YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM’UNA CHAPTER 23 BY HARUNA USMAN

YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM’UNA

CHAPTER 23 BY HARUNA USMAN

Www.bankinhausanovels.com.ng

MUN TSAYA 

Sham’‘una ya tambaya, “Su wane ne shugabannin yakin.”

Wani aljani da sarautarsa ke matsayin Magayakin birni na sha dayan ne ya amsa masa cewa, “Wuta da rana su kare ka, wani jarumi ne dan Adam ke shugabantarsu, yana kuma yi mana muguwar Barna, ya kashe:-mana dakaru da jarumai babu iyaka, yana kakkarya wuyaye kamar da sihiri, wannan babu shakka karawa da shi sai kai.

Kuma ran sarkin aljanu ya dade, a can gefen Gabas

Sarki Ifritu ne rike da wani gwalmi, duk bugawa daya

, aljanu kusan ashirin ke zubewa. Daga gefen Arewa akwai wani jarumi da suka zo da shi wanda babu ko alamar cewa ya yi niyyar barinmu da rai, don kuwa yanka ya ke yi kamar yana wasa.”

Zuciyar Sarki Sham’‘una ta yi kunci, fuskarsa ta sauya, gashin girarsa ya mike tsaitsaye, idanunsa suka yi jawur kamar garwashin wuta, bakinsa kuma sai wani irin tururi ke ta fita don tsananin fushi.

– Sharri da’ sake-sake suka cika zuciyarsa don tunanin irin kisan da.zai yi wa wadannan abokan gaba nasa. Sham’‘una ya ce, “Da mutumin zan fara, in cinye shi danye da ransa.”

Ya debi aljanu dubu goma daga cikin dubu talatin

ZAMU TASHI

din da ya zo da su, sauran dubu ashirin din ya ce su auka fagen fama su kai dauki. Ya tarar da mazaje suna ta karen-batta da jarumi Idrisu, shi kuma ga mutumin naka nan a kan dardumarsa, ya kai gwauro ya kai mari yana ta tsinke wa aljanu kawuna. Shi kansa Sarki Sham’una ya yi mamaki.

Sham’una ya daka wa wadanda ke karawa da Idrisu tsawa a kan cewa su janye, ai suna lura cewa shi ne sai murna ta lullube su don sun tabbatar cewa yanzu salon yaki zai sauya, yanzu za a yi ta ta Kare. Ya ba da umurni ga dubu goman da ke tare da shi a kan cewa su kamo masa Idrisu, amma fa kada su kuskura su kashe shi, don yana buKatar cinye shi danyensa ne da ransa, yana ji yana gani.

Nan take askarawan aljanu suka yi wa Idrisu dauki, kamar za su yaki jama’a dubu dari. Da suka kusa sai suka dauki wata dabara irin ta yaki, suka fara yin wani irin jerin gwano suna zagaye shi a hankali, shi kuwa da ya farga sai ya girgiza takobinsa, sai ga takobin ya kara tsawo. Askarawan nan ko suka rufar masa, sai dai kuma ba don su jarumi Idrisu ya fito ba.

Trin jerin da suka yi a kan kuskure sai ya bai wa jarumin wata irin dama a kansu, musamman a farkofarkon karawar, don kuwa duk lokacin da ya sara ya tafi da kaifin takobin nasa a shimfide sai kawai ka ga

Www.bankinhausanovels.com.ng akalla kawunan aljanu dari a Kasa, kai a taKaice dai kafin ka gama tunani da ta’ajjubin yadda wannan lamari ke faruwa tuni cikin jama’‘ar nan ta Sarki Sham’‘una su dubu goma da ya zo da su saura ba su wuce dari shida ba wadanda suka rika ja da baya har suka koma wurin Sarkinsu.

Sarki Sham’‘una ya mari fuskarsa, ya yi wuf ya bangaje wasu daga cikin wadanda ke KoKarin rugawa din ya kutsa ta tsakanin su a fusace ya nufi wurin jarumi Idrisu, yana zuwa sai ya tsaya cak, ya ce, “Kai mutum! Daga ina? Mene ne labarinka? Kuma ma me ya sa kake yakar mu kake ta kashe mana jarumai tun

_ daga birni na farko har zuwa nan na sha daya? Me kake so, dukiya ko me?” Sai Idrisu ya ce masa, “Ai sai na san ko kai wane ne kafin in mayar maka da amsoshin tambayoyinka.” Sham’una ya ce, “Ai ba sai an gaya maka ba, da ganin Sarkin aljanu yaro ba sai an nuna maka ba.”

Sai jarumi Idrisu. dan Hamidu ya ce, “Alhamdulillahi! Yau mun gamu ke nan.  dan nema! Kai ake cewa Sham’‘una ko? Mugu jinin muguwa. Da ma musamman don kai na zo, kai da muguwar kakarka Bakayalu. Kuma ina tafe muku da albishir ne cewa ni ne nan zan salwantar da ku!”

Nan take mamaki da bakin ciki a lokaci daya suka

Www.bankinhausanovels.com.ng
lullube Sarkin aljanu Sham’una. Dalilin mamakin shi ne irin yadda tun farko wannan dan Adam din ya san sunansa, har ma da na kakarsa, lallai babu shakka wannan saurayi yana tattare da labarai. Sai Sham’una ya yi tunanin cewa, “Bari sai ya zo hannu tukuna, in yi masa tambaya kafin in halaka shi.”

Dalilin bakin cikin Sarki Sham’una kuma shi ne tun da aka haife shi ba a taba zagin sa a gabansa ba, sai ga shi yau wani saurayi, dan Adam ma, yana surfa masa, ba kunya ba tsoro. Ya tuna irin ikonsa da jaruntarsa da irin yadda dukkan aljanu ke tsoro har wasunsu ke bauta masa, sai ga shi yau mutum ne har babban birninsa da yaki, har ma da zagin sa shi da uwar matsafa Bakayalu.

A fusace Sarkin aljanu ya daga hannayensa sama kamar zai karbi wani abu, kawai sai ga wani irin takobi ma‘abocin tsawo, girma da fadi a hannunsa, wanda za a iya siffantawa da gaya-wa-jini-na-wuce, amma irin nasu na aljanu, a daya hannun kumasai ga wata irin garkuwa wanda akalla sai an sami Karfafan aljanu guda dari za su iya daga ta, ya nufi Idrisu yana tafiya yana wani irin Karaji mai ban tsoro, yana ihu da

hargowa irin na jarumin da ke ji da kansa. Jama’ar Sham’una da suka ga haka sai suka sakankance cewa yanzu kam yaki ya Kare don ko zai kamo Idrisu ne

Www.bankinhausanovels.com.ng kamar agwagwa.

Ganin Sarki Sham’‘una ya tunkaro shi sai ya zama jirace da shi. Ya girgiza takobinsa a daidai lokacin da shi kansa ya yi wata irin budawa, shi kansa a lokacin sai da ya ji takobinsa ya dan Kara nauyi, wanda hakan ya sake tabbatar masa cewa lallai wannan karo na musamman ne. °

In dai ba a manta ba, daga cikin horon da jarumi Idrisu ya samu a wurin Shaihi Ibrahim a zaman da suka yi akwai yin’yaki ba-tare da garkuwa ba, wato wata baiwa:wadda Shaihin ne: kawai ya fi kowa dacewa da ita a ciki da wajen duniya, sai kuma yanzu shi Idrisu

Karar haduwar takubban Sarkin aljanu Sham’una da jarumi Idrisu ta sanya duk wanda ke fagen sai da hankalinsa’ ya -dawo wurin’ kafin a ci gaba da gwabzawa. A dalilin haduwar takubban ne fa sai da wata irin wuta ta yi tartsatsi ta tashi sama ta yadda su ma kansu jaruman wato Idrisu da Sham’una sai da suka yi baya kafin kowannensu ya sake gyarawa don sake bugawa. Www.bankinhausanovels.com.ng

Baudiya da kariya wasu abubuwa ne da saurinsu ya kama hanyar na walkiya a-wurin mai kallon wannan karawa ta Sarki Sham’‘una da jarumi Idrisu; don irin tsananin kwarewar jaruman. Kai abin.dai kamar’a

Www.bankinhausanovels.com.ng labari.

Yawan bugawar da ake yi ta sa har takobin da ke hannun Sarki Sham’una ya fara lauyewa. Hakan ya yi matukar ba shi mamaki, da tafiya ta yi tafiya sai ya tabbatar wa kansa cewa yanzu takobin ba shi da sauran Karfin da za a ci gaba da gwabzawa da shi, saboda haka sai ya wurgar da shi, ya daga hannu sai ga wani mulmulallen bakin Karfe mai wasu irin hakora, ya riKa kai wa Idrisu bugu da shi jarumin yana gocewa, can da Idrisu ya sami sa’a sai kawai ya sa kaifin takobinsa ya sare tsakiyar mulmulallen Karfen, ai nan take ya watse.

A irin haka Sarki Sham’una yana kawo miyagun makamai Idrisu yana lalatawa har sai da ya kawo guda tamanin. Abin da kawai bai lalace a hannun Sham’una ba tun fara gwabzawarsu da jarumi Idrisu ita ce garkuwa.

Akwai wata babbar bishiya a kusa da inda gumurzun nasu ya kai su, kuma a takaicen takaitawa itaciyar ta kai shekara dari biyar a wurin, ai kawai sai Sarkin aljanu ya sa hannu ya fisgo ta don yin bulala da ita, a daidai lokacin da jarumi Idrisu ya bi shi ya daga takobi ya kai masa sara, babu shakka Sham’una ya isa jarumi, don irin gocewar da ya yi akwai matukar mamaki, sai kawai ya kare saran da wannan

Www.bankinhausanovels.com.ng itaciya da kuma garkuwarsa.

Irin dirar mikiyar da jarumi Idrisu ya yi masa da sara shi ne karshen labarin wannan itaciya da kuma garkuwa ta Sarki Sham’una, don ita wannan shahararriyar garkuwa rabewa biyu ta yi.

Jikin Sarki Sham’una ya yi matukar sanyi, kuma

wannan abin mamaki ya sa ya mike ya dafe keya a guje. Jama’arsa da ke gefe suna kallon yadda fafatawar ke kasancewa ba su bari ya Karaso inda suke ba, su ma sai suka juya a guje, suka fuskanci babban birninsu na goma sha biyu. Sauran aljanun da ke cikin fagen fama kuwa da ma azabar Sarki Ifritu da na wancan matashin jarumi ta gallabe su, saboda haka ganin shi kansa uban tafiyar ya ranta a na kare sai su ma suka ce Kafa me na ci ban ba ki ba, suka juya karce suka rufawa jagoransu baya. Wato dai suka bar fagen faman da kuma birninsu na sha daya a hannun abokan gaba.

Suka shige birninsu na goma sha biyu suka rufe shi bam yadda ko allura ba za ta iya shiga ba.

Ko bin sawunsu ba a yi ba, an ci wannan birni ke nan, ya shiga hannu. Aka yanke shawarar kada a tsaya wani Bata lokaci kawai, a nufi birni na sha biyu cikin natsuwa ana tafiya ana sake kintsawa da hutawa, wato birnin Sham’una shi da kakarsa Bakayalu, birni

Www.bankinhausanovels.com.ng na Karshe, don ayi ta ta kare. SARKIN aljanu Sham’una dan Damsalu ya isa wurin kakarsa Bakayalu cikin wani irin tashin hankali da bai taba mafarkin tsintar kansa a ciki ba. Ya fadi a gabanta ya yi mata sujuda. Duba daya kawai ta yi masa ta fahimcei irin halin da ya ke ciki.. Ya ce, “Ya ke kakata ke ce kika raine ni, kika koya mini tsafi da muguntar da nake cikin sa, hasali ma ke ce kika kai hi ga wannan daukaka ta sarautar aljanu da duk duniya da wajenta kowa ke shakka ta, to yau tabbas ga abin da ke neman fin Karfina, dole in ba ki sa hannu ba, to za mu tozarta.”. -‘ Ya kara da ce mata, “Makiya suna nan kan hanyarsu ta zuwa babban birninmu. Mun buga ni da wancan jarumi dan Adam din kuma ba yadda ban bullo masa ba amma abin ya gagara. Duk tsawon lokacin da muka dauka muna gumurzu da shi babu wani labari, sai shi ne ma ke neman kunyata ni, ko kuma ma in-ce ya kunyata ni din, don ban taba juyawa a fagen fama ba sai wannan karon! Wani irin takobi ya ke da shi mai tsananin ban mamaki. A gaskiya na hadu da jarumai ban san iyaka ba wadanda na karairaya tare da turmusa hancinsu,

Www.bankinhausanovels.com.ng na shayar da su dacin mutuwa, amma ban taba haduwa da jarumin da na ji cewa wai ina fada ne ba, jin banda Sarki Ifritu wanda muka taba daukar lokacin da gaba daya bai wuce sa‘o’i uku da rabi muna karawa kafin akarshe insami galabarsaba. =

Wani abin mamaki ma game da wannan jarumi dan Adam shi ne irin yadda har ya san sunanki da sunana. Wai ma har yana cewa musamman don mu yazo.” .
‘Da tsohuwa Bakayalu ta ji wannan bayani daga ‘bakin jikanta sai ta-yi shiru tare da tsunduma cikin tunani, san-nan ta ce, “Duk yadda: aka yi wani ya ‘ munafunce mu ke nan, an fita da bakin littafi zuwa ga hannun makiya. ‘ Sham’una-ya tambaya, “Kaka, -me. ya. hada matsalarmu da wani bakin littafi can?” Bakayalu ta ce, “Dangantaka ta kut-da-kut kuwa. In‘ba ka manta ba na taba sanar da kai shekaru masu “yawa da suka wuce cewa asirin rayuwarka na wurina ‘ kuma babu wanda zaitaba iyakashekako? Sham’una ya amsa, “E na tuna kwarai, ai ba zan ’ taba manta irin wancan albishir ba, shi ne ma dalilin “da ya sa na fara tunkatar wadanda nake jin tsoro ada, har ya zo ya kasance babu wanda nake tsoro a cikin tarayyar aljanu da mutane sai dai ni ake jin tsoro.” Www.bankinhausanovels.com.ng

Sai Bakayalu ta ce, “To asirin gagarar taka da rayuwarmu ni da kai gaba daya suna cikin littafin ne.

A kansa ne na taba sa ka je ka nemi aljani Ziri-muzi ka kashe shi, lokacin da na yi zaton ya taba bude littafin, a wancan lokacin ba ka san dalilin ba amma na baka umurnin cewa in ka je ka zagaye garin da ya shiga ka kashe shi taredawadanda suka ba shi masauki.”

Bakayalu ta ci gaba da cewa, “Abin da ban fada maka baa wancan lokaci shi ne, wurin koKarin mayar da kai gagararre, da kuma kare rayuwarka yadda babu wanda zai iya samun nasara a kanka ballantana wai har ya kashe ka. Mun yi amfani da wani irin tsafi ne ajin farko daga cikin tsafuffukan farkon zamani, irin tsafin da yanzu babu irinsa ya bace sai dai tarihi.

Shi ne na sami labari daga cikin kakannina cewa matsafi guda daya tak da ya rage da irin wancan tsafi a wancan zamani wato aljani Jamboro kasancewar ba shi da magaji sai ya dauke bayanan tsafin ya kai wata duniya can mai wahalar zuwa ya Boye, wanda kuma zuwa waccan duniya sai matsafin aljanin da ya isa tukuna. Ni ma nan da ka gan ni sa’ar gaske na samu

har na sami shiga waccan duniyar a cikin irin tafiyetafiyen da na rika yi. Ya kai jikana, ka sani cewa shekara daya da wata -_ –

Www.bankinhausanovels.com.ng takwas na yi ina lalube-lalube har na yi nasarar tono wanda ya Boye, ko da yake a karkashin haka saura kadan ni ma in halaka, kai hasali ma ban taba cin bakar wahala kamar ta samo wancan tsafi ba.

Ya kai Sham’‘una, lokacin da na gamsu da biyayyarka shi ne na hada maka tsafin, har ka zo ka gagara. Saboda kuma tsananin Kaunar da nake yi maka na sadaukantar da raina a matsayin fansa ga tsafin.

Sai Sham’‘una ya ce mata, “Ke ma kaka akwai naki kuskuren! Ta yaya za a aikata irin wannan ganganci haka? Yanzu ya kamata ace Sarkin aljanu mai yawan makiya a rubuta wani sirri nasa a ajiye haka kawai ballantana kuma har asirin rayuwata?

Sai Bakayalu ta ce, “Abin da ka sani ne wanda kuma ba sai na sake maimaita maka ba cewa duk, kuma kowane irin tsafi yana dauke da wata illa ko cutarwa Boyayyiya ko bayyananniya ko kuma duk biyun ga wanda ya aikata shi kansa. To ai bayyanar bakin littafin ne abin da ke nuna cewa tsafin ya hadu, kuma salwantar da shi babban hadari ne, duk da cewa yana Kunshe da bayanin abin da zai kawo karshen tsafin.

A cikin littafin ne aka yi bayanin wasu miyagun makamai da suka gagari kowane irin tsafi, har ma aka

Www.bankinhausanovels.com.ng siffanta rijiyar da suke a cikin duniyar ‘yan Adam, kuma sai dan Adam din ne kawai zai iya fitar da su ya mallakesu to.kuma duk wanda ya mallakesu to shi ma ya zama gagararre ke nan, shi ya sa da ka ce mini daya daga cikin shugabannin yakin dan Adam ne ka gaina tunani.  . A wadancan shekaru na farkon hada tsafin, ni da Kaina na rika zuwa dajin da makaman suke ina tsaron
rijiyar, amma da na ga alamar babu komai sai na , daina zuwa, don akwai wahala ko da a mafarki wani mahaluki ya taba sanin irin sarkakiyar matakin da za – a taka wurin.halaka mu, shi,ya sa na ce babu shakka ; wani ya munafunce mu ya fita da wancan bakin littafi.A gaggauce tsohuwa Bakayalu ta nufi dakinta cikin taskar da take ajiye kayayyakinta mafi muhimmanci ta. bankada .inda-:ta ajiye littafin sai kuwa ta gan shi ‘kamar ba,a;taba.motsa shi daga, wurin ba, saboda – haka sai ta dauko shi.ta fito ta sami Sarkin aljanu Sham ‘una a inda ta bar,shi tun dazu a durKushe. Ta . Nuna tare da ce masa, “Ashe.muna neman tayar da hankalinmu, bakin littafi dai yana nan a inda na bar shi, kuma ina zaton babu wanda ya taba shi. Sai ta gabatar da waniirin sihiri, ai nan take sai ga taswirar fuskar Dailanu a jikin littafi,,, . . Bakayalu ta ce, “Babu shakkayari yarnan Dailanu
ce ta taba littafin nan.” Saboda haka sai ta fita ta sa aka kamo Dailanu aka fara azabtar da ita da wata irin ukuba mai tsananin gaske.

Bakayalu ta zo tana tuhumar Dailanu a game da fita da littafi, ta ce, “Ke ce ki ka fita da wannan littafi, don ga taswirar fuskarki nan a jikinsa.”

Aljana Dailanu ta yi wani irin marairaicewa ta ce, “Ya ke kakata, kin sa ana ta azabtar da ni alhali ban san maganar fita da littafi daga cikin dakinki ba. Kuma maganar ganin fuskata kada ki manta ni kadai ce ke shiga ko’ina a dakinki. Kuma fa ba a dade ba da ki ka umurce ni a kan cewa in share tare da goge ko ina a dakin, to yaya za a yi in share ko kuma goge wani abu ba tare da na taba shi ba?”

Aljana Dailanu ta ci gaba da bayani ga kakarta Bakayalu cewa, “Littafi dai yana nan, duk da cewa ba a fada min abin da aka Boye a cikinsa wanda ya Bace ba. To ko ma dai mene ne kada fa mu manta cewa masifar yaki ne ta tunkaro mu gaba daya, kuma a matsayina na jinin gidan nan ina ganin wannan ba lokacin da za a tsaya zargi ba ne, don wannan masifa in aka yi sakaci za ta yi wa gidan sarautar nan muguwar Barna gaba daya.”

Jin wannan zance fa sai tsohuwa Bakayalu ta sa aka

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *