YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM’UNA
CHAPTER 13 BY HARUNA USMAN
Www.bankinhausanovels.com.ng
A JIYA MUN TSAYA
Can sai aka hango wani mutum ya keto fili a kan doki ga Waziri biye da shi tare da wani kyakkyawan saurayi. Kuma shi wannan mahayi ya rufe fuskarsa, sai idanunsa kawai ake iya hangowa. Mutane sai suka rika zaton cewa wannan lallai wani babban amini ne na masarautar ya halarci wurin nadin Sarki, shi ma sabon Sarki haka ya ke zato. Saboda haka nan da nan aka ba shi kujera ya zauna a cikin tantin da Sarki ya ke. Albarkacinsa shi ma Bashari ya sami zama cikin wannan babbar inuwa.
Ita ko Bingyel ‘yar Fulani da ke can cikin taro da ta hango saurayinta sai ta fara tsalle tana daga hannu wai ko zai hangota, amma ina, saboda yawan jama’a.
ZAMU TASHI
Sarkin Fulani ya tambaye ta dalilin daga hannunta, sai ta ce, “Dubi babban bakon can da ya zo yanzu, kusa da shi wane ne zaune?”
Dattijo ya kyalla ido sosai, ya ce, “Ai kuwa Bashari ne, yaya aka yi ya sami zama cikin sarakuna?”
Bayan an kintsa, sai aka fara al’adun da aka saba na nadin Sarki, aka kammala aka yi addu’o’i sannan aka dauki rawani wanda nada shi a kan zababben Sarki shi ne tabbatuwar sarauta. Sai suka ji wata irin tsawa tace, “Kul! Kada a nada rawanin nan.”
Duk sai hankalin jama’a ya komo ta inda tsawar ta fito, sai aka ga ashe mahayin nan ne da ya zo dazu. Nan take sai ya bude fuskarsa.
To fa, da mutane suka ga Sarkinsu ne da suke matukar Kauna, sai shewa mai cike da mamaki ta cika wurin. Wadanda ke kusa kuwa sai suka fara zubewa kasa don gaisuwa. Wasu kuma cewa suke yi fatalwa ce.
Kanin Sarki saboda rudewa sai ya jawo wata gorar ruwa da ke kusa da shi yana wanke fuska don tunanin ko idanunsa ne ke zagi. Wuri ya rude haya-haya sai Sarki ya ce, “Jama’a don Allah a saurara, akwai labari.”
Wuri ya yi tsit, Sarki ya cewa Bashari ya tashi ya labarta wa mutane abin da ya faru. Ya mike ya labarta Www.bankinhausanovels.com.ng
ba tare da rage komai ba, yana ma gab da kammalawa ne sai kawai ya hango ‘yar Fulani a cikin taro ita da mahaifinta, sai ya kira su ya nuna wa jama’a ya ce, “Wadannan bayin Allah a gidansu muka yi jinyar Sarki har na misalin wata uku.”
Da mutane suka ji wannan labari sai takaici ya kama su, wasu ma har kuka suka yi ta ribzawa. Nan fa mutane suka nemi yin hargowa suna cewa, “A ba mu su mu kashe! A tsire su! A dafa su da ransu!”
Sarki ya sa aka kama su don gudun abin da jama’a za su iya yi musu a wurin, amma da ya ke mutane sun san halinsa na tsananin tausayi da yafiya, sai nan take suka birkice a kan cewa lallai a wurin suke bukata a mika su zuwa ga Alqalin Kasar ya yanke musu hukunci kafin a ci gaba da komai don kuwa maciya amanar kasa ne.
Sarki ya rasa yadda zai yi, kuma ya tabbatar yadda hankalin jama’a ya tashi, matukar ya hana wannan bukata tasu, to komai na iya faruwa. Akan dole ya amince aka mika wa Alkali shari’ar. Shi kuma ba tare da bata lokaci ba, ya ba da umurnin a tafi da su jakara a tsire su gaba daya. Jama’’a dai ba su sakankance ba sai da dubban mutane suka bi su a baya suna tsine musu albarka. A takaice ba a kyale su ba sai da aka tabbatar sun sami masauki na dundundun a lahira Www.bankinhausanovels.com.ng tukuna, sannan aka dawo filin nadin sarauta.
Sarki Shahzad ya yi godiya saboda irin kaunar da aka nuna masa, sannan ya kammala jawabinsa da cewa, “Jama’‘a kun dai san ba ni da da, to daga yau ku shaida wannan yaro Bashari ya zama dana, shi ne magajina.” Fili sai sowa, mutane suna cewa, “Mun amince! mun amince!”
Aka fa shiga shagalin dawowar Sarki abin kamar Sallah. Bata gari kuwa nan da nan kowannen su sai Kokarin barin gari, murna ta koma ciki.
Bayan an gama natsawa sai Sarki ya kira Bashari ya ce masa, “Ya kai dana, ina rokon ka da ka kare mutuncinka a cikin wannan al’umma, wato ka kiyaye mana mutuncin da jama’a ke ganin mu da shi, kar ka yi abin da za mu ji kunya. Daga yau zan fara karantar da kai ilmi na addini da sauran harkokin yau da kullum, in Allah Ya yarda. In kuma na ga ka kware tare da gogewa game da sha’anonin mulki, to akwai abin da nake shawartawa a cikin zuciyata.”
Bashari ya yi godiya.
Sarki ya ci gaba da cewa, “Abin da nake bukata da kai yanzu shi ne, ka je rigar Sarkin Fulani ku zo tare da shi.”
Nan da nan Bashari ya zaburi doki sai rigar Fulani.
Www.bankinhausanovels.com.ng Ya ko yi saa ya tarar Ardo Jumare zai fitake nan, ya – gaishe shi cikin girmamawa.
Ardo ya ce, “Bashari amma ku mutanen birnin kuna da wayo, ashe Sarki ne muka zauna da shi na tsawon wata uku amma bamu sani ba?”
Shi dai Bashari bai iya cewa komai ba sai dai murmushi kawai.
Bashari ya ce, “Allah Ya taimaki Ardo, mai martaba Sarki ne ya ce don Allah yana da bukatar ganin ka.”
Sarkin Fulani ya ce, “Yaro, waye zai Ki kiran Sarki?”
Bashari ya fara shafa keya yana cewa, “Kafin ka kintsa bari in dan shiga daji in duba kanwata a wurin kiwo, mun kwana biyu ba mu gaisa ba.”
Sarkin Fulani ya ce, “E ita ma ko dazun nan take ta maganar ka, ashe dan halas kana tafe.”
Shigar Bashari daji fa ya ga ‘yar Fulani sai hira ta sarke, bai farga ba sai da rana ta fara shigowa cikin inuwar da suke, sannan firgigi ya ce, “Ke! Na bar yana can yana ta jira na za mu tafi wurin Sarki da shi. Kin ga kin sa na zama mara kirki ko? Na bar tsofaffi suna ta jira.” Suna cikin haka sai ga dan Fulanin can mai taya ta kiwo ya zo, ya yi niyyar daga sanda ya sheme Bashari sai dai wata zuciya ta hana shi. Ya wuce dai bai ce Www.bankinhausanovels.com.ng komai ba. Ardo da Bashari suka rankaya zuwa gidan Sarki a birni. Suka yi gaisuwa ya amsa musu da irin murmushin nan nasa mai ban sha’awa kuma mai cike da Kauna. Ya taso daga kujera ya rungume Sarkin Fulani, ya ja shi don su zauna kamar yadda suka saba yi a riga lokacin da ya ke jinya. Idan ka gan su sai ka dauka wa ne da Kani. Ga su farare, masu fararen gemmiai da saje. .
Bashari ya nemi izini ya fita daga waje. Bai yi nisa ba don ya san zaa iya neman sa. Sarki ya dubi Sarkin Fulani ya ce, “Ardo.” Ardo ya amsa, “Ran Sarki ya dade.”
Sarki ya ce, “Ardo daga yau ina son in sanar da kai cewa ka zama dan’uwana, tsakanin ni da kai babu iso. ‘Tun lokacin da na zauna da kai na fahimci cewa kana da ilmin addini da mutunci da karimci. Saboda haka na ba ka amanar kaina, matukKar ka ga na yi wani abu wanda ya kamata a ce an kwaba mini amma ka kyale ni, to ban yafe maka ba.
Ni da ‘yan majalisata mun zauna mun yanke shawarar nada ka Sarkin Fulanin wannan Kasa baki daya, maimakon Sarkin rigarku kawai. Sannan kuma yanzu kana daya daga cikin ‘yan majalisar Sarki. Za a yi nadin ne ba da dadewa ba, kamar
Www.bankinhausanovels.com.ng Juma‘a mai zuwa. Kana da ikon dawowa gari da zama duk lokacin da ka ji hakan ya yi maka dadi.
Na riga na sa an shirya maka gidanka yadda ya kamata. Kuma akwai wasu kayayyaki da na tabbatar cewa za su dace da kai na sa an shirya su yanzu, in za ka koma zaa bikadasu.”
Sarkin Fulani tun yana godiya har ya koma ya yi
shiru, ya zura wa Sarki ido kawai kuru. Can sai suka koma suka ci gaba da hirarsu kamar yadda suka saba.
Sarki ya ce, “Don Allah in Ardo ba zai damu ba, ina da wata bukata guda daya ko kuma alfarma da nake nema ayi mini.”
Jin haka sai Sarkin Fulani ya ce, “Ran Sarki ya dade ai ka wuce nan. Fadi abin da kake bukata kawai in har lallai kana da bukatar fada din, amma ko ma mene ne nina amince.”
Sarki ya ce, “Ina so ne ka aurar da ‘yarka Bingyel ga dana Bashari.”
Sarkin Fulani ya ce, “Na ba shi. To ai ni wannan kamar Karin girma ne a gare ni. ‘Yata ta auri dan mutunci kuma dan Sarki mai adalci.”
Abin ka da dattijai, nan suka yanke shawarar za a yi bikin cikin wata biyu masu zuwa. Shi ma abin da ya
sa za a dan dauki lokaci haka shi ne dalilin da Sarki ya
Www.bankinhausanovels.com.ng bayar cewa wasu daga cikin manyan bakin da za a gayyata daga nesa suke, kuma bai kamata a ba su dan gajeren ‘okaci ba, don baa san irin hidimomin da ke gabansu ba, musamman kasancewar mafi yawancinsu ba su dade da barin garin ba a dalilin nadin sarauta da suka zo.
Sarki ya yi kiran Bashari ya ce masa, “Ai sai ka ba da tukuici, babanka Sarkin Fulani ya mallaka maka Kanwarka kake ce mata ko? To za a yi bikinku cikin wata biyu.”
Bashari bai san lokacin da ya buga tsalle ba saboda tsananin murna, ya manta cewa a gaban Sarki ya ke, watakila kuma kasancewar don ya riga ya saba da su ne? Nan take ya fara zabgawa Sarki kirari da addu’a, “Hadari sa gabanka inda kake so. Allah dai Ya sa ka gama lafiya.” Ya juya wurin Sarkin Fulani ya yi godiya cike da kunya.
Sarki ya yi magana, “Yauwa Bashari sai ka je da babanka ka nuna masa gidansa?”
Sarkin Fulani da Sarki suka yi sallama, Bashari kuma na gefe ya kasa zaune ya kasa tsaye, har sai da suka fita suka nufi sabon gidan Sarkin Fulani. Bayan ganin gida sai ya rasa abin da zai ce, da Kyar Bashari ya ciyo kansa ya hau ingarman dokin da aka ba shi ya
nufi riga, don da ya ce ne sai ya sake komawa ya yi wa Sarki godiya.
Kafin Ardo ya isa gida, tuni Bashari ya kewaye a sukwane zuwa can cikin daji inda budurwarsa ke kiwo, don ya rigaya ya san cewa ba ta riga ta taso zuwa gida ba. Yana zuwa ransa a bace ya ce mata, “Kin ji wai za a yi mini aure nan da wata biyu.”
Ta ce, “To mene ne amfanin ka zo ka fada mini? Da mana gaya maka ina ‘yar Fulani mai kiwo ina dan Sarki>”
Bashari ya katse ta, “Af na manta ban yi miki albishir ba, Sarki ya yi wa babanki sarautar Sarkin Fulanin wannan kasar gaba daya, sannan kuma yanzu shi ne babban mai ba Sarki shawara na musamman.”
“Yar Fulani tana jin haka sai cikin bacin rai ta ce, “Da ma mahaifina ai Sarkin Fulani ne, kuma wannan abokantaka da Sarki babu wani amfani ko kuma tabbas ciki, don da a ce yana son sa ai ba zai hana dansa ya auri ‘yarsa ba. To ni zan fada wa babana kada ya amshi ko daya daga cikin abin da Sarki ya ba shi, kuma jibi-jibin nan za mu tattara mu bar muku Kasarku, kai kuma ka je ka auri Sarauniyar kyau ta duniya. Da ma an ce mini ku kado ba ku da alkawari amma Www.bankinhausanovels.com.ng ji ba, na ga kamar kai daban ne. Amma babu komai.” Ya jawo sarewarsa ya fara yin wata irin busa da sukan yi tare, sai ta sa hannu ta fisge, ta ce, “Kaicona da na koya maka yadda ake busa wannan abu, ga shi yanzu za ka je kana busa wa wata.”
Bashari ya Kyalkyace da dariya sannan ya ce, “Ke, ba na son shirme. Ga sanarwa ta musamman, Bashari dan Salihu kuma dan Sarki Shahzad, kado, zai auri Bingyel ‘yar Fillo a cikin watanni biyu masu zuwa. Kuma ga ta nan a gabansa tana kallon sa har an gama shirya komai tsakanin Sarki da mahaifinta.”
Murna kuma ba sai an labarta ba.
Sai ya kasance a duk ranar da babu karatu ko kuma wata hidima da zai yi wa Sarki, to Bashari yana wurin ‘yar Fulani a cikin riga suna tsimayin bikinsu. Ji suke yi kamar su jawo ranar.
Sarkin Fulani kuwa tuni ya yanke shawarar cewa sai an yi bikin ‘yarsa sannan zai koma cikin birni ya tare.
Ana nan dai har ya kasance yanzu saura kwana uku kacal a daura auren.
Bashari ya nufi riga don ganin budurwarsa, amma abin da ya tarar ya yi matukar ba shi mamaki, wato bukkokin gidan Sarkin Fulani ne gaba daya a Kone.
Www.bankinhausanovels.com.ng Ya yi tunanin samun wani Bafillatani ya tambaya amma sai ya sauya shawara don babu kowa a wurin, kuma kasancewar tsakanin gidan Sarkin Fulani kafin a sake samun wani gidan akwai tafiya mai ‘yar tazara.
Ya ji kamar zai zautu don tsananin rudewa. Ya nufi inda suke kiwo, ba kowa, ya dauko sarewarsa yana busawa ko ta ji ta amsa, amma shiru. Sai ya yankewa kansa shawarar cewa lallai duk yadda aka yi ‘yar Fulani yaudarar sa ta yi ba auren sa za ta yi ba, tun da dai ga shi sun kora dabbobinsu sun gudu. Kuma abin mamaki ita da dattijo babanta.
Ya rasa inda zai sa kansa. Ya sake komawa can riga din amma dai abin da ya bari shi ya tarar.
Daga Karshe dai ya dauki dangana.
Ya hau dokinsa don komawa cikin gari. Ya fara tafiya ke nan sai ya hango tarin wani abu a cikin ganyayyaki. Da ya matsa sai ya ga ashe Sarkin Fulani ne kwance male-male cikin jini, ya Kusa da shi kuma Harande ne dansa, Kanin ‘yar Fulani, shi wannan ma ba sai an tambaya ba, daga gani ka san ya mutu. Ya gaggauta ya dora su a kan doki ya daure ya wuce gaba yana ja har cikin gari. Ya je ya ba Sarki labarin irin wannan abin bakin ciki da ya afku. Aka dauki Sarkin Fulani aka shiga da Www.bankinhausanovels.com.ng shi. shi don fara yi masa magani, shi kuma marigayin aka yi masa janaza.
Zaton sarki yafi karfi a kan cewa ko makiyansa ne suka yi wa Sarkin Fulani wannan aika-aika don irin taimakon da ya bayar wurin jinyarsa. Suka yi zaton shi ma Sarkin Fulanin sun halaka shi ne, suka kwashe masa dabbobi, suka kashe masa da, watakila ma ita kanta yarinyar ba a nan suka kashe ta ba. Daga Karshe dai aka yanke shawarar saurarawa har sai Sarkin Fulani ya farfado don gane hakikanin wannan danyen aiki.
Kafin nan sai aka baza jarumai, Kudu da Arewa, Gabas da Yamma ko za a dace a samo dabbobin tare da kamo wadanda ke kora su kafin su Ketare kasa.
Kana ganin Bashari ka san yana cikin tashin hankali, don duk ya fita hayyacinsa. A kullum yana cikin dajin nan inda suke kiwo da ‘yar Fulani, wani lokaci ya dauki sarewa yana wata irin busa wanda duk rashin tausayinka za ta iya sa ka hawaye, in ma ba ka barke da kuka ba.
Bayan misalin kwana uku da faruwar lamarin, sai aka samu Sarkin Fulani ya farfado yadda zai dan iya magana. Aka tambaye shi abin da ya faru, sai ya rika nuna wa Bashari alama, hadi da ‘yan kalmomin da ke iya fitowa daga bakinsa cewa ita ‘yarsa ba a kashe ta Www.bankinhausanovels.com.ng ba An tafi da ita ne, kuma ba kowa ne ya aikata wannan ba ta hanyar dauko jingar miyagu, sai Jae, wato dan Fulanin nan da ke taya su kiwo. Jin wannan fa sai hankalin Bashari ya tashi. Nan take ya nemi izinin Sarki cewa yana son a ba shi dama ya je ya nemo ta duk inda take, Sarki kuwa ya amince. Aka hada shi tare da jarumai dari da isasshen guzuri. Ya yi sallama bayan an yi masa addu’ar samun dacewa.
Abin da ya fara yi sai ya koma rigar su Sarkin Fulani, daga nan sai ya wuce inda suke kiwo ya daga hannunsa ya nuna wa jarumansa Kudu ya ce, “Ina zaton ‘yar Fulani wannan hanyar aka bi da ita, saboda haka nan za mu bi.” Ya wuce gaba suna biye.
Kwana tara suna tafiya ba dare ba rana, sai dai in gajiya ta yi yawa a tsaya a huta. Kusa da kan iyakar Kasa sai suka hango shanu fululu farare fat, Bashari ya cewa jama’arsa su dakata. Ya lababa har sai da ya kai kusa da dabbobin sosai ta yadda zai iya tantancewa, kuma cikin gaggawa ya tabbatar wa kansa cewa babu shakka wadannan shanun su ‘yar Fulani ne. Sai dai kuma abin mamaki ga shanun nan su kadai suna tsaye babu kowa tare da su. Saboda haka sai Bashari ya yi zaton ko sun ya da zango ne don hutawa. Www.bankinhausanovels.com.ng ya koma zuwa ga jama’arsa ya ba su izinin yi wa yankin wurin gaba daya zobe amma cikin dabara. Shi kuma Bashari sai ya nufi cikin dabbobin shi kadai. Dan Fulani da sauran abokansa ashe duk suna kan bishiyoyin da ke wurin, kuma ganin Bashari ya nufi cikin shanu sai suka dudduro. Murna ta rufe Ja’e dan Fulani kasancewar yau ga shi ga Bashari su kadai, zai aika da shi lahira. Da ma tun asali shi dan Fulani ya rabi Sarkin Fulani ne kan nufinsa na samun damar lallaBar ‘yar Fulani ta aure shi har ya sami kusantar dukiyar, to ga shi wannan kadon ya shigo duk ya lalata masa shiri, yana neman tashi a huhun-ma’aho. Wai har kado zai aure yarinya shi kuma Ardo zai koma cikin birni. Saboda haka sai ya yanke shawarar gayyato abokansa suka zartar da wancan danyen hukunci, suka sace yarinyar suka tattara dukiyar gaba daya suka gudu. Daga dirowar dan Fulani sai ya fara surfa wa Bashari ashariya tare da cewa, “Yau kwananka sun Kare.” Amma kafin shi da mutanensa su isa wurin Bashari, tuni askarawa sun kawo kan su. Sun yi Kokarin kariyar kai wanda a sanadin haka, biyu daga cikin Bata-garin suka rasa rayukansu, aka kama sauran har da jagoransu dan Fulani. Bashari ya tambaye shi inda’yar Fulani take, amma takaici da taurin kai suka hana shi magana. Aka yi aka yi amma ina. Daga karshe dai Bashari ya tunzura ya ce su yi ta bugunsa ko zai mutu shi ake so ya mayar da jawabi ba sauran abokansa ba. ‘Yan cika aiki suka fara aikinsu, har sai da dan Fulani ya tabbatar da cewa yana gab da tafiya kiyama matukar bai yi magana ba, sai ya ce zai yi magana.
Ya ce shi dama a cikin zuciyarsa ya san cewa ba shi da wata cikakkiyar bmkata ta auren ‘yar Fulani. Kuma abin da kawai ya sa bai kashe ta ba tun farko saboda ya tabbatar da cewa in ya sayar da ita, to zai sami isasshen guzuri da Karin dukiya don tana da kyau. Ya ce kwana biyar ke nan da ya sayar da ita dinare dubu uku ga wasu fatake, kuma sun riga sun tsallake Kasa da ita. Ya nuna hanyar da suka bi.
Bashari ya ware mutum talatin daga cikin askarawansa, ya ce su kora shanun da masu laifin su kai su wurin Sarki, kuma su sanar da shi cewa shi ya shiga cikin wata kasa neman ‘yar Fulani don kuwa an sayar da ita. Aka yi wa dan Fulani daurin goro shi da abokansa hudu da suka rage, aka kama hanyar babban birni da su. Bashari kuwa da sauran jama’arsa sai suka bi hanyar da aka nuna musu, suka fara tafiya kwana da kwanaki. Kwatsam ba zato ba tsammani sai suka shiga wani yanki cikin wata kasa wanda babu komai cikin sa sai rairayin hamada. Amma tunanin cewa zai Kare da wuri sai suka yi ta kutsawa ba dare ba rana har dai guzurin ruwansu ya Kare, suka fara mutuwa da daidai da daidai. Babu damar komawa baya, gaba kuma ba a san yawan nisa ba. Kafin kwanaki kadan duk sun fadi sun mutu in banda Basharida mutane shida kawai. Baa . ma maganar dawakansu don yanzu babu ko daya. Allah cikin ikonSa sai aka yi sa’a wani dan Sarki ya Zo zai wuce ta hamadar. Ya ci karo da mutane duk sun marmace, ya ce a bincika ko akwai masu sauran shan ruwa, shi ne fa aka samu aka ceci Bashari da sauran wadanda ke tare da shi. Aka ci gaba da tafiya ana jinyar su don duk ba su san inda suke ba. Bayan sun wuce wannan hamada sai suka iso bakin wata Korama wadda ke kewaye da korayen ciyayi laya-laya. A nan suka yada zango har aka kammala jiyyar marasa lafiya, suka murmure tare da dawowa cikin hayyacinsu. Ya yi wa dan Sarkin matukar godiya tare da labarta masa dalilin fitowarsa daga gida. Dan sarki ya ce, “Ashe duk kanwar ja ce, mu ma abin da ya fito da mu ke nan, soyayya Ce. Www.bankinhausanovels.com.ng Ya fara ba Bashari labari cewa, “Sunana Amir. Ni dan Sarki me, wanda ya fada cikin wata irin matsananciyar soyayya. Mun yi alKawari ni da wannan yarinya cewa za mu yi aure bayan watanni uku, kawai sai yarinya ta Bace. Mun yi nema ni da rundunata da ‘yan leKen asirina cikin duniyar nan lungu-lungu ko za mu dace, amma ina? Mun fara yanke tsammani ke nan sai muka sami labarin cewa akwai wani shahararren Sarki a can Kasar Arewa wanda za a iya samun cikakken labari a wurinsa, don shi ma irin wannan ta faru ga ‘yarsa, ta Bata Bat. An ce wani Sarkin aljanu ne ke sace ‘ya’yan mutane kyawawa yana tafiya da su. Weannan shi ne dalilin da ya sa na karkato na fuskanto gida don in sake shiri mu tafi Kasar wancan Sarki don samo labari, daga can kuma mu wuce neman wannan barawo na ‘ya’yan mutane. Ba aljani ba ko Shaidan ne sai mun ga abin da ya ture wa buzu nadi.”
A haka ayarin Amir dan Sarki ya mika, a kwanaa tashi har suka isa garinsu. Labarin dawowarsu ya bazu ko ina a gari, mata sai rafka guda suke ta yi, babu abin da ake ji ko ina sai kade-kade da wakewake; kowa yana ta murnar cewa wani nasa ya dawo. Dan Sarki da Bashari suka wuce unguwar dan Www.bankinhausanovels.com.ng Sarki don kintsawa kafin su je gai da Sarki. Cikin lokaci suka fito suka nufi fada, in ka ga samarin nan biyu sai ka dauka wasu taurari ne saboda irin kyan da Allah Ya yi musu.
Sarki ya rungume dansa yana mai cike da murnar dawowar sa. Ya ba mahaifinsa labarin Bashari, shi kuma ya karbe shi cike da girmamawa.
Sarki ya ce, “Ku dai samarin wannan zamani al’amarinku sai ku, yanzu kowannenku ya bar yankinsu, ya shiga cikin hadarin neman yarinya? Kun san halin mata kuwa? Ko da yake yanzu dai duk a Kyale wannan zance. Shin ka yi nasara game da abin da ka fita nema?”
Yarima Amir ya ce, “A’a, Allah Ya taimaki Sarki, amma na sami labarin inda za mu iya samun labarinta. Shi ne na dawo in shirya in sake fita, an ce can kasar Arewa akwai wani Sarki wanda shi ma hakan ta faru ga ‘yarsa kuma an tabbatar cewa yana da cikakken labari. Daga wurinsa kuma sai in tsunduma duniya neman ta.” Da Sarki ya ji zancen dansa sai ya ce, “Ya kai dana, ina ji maka tsoron yawo cikin duniya, ka dai ga dan Karamin misalin abin da ya faru ga abokinka, mafi yawancin jama’‘arsa sun rasa rayukansu, kuma ga shi kai ne mutane suka sa wa ido a matsayin magajina.
HMMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG