YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM’UNA
CHAPTER 6 BY HARUNA USMAN
Www.bankinhausanovels.com.ng
A JIYA MUN TSAYA
Lokacin da suka zama su biyu sai Idrisu ya gutsura wa Sarki wani bangare daga cikin labarinsa, ya ce, “Ya kai wannan Sarki ni matafiyi ne, ina so zan je wurin wasu tsibirai ne can a bayan duniya. Dalili kuwa shi ne don in yaki wani mugun aljani wanda ya sace ‘yan mata ‘ya’yan mutane ya tara su a can, su kamar hamsin da doriya. A can ya yi musu gida, kuma su wadannan duwatsu suna cikin wata babbar teku ce. Wannan wuri yana da wahalar zuwa.” Da Sarki ya ji zancen Idrisu sai ya yi wuf ya rungume shi yana zub da hawaye. Ya ce, “Ya kai Idrisu ina maka fatan nasara. Ka gan mu nan mu ma mun fito neman ‘yata ne. Ita ke nan guda daya a wurina, na karantar da ita fanni daban-daban na ilmi, ina alfahari da ita, ina sonta so mai yawa saboda hankalinta. Muna cikin shirye-shiryen yi mata aure da wani saurayi wanda shi ma bako ne, sai abin da ya
ZAMU TASHI
faru ya faru Shi wannan saurayi yanzu shi ne Wazirina kuma a halin da ake ciki yana shugabantar daya jirgin ruwan nawa na yaki wanda in Allah Yaso za su tarar da mu ba da dadewa ba. Ana cikin tsakiyar shirye-shiryen aure, wata rana yarinyar tana cikin kuyanginta a tsakiyar rafi suna wasanninsu, sai kurum sauran ‘yan matan nan suka ga wani abu ya dauke ta ya yi sama da ita, suka yi ta ihu amma ba za su iya yin komai ba, suka rugo suka sanar mana. Malamai Www.bankinhausanovels.com.ng suka ce babu shakka wani aljani ne ya dauke ta. Mun tafi garuruwa masu yawan gaske amma babu labari. In mun fita na dan tsawon lokaci sai mu koma gida mu sake shiri mu sake fita ko za a dace. Yanzu haka watanmu daya ke nan a cikin wannan teku babu ko labari.” Da Idrisu ya ji zancen Sarki sai ya ce, “Babu shakka ‘yarka tana cikin ‘yan matan nan da wannan mugun aljani ya sace, amma ka yi murna tun da ka fara samun dan labari, kuma ni na yi alKawarin sai na fatattaka wannan aljani, in Allah Yaso.” Murna ta kama Sarki, ya sa aka shirya KwaryaKwaryar liyafa a cikin jirgin ruwa, aka ci aka sha, aka yi ‘yan kade-kade da bushe-bushe irin nasu na sarakuna. Bayan an kammala sai Sarki ya ce, “Ya kai Idrisu ina da sha’awar ku sadu kai da Wazirina don gaba. Ina zaton zuwa jibi zai iso nan, saboda haka zan ba da sanarwar a tsaya a jira har sai ya iso.” Idrisu ya ce, “Godiya nake ranka ya dade.” Nan da nan jirgi ya tsaya cak a cikin teku don cika umurnin matukansa ga umurnin Sarki. Can kusan La‘asar sai suka hango wasu jiragen yaki manya-manya guda shida suna tunkaro su. Aka je aka shaida wa Sarki, ya ba da umurnin yin damara da shiryawa don jiran ko-ta-kwana, amma kada a kuskura a kai hari har sai in su ne suka fara kawowa tukuna sannan a mayar. Lokacin da aka zo gab da gab sai Sarkin wadancan – jirage ya turo jarumai shida don neman labarin wannan jirgi, aka kai su wurin Sarki, shi kuwa sai ya ce, “Ku je ku sanar da Sarkinku cewa mu ba masu son yaki ba ne, mun fito ne don neman wani abu namu da ya bace.” “Yan aike suka koma suka shaida wa nasu Sarkin abin da aka ce, sai shi wancan Sarki ya sake aikowa amma yanzu a rubuce cewa in dai har Sarki ba ya son yaki, to ya ba da dinare dubu dari. Bayan Sarki ya karanta sai ya sauya fuska. Da Idrisu ya lura, sai ya amshi takardar daga hannunsa shi ma ya karanta, sai ya cewa Sarki, “Ranka ya dade ai kawai ka ce musu su je su shaida wa Sarkinsu cewa gobe za ka aiko da sako.” Haka kuwa aka yi, shi kuma wancan Sarkin ya amince sai goben. Sarki ya tambayi Idrisu, “Ka ce a ce musu sai gobe za mu aiko, to yanzu mene ne abin yi? Ka ga dai jirgina guda daya ne su kuma nasu shida, kuma ga Wazirina bai iso ba tukuna, saboda haka abin da nake gani shi ne gobe kawai za mu tattara abin da suka ce din wato dinare dubu darin mu aike don zaman lafiya, in kuwa ba haka ba, to za su yake mu, ka ga sun fi mu yawa, dole za su yi nasara a kanmu, mun zama bayinsu ke nan.” Da Idrisu ya ji maganar Sarki sai ya ce, “Ko dinare daya ba za mu ba su ba, kai dai Allah Ya kai mu gobe in je in sami Sarkin nasu in ji abin da ya ke nufi.” Hantsin washegari na dagawa, sai Idrisu ya dauki takobinsa da mashi ya shiga Karamin kwale-kwale ya nufi jirgin da www.bankinhausanovels.com.ng wancan Sarki ya ke, aka kama masa ya shiga ya ce yana so ya ga Sarki, domin yana da sako daga wurin Sarkinsa. Nan da nan fadawa suka cika aikinsu suka yi masa iso, aka ce ya shiga. Idrisu ya je gaban Sarki ya yi gaisuwa, sai fadawa suka ce, “Wannan wane irin yaro ne haka da tsaurin kai? Ai shimfidewa za ka yi ka dibiya fuskarka bisa Kasaa gaban Sarkin duniya ka yi gaisuwa. Ba ka san gaban Sarki Mulkanu mai mulkin daular Kaufisa ka ke ba?” Sai Idrisu ya ce musu, “Ai babu wanda ya isa a yi masa sujuda sai dai Allah shi kadai, don addininmu ya yi hani game da hakan.” Fadawa suna jin maganar Idrisu sai suka yi masa ca, sai Sarki ya ce musu, “Ku bari tukuna har sai mun ji sakon da ya ke tafe da shi kafin mu san abin da za mu yi da shi, kun san ba a kashe dan sako sai dai mu yanke masa hannu daya. Yaro me Sarkinka ya aiko da shi?” Idrisu ya ce, “Sarkina ya ce in gaishe ka, gaisuwa mai cike da girmamawa, kuma ya ce in sanar da kai cewa shi ba ya fito yaki ba ne, yana neman ‘yarsa ce wadda ta bace, kuma dinare dubu dari da ka ce, ya ce a sanar da kai ka yi hakuri ba zasu samu ba.” Da Sarki ya ji abin da Idrisu ya ce sai ya fusata, fushi mai tsananin gaske, ya ce, Www.bankinhausanovels.com.ng shi yasa ka nuna mana tsaurin kai? Ka Ki zubewa ka yi sujada? To baa kashe dan sako amma zan yanke maka hannu daya don ka san cewa ka zo gaban Sarkin duniya.” Sai Idrisu ya ce masa, “Ya kai wannan Sarki mai tsananin Karfi, ina roKon ka yi hakuri ka Kyale ni, don kuwa ni dan aike ne, shi kuwa dan saKo ko marin sa bai kamata a yi ba.” Sarki ya ce, “T’o dan samari na yarda ba zan yake ku ba, kuma ba zan yanke maka hannu ba. Ka koma ka shaida wa Sarkinka cewa ya tuka jirginsa ya tafi amma fa duk wannan akan sharadi guda.” Da sauri Idrisu ya ce, “Ranka ya dade mene ne sharadin?” Sarki Mulkanu ya ce, “Takobin nan da ka rataya za ka ba ni. Kana ba ni shi ke nan babu yaki a tsakaninmu, kuma hannunka ya zama naka.” Da Idrisu ya ji maganar Sarki sai ya ce, “Ranka ya dade, ku kuwa sarakuna ba ku rabuwa da ba’a, ko kuma in ce mafarki, ko kana wasa ne ranka ya dade? Haka kawai abu ba naka ba ka ce lallai sai an ba ka?” Sarki na jin wadannan maganganu da Idrisu ya fada, sai ya bude baki yana mamaki, can sai ya yi kamar wanda ya farka daga barci, ya cewa dakarunsa, “Kuna jiran mene ne da shi?” Kafin Sarki ya rufe baki sun yiwo kan Idrisu, masu kai duka da kulki na yi, masu Kokarin kai sara da takobi da masu suna yi, shi kuma dan Hamidu sai ya shiga baudewa da gociya, babu wanda ya taba jikinsa. Can da ya fahimci cewa da gaske suke yi, sai ya ja damara, ya juya gindin mashinsa yana ta bugun fadawan nan suna faduwa, shi kuwa Sarki sai mamaki ya ke yi. Nan take Sarki ya sa aka busa Kahon yaKi, jarumai suka nufo inda Sarki ya ke. Da Idrisu ya tabbatar da cewa jaruman nan ransa suke nema sai ya zare takobi. Fada ya Barke, duk inda Idrisu ya kai sara da takobin nan sai ka yi ta ganin kawuna suna gungure a kasa, kafin lokaci kadan ya kashe mazaje masu yawa, can sai ya nufo Sarki yana zaune a kan kujera. Ko da Sarki ya fahimci cewa shi ya nufo bai yarda an hade ba, ai sai kawai ya yi waje ta taga ya zagaye ya fice, ya tsallake zuwa daya daga cikin jiragen. Shi kuma Idrisu sai ya juyo kan sauran jaruman da ke cikin wannan jirgi don dorawa daga inda ya tsaya. Ya hau su da kisa, bai bar kowa ba daga cikin jaruman da ke harabar. Da ya tabbatar ya kammala, sai ya juya akalar jirgin ya nufi wurin Sarkinsa. Yana isowa sai ya fita ya shiga jirginsu, da ma Sarki yana waje yana hango irin markabun da ya ke ta yi yana mai mamakin irin jaruntarsa. Www.bankinhausanovels.com.ng Idrisu ya shaida wa Sarki irin abin da ya wakana har ya janyo fada. Sarki ya yi masa godiya, kuma ya cewa askarawansa, su je su shiga cikin wancan jirgi duk gawarwakin nan a jefa su cikin teku a wanke jirgin a kafa tutarsu. Jirgi ya zama ganima. Aka zuba masa askarawa dari uku don kulawa da shi tare da mayar da hankali wurin shirye-shiryen gwabzawar da za a yi gobe. Shi kuwa wancan Sarki da ya tsallake sai ya zauna yana ta mamakin irin jaruntar wancan saurayi, yana tunanin ko ba mutum ba ne? Ya tara askarawansa ya ce lallai gobe su Kwato masa jirginsa ko kuma duk ya sare musu kawuna, kuma lallai yana son a yanko masa kan mayakin nan da na Sarkinsa. Jarumai suka ce an gama. Suka shiga wasa kayan yaki suna ta kuri irin nasu na jarumai, duk da cewa a gefe daya na zuciyar Sarki yana tantama game da fuskantar jarumi Idrisu amma kuma daya bangaren na zuciyarsa yana fada masa akasin da aka samu bacin rana ne kawai, amma yanzu suna shirye. Kowane bangare ya tabbatar cewa gobe dai za a yi ta ta kare. | Gari na wayewa aka fara fafatawa, rayuka suka shiga salwanta, can sai aka hango wani katafaren jirgin yaki yana zuwa yana busa, ga tuta nan sai kadawa fal-fal-fal take yi. Sarkin su Idrisu ya ce masa, “Wancan jirgina ne, wanda Wazirina ke yi wa jagoranci.” Nan take murna ta kama su. Waziri na isowa sai ya ga yakin da mutanensa ake yi, saboda haka babu jira ya ba da umurnin a auka wa abokan gaba. A ranar hatta namun ruwa sun san ana yaki. Gawarwaki sun cika gaba dayan bangaren da artabun ke faruwa. Yaki ya yi yaki, can sai aka nutsar da jirage biyu na Www.bankinhausanovels.com.ng abokan gaban su Idrisu. Yaki dai ya ci gaba, abin sai wanda ya gani. Kafin Magriba aka nutsar da jirgi na uku. A Karshe dai da hannu Idrisu ya kame Sarki Mulkanu ya daure ya mika wa Sarkinsa. Sarki ya gode wa Idrisu, ya sa masa albarka, kuma ya roKa masa nasara a kan buKatarsa. Da aka kammala yaki Waziri ya shiga wurin Sarki ya yi gaisuwa, Sarki ya amsa masa da murna, sannan ya gabatar da shi zuwa ga Idrisu. Yana ganin Idrisu sai ya ce, “Wannan ba Idrisu ba ne?” Shi kuma Idrisu ya ce, “Ba Abubakar ba ne wannan?” Suka rungume juna, Sarki da sauran jama’a suka yi ta mamakin kamannin wadannan samari Bayan ‘ya’yan Haji Hamidu sun gane juna, sai Sarki ya sa aka shirya walima don farin ciki biyu, wato samun nasarar yaki da kuma_ saduwar Wazirinsa Habu da dan’uwansa Idrisu. , Ana kammalawa sai Waziri Habu ya yi sallama da Sarki ya koma jirgin ruwansa shi da dan’uwansa, suka shiga dakin Waziri. Ranar ba barci. Waziri Habu ya fara ba shi labarin yadda ya zama Waziri. Ya ce, “Ya kai dan’uwana, bayan mun tarrabu, sai na kama tafiya ba dare ba rana, sai nutsawa nake yi cikin dazuzzuka, wani lokaci in Www.bankinhausanovels.com.ng kwana a kan bishiya, wani lokaci cikin kogon dutse, wani lokaci a kan falalen dutse, haka dai kuma Allah Yana ta kiyayewa. Wata rana na isa wurin wani kogi wanda dabbobin daji ke shan ruwa, kuma kasancewar Magriba ta kawo jiki, sai na yanke shawarar kwana a kan wata babbar bishiya da ke daura da kogin. Na haye kan wani katon reshe mai fadi na yi rigingine. Ina nan ina tunanin duniya kafin barci ya dauke ni, sai ga wasu mahaya Katti masu gashin baki buyabuya sun iso gefen kogin. Suka sauka daga kan dawakansu, suka je suka sha ruwa suka zuba a jikinsu, sannan suka ba dabbobinsu, suka sauke musu sirada, sannan suka dawo gindin bishiyar da nake kai suka zauna. Ashe daya daga cikin su mace ce yarinya budurwa, sai dai kuma sun daure mata hannayenta daigiya tamau. Suka bude wata jaka mai girma, suka dauko abinci suka ci, suka kuma gutsiri waina suka ba yarinyar nan sannan suka je suka daure ta a jikin wata ‘yar bishiya ta kusa suka dawo suka zauna. Allah da ikonSa, Bai ba su ikon daga kawunansu sama ba ballantana su hange ni. Suka dauko tulunan giya suka bude suna ta daddaka, can kuwa sai shegiyar ta fara aikinta. Cikin hirar da suke yi sai gardama ta sarke tsakanin Www.bankinhausanovels.com.ng su, wasu na ce waa kashe ta tun da dai Waziri ya biya su a kan haka ne, wasu kuma suka ce, a’a, kada a kashe ta, a je a sayar da ita ne kawai don a cewarsu, “Kudin za su yi mana amfani.” Musu ya yi tsanani a tsakanin su, kuma ga su ba sa cikin hayyacinsu saboda giyar da suka rigaya suka kwankwada. Wasu daga cikin wadanda suka ce a kashe ta sai suka harzuka suka zare takobi suka nufe ta don aikewa da ita barzahu, su kuma sauran da basa son a yi kisan, sai suka tashi suka tare su. Nan fa fada ya kaure tsakanin su, suka yi ta sarar juna har ya kasance saura mutane biyu kadai suka rage, kuma aka yi sa’a cikin wadanda basa son kashe ta ne. Suka komo gindin bishiya suka ci gaba da shan barasarsu, bayan sun yi tatul ta kama su sosai, sai barci ya kwashe su. Ni da ke sama sai na lallaba na sauko, na debe makamansu, sannan na je wurin yarinyar don kwance ta daga dauri, amma sai na ga tsoro ya kama ta, ta kadu sosai tana zaton ko ta sake fadawa mugun hannu ne. Na dai kwance ta alhalin duk hannayenta sun zage saboda dauri. Tana duba na sai ta ce, “Na tabbata wannan kyakkyawa ba zai zama mugu ba, da gani wannan kyan har cikin zuci ya ke.” Da na ji jawabinta sai murna ta kama ni,Www.bankinhausanovels.com.ng don na san Www.bankinhausanovels.com.ng ta Kyasa ne Sai na ce mata, “Babu shakka kina cikin aminci.” Habu ya ci gaba da yi wa dan’uwansa Idrisu bayani cewa, “Ya kai dan’uwana, ba daidai ba ne in ci gaba da ba ka labari ba tare da na dan gutsura maka bayanin kyan wannan yarinya ba. Tun da Allah Ya halicce ni na rayu har na zama mutum, ko mafarkina bai taba gwada mini mace mai kyau da cikar halitta kamarta ba. In dai har ka gan ta, a matsayinka na mutum, to babu shakka sai ka yi kwana da kwanaki cikin bege, irin halittun jikinta… yayana ka yi hakuri kada ka ce nayi rashin kunya. Ni dai na tabbata da a ce wadancan mahaya sun kashe wannan yarinya, to na rantse da sun yi wa maza asarar kyakkyawa. Bayan na kwanceta sai na tambaye ta abin yi? Koda ya ke kafin nan, a da na yi shawarar daukar takobi ne in fille wa mutanen nan biyu kai, sai na tuna babu dalilin da zai sa na fito neman ilmi in fara da kisan kai. Sai shawara ta daidaita tsakanina da yarinya, muka sami sanduna muka yi ta jibga tare da tikar bugaggun nan, sai da muka yi musu tilis ko motsi ba sa iyawa, sannan muka sa igiya muka daure su tamau, muka dora su a kan doki muka sake daurewa. Daga nan sai na tambayi yarinya kyakkyawa labarinta, sai ta shaida mini dan kadan. Ta sanar da ni cewa sunanta Fa’izah, kuma ta roKe ni ko zan iya raka ta zuwa garinsu don tana jin tsoro, na ce na yarda. Kafin mu kama hanyar garin nasu, sai da ta yi shiga irin ta maza ta yi nadi, da ganin ta babu wanda zai gane kai-tsaye cewa mace ce. A kwana a tashi har muka shiga gari cikin dare. Ba mu zame ko ina ba sai wani gida mai kyan gaske, ta Kwankwasa sai ga wani dattijo ya fito, ita kuma ta shige cikin gida ta bar ni a waje da mutanen nan biyu da ke daure, can sai ga ta tare da wani dattijo da wasu Katti su hudu, ya ba su umurni suka yi awon gaba da daurarrun. Ni dai ban san inda aka kai su ba. Dattijo ya kama hannuna ya shige da ni ciki. Na yi mamakin kyan wannan gida da kuma irin alatun da aka shirya a cikin sa. Ga dakuna nan birjik sai dai abin mamaki wannan dattijo ne kadai a gidan, sai dai bayi masu yi masa hidima. Yarinya ta tafi ko sallama ba mu yi ba. Dattijo ya nuna mini makwancina, wani Katon daki mai wani Www.bankinhausanovels.com.ng gangamemen gado irin na alfarma, sannan kuma ya nuna mini wani daki mai cike da kayan ado, ya ce mini ga kaya nan duk lokacin da na _ bukaci musanyawa. Na shiga na yi wanka, na sauya sutura na dan Www.bankinhausanovels.com.ng kashingida a bakin gado. Abin ka da gajiyayye, nan take barci mai nauyin gaske ya dauke ni. Can sai na ji ana tashi na, na farka sai na ga mutuniyata ce ta yi wata irin kwalliya da wasu irin kayan Kawa na ban mamaki. Kai idan ka gan ta sai ka gigice. Bayan na tashi na zauna sai ta rika gode mini. Na tambaye ta labarin abin da ke faruwa ta ce in bari nan gaba zan fahimci komai. Tun da na ga irin shigar da yarinyar nan ta yi na tabbatar da cewa ita wata aba ce a garin. Tayi mini jagora muka je dakin da dattijon nan ya ke, muka same shi a tsakiyar littattafai, ta yi masa gaisuwa irin ta girmamawa, ni ma na aikata kamar yadda ta yi. Ta dauko wani babban littafi, suka shiga karatu abin gwanin ban sha‘awa, ai sai na ji na dada rudewa a kan ta,Bayan ta kammala sai ya umurceni cewa bismillah. ‘Da ma abin da na fito nema, ga shi na samu cikin ruwan sanyi. Lokacin da muka kammala, sai bayi suka kawo abinci muka ci, muka Koshi sannan muka yi sallama da malam muka fita muka sami wuri muka zauna muna ta labarin duniya wanda har zancen soyayya ya fara kunnowa a ciki, babu shakka mun kamu da son junanmu. Muka yi sallama da ita ta ce mini sai gobe da dare amma da safe lallai in je wurin malam in dauki karatu, sannan kuma ta ce in saki jikina in dauka cewa ni dan gida ne, kada wani abu ya dame ni, nace mata, “to.” Da safe aka kawo mini kalaci na ci na yi Kat, sannan na je dakin malam na gaishe shi ya amsa mini da irin murmushin nan na malamai. Ba tare da bata lokaci ba muka shiga karatu har zuwa hantsi, na yi sallama da shi na koma dakina. A taKaice dai ya kasance sai dai in wanke goma in tsoma biyar kawai. Bayan cin abincin dare sai na wuce wurin malam, na kuma lura yana murna da ni, don ya fahimci ina da sha’awa game da koyon ilmi, kuma daidai gwargwado ina fahimta. Muna cikin karatu sai ga yarinya ta iso, ta gai da shi sannan ta juyo ta yi mini irin murmushin nan da kan sa zuciyar masoyi narkewa. Muka yi karatu muka gama kamar kullum, muka bar wurin malam, na dauko karatuna ina bita, inda na yi kuskure ta gyara mini, don ta yi ilmi fiye da ni. Www.bankinhausanovels.com.ng Daga baya muka yi sallama ta koma. Sai da muka shafe wata shida a haka, to ashe abin da ya faru ita wannan yarinya Fa’izah ‘yar Sarkin wannan garin ne ni ban sani ba, kuma wannan malami da muke karatu a wurinsa kawunta ne, a wurinsa ta girma. Mahaifinta Sarki Zulkiflu yana da wani Waziri, wanda Sarkin ya amince wa, kuma ya yarda da shi. Saboda son da ya ke yi masa ya sa ya sakar masa komai. Duk abin da Sarkin nan ke yi, Waziri Jatau ba ya Kaunar sa ko miskala-zarratin. Ya shirya maKarkashiyar da zai kawo wa Sarki bakin jini wurin jama’‘a baasan iyaka ba, amma kuma duk Allah Yana kiyayewa, don kuwa alherin Sarkin yana da matukar yawa. Yana son talakawansa, ga tawakkali da sanin ya kamata. Wannan ya sa su ma talakawan ke matukar son sa kamar su lashe shi. Wani abin mamaki shi ne, ko Sarki Zulkiflu ya gane munafuncin da Waziri Jatau ke shiryawa sai ya Kyale shi ya yi kamar bai fahimta ba. Da Waziri ya ga ya kasa dugunzuma ran Sarki, sai kawai ya yanke shawarar halaka wani abu wanda Sarkin ke matuKar Kauna, saboda haka sai kawai ya yanke shawara a kan cewa zai saa sace Fa’izah wadda kuma ita ke nan abar da Sarki ya taba haihuwa a rayuwarsa, don ya sa a halaka ta. Ya tabbata cewa in aka yi haka, to zuciyar Sarki za ta sami tsananin kunci yadda mai yiwuwa ma ciwon Zuciya ko Www.bankinhausanovels.com.ng tsananin damuwa su zautar da shi ko kuma ma su yi sanadin halaka shi kowa ya huta. In ya so sai shi Wazirin yaci sarauta. Shi ne dalilin gayyato wadancan mahayan majusai su shida don su cika masa wannan babban kudiri nasa. Allah Ya yi sauran kwananta na gaba muka hadu da ita da yardar Allah kuma na cece ta. Ashe lokacin da muka shigo cikin garin nan da dare Sarki ba ya nan, ya shiga cikin duniya neman ta, kuma Waziri shine ya ke rike da gari. Da muka zo sai ta kawo ni wurin malami kuma kawunta. Ta shiga gidansu babu wanda ya sani don kada Waziri ya sake shirya mata wata maKarkashiyar. Duk garin babu wanda ya san ta dawo, daga malam sai mahaifiyarta. Bayan wata shida sai ga Sarki ya dawo don sake sabon shirin fita, duk ya rame ya fita kamanninsa, saboda tsananin Kawazucin ‘yarsa. Ya shiga gida mutanen gari suna ta murna, ana ta kade-kade da bushe-bushe saboda murnar dawowarsa. Matan gida, barori da bayi suka shiga hada-hadar da suka saba in Sarki yana gari. Lokacin da kowa ya bar shi don ya huta, abin mamaki sai ga ‘yarsa da yaje nema ta zo ta rungume shi. Mai martaba ya ji kamar mafarki ya ke yi. Sai da ya
HMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KU KASANCE DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG