YARIMA MUS’AB CHAPTER 5

YARIMA MUS’AB CHAPTER 5

                   Www.bankinhausanovels.com.ng 

Ammi tayi mamakin jin cewar zasuyi tafiya da Malam amman batayi musu ba ta shirya kayanta a jaka kala biyu dan ba’a sanar da ita ko tafiyar ta kwana bace hakama Mami da Inna sun shirya nasu kayan+

“Wai Mlm ya kukayi ne da maneman auren diyar waccan matar” cewar matar Bappa Auwalu

Bai amsata ba tunda ya shigo yake ta tunani shi da farko yaji mamakin jin cewar dan sarki keson Mami yaso ace ‘yarsa suka zo nema to amman gabadaya ynx kwakwalwarsa a dame take da maganganun Malam wanda bai fahimci komi ba sedai yaji dadin cewa da akyi dashi za’a tafi Bauchin gobe

A Bauchi kuwa bayan isowan su direct Fada suka wuce Abba Sadiq ya isa wurin ‘yar uwanshi suka tattauna sunyi akan goben ta taho gidan mahaifinsu tare da Hafsa da kuma Yarima nan shima Mus’ab yake jin yadda sukayi a Gombe yaso ya daga hankali amma Ummy ta nuna mishi yy hkr zuwa goben suga abinda Allah zaiyi domin haka kawai mutumin bazai nemi ganin Kakansa kawai don zai bashi aure ba dole akwai lauje cikin nadi

Daga fada Abbah Sadiq direct New GRA ya wuce gidan mahaifinsu  bayan gaisawa da matan su biyu ya wuce bangaren Abbu kwance ya tardashi yana jan carbi Dattijo ne kyakkyawa wanda kallo daya zai tabbatar maka da cewar shi cikakken bafillace ne da kuma tsananin kamar da sukayi da dan nashi da kuma Yarima don babu abinda Prince ya bari daga kamannin tsohon in banda bambancin shekaru da ya raba su

Murmushi dauke a fuskar sa ganin dan nasa kwaya daya tal namiji a hankali ya mike ya zauna sukayi musabaha bayan sun gama gaisuwa yace “Abbu yadai yau na ganka kamar baka jin dadi”

“Lafia lau nake Abubakar kawai yanayin jikin tsufa sai kuma kwanaki biyun nan mafarkin Hafsatu dake yawan zuwar min na rasa dalili sedai in ban kwanta bacci ba sai na ganta”

Share hawayen da ya zubo mai yayi duk da cewar yana karami amman har yau ya kasa cire rashin mahaifiyar tashi a ransa sbd yadda suka shaku da ita sosai nan ya sanar da Abbu abinda ya faru yau a Gombe baiji komai a ransa ba yace “to Allah ya kawo su lafia in ka fita ka sanar dasu muna da baki a shirya abin tarbansu”

Amsawa yayi da to suka dan taba hira kafin ya mike ya masa sallama sai zuwa goben

Washegari

Karfe sha daya tayi wa su Ammi a Bauchi fada suka wuce daman Yarima na jiransu kasancewar Sadiq baisan gidan Abbu ba shi ya musu jagora daman su kawai ake jira Ummy da Abba Sadiq sun dade a can bayan an gaisa suka nufi falon Abbu yanayin abubuwan gidan tamkar dai gidan Sarauta ga kuma ma’aikata birjik suna hidimomin su

Zaune yake bisa kujera sukayi sallama Abba Sadiq ke gaba Malam da Bappa suna biye dashi sai su Ammi da sauran yaran a bayan su gaba daya a kan kafet suka zazzauna banda Malam da ya samu waje gefen Abbu bayan sunyi musabaha kowannen su dauke da murmushi kamar dai sun san juna gaggaisawa akayi sannan Malam yayi gyaran murya “amm..wato ranka shi dade maganace ke tafe dani mai muhimman ci sbd haka nake son duk wani dake cikin ahalinka y kasance a nan”

Duban Yarima Abbu yayi “Mus’abu kira su Yafendo duk kace ina son ganinsu ynx”

Cike da girmamawa ya amsa ya fita jim kadan suka dawo tare da mata guda biyu ganin taron ya basu mamaki suka kalli juna Abbu yyi musu nuni da wajen zama suka zauna tare da gaida Malam dasu Inna bayan kowa ya nutsu Mlm ya bude jakan da ya shigo dashi ya ciro wasu hotuna guda biyu da zani ya mika wa Abbu yace ko kasan wannan

Tun ganin zanin jikinsa ya fara rawa da hanzari ya karbi hoton yana kallo hawaye ne suka fara zuba a idanun shi ko da a mafarki ne bazai taba manta wannan fuskar ba babu wanda yayi magana sai da Abbu ya share hawayen sa ya dubi Malam yace “ina ka sami wannan bawan Allah tabbas nasan su ba shakka a kwanakin nan Allah ya nuna min bayyanar su a mafarki na suna Ina”

Yafendo da tunda taga zanin itama take zufa ta gyara zama don bazata taba manta ranar ba wanda yy sanadiyyar yayewan farin ciki a rayuwar su bayan a tunanin su hakan ne maslaha garesu amma sabanin hakan ne ya kasance domin daga ranan basu sake gane kan Mai gidan ba in fact abinda sukayi domin shin ma a lkcn suka rasa shi Malam ne ya katse mata tunani da ya fara magana

STORY CONTINUES BELOW

“Suna na Abubakar ni haifaffen garin Alkaleri ne amman tun ina saurayi na rasa iyaye na kuma ni kadai suka haifa sbd haka bayan rasuwar su akwai diyar aminin Baba na Aisha da muke son juna aka aura min ita Mahaifina manomi ne sosai sbd haka ko bayan rasuwan shi ban daina noma ba ina shigarwa garin Bauchi da Gombe domin in siyar to gaskia nafi samu ta Gomben sosai sai nafi karfafa zuwa can din a haka har nayi abokai da dama muna zaman mu lafia da Indo har mukayi wata biyar da aure

Wata rana ina gona sauri nake in tattara kaya na sbd Magriba tayi min na gama tattarawa nazo daukan babur dina jikin bishiya naji kamar kukan mace ta baya da farko naji tsoron dubawa amman jin muryar na karuwa yasa na duba ilai kuwa macece mai ciki ga kafafun ta duk jini alamar taji ciwo bata ko iya bude idanun ta ganin tana neman rasa ranta yasa nayi gaggawan dauko goran ruwa na bata tasha sai ta dan fara bude ido tana fadin in taimaketa banji wani dar ba don nasan tana bukatan taimakon  haka na dago ta a daddafe tahau mashin din amman abu ya gagara in takaice maku dai a wajen ta haihu na tafi nemo maganin da zan saka ma raunin kafar nata na dawo na tarar da jaririya kwance cikin zanin da tayi lullubi dashi tana jin jiki sosai ko hanunta bata iya dagawa ta tambye ni me ta haifa nace mace ce tayi murmushi bawan Allah na gode da taimakon da kamin kuma har cikin raina naji na aminta dakai ina rokon ka da ka rike min diyata amana na mallaka maka ita halak malak wannan shine abinda ta fada hankali tashe nake tambayar ta wacece ita daga ina ta fito a wahalce ta ce sunana Hafsa inda na fito kuma wajene da bana fatan komawa duk da cewar nabay ‘ya’ya biyu da kuma mijina aman wajen yafi karfi na bazan taba komawa ba daga masarautan Bauchi nake amma ina rokon ka da kada ka maida diyata can kasheta zasuyi na rokeka bawan Allah

Daga wannan kalaman bata sake cewa komi ba rai yayi halinsa na rasa yadda zanyi ga yarinyar sai kuka take kuma tuni dare yayi haka na dauketa cikin zanin har zan wuce naga hoto a gefen matar haka na dauka na tafi gida dare yayi don haka babu wanda ya lura da abinda ke hanu na ina zuwa matata ta karbi jaririyan na bata umarnin ta mata wanka ina zuwa ko sallah banyi ba na fita cikin kasuwa na siyo kayan yarinyar kala uku da madaran yara na dawo gidan na tarar tayi abinda nace har ta shafa mata man zaitun kayan aka saka mata ta dama madaran ta bata tasha nan tayi bacci abinta sai da nayi sallah na sanar da Indo abinda ya faru har kuka sanda tayi kuma ta sanar dani zata rike yarinyar ba zata taba barin tayi maraicin uwa ba don tun ganinta taji tana kaunar ta

   A daren muka yanke shawaran da safe zamuje mu sami iyayenta mu sanar dasu abinda ake ciki amman da asuba aka ga gawar wannan matan a daji liman ya jagoranci mutane aka mata sutura aka binne naji dadi kwarai da gaske bayan mun dawo daga makabarta ina isowa kofar gidana naga mutane cike wasu na ciki ga wasu nan a waje maza da mata koda na shigo sai ido ya dawo kaina dakin Indo na nufa tana rike da yarinyar sai kuka take ashe wai tunda jaririyan ta farka take kuka taki karban madaran to kukan yayi tsanani har makota sukaji shine abinka da kauye daga shigowarsu suka ganta dauke da ‘yar danyen haihuwa shine kan kace kobo magana ta yadu cewar Indo ta haihu wata biyar da aure kowa na karawa da abinda bai ma gani ba maganar har ta isa gidan su Maman ta tazo

Duk yadda muka so muyi bayani abin yaci tura har takai raina ya baci na amsa cewar diyata ce ayi abinda za’ayi jin hakan yasa Hakimi yace an koremu daga garin iyayen Indo sukace babu su ba ita haka muka tattara tana kuka muka fito daga mahaifan mu sanadin wannan kaddara da ta fada mana a dare daya abokina da muke tare sosai shi ya fado min don haka muka shiga mota sai garin Gombe nasan har gidanshi don idan kwana ya kamani a garin gidansa nake zama shi kadaine a gidan matar shi ta rasu wurin haihuwa tabar yaran ‘yan biyu har sun fara girma ma sbd haka muna sauka a kofar gidan muka tarar dashi ya mana barka da zuwa muka shiga ciki a nan na sanar dashi duk abinda ya faru ya jimanta kwarai da gaske ya kuma ce mu zauna a gidan sa baida matsala amman nace ba za’ayi haka ba ya dai nema min gida in siya a nan unguwar tunda ina da kudi na siyar da duk kayan gado na da zamu bar garin kwanan mu biyu kuwa na sai gida muka koma da matata da kuma diyarmu da na mata huduba da suna Fatima

   A haka Fatima ta taso bata taba sanin bani na haifeta ba har takai aure na hadata aure da daya daga cikin ‘ya’yan amini na a kullum ina son sanar da ita asalinta amman banso hankalinta ya tashi ina ta tunanin kar na mutu nabar baya da kura amman na kasa fadan har wannan magana ta yaran nan ya taso wanda shine dalilin da na yanke shawaran fito da wannan sirrin”

Kowa yayi shiru yayinda banda kuka babu abinda Abbu keyi Malam ya dafa shi yace “idan har hasashena gaskia ne to ita din diyarka ce” ya fada yana nuna Ammi itama tun sanda taji an ambaci Fatima tasan kanta ake magana ta fara kuka sosai

Malam ya kirawo ta ta taso ya rike hanunta ya hada da na Abbu yace “Fadimatu na wannan shine asalin mahaifinki bani ba”

Da wani azama ta rungume Abbu tare da sakin wani kukan mai tsuma zuciya kowa hawaye yake Ummy da Abba Sadiq suma suka hadu suka rungumesu suna farin cikin ganin kanwarsu sosai zasu baka tausayi idan ka gansuKowa farin ciki yake in ka dauke mutum biyu a wajen wato Yafendo dake ganin lallai karshenta yazo da kuma Bappa Auwalu dake danasanin duk abinda ya aikata wa Ammi da ‘ya’yanta duk da cewar yana da dalilansa amman yasan bai kyauta ma Dan uwansa wanda suka fito duniya tare kuma yake matukar kaunarsa

Kiran sallar azahar ne ya tadasu mazan suka nufi masallaci yayin da matan suka koma cikin gida daman har yau dakin mahaifiyarsu na nan sbd haka suka shiga bayan sunyi sallah nan aka kawo musu abinci suka ci kowa yana farin ciki su Hafsa kamar su hadiye juna dan farin ciki ynx suka gane cewar kaunar da sukewa juna ba a banxa bane ashe su din ‘yan uwan juna ne

Bayan kowa yaci abinci Yarima ya shigo ya kirasu suka koma falon Abbu cikin farin ciki ya jawo su Sadiq da Hafsa yace kuxo jikoki na ya rungumesu yana jin dadi mara misaltuwa sai a ynx Ammi ta gane dalilin da yasa lkcn da ta haifi Mami yace a saka mata suna Hafsa wato ashe sunan mahaifiyarta ne gefen Inna ta koma ta rungumeta tana jin wasu hawaye suna sauko mata a hankali ta fara magana “ko da ace bake kika haifeni ba Inna banida mahaifiyar da ta fiki sbd abinda kika min bana zaton akwai Dan Adam din da zai yishi kika bar iyayenki da garin ku duk sbd ni bani da bakin da zan gode muku Allah ne kadai zai biyaku ladar abinda kukayi”

Nan shima Abbu ya shiga godia Malam yace bb komi su sbd Allah sukayi kuma basu taba nadaman taimakon nan ba don Fatima ta kasance ‘ya mai biyayya bata taba saba ma umarninsa ba har yau

Abbu ya fara basu tarihin shi kamar haka “ni sunana Umar farouq Lamido an haifeni a gidan sarauta gaba da baya na taso ni kadai ne Namiji sbd haka ina fuskantar tsangwama daga matan mahaifina a lkcn shine sarkin Bauchi mahaifiyata ta rasu tun ina Secondary Schl dan haka Abba na ya turani karatu England inda nake karantar Business Admin ni amini na dan kanin Abba kuma  Waxirin sa mai suna Mu’ayyad komi tare mukeyi har muka gama muka dawo to bayan dawowar mu da watanni aka mana aure da diyar sarkin Kano mai suna Anoosha bayan watanni biyar Allah yayi wa Waxiri rasuwa sai  Abba yayi murabus ya daurani duk da na gwada mai banson harkan sarauta amman yace dole haka zanyi aka nada abokina Mu’ayyad a matsayin Waxiri na muka cigaba da sarautar garin nan tare. Zaman mu da Anoosha zama ne ba na jin dadi ba domin sam bata da tarbiyya ko kadan bata ragar wa na kasa da ita sai tsananin mugunta da taka wanda taga dama sedai idan na gani in tsawatar mata shekarunmu uku d aure ko batan wata bata taba yi ba ga mahaifina yana matukar son yaga Dana a duniyar nan cikin haka aminansa guda biyu suka bani ‘ya’yan su Bahira da Muniba nan ma umarni y bani akan dole in auresu kodan yaga jikokinsa akayi bikin rana daya suka tare to cikin hukuncin Allah suma an shekara biyu babu alamun haihuwan Abba yaso ya daga hankali amman na nuna masa kar ya manta haihuwa Allah ke bayarwa kuma In Sha Allah nima zan cigaba da rokonsa ya bani sbd ina matukar son yara nima, na fahimci Bahira da Anoosha sun hade kai sun kuma ware Muniba ina sane da duk abinda ke faruwa amman na kauda kai kuma cikinsu sai hankalina yafi kwanciya da ita Muniba don tana da nutsuwa sosai bb ruwanta da hayaniya ga yadda take kula da mahaifina sai nake jin dadi sosai nima a raina

Wato ni da Mu’ayyad muna da wani al’adan fita da dare mu badda kama babu wanda zai ganemu cikin haka wataran mun fita bayan Magriba muka shiga mota Mu’ayyad ke driving ya dauki hanya ta baya duk tadi ya shagalar damu kawai naji ya taka birki kiiiiiiii da motar yana salati da sauri muka fita ashe har ya dan ture ta ma yarinya ce sanye da kayan saki na Fulani sai dan mayafi yane akan gashinta duqawa mukayi muna mata sannu ta firgita sosai ta tashi tana karkade jikinta fitilar motar a kunne take tana hasko mu don haka na lura ta dan ji ciwo a gefen hanun ta yana dan jini ruwa na dauko cikin mota nace gashi ki wanke hannun ki yana jini dagowar ta muka hada ido take naji zuciyata ta buga girgiza kai tayi ta dauki ledar da ta yar da alama aika ta fito zata tsallaka titin ta fara tafiya tana dan dingisa kafar ta alamun ta buge kafar nikam tun ganinta na kasa ko kwakkwaran motsi ne Mu’ayyad ne yy karfin halin cewa ke ‘yan mata ki tsaya mu kaiki gida amman taki fir cewar ta ai Ruggar su babu nisa ynx zata isa ya tambayeta ina ne gidan tace Wuro Jauro to nan muka gane Kangere muka xo dan garin bb nisa da cikin garin Bauchi a hanyar Gombe yake har tayi mana nisa na daga murya nace to yaya sunan ki tace Su’ad tayi tafiyarta harda gudu haka muka shiga motar muka koma gida

Tun daga ranar da naga Su’ad ban taba minti biyu ban tuno ta ba tun ina sharewa har na kasa na sanar da aboki na Mu’ayyad yayi murmushi ya dafa kafaduna yace ai duk laifinka ne Farouq na dade da gane ka afka son ‘yar fulani amman na share ina jira ka furta da kanka ya mike tsaye yana fadin finally king ya fada soyayya da hanzari ya fita bnsan ina ya nufa ba sai washegari ya shirya da abokansa suka fita ban kawo komi a raina ba don sun saba irin fitar saida suka dawo ne naga ashe harda Mu’ayyad ya shigo falo ya sameni ya fara min tsiya yana fadin Angon Hafsa ashe wai daga Ruggar su Su’ad suke nan yake sanar dani ai ainahin sunan ta Hafsa ake kiranta Su’ad kuma ya tabbata mahaifinta ya bani auren ta nan da sati biyu za’ayi bikin mu da sauri na rungume Mu’ayyad ina farinciki da sanya mishi albarka domin tabbas shi aboki ne kuma dan uwa nagari mukayi ta farin ciki a kuma daren ne na tara mata na su uku na sanar dasu xanyi aure nan da mako biyu Anoosha ce ta fara mikewa tace ban isa ba inma sbd haihuwa nakeyi ai nine mai matsalar basu ba yaro karami dani gigin sarauta na diba na sai tara mata nake ta gama dai maganganun ta ta fice daga dakin itama Bahira ta tashi taja tsaki tare da fadin ayi dai mugani tabi bayan ‘yar uwanta ya rage daga ni sai Muniba kusa dani ta dawo tana murmushi tace kar ka damu kishi ne kasan matsalarmu mata bama iya dannewa sai a hankali Allah ya sanya Alkhairi ta mini muka dan taba hira har nake bata lbrn Su’ad

Shirye² ake tayi na gagarumin bikin da za’ayi don ni kaina lkcn ne nake jin zanyi aure don ynx ne zanyi auren soyayya sau daya naje gidan su Su’ad muka danyi hira bata wani sake ba sosai tsakani na dasu Bahira kuwa babu jituwa har ranar da aka daura aurena da Hafsat Su’ad”

Kiran sallan la’asar ne ya katse Abbu suka mike don tafiya masallaci 

Bayan an dawo daga sallar la’asar Abbu ya cigaba da lbr
“Gagarumin biki akayi na gani a fada a garin Bauchi yayinda hakan ya sake bakanta ran Bahira da Anoosha wacce a cewarta ko ita dake diyar sarki ai ba’ayi wannan bikin ba sai wata can diyar Fulani wadda ba ‘yar kowa ba da dai sauran kananan maganganu na mata
   Bayan auren mu da Su’ad matana biyu suka kafa mata kahon zuka sam bata da sake cikin gidan ta in kaga tana dariya to sedai tare da Muniba wacce suke kusan sa’anni domin fulanin su Su’ad basu irin auren wurin nan to akalla takai shekaru ashirin da daya naji dadi kwarai yadda take kula da Su’ad da nuna mata abubuwan da bata sani ba gameda al’amuran gidan haka dai suke zamansu lafia lau watan mu uku da aure Su’ad ta sami ciki munyi murna mara misaltuwa musamman Abba na tamkar ya zuba ruwa a kasa yasha sbd yana son yara amma ni kadai Allah ya bashi dan haka Extra kulawa ake bata a gidan yayinda su Anoosha ji suke ina wuta su jefa ta duk wani makirci sunyi dan su rabata da cikin amman abu ya faskara Allah bai basu iko ba a haka har ta haife diyarta mace ranar suna taci sunan mahaifiyata Halima gagarumin bikin suna akayi yarinya ta taso cikin gata da kulawa musamman wajen Muniba wacce take kira da Mama ta gefe daya kuma Anoosha (Umma) da Bahira (Yafendo) suke takura mata idan abin yafi karfin Muniba sai ta fada min na tsawatar amman a banxa ita kuwa mahaifiyarta bata ko daga idanu ta kallesu sbd kunya da kawaici irin na Fulani sai ranar da maganar takai kunnen Abba ya tsawatar musu domin ya nuna musu akan yarinyar zai iya korarsu a gidan abin ya bata musu rai matuka amman suka shanye suka daina kulata
Tun bayan haihuwarta ba’a sake haifar wani dan ba saida ta shekara goma Su’ad ta sake haifan danta namiji Abubakar Sadiq wannan haihuwa kam ya daga ma su Anoosha hankali musamman da mutane ke kiransa Magaji
Tun tasowar Sadiq ya nuna sam baya sha’awar sarauta don ko fada baison zuwa in an kaishi zaita kuka sai an maidashi gun mahaifiyarsa lkcn yana primary schl Sadiq yana da Shekara hudu Su’ad ta sami wani cikin wannan karon kam karara Bahira suka nuna bakin ciki a fili ita kam bata ko kulasu domin mace ce wacce bata son hayaniya sam kuma ma wannan Karon cikin yana bata wahala sosai kullum ba lfy ko abinci ba wani na kirki take ci ba wannan yasa bata cika ma fitowa daga daki ba
Watarana wanda yana daya daga cikin ranakun da bazan taba mantawa ba na shigo daga fada Muniba ta shigo bangare na hannun ta rike da na Sadiq da gudunsa ya karaso jikina na dagashi na daura kan cinya ina tmbyrsa ina Yayar shi yace tayi bacci a dakin Amma(Su’ad) Muniba ne ta gaisheni muna dan taba hira nake tmbyr ta ina Su’ad tace ta shiga dazu tana ga wanka take bata sake komawa ba kuma itama bata fito ba nace to dubota ko jikin ne naga bataxo ta gaisheni ba tun shigowata Muniba ta mike ta fita shiru² tafi minti talatin sai can ta dawo hankali tashe tace min bata ganta ba ta duba har bandaki bata nan kuma Sadiya ma yadda ta barta tana bacci kan kafet har ynx gurin take anya lfy kuwa na tashi da kaina muka fita nema abu kamar wasa an bincike kaf cikin fada babu ita na aika gidan abokina Mu’ayyad ko taje gidan shi tunda suna shiri da matarsa Zainab amma akace bataje ba  hankali ya tashi domin bata taba fita ban sani ba sbd haka jikina ya bani babu lfy wasa² har washegari babu Su’ad muna ta faman nema wani dake kula da barga yaxo da Dan kwalin ta a hanunshi cewar a kofar baya ya samu nan muka tabbatar fita tayi aka bazama cikin daji amman har babu ko alamar ta cikin haka lbr ya iske Abba na take ya yanki jiki ya fadi domin yana matukar kaunar Su’ad tamkar diyar cikinsa aka kira likita yace ciwon zuciyansa ne ya tashi yayi mai allurai bai farfado ba aka nufi asibiti dashi nan fa tashin hankalin mu ya karu ga matana sai kuka suke haka ma Sadiya da yake da girmanta ga Sadiq shima kukan yake yana kiran Amma abubuwan duk da ba sauki kullum cikin neman Su’ad muke amman babu ko lbr ga jikin Abba kara tsanani yake gaba daya banda kwanciyar hankali harkokin fada ma sai Waxiri Mu’ayyad ne yake gabatar dasu iyayen Su’ad kullum cikin bani baki suke kan inyi hakuri indai tna raye za’a ganta amman ina har bayan shekaru biyar babu Su’ad ga Sadiq har ya gama Primary Schl amman kullum sai ya tambayi Muniba ina Amman su hakan yasa na tattara na kaishi England ya sami wanshi Mubin wato Babban dan Waxiri wanda ke Uni a chan tun daga nan bai dawo Nigeria ba saida ya gama Sec Schl nakan kai masa ziyara dai tare da yarshi Sadiya kuma dawowanshi yayi dai² da lkcn bikin Sadiya da Mubin sun nuna suna son junansu kuma munyi farin ciki babu bata lkc tana gama karatun ta  aka sa auren su anyi bikin da sati daya ciwo ya kama Anoosha anyi jinyan asibiti amman ina basu gano ba ana ta faman na gida  amma babu cigaba
Wataran da dare ciwon ya tashi sosai da kyar take numfashi ta aika aka kirawo ni nan take fada min maganganun da suka daga min hankali a cewarta sune sanadiyyar barin Su’ad gida aljanu suka tura mata sukai mata barazanar zasu kasheta in bata fita ba amman in yafe ta tayi hakan ne sbd kishi da kuma bakin cikin bata haifi wanda zai gajeni sarauta ba shima Sadiq taso kassara shi amman Allah bai nufa ba tayi ta rokon in yafe mata har Abba da yaxo dubata yaji maganar nan ya yanki jiki sai gawanshi aka daga daga gurin yayinda itama Anoosha a daren tace ga garinsu rai yayi halinsa
Washegari da safe akayi jana’izar su aka kaisu makwancinsu nayi kuka sosai sbd abinda ya faru ya daga min hnkl jin cewar sbd sarauta abin banxa an rabani da masoyiyata da abinda ke cikinta gashi kuma sanadiyyar hakan na rasa mahaifina take na yanke shawara cikin zuciyata kuma banyi kasa a guiwa ba bayan anyi kwanaki bakwai da rasuwan na tara mutanen fada na sanar dasu cewar nayi murabus
Kowa yayi mamaki tunaninsu ai Sadiq bai kai wanda zaiyi sarauta ba na fahimce su sai nayi murmushi nake sanar dasu ai Sadiq sam baya sha’awar sarauta don haka na daura Waxiri daga yau Mulkin garin nan ya koma gidan kanin Abba tunda daman ai duk mune amma ga mamaki na sai Mu’ayyad ya mike shima yace kafata kafarsa indai babu ni bazai iya mulki ba don haka sedai Mubin yayi to wannan shina asalin dalilin da ya maida mulki gidan Waxiri kuma Dan uwana Mu’ayyad nayi hakan ne kuma sbd hukunta matata Bahira domin Anoosha ta sanar min cewa da sa hannun ta a lamarin batan Su’ad wanda ita a tunanin ta har yau ban sani ba to kunji abinda ya faru kuma a ynx Mubin shi ke mulkin garin nan kuma mahaifin Mus’ab wanda yaje neman jikata a Gombe”
Abbu ya karasa lbrn kowa sanda ya tausaya masa ita kuwa Yafendo banda kuka babu abinda take ta shiga neman gafaran su Abbu yace ya yafe mata daman Allah ya kaddara rabuwarsu da Su’ad a lkcn koda batai sanadi ba amman ta nemi gafaran ‘ya’yan da ta rabasu da mahaifiyarsu musamman ma Ammi da ko ganinta bata taba yi ba suma sukace sun yafe mata
Malam yaso su koma Gombe ranan amman fir Abbu ya hana yace dole su kwana biyu a gaisa da ‘yan uwa Ummy tace zasu tafi da Ammi gidanta amma Mama wato Muniba ta hana cewarta sai gobe itama tanaso suyi hira da diyarta a dole ta hakura ta kwashi su Mami ta tafi dasu Sadiq kuwa yace kwana zaiyi da kakan shi Abbu susha hira to shima Yarima hakan yace duk da yaso yau su kwashi soyayya da Mamin shi amman baison rabuwa da dan uwa kuma amininsa Sadiq don haka ya zauna
Ammi kuwa sai goma tabar sashen mahaifinsu yana bata lbrn mahaifiyarta wanda ya fahimci kaf halayyarta tayo itama dai Mama hirar Su’ad tayi ta mata har suka raba dare kafin sukayi bacci

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *