YAR ZINA CE CHAPTER B KARSHE
Y’AR ZINA CE
(KADDARAR IYAYENA)
MUNEERA
PART 2 PG~1
HAKIKA A KULLUM KUNA RAINA INAYIN KU IRIN OVER DINAN PAGE DIN NAN NAKU NE KU KADAI
My jidodo
Fulani Mrs iliyasu
Ummie mama
Rashida Muhammad
Mmn Jawad
Nusaiba
Aunty Khadija
Real Aunty zee
Aysher gombe
Mmn twins
Nana bawa
Khady pinky
Mmn fukaihat
Mummyn harun
Yancy
Mummjay
Aynah
Sakina
Oubi
Habeeebatee
Maman Amira
Mommyn sayeed&noor
Binta unknown
Fatima saulawa
Jidda🌹
Miss independent
Hjy Aisha
Mmn Arphat
Mmn sameer
+
WASH GASKIYA KUNA DA YAWA BAZAN IYA LISSAFO KU DUKA BA AMMA KUSANI INAYIN KU OVER
Gaban Hashim ne ya Fadi ya Rike hanun meenat tsam ajikinsa ya dage ya hado kalmomin daze ma Abban nashi sannu da zuwa.
Karasowa yayi fuskar shi dai ba yabo ba falassa Hashim ji yake kamar ya arta a guje saboda irin kallon da Abban nashi yake Masa.
Da kyar ya hadiye want yawo yace “Abba barka da ‘karasowa”
Be Amsa ba ya maida kallon shi ga mommy wace itama ta had’e fuska babu alamin annuri a tatare da ita saboda tasan halin mijin nata tinda ta sanar Masa da labarin meenat da Hashim a waya be ‘kara kiranta a waya ba Kuma Koo yau da zezo be sanar Mata da zuwan nashi ba.
Zainab cikin farin ciki da nuna Jin dadin zuwan Abban tace “Abba Bismillah ka karaso Mana”
Bece da ita ‘kala ba ya ‘karasa kan kujerar ya zauna Yana mommy ma ta nemi wuri ta zauna
Hashim da yaki sakin hanun meenat suka zauna, zainab taja hanun nihla suka zauna suma duk kansu a ‘kasa (saboda baban hashim mutum ne me tsatsaran ra’ayi Amma Kuma Yana tsananin son hashim din saboda shi kadai Allah ya bashi)
Ya kalli Hashim yace “Hashim” ji yayi Kayan cikinsa su haitsune ya Amsa murya a da’kile.
Ya kalli mommy yace “Amina” itama ta amsa sanan ya kalli zainab itama ya Kira sunan ta itama ta Amsa sanan ya fara magana
“Ha’ki’ka naji duk abinda ya faru inaso ku bude kunuwan ky dakyau kujini abinda ya faru dai ya Riga ya faru KADDARA TA RIGA FATA seda mu rungometa hannu bibiyu” ya kalli meenat yayi Mata nuni da kusada shi alamun tazo ta tashi ta karasa wurin da ya nuna Mata yace
“Ya sunan ki?”
Meenat tace “Amina (meenat)”
Ya rungometa a jikinsa ya kalli zainab yace zainab wanan yarinya dai Amana ce a wurin ku duka kece uwa ke Zaki kokarin had’a kan yaranki wato nihla da ita Meenat.
Zainab ta Dan goge kwlar idon ta tace insshaa Allah Abba
Yace toh tare da kallon Hashim yace kaikuma seka kiyaye gaba ya Amsa da toh sanan yace ki shirya gaba daya gobe duka zamu ne kauyen Ridawan suka Amsa da toh
Washer gari👉
Gaba daya sun Gama shiri, suka hau jirgi daga Abuja zuwa Kano sun karasa gida sun Kuma yin wanka suka shirya sanan suka dauki hanyar RIKADAWA
(FANS KUMA KU TAHO MU TAFI KAUYEN RIDAWA MUGA ME ZE FARU 🤸🤸)
Meenat tsaf ta gane hanya mutane see kallon motocin su Hashim suke in sun hango meenat a ciki su fara ihuu suna laa ga meenat y’ar Zina wanan kalmar tana Sosa zuciyoyin su gaba daya Banda meenat wace sedai tayi murmushi kawai.
Tun kafin su Isa gidan Kaka yara sunje sun sanar Mata ga meenat Nan itada wash Yan birni sun shigo gari a gaskiya bazan iya fasalta muku irin murnar da Kaka ta shiga 🏊🏊ba sedai kawai na bar ku ku kwnatata kugani
Hashim ne yafito Rike da hanun meenat zainab da nihla ma suka fito nihla se ya mutsa fuska takeyi tana kallon yaran da suka zagaye motar tana Kuma yatsine fuska
Meenat ce ta fara shiga Kaka da yanzu da kyar take iya takawa saboda tsufa (karku manta Kaka fa kakar sakina ce ba meenat ba) ta karaso tana fadin Aminatu sannu ku da zuwa meenat ta rungume Kaka tana farin ciki.
Naji ance da ba’ki kuke Bari na shimfina muku tabarma sannu ki sannu ki meenatu na Kinga yarda Kika Kara kyau gaskiya meenatu na birni ta karbe ki tana maganar ne tana shimfida tabarma.
Sanan ta kalli meenat tace maza ce su shigo meenat ta fita ta sanar ma dasu Abba Nan suka shiga
Mommy ce to fara shiga Kaka se faman yi musu sannu da zuwa take see hashim ya shiga tuni annurin fuskar Kaka ya dauke ta mi’ke tana nuna shi da yatsa sedai Bata Kai da yin magana ba Abba ya shigo.
Zare Ido tayi ta dafe kirji tana Kiran sunan sa “USMANU” Abba ma ya zaro ifo yana fadin gwgo hafsatu duk jarumata irinta Abba Sega kwla a idon shi ya fada yana karasa shiga gidan mommy da Hashim har ma da Zainab da nihla da meenat duk sakar Baki sukai suna kallon su day Alamar tambayar dama sun san juna a fuskar su.
Kaka ta mikawa Abba kujera y’ar tsuguno tana fadin dama munada rabon ganin juna usmanu dama zamu ‘kara ganin ka Ina Dan uwana kabiru Abba ya girgiza Kai yace Allah ya Masa rasuwa (Kabiru shine mahaifin Abba Kuma shine suke uwa daya uba daya da Kaka lokacin da iyayen su suka rasu ya tafi birni neman kud’i Ya samu rufun asiri ya dawo kauyen su na madobi yayi aure A lokacin Kaka ta haifi kawu audu toh bayan tafiyar shi matar shi ta Samu ciki ta haifi usman wato Abba Nan suka dawo kauyen madobi da Zama har usman ya girma yakai shekara 14 a Nan Kuna yawanci a gidan Kaka yake wasa toh Yan gari ganin Yana samu sukai Masa asiri ya bar garin shida matar shi da Dan shi tun Usman na Dan shekara15 suka bar garin tunda ya tafi ya fara kasuwanci Kuma Allah ya daga shi Yana kamfanoni a Kano sun fi biyar sedai kullum Yana so ta dawo garin su amma Kuma ya kasa ya rasa dalili wata Rana Usman ya tafi makaranta wato lokacin Yana University lokacin shekaran sa 22 Kabir wato baban Abba suka shirya Dan tahowa garin madobi yaga Yar uwar sa sedai a hanyar su ne ta tafiya sukai mumuna hantsari duka suka mutu Dan ko auran Usman Basu gani ba Kuma Shima usman din se yaji kwta kwata baya son zuwa garin iyayen nashi Dan ko lokacin auren su da Amina(mommy) abokan kasuwancin mahaifin sa ne suka tsaya Masa) wanan kenan
Fatiman ku ceY’AR ZINA CE
(KADDARAR IYAYENA)
MUNEERA
PAGE DIN NAN SADAUKARWA NE A GAREKI MY RAHEEMA 😘😘 ALLAH YA BADA ABINDA AKAJE NEMA, AYI KARATU DAKYAU😂 IN BA HAKA BA DA DORUNA ZANZO NA………KINDAI GANE AI
TUKUICI A GAREKI MY AUNTY😍 AUNTYN MUNEERA & RAHEEMA. ALLAH YA RAYA MIKI MU 🤣😂KIGA JIKOKIN MU😎
PART 2
PG~2
Kaka ta goge kwlarta Tana fadin Allah ya jikan ka Dan uwana halinka na gari ya bika Allah yasa ka huta
Dukan su suka Amsa da Amin sanan Abba yayiwa su mommy bayani akan kaka, mommy cikin farin ciki ta Kuma karasawa inda Kaka take Dan ta Dade tana cewa Abba yakaita wurin Yan uwan shi Amma se yace lokaci yake jira Ashe tanada rabon ganin Yan uwansa a duniya
Kaka ta fashe da kuka tana fadin Allah ya jikan ki Raheema (mahaifiyar sakina) cikin zaro Ido Abba yace Raheema ta rasu ne Kaka ta gyda Masa Kai ta Dora da cewa
Raheema ta rasu wajen haihuwar sakina y’ar ta Abba yace Ina ita sakinan? Kaka ta Kuma goge kwlarta tace
“Sakina itace mahaifiyar meenat bayan ta haifi meenat da shekara bakwai ta rasu itama Allah ya Mata rasuwa”
Kaka ta ‘karasa maganar tana kallon Hashim wanda yayi ‘kasa dakansa baya Koo iya had’a Ido da Kaka+
Abba yace abinda ya faru ya Riga ya faru gwgo hafsatu sedai fatan Allah ya kiyaye gaba yanzu da gwgo hafsatu Zaki shirya ne mu tafi dake Dan bazamu barku anan ba
Kaka tai saurin fadin babu inda zani usmanu ai ni da barin RIKADAWA sedai in gawata zaku dauka Amma bazan bar garin Nan ba
Mommy tai saurin fadin” ai kuwa gwgo kafata kafarki in har ke bazaki bi mu ba mu zamu zauna dake anan”
Seda akasha tata birza da kaka sanan ta yarda zata bisu Amma fa duk lokacin da Hashim da Kaka suka had a Ido se kaka ta cillawa Hashim harara😂 shi Kuma se yayi kasa da Kai Yana sisine fuska
Toh fa se yamma lilis sanan suka shirya zasu tafi Kaka makota babu inda Bata shiga ta musu sallama ba😂in an tambaye ta Ina zata koma se tace birni in ance birni wani gari setace kaii ni ohoooo😆 haka gida² ta dinga shiga harda gidan su maimuna 😁 ta muneera novel group
Mutanen gari aka fifito ganin Kaka zata tafi birni )se wasu daga gefe Dana hango gungunsu guda😂 Wai Suma zasu raka Kaka birni gaba daya y’an muneera novel group seda sukazo raka Kaka.)
Motar da hashim yake ciki akace Kaka tashiga Amma fafir tace bazata shiga Nan ba se motar su mommy ta shiga tana wulawa Hashim wata uwar harara.
Babu yarda zeyi ya Hana Kaka harar shi saboda yasan har yau fushi take dashi Kuna tabon da yayiwa sakina har yanzu be gushi ba
Yana Tu’ki Yana tunin Ina ma sakina tana Raye ya wanke kanshi daga lefin da yai Mata ta nemi yafiyarta suyi auren su,su Rike meenat dinsu, shifa har yanzu Yana ji ajikinsa sakina Bata mutu ba zata dawo gareshi
Toh tunda suka fara tafiya jikin zainab yayi mugun sanyi Dan tana kokwnto akan mutuwar sakina ta kalli Hashim wanda hankalin sa baya kanta gaba daya
Dole tasan wata Rana asirin ta ze tonu tunda har sakina take sance y’ar uwa a gurin Hashim Lalai ta tafka babban kusukure(toh fa fans kome zainab ta aikata? Mudai je zuwa)
Sun sauka A makeken gidan su Hashim dake cikin garin Kano Wanda take a unguwar mandawari
Abba ne dakanshi ya budewa Kaka kofa ta fito daga kanta tayi tana kallon jerin benayen gidan.
Se waige² take tana kallon girman gidan zainab na lura da ita se ta’be Baki take tana Jan tsaki a zuciyar ta.
Nihla ma dasun hada Ido da meenat seta ‘bala Mata harara ita ma meenat da taga gata ga Kaka inta harareta seta rama nihla setaji kamar taje ta shake meenat, meenat kuwa seta Mata gwlo da alamun 🤷
Mamakin Kaka be Kare ba seda suka shiga cikin gidan sosai taga irin kudin da aka kashewa gidan a zuciyar ta tace anya zata iya zaman gidan Nan ai se yasa ta rasa imanin ta.
Abba ya katse Mata tunani da fadin gwgo
“Karaso Mana” kamar bazata karasa ba Amma se the bishi tana kybe Baki a zuciya tana fadin zaman gidan Nan be kamata ba Dole ta koma kauye Dan RIKADAWA tafi Mata nan.
Daki aka bawa Kaka Kato guda meenat ma cewa tayi a wurinta zata kwna
Hashim da zainab da nihla kuwa suka nufi part din Hashim
Washe gari
Komai seda meenat ta koyawa Kaka Dan Bata iya amfani dasu ba har toilet seda meenat ta koyawa Kaka yarda ake amfani dashi tana koya Mata tana dariya Kaka kuwa tace ke ni bazan iya da abin Yan birnin Nan ba Kyle ni
***********************
Zaune take fuskar ta taci uban spectacle me tsada fatar ta ta ‘kara fresh kamar baturiya doguwar Riga ce ba’ka a jikin ta ta mata kyau sosai ta Kara fito da kyawunta takalmi ne dogo a kafarata me tsini sosai tayi rolling da mayafin rigar sedai duk da haka seda jelar gashin ta fito ta baya Nude make up ce a fuskar ta
Cikin siririyar muryar ta take cewa kawu Abdul kawu Abdul tana yin maganar ne da d’an karfi kawu Abdul ta Kuma fada cikin farin ciki ka fito kaga abinda Hashim ya Dora a Instagram hoton su harda……………
Dan Allah duk Wanda ya karanta page din Nan yasa yayata a ADDU’A Allah ya sauketa Lafiya Nagode
Se bayan sallah inshaAllah Zan cigaba typing
Fatiman ku ce 👌Y’AR ZINA CE
(KADDARAR IYAYENA)
MUNEERA
BAN SAN MASOYAN LITTAFIN NAN NADA YAWA HAKA BA SE KWNA BIYUN NAN DA BANA ONLINE INA BUDE DATA MESSAGES HAR YAWA SUKA MIN BAYAN WANDA SUKA KIRANI GSKY NAGODE DA WANDA KUKA MIN BARKA KUMA NAGODE SOSAI ALLAH YA BIYA DA GIDAN ALJANNA.
NUSAIBA TA MUNEERA NOVEL GRP ALLAH YA RAYA BABY YASA CIKON ADDININ MUSULINCI NE😘
SADAUKARWA GA MAHAIFIYATA MAMYNA ALLAH YA KARA MIKI NISAN KWNA ALLAH YA BIYA MIKI BUKATUN KI ALLAH YA BAKI ALJANNA ALLAH YA RAYA MIKI MU ALLAH YA BAMU IKON KYAUTATA MIKI ALLAH YASA KI CI ARZIKI NA 🙏
Part2
Pg~3
Kawu Abdul da tuntuni yake jinta Amma jikinsa ba kwri sabida raunukan jikinsa da sandar tashi ya cigaba da dafawa har ya ‘karaso inda take cikin tsantsar farin ciki ta nuna masa wayar ta fadin Hashim nagani da meenat Kuma ga Kaka a gefen su.
Waro Ido yayi ya Dan cije Baki saboda yanayin raunukan jikinsa ya karbi wayar yana dubawa d’an zaro Ido yayi yace daughter Kaka nake gani kusa da usmanu ga Hashim Kuma a gefe toh meye had’in Hashim da usmanu kansa ya dafe.
+
Ita Kuma ta temaka Masa ya ‘karasa ya zauna kan d’aya daga cikin kunerun dakin
Sanan itama ta zauna tana fadin tabbas Asirin zainab ya kusa tonuwa na kusa falasawa duniya su San ko ita wacece tunda yanzu Kabir mun had’u dashi Kuma ya yarda ze sanar min da komai akanta ta Dan yi murmushin gefen Baki sanan ta goge kwlar idonta ta tana kallon wayar hoto Hashim ne da meenat Yana Mata kiss a kumatu Kuma goge kwlarta tayi ta Kali wani Wanda meenat ce tsaye tana murmushi.
Kawu Abdul ya katse Mata tunani da fadin kuka ba naki bane a yanzu jaruma ya kamata ki Zama ki kwtarwa kanki y’anci da Y’ar ki Dan tabbas a yanzu tunda zainab ta bar kanki kan yarinya ki zata koma ki cire tsoro ko fargaba ko kuma wani kokwnto kiyi shawara da zuciyar ki karki ce Zaki zauna ki zuba ido har ta kashe Miki yarinya Nima yanzu jira nake na karasa samun sauki naje gidan su Hashim din tunda nagan su tare kuma ga usmanu a gefe tabbas nasan AKWAI boyayen Al-marri Wanda nida ke bamu San shi ba.
Ta girgida Kai kawai tace insshaa Allah, kawu na Allah ya baka lafiya yasa kaffara ne ya Amsa da Amin.
Ita Kuma ta yafa mayafin ta Wanda kanta yasha daurin Zahra buhari 😉tace kawu se na dawo yace a dawo lafiya Kuma ki tsare mutunci ki seda taji wani dass kwla ta fito daga idonta Wanda ba ta Bari kawun ya gani ba tace insshaa Allah ta fice ta hau tsaleliyar motar ta wace ta nufi State road da ita Dan cinma wani aiki da take son ‘karasawa.
*******
Ni wanan uban hoto ya ishe ni Abu ya’ki ci ya ‘ki cinyewa ni nagaji ta ja wani uban tsaki ta zauna Abba ya girgiza Kai a ransa yace Su gwgo hafsu duk Rigima tsufa ce kamar tasan me yake fada ta dago tana fadin me kace ? Yace cewa nayi sannu duka suka kwshe da dariya Shima me hoto ganin haka ta Kuma yi musu wani Basu sani ba.
Hashim dai mikewa yayi ya fice Dan Yana son zuwa State road ya karbi wani sa’ko
Wajen government house duk ya cika sanadiyar governor da tawagarsa zasu fita hashim yaja tsaki Yana kallon gefensa saboda haushi sedai wace ya gani din ne yasashi yin turus Yana goge Ido Dan ko daga bacci ya tashi ze sheda cewa wanan sakina ce Kuma ba gizo take Masa
Fita yayi daga cikin motar ze karasa inda yaga motar sedai Yana fito motocin governor sun wuce an bada hannu kowa ya wuce motar ya kalla ya koma motar shi a million ya fara Jan ta Yana bin bayar mota hardai ya samu yasha gabanta.
Wani mutumi ya fito Yana fadin malam lafiya wanna wani irin hauka ne kakeyi a titi koka bugu ne mutumin tsayawa Yana fadin senator hashim dama Kaine hashim ya d’aga Masa Kai kawai Yana kokarin komawa mota Dan harsun fara hada goslow jama’a Kuma se kallon hashim akeyi ana nuna shi cewar ga senator hashim.
Shidai Hashim motar shi ya Kuma yayi youtoun ya koma ya nufi inda zashi Amma se dad’a fad’a yake a ransa cewar tabbas sakina ya gani
Yahuza ya nufa Dan dama anan sukai zasu hadu da bawan Allah da ze karbi Abu a hanun sa yana Koo Gama parking beyi ba ya gano sakina na mi’kawa wata hannu suna gaisawa fuskar ta cikin glass da sauri ya sauko ya karasa wurin sedai seyaga matar kawai Amma babu sakina ya tambaye ta tace ita Bata San wata sakina ba.
Wuri ya samu ya dafe kansa Wanda a ransa take fad’in tabbas kece ba gizo kike min ba ki dawo gareni Dan Allah na tuba sakina haka yayita sumbatu shi kadai.
Ya Mike ze tafi kenan mutumin da yazo danshi ya karaso ya Mika Masa hannu suka gaisa hashim ya tambaye shi lafiya yake ta nemansa mutumin yayi murmushi yace lafiya yallabai ga wanan dau sa’kon akace na baka in kaje gida ka duba
Ba tare da Hashim ya kawo komai a ransa ba ya karbi envelope din ya shige mota
Tafiya yake Yana tunanin abin al-ajabi da ya gani Wai sakina idin shi ta gane Masa tabbas dama shi Yana ji ajikinsa sakina na Raye Bata mutu ba Zata dawo gareshi
.
Da wanna tunanin ya karasa gida duka suna zaune a Palo Kaka nata sasu dariya hashim ya shigo ko kallon su beeyi ba ya wuce part sa envelope din ya bude Yana fito da abinda ke ciki a hankali ya juya hoton Dan ganin menene sedai ganin Zainab rungome da Kabir yasashi sakin hoton ya Fadi kasa dai² kafar mommy
Zaku cigaba da jina shiru harse komai ya dai²ta sakamakon haihuwa da aka mn banida lokaci sosai nayin typing Amma da na samu lokaci zaku jini
Fatiman ku ce 👌’YAR ZINA CE
(KADDARAR IYAYENA)
Muneera (maman Arpha)
SADAUKARWA GA MAHAIFINA ABBANA ALLAH YA BIYA MA BU’KATUN KA YA BAKA ABINDA KAKE SO YA RAYA MAKA MU ALLAH YA KARA NISAN KWNA DA ARZIKI
PART 2
Pg~4
Kallon mommy yayi idon su Sunny jajir mommy takai hanun ta ta daga hoton tana kallo mommy Kinga yarda zainab ta min koo? mommy Mena Mata meyasa zata saka min da haka dama karya ta min akan Kabir dama sun san juna mommy zainab ta cuce ni Amma ni ma fara cutar kaina gaskiya mommy se Kuma yayi shiru ya fice a fusace Yana Kiran Zainab da karfi a firgece gaba daya suka fifito zainab na zare Ido Bata Gama furgita ba seda taji sallamar Wanda ko a mafarki bazata manta muryar shi ba Basu Gama tsinkewa ba seda sakina tayi sallama ita da audu Kaka cikin zaro Ido da firgici take kallon sakina a ganin ta fatalwa take gani meenat da take hanun kaka tana ta kokarin fusgewa ta gudu wurin mamanta Amma Kaka taki sakin ta a cewar ta sakina fatalwa ce da kyar ta fusge tayi wurin sakina da gudu ta rungume ta.
Zainab kusa ihu kuka ta saki kafafuwan ta suka kasa daukar gangar jikinta ta zube kowa na bin ta da Ido Abba ne yayi jarumta cewa Bismillah ku zauna sakina ta jawo ta temaka kawu audu ya zauna Abba ya kalli audu yace audu Ina ka shige ana ta nemanka Kuma ita wanan wacece kafin ya bada amsa Kaka tayi caraf ta amshe da cewa itace sakina+
SHIN MENENE AINAHIN ABUNDA YA FARU DA SAKINA BAYAN MU MUNSAN TA MUTU SEGA TA TA DAWO?
Sakina ce ta Gama shirya meenat domin kaita school duk da ranar tunda ta tashi take jin gabanta na faduwa Amma tayi dauriyar danewa Kar Kaka ta fahimci halin da take ciki fitowa sukai ita da meenat ta ajiye meenat kenan ta shige school wata ba’kar mota tazo ta dauke ta tana finceke² suka cusa ta ciki tare da sha’ka Mata wani Abu a hanci suka toshe Mata Baki Bata Jima ba ta Dena motsi tayi kamar mataciyya, dga Nan Bata Kara sanin inda kanta yake ba se ganinta da tayi a wani d’aki Wanda duhu ya cikashi
Wata Mata taga ta doso inda take wace kana kallon ta kaga hajiya wato kudi sun zauna ta kalli sakina ta yamutsa Baki ta topar da yawu ta kalli sakina, sakina kuwa ta saki Baki ta zuba Mata matsakatan idanunta matar tace mijina ya rasa wace ze so kuma wace zewa cikin shege seke ‘yar kauye dake ta taso ta Kama fuskar sakina wace tsoro gaba daya ya Gama cikata ta dago ha’bata ta buga Mata kan bundiga a goshinta tuni jini ya fara kwrara sakina ta dafe wurin cikin cije le’be tace baiwar Allah me kike so a wurina mena Miki kums waye mijin naki daki ke magana ta ‘karashe maganar tana Kuma dafe goshin ta saboda jinin dake zuba.
Mari ta kwdawa sakina tace wato want mijin nawa Ashe ba mijina kawai aka cuta ba toh nice zainab matar Hashim in ba so kike na kashe ki ba wallahi ki boyewa ganin hashim Dan Yana Nan Yana neman ki ki boyewa ganinsa inba haka ba Sena kashe ki nakashe shegiyar y’ar ki tuni cikin sakina ya duri ruwa Dan nata so abinda ze taba Mata iyalinta Dan in ita kadaice abun da sauki Amma bazata it’s juri ganin Kaka da meenat harma da kawu audu a wani yanayi Mara kyau ba buga Mata bundigar ta karayi a ha’ba ta wanada yasa sakina sakina Yar Kara tana nuna alamun Jin zafi.
A gurguje🤦
Abin Nan katin da suka dauko ta ne suka dawo da ita suka ajiye chemest ta wuce aka gyra Mata ciwon sanan ta cewa me chemest yayi Mata yarda baza a game ba Nan dai yayi Yan dabarun say ta dawo gida Nan ne tana dawowa gida suka hadu da kawu audu Bata Bari sun shiga gida ba ta zayane Masa yarda sukai da zainab anan ne suka tsara yarda za’a ce to mutu har ta Samu ta bar garin Amma a lokaci da aka fito da sakina bawai makabar ta suka wuce ba Aa gidan abokun kawo audu suka wuce aka ajiyeta kawu audu ya biya Wanda suka dauko ta kafin kawu audu yaje ya dawo sakina har ta nufi Tasha ta hau mota zuwa Kano daga Kano ta Kama hanyar Lagos acewar ta Bata so ta saka kawu audu a cikin Kaddara ta ta sshafe shi
Wanna kenan
Tunda ta sauka a garin Lagos ita batasan kowa ba Kuma ba Wanda ya Santa hasalima Koo Kano Bata taba zuwa ba se sau daya abinda yasa Bata tsaya a Kano ba saboda tasan Hashim ya fada Mata shi Dan cikin garin Kano ne
Tasha fama da yunwa harda kishi Ruwa kafin ta Samu wata me tuwo² ta dauketa aiki sedai matar idon ta abude yake Kuma yawancin ma’aikatan ta Yan kwya ne abun yna tsorata sakina Amma babu yarda zatayi haka take zaune a wurin.
Akwai wani Wanda ake Kira da KB Yana mugun tausayin sakina yaso sanin tarihin rayuwar ta Amma fafir taki fada Masa ita wacece wata Rana ya bar wayar shi a hanun sakina ta sama Masa chaji tasa Masa taga wani hoto ya bayana ta kalli fuskar wace bazata ta manta fuskar wacece ba wato zainan matar Hashim tuni hawaye ya mamaye fuskarta tana kuka a half har Kabir yazo amsar wayarshi ta tambaye shi wacece zainab a wurin shi da yaso kin fada Mata amma abinda ysa ya Yankee hukuncin fada Mata wacece zeey Nan ya fara bayani
Zainab wace akafi sani da zeey budurwa ta CE tun tana budurwa har yanzu da tayi aure bamu fasa holewar mu da ita ba Kuma Mata CE a wurin Hashim wanda baban shi babban aminin babana ne hakan yasa ake kirana da kanin sa wato mutanen ke ganin kamar cousins ne mu lokacin da zainab zatayi aure tazo ta neme ni da muyi wani Abu ace fyde na Mata bayanin ni ba fyde na Mata ba ta runjaye ni na aikata abinda tace nace na aikata muka tsara komai…………
Maman Arpha’YAR ZINA CE
(KADDARAR IYAYENA)
MUNEERA(mmn Arpha)
PART 2
PG~5
😪bansanma DA idon DA Zan kallekuba😵 nashiga sabgogi DA yawa ne Amma nikana so nake nagama muku shi nahuta DA wanan nauyin
✍🏻zan dawo posting Amma gsky na kullum ba sedai kuyi hkr saboda Ina xuwa school banida ishshen time fatan zaku fahimce ni nagode1
Cikin mamaki sakina ke kallon kb shi kuma yana kuma tabbatar mata da abinda ya fada shiru tayi tana nazarin maganganun kabir, Rokon ta yayi yana fadin sakina ni Dan gata ne gaba da baya Amma sanadin zainab nadawo me yawo a garin da ba nawa ba hasalima zaman garina ya gagareni saboda kunyar iyayena da tofin Allah tsine da mutane ke min shin Sakina kinsan zainab ne?
Kallon shi tayi tareda girgiza Kai hade da hadeye wani Abu a makagironta
Ki fada min inshaa Allah Zan temake koo kuma ni ki temake ni Dan Allah sakina shirutayi na yan muntuna kafin wata kwla ta sauka akan kuncinta tace nasan ta yace eheen
Nan ta bashi labarinta Dana zainab duka hamdala yayi tare DA cewa lokaci yayi Wanda Dani dake zamu koma mahaifarmu sakina ta dago ido ta kalle shi tace tayaya fa? Murmushi yayi yace inhar zaki bani hadin Kai dukan mu zamu koma cikin iyalan mu amma kafin man ki shirya Zan mana booking flight zamuje kano sakina kamar bata yarda ba Amma ta girgiza masa kaii
Washe gari ta gama hada kayanta tayiwa madam dinsu sallama kabir yazo suka wuce basufi 1hr ba suka sauka a garin kano ta dabo tumbin giwa😍 me dala da gwron dutse garin karamci,mutunci da girmama Dan Adam💃🏽
Basu wani jima ba kabir yayi waya akazo daukar su tafiya suke kiiiiiiiii drivern su ya bige wani a gigice suka fito Dan ganin wanda aka bige ba kowa bane illa kawu audu ihuu sakina tasaka tana ambaton sunan kawu audu amma baya motsi
Daukarshi sukai zuwa asibiti aka hau bashi temakon gagawa ba abinda sakina take se kuka kabir daya tamvaye ta, Tace shine kawu audu(toh wanan shine sanaduyar dayasa aka nemi kawu Audi kawu aka rasa) lokacin DA Likita ya fito kawu DA sakina sunyi murnan ganin junansu
Yayi kusan wata 1 yana jinya saboda manyan ciwukan dayaji ranar da aka sallameshi keraren gida kabir ya basu su zauna sanan suka Fara bin didigin halin DA zainab ke ciki itada Hashim inda kawu ba shi da magana seta kaka gashi ba’a fiye so yayi motsi ba Dan KO tafoya KO ya masa akeyi da wasu abubuwan da ba a rasa ba Kuma kabir na basu kykyawar kulawa inda suna shirin yarda zasu tarfa zainab Ana haka ne sakina ta gano hoton Hashim dasu kaka da meenat a hanunsa wanan ga sakina dama takuma kilewa an waye😂waye. kaushi duk ya goge🙊 anyi klin da cleaner wanan kenan👈🏻kenan👈🏻
Sakina tana gama bada labarin zainab ta Saki ihu tana yunkurin shakota sakina Hashim yayi saurin rike zainab tareda watsata gefe yana fadin karki kuskura🖕🏼
Da huci yace dama na sake ki Saki 3 yanzu bawata alaka tsakanin mu inba so kike na lakada miki na jaki ba kibar gidan nan Nihla dake gefe tunda aka Fara lamarin babu abinda take se kuka zainab ta kaleta tace taho mutafi Nihla tayi tsale ta koma wurin Hashim tace no nibazan bar dad Dina ba Hashim ya rungometa yana me jin tausayin halinda Zara shiga inta San bashine mahaifinta ba
A gurguje
Hashim DA sakina sunyi aure inda da kyar sakina ta yarda sun rungumi yaransu nihla da Meenat
Inda kabir yaa auri zainab Amma kullum cikin zargin ta yakeyi
WANAN SHINE LABARIN HASHIM DA SAKINA DA ZAINAB HARDA KABIR INDA MUKAJI DUKANSU SUNSHIGA KUNCIN RAYUWANE AKAN SABAMA ALLAH DA SUKAYI ZINA A YANZU TAZAMA RUWAN DARE A CIKIN AL’UMMA INDA YAN MATAN YANZU BA KOMAI BANE SUBAWA SAURAYI KANSU KO IYA WANAN YASA ALLAH YA JARABCE MUDA ABUBUWA DA YAWA SANAN KUMA WASU SAKACIN IYAYENE YANZU NE ZAMU FARA LITTAFIN YAR ZINA INDA ZAMUJI YAYA RAYUWAR MEENAT ZATA KASANCE HARMA DA NIHLA DA BA TASAN HASHIM BA MAHAIFINTA BANE👌🏻
TOHM HARDA MASU CEWA BASIRA TA KARE MIN😅DA MASU ZAGI NAKI CIGABA BAYAN DUK BAKUSAN UZURIN MUTUM BA ANYWAY THANK YOU
1
FATIMAN KUCE👌🏻Y’AR ZINA CE
_KADDARAR IYAYENA)
NA
MUNEERA
ALHAMDULLILAH WAYYO BANSAN DA IDON DA ZAN KALLE KU BA AMMA DAI KUSANI KUNA RAINA KULLUM YANZU ZAMU CIGABA
DEDICATED TO 👉🏼 ZAINAB A GAMBO(MUMCY) I LOVE YOU SO MUCH DABANDAN KEBA DABA CIGABA DA LITTAFIN NAN BA
_
My Raheema, Habibty,Aunty nappy, Habibty Ayush, Saheeba Ummu nabeel 💕💕ina miko gaisuwa
Part 2
Page 6
❤❤❤❤❤❤❤❤❤
Bayan duk abinda ya faru tsakanin wanan iyalin ba abinda ya canza se karuwar farin ciki sabanin Nihla da kullum cikin damuwa take sakamakon Rashin mahaifiyar ta a kusa daita sanan tunanin ta be canza ba Dan har yanzu Hashim be sanar Mata da bashine mahaifinta ba ya cigaba da kula dasu itada meenat
+
Zainab ma kabir na son ta sedai ya kara aure Dan zainab ta jima bata haihu ba dangin kabir kullum cikin gori suke mata gashi shi kuma kabir kullum cikin zarginta yake
************
Akwana a tashi ba wuya a wurin ubangiji yanzu har anyi 6yrs da yin auren sakina da hashim se lokacin Allah ya sa sakina ta samu ciki lokacin meenat da Nihla shekarar su 15yrs duka suna SS2 Nihla tana’nan yarda take ba abinda ya canza daga dabiun ta wato ‘kin na ‘kasa da ita da wulakanta tallaka, gata da nuna isa tsabanin meenat da take me hakuri tausayi da girmama na gaba da ita.
Tafe suke cikin school su biyu wato meenat da Nihla meenat ta kalli nihla tace “Nihla ga exam din Third term ta taho yanzu za’a fara sace note yakamata mu kula” Nihla tayi yar dariya tace “meenat kenan Ai masu hakuri irinku ake sacewa note ba irin mu ba Dan ko mutum ya sace dole ya fito mana Dashi” meenat ta tabe baki gameda cewa “Ai nihla abinda hakuri be bada ba Rashin sa baze bayar ba” nihla tayishiru bata kara cewa komaiba harsuka karasa wurin motar su zasu shiga kenan sukaji wata murya a bayansu yana fadin
“Yar zina ce!yar zina ce! A tare suka juya Dan ganin ko waye? ya kuma kallon meenat yana gwalo yana kiranta da yar zina tuni kwala ta cika idon meenat nihla tayi kan yaron A fusace zata kwada masa mari Amma da sauri meenat ta rike mata hannu tana girgiza mata Kai Alamar kartayi Ai kamar ta kuma harzuka ta fadi take”senaga ubanda ya tsaya maka Kai wanine dakake kiran yar uwata da mumunan suna ita tayi kanta? ko ita taso tazo a haka?
kaima ba dabararkace yasa iyayen ka suka haifeka ta hanyar aure ba yaron da befi sa’ansu ba yana tsaye ko gezau beba ita kuma nihla tana kokarin cafkar shi Amma inaa meenat tuni ta jata da karfi ta shigar da ita motar driver yajasu.(Abinda na lura dashi shine duk da halinsu ya banbanta Amma suna matukar son junansu tareda kishin junansu wanda hakan ya samu tushene daga wurin iyayensu)
A palo suka samu sakina da katon cikinta wanda ya zauna a cinyarta saboda tsabar girma nihla ce tafara shiguwa sanan meenat sakina ta lura ba walwala a taredasu sannu da gida suka mata suna kokarin wucewa tace lafiya? Waya tabaku nihla zata fara magana meenat tai saurin tabota alamar karta fada dasauri nihla tayi yunkurin kara fadar abinda ya faru meenat tayi saurin tarar numfashin ta tace” mamy yau mugaji bari muyi wanka muna zuwa kafin sakina tayi magana meenat taja hanun nihla suka shige dakin su, dan lokacin dasuna yara an raba musu daki Amma suka hade a dakin meenat
Meenat ta kalli nihla tare da fadin”haba yar uwa dake seki fada bayan kinga mamy halinda take ciki ba a son ana daga mata hankali sabida gudun afkuwa matsala Dan Allah kidinga sawa zuciyarki Ruwan sanyi “nihla tace “okay”
*********
Yau sakina ta tashi da matsananci ciwon mara da kwankwaso tun tana daurewa harta kasa suka nufi asibiti itada Hashim su meenat suna school lokacin
Basufi 1hr da zuwa ba sakina ta haifi yaranta maza guda biyu lokacin da aka fada masa abinda sakina ta haifa seda yayi Kwalla yana me godiya ga Allah yau daya bashi yaran dayasame su ta hanyar Aure ba sabanin haka ba.
Sakina kanta kuka take tana tuna Lokacin data haifi meenat ashe itama zata haihu ta haifi yara ta hanyar Aure ba ZINA ba
**************
Lokacin dasu Nihla suka dawo Abbansu ya Dawo daukar kayan baby ya sanar musu ko uniform basu cire ba suka bishi A mota aikowa se musu suke wanan yace shida wancen yace shida usaini shidai Hashim yana jinsu se dariya suke bashi nihla harda cewa sedai meenat ta dauki hassan Dan ance hassan sune masu hakuri haka sukaitayi harsuka karasa asibitin
Lokacin da suka karasa sakina ta tashi daga bacci babies din ne keta bacci a jera su a gadon da aka tanada koda suka isso kallon babies din suka fara meenat ta kalli sakina tace Mami sannu ta Amsa mata itama nihla ta mata meenat tace naji din ke nihla na dauki hassan saboda sunfi kama da abba nihla tayi dariya tace yarinya Aiduk kamar su daya duka suka sa dariya kafin wani dan matanshi Doctor ya shigo wanda baze wuce 32-34 ba yanada dan tsayi sanan shiba fari bane kuma ba baki ba wato dai shi chocolate color ne tsayawa yayi yana kallonsu sanan yace zasu bawa Sakina sallama tunda Alhamdullilah bawani abu dake damunta meenat dakanta ke duke ta dago a hankali ta kaleshi sekam suka hada ido tayi saurin janye Nata shikuma yacigaba DA kallonta seda hashim yace yes inajinka
Fatiman kuceY’AR ZINA CE
(KADDARAR IYAYENA)
NA
MUNEERA
PART 2
PAGE 6
DEDICATED TO MY RAHEEMA❤
Seda Hashim yace yes sanan doctor yadawo hayyacin sa yacigaba da musu bayyani suka masa godiya sanan ya Kara kallon inda meenat take yarda ta dukar da kanta kasa har lokacin bata dago ba sanan ya dice
Zainab ce zaune a cikin jerun kujerun dake palon dauke da remote a hanunta da Alama dai kallo take kuma gaba daya hankalinta ya karkata ga kallon wayarta dake gefe ta hau Ruri zainab ta mika hannu ta dauka batareda ta duba sunan ba “hello mommy barka da war haka fatan kina lafiya” murmushi dauke a fuskar zainab jin muryar yarta tace lafiya lau Daughter “mommy Allah ya sauki mamyn mu lafiya ta Haifa mana yan biyu duka maza” ta fada cike da zumudi Murna fal muryata zainab da taji gabanta ya fadi tace “karkice min Salina?” Eh ita mana mommy kitaya mu murna ” gyran murya tayi kafin tace toh Allah ya raya nihla ta Amsa kana takashe wayar.
Hawaye zainab taji suna kokarin zobowa daga idonta Dan har yanzu tana son Hashim shine mijin daya rufa mata Asiri a lokacin da Asirinta yakusa tonawa yazauna da ita dukda kuwa mugayen halayenta Hakika tayi nadamar Aikata abinda zuciya ta tunzura ta ta Aikata goge kwlar idonta tayi lokacin dataji Khadija kishiyarta nashigowa+
A wulakance khadija ta kaleta tare da zama da katon cikinta sanan tana Rike da hanun wani yaro tace” mutum dashi dababu duk daya yazo ba abinda ya iya seci da yin kashi hanan Wato kanwar khadija ta karaso dakin tana cewa yaya kedawa kuma Khadija ta numfasa tace “kinsan kowa yayi zagi a kasuwa yasan da Wanda yake kuma habaicin kura name kare ne” hanan ta kalli Zainab sanan ta maida kallonta kan khadija tace maganarki hakkun zainab maganar ta kona Mata rai Amma seta ce “uhmm darajar kwrya ragaya inta sau kasa ta canza suna” khadija tai shewa gamida cewa ohoo dai komai lalacewar masa tafi kashin shanu tana gama fadar haka batajira cewaar Zainab ba sukai ficewar su daga palonZainab kuwa ta fashe da kuka a wurin bame rarashinta
Sun gama shiri tsaf da komawa gida daga Asibitin motar dasuka zo da ita ta musu kadan Dan haka Hashim ya daga waya ze Kira mudi driver Dan ya kawo wata motar su wuce gida gaba daya da sauri doctor dinan ya karaso yana cewa Hashim inba damuwa shi seya Kai musu kayan gida Hashim ya masa godiya suka zuba kaya a motar doctor su kuma suka shiga motarsu Hashim yaja suka tafi
Lokacin da suka isa Hashim ba karamin godiya yayiwa doctor nan ba shikuma yace ai yiwa kaine Hashim ya juya yace Meenat ta juyo shikam doctor ganin meenat ta juyo a zuciyar shi yake maimaita sunan yana fadin dama sunanta meenat Hashim yace maza kituro su illu su debi kayan nan tace tohm cikeda girmamawa sanan ta juya
Suna shiga suka tarar da kaka da momy a zaune nihla da gudu tayi wurin su tana rungume kaka itama meenat ta rungume momy kaka kam tsufa ya kara bayyana danma da hutu saboda dama a wurinsu momy take kaka tacewa nihla “ni daga ni kafin ki karasa ni” duka sukasa dariya kaka takara da cewar a miko min sababin jini na dauka ba Ku gadan gadan dakuba duka suka Karasaka dariya
Bayan kwna bakwai
Aka rada ma yara sunan daddy da sunan baban sakina wato usman da Muhammad Ansha shagalin suna Dan yan kauyen *RIKADAWA DA MADOBI* duk sunzo zainab da kabir ma sunzo kabir se kallon nihla yake yarda take sabgoginta taya ze fara sanar mata dashine mahaifinta domin yana son yarshi tasan gaskiya Amma ya Bar maganar zuwa lokacin daya dace ya fada Mata
*Bayan wata daya*
Doctor Yusuf yazo ya sanarwa da hashim manufarsa akan meenat kuma har yakanzo suyi hira da meenat intana tare da Dr takanji duk wasu matsaloli nata sun kau nihla kam sejin dadi take yar uwarta ta samu mijin Aure abinda kullum take addua DA yin fata kenan
Kamar kullum yau doctor yaxo wurin meenat gyran murya yayi sanan ya kalleta ya tabe baki yace
“Inason ne na samarwa yarana uwa ta gari me Asali wace aka haifeta ta tsaftataciyar hanya ba Kazanta ba Ashe dama ke kazama ce ta hanyar Kazan ta aka sameki wato ke *Y’AR ZINA CE* nayi dana sanin Sani ki bazan Aureki ba kizo ki haifa min mazinatan yara Dan dama Ance *ZINA* Jini take bi nahakura dake meenat wato da an rufe ni za a aura min *’YAR ZINA* toh yanzu nasani sedai a nemi wani sarkin baniba”
Tunda ya fara magana Meenat ke kwlla ta toshe bakinta shikuma ya juya ze wuce ya tafi karka min haka Yusuf karka rabu Dani Dan Allah Yusuf ka Cece Raina Nima banson raina ne Nazo a hakaba _KADDARAR IYAYENA_ ce KO juyowa beba yajuya ya fice daga dakin ita kuma ta kwnta a wurun tana kuka me tsuma zuciya tana Ambaton sunan DA a hankali tana Yusuf Yusuf kana ta mike tareda yowa waje lokacin dayake tashin motar sa tace masa karka tafi dan Allah Yusuf kajikaina Ina sonka bansan meye so ba se akanka Dan Allah Yusuf shigewa yayi cikin motar zuciyarshi na kuna Dan KO muryata baya sonji tana kallon kurar motar shi yayinda ya fice daga gidan
A kasa ta zube tana fadin Allah in na maka lefi ya rabbi kayafeni karka jarabeni da abinda bazan………
Fatiman kuce*Y’AR ZINA CE*
_(KADDARAR IYAYENA)_
*PART 2*
_PAGE 8_
_AFUWAN JIYA NAYI MISTAKE WURIN NUMBERING PAGE 7 ZANSA NASAKA 6 YANZU ZAMU TASHI PAGE 8 KENAN_
Ya rabbi karka jarabeni da abinda bazan iya ba kuka takeyi sosai me tsuma zuciya ta mike a hankali tanajin wani irin jiri tashige cikin gidan taci sa’a bataga kowaba harta shiga daki ta zube a kan gadon su alamar motsi taji a toilet hakan yasa ta goge kwlar idonta tana kallon kofar nihla ce ta fito daga toilet din tana goge gashinta da karamin towel
Nihla ta kalli meenat setaga duk jikinta asanyaye da alama kuka ma tayi zama kusa Da ita tayi tace sis menene waya tabamin ke wani abun ne ya same ki? Meenat ta girgiza kai kwlla nazubowa daga idon nihla tace “subhanallilah meenatuna menene me aka miki Dan Allah ki fada min” meenat ta hadeye wani kafin tace “nihla dama ni kaxanta ce? Meye lefina anan,? Ninayi Kaina? Mena aikata? Bani na aikata lefi ba Amma meyasa lefin ze kare akaina Wanan wace irin duniya ce nasan bani kadai bace wanda iyayena suka sameni ta wanan hanyar wasu suma sun fada mumuna hanyaSaboda kyma da kyma Da tsangwma dasuke fama da ita nihla ta sauke numfashi yayinda meenat ta kara fashewa da kuka nihla tajawota jikinta ta rungumeta tace sorry sis Amma ki fada min abinda ya faru pls Meenat ta gyra zama sanan ta goge hawayenta ta fada mata duk abinda ya faru tsakanin ta da Doctor yusuf jitayi itama hawaye na zubar mata Nihla baya sona saboda lefin da ban aikata ba menayi ni 😭 suma iyayena ai kaddarar su ce yasa suka sameni ta hanyar dabe dace ba *kaico na* nihla ta janyo meenat jikinta tace sis baki aikata komai ba dan Allah kibar maganganun yusuf bashida hankaalin ne kuma dama chan Allah beyi mijinki bane may be ba alkhairi ne a gareki ba shiyasa kuka rabu Allah ya baki wanda ya fishi ya baki wanda yake alkhairi atare dake Meenat ta Amsa da Ameen sanan ta tashi ta shige toilet tayi wanka ta dawo dakin tayi sallah isha’I Dan nihla har tayi shirin bacci itama shiryawa tayi ta kwnta Amma setaji takasa baccin wayarta dake bed side ta dauko ta kuna data Dan ganin sakauni a hankali tayi murmushi ganin an turo book din data fiso wato *ZAMAN HOSTEL* fara karantawa tayi senaga ta fashe da kuka a fili ta furta gaskiyan marubuciyar nan tayi kokari gashi nima nawa iyayen shigen rayuwar dasukai kenan suka sameni ajiye wayar tayi ta kwnta seta fara juye juye har bacci barawo yasace ta.
+
Washe gari yakama monday zasu fara wa’ec se zumudi nihla take da murnar zasu bar school suna gama wa’ec da neco dinsu dama sunyi jamb har yanzu dai ba’a saki result ba zama sukayi a dining din suna breakfast hashim gaba daya hankalin shi nakan meenat dayaga ta canza komai slow take yinsa tea ma spoon biyu tayi tace ta koshi nihla tasame ta a mota dukansu suka zuba mata ido sakina tace nihla meke damunta ne yayinda meenat takeyin gaba nihla tayi gyran murya ta fada musu duk abinda ya faru tsakaninta da yusuf bata boye musu komai ba Daga sakina har hashim ajiye spoon din hanunsu sukayi suna kallon nihla cike da tashin hankali a fuskokinsu nihla ta dauki jakarta ta barsu bawanda yace da kowa komai Hashim ne ya fara kwalla yace kaicona ni hashim na akaita lefi Amma lefin kan y’ata yake komawa sakina tace meenat bata canci haka daga wurin mutaneba mune muka dace a mana haka Hashim ya tashi sakina ma haka suka rungome juna suna kuka tare da tausayawa kansu da yarsu
Koda nihla ta karasa cikin motar illu yajasu nihla tayita kwntarwa da meenat hankali
Bayan wata biyu
Rayuwar iyalan haka ta cigaba da gudana domin meenat tayiwa kanta alkawarin dena kula kowani da namiji result dinsu na jamb dana wa’ec ya fito inda dukansu sunci bawanda ya fadi murna wurinsu kamar………hashim ya karbi result ya nema musu *B.U.K* dakenan kano kuma sun samu
Tafe suke sun dawo daga islamiya suna ta tataunawa kan maganar yarda zasu fara zuwa uni… Dinsu nihla take cewa yakamata a fara barin mu muna driving tunda dai yanzu muba yara bane meenat tace toh sannu manya sukasa dariya
Wata hadadiyar mota ce tazo ta wuce ta gabansu har motar tayi gaba ta dawo wani katon mutumi ya dawo ya bude glass din motar ya kalli meenat sanan ya lashe baki Ya gyda kai bece musu komai ba Seda sukayi nesa dashi sanan yadinga bin bayan su har suka shiga gida ya juya ya tafi
Da dare meenat na sallah taji alamar motsi a bayan gidan su lekawa tayi setaga mutane na dirowa ta baya fuskar su rufe da bakin kyle meenat ta dawo tana toshe baki ta tashi nihla. Meenat tacewa nihla yan fashi ne suka shigo zata saki ihuu meenat ta toshe mata baki basu karasaba suka ji anbanko kofar main palo dinsu nihla tace meenat kinsan irin fashin dasuke yanzu har fyde sukewa yan mata meenat tace munshiga uku
Nihla ta kama hanun meenat tasata a cover zata rufe meenat tace kefa nihla tace Aa meenat bazantaba barin wani abu yasamekiba tayi sauri ta rufe murfin siff din tasa key meenat ta fashe da kuka
Suna haka aka banko dakin nihla ta kalle su katon mutumin yace wuce muje ki kaimu dakin iyayenki nihla tasa kuka ta wuce meenat ma tasaka kuka mara sauti wuce muje nace nihla tasa ihuuu segasu sakina sun fito boss din yace hands up duka suka daga hannu sama suka zube babban su ya kale meenat yace ke ina kanwarki nihla tace banida kanwa ai ya daka mata tsawa yace ke karki mana wasa nihla tace banda kanwa ni se kawata ta islammiya kuma ba’a unguwarnan takeba………………
*Fatiman kuce👌🏽*
Not edited*Y’AR ZINA CE*
_(KADDARAR IYAYENA)_
*PART 2*
_PAGE 9_
*DEDICATED TO MY HABIBTY UMMI ONTOP🥰❤*
_*afuwan fa bana typing sosai kuma kan lokaci saboda matsalar idona👀 se anayi ana kiyayewa*_
Suka maida kallonsu ga hashim wanda ba abinda jikinsa yake se kyarma kallon Nihla yayi yadan lashi bakinsa yace ke tashii muje nihla tasa kuka ta kalli baban ta tace Abba ka temake ni mamyna wayoo Allah da gudu hashim ya mike ze kama hannun nihla ba wani qauqautawa ogan yadawo ya buga masa bindiga akai yacewa nihla ta wuce ihuuuuuu tasa tana fadin wayoooo.
Tushhhh kakejin karar bundiga Alamun anyi harbi wanda hakan yasa sakina sakin kara kallon kofar dakin tayi se kuma ta kalli Dan fashin da aka harba da gudu suka shigo Suka murde hanunsa sukasa sauran duk suka ajiye gun dinsu sanan suka tasa keyar su a gaba suka wuce
(Ni Fatsima nace su nihla anji bahur😂)
Da gudu nihla tayi daki ta bude meenat, meenat ta fito tana tabata tace ba abinda suka miki koo Nihlaa ta daga kai tana jan meenat zuwa palo hashim kuwa har lokacin yana kwnce besan inda kansa yakeba meenat da nihla suma wuce suka debo yan biyu kafin su wuce asibiti……..
Koda sukaje hashim bawani ciwo yaji bah tsabar buguwa ce kawai da Razana da yayi kafin wayewar gari aka sallame su Nihla tayi gaba dasu hashim meenat ta tsaya gyra takalminta daya cire ta gama gyrawa ta mike A hankali zata bar wurin daga kan dazatayi suka hada ido da dr yusuf da sauri tayi gaba har tana hardewa kwla na kokarin zubuwa daga idonta
+
Haka suka koma gida suna jimamin abinda ya faru dasu su kaka sunzo sun musu Allah ya kiyaye dukda jikin kakar se a hankali se fama take da ciwo² na tsofafi wanda baa rasa ba ga ciwon kafa Da take fama dashi
Kamar kullum yau ciwon kaka ya tsananta ba sunan wanda take kira irin sakina a Kira mata sakina tasan mutuwa zatayi Ana rarashin ta Amma Ina
A firgece sakina ta karaso asibitin sedai kafin ta karasa dakin da kaka take kaka Rai yayi halinsa
A hanki ta tura kofar dakin tashiga mom a durkushe tana kuka da sauri ta karasa tana fadin mom kukan me kikeyi ta kali inda aka kwntar Da kaka an rufeta da farin kyle kuka taji a idon ta a hankali tafurta Allah ya jikan ki kaka lokaci yayi sanan ta daga mom data durkushe tace mom kiyi hakuri kaka addua mu kawai take bukata domin kuwa kaka Allah ya bata tayi tsahon Rai Allah sa mutuwa hutu ce a gareta mom ta amsa da Amin sanan aka kira dad da hashim aka sanar musu
************
Bayan rasuwar kaka abubuwa da yawa sun faru ciki kuwa harda yarda nihla ta gano cewa itama ba yar hashim bace itama Y’AR ZINA CE tayi kuka harta gode Allah sanan ta samu miji tayi aure ita kuwa meenat mutane da dama sunzo neman auran ta amma Da zarar anji asalinta se a gudu wasu suce sun yarda Amma iyyayen su basu yarda a haka hartayi zurfi a karatun ta Dan ta cirewa kanta son Aure kuma tama kanta Alkawarin bazata Kara soyaya ba
Tafiya take da sauri sanadin iska da Akeyi kuma da hadari a garin da alama ana San ruwa ze sauka kara saurin tayi saboda tana gudun kar ruwan ya sauka akanta
Kiiiiiiii kakeji alamar tsayawar mota ba shiri a fusace me motar ya fito ze mata masifa, “baky kallon gaban ki ne zakisa na bigeki” dagowa tayi tana rawar sanyi tace Allah ya baka hakuri tayi gaba shikuwa tsayawa yayi yana kallonta harta danyi nesa da ita da sauri ya hau motar yabi bayanta harta shige gidan su yana kallon ta girgiza kai yayi yace Ashe nan ne gidansu kenan makociyar mu ce
Fatiman kuce*Y’AR ZINA CE*
_(KADDARAR IYAYENA)_
*NA*
*MUNEERA*
*PART 2*
_PAGE 10_
Kamar kullum yanda meenat tasaba tafiya school haka yauma akayi tana zaune a bayan mota driver najanta, kallon titi take ta window zuciyarta cike da tunani kala’kala.
Motar suce ta tsaya nan driver yafara kokarin tayar da motar, ganin bazata tashi ba yasa yafita waje danya dubata yana fadin hajiya meenat kiye hakuri barin duba matsalan
Kusan 15minutes sai famar abu daya akeyi motar taqi tashi ganin haka yasa meenat fitowa bakar abaya mai dauke da beat hade da ratsin brown a gabanta shine sanye a jikinta a kai ta yafa siririn gyalan wanda ya rufe mata wuya brown zara mini bag ce rige a hannunta takalmin dake sanye a kafarta kalan jakarce sai baqin agogo dake sanye a hannunta. Tabbas tayi kyau dukda ba kwalliya a fuskarta bayan powder da nude lipstick sai k’walli da tasa ma kwayar idonta.+
Cikin girmamawa wanda daman tsabi’antace a jininta yake takarasu kusa da driver tace baba meke faruwa ne?
Da yake driver dattijo ne.
Hajiya meenat wlh nima bansaniba amma ina dubawane yanzu zamu tafi da yardan Allah kiye hakuri
Matsawa tai gefe hade da jingina da jikin motar tana kallon titi, wata bakar marcendez venz mai dauke da tinted glass tazu tawuce saikuma motar tai slow tana dawuwa da baya da baya.
Itakam meenat hankalinta nakan dan karamin jote note din dake hannunta tana sake reversing karaton datai jiya da daddare danko test ne daita da safe nan.
Ta cikin motar yake kare mata kallo murmushi yai sanan yafurta tabbas ta hadu gakuma nutsuwa atare daita, ton jiya dana daura ido akanki nakasa samun nutsuwa sai tinanin’ki nakeyi
Agogon hannunta ta kalla gani tai saura 15minutes karfe takwas tayi cikin nutsuwa tace baba barin hau kekenapep kawai ina da test karfe takwas kuma malamin bashi da mutunci ko minti daya na kara bazai barni na shiga ba.
A’a hajiya meenat wani irin kekenapep a’a kibari nakira gida sai a kawu wata motar, murmushi tai sanan tai gaba tana fadin nayau kawai dazan hau karka damu baba ka kira mechanic a tafi da motar
Yana zaune cikin mota duk yana sauraranso da yake yasauke glass din, jin haka yasa yafito dasauri yanufi inda take
Hannu tasa tana tsaida napep karasuwa gabanta yai game daciwa assalamu alaikum
Kallonshi tai sanan ta amsa sallamar ciki ciki, koda suka hada ido tsaf ta ganeshi shine na jiyanan wanda yakusan bigeta da mota sanan ya hauta da masifa.
Bata karasa tunanin da takeba taji muryanshi naciwa idan bazaki damu ba muje na saukeki a school mana karkiyi late
Kin yarda tayi saida yaita bata hakuri ganin zatai late yasa tashiga sanan duk napep din data tsayar sai yace mishi yawuce kawai.
Shida kanshi yabude mata gaban mota tashiga, sanyi Ac hade da kamshin tularenso ne ya gauraye motar yabada wani kamshi mai dadi, driving yake kana ya juyu ya kalleta yace wani school zamu nufa.
B.U.K abinda kenan tace murmushi yai sanan yace sunana Aliyu unguwan mu daya bamu dade da dawuwa unguwar ba.
Ok
Abinda kenan meenat tace
Ya lura bata cikason magana ba, amma hakan be hanashi mata tambaya ba, ya sunan…..
Be karasa ba tace sunana Ameenatu ana kirana meenat ka kwantar da hankalinka basai ka tambaya’ba ina da niyyan sanar dakai, nune ta mishi da wani gate tana fadin ta gate dinan zaka shiga.
Godiya ta mishi sanan tafita a motar cikin sauri sakamakon late din da tayi
************
Yauta kasance Saturday ba aiki zaune iyalan gidan suke a parlor sai hira suke cikin nishadi suna dariya twins kowa sai wasa sukeyi.
Daka bakin kofa sukaji sallama dasauri meenat tai mige hade da rungume nihla tana fadin oyoyo sannu da zuwa, shine baki fadamin zakizu ba
Hannunta rige dana meenat take fadin surprise nace zan miki, karasawa gurin Hashim tai tana fadin daddy ina wuni sanan tajuya gurin sakina ta gaisheta.
Amsan gaisuwa yai sanan suka soma hira cikin farin ciki sunjima suna hira daka bisani nihla taja hannun yar’uwan nata sukai daki.
Kallon table din dake gefe nihla tayi wanda daman anyishi dan karatu ne books da hangout ne baje akai murmushi nihla tai kana tace meenat kenan duk karatun test dinne haka aka baza text books da handout kamar wani exam.
Itama murmushi dauke a fuskarta tace kema haka yakamata kifara wanan semester inaso grade dinki yafi nawa
Kwanciya nihla tai game daciwa tafdi wani ne?
Ai brain Dina bayaja kamar naki karfa ki manta G.P.A dinki yafi nakowa a class dinmu tonda muka shiga gaba kikeyi baki taba dawuwa baya ba nasan kezaki fita da first class tare da samun gifts kala’kala
Shiru meenat tayi nadan wani lokaci sanan tace nihla bani dawani abu daya kamata na maida hankali akai dayawuce karatu so nake nayi karatu mai zurfi shi kadaine a gabana. Dafa kafadan meenat tayi hade daciwa meenat ya baton aure?
Wasu hawayeni yazuba a idonta sanan tace nihla na cire aure a zuciyata na hakura da aure har karshen rayuwata kamar yanda na fada miki karatuni a gabana kawai wasu hawaye ne yasake sauka a kuncinta sanan tace nihla inaso zuciyata ta huta inaso na gujema gori da wulakanci daka guri masu ciwa suna kaunata, sanin kankine duk wanda yace yana sona da yaji ta hanyar da aka sameni sai ya rabu dani, da rabuwa sukeyi dani batare dasun cutar dani da bakaqen magana ba abun da sauki so na hakura da aure hasalima a yanzu bana kula maza bana sauraran duk wani wanda yazumin da maganar soyayya.
Itama nihla kuka tasa tana fadin meyasa haka ke faruwa dake bayan nima yar zina ce, meyasa haka bata faru dani ba saike baiwar Allah wace kaddara ce ta fadama iyyayanki
Murmushi mai ciwu meenat tayi kana tace kidaina hada kanki dani nihla danko ke asirinki a rufe yake nikuma nawa a bayyane yake….. Da munbar zancan nan inaga haka zaifi.
Tashi nihla tai game da ciro wayarta a jaka gallery tashiga hotan wani saurayina ya bayyana fari ne tas dashi cikin kananan kaya ya jingina jikin wata tsadadiyar mota an kashe mishi portrait… Lol
A takaice dai guy din ya hadu ga kudi ga kyau dukda dai nihla bata riga ta fadamana ko waye shi ba😊
Migama meenat wayan tai kana tace kinganshi sunanshi prince yazeed yaron tsohon shugaban k’asa ne abokin mijinane tonda yaga hotanki ya rude sai maganarki yakeyi amma naqi bashi dama akanki ina ganin shima kamar sauran wayancan mazan ne
To saidai ba haka bane danko ya tabatarmin daciwa shifa auren ki yakeso yayi da naga ya nace shine nasanar dashi komai game dake tabbas ya tausaya miki meenat kuma yace zai aureki a haka. kuma ya tabbatarmin daciwa bashi dawata matsala ta bangaran iyayanshi zasu amince da maganar aure.
Daukar wayan meenat tai tana fadin barinsa miki number dinshi dan yana da number dinki dama yakejira yasamu saiya fara kiranki.
Itadai meenat batace komai ba sai hawaye dake zarya idonta, hannu nihla tasa ta share mata hawayen tana fadin kidaina kuka sanin kankine bazan kawu miki abinda zai cutar dake ba, nidai kawai abinda nakeso dake shine karkiyi saurin karaya bamusan inda zamu dace ba.
Migewa tsaye meenat tai cikin kuka take fadin nafada miki nacire aure a zuciyata… ba aure na zaiyiba, shima zai gujeni kamar yanda sauran sukeyi, nagaji, nagaji, nagaji kibar zancan kawai bani da ra’ayi akan duk wani da namiji a yanzu ba dole sai nayi aure ba zan karasa rayuwata a haka
Fatima kuce👌🏽👌🏽*Y’AR ZINA CE*
_(KADDARAR IYAYENA)_
*NA*
*MUNEERA*
*PART 2*
Happiest birthday to princess Aysher❤ I wish and pray that you stay blessed I wish that you get all what you wish for I just want that you stay happy forever You are and will remain my special friend Happy Birthday to you May God bless you!
+
_PAGE 11_
Karasa maganan tai da fashiwa da kuka, itama nihla kuka tasa dan meenat tabata tausayi sossai.
Sunkai ten minutes a haka kafin nihla ta lalashi zuciyar ta game da share hawayenta, rungume meenat tai a jikinta hade da bubuga bayanta tana fadin calm down, calm down my dear, stop crying please banson ganin hawayanki karasa maganan tai dasa hannu ta share mata hawaye.
Ajiyar zuciya meenat take saukewa yayinda nihla kecigaba da bubuga mata baya saida nihla taga hankalinta yadan kwanta sanan ta mige hade da debu mata ruwa mai sanyi ta bata.
Shanye ruwan tai kana ta aje cup din tana fadin nihla nagode, murmushi nihla tai sanan tace meenat na fahimce duk abinda kike nufi dakuma abinda kike gudu na fahimce abinda yasa bakiso kiye accepting prince yazeed amma meenat inaso ki janye ra’ayinki kamar yanda nafada miki a baya yanzu zan sake fadamiki karda kiye saurin karaya bakisan inda za’a dace ba nidai kawai kicemin kin amince meenat idan ba haka ba nima zan kashe aure na kinga saina dawu gida muyita zama anan
Dasauri meenat ta toshe bakin nihla hade da fadin subhanallahi Allah ya kyauta ki kwantar da hankalinki na amince nihla farin cikin ki shine nawa
Aida sauri nihla ta rungume meenat tana dariya hade da fadin yauwa tawan nagode meenat, nagode sossai daukar wayan meenat tai tana fadin zan bashi izini yakiraki karasa maganan tai da bata peck a kumatu tana fadin inason ki meenat.
Murmushi meenat tai sanan tace nima inason ki nihla.
***************
Tohm a bangaran Aliyu kowa yakasa samun sukuni danko ya Kamu da son meenat yarasa inda zaisa kanshi, gashi ton ranan daya sauketa a school basu sake haduwa ba har fitowa yake yazauna a kofar gida ko zasu hadu amma ina basa haduwa hakan yasa ya yanke shawaran zuwa gidanso.
Knocking gate din yakeyi mai gadi ne ya amsa daciwa ana zuwa, koda mai gadi ya bude hannu yabama Aliyu suka gaisa dan sun saba haduwa a masallaci magana ce bata shiga tsakanin’so.
Dan’Allah meenat nake nima sallama zakaimun daita.
Cikin mamaki mai gadi yanufi cikin gidan dan yayi mishi sallama da meenat dan yasan ba fitowa zatai ba sauda dama ana zuwa nimanta amma saitace ace batanan.
A parlor ya sameta cikin girmamawa yace hajiya meenat ana sallama dake a waje, bata fuska tayi kana tace je kace bana’nan. Sakina dake zaune a gefe tace haba meenat aiya kamata kifara tambayan ko wanine kafin kice ace bakinan.
Kallon mai gadi tai sanan tace wanine ke nimata?
Mai gadi ne yace wallahi bansan shiba amma dai muna haduwa a masallaci kamar a unguwar nan yake
Sakina ce tace to kingani dan’Allah tashi kije bakisan ko wanine ba je kiji… Ba yanda meenat ta iya haka ta tashi riga da skirt ce ta atamfa a jikinta ta daura dankwalin a kanta fuskarta ba kwalliya.
Mai gadi na gaba tana biye dashi a baya harsuka karasa, tana lega waje suka hada ido da Aliyu, kallonta yakeyi batare daya gifts ido ba danba karamin kyau tamishi a haka ba.
Hade fuska tayi sanan tace kaine kake nimata?
Lafiya dai ko?
Gyara tsayuwanshi yai game da kalmashe hannayan’shi sanan yace gaskiya ba lafiya ba meenat akwai babban matsala, fito da ido waje tai kana tace ba lafiya ba meke faruwa?
Fito da wayarshi yai ya miga mata yana fadin samin number dinki zamuyi magana a waya, tsintar kanta tayi da kasa hanashi number dinta
Amsar wayan yayi yana fadin zan kiraki zuwa anjima bayan magrib zamuyi magana
Tohm shikenan Allah yasa naji alkhairi abinda kenan tace sanan sukai sallama ta koma cikin gida koda tashiga gida saida sakina ta tambayeta wanine
Nan tayi mata bayanin duk abinda yafaru dakuma farkon haduwanta da Aliyu.
A bangaran yazeed kowa bada wasa yakeson meenat ba yazu yaganta har gida tabbas ya yaba da hankalinta kuma har zuciyarshi aurenta zaiyi ya lura da babu kaunarshi a zuciyarta amma be damuba ya tabbata a hankali kuma a sannu zata so shi.
Kamar yanda Aliyu yasanar da meenat bayan magriba zai kirata aiko haka akayi number ce taga tana kiranta kamar bazata dauka ba saikuma ta dauka data tina Aliyu yace zai kirata after magrib.
Muryar’shi ce ta bugi kunnenta amsa sallamar tayi sanan tayi shiru
Nasan bakisan wake magana ba kor?
Dafarko dai sunana Aliyu zailani wanda yace zai kiraki bayan magriba
Ok
Ina jinka abinda kenan meenat tace
Meenat kamar yanda nafada miki sunana Aliyu Zailani ne ma aikacin governati ne kuma ina business a haka nake samun nashan garin rugo, wallahi tonda na daura ido akanki na Kamu da sonki nakasa sokuni.
Meenat dan’Allah na rugeki kibane dama na nuna miki irin kaunar da nake miki karda kice baki sona tonda nake a rayuwata bantaba furta ma wata mace Kalmar ina sonta ba ban taba taran mace da baton soyayya ba mata su suke ciwa suna sona amma basa gabana dan na dauki hakan a rashin kamun kai. Akanki nafara taran mace da maganan soyayya
Dan gunton tsaki meenat taja wanda saida Aliyu yaji
Hmmm meenat kice wani abu ba tsaki zakiyi ba bansan mezance ki yarda ina kaunar kiba ban iya kalamai ba ko?
Inaso ki yarda dani kuma kisa ma zuciyarki Aliyu na matukar kaunarki
Tsaki ta sakeyi hade da fadin mallam da nasan abinda kenan zaka cemin wallahi daban baka number taba, nazata wata magana mai muhimmanci ce ashe da shirme kazu.
Aliyu ne ya katseta daciwa meenat wallahi bada shirme nazu ba, wallahi ina sonki believe me i love you in a way i can’t explain karasa maganan yai muryanshi na rawa kamar zaiyi kuka
Lumshe ido meenat tayi a zuciyarta tace da kasan ne,YAR ZINA CE da bazaka bata wanan lokacin a kaina ba
Sunanta yakira..meenat..
Naamm uhmm Aliyu sunanka kor?
Dan’Allah kafita harkata idanma da gaske kake kana sona ka gagauta cire soyayyata a zuciyarka dan Ameenatu bata soyayya karasa maganan tai daciwa nagode sossai dan dole na godema wanda yace yana sona koda da wasa ne.
Dakatar daita yai daciwa meenat dan’Allah kibani dama na nuna miki kaunan da nake miki
Dariya tayi sanan tace am not interested i hope you understand?
Meenat wallahi ina sonki so bana wasa ba nasan duk abinda zan fada miki bazaki yarda ba nidai abinda nasani words are not enough to express how much i truly love you, I love you in a way i can’t explain……
Kashe wayarta tai game da cillata gado sanan ta lumshe idonta maganganun Aliyu na yawu a kanta
Shima a bangaran’shi dafe kanshi yayi yanajin wani zafi a zuciyarshi, a fili yafurta Allah kasan zuciyata da kya’kyawan zuciya dakuma niyya mai kyau nakeson meenat bada wata manufa ba.
Zirga zirga ya farayi a daki yana fadin daman haka soyayya take?
Haka yan mata da sukeciwa suna sona sukeji?
”’Tohm kunji wata sabuwa fans tsakanin yazeed da Aliyu wa kuke ganin zuciyar meenat zatai accepting?”’
”’Towai da gaske sukema? tsakani da Allah suke sonta🤔”’
Fatima kuce👌🏽👌🏽*Y’AR ZINA CE*
_(KADDARAR IYAYENA)_
*NA*
*MUNEERA*
_Wattpad👉🏻Fatimamuneera001_
*PART 2*
_PAGE 12_
”’After one month”’
Zuwa wanan lokacin meenat tafara sakin jiki da yazeed bawai tafara sonshi bane dukda ba gari daya sukeba but every weekend yana kano saboda meenat.
Ton tana wulakanta Aliyu tanaqin daukar wayarshi, idan sun hadu a waje ta shareshi koda yai mata magana, sauda dama yasha binta school danko gadinta yafarayi dawuri yake shirin zuwa office saiya packer mota yazauna a ciki dazaran yaga driver meenat yafito saiya bisu a baya har school.
+
Amma duk abinda yakeyi a banza danko meenat bata sauraran’shi, yanda yake turo mata text messages na soyayya dakuma ban hakuri akan ta dinga daukar wayarshi hakan yasa meenat tausaya mishi harta fara daukan wayan amma abunda yabata mamaki shine tana daukan wayan Aliyu ya saka kuka yana fadin haba meenat abinda kike kina ganin yadace kinsan yanda kike azabtar da zuciyata kowa?
Meyasa kike wulakantani bayan bani nasa ma zuciyata kaunar kiba, Allah ne ya jarabceni dan Allah kiye hakuri ki sasautamin ki amsa soyayyata bazaki tabayin dana sani ba dan’Allah meenat
Tausayin Aliyu ne yacika zuciyarta gaba daya sai taji tana matukar tausaya mishi wai itace namiji kema kuka yau…Allah sarki
Cikin sanyi murya meenat tace dan’Allah kadaina min kuka fadamin me kakeso amma banda maganan soyayya dan meenat bata soyayya bazata iya mallaka wa kowa zuciyarta ba.
Dogon ajiyar zuciyar yasauke kamar zaice wani abu saikuma yace to shikenan amma dan’Allah na rugeki kidinga daukar wayata sanan duk sanda nazu nimanki kifito kitaimakamin meenat ne kaina bansan irin kaunar da nake miki ba
Tsintar kanta tayi dajin tausayinshi cikin sanyin murya tace to shikenan
Kamar yanda Aliyu ya roga meenat akan ta amince mishi yadinga zuwa gurinta haka kowa akayi ta amince mishi yana zuwa amma a kwanakin da yayi yana zuwa babu abinda ta lura dashi bayan tsan’tsan kaunarta a zuciyarshi tabbas a yanzu ta yarda Aliyu na sonta so mai karfi wanda ita kanta abun nabata tsoro.
Kamar kullum motar gidanso ta danno kai waje dan kaita makaranta dasauri Aliyu yafito daka motar shi sanan yakarasa gurin motan
Knocking window yayi hade da kallon meenat yana smiling, itama kallonshi takeyi saboda yayi mata kyau
Aliyu dai baqi ne amma kyakyawan ne wanda samun irinshi a cikin baqaqe zaiyi wuya, murmushi dauke a fuskar meenat tabude motar tafito
Atare suka furta kinyi kyau… Kayi kyau…
Murmushi tayi sanan tace nikam babu wani kyau da nayi amma ka ganka kowa barin maka hoto, nanta shiga kashe mishi hoto sanan sukayi wasu tare.
Agogon hannunta ta kalla kana tace yakamata natafi karnayi late
Hannu ya daga mata game daciwa
Ok byee
I luv you
Murmushi tai batare da tace komai ba
Kwance Aliyu yake a bed sai juye’juye yake yana tunanin yanda zai bulloma lamarin meenat, shi kanshi besan wani irin so yake mata ba tabbas bashi dawani buri daya wuce yaga ya mallaki meenat amma ya zaiyi? Wani tunani yayi wanda yasa yasauri ya mige tsaye yana fadin yauwa ina ganin zansamu mafita ta haka, cikin hanzari yafita daka dakin.
Babban parlor yanufa inda ya iske iyayan nashi su uku suna zaune hira(Maman Aliyu tana da kishiya itace uwargida amma zaune suke lafiya ba tashin hankali akwai fahimta mai karfi a tsakaninso)
STORY CONTINUES BELOW

Durkusawa yai yazauna a kasa game da gaishe so amsawa sukai sanan mum ta kalleshi tace Aliyu yanaga kayi shiru kamar dawata magana a bakin’ka(mum itace kishiyar Maman Aliyu)
Eh mum daman wata magana nazu daita alfarma nake nima a gurin daddy
Daddy ne ya maida hankalinshi kan Aliyu sanan yace menine Aliyu
Ina sauraranka
K’asa yai da kanshi kana yace daddy daman aure nakeso ka nimamin nasamu mata shine naga ya kamata manya su shiga abun
Wani irin farin ciki ya lulube umman Aliyu ba ita kadaiba harda mum da dad.
Allah ya tabbatar da alkhairi aihaka mukeso mum ce tai magana
Umma ce tace Aliyu aina yarinyan take?
Shima Dad abinda kenan ya tambaya?
Daddy yar makwaftar muce nan Aliyu yasanar dasu gidanso meenat.
Shiru dadi yai nadan wani lokaci sanan yace zanyi bincike akan tarbiyyan yarinyan kafin naga mahaifinta
Da farin ciki Aliyu yakuma dakin’shi danko ya tabbata meenat nada tarbiyya baza’a taba samunta dawata muguwar dabi’a ba.
**************
Kamar yanda daddy yace zaiyi bincike akan meenat haka akayi yayi bincike akanta tabbas tasamu kya’kyawan shaida inda kowa ke yabawa da kyawawan dabi’arta saidai kuma abinda mahaifin Aliyu yaji dangane daita ya daga mishi hankali saida yai tunani yaga yarinyan tasamu kya’kyawan shaida kowa na shaida ga tarbiyya sai hankalishi ya kwanta.
Zaune suke a parlor Aliyu na zaune a kusa da mahaifanshi
Daddy ne yakira sunan shi
Aliyu
Naam daddy
Nayi bincike akan yarinyan da kazumin da maganarta wato Ameenatu.
Mahaifiyar Aliyu ce tace yauwa Alhaji wani irin shaida kasamu game daita?
Maida kallonshi yai gurin umma sanan yace tabbas yarinyan tasamu kya’kyawan shaida mutane da dama sun yaba da hankalinta ban sameta dawata muguwar dabi’a ba but saidai an tabbatarmin daciwa YAR ZINA CE bata hanyan aure aka sameta ba.
A firgice Aliyu ya daga kai yana kallon daddy game da fadin ina karya sukeyi daddy daka gidan mutunci meenat tafito sharrin mutanine kawai SHARRI suke mata.
Shiru daddy yayi harsai da Aliyu yagama surutan’shi sanan yace
Aliyu kagama banbamin naka?
Yakamata kasani babu wani sharri a cikin wanan maganan tabbas haka lamarin yake meenat YAR ZINA CE saboda mutanan da suka fadamin haka sunfi goma kuma mazaunan unguwar nan ne kaiiii bari kaji harta driver gidanso ya tabbatarmin da haka.
Tsohon driver ne ya dade yana musu aiki da mutane suka sanar dani ban yardaba harsai dana tuntubi driver nan yasanar dani gaskiyan lamarin kuma ya rogeni dana amince ka aure meenat dan yarinyace mai tarbiyya bata da matsala ko kadan itama ba laifinta bane kaddarar iyaye ce karasa maganan yai daciwa Aliyu na amince ka aure meenat a shirye nake dana nima maka aurenta.
Umma ce ta mige tsaye game dafara zazagu masifa tana fadin ina ban amince ka aureta ba yarinyan da akace Yar ZINA CE shine zaka kawu mana kazanta gida banyarda ba gwara ton wuri kafita harkanta.
Mummy ce ta tari numfashin umma tana fadin haba hajiya abu nikam banga wani abuba idan Aliyu ya aure yarinyan tonda dai yarinyan nada tarbiyyan arziki da halayya mai kyau inaga ai shikenan
Aliyu haryanxu yakasa yarda mamaki yakeyi wai meenat ce yar zina, gani da yayi mahaifiyarshi sai masifa take sai yaji duk babu dadi tashi yayi yakuma kusa daita yana fadin umma kiye hakuri kibar daddy ya nimamin auren meenat wallahi ina matukar kaunarta idan ban aure taba komai zai iya faruwa
Hanyar daki umma tanufa tana fadin idan ka aure meenat to bana numfashi ne amma bazan taba yarda ka aure yar zina ba.
Haka kowa yakuma daki zuciya babu dadi.
Yazeed ya nime meenat tabashi izini yaturo magabatan’shi badan tana sonshi ba ta amince mishi daya turo magabatan’shi kuma tasanar da Hashim.
Daka Hashim har sakina ba karamin farin ciki sukayi ba
Yazeed ya turo magabatan’shi an tsaida lokacin aure ba’aja abun da tsawu ba danko five month akasa bikin.
Tonda meenat taga an tsaida maganan aurenta da yazeed tafara kokarin sama zuciyarta kaunar’shi kokari take taga tafara sonshi kamar yanda yake sonta.
Mahaifin Aliyu bebi takan umma ba yaje ya nimama Aliyu auren meenat
Yaci sa’a Hashim na gida a babban parlor suka zauna bayan sungama gaisawa Hashim ya kalla mahaifin Aliyu yace amma saidai kuma ban gane kaba.
Murmushi mahaifin Aliyu yayi sanan yace eh a gaskiya baka San niba sunana Alhaji Zailani bamu dade da dawuwa unguwar nan ba, daman nazu nimama Dana auren yarka meenat ina fatan za’a bamu?
Murmushi Hashim yao kana yace Allah sarki amma meenat nada mijin ansa ranan aurenta nadan wata biyar Insha’Allahu zan aurar daita.
Mamakine yacika zuciyar mahaifin Aliyu gani yake kamar karya hashim yakeyi ba yanda zaiyi haka yaima Hashim godiya sanan yakuma gida.
Koda yasanar da iyalanshi yanda sukayi da mahaifin meenat ba karamin farin ciki umma tayiba, shikowa Aliyu hankalinshi yai matukar tashi inda yake ciwa
Daddy babu wani miji da sukai mata meenat bata sanar dani wanan ba, dan girman Allah daddy ka taimakamin wallahi ina son meenat, umma ce ta katse shi daciwa Aliyu ka gagauta cire yarinyar nan a zuciyarka in banda kaida abinka mezakayi daita ai kafi karfinta takoina kaida kake tsabtace ya kake kokarin dauko kazanta wacce aka haifa ta gurbataciyan hanya ton wuri kacire son yar zina a zuciyarka
Mummy ce ta dafa kafadan Aliyu tana fadin yarona ka kwantar da hankalinka kabar komai a hannun Allah idan meenat matar kace duk yanda akaso da hanaka sai kaga ka aure ta nidai Allah yasani ton banga yarinyar nan ba naji ina kaunarta har zuciyata.
Maida kallonta gurin umma tayi tana fadin hajiya abu kibar Aliyu ya aure yarinyar nan kiye tunani ba laifinta bane kaddarar iyaye ce
Tashi umma tayi kana tanufi daki tana fadin kaddara a aikin sabon Allah lallai kam, ai yanzu magana ta kare tonda mahaifinta yai mata miji
A kwance take a gado wayarta tafara ringing
Hello
Zuciyata ina fatan kin wuni cikin koshin lafiya?
Alhamdulillah! Ina fatan kaima haka abinda kenan meenat tace
Cikin damuwa Aliyu yafurta a’a nikam ina cikin damuwa
Kasa tai da murya sanan tace wace irin damuwa
Hmmm meenat ashe anyi miki miji shine baki sanar dani ba?
Kodai dad dinki yafadane kawai?
Murmushi meenat tayi daman jira take yamata magana dan Hashim yasanar daita yanda sukai da mahaifin Aliyu nanta sanar da Hashim duk abinda ke tsakanin so.
Aliyu kamar yanda daddy yasanar da dad dinka anyimun miji to tabbas haka abun yake kayi hakuri.
Ji yayi zuciyarshi na bugawa da karfi da karfi ga wani jiri da yake gani daka zaune, tine yafara ambaton innalillahi wa’ina ilaihi raji’un meenat ya zanyi?
Ya kikeso nayi da rayuwata?
Idan ban aure kiba zan iya rasa rayuwata
Ita dai meenat shiru tayi dan Aliyu na masifan bata tausayi cikin tausayawa tace kayi hakuri Aliyu
Fatima kuce👌🏽👌🏽*Y’AR ZINA CE*
_(KADDARAR IYAYENA)_
*NA*
*MUNEERA*
_Wattpad👉🏻Fatimamuneera001_
*PART 2*
_PAGE 13_
Auren meenat sai matsowa yake danko saura wata biyu izuwa wanan lokacin yazeed yayi nasaran sace zuciyan meenat tafara sonshi soyayya sukeyi sossai kullum cikin godiyan Allah take daya kawu yazeed cikin rayuwarta yasan komai game daita amma dukda haka yana kaunarta.
Aliyu da meenat basu fasa waya ba kuma suna haduwa amma daya dauko mata maganan soyayya take dakatar dashi tausayi yake bata.. Tarasa meye dalilin da take tsananin tausayin Aliyu bataso taga yana mata kuka amma aduk sanda suka hadu saiya zubda hawaye yana ruganta ta karba soyayyan’shi.
+
A tsaitsaye Aliyu sai Rama yakeyi iyayanshi sun lura da haka sauda dama daddy yasha zaunar dashi yayi mishi nasiha akan yabarma Allah komai kuma yayi kokarin cire meenat a zuciyarshi dan matar wani ce mahaifinta yai mata miji.
Auren meenat saura 2weeks inda haduwa ita da Aliyu yai musu wahala sakamakon gyaran amarya da ake mata tonda bikinta ya matso hankali Aliyu ya dada tashi fiye da’da
Sauda dama yakan ruga Allah akan yacire mishi soyayya meenat a zuciyarshi tonda bazasu kasance a matsayin mata da miji ba, abinda ya yarda dashi Allah ne ya jarabce shi da soyayyan meenat a matsayin kaddara a rayuwarshi.
Sanye take cikin riga da skirt na atamfa wanda dinki ya amsa jikinta, ba kwalliya a fuskarta amma tayi matukar kyau sai glowing takeyi tana shige hasken farar fatarta ta sake fitowa tamkar a taba jini yafito, tsaye take jingine jikin mota yayinda shima yana tsaye a gabanta hira suke suna dariya dakin ganso kinsan suna cikin nishadi sanan akwai soyayya mai karfi a tsakaninso.
Meenat wallahi kamar karna tafi banaso nayi nisa dake, cikin sanyi murya tace final choice saurin me kakeyi yaufa saura kwana goma a daura aurenmu zamu kasance tare harsai kagaji da ganina
Hannunta ya rige yana fadin waya fadamiki zan gaji da ganinki bana gajiya da kallonki, jin muryanki komai naki bana gajiya dashi meenat a lokaci daya kika sace zuciyata ton randa naje gidan nihla naga hotanki a parlor dinta shikenan na gagara samun nutsuwa ashe Allah yayi ke rabu tace
Sunanta yakira
Ameenatu
Kanta na sunkuye a kasa ta dago ta kalleshi tare daciwa naaam
Murmushi yayi sanan yace idan natafi yau shikenan bazamu sake haduwa ba sai ranan da aka daura auren’mu.
Shiru tayi batare da tace komai sai murmushi da tayi
Ton lokacin da meenat da yazeed suka fito daka cikin gida Aliyu nazaune cikin motarshi yana kallonso basu lura dashi ba saboda motar tana nisa dasu kuma tinted glass ce dan haka baza suga wanda ke ciki ba
Waya yazeed yaciro a aljihun’shi yashiga daukanso huto shida meenat yana fadin wanan shine last pic din dazamuyi kafin muzama mata da miji.
Bayan sungama picz dinne meenat tace zata shiga gida shima yakamata yatafi tonda karfe biyar da rabi flight dinso zai tashi zuwa abuja yanzu kuma biyar da minti goma.
Kalmashe hannayanshi yai a kirjinshi kana yace ne bazan tafiba har idan baki kalla cikin idona kincemin I love you ba
Sunkuyar dakai tayi kasa sanan tace ne ina sonka yazeed. Matsawa kusa daita yai sanan ya tallafu fuskarta yace haba meenat dan’Allah ki kalleni ido cikin ido ki furtamin wanan kalmar dan Allah meenat kunya ce taji ta kamata dasauri ta shige gida a guje
Aliyu kowa dake zaune cikin mota yana kallonso zuciyarshi ce take bugawa da karfi yanajin wani bakin ciki daya tokare makoshin’shi wanan shi ake kira da son masu wani koshin wahala dakyar ya tada motar shi yakarasa gida
STORY CONTINUES BELOW

Ton daka wanan ranan Aliyu karfi hali kawai yakeyi amma ba lafiya bane dashi
*****************
Yau auren saura sati daya yau aka kawu komai da komai daka sadaki har kayan lefe, an kashe kudi ba kadan’ba an baza dukiya a lefen haka suma su Hashim sun basu tukuici mai soka inda sukai musu tarba mai kyau… Hmmm nikam Muneera nace abinka da auren manya.
Ganin meenat yayima Aliyu wahala hakan yasa yasake shiga cikin wani hali.
Tana dakin sakina wata yar uwarso ta shigo hannunta rige da waya dana fadin meenat sai waya ake miki ton dazu. Da yake gidan yafara cika da baki yan Rikadawa sunfara zuwa.
Amsa wayar tayi sanan tafita daka dakin.
Meenat dan girman Allah kifito waje inason magana dake danAllah meenat
Aliyu a gaskiya bazaiyu nafito ba kayi hakuri karfe tara da rabi fa yanzu yaza’ai nafita waje dukda ana hidiman biki nayi maka alkawari gobe da safe mu hadu a kofar gida inaga wanan haduwan ita zata kasance haduwarmu ta karshe dan jibi zamu fara event.
Sama sama taji yana fitar da numfashi sanan yace ina ganin kamar mutuwa zanyi meenat da wuya idan zankai gobe ninasan yanda nakeji a jikina dukda banjin dadin jikina haka nai kokari na taku kofar gidanko, meenat na tabbata daka randa aka daura aurenki rayuwata tazu karshe da kinyi hakuri kinfito koda fuskarki na kalla zanji dadi watakila yau itace rana ta karshe dazaki sani a ido kafin Allah ya dauki rayuwata
Hawayeni ke zuba a idon meenat tabbas tana tsananin tausayin Aliyu tsinta kanta tayi dace mishi bazaka mutu ba Aliyu Allah zai hadaka da wace tafini komai ka jirani ganinan fitowa
A boye meenat tafita daka gida bakar jalabiyya ce a jikinta inda ta yafa farin gyale a kanta ba kwalliya a fuskarta amma tayi matukar kyau
A bakin gate ta tsaya inda haske bump ya haska ko wani bangare da lungu nagurin iska ne ke kadaga mai dadi yayinda flowers ke motsi sai waige waige take ko zataga Aliyu gaba ta sakeyi kadan mutum ta hango a tsugoni sanye cikin bakin wando da farar riga.
Dafarko tazata ko fitsari yakeyi saita tsaya hade da juyawa mishi baya amma yunkurin amai da taji yasa tai sauri juyawa hade da nifan gurinshi
Haske bump din dake gurin ne ya haska mata fuskan Aliyu inda yabata rigarshi da amai jini
Dakarfi tafurta amai jini?
Cikin tashin hankali ta dafa kafadanshi hade da tsugonawa kusa dashi ta rungumeshi a jikinta ita kanta batasan sanda tai haka ba
Kuka tasa tana fadin Aliyu sannu meke damunka haka? ne Ameenatu nashiga uku. Aliyu kazama mai yarda da kaddara karda ka kashe kanka kaima iyayanka asara akaina.
Koda yagama amai zamewa yai yazauna a kasa itama meenat din a kasa tazauna kanshi na kirjinta yayinda tanajin bugawan zuciyarshi da karfi da karfi. Hannunta ya rige sanan ya daura daidai saitin zuciyarshi yana fadin meenat kinji yanda zuciyata ke bugawa na tabbata mutuwa zanyi
Da karfi zuciyarshi ke harbawa yayinda gurin yadauki zafi kuma nace ilahirin jikinshi yadauki zafi, kuka tasa tana fadin ne meenat nashiga uku yazanyi?
Murmushi yai sanan yace ki taimaka min mu karasa kofar gidanmu mai gadi zai karasa dani ciki. Dare nayi yakamata ki shiga gida ina miki fatan alkhairi a auren daza kiye Allah yabaku zaman lafiya. Tabbas nayi farin ciki sossai da kika fito muka hadu karasa maganan yai yana kokari tashi.
Ita dai meenat hawaye ne kawai kefita a idonta takasa furta komai bata da halin taimakon Aliyu batasan wani irin taimako zata mishi ba, iya karfinshi tasa yayinda ya ratayu hannunshi wuyanta jingina yai daita suna tafiya dakyar yake daga kafarshi dan shikadai yasan halin da yake ciki
A haka suka karasa kofar gidanso Aliyu zaunan dashi tai adan wani dakali tana fadin barinyi knocking….
Bata karasa magana ba yafara amai still amai jini yakeyi, zama tai kusa dashi tasa kuka a yanzu harta hanci jini kefitar mishi rigarshi dukda baci da jini haka itama meenat farin gyalanta yai kaca’kaca.
Nashiga uku Aliyu danAllah karki mutu kokari tashi take daka kusa dashi so take tai knocking gidanso tasanar dasu halin da yake ciki amma ya rige hannunta tsam cikin nashi yana fadin meenat kibari Allah ya dauki rayuwata ina kusa dake dan’Allah
Hankalinta sake tashi yai saboda bugawan zuciyan nashi ta tsanta tanajin yanda zuciyar ke harbawa bat..bat..bat. Gashi dakyar yake sauke numfashi
Aitine zama a takali ya gagara tine suka sauka kasa idan ba hakaba fadawa quarter dake bayanso zasuyi dukda quarter mai tsafta ce amma idan suka fada zasuji rauni.
Kalman shahada Aliyu yafarayi yayinda hawaye kezuba a idonshi idonshi akan meenat yana kallonta yana murmushi, shiru taji komai nashi ya tsaya cak yadaina motsi
Cikin tashin hankali tashiga girgiza shi tana kuka amma shiru aida sauri ta janye jikinta daka nashi gani tayi ya fadi kasa nan hankalinta yasake tashi gate din gidanso Aliyu tashiga kwan’kwasawa da karfi tana fadin dan’Allah kuzu kubude karya mutu.
Hakan yayi daidai da fitowan daddy daman part din Aliyu zai shiga, jida yayi ana knocking kuma mai gadi befito ba yasa yanufi gurin gate din.
Waye anan?
Me gadi ne yafito yana daure mazagin wando hade da fadin ana zuwa za’a balla kofar ne?
Muryan mace sukajiyo tana kuka hade da fadin dan girman Allah ku bude… Daddy ne yabude kofar batare daya fita waje ba saboda yanayin rayuwan
Kallon meenat yai gani yai hannunta da gyalanta duk jini sanan yace daka ina kike?
Cikin kuka tace sunana meenat… Aliyu… Aliyu… Aliyu
Sai yanzu daddy ya ganeta, cikin rashin fahimtar abinda zatace daddy yace Aliyu kike nima a daran nan?
Girgiza kai tayi sanan tai mishi nune da inda Aliyu yake tana fadin ya mutu, ya mutu.
Aida sauri daddy yafito waje dan yaga abinda take nuna mishi
Rungume Aliyu yai a jikinshi yana fadin me kika mishi kin kashe shi ko?
Kafin kice meye ai iyalan gidan Alhaji Zailani sun taru a waje sai kuke kuke suke yayinda akasa Aliyu a mota za’a tafi asibiti dashi gurin motar meenat tanufa tana kuka itama zata shiga ciki, mahaifiyar Aliyu ce ta hankadata gefe tana fadin karda ki kuskura ki shigo nan har idan kin kashemin dana sai nayi shari’a dake idan ba watsa’tsiyar mace ba ai yanzu yakamata ace kina gidan ubanki
Cikin kuka meenat tace wallahi bani na kashe shiba karda kuga jini a jikina ku dauka ko wani abu na tsoka mishi banyi mishi komai ba amai jini yayi karasa maganan tai da kuka.
Tanaji tana kallo suka wuce suka barta a gurin
Cikin gidanso takuma koda tashiga gida an riga an rufe kofar parlor dazai sadata da dakinta nan tashiga kwan’kwasawa sakina da Hashim ne suka fito suna fadin waye anan?
Cikin kuka tace marmy meenat ce
Meenat me kikeyi a waje?
Koda suka bude mata kofar a guje ta rungume sakina tana kuka.
Hade da fadin marmy shikenan ya mutu nashiga uku na kashe shi nashiga uku gaskiya yan’uwanshi suka fada da sukace na kashe shi.
Daka Hashim har sakina tsoro da fargaba ne yasaukan musu lokaci daya, mayafin dake kan meenat hashim yacire hade da kare’mishi kallo jini yagani dukya bata mayafin itama sakina hannun meenat ta rige inda taga duk jini ya bushe a hannu
Mari sakina ta tsinka mata sanan tasa kuka tana fadin wa kika kashe meenat?
Kiye mana bayani mun shiga uku badai kin dauko mana masifa ba
Fatima kuce👌🏽👌🏽*Y’AR ZINA CE*
_(KADDARAR IYAYENA)_
*NA*
*MUNEERA*
_Wattpad👉🏻Fatimamuneera001_
*PART 2*
_PAGE 14_
Durgu’shewa a kasa meenat tai sanan tasaki kuka, Hashim ne ya durgusa a gabanta game da dago fuskarta sanan yace meenat bude baki kiye mana bayani wa kika kashe?
Cikin kuka tai musu bayanin duk abinda yafaru, saida sukaji bayaninta hankalinso ya kwanta
Ajiyar zuciya sakina ta sauke sanan tace idan ya mutu Allah yayi mishi rahama amma na tausaya mishi Hashim ne ya dafa kafadan meenat kana yace tashi kije ki kwanta Insha’Allahu bazai mutu ba nan hashim da sakina suka kwantar mata da hankali da maganganu masu dadi.
+
Koda tashiga dakin kuka tayi sossai sanan tai wanka tare da dauro Alwala. Sallah tai tayi wanda ita kanta batasan iya raka’oin da tayiba duk sujadar da zatayi kuka take tana rugan ma Aliyu samun sauki daka gurin ubangiji.
Babban asibitin Aminu kano teaching hospital(AKTH) Aka wuce da Aliyu a wanan daran inda likitoci suka taru akanshi anyi sa’a be mutu ba amma dakyar suka cito rayuwarshi inda akace zuciyarshi gab take da bugawa yakamata a bashi abinda yakeso
Tsaye mahaifiyan Aliyu take a kanshi yayinda take zubda hawaye a yanzu ta amince Aliyu ya aure meenat kodan yacigaba da numfashi a doran kasa ta fahimce idan be sametaba zai iya rasa rayuwarshi. Gaba daya ya zabge ya rame oxygen ne makale a hancinshi wanda yake taimaka mishi gurin fitar numfashi tare da wasu na’ura da akasa mishi a jiki duk wanda ya ganshi sai ya tausaya mishi babu wanda zaice akwai sauran rayuwa a tare dashi.
Dakyar aka samu iyalan gidan Alhaji Zailani suka tafi gida yayinda aminin Aliyu mai suna muazzam ke zaune dashi a asibitin
Koda suka kuma gida kuka mahaifiyar Aliyu tasa tana rugan daddy akan yaje yasamu mahaifin Aliyu yabashi hakuri ya taimaka ya aura mishi meenat
Mummy ce tasa kuka tana fadin Alhaji kamata yai ka daukeshi kuje asibitin dan yaga halin da danmu yake ciki
Daddy ne ya jinjina kai cikin tashin hankali yayinda ya rasa taina zai bullo ma lamarin sanan yace bana tunanin mahaifin meenat zai aura mata Aliyu yaufa aurenta saura kwana bakwai bana tunanin zai bamu yarshi
Washe garin ranan kamar yanda mummy suka bama daddy shawara haka akayi
Har asibiti Hashim da sakina sukaje ganin Aliyu tabbas sun tausaya mishi amma suma basu da yanda zasuyi hakuri kawai Hashim yabama mahaifin Aliyu sanan suka koma gida
Anfara hidaman bikin meenat sunfara event gaba daya bata da walwala tunaninta da zuciyarta ya karkata gurin Aliyu ton ranan da aka kaishi asibiti haryau be farkaba kuma likita yace a tabbata a lokacin dazai farka abinda yakeso ta kasance a kusa dashi hakan zai rage mishi tashin hankali.
Yauta kasance ASABAR yayinda duban mutane da dumbin jama’a suketa zuwa massalacin gidan sarki Domin halattar daurin auren Ameenatu da yazeed karfe goma sha daya na safe akasa daurin auren amma ton kafin lokacin masallacin yacika
A bangaran meenat kowa tarasa mezata kira wanan ranan a rayuwarta shin farin ciki takeyi ko bakin ciki ita kanta takasa tantan’aciwa…. Mahaifin Aliyu kowa ya tabbatar da zaran an daura auren meenat shikenan ya rasa danshi dan gani yake da wuya Aliyu yacigaba da numfashi a doran kasa batare da meenat ba, shima yayi kokari zuwa gurin daurin auren.
Karfe goma da rabi ne yanzu yayinda wayarta tashiga ringing
Daga wayar tayi kana tace amincin Allah ya tabbata a gareka Habibi na
Daka dayan bangaran naji yai murmushi sanan yace Amin thumma Amin tare dake saheebata saura minti talatin kacal kizama matata
Wanan haka yake Habibi ancemin abokan ango duksun iso amma babu ango a cikinso ko meyasa?
STORY CONTINUES BELOW

Eh yanzu zamu tawu nida babban abokina sufiyan kafin 11 jirginmu zai sauka dana iso zan sanar dake
Tohm shikenan Allah yakawuka lafiya.
Amin ina sonki meenat, ina sonki, ina sonki
Murmushi tayi sanan tace nima ina sonka sossai nan ya kashe wayan.
Taro yai taro inda duk wasu manyan baki da zasu halicci daurin auren sun halatta yayinda wakilan ma daura auren suke kokarin daurawa ma roga kuma na magana a laund speaker inda sukeciwa a saurara yanzu za’a daura auren Ameenatu da Yazeed.
Wayan mahaifin yazeed ne yashiga ringing nune yaima Hashim da yatsa yana fadin minti daya ina zuwa, saboda cikowan jama’a besamu yafita daka wajeba saidai yadan matsa inda zai samu ya amsar wayar
Innalillahi wa’ina illaihi raji’un yafurta sanan ya tafi tagaga zai fadi wani saurayine ya rigeshi yana fadin subhanallahi lafiya?
Dukda akwai farin glass a idonshi amma hakan be hana jama’a ganin hawayen dake zuba a idonshiba, ciwa yayi a dakata da daurin auren angon sun samu hasarin jirgin sama wato plane crash
Nan gurin ya hautsine da sallati tare da jimami da kinga mahaifin yazeed kinsan yana cikin tsananin tashin hankali haka shima Hashim mutuwan ta tabashi
Mahaifin yazeed jarumine wanda yake kokarin miga lamarin shi ga Allah cikin tashin hankali ya dube Hashim yace nida yan’uwana zamu tafi domin muyi jana’izan shi dukda ance ba’a samu ganin gawanshiba amma zanje naga yanda abun yake da idona… karda kufasa daurin auren a daura da wanan yaron wanda ke kwance a asibiti.
A lokacin da Hashim yaga halin da Aliyu yake ciki yasanar da mahaifin yazeed komai shima mahaifin yazeed ya tausaya wa Aliyu yayinda yai mishi addu’a samun sauki
Bawani bata lokaci aka daura aure da Aliyu daman mahaifinshi yana kusa, wanan shi ake kira da matar mutum kabarinsa duk abinda rabonka Kane bazai taba wuce kaba har idan nakane
Duk abinda ke faruwa meenat da sakina basu da labari basusan wainar da ake toyawa ba
Meenat kowa sai kiran yazeed take a waya amma bata shiga bata wani damuba dan tasan yana cikin jama’a maybe shiyasa ya kashe wayarshi.
Innalillahi wa’ina illaihi raji’un sakina take furtawa sakamakon abinda Hashim yasanar daita ita kowa nihla kuka tasa dan tausayin halin da meenat zata shiga take hangowa, kafin kice wani abu labarin ratsuwan yazeed ya riski meenat wani mai dogon baki aka samu a cikin abokan ango yakirata dan yayi mata ta’aziyya
Sallam meenat ya mukaji da hakuri ashe Allah yayi keda yazeed bazaku rayu tare ba Allah yajikan shi da rahama
Tine jikinta yadau rawa cikin rashin fahimtar abinda zai sanar daita take fadin ban fahimce kaba me kakeso ka fadamin wani yazeed dinne ya ratsu dajin haka dai ya kashe wayarshi dan ya fahimce labarin mutuwan bata riske taba
Yawancin yan’uwa wayanda sukazu biki labarin mutuwan ya riskeso koda meenat tafito daka dakinta cikin tashin hankali tana kuka zata nufi dakin sakina duk inda ta wuce sai mutane sun tausaya mata
Tana shiga dakin taga nihla na kuka haka itama sakina Hashim na lalashinsu. Da gudu takarasa tare da fadawa jikin nihla tana kuka mai karfi hade da fadin nihla da gaske ne yazeed ya rasu?
Yanzu abokinshi yakirani wallahi ban fahimce abinda yake nufi ba
Itama nihla kuka tasa batare da tace komai ba, barinta sukayi saida tai kuka mai isanta sanan sakina tace meenat kiye hakuri ke kuma haka taki kaddarar take tabbas yazeed ya ratsu ko gawan shi ba’a samu daman gani ba shida abokinshi babu wanda akaga gawanso sun kone kurmus
Ganin meenat kawai sukai a kasa bata numfashi, nan hankalinsu yatashi Hashim ne yasa hannu ya dauketa sakina da nihla kowa suka bisu a baya cikin kuka
STORY CONTINUES BELOW

Tsohon cikine da nihla basu karasa saukowa daka upstairs ba jiri ya debeta ta fadi akan cikinta sai jini. Tine gidan ya hautsine da kuke’kuke yayinda aka nufi asibiti dasu
Ana zuwa asibiti bawani bata lokaci sai haihuwa amma tazubar da jini hakan ne yasa basu sallameta ba. Koda nihla ta dawu cikin hayyacinta bakinta na ambaton ina meenat? Ina meenat ina yar’uwata sukaita gurinta.
Koda meenat ta farfado nasiha mai ratsa jiki mummy tai mata wato kishiyan Maman Aliyu zasu shiga gidanso meenat kenan sukaga anfito daita a sume ansa a mota can kuma ga nihla wace take zubda jini harta mahaifiyar Aliyu ta tausaya wa iyalan gidan Hashim dan basai an fada mata ba tabbas suna cikin tashin hankali
Kiye hakuri Ameenatu kinji kizama mai yarda da kaddara Allah yayi Aliyu shine mijinki dashi zaki zauna a matsayin miji haka Allah ya kaddara lamarin kadan daka cikin lamarin ubangiji kenan
Kallon mummy meenat take sanan tace kina nufi an daura aure na da Aliyu?
Hashim dake zaune agefe ne yace eh meenat da Aliyu aka daura nan yashiga mata bayani komai tare da kwantar mata da hankali.
Asibitin da aka kwantar da Aliyu nan aka kwantar da meenat da nihla wato asibitin
Koda meenat taje taga nihla ta haihu tayi murna sossai daka nan inda aka kwantar da Aliyu tace a kaita dan tonda aka kwantar dashi batazu asibitin ba
Kuka tasa hade dazama a kujeran dake kusa da gadonshi babu wanda zaice yana numfashi sakamakon na’ura dake aiki a ilahirin jikinshi. Cikin kuka tace mummy anya kowa Aliyu na numfashi ko motsi ba yayi fa
Cikin tausayawa mummy tace be mutu ba ai yanzu jikin nashi da sauki ma dan likita yace tsakanin yauda gobe zai farka dan tonda aka kawushi be bude ido ba. Har idan be farfado gobe ba to ya zama dole a fita dashi waje akwai asibitin da zasu turamu inda gwararune akan matsalar zuciya.
Hawaye nafita a idon meenat tafurta Allah yabaka lafiya Aliyu na rasa yazeed bana fatan na rasaka. Domin na tabbata bazan taba samun wani tamkar kaba karasa maganan tai da kuka
******************
A washegarin ranan aka sallame nihla harzuwa wanan lokacin Aliyu be farka ba hakan ne yasa suka yanke shawaran turaso wani babban asibiti dake Germany.
Daka meenat sai mahaifin Aliyu tare da wani doctor aka tafi…
Kwananso daya a asibitin amma harzuwa wanan lokacin Aliyu be farka ba gashi dai shiba mutuwa yayi ba amma farkawa ya gagara sunyi iya baki kokarinso tare da baje duk wata basira akanshi inda sukesa rai a daran yau zai farka kokuma gobe da safe.
Daddy ne yashigo dakin da Aliyu ke kwance sanan yayima meenat sallama zai tafi gida zuwa gobe da safe zai dawu.
Daddy nafita ta tashi daka kujeran da take zaune kwanciya tayi a gadon da Aliyu ke kwance game da saka hannunta cikin nashi sanan tasaki kuka mara sauti sai sha’sheka dake fita kawai
A fili take furta Aliyu dan’Allah katashi karka mutu idan ka mutu na tabbata rayuwata tazu karshe domin bani da sauran wani farin ciki a duniya, a baya nazata tausayinka kawai nakeyi a’a sai daka baya na fahimce nima nakamu da sonka cigaba tayi da kuka tana fadin Aliyu ina sonka.. Aliyu ina sonka… Aliyu ina sonka. Ka bude idonka meenat na kaunar ka.
Kamar da wasa taji hannunshi dake cikin nata an rigeshi tsam yana motsi dasauri ta daga idonta ta kalla hannu tabbas hakane shiya rige mata hannu cikin hanzari ta maida kallonta kan kwayar idonshi aiko tana kallonshi suka hada ido
Idonshi akanta fuskarshi dauke da murmushi rungumeshi tai hade da fadin Alhamdulillah Allah nagode maka. Allah nagode maka saukowa tai daka gadon tana fadin barin sanar da doctor yace dazaran ka farka nasanar dashi
STORY CONTINUES BELOW

Shidai da ido yake kallonta ba halin magana sakamakon oxygen dake hancinshi
Bawani bata lokaci saiga likita yazu nan ya dodu bashi tare da cire wasu na’ura dake jikinshi harda oxygen din yacire yanzu zai iya fitar da numfashi batare da oxygen ba.
Doctor nafita Aliyu ya kalla meenat yana murmushi saikuma hawaye suka zubo a idonshi, cikin sauri ta matsa kusa dashi zama tai kusa dashi tare dasa hannu ta share mishi hawaye tana fadin kadaina kuka kuma kadaina zubda hawaye akan meenat, Ameenatu mallakin kace matar kace nahar abada ka kwantar da hankalinka a yanzu mata nake a gareka domin an daura mana aure
Hannun’shi ta rige tana fadin Aliyu ina matukar kaunarka dan’Allah ka kwantar da hankalinka kozaka warke cikin sauri.
Farin cikin da Aliyu ya tsinta kanshi takasa boyuwa duk radadin ciwan da yakeji sai yakejin jikinshi tamkar ya warke, hannu yasa tare da janyo meenat jikinshi lafewa tai a kirjinshi yayinda da takejin bugawan zuciyanshi da karfi da karfi. A hankali taga yana motsa bakinshi sunanta yakeso yakira mee..nat dakyar ya iya furta haka
Tabbas taji dadin jin haka nan ta kwanta a kusa dashi tareda lulubeso da bargo tana fadin karda ka wahalan da kanka gurin kiran sunana na tabbata zuwa gobe bakinka zai bude.
Rungume suke da juna yayinda sukeyi bacci hankali kwance ita kanta meenat batasan gari ya waye ba sai motsi da taji a kanta dasauri ta bude ido likita tagani a fili tafurta Alhamdulillah ba daddy bane
Koda daddy yazu yaji dadi kuma yayi murna da yaga Aliyu yasamu sauki, zama daddy yai a kujeran dake kusa da gadon Aliyu sanan yakama hannun Aliyu yana fadin to sarkin soyayya Allah yayi kana da sauran numfashi a duniya Allah yabaka meenat a yanzu meenat mata take a gareka saika kwantar da hankalinka.
Murmushi kawai Aliyu yai yana kallon daddy
Kwana biyu da faruwan haka Aliyu yaji sauki sossai inda a yanzu yana magana sossai. kota ina samun sauki ya bayyana a gareshi.
Soyayya sukeyi sossai shida meenat daka kwancan nan da yake kokari take tana boye damuwar ta akan mutuwan yazeed amma kullum saita zubda hawaye a boye batare da Aliyu yagan taba dan bataso hankalin shi yatashi.
Kamar kullum wanda yake taimaka ma Aliyu yayi wanka tare da shirya jikinshi. Shine yashigo dakin danya taimaka mishi
Cikin harshan turanci Aliyu yace mishi yatafi matarshi zatai mishi komai yau. Dasauri meenat ta kalleshi tare da girgiza kai tana fadin a’a Aliyu bazan iya maka wanka ba daka bari yai maka be saurari meenat ba yasa mutumin yatafi
Kallonta yai sanan yace kizu ki taimakamin, sauko da kafarshi yai daka gadon yayinda take rige dashi harsuka karasa bathroom din, rasa abinda zatai mishi tayi dasauri tajuya zata fita a bathroom din tana fadin aizaka iyayin wanka da kanka naga jikin naka yai gwari
Meenat
Tsayawa tai batare data juya ta kalleshi ba
DanAllah ki taimaka min nasamu nayi wanka danAllah
Gurinshi ta nufu tare da taimaka mishi yacire rigan jikinshi sanan yacire wando, daka shi sai boxers yanzu.. jikin tani yadau rawa dan tonda take bata taba ganin namiji a haka ba
Aliyu yalura da haka nan yai kasa da murya tare daciwa shikuma boxers din baza’a cire bane?
Muryanta na rawa tace saimun gama wanka za’a cire, sponge ta dauka tare da saba sabulu sanan tashiga mishi wanka bata dai cire wanan boxers dinba, saida tagama wankeshi tass sanan ta dubeshi tace nagama bata tsayajin abinda zaice ba tai waje da gudu
Dariya yayi sanan yakarasa wankan shi
Watan Aliyu daya a germany ya warke sumul inda ba wanda zaice shi yayi wanan ciwan saidai kawai ramewa da yayi, zaune suke shida meenat suna hira wasa take da zoben dake hannunta sanan ta dubeshi tace Aliyu nikam inaso na tambayeka wani abu.
Tohm meenat ina jinki
Daman kana da ciwan zuciya ne kokuma saida ka hadu dani ka Kamu da cutar
Murmushi Aliyu yai sanan yace ko kadan bani da ciwan zuciya haduwata da Ameenatu na Kamu da ita soyayyata a gareta mai karfi ce
Aliyu ya warke yayinda suke shirye’shiryan komawa Nigeria
Shirya wa suke sosai Aliyu ya karaso kusa d meenat ya rungumeta ta baya yace haka zamu bar kasar nan batare dana yi ajiya anan ba ya fada yana me Nuna cikinta sharewa tayi kamar bataji meyace ba
Knocking sukaji anayi Aliyu yaje ya bude daddy ne yace kuyi sauri kar muyi loosing flight meenat ta karaso tanajan jakansu tace daddy mun gama Haka suka bar kasar cike da farin cikin samun nasara
*****
Sanda suka karaso 9ja suna sauka wani convoy ne n bakaken motoci sukazo tafi dasu
Kowa yayi farincikin ganin Aliyu ya samu sauki musamman mamanshi tun kafin su huta Maman Aliyu ta dinga bawa meenat hakuri
Nan meenat suka koma part din Aliyu da zama kafin su tare sabon gidan su
Rayuwa me cike da farinciki Aliyu d meenat sukeyi
Inda meenat ta haifi yaranta biyar nihla ta haifi yara shida ciki harda yan biyu
Yan biyun sakina sun girma sosai dan suna kaiwa yan uwan nasu ziyara akai akai
Sakina da hashim kuwa suma suna zaune kalau cike da farin cikin yaransu suna zaune gidan mazajen su lafiya
Zainab da kabir kuwa suma sun dai daita kansu sanan haryau zainab bata haihu ba kishiyata kuma bata dena mata gori ba
Kamar kullum yau yan biyu sunkaima sakina ziyara sunata wasa da yaran yar uwa tasu Aliyu ya shigo yace su tashi duka zaauje gidan nan suka shirya suka zo gida inda suka sami nihla da yaranta mijinta suma sunzo anci ansha anyi murna hashim da sakina sunata washe Baki ganin sun hada kan iyalansu yanzu Ana haka mommy Da daddy din Hashim sukashigo mommy tace ba’q gayace muba gashi muma munzo duka suka sa dariya kyaras aka dauke su huto nikuma cak birona yatsaya najuya zan tafi Ina me kewar wanan iyalan naji hashim yace muneera najiyo yace dan Allah kija kunen yan mata da samari akan aikata zina nagyda na fice
*TOH ANAN NAKAWO KARSHEN LITTAFIN NA ME TAKEN YAR ZINACE CE KADDARAR IYAYENA ABINDA NAYI DAI² ALLAH YA BAN LADAN WANDA NAYI BADAI DAI BA ALLAH YA YAFEMIN*
FATIM MUNEERA 👌🏽