YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM’UNA
CHAPTER 12 BY HARUNA USMAN
Www.bankinhausanovels.com.ng
A JIYA MUN TSAYA
To yadda al’adar mutanen garin ta ke, in Sarki ya rasu, sai an yi watanni uku sannan za a nada wani. Haka al’amarin ya kasance, wato sai aka shiga jira tare da ‘yan shiryeshiryen da suka dace kafin zuwan lokaci. . Amma shi Bashari sai ya ci gaba da tafiya yana jiyyar Sarki gwargwadon iyawarsa da dan abubuwan da ya sani har Allah Ya kawo shi wata riga ta Fulani. Aka kai shi wurin Sarkin Fulani wanda ake kira Ardo Jumare, wani dattijo mai farin gemu da yawan shekaru. Bashari ya yi gaisuwa cikin ladabi da girmamawa, sai Ardon ya tambaye shi labarinsu, amma tsoron rashin sanin wadanne irin mutane ne zai sake haduwa da su, da kuma tunanin in ya fadi gaskiya labari na iya komawa kunnen wadancan mutane su sake zagayowa su halaka su, sai Bashari ya ce, “Mu fatake ne ‘yan kasuwa ni da mahaifina, sai na nemi izininsa don zuwa in wanke rigata wadda ta yi dauda,
ZAMU TASHI
‘yan fashi suka far masa suka Kwace mana dukiyarmu. Shi kuma suka yi masa dukan tsiya, na dawo na same shi cikin wannan hali.”
Nan da nan Ardo Jumare ya sa aka ba su bukka, ya ce aje wurin ‘yarsa can cikin daji a ce ta kawo madara mai zafi za a ba baki.
Wannan Ardo yana da shanun da sun fi dubu biyu. A dalilin haka ne ya dauko jingar wani saurayi yana taya ‘yarsa da suke yi wa lakabi da Bingyel da Kaninta mai suna Harande kiwo.
Yarinya ‘yar Fulani ta tatso madara ta cika gora – makil ta kawo. Mahaifinta ya umurce ta cewa ta mika wa bakin da ke cikin bukka, sannan ta gaggauta ta koma daji ta hado wa mara lafiyar maganin jini. Lokacin da ta shiga cikin bukkar don mika madarar, sai suka yi ido hudu da Bashari. Nan fa suka Kurawa juna ido kamar sun san juna, shi bai karbi gorar ba yana kallonta, ita kuma ba ta ajiye ba. Can sai kunya ta kama ta, abin ka da mace kuma bafillatana, sai ta ajiye gorar madarar ta ruga cikin daji don kawo maganin.
Fitarta ke da wuya sai Bashari ya fara sambatun cewa, “Allah da iko Ya ke, tun da na zo duniya ban taba ganin yarinya mai kyau da cikar halitta irin wannan ba, kuma ikon Allah a cikin rigar Fulani. Ni
Www.bankinhausanovels.com.ng na tabbata ko birnin Misra ko Sin da ake cewa manyan birane ne a duniyar nan ba za a sami mai kyan ta ba.” Ya tsiyayi madara ya tallafo kan Sarki ya dura masa. Can bayan wani lokaci sai Ardo ya fito da wani garin bakin mahadi ya cewa Bashari, “Gobe tun kafin mara lafiyar ya ci abinci, a duntsi maganin dan daidai Kima a gauraya shi da wanda yarinya za ta kawo. Maganin ya zama shi ne zai fara sha, kuma a cika masa cikin sa da shi.” Da yamma yarinya ta dawo daga daji rike da wasu saiwoyin magani, tana zuwa ta gyara su ta hau su da daka har sai da suka daku likis, sannan ta kwashe a cikin wani akushi ta rufe ta miKawa Bashari kanta a sunkuye. Watakila saboda kunyar kada a maimaita abin da ya faru dazu. Bayan an kammala cin abincin dare, sai ta dauko wata sarewa ta fito waje ta yi kwanciyarta rigingine a kan buzun ragon da ta shimfida cikin hasken farin wata. Busarta na tattare da wani irin sanyi wanda a cikin zuciya kawai ake iya jin sa. A daidai wannan lokaci kuwa, shi Bashari abin ya gauraye masa ne da cewa yana can gefe daya kwance a kan tasa tabarmar. Zuciyarsa ta yi sanyi, idanunsa kuma na ta kallon yadda wata ke ta kaiwa da komowa cikin giragizai, -_
Www.bankinhausanovels.com.ng ko kuma giragizan ne ke kai wa da komowa? Oho! Shi dai ba ya iya tantancewa.
Lokacin da dare ya dan daga, sai yarinya ta shige cikin bukkarta. Shi ma kamar ita ya ke jira, tana shigewa sai ya yi zumbur ya mike ya shige wurin mara lafiya. Har gari ya waye dukkan su shi da ‘yar Fulani babu wanda ya samu ya yi wata cikakkiyar runtsawa. Tabbacin cewa sun fara kamuwa da son juna.
Wayewar gari ke da wuya, sai Bingyel ‘yar Fulani ta tatsi madara ta dafa ta zuba zuma ‘yar kadan ta nufi bukkar su Bashari. Tana zuwa sai ta yi sallama, ta shiga ta gaishe shi cikin ladabi, ta ba shi ta ce masa – nasa ne shi kadai tare da tunatar da shi cewa mara – lafiyar ba zai ci komai ba wannan safiyar sai dai magani kadai. Ta yi murmushi shi ma ya yi, ta dukar da kai ta juya cikin . hanzari
Bashari ya tallafo Sarki ya ba shi hadadden maganin nan. Abin mamaki aka yi sa’a ya yi ta sha har sai da ya rage kadan, shi kuma Bashari ya dauki madararsa ya shanye sai kwaryar. Yana ajiyewa sai gyatsa.
Bayan dagawar hantsi sai ga Sarkin Fulani ya shigo don duba mara lafiya. Ya tarar barci ya dauke shi, sai ya cewa Bashari “Da ma na san barci zai dauke shi
saboda haka al’adar maganin ta ke, kuma ba zai tashi ba sai misalin yammaci. Saboda haka kada ka kuskura ka tashe shi sai ya tashi da kansa.”
Bashari ya ce, “To Baba, Allah Ubangiji dai Ya saka muku da alheri.”
Ardo ya amsa da cewa, “Amin yaro, ai irin wannan yi wa kai ne, yau gare ka ne gobe ga waninka.”
Ardo Jumare ya fice ya nufi gindin wata itaciyar cediya ya zauna yana tufkar igiya.
Bingyel ta fito ta nufi garkensu ta kora shanu zuwa cikin daji, tana tafiya tana busa sarewar nan ta jiya. Shi kuwa Bashari gaba daya sai hankalinsa ya rika bin inda sautin sarewar ke nufa. Can bayan wani lokaci, kasancewar ya san cewa mara lafiya ba zai neme shi ba, sai ya sulale ya nufi inda sautin sarewar nan ya nufa dazu. Ya yi tafiya mai tsawo amma bai gan ta ba, ya sami gindin wata bishiya ya zauna tare da tsunduma cikin kogin tunanin abubuwa mabambanta.
Can sai ya sake jiyo sarewar na tashi, ai kamar wata kibiya ya mike ya nufi wurin. Yana zuwa sai ya gan ta a kan reshen wata bishiya tana wasa da Kafafuwanta. Bashari ya yi zamansa KarKashin bishiyar alhalin ita ba ta ma saniba.
Can sai hankalinta ya yi wo Kasa, sai ta ga mutum
Www.bankinhausanovels.com.ng zaune, kuma ba tare da bata lokaci ba ta gane ko wane ne. Mamaki ya rufe ta, sai ta diro.
“Yar Fulani ta ce, “Kai kado yaya aka yi ka zo amma ba ka yi mini magana ba
Bashari ya ce, “Don Allah ki yi hakuri, busarki mai sanyaya zuciya nake matukar jin dadi, sai na yi tunanin in kin san na Zo, to kina iya dainawa, shi ya sa ko sallama ban yi ba. Sai na yi burin da ace ni ma na iya busa irin wannan sarewar mai daukar rai fa?”
Sai ta yi murmushi ta duKar da kai ta ce, “Ai babu wuya, duk abin da mutum ya saa ransa cewa zai koya, ai zaiiya matufKar dai akwai mai koya masa a kusa.”
Jin haka sai Bashari ya ce mata, “Ai kuwa da wannan mai koyo ya yi sa‘a.”
‘Ta mika masa sarewar ta ce ya rike, ita kuma sai ta ruga cikin daji. Can bayan kamar rabin sa‘a, sai ga ta ta dawo rife da gwandar daji masu kyau sun nuna lugub-lugub, ga kuma Kokiya da tsada duk ta hada ta mikawa Bashari. Ya yi godiya a daidai lokacin da ya dauki wata tsada ya jefa a bakinsa.
“Yar Fulani ta ce, “Ya kai wannan saurayi, ni ko wani abu ne ya ke ta ba ni mamaki.” Bashari ya ce, “Ya ke ‘yar Fillo ke kuwa mene ne ke ta ba ki mamaki?”
Ta ce, “Tun ranar da ka zo sai na ji kamar wata
Www.bankinhausanovels.com.ng sabuwar rayuwa ta zo mini, don ko tunaka na yi sai in ji wani farin ciki na shiga cikin zuciyata, in kuma kana kusa da ni, duk sai in rude. Ka ga daren jiya ma na kasa yin barci saboda tunanin ka, wai mene ya sa haka ne?”
Bashari ya Kyalkyace da dariya. “Yar Fulani ta yi wani sansaraKwai tana mamakin mene ne abin dariya a cikin maganarta, don ita tana ganin iyakar gaskiyarta ta fada. Can sai Bashari ya sake kallon ta da kyau sannan ya gyara murya ya ce, “Yarinya ‘yar Fillo, wannan abu da kike ji ya nuna miki saurayi kado ya yi kasuwa ke nan. A taKaice dai wannan abu shi ake kira soyayya.”
Ta dukar da kai da fahimtar cewa lallai abin da ya fada fa haka ne, sai ta ce, “Ai ko kadan haka ba za ta yiwu ba.”
Bashari da ke kashingide jikin bishiya, sai ya gyara zama ya ce, “Ko mene ne dalilinki na cewa hakan ba za ta yiwu ba?”
Ta amsa da cewa, “Ya kai saurayi, shi so nauyi gare shi, ya fi dutse nauyi kuma ya fi teku zurfi. Yana da dadi da Kanshi da kuma haske. In kuma baayi sa’a ba, to shi so babban hadari ne, kuma ga yawan mahassada a cikin sa.
Ya kai saurayi, idan muka shiga cikin kogin so ni da
Www.bankinhausanovels.com.ng kai, to ina ganin ma abin zai yi wuya. Ka ga da farko dai kai ba dan Fulani ba ne, halayenmu da naku sun sha bamban. Mutanen gari za su rika zunden ka cewa ka auro ‘yar Kauye, sannan kuma daga ganin ka kai da mahaifinka masu wadata ne, mu kuwa talakawa ne.”
Sai ya katse ta ya ce, “T’saya kada ki yi nisa. Ke Bingyel, ba ki da hujja ko daya, zan iya ci gaba da rayuwata gaba daya a riga ko daji saboda ke, in hakan kika fiso. Zancen ni ba Bafillatani ba ne ki kau da shi, in kuma zai fi miki dadi, to ni ma daga yau ina iya zama dan Fulani.
Ya ke hasken wanda ya yi sa’a ya gan ki, maganar arziki da ki ka yi, to shi so babu ruwansa da arziki ko sarauta ko talauci, kuma ni ina ganin duk son da ya ke duba wadannan abubuwa, to ba hakikanin son gaskiya ba ne. ‘To wai ma in kina maganar arziki ne, shin kin san cewa mahaifinki da a cikin gari ya ke dole a kira shi Sarkin kudi?
Ya ke farin cikina, ina so daga yau ki sani cewa babban abin da soyayya ke bukata shi ne alkawari. Ke in takaice miki ni na sadaukar da kaina zuwa gare ki, sai dai ko in ke kika ki ko kuma mahaifinki. Ni dai sai yadda kika yi da ni.”
Murna ta lullube ‘yar Fulani, ta ce, “Ya kai masoyina, ni kuma na dauki alkawari in dai muna da
Www.bankinhausanovels.com.ng rai, to babu mai raba mu. Sai dai matsala daya ce kawai nake ganin za ta iya kawo mana dan cikas.”
Ya tambaye ta, “Wace irin matsala ce?”
‘Yar Fulani ta ce, “Ina kyautata zaton, ko kuma in ce maka mun riga mun yanke shawara nan ba da dadewa ba za mu bar wannan Kasar zuwa wata, don kwanciyar hankalinmu gaba daya. Akwai kanin Sarkin kasar nan wanda ya nuna cewa wai dole in so shi ni kuma na ki, kuma ga shi yanzu shi za a yi wa sarauta. Wannan ya sa za mu tashi mu bar masa Kasarsa da zarar an nada shi, kada ya zo ya ci mana mutunci.”
Hakan ya tsunduma Bashari cikin tunanin irin rudanin da soyayyarsu za ta shiga. Ko kuma wane irin hali shi kansa zai shiga in har wani can daban ya aure ta? Ya shiga sake-sake a zuciyarsa yana cewa “In kuwa haka ne, to wannan dattijo da nake jiyya yana samun sauki za mu yi sallama in tsallake in bi Fulanin nan duk inda za su.”
“Yar Fulani ta yanke masa tunaninsa ta ce, “Ya kai saurayina kana tunanin mene ne?”
Sai ya ce mata, “Ke nake tunawa.”
Ta ce, “To ai ga ni kusa da kai. Kuma ai mun riga mun yi wa juna alkawari.”
Suka dubi juna suka yi wani murmushi a daidai
Www.bankinhausanovels.com.ng lokacin da wancan dan Fulani da aka dauka don taya ta kiwo ya iso wurin. Samun su a cikin irin wannan hali wanda ke nuna cewa akwai soyayya ya sa zuciyarsa Kuntata, ransa ya baci, ya rasa abin da ke yi masa dadi a duniya. Ya wuce dai bai ce komai ba.
Suka zauna nan gindin bishiya, ta fara koya masa yadda ake busa sarewa. La’asar sakaliya suka tashi suka koma riga cike da farin ciki da annashuwa.
Wancan dan Fulani makiyayi kuwa sai da ya san yadda ya yi ya kewaya ya je ya sami Ardo ya tsegunta masa cewa ya ga ‘yarsa tana zance da wani bako kado. Nan da nan Sarkin Fulani ya kwabe shi tare da umurnin cewa kada ya sake jin irin wannan magana daga bakinsa. Tun daga wannan rana kuwa dan Fulani ya shiga Rulle-Kulle a cikin zuciyarsa, amma fa ba Kullin alheri ba.
Dawowar wadannan yara sai suka tarar da Sarkin Fulani a wurin mara lafiya, wanda a karon farko ya fara samun sauki har an fito da shi yana jingine a jikin dannin gidan. Murna ta kama Bashari duk da cewa har yanzu mara lafiyar bai fara iya magana ba, sai dai daga hannu kawai.
Da Magriba ‘yar Fulani ta kawo wa Bashari dambu ya ci, bayan Isha’i kuma, sai ta dauko tabarmarta ta je can kusa da bukkarsa suka zauna suna ta zantawa har
Www.bankinhausanovels.com.ng dare ya fara shiga sosai kafin ta tashi ta shige tata bukkar.
Haka makamancin wannan al’amari ya yi ta faruwa, in Bashari ba ya wurin majinyacinsa, to yana cikin daji wurin ‘yar Fulani suna hira.
A haka sai da suka sami kusan watanni uku.
Yanzu Bashari ya kware sosai a fagen busa sarewa ta yadda in yana busawa, sai ka ga shanu sun kewaye shi a cikin daji suna saurara. Soyayya kuwa tsakaninsa da ‘yar Fulani sai abin da ya kara gaba.
Mara lafiya kuma ya gama murmurewa, sannan duk abin nan da ake yi bai taba gayawa Bashari ko kuma sabon abokinsa Sarkin Fulani cewa shi ne Sarkin wannan kasa ba. Wata rana suna cikin hirarsu irin ta dattijai, sai ya cewa Sarkin Fulani, “Babu shakka akwai soyayya a tsakanin dana da ‘yarka, ko mene ka gani?” Sai Sarkin Fulani ya ce, “Ai niba ni da ta cewa, abin da ‘yata take so shi nake so, don na fi son farin cikinta fiye da komai. Ita da dan’uwanta fa kadai suka rage gare ni.
Akwai dai wani abu ne da muke hange. Wato Kanin Sarkin wannan kasa tamu yana son wannan ‘ya tawa amma ita ko kadan ba ta Kaunarsa, to kuma ga shi goben nan shi za a nada Sarki, kuma na tabbata
Www.bankinhausanovels.com.ng zai kyale mu ba. Saboda haka muke ta shiryeshiryen washegarin nada shi mu kora shanunmu mu bar masa Kasarsa don kada ya tozarta mu. Ba don rashin lafiyarka ba ma da tuni mun yi nisa.
Dama ka san shi kanin Sarki yana shakkar tsohon Sarki ne saboda ba zai yardar masa da zalunci ba. To yanzu abu ya lalace, don ko shiga gari da na yi ranar kasuwa, duk mutane suna ta dari-dari kan wannan sarauta tasa. In ka ga irin mutanen da aka gayyato don bikin nadin ma kawai abin zai ba ka takaici, ko ina gari ya cika da shaidanun mutane suna ta sheKe ayarsu, kai abin babu kyau. Babu shakka mun yi rashin adalin Sarki.” Jin haka sai Sarki ya ce masa, “Ai komai na Allah ne. In niyyarsa ba ta alheri ba ce sai ka ga wani abu ya faru, sai dai kuma akwai wani abu da nake roKo ka yi, wato Kokarin halartar bikin nadin sabon Sarki, don akwai hikimar da ta sa na ce maka haka. Ni da dana ma duk za mu halarta,in Allah Ya so.” Sarkin Fulani zai yi jayayya, sai kuma ya lura da yanayin da abokin nasa ya yi masa magana. Sai ya yanke shawarar yin shiru tare da amincewa.
Sarki Shahzad ya fara tunani cewa, “Ikon Allah, yanzu har watanni uku sun cika, ashe ni lissafina ba daidai ba ne.”
Www.bankinhausanovels.com.ng
Bayan kiwo su Bashari suka koma gida. Yana kammala dauraye jikinsa sai ya shige cikin bukkarsu ya tarar da Sarki zaune yana lazimi. Bayan ya kammala, sai ya gaishe shi cikin girmamawa, shi kuma ya amsa cike da murmushi.
Sarki ya ce, “Ya kai dana Bashari zauna ina son mu yi magana ni da kai.”
Bashari ya nemi wuri ya zauna yana saurare a tsorace abin da Sarki zai ce, don shia zatonsa ko ya yi wani laifin ne.
Ya ci gaba da cewa, “A wancan lokaci da wannan masifa ta faru da ni na san wadanda nake tare da su, har suka yi Kokarin salwantar da ni, wato ba barayi ne suka nemi halaka ni ba kamar yadda mutanen gidan nan suke zato. Saboda haka ina son ka ba ni labarin hakikanin abin da ya faru tun daga farko har karshe. A takaice kuma ina son in san labarinka kai kanka.”
Bashari ya kwashe labari bai rage komai ba ya ba Sarki, tun daga fitowarsa gida har zuwa zamansu
gidan Sarkin Fulani da kuma dalilin da ya sa ya yi Karyar cewa barayi ne suka nemi halaka shi har ma don su yarda ya ce musu mahaifinsa ne.
Sarki ya ce, “Ya kai dana, na gode maka, Allah Ya saka maka da alheri, Yasaka gama lafiya.”
Daga nan sai Sarki ya ba Bashari labarinsa tare da
Www.bankinhausanovels.com.ng sanar da shi cewa gobe tun Asubahin fari za su nufi gari, kasancewar bayan Sallar Azahar ne a kan yi nadin sarautar. Ya kammala da cewa Bashari, “Sai dai kuma ina fata wannan labari namu ya ci gaba da kasancewa sirri har zuwa lokacin da za a bayyana shi.”
Suka sami Ardo suka yi masa godiya mai tarin yawa tare da sanar da shi cewa tun Asubahin fari za su tafi. Sarki kuma ya Kara jaddada roKonsa ga Sarkin Fulani a kan cewa lallai yana buKatar ya halarci wurin nadin sabon Sarki gobe.
Bashari da ‘yar Fulani kuwa har kuka suka yi saboda za su rabu. Ya yi mata alKawarin cewa za ta rika ganin sa, zai rika zuwa duk inda take.
Asuba na yi suka kama hanya. Bayan sun dan fara tafiya kadan, sai Sarki ya sauya shigarsa ya yi irin ta makiyayan daji, sannan ya kawo wani rawani ya nade kansa ruf, ba ka ganin komai sai idanu. In ka gan shi sai ka rantse cewa wani Ridahumin bakauye ne.
Suka isa cikin gari, sai suka ga an Rayata shi da tutoci da sauran kayan Kawa, ko ina ka duba sai gungun baki, masu goge na yi, masu molo da dara na yi, ‘yan caca da masu bori kuwa kowa ya baje hajarsa. “Yan daudu da karuwai sai rangwada suke suna ta kurkurdawa tsakanin jama’a suna sheKe ayarsu wai
Www.bankinhausanovels.com.ng nasu ya kama, gari ya zama nasu.
Sarki na gaba Bashari na biye da shi, ba su zame ko ina ba sai gidan Waziri, suka tarar da zaurensa a bude kuma ga dukkan alama yana ciki, saboda haka sai suka shiga. Suka tarar da shi zaune a kan buzu ya yi tagumi, cike da bacin rai. Sarki ya ce, “Salamun alaikum ya kai Waziri.”
Waziri ya yi wuf ya dubo zuwa gare su da mamaki don ya ji muryar ta yi kama da ta Sarki. Ya mayar da sallama sannan ya ce, “Ku su wane ne, kuma mene ne labarinku?”
Sarki ya warware nadinsa.
Waziri ya yi tsalle ya tsallake kujeru ya yi cikin gida a guje yana cewa, “Ni mene ne nawa a ciki za ka yi mini fatalwa? Je ka can wurin Kaninka shi ne zai haye maka karaga.”
Da Sarki ya ga cewa lallai Wazirinsa ya firgita, sai
ya zauna kan kujera tare da umurtar Bashari cewa shi ma ya zauna. Zamansu ba dadewa sai ga dan Waziri ya shigo da cikakken tabbacin cewa mahaifinsa ne a cikin zauren, amma sai ya yi arba da Sarki a zaune, mamaki ya kama shi. Ya yi tirya-tirya zai gudu, sai Sarki ya kira sunansa, “Abdallah.” Sai ya tsaya ya sakankance cewa lallai wannan Sarki ne, saboda haka sai ya yi gaisuwa.
Sarki ya ce masa, “Ka je ka cewa Waziri ina son ganin sane.” Yaro ya shiga cikin gida ya tarar da mahaifinsa wato Waziri cikin halin tsoro, yana ta kyarma.
Waziri ya tambaye shi, “Ia ina ka biyo da za ka shigo? Ba ka ga fatalwar nan ba a zaure?”
Yaro ya ce, “Baba ka kwantar da hankalinka, ba fatalwa ba ce, Sarki ne da kansa ya ce yana son ganin ka. Ina ganin gara ka je, wataKila akwai wani al’amari ne wanda muka kasa ganewa.”
Da kyar Waziri ya fita. Sarki ya ce masa, “Haba Waziri, ko dai da ace ni fatalwa ce ka san ba zan cuce ka da komai ba.” Ya dafa kafadarsa ya ce, “Kwantar da hankalinka.” Waziri ya dan sami natsuwa, ya yi gaisuwa cike da mamaki. Sarki ya dan gutsura masa labarin a taKaice Kwarai sannan ya ce masa ya tashi yanzu babu lokaci. Ya ce, “Abin da nake so da kai yanzu Waziri, ka je ka kawo mini kayan yaKi, amma fa kada wani ya sani. Kuma ka gargadi yaron nan Abdallah ya kame bakinsa.” Aka kawo wa Sarki sulke ya shige, haka nan shi ma Waziri, don ko data Baci. Jama’‘ar gari da baki, babba da yaro, mace da namiji, duk kowa ya hallara a filin nadin
Sarki. Sarkin Fulani Www.bankinhausanovels.com.ng da’yarsa su ma suna cikin ‘yan kallo. Yanzu Waziri da sabon Sarki kawai ake jira don aci gaba da gudanar da harkokin nadi.
Jimawa kadan sai aka ji tambura na tashi, sabon Sarki ya tunkaro ke nan. Ya zo ya zauna, yanzu sai dai masu nadi kawai su fara aikinsu. Kuma a daidai wannan lokaci zuciyar Sarkin mai jiran gado tuni ta harzuka irin yadda wai har Waziri ne ya yi sakaci har ya riga shi fitowa. Ya Kulla a cikin ransa cewa ana
nada shi cikin jawabinsa na farko zai fara ne da sauke Waziri ya nada nasa. Wato an sami dalilin da za aba jama’‘a na sauke Waziri; komai ya zo da sauki ke nan.
Can sai aka hango wani mutum ya keto fili a kan doki ga Waziri biye da shi tare da wani kyakkyawan saurayi. Kuma shi wannan mahayi ya rufe fuskarsa, sai idanunsa kawai ake iya hangowa. Mutane sai suka rika zaton cewa wannan lallai wani babban amini ne na masarautar ya halarci wurin nadin Sarki, shi ma sabon Sarki haka ya ke zato. Saboda haka nan da nan aka ba shi kujera ya zauna a cikin tantin da Sarki ya ke. Albarkacinsa shi ma Bashari ya sami zama cikin wannan babbar inuwa.
Ita ko Bingyel ‘yar Fulani da ke can cikin taro da ta hango saurayinta sai ta fara tsalle tana daga hannu wai ko zai hangota, amma ina, saboda yawan jama’a.
HMMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG