YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM’UNA
CHAPTER 4 BY HARUNA USMAN
Www.bankinhausanovels.com.ng
A JIYA MUN TSAYA
Sarkin aljanu Sham’una ya ci gaba da zuwa har ranar Juma’a. A ranar Asabar wasu daga cikin Musulmin ‘yan matan nan suna zaune suna karanta wata sura daga cikin AlKur’ani mai girma, sai ga aljana Dailanu. Tana isowa ta ji karatun nan sai hankalinta ya tashi, ta rude jikinta ya yi sanyi, ta ji ba abin da take so kamar karatun, saboda haka sai ta sami wuri ta koma gefe ta zauna har sai da suka gama. Kafin su kammala sai ga aljana tana hawaye saboda irin firgicin da karatun ya jefa mata. Suna gamawa sai suka ga Dailanu ba kamar kullum ba,
ZAMU TASHI
don hankalinta a tashe ya ke har yadda su ma sai da suka ji tsoro, suna zaton ko wani abu ya faru ne. Yarinya Nur ta tambaye ta, “Ya ke wannan kyakkyawar yarinya, yau mene ne lamarinki muka gan ki cikin wani irin hali da ba mu taba ganin ki a cikin irin sa ba, kuma na bacin rai. Ko kuwa mun bata miki rai ne? To a gaskiya ba da niyyarmu ba ne, sai ki yafe mu Sarauniyar matan aljanu.” Da aljana ta ji zancen Kawarta Nur sai ta rungume ta, tana hawaye ta ce, “Ya ke Nur, babu wani abu da kuka yi mini na baci, wato abin da ya sa ni cikin damuwa shi ne lokacin da na iso nan na ji kuna wani abu kamar waka amma kuma na tabbatar ba waka ba ce, na jima cikin jikina cewa lallai gargadi ne mai ban mamaki, shi ne na ji na dimauce,
hankalina na ji ba wani abu da nake so kamar wannan abin da kuke yi.”Sai Nur ta ce mata, “Ya ke Dailanu, wannan abu da kika zo kika tarar muna yi shi ne muke kira karatun Alkur’ani, kuma shi ne addininmu, addinin gaskiya. Ya ke Dailanu, wannan Alkur’ani da muke karantawa babu abin da babu a cikin sa na shiriya, amma fa sai wanda Allah Ya shiryar ne kawai zai yarda da shi. Naji rannan kina yin rantsuwa da rana, to rana ita kanta baiwa ce ta Allah, ba ta da ikon kanta har sai an ba ta umurni, haka nan wata da taurari, wuta da ruwa, duwatsu da mu kanmu mutane har da ku aljanu, duk muna Karkashin ikon Allah din ne wanda Ya samar da mu tun asali.” Bayan ta kammala yi mata wannan bayani da wasu bayanan masu karfafa na farko sai ta ce mata, “Ina ba ki shawarar ki shigo cikin addinin Musulunci, ki bar bautar rana.” Ba tare da bata wani lokaci ba aljana Dailanu ta karbi kalmar shahada ta musulunta, amma ta ce ba za ta taba yarda kakarta Bakayalu ta sani ba, don in har ta sani, to ta shiga uku ke nan. Aljana Dailanu ta ce, “toni ma ina so in koyi wannan karatu.”Sai Nur ta ba ta amsa da cewa, “Ai dama yin wannan karatu ga Musulmi dole ne, don in babu karatun ai babu yadda za ki san addinin naki sosai.” Daga nan sai Dailanu ta bude wani dan karamin bakin akwati ta dauko wani bakin kundi ta cewa su Nur, “Wannan shi ne littafin da labarin ran Sarkin aljanu Sham’una ke ciki. Ina so ku juyi abin da ke ciki gaba daya don in zan koma in tafi da shi Sai dai ku yi hakuri ina tsoron kada wata ta taba shi da tafin hannunta, kuma ni na san dalilin da ya sa nace haka, saboda haka zan rika dago muku shafukansa daya bayan daya kuna juyewa, in kun lura ma littafin ba Www.bankinhausanovels.com.ng shi da yawan shafuka, ko mutum biyu ma kadai za su iya.” Nan da nan wasu daga cikin ‘yan matan suka dauko takardu da alkaluma, suka juye shi kaf! Dailanu ta mayar da shi ta hada cif! Sannan ta sa shi cikin akwatinsa. Lokacin tafiyarta ya yi suka yi sallama a kan cewa in ta zo makon gobe, za su shawarta a kan yadda za su bullo wa bayanin da ke cikin kundin. Www.bankinhausanovels.com.ng TAFIYAR aljana Dailanu ke da wuya, sai ‘yan matan nan suka shirya shafukan da suka juye tsaf! Daga nan sai Nur ta dukufa wurin nazarin bayanan da aka rubuta don suna da sarkakiya da wahalar fahimta, amma saboda irin zurfin ilminta bayan wani lokaci sai ta fara yi musu bayanin abin da ta iya ganewa. Tace, “Muddin ana so a kashe Sham’una, to da farko sai an kashe kakarsa mai rayuka biyu, wato bayan an kashe ran farko na cikin jikinta sai kuma an kashe na biyu dake matsayin wata irin hatsabibiyar macijiya mai mazauni a wani kogon dutsen da ke cikin wasu manyan duwatsu a bayan duniya. Kuma an nuna cewa kuskure ne babba yin kisa na biyu baa cikin kogon dutsen ba. Bayan samun nasara a kan wannan sannan sai a fafata da shi kansa Sham’una, in an sami nasara a kashe shi. In baa aikata haka ba, to aljani Sham‘una dan Damsalu ba zai taba halaka ba. SO Dole sai an bi ta hanyar da aka tsara sannan za a iya yin nasara, in kuwa aka bi ta wata hanya, to kuwa tabbas za a halaka.” Nur ta gyara zama sannan ta ci gaba da bayani, “Dole ne wanda zai dauki wannan kasada ya sami abubuwa biyar masu ban mamaki. Na farko da na biyu kuwa su ne shahararren takobin nan da kuma mashi wadanda babu mai iya daga su sai mai su, na uku sirdin zinare, na hudu darduma mai tashi sama. Cikon na biyar din kuwa shi ne dole mai irin wannan Kalubale a gabansa ya san cewa ba ya yiwuwa a kan gama-garin doki, aa, dole sai an sami zakakuri kuma ingarman doki. Yadda za a iya samun wadancan abubuwa hudu kuwa shi ne sai an shiga cikin duniyar mutane, a tsakiyar wani Kungurmin daji da ake kira Surkukin-gagara wanda ba a taba samun mutumin da ya ratsa ta cikin sa ya fito da ransa ba. A cikin dajin akwai wata rijiya wadda a cikinta wadannan kayayyaki na ban mamaki suke. Yadda za a sami wadannan kaya daga cikin rijiyar kuwa shi ne, akwai wani dan Karamin rafia kusa da ita, a kullum za a debi ruwan cikin sa tulu goma daidai ana zubawa a cikin rijiyar har na tsawon kwanakin shekara. A ranar da aka kammala ne rijiyar za ta cika har baki ta yiwo ambaliya. Ruwa zai fito da sirdin doki na zinare da darduma a kan sirdin, nannade cikin Shi dardumar Www.bankinhausanovels.com.ng akwai takobi da mashin da ake magana. Wadannan su ne kayan fadan da kawai za su iya kashe Sarkin aljanu da kurwarsa, kuma wannan sirdi shi ne sirdin dokin jarumin. Sai dai kuma duk wanda zai isa wurin Sarkin aljanu da wancan nufi na kisa, to kafin ya isa tabbas zai sha gwagwarmaya mai tsanani, zai yi karo da dodanni da aljanu da mutane, kuma dole hanya daya ce tak zai bi don babu wata hanya sai ita.” Yarinya Nur dai ta dakatar da wannan bayani tare da cewa sauran ‘yan matan, “Lallai wannan mugun aljani ransa zai yi wuyar kashewa, amma in Allah Yasozamu sami nasaraakansa.” A wannan lokaci dare ya riga ya yi, sai suka tsayar da shawara a kan cewa su bari sai ranar Asabar in Dailanu ta zo, ‘yata Nur zata ba da sako a kawo mini. Wannan makon ma haka ta kasance, Sarkin aljanu ya rika zuwa kamar yadda ya saba har zuwa ranar Juma’ a da ya yi sallama da su sai Lahadi ke nan. Gari na wayewa Www.bankinhausanovels.com.ng ga aljana Dailanu cikin farin ciki da walwala, suka gaisa tare da sanar da ita cewa sun fahimci duk abin da suka juya a wancan makon, amma sun fahimci cewa lallai abin zai yi wuyar gasken-gaske. Dailanu tace, “Ai dama na riga na fada muku.” Sai Nur ta ce mata, “Ina da wata shawara dake Dailanu wadda ina fata za ki taimaka.” Aljana Dailanu ta ce, “Ya ke aminiyata Nur, ai kamar yadda na ce ne tun tuni, kuma ina kara maimaitawa yanzu cewa ko zan rasa raina ne, to na yi alkawarin zan taimake ku. Kuma ai ni yanzu sunana aljana ce kurum, amma ai na zama daya da ku, kuma mu aljanu ba ma karya alkawarin aminanmu.” “Yata Nur ta ce mata, “Wata shawara ce muka yanke cewa wannan bayani na rayuwar Sham’una, zan rubuta takarda ki hada da shi ki kai wa mahaifina. Daga nan in kin je sai ki yi masa bayanin kanki. Ki je masa cikin siffar mutane ne. Zan sanar da ke sunan garinmu da misalin gidanmu. In kuma kin gan shi, to ina so ki roke shi ya karantar da ke karatun Alkur’ani mai tsarki da kuma ilmin addinin Islama, don kin san shi addinin Musulunci ba a yin sa da jahilci. Kuma idan kin amince ya ke Dailanu, ina so ki je gefen dajin nan, ki gina wa mahaifina Katon daki da kuma wani karami kusa da shi. Shi wannan daki a ciki za ki riKa koyon karatu, kuma ina so ki rika yi masa abinci safe da yamma. Sauran bayani kuma za ki ji a wurin mahaifin nawa. Kuma zan sa Sarkin aljanu ya yi lambu kusa da dakunan inda zan rika zuwa kowane dare har tsawon shekara daya daga ranar da aka sami jarumin da muke kyautata zaton cewa zai iya, don mu rika debe masa kewa.” Aljana Www.bankinhausanovels.com.ng Dailanu ta ce, “An gama ya ke Nur.” Dattijo ya bude wani littafi ya janyo wata takarda yadda shi ma kansa Idrisu yana iya kallon abin da aka rubuta. Shaihi ya ce, “Yauwa Idrisu, ga takardar da ta rubuta din. T’ace, “Zuwa ga mahaifina wanda nake kauna har abada, kuma wanda nake girmamawa fiye da duk wanda ke numfashi. Ya wanda haskensa shi ne nawa, ina fata ka yi mini gafara saboda rashin gani na wanda na tabbatar kana cikin juyayi, kuma na tabbata za ka yi mamaki ya kai mahaifina mai girma, irin ilmin da ka karantar da ni, da kuma irin tarbiyyar da ka yi mini, kai kanka ka san ni ba irin ‘ya’yan da kan gudu su bar iyayensu ba ne ba tare da wani kwakkwaran dalili na Shari’a ba. Kaddara ce ta faru da ni, amma ina so ka kwantar da hankalinka don ina nan lafiya lau. Ya babana mai daraja, na tabbata kuyanginka da muke wasa da su sun ba ka labari cewa ba su ganni ba bayan farkawarsu daga barci mai nauyin da ya dauke mu gaba daya, to ni dai na farka ne kawai na gan ni a cikin wani makeken gida wanda akwai wahala a sami dan Adam da ya taba ganin mai kyansa, kuma shi wannan gida yana kan wani tsibiri ne daga cikin uku mafi girma da ke bayan duniya. Dalilin zuwana wannan gida shi ne wani mugun Sarkin aljanu né mai suna Sham’una dan Sarkin aljanu Damsalu ya dauko ni ya kawo ni. Ba ni kadai ya sato ba, akwai sauran wasu hamsin duk ‘ya’yan mutane, kuma ‘yan mata. Ya nuna cewa ni ya ke so, shi ya sa ma wai ya kawo mini sauran ‘yan matan don wai su debe mini kewa. Da muka fahimci haka sai muka kwantar da hankalinmu don mu sami labarinsa. Babu dama in zo da kaina wurinka, don in Sham’una ya sani, to duk zai halaka mu. Shi ya sa na aiko wannan baiwar Allah don ta kawo maka wannan takarda. Www.bankinhausanovels.com.ng ita wannan aljana kawarmu ce, sunanta Dailanu, ita da Sarkin aljanu Sham’una dan wa da ‘yar kani suke. Ita ma wannan aljani yayi mata wulakanci bayan ya karya alkawau A dalilinsa ta kashe ‘ya’yan mutane da yawa ba tare da hakkinsu ba, mu ma Allah ne Ya yi nufin kwananmu na gaba, don kuwa har ta yi niyyar halaka mu, amma daga baya ta zama kawarmu har ma ta Musulunta. Sannan kuma dai ita ce ta kawo mana wannan bayani na asirin ran Sarkin aljanu Sham’una. Ta yi mini alkawarin za ta kai ka dajin da aka ambata ta gina maka dakuna babu nisa sosai da rijiyar da aka ambata, sannan kuma za ta rika kawo maka abinci sau biyu a kowace rana, kuma tana son yin karatu a wurinka don sanin addinin Islama sosai. Zan bukaci Sarkin aljanu ya yi mini wani babban lambu a cikin dajin don a rika kawo mu a kowane dare muna shakatawa a ciki har zuwa lokacin da bukata za ta biya, kuma na tabbata zai yarda. Www.bankinhausanovels.com.ng Za ka rika samun labarina daga wurin aljana Dailanu. Ka huta lafiya, ni ce ‘yarka Nur. Dattijo ya ci gaba da ba saurayi Idrisu labari cewa, “Lokacin da ‘yata ta kammala rubuta wannan wasika, sai ta ba aljana. Ran nan Dailanu ba ta bari yamma ta yi ba, kuma abin ka da aljan, da Magriba na yi Sallah ina cikin turakata ina jiran lokacin Sallar Isha’i sai na ji wani irin kamshin turare wanda ban taba jin irin sa ba, can sai na ji muryar mace ta ce, “Assalamu alaikum.” Nan da nan sai na amsa, sai na ga wani hayaki ja, sai ga shi wannan hayakin ya koma wata mace kyakkyawa, sai na ji gabana ya fadi, na tsorata, amma kuma na tuna cewa da sallama ta fara, sai na sami natsuwa. Duk da haka dai sai da na yi addu’o’’i irin na neman tsari kafin yarinyar nan ta zauna kusa da buzuna ta gai da ni cikin ladabi da girmamawa, sannan ta ce, “Ko kai ne Ibrahim dan Yahaya mahaifin Nur?” Nan da nan na amsa cewa ni ne, “Mene ne labarinki?” Sai ta miko mini takarda. Ina budewa sai na ji gabana ya fadi ras a dalilin ganin rubutun ‘yata. Na fara karanta takarda ina hawaye wanda ya samu a sanadin begen ‘yata da kuma farin cikin cewa tana raye. Na karanta takardar tun Www.bankinhausanovels.com.ng daga farko har Karshe. Bayan kammalawa, sai na gode wa Allah Madaukakin Sarki saboda amsar rokona da Ya yi a game da gudan jinin zuciyata. Aljana ta miko mini bayanin ran Sarkin aljanu na amsa. Bayan mun gaisa ta yi mini alKawarin za ta dawo bayan kwana uku, don tana so ta je ta gina dakin nan a wannan dajin kusa da rijiyar da ke cikin bayani, na ce mata daidai ne. Ta tafi ni kuma na ci gaba da nazarin bayanin da ta kawo din wanda kuma na fahimta daidai gwargwado. Cikin kwanaki uku na shirya tsaf, na hada litattafaina Kiriga Kiriga, wadanda zan taho da su wannan daji. Bayan kwana ukun da La’asar sai ga yarinyar aljanar nan ta iso, ta ce ta gama gina dakina, kuma kusa da rijiya, duk abin da nake bukata yana ciki. Sai na tambaye ta ko za a iya kai mini litattafaina can? Ta ce, “Yanzu kuwa ya Babana.” Kafin ka ce mene ne wannan littattafaina sun Bace tare da aljana, bayan kamar rabin sa’a sai ga ta ta dawo, ta ce mini, “Mu tafi.” Tace in runtse idanuna, na runtse, sai na ji an yi sama da ni, kafin lokaci kadan sai na ji an sauke ni a bakin Kofar wannan daki. Na gan shi kamar yadda kake ganin sa, an dan kewaye shi saboda namun daji. Na shiga ciki sai na tarar da wurin ashe Katon daki ne, babu abin da babu a ciki, kuma ga littattafaina nan an shirya su gwanin ban sha‘awa. Ya kai Idrisu, bayan an kawo ni wannan daji, sai ya kasance wani lokaci in kwana nan wani lokaci kuma in sa almajirata Dailanu ta kai ni gida in kwana. Kumaa kullum sai Dailanu ta zo ta dauki karatu. A takaice dai dalilin zuwana wannan daji shi ne don in sanar da mai rabo asirin wannan rijiya, don in mutum bai san asirin ba, to har abada ba zai gane komai ba. Wata ranar Lahadi, ana sauran ‘yan kwanaki kadan ka iso nan, kuma kamar dai yadda aka saba Sarkin aljanu Sham‘una ya tafi wurin ‘yan matansa, sai ya tarar kowaccensu ta yi wata irin kwalliya ta musamman. Www.bankinhausanovels.com.ng “Yata Nur kuwa a ranar in ka gan ta sai ka dauka wata ne dan daren goma sha hudu a cikin taurari. Sham’una ya samu suna ta kade-kade da wake-wake da wata irin rawa da rausaya mai daukar hankalin duk wanda ya gan su. Suna yi suna sa sunansa a ciki. Tarar da su cikin wannan hali ya sa shi barkewa da rawa tare da su. In ya yi juyi saboda tsananin jin nishadi da murna, sai ya daga hannunsa sama, nan take ya cika da lu’ulu’u da jauhari da yakutu da azurfa da zinare, ya watsa cikin su, su kuma sai su yi ta warwaso da tureneniya shi kuma yana jin dadi don ‘yan mata kyawawa suna kokawaa gabansa. Bayan sun gama nishadinsu sun gaji, sai suka zauna suka kewaye Sarkin aljanu, shi kuma yana ce musu, “Ya ku wadannan ‘yan mata, tun da nake babu wani abu da ya taba damu na. Ga shi ina da mulki, ban taba rasa komai ba, ga shi kuma ni Kasaitaccen jarumi ne, aljanu ma su kan su bayan tsoro na da suke ji har bauta mini suke yi, tun da na karya Ifritu na wargaza rundunarsa, na kashe masa jarumai da dakaru, saboda haka ni ne Sarkin aljanu na duk duniya. Ba na tsoron komai, kuma ba na tsoron kowa, amma duk daular nan da nake ciki, ban taba samun abin da nake jin dadi da murna da sha’awa ba kamar in zo wurinku.” Da ya gama labarinsa sai yarinya Nur ta matsa kusa Www.bankinhausanovels.com.ng da shi ta ce, “Ya kai wannan kyakkyawan Sarki mai Karfi, babu shakka ni na amince fiye da kowa cewa babu mahalukin da ya isa a karan kansa ya karya ka, kuma ya kai Sham’una, muna jin dadin kasancewar ka tare da mu. Sai dai kuma akwai abin da nake son in fada maka, cewa ka san mu mutane ne, kuma al’adarmu da ku ta sha bamban. Wani abu ne ya dame mu, muna fata kuma za ka share mana hawaye.” Jin wannan zance sai Sarkin aljanu ya yi zumbur yace, “Ya ke yarinya mai kyau, mene ne bukatarku, ko kuna so in kai ku duniyar wata ne ku yi kallo?” Nur ta amsa, “A’a, ko kadan ba muna son zuwa duniyar wata ba ne, sai dai gani muka yi kasancewar kana tafiya ka bar mu, in dare ya yi kuma begen ka yakan hana mu sukuni, shi ne sai muka ga cewa maimakon mu yi ta zama a wannan wuri wanda ke sa mana shauki da kewar ka, sai muka yanke shawarar cewa akwai wani daji wanda ake kira Surkukin-gagara can cikin duniya da muka taba jin labarin cewa babu wani dan Adam da ya taba zuwa wurin sai dai namun daji kawai. Shi ne muke son ka sa a yi mana lambu a wurin, a kullum dare a kai mu can mu yi wasanninmu, in kuma lokacin barci ya yi a dawo da mu, amma fa sai in Sarki ya amince.” Yana jin wannan zance na Nur sai ya kyalkyace da Www.bankinhausanovels.com.ng dariya, ya ce, “Ku kuwa mutane kukan ba ni dariya, abin da bai taka kara ya karya ba, sai ku dauke shi wani babban lamari. Bayan wannan kuma babu wani abu da kuke bukata?” Ta ce, “A’a bayan wannan babu wani abu da muke buKata, da ma ai mu babbar buKatarmu ita ce mu rika ganin kaa kullum.” Nan take sai Sarkin aljanu ya yi tafi sau uku, ya yi wata irin magana wadda ba su san abin da take nufi ba, sai ga wasu Kattan aljanu su goma da siffar mutane sun bayyana, suna zuwa sai suka zube suka yi gaisuwa. Nan da nan ya ba su umurnin gina lambu irin wanda ake iya dauka, a Kawata shi da duk kayan alatu, sannan kumaa gina daki guda daya wanda ‘yan matan za su rika shiga in zaakaisulambun dakuma in zaa dauko suke Www.bankinhausanovels.com.ng Sannan kuma lallai dakin ya kasance ma‘abucin fitilu masu haske a bayansa don ya rika haska musu wasanninsu. Yana so kuma a kammala wannan aiki ne a cikin kwanaki uku. Kartin aljanun nan suka ce an gama sannan suka bace. Wata rana suna zaune suna tsotson tatsattsun kayan marmari, shi kuma Sarkin aljanu yana kashingide a kan kilishi, wato kwana uku ke nan da ba da wancan umurni, sai suka ji wata irin rugumniya, aljanun nan sun dawo. Suka zo suka fadi suka yi gaisuwa tare da
Hmmm labari nata tafiya fa shin koya zata kaya kudai kuci gaba da kasancewa damu a koda yaushe Www.bankinhausanovels.com.ng