YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM’UNA
CHAPTER 22 BY HARUNA USMAN
Www.bankinhausanovels.com.ng
MUN TSAYA
Tafiyar wannan gagarumar runduna ta su Sarkin
Www.bankinhausanovels.com.ng aljanu Ifritu da jarumi Idrisu a sararin samaniya, da a ce mutum zai ji rurinsu, to babu shakka zai hakikance cewa duniya ce za ta tashi.
Wannan runduna ba ta bata wani lokaci ko kuma wani hutawa ba saukarsu gari na farko sai suka yi fata-fata da shi. A irin wannan karon ma ko damuwa da kama aljanu ba su yi ba, kisa kawai suka yi ta aiwatarwa, kuma ba su kyale duk wani kakkarfan aljani ba. “Yan kadan da suka tsira suka ruga zuwa gari na biyu suka sanar da su irin bala’in da ke tafe.
Aljanun gari na biyu suka shirya cikin gaggawa suka fito don tunkarar abokan gaba. Kwana biyu kawai ana gwabzawa aka ragargaji wannan gari, masu tserewa suka tsere.
Abin da kawai wannan runduna ta Idrisu da Sarki Ifritu ba sa tabawa shi ne basa kashe Kananan yara da tsofaffin aljanu, wato sabanin Sarki Sham’una wanda in yana yakar wata kasa, shi har jarirai ya ke halakawa.
Kai kafin dai wasu kwanaki an lankwame garuruwan Sarki Sham’una har guda tara, wanda hakan ya sa babu makawa Sarki Sham’una ya sami labari, don a Ka’ida, masu kwatankwacin mukamin hakimai da dagatan da Sham’una ya nada don jagoranci a wadannan garuruwa dole ne sai sun yi
ZAMU TASHI
iyaka iyawarsu wurin murkushe kowane irin yaki da ya tunkaro su kafin har labari ya kai zuwa wurin Sarki, in kuwa ba haka ba, to su sun san sauran. Shi yasa ma har abin ya kai haka kafin ya sani. Kuma ma a tarihi ai baa taba taka irin wannan mataki ba sai yanzu.
Mamaki ya rufe Sarkin aljanu Sham’una jin cewa wai an nufo shi da yaki har gida, kuma ma wai maganar da ake yi har an lashe birni na tara, alhali shi yana birni na goma sha biyu ne shi da kakarsa Bakayalu.
Sham’una ya yi tunani da kyau cewa, to ai duk cikin
aljanun da ke raye babu wanda zai taba yin irin wannan mafarkin ma sai dai Sarki Ifritu, shi kuma ai yana can sarkafe a inda babu mahalukin da zai iya ceto shi. YANZU kam Sham’una ya hakikance cewa Sarki Ifritu ne tare da wani jarumi dan Adam suka kawo masa yaki. Wannan labari ya yi tsananin bakanta masa rai, hankalinsa ya tashi, ta yadda aljanin da ya kawo labarin ma bai tsira ba, don kuwa an yi rashin sa‘a, irin dundun da Sham’una ya dunkula hannu ya yi masa a baya shi ne sanadiyyar rugurgujewar bayan aljanin, bai dade ba ya mutu.
Sarki Sham’una ya shiga tunanin yadda aka yi har
Sarki Ifritu ya sami kubuta, da kuma yadda aka yi har mutum dan Adam ya iso nan da ransa. Lallai babban al’amari na tunkaro shi Ya sa aka tsaurara matakan tsaro a birni na goma, aka kai gudummawar jarumai da dakarun aljanu don kara karfafa tsaro da shirin tunkarar yakin da za a yi gobe, Ya ba da.umurnin cewa a kashe duk abokan hamayya, ba ya ma bukatar ganin su. Washegari, wato ranar da za a gwabza da aljanun birni na goma sai wani babban abin Bacin rai ya faru ga Idrisu, wato tun da safe sai ya, lura cewa dokinsa Jagora na fama da matsanancin. rashin lafiya, saboda hhaka sai ya ja shi zuwa KarKashin wata yar inuwa ya sa shi ciki yana mai rarrashin sa cewa, Jagora ka yi hakuri, kuma Allah. Ya ba ka lafiya, in Allah ‘Ya so munkusahutawa.” sa – Idrisu ya koma gefe ya yi zugum yana tunanin . yadda zai bullo wa lamarin wannan yaki, kwatsam sai ya tuna.dardumar tashinsa, sai ya yi sauri ya kwanto ta, sannan ya kwance wa Jagora sirdi ya ce,,,”Jagora kanta huta.” Ya kama shi ya kwantar da shi kamar zaiyikuka saboda.irin tausayin halin da ya ganshi aciki. Ya sake shafa kan ;~gora yana mai cewa, “Allah Ya ba ka lafiya, ka ji?”
Www.bankinhausanovels.com.ng
Daga jin irin rugugin da ke tashi daga nesa Idrisu ya hakikance cewa yanzun nan za a fara karawa. Ya warware darduma, ya dora sirdin dokinsa a kai sannan ya rike mashinsa ya rataya takobi ya ce, “Sama da ikon Allah.”
Darduma ta tashi da shi kamar tsuntsu, ya nufi fagen fama. Sarki Ifritu ya yi matukar mamakin ganin jarumi Idrisu a cikin wannan yanayi. Suka raba runduna biyu, kowanne ya ja nasa gefe. Bakaken aljanu suka yiwo musu dauki, nan take yaki ya kaure, sai wuta kawai kake gani tana tashi, ba ka jin komai sai hargowar jarumai. Irin kisan da Idrisu ya yi wa wadannan bakaken aljanu a ranar abin sai wanda ya gani, duk inda ya juya sai dai kawai a dare. Kai ya zubar da kawuna baa san iyaka ba.
A daya gefen kuma Sarki Ifritu ne ya ke tasa budawar, da ya buga kokarar nan tasa, bugawa daya sai ya zubar da aljanu sama da goma nan take su mutu, wani lokaci ma saboda kosawa hannu ya kan sa don cafko bakin aljani ya karairaya shi ya watsar, su kuma jama’a mayakan Sarki Ifritu kamar wadanda hankalinsu ya rabu da su saboda irin yadda suka sami
gangara suna ta wulakanta jama’ar Sarkin aljanu Sham’una. Wani abu wanda ya ba jarumi Idrisu da Sarki Ifritu
Www.bankinhausanovels.com.ng da jama’arsu mamaki shi ne irin yadda a can gefe wani kyakkyawan saurayin aljani ya ke ta nuna irin tasa bajinta da jaruntar wurin yakar jama’ar Sarki Sham’una. Shi wancan saurayi duk wurin babu mai irin kyansa, fuskarsa sai wani irin kyalli take yi, sannan kuma ga shi da wani irin gashi mai kyau layalaya a kansa, ga shi kakkarfa, ya yi shigar kayan yaki
irin nasu na jaruman aljanu, ba ya komai sai kisa, duk inda ya waiga sai fili, babu shakka bakaken aljanu sun yi matukar firgita da shi.
Ba a kuma san kowane ne shi ba. In ya yiwo kora, sai Idrisu ya taro, shi kuma Sarki Ifritu ya tarba.
A wurin yakin aljanu babu maganar dare ko rana, duk daya ne, kuma babu maganar hutawa. A haka sai da aka kwana uku ana hudu kafin a sami nasara a kan jama’ar wannan birni na goma na Sarki Sham’una. Aka kacaccala su aka karkashe, wadanda suka gudu cikin gari aka bi su aka kakkama aka zuba cikin ankwa.
Aka shiga cikin gari, aka gabatar da abin da baa taba yi ba; Sallah, har ma da dubban aljanu bisa dubbai cikin jam’i!
Bayan hankali ya dawo jiki duk sai aka koma ana ta yi wa juna barka da arziki. Aka duba ko ina don ganin jarumin saurayin aljanin nan mai tsananin yaki
Www.bankinhausanovels.com.ng amma babu ko alamarsa. Mamaki ya kama jarumi Idrisu har ya tambayi Sarki Ifritu cewa, “Shi kuwa wannan wane irin jarumi ne? Ana son a san ko shi wane ne amma yayi tafiyarsa?”
“Af, don wannan? Ai ko kadan kada ka damu kanka, mu aljanu haka muke, yana taimakonmu ne saboda wani dalili, ko dai shi Musulmi ne, ko kuma Sham’una ya taba zaluntarsa ko wani nasa, ka san mu aljanu sai mu yi hamayya tun ta kakanni.”
Suna gama tattaunawa sai jarumi Idrisu ya mike ya nufi bayan gari, wurin dokinsa Jagora, ya tarar dai har yanzu babu wani alamar karsashi a tattare da shi, ya shafa jikinsa yana mai yi masa addu’o’in samun lafiya. Ya dai san wannan yaki dai da wahala a yi shi da Jagora, aKalla dai a bar shi na wasu ‘yan kwanaki ya sami sauki. Ya janyo shi zuwa cikin gari don’ samar masa da inda ya dace da doki mai daraja irinsa, tun da dai yanzu gari ya Zama nasu.
Tun a hanya ya tattaro masa game-gamen sauyoyi da sassaken itatuwa wadanda zai jika masa a cikin ruwan shansa. A daidai lokacin shigowarsu gari sai ya tarar da Sarki Ifritu yana ta koKarin shirya dakaru kamar dai yadda suka shirya da jarumi Idrisu din.
TSOHUWAR aljana Bakayalu! Gara a ji labarinki da a gan ki!
In dai ba wata irin kariya daga Ubangiji Allah ba, to ko a mafarki ta ziyarci aljani ko mutum da mugun nufi babu ko shakka ba zai kwana da rai ba, saboda irin mugun alkaba’inta.
‘Tsohuwa ce wadda babu mahaluKkin da zai ce maka ga ainihin shekarunta, sai dai a lalace ta bai wa shekara dubu hudu baya. Gata ta tamuke, ta yankwane, ga wani irin farfarin gashi a duk jikinta. Tana da miyagun jajayen idanu da wasu irin hakora zako-zako, sannan kuma gashin girarta a tsaitsaye suke.
Tana da tsananin tsawo sannan kuma ga Kusumbia baya da keyarta. Wani abin mamaki kuma ma shine _ irin yadda silin gashin kanta kowanne ke da wasu irin
hakora-hakora a jikinsa. Kai duk wanda zai ba da labarinta sai dai ya takaita kawai saboda ba a taba iya
KARE mata kallo.
A matsayinta na shugabar tsafin aljanu gaba daya,
sai ta zamanto wani gunki da ake bauta wa. Kai, da Bakayalu da sharri duk ma’anarsu daya!
Kisa ba wani abu ba ne a wurinta, musamman ga duk wanda ya nuna jayayya ko kuma rashin biyayya ga sabon matsayin allantaka da ta daukar wa kanta, to tabbas kuwa za ta halaka shi, ko wane ne. Misali shi ne irin yadda ta kashe danta na cikinta, wato Kailanu, mahaifin aljana Dailanu Kawar su yarinya Nur. Dalilin kisansa a wancan lokaci shi ne rashin biyayyar da aljana Bakayalu ke ganin cewa yana nuna mata a duk lokacin da ta ba da umurnin kashe aljanu, shi kuma sai ya rika nuna mata cewa hakan bai dace ba.
A irin haka wata rana ta sa shi yin azaba tare da kashe wasu aljanu da ba su yi mata sujuda ba a lokacin da ta zo wucewa, ko da yake sun yi rantsuwa da wuta da rana cewa ba su gan ta ba ne, amma duk da haka ta ce a kashe su don zama darasi ga sauran aljanun Kasar, cewa a duk inda aljani ya ke ya rika zama cikin taka-tsantsan don tana iya wucewa ko yaushe ta ga dama.
Aljani Kailanu da aka sa yin wancan kisa sai ya nuna wa Bakayalu cewa hakan bai dace ba tun da dai
WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG sun ce ba su gan ta ba, to sai aka yi rashin sa’a tana cikin tsananin fushi a lokacin da ya riske ta da maganar, ai nan take ta aikata wani tsafi irin na ajin farko, Kailanu danta da aljanun da aka sa ya halaka din suka kone Kurmus, tokarsu ma tashi sama ta yi. Watakila irin abin nan da akan ce, ‘A tauna tsakuwa don aya ta ji tsoro.’
Daga cikin aljanun da suka fi KoKari wurin bauta mata akwai wani na hannun damanta mai suna Zirimuzi wanda wata rana ya amshi addinin Islama, kuma a dalilin sanin halinta sai ya yi gudun hijira don tsira da ransa da addininsa kamar yadda wasu suka taba yi. duk wannan ba shi ne ya fi tayarwa Bakayalu hankali game da shi ba sai lokacin da tsafinta ya nuna mata cewa a dalilin yarda da shidata yi har awancan lokacin yake da damar shiga har cikin dakin bautar da sauran aljanu ba su da ikon shiga, ya taba ganin littafin nan wanda asirin ransu ke ciki ita da jikanta Sham’‘una, kuma har ya taba littafin da hannunsa, sannan kuma ga shi yanzu ya gudu, yana kuma tare da abokan gaba! Saboda haka sai ta sa Sham‘una ya bi shi har Kasar da ya Musulunta din ya kashe shi har da Sarkin garin da sauran jama’‘a masu dumbin yawa, ba don komai ba sai don kawai Bakayalu tana kyautata zaton Zirimuzi ya taba bude
Www.bankinhausanovels.com.ng littafin, to a wurinta ko ma dai bai bude baa kashe shi kawai tunda dai hannunsa ya taba tabawa, kuma tun daga wancan lokaci ta sake wa littafin ma’ajiyar da in banda Dailanu babu mai shiga, kuma ta san ita Dailanu ba ta damu da komai ba sai harkar gabanta kawai.
‘Tabbas irin wadannan kashe-kashe da azabtarwa da Bakayalu kan yi har ga wadanda suka fi kusanci da ita kuma ba tare da bayyana wa jama’a wani dalili ba ya sa aljanu suka kara shiga taitayinsu a game da lamarinta.
Saboda tsananin sharrin wannan ‘ aljana, musamman a wancan lokaci da take ganiyar abin, babban danta ma fa ita ta halaka shi, duk da cewa shi kadai ya rage mata, wato Sarkin aljanu Damsalu, mahaifin shi kansa Sarkin aljanu‘ Sham’‘una, a lokacin Sham’unan yana Karami ita*kuma Dailanu tana ciki ba a haife ta ba. Shi kuma dalilin halakarsa shi ne wata rana ya sami aljana Bakayalu tana cikin tukukin bakin cikinta ya ce shi yana sha’awar irin halin da Musulmin aljanu ke ciki da irin dabi’unsu da sauransu. Aiba ta san lokacin data sa Kafarta ta haure shi ba, kuma a Ka’ida duk abu mai rai da tsohuwar aljanar nan ta haure da Kafarta, to kuwa nan take zai halaka, kai ko babban dutse ne, to zai fashe. Nan dai
Www.bankinhausanovels.com.ng Sarkin aljanu Damsalu ya bakunci lahira. Ko da yake ba ta taba da-na-sani baa rayuwarta sai wannan. WataKila shi ya sa duk soyayyarta ta koma kan Sarki Sham’‘una, musamman kasancewar ko kadan bai bar mugun halinta ba, kuma take matukar takatsantsan ba ta yin fushi da shi, ko me ya aikata kuwa. “Tana da wani daki na tsafi wanda takan shiga ta sake girka kanta a cikin duk shekara dari, kuma in ta shiga takan dauki tsawon kwanakin shekara ne cur _kafin ta fito, babu abin da ya isa ya kusanci dakin _tsafin matukar ta shiga cikin sa, ana ma zaton in ta shige cikin wannan daki wata duniyar can take Bulla don aiwatar da girkar. Duk lokacin da ta fito daga irin wannan tsafi, to takan fito da wata sabuwar mugunta mai tsananin gaske, shi ya sa a duk lokacin _da aka ji labarin fitowarta kowane aljani kan shiga taitayinsa don kada fushinta ya rutsa da shi. Ga shi. kuma yanzu an cinye birni na goma, _tsohuwa Bakayalu tana can wurin girka. Hankalin Sarki Sham!‘una ya yi matukar tashi don shi ma duk da kasancewarsa jikanta ba zai iya kusantar dakin ba ko da kuwa wani irin bala’i ne ke faruwa da shi, , ballantana har ya sami damar da zai kai mata kukansa. – Ana cikin haka sai Sarki Sham’una ya rika jin
Www.bankinhausanovels.com.ng Karkashin fadarsa na wani irin girgiza. Ai sai ya mike cike da farin ciki da murna don kuwa hakan alama ce da ke nuna cewa nan da wasu ‘yan sa’o’i kadan kakarsa Bakayalu za ta bayyana ta cikin dakin da takan shiga.
Haka ko aka yi.
Sham’una ya zube a gabanta yana yi mata wani irin kirari, nasu na manyan bakaken aljanu.
Aljana Bakayalu ta yi kekkewa sannan ta Kyakyace da dariya. Ta ce, “T’safi da wuta da rana su kare ka ya kai jikana dan dana Damsalu. Yaya na gan ka a haka? Wani ya saba maka ne? Wa kake so a toya shi da ransa ya kai abin da na fiso a rayuwata?”
Sham’una ya mike sannan ya sake rusunawa, ya ce mata, “Ya ke kakata wadda babu irinta a ciki da wajen duniya, ina son in sanar miki ne cewa lamari mai Karfi ya tunkaro mu, maganar da ake ciki yanzu biranena guda goma suna hannun abokan gaba, yanzu sun tunkaro birni na sha daya. Yanzu na zo neman yardarki ne in je in tarbe su a can in karairaya
su gaba daya.”
Bakayalu ta ce, “Ya kai jikana, tun da ake babu wanda ya taba cin wannan Kasa da yaki, saboda haka duk wasan Kananan yara suke yi. Wane aljani wane mutum? Irin wannan rashin kunya ai kananan aljanu
Www.bankinhausanovels.com.ng ake yi wa a kwana lafiya. Mu da ke neman tashin hankali da fitina da bala‘i ruwa a jallo balle kuma sun biyo mu har gida.
Kai Sham’‘una, shin ba ka san cewa kai ke da nasara a kan duk abin da ka tunkara ba? Nice nan fa na raine ka da kaina, kuma ina jin dadi cewa irin bakar muguntata da mugun nufina da rashin tausayi da kuma sharrina duk ka koye su ka iya. Babu shakka ka yi nisa a fagen sharri, shi ya sa ma ka ga ban cika shiri da ‘yar’uwarka Dailanu ba, don ita ina ganin alamun tausayi tattare da ita, kuma shi ya sa kakan ji ina gwaba tare da goranta mata cewa ta musulunta mana kowa ya huta don na ga kamar tana da wasu halaye irin na Musulmin aljanu.”
Bakayalu tana da wani irin madubin tsafi na Karau, duk abin da ke wakana in tana buKatar ganin sa sai dai kawai ta duba madubin. In ma ta ga dama ta cikin madubin kawai sai ta halaka abin. Ta ce, “Bari in ga su wane ne suka kawo kansu ga halaka.”
A wannan karon abin ya yi matukar ba ta mamaki, don tana dubawa sai dai ta rika ganin wani irin haske yana walkawa kawai, amma bata ganin kowa. Hakan ya faru ne a dalilin mashin da jarumi Idrisu ke dauke da shi, shi ne ke dasashe madubin nata ba taiya ganin su. Asalin burin aljana Bakayalu a lokacin shi ne a
Www.bankinhausanovels.com.ng gaban Sham’una ‘ta halaka shugabannin yakin ta ‘cikin madubi don shi maya koyi yadda ake yi. Ta yi iyaka iyawarta amma ina. Tun lokacin da aka samar da wannan madubi’ ta hariyar wani irin gagarumin gamayyar tsafi na taron matsafa, shekaru dubu biyu da dari biyu da ashirin da biyu ke nan, bai taba kasawa irin na yau ba! Ta ce, “Tashi ka tafi’na amince maka! Je ka tunkare ka cinye-makiya danyayyu da ransu! Kada ‘ka’ kuskura ka bar ko “kwaro!” F Sham‘una ya duka ya yi’ban-kwana: Ya debi ~ zaratan jarumai dubu talatin ya nufi birni na goma ‘ sha daya. Isar sa fagen fama ke da wuya sdi ya tarar ashe tuni -abokan gaba sun dade da tayar da hankalin bakaken aljanunsa na birnin. Jarumi Idrisu dan Hamidu ya takura gefen Yamma, Sarki ifritu ya kange Bangaren Gabas, shi kuma daya saurayin jarumin nan da ba a san shi ba ya toshe sashen Arewa; kakkaba: kawai sukeyi,° Ta fuskar Kudu ne Sham‘una ya shigo. Jama’arsa na ganin sa sai suka ga ai shi ke nan yaki ya kare, an ” cinye abokan gaba an gama, don ga uban gayya nan da kan sa ba sako ba. Suka labarta masa cewa tun da suke yaki ba su taba ganin yaki mai wahala da ake
Www.bankinhausanovels.com.ng samun galaba a kansu irin wannan ba.
Sham’‘una ya tambaya, “Su wane ne shugabannin yakin.”
Wani aljani da sarautarsa ke matsayin Magayakin birni na sha dayan ne ya amsa masa cewa, “Wuta da rana su kare ka, wani jarumi ne dan Adam ke shugabantarsu, yana kuma yi mana muguwar Barna, ya kashe:-mana dakaru da jarumai babu iyaka, yana kakkarya wuyaye kamar da sihiri, wannan babu shakka karawa da shi sai kai.
Kuma ran sarkin aljanu ya dade, a can gefen Gabas
Sarki Ifritu ne rike da wani gwalmi, duk bugawa daya
, aljanu kusan ashirin ke zubewa. Daga gefen Arewa akwai wani jarumi da suka zo da shi wanda babu ko alamar cewa ya yi niyyar barinmu da rai, don kuwa yanka ya ke yi kamar yana wasa.”
Zuciyar Sarki Sham’‘una ta yi kunci, fuskarsa ta sauya, gashin girarsa ya mike tsaitsaye, idanunsa suka yi jawur kamar garwashin wuta, bakinsa kuma sai wani irin tururi ke ta fita don tsananin fushi.
– Sharri da’ sake-sake suka cika zuciyarsa don tunanin irin kisan da.zai yi wa wadannan abokan gaba nasa. Sham’‘una ya ce, “Da mutumin zan fara, in cinye shi danye da ransa.”
Ya debi aljanu dubu goma daga cikin dubu talatin
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG