YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM’UNA CHAPTER 8 BY HARUNA USMAN

 YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM’UNA

CHAPTER 8 BY HARUNA USMAN

Www.bankinhausanovels.com.ng 

A JIYA MUN TSAYA 

Ni ne Sarkin lambu, akwai masu aiki nan kamar mutum dari Karkashina, yau ranar hutunsu ce, kuma a irin wannan ranar ne Sarki kan zo gewaye, shi ya sa ba ka ga kowa ba.” Sarkin lambu ya ci gaba da cewa, “Babu shakka ina da tambayar da zan amsa a kan wannan gwanda da ka tsinko. In Sarki ya ji, in ban yi sa’a ba yana iya yanke mini mummunar hukunci don a gaskiya Sarkin namu yana da zafi. Abin da kake ganin ba a bakin komai ya ke ba, shi wannan Sarki sai ya dauke shi da babban muhimmanci don ya sami damar hukunta mutum.” Da Yahaya ya ji jawabin Haladu Sarkin lambu sai yace, “To tun da yake haka ne, mu gudu mana kafin Sarki ya iso.” . Mai lambu ya ce, “Yaro dai yaro ne “in na gudu to lallai Sarki zai yi zaton akan wannan gwandar daya ne, saboda haka zai ‘sai a kama iyalina yasa a kashe su 

ZAMU TASHI 

Ka ga kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba ke nan. Ina ranar da namiji zai gudu ya bar iyalinsa cikin wahala?” Sarkin lambu ya ci gaba da yi wa Yahaya bayanin cewa, “Abin da nake so da kai yanzu shi ne, ka fita daga cikin wannan lambu ka kama hanyar zuwa wani gari, banaso Sarki ya zo ya same ka nan.” Yahaya ya ce, “Yallabai ai babu yadda zaa yi in tafi in Kyale ka cikin hadari.” «Sai Sarkin lambu ya zaro takobi ya ce masa, “Ko ka bar wannan lambu yanzu ko kuma in fille maka kai.” Da Yahaya ya ga da gaske ya ke yi, sai ya kama hanyar ficewa, amma sai Sarkin lambu ya kira shi ya ce, “Zo nan Yahaya.” ~ fSarkin lambu ya cika jaka da kayan marmari sannan ya kawo wasu ‘yan kudi ya hada masa ya ce, “Ga wannan ka dan yi guzuri.” Suka yi sallama suna kuka. Yahaya ya ci gaba da kukansa yana tafiya yana . tunanin irin karimcin Haladu Sarkin lambu da kuma irin abin da zai faru a kansa in Sarki ya zo. Da ya dan yi nisa da lambu sai ya zauna a gindin wata itaciya.shi ma bai san dalilin zamansa ba.

Www.bankinhausanovels.com.ng  dai san tsawon lokacin da ya kasance a cikin wannan hali ba sai dai kawai ya rika jin tambura suna  tashi, ashe Sarki ne ya tunkaro. Fahimtar haka sai Yahaya ya gaggauta ya koma ta baya, ya haura dannin lambun ya shige. Ya sami wuri ya labe kamar ya sani don kuwa in Sarki ya shiga, to askarawa kan yi wa wurin zobe ne, ba shiga ba fita. Yahaya ya sauya shawara daga labewa a cikin sarkakiya zuwa hayewa wata itaciya mai duhuwa, kuma duk abin da ake yi Sarkin lambu bai gani ba. Shigowar Sarki kai-tsaye sai ya fara kewaya wani bangare na lambun wanda aka daddasa tushe dubu biyar na wani irin dan itacen inabi da aka kawo masa daga Kasar Misra. Kafin ya gama har an kafa tanti an shimfida kilisai da matasai, an baje kayayyakin jin – dadi mabambanta, sannan Sarkin lambu ya kawo wankakkun kayan marmari iri-iri ya ajiye. Zaman Sarki ke da wuya sai Sarkin lambu ya zo ya zube a gabansa, fadawa suka dauka gaba daya, “An gaishe ka Sarkin lambu.” Sarki ya ce, “Sarkin lambu yaya lambu?” Sarkin lambu ya ce, “Lambu lafiya lau ranka ya dade.” Sarki ya ce, “To yau dai ina so in sha gwandar nan da na yi ta cewa ka kula mini da ita da kyau, saboda haka sai aje a zunguro ta, amma kada a kuskura a bari ta fadi kasa. A ba mai dafa mini abinci ya fere ta, zanci kadan yanzu, saura kuma ina so in tafi da ita gida. Gwandar ce ma tasa na shigo, don a gaskiya yau ban yi niyyar zuwa nan ba, kilisa na so tafiya.” Da Sarkin lambun ya ji dogon jawabin da Sarki ya yi game da gwanda, sai ya yi kasaKe gabansa ya fadi, zuciyarsa ta shiga bugawa uku-uku, yace a cikin ransa, “ta faru ta Kare.” Sarki ya dube shi ya ce, “Ko ba ka ji ba ne?” Sarkin lambu ya dukar da kai Kasa ya cewa Sarki, “Ranka ya dade tuba nake yi, na yi laifi tuba nake yi, ina roKon Sarki ya yafe mini. Ba zan sake irin wannan kuskure ba.” Sarki ya juyo gaba daya cikin fushi ya ce, “Mene ne ya faru Sai Sarkin lambu ya ba shi labarin saurayi Yahaya, ya kuma je ya dauko gwandar ya nuna masa. Cikin KanKanin lokaci kamannin Sarki suka sauya, ya yi fushi mai tsananin gaske, ya tashi ya dakawa Sarkin lambu tsawa, “Wato wulaKancin da aka ce kana yi har ya iso gare ni ko? Ni ina Sarki kuma gona tawa, na danKa maka amana har na yi maka Sarkin lambu, kuma ita wannan gwanda ba sau daya ba sau biyu ba ina yi maka gargadi a kan ta, amma don tsananin raini a gare ni shi Barawon gwandar ma sai ka Kyale shi ya gudu. Saboda haka yanzu za a yi ta zabga maka bulala ko za ka mutu ne.” Www.bankinhausanovels.com.ng Duk abin nan da ke faruwa Yahaya na sama yana kallon su, a cikin zuciyarsa yana cewa, “Lallai wannan mutum yana da mulki, ga kuma kwarjini, Jallai da ganin sa ka ga babban Sarki.” Sarki ya ba da umurni, nan da nan ‘yan cika aiki suka shiga bulale Sarkin lambu, tun yana tsaye har sai da ya fadi. Da Yahaya ya ga haka, sai ya duro daga itaciyar da ya Boye ya rugo a guje, yana isa sai ya fada kan Sarkin lambu yana tare bulalar, yana cewa, “Ku buge ni ku bar Sarkin lambu.” Sarkin lambu ya ce, “Kai Yahaya mene ya dawo da kai? Ba ka jin tsoron ranka?” Yahaya ya ce, “Na dawo ne saboda karimcin Sarkin lambu da kuma tsoron abin da zai faru gare shi bayan na tafi. Ina tafiya zuciyata ta kasa natsuwa, saboda haka na dawo, zan yi farin cikin rabuwa da raina saboda rayuwar Sarkin lambu ta dore. Ai darajarsa ta fi Karfin sarautar lambu, sai dai Sarkin wannan gari.” Jawabin Yahaya ya sa Sarki ya dada gyara zama, ya ce, “Kai yaro ka san gaban wanda ka ke kuwa?” Yahaya ya ce, “E na sani gaban Sarki na ke.” Sarki ya tambayi Yahaya, “To mene kake nufi da cewa Sarkin lambu shi ne ya kamata ya zama Sarki a wannan gari?” Yahaya ya amsa da cewa, “Saboda ka ga shi Sarkin Www.bankinhausanovels.com.ng lambu karimcinsa da gaskiyarsa da tausayinsa da sanin yau da kullum ne suka jefa shi cikin wannan wahala. Kuma duk wadannan abubuwa da na ambata abubuwa ne da suka kamata a ce duk Sarki mai adalci yana da su. Na tabbata in da ace shi ke da wannan Katon lambu, to zai iya bar wa talakawansa su rika amfana da kayan marmarin da ke ciki, amma sai ga shi Sarkin gari guda zai halakar da bawansa mai tsananin yi masa biyayya saboda Kwayar gwanda daya tak. Ba kwa tsoron a rubuta mummunan tarihinku ya zama abin tunawa ko karantawa na har abada? Ko da yake an ce kai Sarki ne mai tsananin zafi, in kuwa ka ji ance haka game da kowane irin Sarki, to azzalumin Sarki ne. Da Sarki Salahuddin ya ji maganar Yahaya sai ya sake tambayarsa, “Yaya aka yi ka sami labarinmu alhali kana bako? Yahaya ya ce, “Ai labarinka ya kai ko ina, kuma ni ga shi na shaida, a kan gwanda Kwara daya tak. Dama ni tsananin yunwa ce ta tsayar da ni, kuma ba tare da na sani ba na shigo cikin wannan lambu naka mai halakar da mutane.” Fadawa da duk sauran jama‘ar da ke wurin sun yi mamakin irin yadda Sarki ya dauki irin wannan  lokaci mai tsawo yana mayar da yawu da wannan saurayi Sarki ya tambayi Yahaya cewa, “Me kake nufi da halaka mutane?” Www.bankinhausanovels.com.ng Yahaya ya amsa, “Abin da ya sa na ce lambu mai halaka mutane shi ne, ga shi a idona za a halaka Sarkin lambu saboda Kwayar gwandar da ya raine ta da hannunsa. Saboda haka ashe ba mu san mutum nawa wannan gona ta halaka ba zuwa yanzu, ni ma sai dai Allah Ya kwace ni.” Sai Sarki ya ce, “Yahaya kake ko? Ba ka jin tsoron da wanda kake magana ba?” Yahaya ya amsa masa da cewa, “Ai duk Sarkin da ba a fada masa gaskiya, to kuwa ya halaka, don kuwa idan na kusa da shi suka fahimci cewa ba mai son gaskiya ba ne, to kullum Karya za su shirya masa.” Yahaya ya kara da cewa Sarki, “A irin haka ne in runtsi ya yi runtsi a fagen fama, dakaru kan bar Sarkinsu. Duk kuwa Sarkin da ka ga dakarunsa sun bar shi a filin yaki, to ba Sarkin kirki ba ne, yana zaluntar talakawansa. Ranka ya dade shi adalin Sarki a kullum za ka gan shi ne tare da malami mai tsoron Allah wanda da zarar ya ga Sarkin zai kauce hanya, to zai kwabe shi don kada ya fada cikin halaka. Amma in ka ga Sarki Www.bankinhausanovels.com.ng ko shugaba babu hulda tsakaninsa da malaman Kwarai sai dai na tsibbu, to babu shakka azzalumin Sarki ne.” Ga alama Sarki ya riga ya fara damuwa da maganganun da wannan yaro ke ta zuba masa, ko kuma watakila sarautar ce ta motsa, sai ya cewa Yahaya, “Yaro ambaci buKatarka ta karshe in biya maka, don kuwazan sa a dauke maka kai ne.” Yahaya ya ce, “Ai ranka ya dade adalin Sarki ne kan ce a fada ya cika alKawari.” Sai Sarki ya ce, “Wato dai kana nufin ni ba adali ba ne? To da farko dai na yafewa Sarkin lambu laifinsa.” Yahaya ya ce, “Adalcin farko ke nan.” Sarki ya ci gaba da bayani, “Tun da nake kan karagar mulki ba a taba samun talaka ya tsaya gabana ya fada mini maganar da ya ga dama kamar wannan yaro mai tsaurin kai ba. Kai Yahaya fadi bukatarka ta Karshe sannan a sare maka kai.” Yahaya ya ce, “Ranka ya dade ka yi alkawarin za ka biya mini buKatata ta Karshe?” Sarki ya ce, “Kwarai kuwa, ai nine Sarki ba kai ba.” Sai wani bafade ya sa baki, “Kai yaro fadi bukatarka kada ka bata mana lokaci.” Yahaya ya ce, “Ran Sarki ya dade, bukatata ta Karshe ita ce, ina son in Sarki ya kashe ni, to ya sake rayar da ni. Wannan ita ce kawai bukatata.” Da Sarki ya ji bukatar Yahaya, sai ya yi shiru ya daga kansa sama, yana hango itaciyar gwandar nan da ta kawo wannan takaddama. Ya tsunduma cikin tunani, yana cewa a cikin zuciyarsa, “Lallai wannan yaro sha’aninsa akwai ban mamaki, ka ga yaro da iya magana kurfa-kurfa?” Can bayan wasu ‘yan dakikoki sai aka ga Sarki kamar ya tashi daga barci, ya daina kallon itaciyar gwandar. Ya kalli fadawa ya ce a saki Sarkin lambu amma yana so a bankare masa Yahaya. Nan da nan fadawa suka cika aiki. | Ya ba da umurni ga Sarkin dogarai cewa a je Jakara – a Zo masa da daya daga cikin wadanda aka yanke wa hukuncin kisa. Ba tare da bata lokaci ba Sarkin dogarai ya cika aiki, ya kawo wani murgujejen Kato. Sarki ya sa aka fere gwanda tsaf, sannan aka ba Katon nan aka ce ya shanye ta. Ai kafin ya kammala shanyewa sai aka ga ya fadi Kasa, yana ta shure-shure, kumfa ta cika bakinsa, kafin ka ce haka, har ya ce ga garinku nan. Nan da nan sai Sarki ya ce, “Abin da nake zato ke nan. Shi ya sa saurin fushi ba shi da amfani, don kuwa ba don yaron nan Yahaya ya zunguro gwandar nan har abubuwan da suka faru sun faru ba, to lallai da ni ne zan bakunci lahira a dalilin wannan gwanda. Ku dubi itaciyar gwandar can da kyau, ga wata macijiya gamsheka can ina hango ta, kuma lallai ita ta sa guba a cikin gwandar, abin da na hango ke nan ya sa don in tabbatar, na ce azo da wannan mailaifin, kuma ga yadda ta kasance. Kun ga da a ce na yi saurin cire musu kawuna, sannan yanzu na farga, to lallai da na yi nadama. Kai kuma Yahaya duk abin da ka fada mini na ji shi sosai, kuma yanzu ya shiga kunnena. Kuma daga yau na nada ka mataimakin Sarkin lambu, kai ne za ka rika kai mini kayan marmari gidana, duk bayan kwana uku. Kana zuwa ka shiga Kai tsaye abinka, zan sanar da Sarauniya.”Bayan Sarki ya gama magana ‘da su Yahaya, sai ya hau ya koma gida yana tunanin abubuwan da suka faru a lambunsa, da irin maganganun Yahaya da kuma irin basirarsa. Yana isa bai zame ko ina ba sai wurin Sarauniya Zizaratu, matarsa ta gaban goshi, ya ba ta labarin abin da ya wakana na daga al’amarin Yahaya da irin jajircewarsa a kan gaskiya tare kuma da irin kyau da Allah Ya yi masa, sannan kuma da irin yadda abubuwan da suka faru din suka zama sanadin tsirar shi kansa Sarki. Kuma ya sanar da ita cewa Yahaya ne zai rika kawo mata kayan marmari Www.bankinhausanovels.com.ng  duk bayan kwana uku. Abin ka da sharrin shaidaniyar mace, da matar Sarki ta ji labarin sai ta ji a duniyar nan babu wanda take so tun kafin ta gan shi kamar Yahaya. Ranar kawo kayan marmari ta zo, Yahaya ya cika kwando ya nufi gidan Sarki, ya je ya tarar ana ta fadanci. Sarkin fada ya shiga da shi ya yi gaisuwa sannan aka shiga da shi wurin Sarauniya. Yana zuwa aka yi masa iso ya shiga, ya gaishe ta, ta amsa cikin murmushi sannan ya ce, “Ga kayan lambu.”  Sarauniya ta kawo abinci irin na alfarma ta ba shi yaci. Bayan ya kammala sai ya yi godiya ya dauki kwandonsa da aka juye zai tafi, Sarauniya ta kawo kudi masu dama ta ba shi ya amsa ya sake yi mata godiya ya juya. Zai fita dai sai ta sake kiransa ta ce, “Ya kai Yahaya ina fata Sarki ya sanar da kai cewa bayan kowadanne kwana uku ne za ka rika kawo kayan lambu nan ko?” Yahaya ya amsa, “E ya sanar da ni ranki ya dade.” Tace, “To shi ke nan, ka tafi.” Yahaya ya fita ya je ya yi sallama da Sarki. Sai Sarki ya ce masa, “Yahaya ga malami, don an ce kana son yin karatu.” Yahaya ya gaishe shi cikin ladabi, sannan ya sake yi  wa Sarki godiya. Sarki ya ce, “Ya kai Yahaya. Na ga maganar ka tana da Kanshin gaskiya, shi ya sa na kawo wannan shahararren malamin kusa da ni don in wani abin ya shige mana duhu, ya rika nuna mana gaskiya.” Sai Yahaya ya ce, “Ranka ya dade ka yi daidai. Allah Ya ja zamaninka.” Bayan Yahaya ya kammala da wurin Sarki, sai ya bi malaminsa a baya don ganin inda ya ke don zuwa daukar darussa. Daga nan sai ya wuce lambu cike da farin ciki ya sanar da Haladu Sarkin lambu duk yadda ta kasance tsakaninsa da Sarki, malami da kuma Sarauniya Zizaratu. To, abin da ke faruwa shi ne ita wannan Sarauniya dai ta rigaya ta shanye Sarki, ba ya iya yin komai sai ta yarda, Karewa ma, Sarki duk ya kori sauran matansa saboda makircinta. Sauran matan da ke gidan yanzu su kamar talatin duk daga Kwarakwarai ne sai bayi, su ma duk suna zaune ne ba don komai ba, sai don ta yarda da zamansu, kuma don su rika yi mata hidima. Shi kuma wannan Sarki, wato Sarki Salahuddin na Kasar Burdan-Yamma shahararrre ne, ko kai wane ne za ka tabbatar da cewa lallai yana da kwarjini, sannan kuma ga shi jarumi. Duk wanda ya takale shi, to babu shakka ya janyo wa kansa jangwam, don Www.bankinhausanovels.com.ng  kuwa sai Sarkin nan ya karya shi. Kana shigowa wannan gari nasa, za kaga yadda mutane suke bin doka, _ ka san akwai mulki. Kai a takaice dai cikin Kasashen da ke kurkusa, babu mai Karfin wannan Sarki. Amma kash! Da zarar ya shiga cikin gida, sai matarsa Sarauniya ta mayar da shi kamar mace, sai abin da ta ce, ba shi da katabus. Duk wanda ta ce ba ta so a wannan gari, to kuwa rannan kansa ba ya kwana bisa wuyansa. Kuma ko da an shirya ne tsaf za a je yaki wani gari amma matar nan ta ce a’a, to wannan yaki an fasa ba za aje ba. Sai dai kuma wani abin haushi shi ne, duk irin wannan dama da wannan mata ta samu daga Sarki, to ba ta da mutunci, hasali ma dai ita fasika ce, kuma kowa ya sani a wannan gari, amma wane ya isa ya tunkari Sarki da irin wannan magana? Duk wadda wannan mata ta san cewa zai iya samun kulawar Sarki ta musamman, to sai da ta tabbatar ta raba su. In kuma babu yadda za a yi ta shiga tsakani gaba daya, to sai ta bi yadda za ta nisanta tsakanin su, wato ba za su zauna kusa da Sarkin tare ba. Irin wannan shi ne abin da ya faru da Gimbiya Lubna ‘yar Sarki, wato ba ta zaune a cikin fada, gidanta daban ita da masu yi mata hidima. Ita wannan yarinya ‘yar Sarki, Allah Ya yi mata  wani abu da ake kira kyau, ga kuma cikar halitta. Ita kuma Sarkin lambu ne ya dora wa Yahaya alhakin kai mata nata kayan marmarin. Ranar farko Yahaya ya debi kayan lambu ya isa gidan ‘yar Sarki don kaiwa, dama kafin isowarsa ta matsu da buKkatar shan mangwaro, kuma aka yi sa’aa cikin kayan marmarin da ya kawo din akwai mangwaro. Aka shiga aka yi wa Yahaya iso aka ce ya shiga, ya same ta kwance a kan darduma tana karatun littafi, kuma ga bayinta nan ‘yan mata duk sun zagaye ta. Yahaya ya gai da Gimbiya amma ko daga kanta ta dube shi ba ta yi ba ballantana amsawa, saboda jin isa irin ta su ta saraki. Nan da nan aka juye aka ba shi kwandonsa. Gimbiya kuma aka kawo mata mangwaro ta gatsa ta fara sha, ta ci gaba da duba littafinta. Can sai ta tuna gwanda, sai ta cewa masu mata hidima, “Akwai gwanda kuwa a cikin kayan da aka kawo?” Wata daga cikinsu ta amsa, “Babu gwanda a ciki ranki ya dade,” Gimbiya ta ce, “Ku kirawo mini mai lambun nan. Yau ga sakarai.” Aka dawo da Yahaya, ko kallon sa Gimbiya ba ta yi ba, ta ci gaba da shan mangwaronta da karatu. Www.bankinhausanovels.com.ng Can sai ta ce, “Kai ina gwanda?” Yahaya ya ce, “Af, ashe kina magana? Gwanda ko? To sai an dubo, wani lokaci in da rabonki sai a kawo.” A daidai lokacin, ta sa mangwaro a bakinta don gatsawa amma jin wannan kalami daga bakin Yahaya sai ta kasa gatsawar kuma ta kasa cirewa daga bakinta, ta waigo cikin fushi suka hada ido da Yahaya suka Kurawa juna ido, ana kallon-kallo. Can sai Gimbiya ta yi kamar ta farka daga barci ta cewa Yahaya, “Kai mai lambu ba ka da ladabi ne, ba ka gaida Gimbiya?”. – Sai Yahaya ya ce, “Ai an ce mini Gimbiya ta zama kurma saboda girman kai, shi ya sa da na zo na gwada yin gaisuwar, sai na ga ashe gaskiyar mutane ne, kurma ce ke.” Gimbiya Lubna ta ce, “Kai! Ka san da wadda kake magana? Shin ka san cewa a tsakanina da kai akwai tazara?” Sai Yahaya ya ce, “E na san ina magana ne da ‘yar Sarki mai fahari, kuma ni dama ba na son matsowa kusa da ke, larurar cewa ni ma’aikaci ne kawai ta sa ni zuwa inda ki ke. Ba irin ku ne ake son matsawa kusa da su ba, saboda girman kai.” Sai Gimbiya ta yi fushi ta ce, “Ni ban taba ganin mai lambu da tsaurin kai kamar ka ba.” Yahaya ya ce, “Ai kin san in mutum na aikata wani mugun abu, sai ya yi zaton kowa ma kamarsa ya ke, shi ya sa kike gani na kamar mai tsaurin kai irin ki.” Ya Kara da cewa, “Don Allah ki sallame ni, ni ba magana ta kawo ni ba.”Gimbiya ta ce masa, “Na Ki in sallame ka din. Ban gama da kai ba tukuna.” Yahaya ya ce mata, “T’o ni tun da halinki ke nan, daga yau sai dai wani ya riKa kawo miki kayan lambu don ni ba zan sake zuwa inda za a ci mini mutunci naba. Ke ni jimla ma na fi girmama ‘yan matan da suke da burin yin aure ba irin ki da ke tunanin sarauta ba.” Sai Gimbiya ta yi murmushi ta ce, “Ai yanzu ina magana da kai ne a matsayin mutum da mutum amma ba a matsayin ‘yar Sarki da bawanta ba, don da a ce ina son yin magana da kai ne a matsayin kana bawana, to da sai in sa a yi maka bulala ko kuma a dauke maka kai.” Yahaya ya ce, “E lallai za ki iya sawa a sare kan -mutum, amma ko silin gashi guda daya ba ki iya halittawa, sai dai mulkin kawai,” Sai Gimbiya ta ce, “Kai mai lambu maganar ta isa haka nan. Ina so jibi ka kawo mini kayan lambu,” Yahaya ya ce, “Ranki ya dade jibi ba zan sami damar zuwa ba saboda zan kai wa matar Sarki nata.” Gimbiya ta dube shi ta ce, “To ni dai ka yi Kokari idan ka kai mata ka zo ka nome mini ciyawar gidan nan.” Yahaya ya ce mata, “A nawa zan nome miki ciyawar?” Gimbiya ta ce, “A matsayin Gimbiya ‘yar Sarki.” Yahaya ya ce, “Albarka.” Gimbiya Lubna ta ce masa, “To don soyayya.” Sai Yahaya ya kalle ta don tabbatar da cewa ita ce da kanta ta fadi abin da kunnuwansa suka ji, kuma tabbatar da hakan ya sa kawai ya ji zuciyarsa da bakinsa a lokaci daya suna amsa mata cewa, “An sayar. Saina Zo.” Ya juya zai tafi sai ta ce, “Mu je in raka ka.” Sai yace mata, “Haba yaya ‘yar Sarki za ta raka bawa mai lambu?” Gimbiya ta amsa masa, “Ba ‘yar Sarki ce ke yi maka rakiya ba, masoyiya ce take yi wa masoyinta rakiya. Kuma ba na fata mai magana ya sake irin maganganun da suka wuce a baya, don da ace a yau mahaifina ba ya wannan duniya, kuma a ba ni damar zabo mai maye gurbinsa, to babu shakka zan ce mai lambu, don irin tsananin dimauta da na yi a kan rashin tsoronsa game da gaskiya.” Sai Yahaya ya ce, “Da ace mai magana ta san yadda

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATA KASANCE KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *