audu segashi Yana kuka yana fadin shikenan sakina kin tafi kin barmu halin ki nagari ya biki kin mana biyaya sakina yana gama fadin haka ya tashi dan zuwa ya fadawa me gari, kafin wani lokaci gidan kaka ya cika da jama’ar kauyen saboda suna zaune da kowa lafiya basu taba fada da kowa ba ba jimawa akaiwa sakina wanka aka shiryata Audu ya shigo da makara aka fito da sakina anasata a ciki gaba daya mutanen wurin suka dinga kuka meenat da gudu ta karasa tana rike sakina tareda fadin, kawun mama ina zaka kai mamana tare muke zuwa unguwa ya zaka kaita yai ita kadai kuma ya kasa ma mamana farin kaya rh kawu ku kyle min mamana koo kuma mu tafi tare gaba daya yan wurin seda sukayi kwla, meenat ta kara da cewa mamana ki tashi ki cewa kawu bazaki ba dani kike zuwa unguwa, mamana zan biki kinji…. Kaka ta karaso ta kama hannun meenat tan cewa meenatun Mama yanzu zasu dawo kinji taho nan, nan su kawu audu suka dauki sakina zasu fita har sunkai kofa meenat ta ruga a guje ta kama kafar kawu audu tana fadin kawu ka tafi dani dan Allah karkai mamana wank wuri zan bita, mama zan biki mama ku sauke min mamana Da kyar aka banbare meenat daga jikin kawu audu tana kuka tana se an sauke mata mamanta ina za’a kai mata mamanta su kyle mata mamanta bawanda bata ba tausayi ba dan har aka kai sakina aka dawo meenat na kuka.+

Kawu Audu na shigowa ta taho da gudu ta rungome shi kawun mama kace tare zaku dawo da mama yana ganka kai daya ina mamana take ? kaka da sauran jama’ar wurin suka sa kuka tausayin meenat na kamasu, kawu mamana fa tace zata kaini wurin babana yanzu kuma ka kaita wani wuri bata nuna min babana ba wayoo mamana ta cigaba da kuka tana birgima da kyar aka samu aka rarashe ta ana fada mata mamanta zata dawo unguwa taje amma in tana son dawowa se tayi shiru…….

________________________________

Sati guda kenan da rasuwar sakina inda kullum meenat se tayi kuka kan cewa itafa se an kaita wurin mamanta tun tana yi har ta dena saboda a tanzu ta gane cewa maman ta ta rasu ta tafi inda bazata dawo ba lalai maman ta tafi unguwar da bazata dawo ba meenat yarinya ce me nutsuwa duk da kanan shekarun ta ga wayo datake dashi, kawu Audu ya shirya dan konawa lagos yayi-yayi da kaka ta barshi ya tafi da meenat Amma kaka taki yarda, hakan yasashi barin musu komi na kayan abinci sanan ya tafi

********************

Nihla yau take birthday din shekara 6 duk An hada mata party sosai wanda gaba daya gidan anyi masa ado se kyli yake yarinyar Kuwa taci wata pink din gown, an mata gyran gashi tayi kyau kamar ba ita ba make up kuwa tashata cake din da aka siya kuwa yakai 100k banda abubuwa da akai mata se gift ake bata domin yarinya hashim da zainab sun dauki son duniya sun dora mata duk abinda take so shi ake mata dan haka yasa bata san babu ba a rayuwata ko me ta nema se an bata shi so na sosai hashim da zainab kewa yarinyar anyi komai lafiya an gama lafiya.

Tunda Audu ya tafi su kaka basu kara jin labarin shi ba ga abincin su duk ya kare se kamame kawai sukeyi gashi da meenat ta fita zaa dinga nunata ana fadin ai *YAR ZINA CE* bata da uba ba’a san asalin ta ba haka zata dawo gida taita kuka tana cewa kaka ita takaita wurin babanta. Rayuwa na shudewa shekara guda har ta wuce meenat yanzu shekarar ta 7 tun bata san me ake nufi da *Y’AR ZINA* ba hartasani yanzu ko an kirata da sunan takan yi murmushi kawai ta kali mutane ta wuce A shekara dayan nan an nemi audu an rasa duk nemanta da zaayi an masa amma ba’a ganshi ba abokan sana’ar sa ma haka sukace basu ganshiba ga shi duk ba abinda zasuci kaka tayi bubuga ta amma basa samu wata rana ma bacci suke basu ci komai ba

Yau dilaliya ta shigo gidan tana fadin gafaran ku dai masu gida kaka ta fito tana amsawa tace bismillah Abu shigo, shiga abu tayi bayan sun gama gaisawa da kaka,kaka ta tambaye ta lafiya tace dama naga yar wurin ki ta taso shine nace koo zaki bada ita akaita birni aiki kaka ta dan numfasa tana tunanin maganar dilaliya kuma fa hakane tunda dai basuda kudi abinci ma wata rana basa ci ga makaranta ma yanzu meenat bata zuwa numfasawa tayi toh abu sena yi shawara zan miki magana abu ta ce toh dai duk yarda kikace dan kuwa jibi zamu tafi ……………..

Fatiman ku ce👌🏻*Y’ER ZINA CE*

     _(k’addarar iyayena)_

*muneera*

Wattpad👉🏻fatimamuneera001

_😗y’ar tsohuwa me baki gajaja da goro😂 hauwa sarki yau page din nakine saboda rikicin tsufa n bki shi ke kadai bn hadaki da kowa ba Allah ya bki lafiya my kululu i luv u wujiga wujiga😍_

Pg~11

Kaka tayi nazari sosai bayan tafiyar dilaliya ta kira meenat dake gefe tana jin yarda kaka sukai da dilaliya, meenat kinji yarda mukai da abu koo meenat ta dagawa kaka kai, meenat kin yardazaki bita birni aiki meenat ta daga mata kai tace duk yarda kikace haka za’ayi Kaka ta goge kwlar idonta tana tuno sakina duk lokacin data zo da shawara sakina ma haka take yi tace ai kaka komai kika yanke akaina dai-dai ne nasan bazaki taba cutar dani rungome meenat tayi tana meenatu na nagode meenat da ta goge kwlar idonta tana tuna maganar mamanta datake fadin “meenat dina kar in kara ji kinyiwa kaka musu komai tace kiyi kice toh” shiru sukai duka itada kaka suna kowa da tunanin da yake a ransa

+

Nihla da ta fito cikin uniform tana taku dai-dai kamar bazata taka ‘kasa ba ta karaso jikin motar, “habu driver! take fada a tsawace da sauri ya karaso jikin sa na karkawa saboda sanin halin yarinya yanzu seta sa a koreshi ba karamin aikin ta bane wanan yarinya karama da ita se feleken tsiya ga iyayi da girman kai gashi bata girmama na gaba da ita, sanan kuma ta tsani talaka shiyasa duk y’an aikin gidan suke Amma ba kowa ne ya sangarta ta haka ba irin zainab, hashim yana iya kokarin shi kan gyra tarbiyyar yarinyar Amma ina sam bata da kunya ga tsiwa a bakin ta,

kaka da suka gama shirin tafiyar meenat dilaliya kawai suke jira kaka se fada takewa meenat, meenat tana gasgata mata kan cewar karta damu zata kula da kanta suna haka abu dillaliya tayi sallama bayan sun gama gaisawa kaka ta tambayeta wani gari zata kai su meenat din dillaliya tace Abuja kaka tace abu anya habuja beyi nisa ba garin shugaban ‘kasa fa kike magana abu ta murmusa tace kaii hafsu ai anfi samun kudi a can ba kamar sauran garuruwa ba saboda can garin masu kudi ne kaka ta jinjina kai tace toh Abu Allah ya kaiku lafiya sedai fa kiyi hakuri dan yanzu banida kudi ki juya min na motar abu tayi dariya tace ai bakomai hafsu   Taja hanun meenat suka nufi kofar fita meenat se juyowa take tanawa kaka kallo har suka fice

Tafiyace suke tayi wanda meenat koda aka shigo garin kano setaji garin ya mata inama ace anan za’a ajiyeta saboda wani irin dadi da anashuwa da take jin ta a ciki se lekeke take tana kallon garin yanda kowa ke gudanar da Al’amuransa, a kala sunkai kusan awa 4 a hanya kafin su isa garin abuja lokacin da suka isa tuni meenat tayi bacci sauran yaran kuwa idon su 👀suna kallon gari, direct maitama dilaliya ta wuce da yaran seda ta kai kowani yaro gidan da tai alkawarin kaisu aka sallameta sanan ta kama meenat suka nufi wani hadaden gidan wanda duk layin yafi su haduwa seda me gadi yayi waya cikin gidan akace ya barsu su shiga sanan suka shiga katon paloun meenat take karewa kallo a zuciyarta tana fadin sekace Aljanna nan tana wanan kalalen matar ta iso baka ce kuma doguwa ce me jiki batada yawan fara’a daka ganta zaka gane hakan meenat data fada zirfin tunani taji ana cewa, wanan ce yarinyar? dilaliya ta kada mata kai, yanzu abu kina ganin wanan zata iyayi min raino dillaliya tace sosai ma ranki ya dad’e matar tace toh zan gwda ta nagani, sanan ta zaro dubu ashirin ta bawa dilaliya tace ga kudin takalmi nan sanan ta zaro dubu goma tace wanan kuma kudin mota ne dillaliya  ta zube tana ta zabga godiya matar ta ce ta tashi taje

Kee!! matar ta fada meenat ta dago ido tana kallon ta, ke ya sunan ki, meenat sunana matar ta tabe baki tace toh muje in nuna miki inda zaki zauna meenat ta bita a baya sedai mai kichen naga ta nufa da ita sanan tace kinga nan meenat ta daga mata kai tace anan toh zaki dinga kwna Meenat tace toh hajiya nagode batareda ta kalleta ba ta fice, zama tayi a kasa wani irin sanyi taji a kasan wanda bata taba jin irin sa ba………….

Kee kee taji an kira sunanta meenat da sauri ta fito tana neman hanyar da zata kaita inda taga matar nan a zaune sedai kashh seta tura wani daki wanda wani mutumi ke zaune yana lalatsa waya jin an turo kofar yasashi daga ido ya kali wurin meenat da duk ta kideme tace yallabai kayi hakuri dan Allah lashe baki yayi yace ya…..Amma ganin matar akansu yasashi yin shiru ya cigaba da abinda yake matar kuwa ta damki gashin meenat tana fadin uban me kika shigoyi dakin mijina iyeee makira wato an koyo miki tunda ga gida koo shegiya da ido kamar na mujiya hawaye Meenat din ta farayi tana hajiys kiyi hakuri dan Allah, inyi hakurin uwarki ai yau dinan bawai gobe ba zaki zo ki fice min daga gida……

Fatiman ku ce👌🏻*Y’ER ZINA CE*

        _(k’addarar iyayena)_

*MUNEERA*

Wattpad👉🏻fatimamuneera001

_*WOW COMMENT DIN KU NASANI NISHADI SOSAI GODIYA ❤ALLAH BARNI TARE DAKU*_

Pg~12

Se lokacin mutumin yayi magana haba jamila ya zaki ce ta, tafi cikin daga murya matar tace saboda kai dan iska ne zakuyi lalata da yarinya shine zakace na barta wallahy yau seta bar gidan nan tunda ba gidan ubanta bane, meenat dake gefe ba abinda take se kuka tana faman bawa matar hakuri amma bata bi takanta ba se zazagawa mijin nata masifa take kamar itace mijin shi kuma matar, shiru ya mata be kara tanka mata ba harta ja yarinya tana kuka ta fice da ita ta watsa ta waje tare da cilo Mata kayanta waje cikin hawaye, ta mike tana fadin hajiya ki temaka min dan Allah bansan inda zani ba in kika kore ni, ki shiga duniya wayace ki kusanci inda mijina yake? aini yarinya ni mijina koo uwarsa bana bari ta kusanci inda yake bale ki jakar kauye , uwarki tayi…….Jin zata zagi mamanta yasata tai saurin tashi taja kulin kayanta ta fice tana waigen gidan, toh ita yanzu ina zata ? ita da batasa kowa ba kuma bawanda yasan ta ,Tayi tafiya me tsahi da batasan adadin ta ba kishi da yunwa takeji saboda Tun abincin da taci da zasu taho bata kara cin komi ba

+

*************************

Dilaliya ta fito da murna dan yau ta cika aljihun ta da kudi kai tsaye tasha ta yi ta kama hanyar kano kowa yaga dilaliya yau yasan tana cikin farin ciki haka suna sauka a kano bata wani jima ba ta nufi tasha ta hau mota zuwa Rikadawa, duk da gajiyar da take tatare da ita hakan be hana ta yin gidan kaka ba da rangad’idiyar sallama ta shiga, kaka duk jikin ta a sanyaye yake ta amsa sallamar abu, abu ta wangale baki tace “hafsu ai kiyiwa Allah godiya domin kuwa milat kuke cewa kome ke Amina dai ta samu gida aiki na kwarai ga kudi kedai baki ga abin arziki ba hafsu, hafsu Allah dai ya mana arziki” ta karasa magana ta dauko wasu kudi data kule su a cikin wata jaka da take daure a k’ugunta, kaka kuwa se murmushi take tana godewa Allah kan abinda abu ta fada mata abu ta kirgo dubu goma 10k ta mikawa kaka, har kwla kaka tayi tana yiwa abu godiya sanan ta ciro 3k ta mikawa abu. Abu kuwa kin karba tayi tacewa kaka ai itama an bata nata kaka tayiwa Abu godiya abu ta wuce gida dan bazata iya zuwa sauran gdn iyayen yaran ba saboda dare yayi sedai ta bari da safe

——————————————

Gefen Titi ta samu ta zauna tana hakki saboda gajiyar da tayi, tai kasa da kanta tana hawaye, ta dan jima a wurin kafin wasu mata suzo su tsaya sunkai su 10 kuma dukan su bame shigar arziki a cikin su dukan su bazasu wuce shekaru 15-17 ba da me mota yazo ya tsaya zasu tafi da gudu suna fadin “sir see my breast(kaga nono na) a haka dai aka dinga daukar su wani ma in su ka masa magana seyace suje in sunje seya taba nonon yace be masa ba itakam meenat abin ya bata mamaki matuka, wata matashiya ce ta taho tana tafiya kamar bazata taka kasa ba ta karasa inda meenat take, meenat ta dauka bata jin hausa amma seta ji tace mata “baby meya zaunar dake anan wurin? ta fada cikin siririyar murya meenat shiru ta mata matar ta kara cewa “ina mamanki?” hawayen idon meenat suka karasa zubowa Matar ta girgida kai ta kuma tambayar ta “ya sunan ki?”  se lokacin meenat ta dago ta kuma karewa matar kallo “meenat” wow meenat toh meyasa kike kuka?” kuka ta saka sosai kafin tace banida wurin da zan kwna  matar ta dan cije baki sanan ta goge kwlar idonta tana tuna wani abh kafin tace zaki bini ki kwna gidana? meenat ta tsaya tana kara kallon matar tana aiyana abubuwa iri-iri a ranta, kamar tasan tunanin da take tace

“taso muje kinji bazan cutar dake ba”

Meenat dai bata ce komai ba ta tashi tabi matar ta, sanan ta dau kulin kayanta ta sa acikin motar ta sanan tasa meenat a gaban motar tajasu suka tafi

wani makeken gida wanda yafi gidan da aka kaita girma suka shiga meenart se waware ido takeyi  Hanun meenat matar taja suka shiga gidan wani makeken palo suka shiga wanda meenat a zuciyar ta tace kamar a aljana , matar ta zaunar da meenart tana mikewa ita akan 3str wani mutum ne ya shigo wanda yasa matar tamke rai tana fadin meya kawoka be jira ta kara magana ba ya rungometa yana fadin haba jamila ya zaki min haka kinsan yarda nake sonki shiyasa kike min haka ya karasa maganar yana shafo boobs din…………. . …..

meenat ganin abinda suke yasata saurin rufe ido ta juya musu baya tana tunani kala-kala a zuciyarta

Fatiman ku ce👌🏻*Y’AR ZINA CE*

_(k’addarar iyayena)_

*MUNEERA*

wattpad👉🏻Fatimamuneera001

Pg~13

A haka har bacci yayi a won gaba da ita Jameela kuwa ture shi tayi tana nuna masa meenat dake kwnce ta cure wuri daya tace “kai Alhj bala baka yarinya bane eyee” ta fada tana hura hanci Alhj bala ya mike ya karasa wurin meenat yana kallon ta tare da fadin” jamcy baby ina kika samo wanan yarinya me kyau haka jamila ta mike ta dauki meenat tana yin sama da ita, ba tare da ta bashi amsa ba ta kwntar da meenat tana kallon yarinya tana jin son yarinya na shiga ranta murmushi tayi ta mike tareda fadawa toilet tayi wanka tana fitowa kayan bacci marasa nauyi ta saka sanan tazo kusa da meenat ta kwnta, Alhaji bala kuwa gajiya yayi da jiran jamcy ya hau saman ganinta da yarinya suna bacci yasashi jan dogon tsaki ya fice yana sumbatu iri-iri , koda asuba da meenat ta tashi se taga jamila akan daduma tana sallah, tana idarwa ta dauki Qu’arni ta fara karatu, da hannu tayiwa meenat nuni da inda toilet yake, a hankali ta mike ta shiga, toh nan fa akeyin ta meenat ta fada ganin tsaruwar toilet gashi bata san ma ina fanfo yake ba bale har ta kai ga yin Alwala, kamar jamila tasan me takeyi ta mike tabiyo bayan meenat ganinta a tsaye yasa jamila janta, ta fara cire mata kaya wanka ta mata sanan ta mata brush Alwala ma ita tayi mata sanan ta nadeta a towel ta dauko ta suka fito Kallon kayan meenat tayi taga duka masu kyau ne wasu ma sababine wata atampa tasa mata sanan ta bata hijab tace tayi sallah yarda jamila taga meenat na sallah abin ya birgeta saboda a nutse takeyi kuma ba gyra a sallah tata tana idarwa taji tana karanto addu’oi ta jinjina kai a zuciyar ta tama fadin duk daga inda yarinya ta fito gidan su da tarbiya, tana iddarwa ta tsuguna tace “hajiya ina kwna” jamila ta dago ta tace “ki dinga kirana da Aunty kinji ni Auntyn ki ce” meenat ta gyda kai sanan jamila ta riko hanun ta suka sauko kasa”jummai” shine sunan da naji jamila na kira, wata yar matashiya ce ta taho da sauri ta zube tace “ranki ya dade” jamila tace kin hada breakfast din, eh hajiya An kamala owk ta fada suna nufar dining din, sosai meenat taci abinci saboda tsabar yunwa da takeji sanan jamila ta dauki meenat suka fita zuwa super maket, Rike da hannun meenat jamila ta fito haka ma hashim lokacin ya fito rike da hanun nihla, kamar ance ya juya, caraf suka hada ido da meenat jiyayi gabansa na faduwa ganin tsantsar kama da yake da yarinya ta wani bangaren kuma tana masa kama da sakina, kafin ya gama tunanin meenat ta hango wani mutum ya saito inda hashim yake da bindiga da sauri ta kwce hanunta daga na jamila ta karasa wurin dai-dai lokacin bullet din ya karaso se cikin meenat, faduwa tayi hawaye na fita a idonta A rikirkice hashim ya jiyo yana kallon yarinya, tabbas shi aka saita Amma yarinya tazo kareshi da gudu jamila ta matso wurin tana jijiga meenat tare da fadin babyna ki tashi na shiga uku innallilah kafin wani lokaci sega motar asibiti tazo suka dauki meenat da jamila, hashim yayi yunkurin binsu Amma nihla tasa kuka kan baze bisu akan wace kazamar yarinyar bazasu fasa siyayarsu ba yarda ya iya dole ya hakura Amma yana tunanin waye ya turo akashe shi ta wank bangaren kuma tunanin sakina kawai yakeyi saboda yanayin yarinyar da sanyinta yasashi gane Anya yarinya bata da alaka da sakina hakadai suka shiga shida masu tsaron shi suka fito+

Jamila ba abinda take se kuka tana aiyanawa a ranta cewar dama meenat ba da ba abinda ze samu meenat dinta kuma Kuka takeyi sosai har suka isa asibitin akai sauri aka shiga da ita saboda se an mata aiki jamila se safa da marwa tajeyi a kofar dakin tanayi tana kuka tana addu’ar Allah ya tashi kafadun meenat dinta doctor din ne ya fito ya kalli jamila wace da gudu ta karaso inda yake tana tambayar shi jikin meenat kwntar mata da hankali ya fara sanan yace Mata da sauki sunyi nasarar cire bullet sedai yanzu yarinya tana bukatar hutu se a lokacin

Jiniya ce ta karade duka asibitin a hankali ya fito yana taku dai-dai hashim kenan dakin da meenat take akayi dashi kai tsaye akai masa kyakyawar tarba jamila kuwa tace “yallabai meya kawoka bayan kaine sanadiyar kwnciyar y’ata anan kuma koo nuna kulawar ka bakaiba a time din dan haka me ya kawo ka. Yarki ko y’ata hashim ya fada mamaki ne ya lulube fuskar jamila yace yes yarinya da kika tsinta jiya har kin fara ikirarin kiranta da yarki(saboda hashim yasa anyi bincike akan jamila an fada masa mace ce me zaman kanta kuma me gadin ta ne ya fadawa hashim cewa tsintar meenat jamila tayi hashim ya bashi makudan kudi ya tafi) Dan haka ya zaro kudi da besan adadin su ba ya mikawa jamila yace gashi nan nagode kula da ita da kikayi Ki tafi jamila da ba yarda zatayi saboda yanda taga masu tsaron sa fuska murtuk ga bindigogi a hanun su ba yarda ta iya haka ta fita tana waigen meenat da take bacci ta fice ………………………

*A DINGA UZURI DAN ALLAH HAKA KAWAI BAZANKI TYPING BA LOKACI NE DAI YANZU BANIDA SHI SOSAI AMMA KU CIGABA DA HAKURI DANI🤭 INA SON KU DUKA KUMA INAJIN DADIN KULAWAR KU AKAINA💗 KUYI KOMAI BA KOMAI🥴MUNEERA NA TARE DAKU😁*

*FATIMAN KU CE👌🏻*Y’AR ZINA CE

    (KADDARAR IYAYENA)

muneera

SOSAI NAKE GODIYA AGAREKU MASOYANA WANDA KUKA KIRA KUKA MIN GAISUWA DA WANDA KUKA MIN TA GRPS DA WANDA SUKA BIYONI PC SUKA MIN GASKIYA NAGODE DA ADDU’OIN KU ALLAH YA BAR KAUNA TSAKANIN MU NAGODE

Pg~14

Haka jamcy ta fita tana waigen meenat saboda harga Allah yarinyar tashiga ranta sedai babu yarda ta ita illah ta bar ta saboda anfi karfinta akan yarinyar Hashim kuwa kujera yaja ya zauna yana kallon yarinyar sonta na ratsa sasan jikin sa tausayin ta na shigar sa shikadai ya furta meya futo da wanan y’ar yarinyar daga gida zeso sanin meya fito da ita meyasa yake jin kamar yasan yarinyar, cikin nutsuwa batare da wani motsi ba idonta ya fara karkarwa Alamun budewa a hankali ta kalli saman dakin kafin ta jiyo su had’a ido da hashim ji tayi gabanta ya fadi seta kuma juyawa kozata ga jamila amma bata ganta ba haka yasa ta kara kallon mutumin kamar zatayi magana se kuma tayi shiru tana nazarin sa shirun da tayi ne ya bashi damar tambayarta “ya sunanki?” kamar bazata amsa ba se kuma ta da lumshe ido tace”meenat”  shiru yayi yace sannu meenat girgiza masa kai kawai tayi saboda ita kadai tasan me take ji a jikin ta dan jan ta da hira ya fara yana mata tambayoyi tana bashi amsa har ta fara sakar jiki dashi kamar me lokaci guda meenat har sun fara sabawa da hashim yace mata “meenat inane garin ku” yun’kurin  tashi ta farayi shi kuma ya temaka mata ta zauna sanan tace “Rikadawa”😳zaro ido yayi yace “tab kano kenan” girgiza masa kai kawai tayi alamar eh a yarda ya lura da yarinya bame son hayaniya bace dan haka se yace ki kula da kanki kinji gobe zan dawo da sauri tace masa ina aunty na, Auntyn ki ta tafi gida zata dawo tace toh ya temaka mata ta kwnta sanan ya fice+

***************************

zaune kaka take tana jin radio aka rangada sallama amsawa tayi tana mikewa jin alamar maza ne yasata saka hijab tana fadin bismillah saboda yanzu kaka da kyar take tashi ciwon kafa yasata gaba saboda yanayin tsufa, karasowa sukai suka nemi wurin suka zauna suna gaida kaka sedai sam kaka bata gane su ba ya sata fadin bayin Allah ban sheda fuskar taku ba wani daga cikin su yace  daga garin madubi muke dama gonar da aka bar sakina gado ma’aikata suka zo suka siyi wurin za’a gida kamfani shine muka kawo miki kudin suka karasa fada suna mikowa kaka kudin dubu d’ari hudu 400k karba kaka tayi tana hawaye ta dinga zuba musu addu’a sanan ta ciro dubu hamsin 50k ta mika musu amma sam suka ki karba suka tashi suka tafi suna fita kaka ta kuma fashewa da kuka a fili take cewa”kaicona Aminatu rashin hakuri na yasa ni turaki birni yin aiki gashi yanzu abinda muka samu ni hafsatu naga Rayuwa ta karasa fada tana goge hawayen idon ta da bakin zaninta sanan ta cigaba da  cewa gashi Abu tayi tafiya nidai dana bata kudi ta dauko min aminatu y’ar Amanar Allah haka dai taita sumbatu ita kadai

————————————————-

Nihla zaune kan cinyar zainab tana koya mata assignment suna kuma dan wasa hashim yayi sallama da gudu ta tafi ta rungome baban nata tana fadin daddy oyoyo d’aga ta sama yayi yans my princess murmushi tayi tace daddy yau ka dade baka dawo ba dafe kai yayi yana fadin ai ky bari na zauna dai koo my princess turo baki tayi gaba sanan suka zauna yana ajiyeya zainab na zaune tana murmushi tana aiyana abubuaa iri-iri a ranta kafin tace yallabai sannu da zuwa Amsawa yayi yana cigaba da yiwa Nihla wasa kafin su wuce suci abinci sanan ya dauki nihla yayi dakinta da ita ya mata addu’a ya fito yana dawowa daki ya tarar hat zainab ta kwnta tashin ta yayi yace yana son magana da ita tashi tayi tana sauraren me ze ce bayani ya mata akan meenat ta gyda kai tace owk toh yanzu wani hukunci ka yanke akan yarinyar, yace zata zauna damu a nan zainab ta gyda kai sanan tace ka yanke hukunci me kyau

Koda safe a gurguje hashim ya shirya yayiwa zainab sallama dan ko takan nihla be ba ya fice wurin Meenat dan koda nihla ta tashi rigima tasawa zainab kan ita bata ga babanta ba saboda ta saba kullum shi yake tashinta a bacci amma yau a samu sa’banin haka.

shi kadai yake tafiya harya karasa asibitin samu yayi meenat na bacci seyaja kujera ya zauna yana kallon ta harta tashi seda ta murza idon ta sanan tace anan ka kwna girgiza mata kai yaui alamar A’a yace ya jikin my daughter jin yace mata my daughter yasa hawaye suka fara zubuwa daga idon ta dan ya tuna mata da mahaifiyarta domin haka mamanta ke kirata kuma ita da bata da baba ina taga matsayin a kira ta da diyar wani, hashim yace subhanallilah lafiya meyasa ki kuka shiru tayi tana cigaba da hawaye a hankali ya jata jikin sa yana dan bubuga mata baya alamar tayi shiru tayi hakuri a hankali ta dinga sauke tagwyen ajiyar zuciya sanan ya goge mata hawayen yana kuma bata hakuri har tayi shiru ya cigaba da kwntar mata da hankali dukda besan meyasata kukan ba kodan ya kirata da daughter ne shi kadai ya fada a zuciyar shi yace meenat ta kale shi ina mamanki ai wank sabon kukan ne ya kuma tahowa mata sedai kafin tai yunkurin bashi amsa sukaga an banko kofar a fusace duka su biyu suka daga suna kallon ta cike da mamaki ba kowa  bace illa nihla ta fara  magana tana dad dama wurin kazamar nan ka taho la barni shiyasa baka………………..

😝😝😝 Oh Allah nihla yanzu seda kika biyo hashim yar bukolu kawai baki san ke yar……..

😁😊 i love you my fans comment dinku na sani na jini ontop lolY’AR ZINA CE

    (Kaddarar iyayena)

Muneera

Pg~15

Kallonshi Nihla tayi tana sauke ajiyar zuciya a hankali shi kuwa kallon mamaki yake Mata saboda be tsamanin ganin ta ba da gudu ta taho ta rungume shi.

Kallonta kawai yake tace “dad ya zaka tafi bamuyi sallama ba yanzu da habule driver be kawo ni wurin ka ba Hankalina baze kwnta ba”.

Ita kuwa meenat kallon su take cike da burgewa tana addu’ar itama Allah ya had’a ta da mahaifin ta, ta nuna Masa tsantsar soyyar ta gareshi Dan Bata da burin da ya wuce taga mahaifin ta da Kuma fatan Allah ya gafartawa mahaifiyarta Nihla CE ta katse Mata tunani tana cewa.

Dad wacece wanan haka ta fada game da ta’be Baki Wanan zataci gaba da Zama a gidan mu ne kinji nihla na fatan Zaki kar’beta hannu bibiyu, zare Ido kawai take tana girgida Kai alamar baze yuyu ba tana ja da baya, shi Kuma ya maida kallon shi ga meenat wace ba abinda take see kallon su shida nihla yarda sukeyi suna birge ta lalai akwai tsantsar shakuwa tsakanin su.

+

Hashim yace meenat gobe za’a sallame ki zamu koma gida tare gyda Kai kawai tayi ya juyo da niyyar yiwa nihla magana seya wayam babu ita Babu alamar ta gitgiza Kai kawai yayi ya cewa meenat se gobe ze dawo tace “toh”

Da sauri ya shiga motar driver yaja shi suka tafi gida ya nufa Yana tunanin Allah yasa Nihla gida tayi

Ajiyar zuciya ya sauke ganin ta kwnce Akan cinyar zainab tana kwntar da Mata da hankali a hankali ya ‘karaso ya duka Yana kallon yarda nihla ta juya kanta Bata ma kallon shi

My princess meke damun ki ne Akan meenat kikejin haushi shiru tayi shi Kuma Yana jawota jikin sa tana fiszegwa rugome ta yayi a jikin sa Yana fadin my Princess kece kawai tawa meenat……..bana son Jin sunan ta dad bana sonta dad duk wani Wanda zan rabashi dakai bana so shi dafe Kai yayi Yana gyda Mata Kai

___________________________________

Kallon katon palon take tana zare ido tace yallabai anan Zan dawo da Zama ya gyda Mata Kai alamar eh yallabai bana son Zama anan nafi son na koma wurin kakata saboda tace zata temaka min na Nemo babana da mamaki ya kale ta yace “ina baban naki ya tafi ‘bata yayi”

Ta gitgiza Kai tace “yallabai aini ban ma San babana ba bantaba ganin sa ba inadai burin ganin sa Ina son nasan babana saboda a Dena CE min YAR ZINA CE tausayij yarinyar ya kamashi ya rungometa

Zainab ce ta karaso tana fadin a Ashe meenat din ta karaso Hashim ya daga Mata Kai meenat ta tsuguna tace Ina wuni zainab ta amsa tana yatsine fuska domin yarinyar Bata Mata saboda tsabar kyau da taga yarinyar tana dashi

Hashim ne ya katse Mata tunani Yana cewa tohm wifey ga amanata Nan kafin wani lokaci a yatsine murya ciki² ta amsa hashim Yana lura da yanayin ta ya kyleta ne kawai saboda baya son Jan magana……

Hashim ya Rike hanun meenat yace muje kinji meenat ta girgida Kai alamar toh suka tashi suka hau sama zainab tabi bayan su da harara tana Jan wani uban  tsaki afili take fadin “haka kawai daga ganin yarinya a titi ya dauko ta ya kawo Mana gida wama ya sani Maya CE” ta  karasa maganar tana yinkwfa

Shi kuwa Hashim dakin dake kusa da na nihla ya shigar da meenat yace Nan ne dakin ta ya Mata bayanin wasu abubuwa harda kayanta da tace ya karbo mata a wurin Jamila ya karbo mata Kuma ya siya Mata wasu ta Masa godiya kafin ta nemi wuri ta zauna akan kujera tana yi ma Hashim godiya tare da Ce Masa Dan Allah inta Kara samun sauki yakaita wurin kakar ta Kuma ya amsa Mata  sanan ya fice.

Nihla CE ta shigo tana ambatar suna mom!mom! Zainab ta amsa Mata ciki² tace mom Wai da gaske ne dad ya kawo wanam ‘kazamar yarinyar gidan Nan zainab ta tabe Baki tace eh “baze yuyu ba mom dole ‘kazamar yarinyar Nan ta bar gidan Nan bazan iya Zama gida daya da it’s ba kin ji mom dan Allah kiyi yarda zakiyi tabar Mana gida”

Hashim ne yake saukowa daga step din a hankali Yana tafiya Yana kallon yarda nihla ta sakankance tana yiwa zainab magana da alama maganar me muhimmanci sukeyi shidai bece musu ‘kala ba ya fice abinsa Basu ma lura dashi ba Dan shi yanzu lamarin nihla haushi take bashi ne San Ina ta dauko wanna mumunar dabiar ba……

Meenat kuwa da ta gaji da Zama itama saukowa tayi dan Koo zata Taya su aiki lokacin da ta sauko ba kowa a palon Dan haka tayi tana gyra gashin kanta da ta wanke……

Nihla ce ta fito cikin want Dan karamin siket da Riga karama itama me hanun vest ta Kama gashin ta wiring day tayi kyau sosai Kamar baturiya haka tai kyau ta karaso inda meenat take seta toshe hanci tana fadin “ohh meke wari haka tana maganar ne tana daga Kai alamar neman abinda yake warin takeyi see kuma ta dawo da kallon ta ga meenat wace ta tsira Mata Ido tana kallon ta

“O my God!! Dama kene like wari Kamar mushe Kai gaskiya Baki had’u ba” ta fada tana damkar gashin kan meenat wace seda ta saki y’ar Kara ta saki sanan nihla tace………….

Kuna ganin Anya nihla da zainab sunyiwa kansu adalci akan Hashim ya kawo yarinya gidan suke wanna abin to ya kukr gani idan Hashim ya gano meenat y’arshi ce wani irin Hali nihla da zainab zasu shiga kudai cigaba da bina………………..

2

Fatiman ku ce👌Y’AR ZINA CE

    (KADDARAR IYAYENA)

Muneera

Hakika banida bakin godiya a gareku sedai in muku fatan Alkhairi har karshen Rayuwa masoyan littafin Allah ya bar kauna tsakanin mu love you wujiga wujiga 😂😂

Pg~16

Kuma Jan gashin meenat nihla tayi da karfi tanayi tana kylkyla dariya gami da fadin Kai wanan kayan warin gwra a tsige shi meenat da karfin ta gaba daya ta had’a ta ture nihla da karfi ai kuwa tuni tayi tangad’i ta Fadi ‘kasa zainab ta ‘karaso da gudu tana rike Nihla da ta tsala wata uwar ‘kara

Meenat ganin haka yasata tashi zata gudu Amma seta hantsila ta Fadi sakamakon ‘kafa da zainab tasa Mata bakin ta ya hadu da tiles din se jini ya fara zuba a bakin ganin jini nata zuba yasa meenat sakin kuka me karfi zainab kuwa da nihla dariya suka sa suna nuna meenat da hannu sanan zainab ta dauki nihla suka bar wurin suna ta dariya nihla harda yiwa meenat gwlo.

Zama tayi tana kuka tare da kallon jinin dake fitowa daga bakinta, mamana ya Zaki tafi kibarni wayoo ni ta fada tana share kwlar idon ta, tashi tayi da kyar ta fara tafiya, baba talati ce ta gano ta da Dan gudu² ta karaso ta dauketa ta tafi da ita boys quarters din da suke zaune ta wankewa meenat bakin tana Mata tare da tambayar ta garin Yaya hakan ta faru, girgida Kai kawai tayi tace faduwa tayi.+

Baba talatu na Aiki meenat na Taya ta suna danyin Hira time-time haka Nan baba talatu taji tana son yarinyar saboda yarda ta lura yarinyar batada hayaniya Kuma Bata da Rawar kai gata a nutse take gata da Aiki.

A zuciyar ta tace dama haka Nihla take da taji dadin halinta Amma yarinya se girman Kai da jiji dakai da Raina na gaba da ita, Meenat ce ta dawo da ita daga tunanin data tafi tace baba wanan Ina za’a ajiye, baba talatu ta kad’a Kai tana karbar abinda meenat take tambayar inda zata ajiye shi.

Yarda meenat take yin Abu se baba talatu ta tuna da sakina y’ar jikar Yar uwata yarinyar tana mata Kama da sakina sosai se Kuma ta tuna da Hashim da ya yodari sakina ya gudu tabbas tasan Hashim tun kafin tazo aiki gidan tasan lokacin da yaje bautar ‘kasa garin su har ya yodari sakina lokacin da ta baro garin dai tasan hafsatu ta fada Mata abinda sakina tayi har hakan yasa su barin garin sanan se daga baya taji Rasuwar sakina Amma tasan sakina ta haifi y’ar ta mace Bata san dai sunan yarinyar ba.

Baba talatu ta kalli meenat tace ya sunan ki” meenat tayi murmushi ta kullum cikin say take Koda ranta a bace yake tace sunana meenat, baba ta Kuma tambayar ta ya sunan garin ku tace RIKADAWA baba talatu ta zare Ido Kar dai zargin ta ya Zama gaskiya wanan yarinyar y’ar Hashim da sakina ce ta Kuma tambayar ta Ina mamanki, meenat idon ta yadan ciko da kwla tace ta rasu baba talatu da hanzari tace ya sunanta meenat tace SAKINA zare Ido baba talatu tayi tana fadin yarinya tazo gidan ubanta ta Kuma tambayar ta ya sunan kakar taki kikace meenat tace hafsa  ya sunan kawun mamanki meenat tace  Audu da sauri baba talatu ta rungometa tana fadin wallahi kece.

Meenat tayi saroro tana kallon Baba talatu kamar wata zautaciyya tace baba talatu tace ya sunan babanki meenat ta fashe da kuka tace har mamana ta rasu Bata fada min sunan sa ba Kuma bansan shi ba Amma banida burin da ya wuce na ganshi a Rayuwa ta baba talatu tace karki damu kinji ni zanyi kokarin ganin na had’aki da mahaifin ki meenat ta sa dariya tace Dan Allah baba talatu tace Mata eh Mana sanan Kuma duk abinda matar gidan Nan zata Miki karki kulata kinji meenat ta gyda Kai sanan baba talatu tace ita Kuma nihla komai ta Miki ki Rama karkiji tsoro Nan ma meenat ta kad’a Mata Kai tace Bari na kirawo kakar ki a waya see kuyi magana Koo meenat ta daga Mata kai.

Baba talatu ta dannawa kaka Kira bugu biyu ta dauka ta na kuka baba talatu tacewa Kaka meyasata kuka, Kaka ta goge kwlar idon ta tace, talatu gidan Aikin da aka Kai yarinya Nan Amina anje sunce ta gudu.

Baba talatu ta danyi murmushi tace hafsatu Ai gani ga Amina a kiss Dani Kaka ta Dan zabura tace talatu banson shirme baba talatu tace inbaki yarda Bari na Baki it’s kuyi magana baba talatu ta mikawa Meenat, meenat tace Kaka Ina wuni wasu hawayen me suka zubuwa Kaka tace Aminatu na meenat ta amsa suka danyi Hira hankalin Kaka ya Dan kwnta , meenat da baba talatu suka cigaba da Hira baba talatu na bawa meenat labarin kuruciyar sakina sunata dariya abinsu

Koda Hashim ya dawo da gudu Nihla ta taho ta rungume shi, Shima ya rungometa Amma gaba daya hankalin sa ba akanta yake ba tureta yayi gamida Hawa step din binshi tayi da kallo saboda be taba Mata haka ba A razane ya fito Yana tambayar zainab Ina meenat wace ta tamke Rai ko kallon shi batai ba, Ina meenat nace Miki zainab da karfi had’e da tsawa itama tace ajiyar ta ka bani da zakazo kana tambaya ta toh bansan inda take ba take wani mugun tsaki tana komawa ta zauna idon shi ne da ya fara canza launi jijiyoyin jikinsa suka tashi da karfi ya Kuma cewa zainab Ina meenat…………..

🙄🙄🙄🙄ni jikar sule nace zainab Gwra ma ki Nemo Masa ita ohh su zainab ko kunya ba aji 🙄 shi Yana Rike da yarki shi ya kawo Miki ajiya shine like Rashin mutunci mudai je zuwa

Wayoo ni masu cewa Ina typing ‘kafan to afuwa nake nema🙄 domin ni lazy writer ce 🤣😂 Dan habibty ma haka ta gani ta Kyle kudai cigaba da hakuri har mukai karshe book din I love irin da yawa da yawa dinan

Fatiman ku ce 👌Y’AR ZINA CE

    (KADDARAR IYAYENA)

PG~17

Muneera

Tagumi zaman jiran ruwan comments din ku 😂😂

Meenat dake tsaye a kofar palon ta ‘karaso ta Rike hanun Hashim tace yallabai gani naje wurin baba talatu ne ya kama hanun ta sanan baba talatu ta karaso tace Hashim Ina son yin magana dakai ba shi kadai ba harsu nihla abin ya Basu mamaki Jin ta Kira sunan Hashim din abinda Bata taba kullum sedai tace yallabai “baba gani ya akayi” ya fada yana hadeye wani makolato tace Ina so muyi magana ne a sirri ba kowa see yaji ba ta fada tana harar inda zainab take, zainab ta tabe Baki taja hanun nihla suka bar wurin baba talatu ta karaso inda Hashim yake tace “Ina fatan dai kasan sakina ta kauyen madobi” ji yayi cikin sa ya murda ya daga Kai Alamar eh da Kuma mamakin ya akai baba talatu tasan sakina , tace “Ina fatan kasan ka tafi ka bar sakina da ciki daka mata” zare Ido ya farayi yana goge zufa tare da girgida Kai Alamar A’a tace to ka tafi ka bar sakina da ciki Wanda cikin shine meenat ai gaba daya ya Gama rikicewa saboda tsabar kidima seda yaji kamar ya fadi.

+

Baba talatu tai tafiya ta, tabar shi a wurin ya durkushe ya kasa cewa komai see hawayen da suka fara zarya a idon sa Yana fadin wayoo ni Hashim na shige su.

Baba talatu zuciya fess ta karasa bangaren su tana jiran Me gidanta ya shigo ta sanar Masa da maganar(dake mijinta shine me gadin gidan)

Meenat kuwa kwnce take Akan makeken gadon nata ba abinsa take see tunanin Ina mahaifin ta yake ya za’ayi ta hadu da mahaifin ta, Taya zata nuna Masa tsantsar soyyar ta gareshi Dan burinta gaba daya na duniya shine ta ganshi ya fada Mata karue ne kalmar YAR ZINA da ake kiranta dashi ya Bata sunan mahaifi ta Dena amfani da sunan gari wanan shine burinta yaushe burin Nan nata ze cika ta fada tana firzar da iska m zafi maganar baba talatu ta tuna na cewa komi rimtsi karta bar gidan in nihla ta Mata Abu ta Rama har ta dinga kylewa Kuma zata temaka Mata wajem ganin sunyi dealing din Nihla tunda Bata da kunya se sun ladabtar da ita murmushi muguta meenat tayi tace nihla Zaki sani ne

(Kome meenat da baba talatu sure shiryawa Alan nihla ohoo😂😂)

Wanka tayi tai sallah ta kwnta abinta tana jiran lokaci yayi taje ta Taya baba talatu aiki

Koda zainab taja nihla sukai daki, kuka nihlan tasa tana fadin wallahi nidai kawai mom kisa dad ya Kori yarinyar Nan bana son ta, zainab ta dafa kafadar nihla tace baby na relax pls karki manta fa ke yar me gidan Nan ce wato senator Kuma baban senator da ake ji dashi a garin Nan way be San mahaifin ki ba ita Kuma wace Yar kauye ce fa please ki dena Had a kanki da ita har kina jin kishi da ita saboda Bata Kai matsayin da Zaki kishi da ita ba.

Nihla ta Kuma shagwbe fuska sanan tace Alright mom but….see Kuma tayi shiru , zainab tace but what? Shiru ta kumayi hakan me yasa zainab fadin just go out, kallon ta nihla tayi tace mom korana kike? Dafe Kai zainab tayi tace no kawai Ina son hutawa ne so ki barni na huta nihla ta saki wani uban tsaki tanayim waje, tana fita zainab ta Mike tsaye tana zagayem dakin gameda fadin gaskiya akwai lauje cikin nad’i  Hashim always abinda yake boyewa gameda yarinyar Nan

Hashim seda yasha kukan sa sanan ya Mike ya nufi bangaren su baba talatu domin yanada tambayoyi fall abakin shi tafiya yake Amma hankalinsa ba’a jikinsa yake ba har ya karaso wurin baba talatu ya gani tana gyran wake tana cin goro hankalin ta kwnce Hashim ya iso baba ta Kuma tamke fuska yau Sega Hashim da gaishe da baba talatu ta Amsa ciki² Dan ita fa hauahin sa takeji kan abinda yayiwa sakina yace baba Dan Allah sakinan yanzu tana wani gari ne? Seda ta Bali goronta tace tana kabari a kid’ime ya kale ta yace, Baba talatu karki ce min sakina ta rasu, eh ta rasu Allah ya amshi abarsa mikewa yayi ya nufi ciki Yana hawaye me cike da abubuwa da yawa.

Meenat kuwa tana tashi la’asar tayi Dan haka sallah tayi ta zauna tana tunanin mamanta yarda take nuna Mata kulawa, A kullum kalmar ta gareta shine”meenatu na ko bayan ba ni ki Kare mutunci ki kinji” tun tana Yar shekara 3 kacal a duniya mahaifiyarta ta take fada Mata wanan kalmar da har yau Bata San fassarar ta ba.

Jin an  bude kofa yasa ta dago Kai ta kalli waye Hashim ta gani idanuwa sun ciciko da hawaye ta karasa da gudu tana Jan hanun shi har bakin gadon ta zaunar dashi tace “yallabai waya dake ka” kallon ta yayi kawai see ya rungometa Yana fadin ki yafe mineenat yallabai aini bakai min komi ta fada tana gogeasa hawayen dake ta zarya a idon sa ba kakwtawa, yallabai kayi shiru na baka want labari shiru yayi tace

Mamana nacewa kuka ya kumshi abubuwa da yawa a rayuwa yallabai tace Akwai kuka na Dana sanin Wanda Dana sanin baze maka amfani ba saboda lokaci ya kure sanan akwai kuka na zafi, wato zafin iri iri ne yallabai tace Akwai zafi na mutuwa Wanda idan mutum ya mutu ana Masa kuka, wanan kukan da akeyi bawai shi Wanda ya mutu ne akewa kukan Aa tace Wanda be mutu ba kansa yakewa kuka domin shi Wanda ya mutu tashi ta rigada takare yallabai a cikin kukan Nan da akeyi akwai Wanda kakeyi kodai kukan Dana sani ko Kuma kukan wani Abu da ya maka zafi Koo?

Shiru yayi ya tsurawa yarinyar Ido tabbas wanna ko tantama babu Yar sakina ce saboda koshi sakina Tasha fada masa wanan kalmar maganar meenat CE ta dawo dashi daga tunanin da ya tafi tace yallabai kayi hakuri kanemi mafita akan abinda kake so bawai kayi kuka ba ya gyda Mata Kai yace to tace kamar ni yallabai kaga kullum mafita nake nema akan na hadu da mahaifina ya fada min cewa kalmar y’ar Zina da mutane ke fadamin karyane ba gaskiya ba Kuma ya fada min sunanshi na dinga amfani da sunan mahaifina vawai sunan gari ba……………..

Jim hayaniya a kasa tayi yawa yacewa meenat tazo suje suga meke faruwa ne Nima binsu nayi Dan dauko muku rahoto👀✍️

Fatiman ku ce 👌Y’AR ZINA CE

     (KADDARAR IYAYENA)

Muneera

Pg~18

Saukowa yayi Yana me Jin gaban shi ya Fadi… Mommy ya gani lamido na shigo Mata da akwaitin kayan ta cikin palon a sanyaye Hashim ya karaso meenat na bayanshi Mommy ta Kama kumatun Hashim tana fadin surprise Dan murmusawa yayi yace mommy zakizo Amma ko kirana bakiyi kin sanar Dani ba mu shiryawa zuwanki, No my son inaso na maka surprise ne ta karasa maganar tana kallon meenat dake bayan Hashim suka karasa kan kujera tana fadin my son Ina ka samo yarinya me Kama dakai haka….. Dasss gaban shi ya Fadi ya kalli meenat ita kuwa meenat seta tsuguna tana gaida mommy jawota tayi tana ya sunanki baby?” Meenat ” mom tace Masha Allah ta maida kallon ta ga Hashim kenan zatai magana taji an rungometa ba tantama tasan zainab ce.

Mommy tayi dariya tana ture zainab tare da fadin Wai ke Kam har yanzu Baki girma ba, turo Baki tayi tana fadin mommy nidai har yanzu yarinya ce a wurin ki gaba daya suka sa dariya zainab taja hanun mommy tayi daki da ita ta hada Mata ruwan wanka tayi wanka ta huta ta fito gani tayi har an cika dining da abinci zainab na ta Kai kawo itada baba talatu meenat ta hango ta window a bayan gidan ta leka see taga yarinyar na hawaye tana Kuma rera wa’ka a lokaci guda.

+

“Mutuwa yanki kauna, mamana kin tafi kin barni lokaci da nake tsananin bukatar ki a rayuwata mamana me yasa Baki nuna min babana ba kafin ki tafi mamana dan Allah ki nuna min babana wayyo ni Aminatu NAGA TA KAINA ta karasa tana share kwlar idonta”

Mommy juyawa tayi zata zagaya taga yarinyar Amma Jin And Rike Mata yasata fadin nihla kece nayi fushi see yanzu Zaki zo yi min sannu da zuwa Aa mommy ni bacci nake yanzu na tashi, toh Yar tsuhuwa Nan sannu da zuwa mommy tayi murmushi tace toh sabuwa yauwa dukan su suka tuntsire da dariya nihla taja hannun Kaka sukayi dining da ita taja kujera ta zaunar da ita sanan ta zauna kusa da ita

Hashim ya fito Yana karasa ‘bale  ma’balin Rigarsa harze zauna see ya tuna meenat tace tana wake zata Sha iska ne da sauri yayi hanyar fita mommy tace Ina zaka yace Meenat Zan dauko tuni fara’ar nihla da zainab ta dauke mommy kuwa murmusawa tayi tace lalai son kana ji da Meenat Dina nan

Samin ta yayi ta hada Kai da gwaiwa ta lulaka cikin tunanin domin sau bit yana Kiran sunan ta Bata amsa ba seda ya taba ta, ta dago Kai fuska shabe² da hawaye a razane yace me akayi Miki girgida Kai tayi tace babana nake tunani karki damu yau Zaki ganshi kinji meenat ta girgida Kai tace da gaske ya daga Mata alamar eh sanan ya dauketa, Bata San meyasa ba a duk lokacin daya dauketa setaji want sanyi a ranta ko da kuwa tana cikin damuwa in taganshi tanajin damuwar tata ta kau.

Katse mata tunani yayi Jin ya zaunar da ita a daya daga cikin kunerun dining din da sauri ta sauka tana fadin yallabai Anya kuwa naci abinci da masu gida bayan ni ba kowa bace afuwa yallabai nidai zanje naji da baba talatu ta fada tana yunkurin juyawa, da sauri Hashim ya riketa Yana fadin haba meenat wayace Miki me ba Yar gidan Nan bace bayan ke y’ata ce nine ubanki duniya da lahira cikin janye jiki daga nashi cike da firgici take kallon shi wanda ba it’s kadai ba har nihla da zainab seda suka razana mommy kuwa Koo gezau batayi ba domin ya fada Mata komai a waya dalilin daya kawota kenan ma.

Nihla ta karaso tace dad mekake nufi kana nufin wanan kazamar yarinyar y’ar ka ce ta Yaya dad bayan duk duniya kowa yasan ni kadai ce Y’ar ka dad talk to me ta fada wasu zafafan hawaye nafitowa daga idon ta kafin ya Bata amsa meenat ta Kuma jefo Masa wata tambayar tace yallabai ta Yaya ka Zama babana Aa bakai bane tabbas shine mahaifin ki sukaji baba talatu na Fadi daga nesa, Rungome shi meenat tayi tana hawaye Shima ya rungometa Yana hawayen farin ciki suka bar nihla da sakin Baki tana kuka.

Jin an danki wuyan bayan Rigarsa yasashi juyawa Hashim dama bayan ni kanada karuwa van sani ba kalmar karuwa ta doke zuciyar sa da yawa yace eh inada ita har da yarinya a tsakanin mu hawaye suka fara zarya a kuncin ta tace Hashim ya Zak min haka meyasa zaka min haka tsaki yaja sedai Jin tassss a fuskar shi yasashi kallon wace ta mare shi wace ba kowa bace illa mommy tana marin nashi taja hanun meenat sukayi dakin ta da ita, Shima juyawa yayi ze bar wurin nihla ta ruko Rigarsa tace dad dama bani kadai ce Y’ar ka ba dad dama kanada wata bayan ni dad pls tell me ta fada tana goge hawayen idon ta jawota yake yunkurin you Amma tuni zainab ta janye ta tana fadin karka sake ka taba min y’a Hashim ta fada maka,kallon ta yayi yace Zainab ki saurare ni karki ce Zaki yunkurin rabani da nihla domin y’a tace bame canza hakan wani miskilin murmushi ta saki tace Hashim kenan nihla ya tace Nika dai yace karya kike zainab Nima nihla y’a tace ba Kuma Wanda ya Isa ya canza wanan………………👀✍️

Nanfa akeyin ta tsakanin Hashim da zainab Kai harma da nihla da meenat

Fatiman ku ce 👌Y’AR ZINA CE

     (KADDARAR IYAYENA)

Muneera

Y’AR ZINA CE

     (KADDARAR IYAYENA)

MUNEERA

PG~19

Ya Isa mom Nihla ta fada tana huci gaba dayansu shiru sukai suna kallon ta, tace “Wai meke Shirin faruwa ne dad” yayi saurin karasowa yace my princess ba abinda ze faru kinji maza tafi dakin ki ya karasa maganar Yana kallon Zainab da itama take yunkurin yin dakinta tana hawaye Wanda suke tatare da abubuwa da dama shi Kuma Hashim zubewa yayi a wurin Yana wasu zafafan hawaye Shima Wanda kukan da yake shi yafi na kowa a cikin su subhanallilah ya fada yana ya rabbi ka shiga lamarina.

+

A sukwne yayi dakin sa ya nemi bakin gadon ya xauna se Kuma ya fashe da kuka Yana fadin “sakina ki yafe min na cuce ki sakina Amma inshaAllah Zan zamewa meenat garkuwa nasan Zaki farin ciki da hakan sakina na cuce ki na cuci kaina ya Allah kana ganin halin da na shiga nida iyalina ya rabbi ka kawo Mana dauki da gagawa nida ke gefe na amsa Masa da Amin👀

A bangaren mommy kuwa tunda ta shiga daki da meenat ta zaunar da ita kan cinyar ta tana kuka Wai yau Hashim ne da yarinya da aka Haifa Bata hanyar aure ba tasan iya tarbiyya ta bawa Hashim sedai Bata San lokacin dayayi wanna aika² ba ta Kuma kallon meenat wace kallo daya zaka Mata kagane tana cikin tsantsar farin ciki da annushuwa mommy ta goge kwlar ta, tana fadin meenat ya sunanki na gaskiya tace hajiya sunana Amina mamana ta cemin sunan kakata ta wurin babana aka samin mommy ta jawota tace tabbas wanan hakane meenat Allah ya jikan maman ki Meenat ta amsa da Ameen tana kokarin mikewa. 

Da sauri mommy ta Rike hanun ta tana fadin meenat Ina Zaki juyowa tayi tana fadin ai mommy wurin baba talatu zanje mommy tayi murmushi tace Aa yau kam baba talatu sedai tayi hakuri domin kuwa yau a wurina Zaki kwna k ba kyson kiyi Hira da kakar taki. Meenat ta Dan yi murmushi Wanda dabi’ar ta ne a Koda yaushe tace mommy inason Hira dake Mana Yar tsohuwa mommy tayi dariya tana fadin ja’ira ni kike tsokana. Meenat ta say dariya tana fadin ai dama ke tsohuwar CE takaice dai kafin wani lokaci mommy da meenat sun Saba se hira suke abinsu Wanda meenat tasa mommy har ta fara manta kunci da take ciki.

Bangaren nihla kuwa ta kasa zaune ta kasa tsaye se mamaki da kuka take ta Yaya za’ace baban ta Yana da wata diyar a waje bayan ita wanan abinda baze yuyu bane se ta San yarda zatayi ta kore yarinyar Nan daga gidan to me ake nufi kanwar tace koo Kuma yayarta? Ita kadai tai tayiwa kanta tambayoyi Wanda ta rasa me amsa Mata a karshe dai ta kwnta tanata nazarin abubuwa da dama.

Zainab kuwa kule kanta tayi a daki tana kuka Wanda Bata San kukan me takeyi ba kukan Hashim ya yodare ta takeyi ko kuwa kukan kasancewar meenat yarsa? Tayaya hashim yayi karuwa a waje Kai wanan lamari da Rikitarwa yake ta dafe kanta saboda wani irin sarawa da yake Mata kwantawa tayi ta dinga juye² tana sakawa da warwarewa.

A wanan dare babu wanda ya rintsa se meenat da ita kadai ce take farin ciki Amma daga hashim, nihla, meenat da mommy ba Wanda ya Runtsa

Shi Hashim kwna yayi akan daduma Yana rokon Allah ya ha‌da Masa kan iyalinsa Baki daya domin yasan akwai baban ya’ki a a gabansa Wanda ze shirya Masa Dan yasan da wuya zainab ta kar’bi meenat a matsayin y’arshi tabbas da kalubale babba a gabansa

Zainab kuwa kwna tayi tana sa’ka yarda akayi Hashim yayi karuwa a waje Bata sani ba

Mommy ma a zaune ta kwna tana tunanin ta Yaya yarda zata fuskanci Abban Hashim da maganar meenat ta juya ta kalli meenat ta shafa kanta tana fadin yarinya me hankali.

Washer gari

Dukan su suna zaune akan dining din daga hashim har zainab da mommy fuskar su babu walwala a cikin ta, meenat ganin baban nata Yana jujuya cokali yasa ta mikewa ta kar’bi spoon din gaba daya hankalin su ya koma kanta Zama tayi a cinyarshi ta debo abincin ta nufi bakin shi dashi Lamar kuwa want soko ya bude bakin shi ta ma sa abincin a Baki ya cinye nihla dake gefe ta saki wani uban tsaki ta Mike ta bar wurin domin zuwa Shirin school

Mommy ta kalli Hashim fuska babu anuri tace hashim inaso yau ka Kai meenat school wace nihla takeyi da sauri zainab ta dago tace Amma mommy….. Yi min shiru zainab bana son jin komai abinda na fada shi za’ayi zainab tana kunkuni taja bakin ta tayi🤐.

Mommy dakan ta taja nihla sukayi daki ta Mata wanka ta shirya ta sanan ta fito dai² lokacin nihla da Hashim suka fito, Hashim ya Rike hannun duka su biyun suka fice mommy dake bayan su ta goge kwlar idonta.

Suna sauka nihla tayi class yayinda Hashim ya wuce da meenat office din me makaranta meenat se murna take tana tambayar Hashim yana Bata amsa.

Me makarantar ya kalli Hashim yace lalai yarinyar Nan take akwaita da kokari zamu kaita primary 2 class din  su y’ar uwarta kenan Hashim yace toh hakan ma ba lefi a Nan aka bawa meenat uniform ta shiga wani daki a office ta canza ta fito uniform din sun Mata kyau sosai Hashim yace ayi karatu dakyau kinji Yar Albarka tace inshallah  Nan me makaranta ya Kira me kula da yaran yace takai meenat pri-2 tace owk

Da fara’a ta shiga class din Yan class din suka zuba Mata Ido Malamar ta kale ta cikin harshem turanci ta tambaye ta sunan ta meenat tace Amina Hashim usman, nihla da ta cika tayi famm ta taso tace, duk wanda yake garin nan yasan babana nikadai y’arshi nikadai ya Haifa Kuma matar shi guda days CE mamana kenan Kuma ke ba Yar mamana bace wace mamanki? Meenat idonta suka ciko da kwla nihla ta cigaba da cewa ni kadai ce ohhh na manta kefa Yar karuwan babana ce ke Y’AR ZINA CE…………………✍️

FATIMAN KU CE👌Y’AR ZINA CE

       (KADDARAR IYAYENA)

MUNEERA

KAMAR YARDA KUKE GANI MUNZO PAGE 20 TOH FA DAMA DAGA NAN NAYI ALKAWARIN DENA TURAWA DAGA FARKO🙏SABODA GASKIYA TURAWA DG FARKON NAN YANA TSAIDA MIN NETWORK KUMA DA WANE MUTUM ZEJI GA TYPING GA FAMAN TURAWA DAGA FARKO.

Pg~20

Hawayen idon meenat da suka ciciko suka karasa gangarowa kan kuncinta nihla tayi yunkurin Kara yin magana Amma da sauri Malamar tasu ta rukota tana magana cikin harshen turanci tace nihla je ki samu wuri ki zauna Yan ajin Kuma tuni se maganganu suke kan lamarin nihla da meenat sanan Malamar ta kalli meenat ta Bata wurin Zama har aka tashi meenat kuka take ta Riga nihla fitowa taga driver nasu ta tsuguna har kasa ta gaidashi shi Kuma Yana tambayar ta lafiya take kuka tace Masa faduwa tayi yazo ze bude Mata mota ta shiga ta hanashi cike da girmamawa tace ai zata iya budewa ta bude ta shiga ta zauna ta cigaba da kukan ta seda suka kusan Rabin Awa suna jiran nihla sanan ta fito tana zuwa ta fara zazagawa driver masifa Wai kan tun da ya ganota be karaso ya karbi Jakarta ba Wanda akala mutumin yayi jika da ita duk abinda suke akan idon meenat tana tirrr da Hali irin na nihla jiki na rawa ya bude Mata baya ta shiga.

+

Kallon meenat tayi tace dalla malama koma gaba meenat ta Mata banza kamar Bata jita ba ta cigaba da kukan ta, bazaki koma ba Ina Miki magana meenat tai Mata shiru shi kuwa Driver yaja motar suka tafi Yana Allah wadaran nihla da halin ta har suka karaso meenat na kuka idon ta yayi jajir duk sun kumbura fuskar Nan tayi jajir kamar kanta har wani sarawa yake saboda yau it’s cin mutunci nihla ta Mata shi Wanda bata taba tsamani ba har suka karasa cikin gidan tana goge kwlar idon ta Hashim da lokacin ya fito ze wuce office ya hango su nihla ma shi ta gano ta tafi da gudu zata rungomeshi Amma se ya kwce yayo inda meenat take tana goge kwlar idonta  janta yayi a jikin sa Yana fadin me aka miki? Waya taba

ki? Ko makaranta ce baky so ta girgida Kai tana kallon Nihla wace se zazare Ido take Kar meenat ta Fadi Abinda ta aikata ta dawo da kallon ta kan Hashim tace da zafi sosai wata kwlar ta Kara fitowa daga idon nata Hashim yace menene da zafi tace faduwa nayi a rikice yace A Ina Kika Fadi bakiji ciwo ba Koo? Tace da ciwo dole ne ya min ciwo,Amma baze fito ba kasa inda maganar meenat ta dosa yayi yace muga inda kikaji ciwon ta girgida Kai tace bnji ba kawai ta fada tayi gaba Shima yabi bayanta da sauri Yana Kuma tambayar ta (da yake Hashim irin mutumin Nan ne me kulaficin yara baya so yaga Abu kankani ya samu danshi).

Nihla shiru tayi seta ji kwla na neman zubowa daga idon ta Wai yau itace dad dinta ko kallon ta be yiba baleya tambayeta ya school ko ta kanta be biba burin shi kawai yaga wacen kazamar yarinyar cikin farin ciki kafin ta Kara wani tunanin se ganin Hashim tayi a gaban ta Yana fadin nihla me ya samu Yar uwar ki kallon shi tayi galala kamar wata sokowa tace dad yanzu baka so na Koo? Se ya sauke wata ajiyar zuciya yace no meya faru nihla tace dad yanzu kafi son wacen kazamar yarinyar gashi ma ka Dena ce min princess dafe Kai yayi yace sorry my princess Naga y’ar uwarki na kuka na kuka ne and……

Aa dad yanzufa baka sona ta fada tana yin dakinta da gudu duk abinda suke mommy na kallon su ta window tayi murmushi tace Hashim ka fara gwgwrmaya kenan toh Allah ya bada sa’a ta koma ta kwnta abinta ranta fess Amma tana me yiwa Dan nata addu’ar Allah ya bashi ikon had’a kan iyalin nasa

Meenat kuwa Koda ta shiga daki uniform dinta ta cire tayi wanka tasa Kaya sanan ta hau kan makeken gadon nata tana tunanin to su Nan ba’a yin islamia ko kuwa karatun qur’ani ta dinga yi a zuciyar ta a haka har tayi bacci

Hashim Yana zaune wayar shi ta fara Ringing dauka yayi banji me akace Masa ba Amma Naga idon shi yayi jajir da karfi ya fara Kiran sunan nihla da meenat Wanda ya fargar da duk Yan gidan ya zainab ce ta fara fitowa ya kaleta Yana fadin Ina nihla da karfi Wanda seda ita kanta ta tsorata.

Meenat ma ta fito mommy ma ta fito nihla ma a dadarare ta fito tana yin bayan zainab a fusace yaje ya figota Yana fadin

Abinda kikaje kikayi a school kenan iyeee dake nake magana nihla ta zazaro Ido tana Kuma yin bayan zainab yaje ya jawo hannun meenat yace kinganta Koo? To ba ita Kika tozarta ba ni kika tozarata ni ubanki ni Kika wulakanta a idon duniya nihla ni Kika ciwa mutunci kince meenat y’ar Zina Koo to ke Y’AR…… Zainab tai saurin toshe Masa Baki tana fadin kayi hakuri Mana Yaya Hashim bazata Kara ba Dan Allah kayi hakuri kayi shiru haka Kar bacin Rai yasa ka Fadi kalmar da zakayi Dana sanin ta. Ya fuzge hanun ta daga bakin shi ya tsuguna ya kalli meenat yace dama shine abinda ya Miki ciwo shine ya Miki zafi ta girgida Kai toh meyasa Baki fada min gaskiya ba?.

Sedai meenat batakai ga bashi amsa ba sukaji taku alamun shigowa sukaji gaba daya hankalin su ya koma kan Wanda yake kokarin shigowa ba kowa bane I’ll daddy din Hashim……..✍️

Kuna ganin daddyn Hashim ze karbi meenat a matsayin jika to ya maganar Kaka Kuma Wai Ina labarin kawu audu Mutuwa yayi ko Kuma Yana Raye toh in Yana Raye Yana Ina? Ya kuke ganin meenat zatayi rayuwa a gidan hashim, toh waima me ya jawo mutuwar sakina? Ya kuke ganin nihla zatayi in ta gano ba Hashim ne mahaifin ta ba? In Kabir ya bayyana Kuma fa? Wai shin labarin da zainab ta bawa Hashim Akan Kabir fyde ya Mata gaskiya ne mu hadu A PART 2

FATIMAN KU CE

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *