YAZEED CHAPTER C KARSHE
Yazeed motarshi yashiga yanufi Gidansu yanashiga ya taradda da dady yauma bai fita parking d’in motarshi tayi yashiga ciki taradda su yayi A Falo
“Mimi morning
Dady morning.”
“Yazeed Antashi lafiya.?”
“Lafiya lau Dady.”
“Ya Muneera?.”
Tana lafiya lau tana gaisheku.”
“Muna Amsawa sosai.”
Yazeed mik’ewa yayi zai tafi
Mimi ta mik’e ina zuwa Bari na d’auko maka d’an gidan muneera kakai Mata.”
Mimi tashiga ciki ba’a jimaba sai Gata d’auke da wata K’aramar cooler
Taba Yazeed bankwana yayi dasu
B’angaren Kaka yashiga
“Tsohuwa mai ran K’arfe
Ina kwana.”
“Yazeedu lafiya ya Jumallah kuma?”
“Kaka kidaina cewa Jumallah Muneera zakice.”
“Banacewa to itama tagaji tabari.”
“Shikenan keda ita.”
M’ikewa yayi zai tafi
“Natafi.”
“Kagaidata Kajiko.”
“Kozakiyimata zaman D’aki ne.?”
“A,a. Kuje can.”
Haka Yazeed da Kaka sukai ta wasa da dariya Kamar ba yazeed ba lalai.
Haka yafito yashiga motarshi yakoma Gidanshi dake Unguwar Sarki.
Yana shiga yaji K’arar television Amma babu kowa
Falon Kashe Kallon yayi yajuya yanufi D’akinshi jiyayi yayi tuntube da Mutum.
Muneera yagani Kwance tana bacci da Alamu Kuma bacci yayi Mata dad’i
Ga sanyi Ac yana Bugunta
Tsaye yayi yana Kallon Muneera gyaramata kwanciyar yayi ya aje cooler ya shiga D’akinshi
Kwanciya yayi tare da runtse idanuwanshi Surar Muneera yake Kallon cikin idanuwanshi
Jiyake Kamar yajita jikinshi yanzu
Amma yasan tsanar da Muneera tayi mashi tayi Yawa yaushe zata Koyi sonshi.
Muneera tana Farkawa taga Kamar bayadda ta kwanta bata kawo ma ranta Komai ba ta Mik’e tanufi D’akinta
Toilet ta Koma ta K’ara watsama Jikinta Ruwa
Wando ne tasa Had’e dawata Riga ta matse ta tumke Gashinta tayi bata d’aura d’an kwali ba tafito
Falon.
Kawai jitayi cikin yafara Kuka yunwa.
Yazeed fitowa yayi da ruwa jikinshi.
Numfashi shi Kusan D’aukewa yayi Ganin shigar da Muneera tayi
Tsaye yayi yana Kallon ta.
Hanyar kitchen tanufa domin ta Samar wa cikinta Abinchi.
Jitayi Anjawota kawai.
Yazeed rikecewa yayi yafara Kissing d’inta muneera ta ko Ina.
Wani Kuka tasaki
“Kasakeni mugu Azzalumi.”
Bugu tafara Kaima Yazeed
Sakin tayi yayi idanuwanshi sun kad’a sunyi jawur Kamar garwashi
“Haba Muneera wai sai yaushe zaki manta da Abinda yafaru ne? ko Allah manayi mashi laifi yayemana Kisani. Kitausaya min pls.”
Kallonnshi tayi Kawai ta watsar
“Kamanta Bagidajiya yar Kauye ce. wadda Kace bazaka tab’a so Har Abada
Tayaya Kake zaton zaka samun soyayyata ne?”
“Sorry My Muneera.”
“Nice taka lailai Kanada Aiki.”
Juyowatayi tanufi Hanyar kitchen
Indomie kawai ta D’ora Minti
Biyar ta dahu ta D’auko tafito
Tana zama idonta yahango
Mata colooer mik’ewa ta d’aukota tana Bud’awa taga
Rice and Beans ne yaji Kayan Had’i yanata tashi.
K’amshi
“Wow fantastic.”
Spoon tasa tafara cinshi
Saida taji babu wurin sannan
Nan tabar kayan tashige D’aki
Bud’a Firji tayi
Ta D’auki ruwa Tasha
Tayi Hamdallah
Takoma gado tacigaba da latsa wayanta
STORY CONTINUES BELOW

Yazeed yadawo masallachi
Nufar inda muneera taci Abinchi yayi wadda taci tarage yafaraci zama yayi
Kujerar data zauna yashiga sunsunawa. Yana shakar K’amshinta.
Haka. Dare yayi muneera kulle D’akin tayi tahaye Gado ta K’wanta
Yazeed shima haka yak’wanta cike son Muneera dake K’ara ruruwa cikin Ranshi.
Luv my Fans🍒🍒🍒
[5/10, 10:51 PM] Indoo k’auye: ❤❤❤❤❤❤❤❤❤
❣❣❣❣❣❣❣❣❣
❤❤❤❤❤❤❤❤❤
*YAZEED*
❤❤❤❤❤❤❤❤❤
*Na*
*HAPSAT MUSA*
*HAPSYBABY*
*PURE MOMENT OF LIFE* *WRITES*
P.M.L.
151_155
*DEDICATED TO ALL MY* *FANS*😘
Muneera baccin take cikin Kwanciyar Hankali, iskan Fanka yana Kad’ata,
Zumbur naga ta mik’e, Kallon Agogon wayanta tayi
Taga 7;30 am dasauri ta diro daga bisa gado.
Towel tajawo tashiga toilet
Tana fitowa Tahau shiryawa sai data Gama shirin tsaf
D’aure da towel tafito,
Kitchen ta nufa ta Samar cikinta.Karin kumallo
Ruwan zafi ta D’aura Minti biyar yatafasa tajuye su flask da toya wainar kwai
D’aukosu tayi tafito palour.
Zama tayi Kasa d’aure da towel tahau bama cikinta kallachi.
Yazeed yana Farkawa yaga safiya tayi tunda yayi sallar Asuba dayakoma Bacci sai Yanzu ya Farka
Toilet shima yashiga ya brush ya watsa ruwa fitowa yayi yasamar musu Kalachi kafin Muneera ta Farka.
Turus yayi ganinta tsakiyar palour zaune tana breakfast
Tsaye yayi yana kallonta santala santalan cinyoyinta ya k’urama idanuwa
Domin towel d’in data D’aura bakai cinyoyi ba ga gashinta sai walniya yake
Jiyake Kamar yaje ya rungomata
Tanagama yaga zatashiga d’aki
Domin bama tasan yana tsaye ba.
Ta Mik’ewa towel ya kwance Mata
Yazeed Kusa Numfashi D’aukewa yayi ganin halittar da Allah yayi ma Muneera.
Gani yayi tafito cikin wata Arbian Gown yallow tayi rolling da Blue d’in mayafi,
Da jakka A Hannuta.
Basai lokacin da ya isa gareta ba
“Muneera inazaki da safen Haka.?
Kallon shi tayi Sama da Kasa
” Zani makaranta ne.”
“Haba muneera kimanta yau ko kwanakin nawa dakawowane.?”
“Bangane nufinka inta zama bazani school d’in ba komai?”
“Bahaka nake nufi kin Bari ko 1 week kiyi ko.”
“Lalai ma sai natazama ko.?
Toni nadai naji nagyamaka sai natafi kama k’yaleni.”
Wuceshi tayi kawai tafita
Yazeed binta da ido yayi
Karar mota kawai yaji Almun har tafita,
Maida Numfashi yayi Bisa Kujerar palour yadawo yazauna
“Allah kakawo man mafita.”
(Nace Ameen Yazeed domin Yanzu tausayi yakeba😉)
KADUNA STATE UNIVERSITY
(KASU)
cikin Fara’a take Driving har tashiga Harabar school d’insu tayi parking D’in motar ta
Fitowa tayi Jikkarta ta d’auko tayima motar key
Waya tazaro.
“Hello Besty nashigo school fa.”
“Kai Tawan dagaske kike.?
Ko wasa.?”
“Tomeye Kuma na mamaki inki shigo kinganni.”
Datse wayanta tayi tanufi class.
Bata jimaba sai ga Janan.
Kallon mamaki tabita dashi har ta iso inda take.
STORY CONTINUES BELOW

“Tawan meke damunki yau kwana biyu dakaiki gidan miji har kinfara zuwa school.?”
“Ashe nifa matar Aurece ki.?”
Janan bugu takaimata
“Bama kisani ba?”
“Aimantawa nake.”
Janan Kallon ta kawai tayi
Malam ne yashigo shine yakatse Maganarsu suka maida Hankali kan lecture.din daake.
Bayan sungama sunfito ne
Inuwar dasuka Saba zama suka nufa.
Suka zauna
“Tawan Gaskiya Zan Fad’a miki Abinda kike ba dacewa bane fa.”
“Menayi uwar shishigi?”
“Au nice uwar shishigin?”
“To meye inbake ba inhar magana wannan mutum zakiyiman gwara kibarta.”
“Uhumm kamar yadda Allah ya jarrabaci yaya Yazeed dasonki Haka kema zaki Fad’a cikin kogin sonshi lokacin babu taimakon dazan baki tunda ke kafiya gareki.”
Haka suka K’ara shiga lecture sai K’arfe 5 pm sannan suka dawo gajiye Muneera ta shigo gidan gajiye gashi Dama bata ci komai sai wani cake da Ayman tasiyimasu shi.
Jikkar ta aje palour tashiga ciki cire doguwar Riga tayi tashiga toilet ta watso ruwa
Allah Sarki Yazeed lokacin har yafita yaje restaurant yayomasu take a way
Jin Almun tadawo yasa yanufi D”akinta don yakaimata nata
K’arar ruwa yaji Almun tana toilet aje mata yayi yafita yakoma D’akinshi
Muneera tanafitowa daga toilet wata yalolowar Riga ce tasa kawai
Tasa kawai tazo ta D’auki wayanta taje kitchen koza samu Abinda zataci.
Leda tagani Gefen Gadon Bud’awa tayi taga Abinci mai rai da lafiya sai tashin K’amshi yake.
Komawa tayi Bisa Gado tazauna tahauci sai data cinye tas sannan taaje
Ciki. Ranta cewa tayi
“Nasan bewuce wannnan mutum Hmm yana zato Zan so shi tab!”
Tashi tayi tadawo palour tahaye bisa Kujera tahau canza tasa Bollywood tabid’,o
Suna film d’in
Waminall hubbi min k’atal
Tanajin Dad’in shirin tun Gida.
Tana Kallon gajiyar school ta D’ebeta sai bacci.
Yazeed fitowa yayi zashi masallachi kayan Kallo yagani kunne ga muneera tana Bacci rigar duk ta yaye Abinka dama K’aramar Riga.
Jikinta
Basai lokacin da ya iso gareta Muneera jin mutum tayi Bisa jikunta Ana kissing D’inta ta ko Ina
Har Ana wuce gona da iri
Zumbur ta M’ike daga kwannce datake tureshi tayi
“Malam lafiya?”
Maida Numfashi yayi
“Haba Muneera kefa matatace Kuma Ina buk’atar ki.”
Muneera tashi tayi zaune wani Kallon ta watsa mishi Wadda Yazeed Kusa sumewa
Tashige D’aki kawai.
Yazeed binta yayi da Kallon har Tashige. Tashi yakoma yasako Alwalla domin wannan ta kare.
Washe gari Haka muneera tayi shirin school tafito.
Yazeed shima cikin shirin office yafito domin baiga Amfanin zamanshi Gidan ba.
Muneera ko inda yake bata Kallah zata fita
Jitayi yakirata
“Muneera”.
Tsayawa tayi
” Kayi sauri Kafad’i Abinda zaka Fad’i iina sauri.”
“Amm muneera bekamata kifita babu izini ba.”
Dariya naga Muneera tasaki
“Wai Kai mijina nikuma matarka ko.?
To brain d’inka tadaina baka haka.”
Yazeed tuno maganar dayayimata can Baya yayi
Kamar yadda tafad’i mashi.
Kan yadawo Tunani har tafita
Maida Numfashi yayi shima yafito yaja mota yanufi Banki.
STORY CONTINUES BELOW

***************************
*************************
Yazeed HAK’URI kawai yake har yau sun samu 6month da Aure Babu Abinda yacanza tsakaninsu
Ko Dady ya tambaye shi “ya zaman su yake” sai yace mashi lafiya Lau
Haka itama Muneera take cewa. Lafeeya lau.
Muneera zaune take yau weekend babu school tana zaune palour
Dirin ,mota taji bata ko motsa ba tasan Yazeed ne.
Haka har ya shigo ko Kallon inda yake batayi ba.
“Barka da weekend.”
“Mswtt”
Yazeed binta da kallo yayi har ta shige ciki
Murmushi yayi domin har yafara sabawa.
Yau Monday ko nasara na tsoranki, Muneera tana sauri domin yau suna test
Cikin sauri ta shirya tafito
Dai-dai lokacin shima Yazeed yafito cikin shirin office.
Kusan tare suka fito Amma muneera tariga shiga motar ta Amma mota tak’i tashi Ganin zata b’ata Mata lokaci
Ta fito Kuma tasan kanta samu Abun hawa dawuya.
Jitayi Ance
“Shigo Muje.”
Muneera marfin mota ta Bud’e tashiga.
Yazeed yayi mamakin ba tayi Gardama ba tashiga.
Cikin Ranshi wani Dad’i
Ko tafara Karyowa ne.
Har suka isa ba tayi mashi magana ba,Janan dake shigowa itama a motar tare sukayi parking.
Tana waigowa taga Yazeed Kuma muneera ce cikin motar dasauri ta isa.
“Yaya Yazeed.”
Cikin Fara’a ya juyo sai Kace ba Yazeed ba.
“Janan.”
“Na’am yaya Yazeed morning.”
“Kin tashi lafiya Lau?”
Nan suka gaisa ba’angare da Muneera take suka juyo,
Har tabar wajen Yazeed girgiza Kai kawai sukayi bankwana yatafi.
Janan Yazeed tausayi yabata wani haushin Muneera taji koda suka je ko ta Kallon ta batayi ba.
Sadda suka fito
“Besty menayi miki ne.?”
Harara tayi ta nufi motar tashiga
Dama test kawai garesu,
Muneera murmushi kawai tayi tasan maganar
Bakin Hanya tafito,
Jitayi tana sin zuwa Gida taga Dady Mimi Ayman sai Kaka.
Tana shiga dagudu Ayman ta taso “sis kece yau?”
“Sister yau bakije school ba?”
“Bamu da lecture ne sai 2:00pm”.
“OK.”
Mimi cikin Fara’a ta tarbeta kamar ta goyata Nan Mimi tashirya ma muneera Abin tand’e-tand’e, da Kallon mai ciki take mata Ganin yadda tayi K’iba, gawani haske datayi.
“D’iyata baki da damuwa Gidanki?”
“Eh Mimi lafiya Lau.”
“Yauwa Aita Hak’uri
Ya jikin mijin naki?”
Muneera shiru cikin sauri
,tace “dasauki Mimi.”
B’angaren Kaka tashiga
“Kakus.”
Bisa cinya kaka tahaye
“Ke D’agani karki idani.”
“Haba Kakus.”
“Ai Gaskiya ce nafad’a tafi kihau ta mijinki.”
“Taki nakeso.”
Nan sai Kaka ta tambeyata “ya zamanta da Yazeed?” tace “Lafeeya lau”.
B’angaren Yazeed Kuwa ko da ya isa Banki ya shiga office D’inshi yafara Aiki
Cikin shi yaji yana ciwo,
Aaa wasa-wasa yaji ya na K’aruwa, jiyayi bazai iya ba, tashi yayi yashiga motar yanufi Gida,
Yasha maganin da aka ruboto mashi.
STORY CONTINUES BELOW

Yana shiga ciwon ya sake taso mashi, jiyayi bazai iya K’arasawaba palour yazube.
Muneera Dady ya dawo shima yayi Farin ciki da zuwan ta
Ya tambaye ta zaman ta da Yazeed tace “lafiya Lau”.
Kar su Karto wani Abu nan tayi musu bankwana ta tafi
Dady yace “bata Bari mijinta
Yazo D’aukarta?”
“tace tana sauri ta D’ora girki
Cikin Fara’a tafito”.
Ayman ta rako ta bakin titi
Ta samu nepep ta nufi
Gida
Cikin Fara’a tashiga gidan.
Turus tayi Ganin yazeed kwance, wuce shi tayi.
Cikin K’arfin Hali Yazeed
Yace “Muneera Amshi wayar nan don Allah ki karaman zaki ga Ansa Doctor 1 ki kjra man shi.”
Wani ciwo ya taso ma Yazeed
Bai san lokacin da ya saki wayar ba
Muneera Gani tayi bai motsi,
Dasauri ta isa Wajen .
“Yaya Yazeed!!!!!.
Sai Jibi Zan muku typing😜
❤❤❤❤❤❤❤❤❤
*YAZEED*
❤❤❤❤❤❤❤❤❤
Na
Hapsat Musa
(Hapsy Baby)
Pure moment of life writes
P.m.l.
156_160
Wannan page nakune
Ummy Aysha & Fateema Bint Zahra & Fateema Zahra
Muneera dasauri ta iso wajen Yazeed, tab’ashi tayi taji baya Numfashi, dasauri tad’auki wayar da yarda har tad’auke sake kunnata tayi,
Contact tashiga taga Ansa doctor 1, Kira tadanna.,
“Hello Yazeed.”
“Bashi bane Don Allah kayi sauri kazo yanzu haka baisan inda yakeba.”
“Subhanallah Ganin zuwa to.”
Muneera komawa tayi ta tsaya wajen, Yazeed wani tausayin shi ya shigar mata lokaci D’aya.
Batasan lokacin da ta d’auka tsaye ba Muryar Doctor taji Bisa Kanta,
“Madam!!!”
Dasauri tadawo daga tunanin datafi,
“Amm doctor har ka iso ne?”
“Eh”
Nufar inda Yazeed yake yayi,
Nan yabud’e Box din dayazo dashi kayan Aiki yafiddo,
Yafara Auna Yazeed.
Juyowa yayi wajen muneera
“Pls Ruwa nake kikawoman masu sanyi.”
Muneera mik’ewa tayi,
Tanufi Firji ta d’auko mashi Ruwa masu sanyi takawomashi.
Yayyafa mashi Yazeed yafarayi yafara shafamushi A Fuska,
Ahankali yafara Bud’a idonsa,
Biji biji Yafara Gani Ahankali yadawo lafiya Lau.,
“Yazeed.”
“Na’am”
Muneera tanaganin yazeed yadawo daidai tunda yayi magana, jikka ta Da’auka
Jikkar da mayafinta tabar Palour,
“Doctor yakayi kasan banafiya ne?”
Madam ce ta kirani Rikece tace nazo baka lafiya bakasan inda Hankali yake bama.”
“Muneera zata Kira Doctor rikece,
Anya Kuwa itada Bata Kaunata meyasa hakan to.?”
“Yazeed.”
Dasauri yadawo daga tunanin dayatafi
“Inajinka Doctor.”
“Meyasa kayi wasa da maganin danabaka Kuma Kasan nafad’amaka matsalarka ko?”
“Kayi Hakuri Doctor matsala Akasamu Amma bazaasake, insha Allah.”
Nan yakara Dubashi yabud’e Akwatin yabashi wasu maguguna,
Yafad’amashi yadda zai yi Amfani dasu Amma yanzu ya tabbatar da yasha wani Abu mai zafi sannan ya kiyaye.,
Yazeed yace mashi insha Allah
STORY CONTINUES BELOW

Haka doctor yatafi yabar Yazeed jingine da Kujera.
Muneera tanashiga D’aki cire Kayanta tayi tashiga toilet domin wani zafi takeji,
Wanka tayo tahad’o da Alwallar sallar magariba,
Wata rigar Atamafa tasa tada sallar da ita tanagama ta cireta zata D’auko wasu masu sakaf tasa
Yazeed cikin dauriya yana daba Bango yatashi yanufi D’akinta.
Tsaye take Gaban Mirror tana Fesa turare ganin mutum tayi yashigo Dasauri ta jawo Hijabin datayi sallah tasa,.
“Kiyi Hakuri kiganni nashigo ko?
Don Allah ruwan tea nakeso kihad’aman zansha magani,
Doctor yace nasha wani Abu mai zafi please Muneera karki komai don Allah.”
Karaf tana d’ago idanuwanta suka Had’u Dana Yazeed wani yanayi taji Domin tunda take bata tab’a yarda suka Had’a ido dashi ba.
“Kaje D’akinka Zan maka to.”
“Nagode”
Haka yadafa Bango yafita,
Muneera tabishi da ido har yafita saka wata t shirt tasa,
Sai wani wando there quarter,
Kitchen tanufa bud’a flask d’in ruwa zafi taji da zafi sosai,
Cup tad’auka ta fifita tashi yayi yadda za’a sha D’auka tayi tanufi D’akinshi wadda tunda take bata tab’a shi gaba,
Tura Kyau’ren tayi wani sanyaya K’amshi yayi Mata sallama har sai data lumshe ido, komai tsaf_tsaf,
Ciki tashiga taga babu mutum Kurya tashiga Gani tayi Babu kowa har zata Aje tafita taji ance
“Muneera.”
Dasauri tajoyo Yazeed tagani dasauri ta runtse idanuwanta Ganinshi datayi Hakan,
“Ga tea D’in”
Matsowa yayi Daf da ita
Duk idonta yana runtse
Mik’a Hannu yayi ya Amsa yahad’o da Hannuta wani shock taji,.
Tanajin Ya Amsa dasauri tabaro D’akin.
Yazeed Murmushi yayi yazauna Bakin Gado yafara shan tea d’in jiyayi ya gardi sosai kodan muneera tayishi ne?
Muneera Kuwa D’akinta tashige dagudu tafad’a Bisa Gado runtse idanuwanta tayi yadda taga Yazeed wani yanayi taji zata shiga dasauri ta kawar da tunanin
Cikin ranta.
_*Sorry kuyi Hakuri da wannan Gobe zakuji Insha Allah*_
Luv my Fans❤
[5/10, 10:51 PM] Indoo k’auye: ❤❤❤❤❤❤❤❤❤
❣❣❣❣❣❣❣
*YAZEED*
❤❤❤❤❤❤❤❤❤
Na
Hapsat Musa
(Hapsy Baby)
*Pure moment of life writes*
P.m.l.
161_165
_*Hmm narasa Abinda zance gareku D’umbin masoyana dabasan Adadinku ba wallahi nagode da kaunar Ku gareni Inasonku fiye da yadda kuke sona* _*Hapsat* *najinjina gareku*❤💛💓_
Dasauri ta tashi tayo Alwalla sallar isha’i,
Tanagamawa ta linke abin carpet D’in sallar, takaishi mazauninshi, ta canza kaya zuwa sleeping dress tahaye gado ,tajawo Blanket tarufe dashi.
B’angaren Yazeed Kuwa yanagama shan tea D’in da Muneera ta kowa
mashi,
Tashi yayi yacanza kaya yahaye Gadonshi shima.
Kwance yake bisa gado yana bacci A hankali tazauna Kusadashi, Shafa Fuskar tafaray A Hankali, kwanciya tayi bisa kirjinshi,
Ahankali yafara Bud’a idonshi.
K’amshin turarenta yafarayi mashi sallama tusa Hannu shi yayi cikin Gashin Kanta yafara ya matsawa,
“Honey menene?”
Cikin shagwaba tace “katashi muje muci Abinchi my One.”
“Shikenan tashi muje.”
“Uhumm uhumm nisai ka goyani sannan.”
“My Baby kincika Rigima taso nagoyaki to.”
Hayewa tayi bayanshi har suka fito,
Dinning table suka nufa,
STORY CONTINUES BELOW

Bisa cinyarshi ya D’orata yana bata Abinchi Itakuma sai shagwaba take mashi.
Suna gamawa ya D’auketa suka nufi D’aki
Bisa Gado ya ajeta
Kissing D’inta yafara yi Ko Ina maida mashi martani tafarayi ta ko Ina
“I love you my baby.”
“Me2 My Husband.”
“Muneera love you”
Firgice yafarka daga baccin dayake,
Mafarkin dayayi yadawo mashi sabo kamar yanzu Akayi.
“Allah yakawo lokacin da mafarkina zai zama Gaskiya.”
Jiyayi Ana sallar Asuba tashi yayi yashiga toilet, ya d’auro Alwalla yafito yanufi masallachi dake wajen gidansu.”
Muneera dayake itama tasaba tashi tun a gida,Ana Fara Kira itama ta mik’e tanufi toilet ta d’auro Alwalla ,
Tanagama Bisa carpet D’in tabaje bacci yadawomata sabo,
Yazeed Kuwa dama yasan zata tashi domin tungida Dady yanatadasu D’akinshi shima kawai ya shige,
Mafarkin dayayi yake Gani ,
Wani Masifafacen so Muneera yana shigar shi.,
Yana Haka har bacci shima ya D’aukeshi.
Muneera K’arar wayanta ya tada,zumbur ta m’ike tanufi wajen wayar, tana Dubawa taga My Betsy.
“Hello Besty”
“Acikin jakkarki kitafiman da Hand out ko?”
“Wallahi nima sai naBu’da naganshi.”
“OK sai muhad’e school Around 3.”
Nan sukayi bankwana ta kashe wayan
Motsi taji zaa bud’e Kyau’ren D’akinta,
Yazeed ne yaturo K’yauren ya shigo.
“Morning.”
Batayi mashi magana dai
“Yau bazakije school bane.?”
“Sai 3”
“Muneera bazaki Hakura dazuwa ba kinga bani lafiya Kuma Kar wani Abu yafaru bakowa.”
Shiru tayi
“Pleased”
Ganitayi yana matsowa kusada ita,
Jitayi kawai yakamo Hannuta ya Rik’e
“Kin Hakura.”
“Sai naduba naga yiyuwar hakan.”
“Pls kikara Had’ama tea d’in kamar najiya pls Had’a Hannushi yana rok’ata,
Zan sha magani”
“Naji”
“Yauwa”
Mamayartayayi yakamata wani hot kiss A fuska,
Yajuya yafita binshi tayayi da kallo har yafita,
“Me wannan mutum yake yanufi dayaga inajin tausayin shi dabaya lafeeya sai Abinshi yayi yawa.”.
Tagumi tayi sannan tasaki wani nauyayayan Azuciyar
” yanzu inhar baka Kuladashi Allah zai Kamani da laifi kaguma mutunchi Dady da Mimi dakuma Girmansu danake gani.
Zan cigaba dabashi Kulawa Amatsayina na mijina kodan na kauce da Fushin Ubangiji.
Amma badon Akwai d’igon sonshi tare Dani ba”
Mi’k’ewa tayi tanufi Kitchen tadora ruwan zafi,
Kafin sutafasa ta kyankyashe kwai biyu
Tasoya Tanagamawa ta d’auko plate tad’ora
Ruwan sun tafasa tasauke su tajuye flask ta D’auki cups biyu tanufi D’akinshi.
Zaune ta iskeshi yahad’a Kai da Kujera sallama tayimashi,
Yazeed dasauri yajuyo yaga muneera ce koba ita bace ko Kuma kunneshi ne,
Itayagani D’in dai
Har gabanshi ta ajemashi
“gayanan”
Kan yayi magana har tafita.
Palour tadawo tazauna Remot ta Da’,uko ta canza tasha *SUNNATV* tabud’a wa’azin dataji Anayi yatsa tasaya tanaji,
Muneera gani nayi tana Kuka shab’e_shab’e A Fuskar ta
“Allah na tuba Allah kayafeman Assatagafurallah!!!
Astagafurallah!!
Astagafurallah”!!!
STORY CONTINUES BELOW

Waazin datajin Kan Azabar daya tanadar kan masu kin biyayar Aure ne,
Babushi babu rahamar ubangiji da irin nau nau in Azabar daya tanadar.
D’aki tashige. Fad’awa tayi bisa gado takara Fashewa da Kuka
“Allah natuba laifin dana Aikata kayafeman Zan Amshi Aure na Hannu biyu biyu Insha Allah,
Bazan K’ara yarda na Had’u da Fushin Ubangiji ba,
Zan rike Aure na Insha Allah.”
Yazeed mamaki yayi yadda Muneera tayi mashi sallama Wanda ko Arzikin Kallon kirki bai Ciba,
Had’a tea Di’n yayi bud’e plate yagani harda wainar kawai murmushi yayi wani dad’i yanashigar shi
Mamaki meke damun Muneera daga jiya zuwa yau ne?
Duk tawani canza. Tayi sanyi.
“Hello Tawan nashigo Baki shigoba meke Faruwa?”
“Hmm bansamu zuwa besty
In kinfito pls kizo inason ganinki.”
“Lafeeya dai?”
“Lafiya lau”
“OK Zan biyo Insha Allah”
Tashi tayi tafita kitchen tanufa tsayawa tayi mezata girka mashi tunda bai lafiya ko yaji Dad’in bakinshi
Ferfesu tayanke tayi mashi kawai,
Bud’a Firji tayi ta dau’ko Nama tayi daga cikin Firji,
Tad’ora shi bisa tukunya,
Tafiddo cefane ta marakad’a blander Naman ta yanka mashi Albasa tarufe
Shi,
Almun yafara tsanewa taji tadau’ko markad’an Raj yup takara yanka Albasa tasamashi Maggi, curry, citta, tafarnuwa, Dukkan kayan Kamshi daake Sama ferfesu
Nanda Gidan yad’au K’amshi
Yazeed yana D’aki baisan Abinda ke Faruwa ba,
Dawowa tayi palour tazauna.
Muryar Janan taji wata K’ara tasaki wadda Yazeed dake D’aki yafito
Rungume Janan tayi
“Besty bakije school d’in ba?”
“Naje dama Bankai da shiga class ba ne shine nace nima Bari na wuto nan”
“Muneera”
Dasauri tajuya Ganin yazeed ne
Janan yagani
“Yaya Yazeed”
Na’am Janan K’arar Muneera Naji nad’auka wani Abu ne.”
“A,a Murna ce babu Komai”
Muneera itadai babu Abinda tace
Haka Yazeed yajuya yakoma D’aki,
Muneera kamo Hannu Janan
Tayi
“Besty zo muje.”
Bakin Gado tazaunar da ita
“Yau Naji wani waazin Kan miji besty da irin Azabar da Allah ya tanadar da masu kinyi biyaya jikina, duk yayi sanyi besty Naji Zan zidda Dukkan wasu makamin yaki dana D’auka kan Yaya Yazeed.
Nayi biyaya Amma Badon inason shi ba”
“Tawan Nagode Allah dakikagane kinsan Kuma Hanyar dazakibi kikara nunamashi ke bagudajiya ce,
Kuma yar Kauye yadda kogaba yaga masu irin halinshi zai Hanashi
Kawo Kunnenki kiji”
Nidake dau’ko muku rohoto banji Abinda suka Fad’aba
“Anya zan iya besty?”
“Zakiya mana.”
“Kinga nad’ora Ferfesu Bari naje kar yak’one gashi ko ruwa bankawo miki ba.”
Kimanta yau Thursday Ina Azumi Bari na tashi naje
Kinga magariba ta Kusa.
Kiyi Amfani da Maganar danayi maki dai.”
“Shikenan zangwada besty bari nazo”
Janan murmushi tayi tace
“Tawan kenan” ta girgiza Kai
Muneera dawo tayi da K’aramar cooler tace “gashi nan inkisha ruwa kinci kigayar da momy pls.”
STORY CONTINUES BELOW

Haka suka fito tarakata
Ita koma tanufi kitchen ta d’auki cooler tanufi Hanyar D’akin Yazeed.
Ahankali ta tura Kyaure…….
❤❤❤❤❤❤❤❤❤
*YAZEED*
❤❤❤❤❤❤❤❤❤
Na
Hapsat. Musa
(Hapsy Baby)
_*Pure moment of life writes*_
P.ml.
166_170
_*Daku nake kwana daku nake tashi kunsan darajar mutum, ga had’in Kai ka mutata kowa kowa nakune Wallahi*_
_*Wato pure moment of life writes ya Allah yakara had’a kan mu*_
_*Wannan page nakune Dukkan wani members na pure moment of life writes*_
*Luv All*😘
Ahankali ta tura k’yauren D’akin tashiga tare da sallama,
Yazeed ya Amsa mata,
Nufar inda yake
“Yaya yazeed ga wannan pls kadaure kaci don Allah.”
Yazeed Kusan suma zaune yayi,
K’ara murza idanuwanshi yaji ko mafarkin dayasabayi ne.
“Yaya Yazeed meyafaru naga kana murza ido ne.?”
Shiru taji tayi maganar dasu kayi da besty ta tuno, cikin
Dauriya tanufi Kujerar dayake zaune Kusa dashi tazauna.
“Yaya Yazeed meyafaru ne wai?”
“Mafarki nake banaso nafarka dagashi ne.”
” Hmm ba mafarki bane”
Bud’e cooler d’in tayi tasa spoon ciki ta d’ebu ferfesun tayi tanufi bakin Yazeed dashi,
“Yaya Yazeed bud’e bakin nabaka”.
Kamar butum mutumi haka Yazeed yakoma,
Haka muneera tacigaba dabashi ferfusu nan
Tashi tayi tanufi firjin d’in D’akin
Bud’ewa tayi ta fiddo juice,tare daruwa
A cup ta tsiyaya juice d’in tabashi,
” karbi gashi kasha”.
Haka muneera ta shayar da Yazeed
Tissue ta D’auka tagogemashi bakinshi.
Yazeed girgiza kanshi “pls in mafarkina nake na Farka hakanan.”
Muneera mintsilinshi tayi
“Ba mafarki kake ba gaske ne.”
Dariya yayi..
Muneera tashi tayi tadawo kusadashi sunaji bugun Numfashi juna.
“Mekakeso na girka da daddare yaya Yazeed.?”
“Kibarshi wannnan ma dakikayiman Nagode naje restaurant naci.”
Dire dire Kafufuwa tafarayi kamar yaran goye.
“Nidai Wallahi banyarda mijina yaje restaurant yaci Abinchi ba nima inason ladan Ai.”
“Shikenan in Akwai kingin ferfusun ki ida kwasomam shi naci.”
Dariya “tom shikenan bye”
Haka tajuya tabaro D’akin
Yazeed kuwa suman zaune yayi Marin kanshi yayi
“Anya ba mafarki nakeba.”
Jiyayi ba mafarkin yake ba dagaske ne.
“Ni Muneera kema yau kamar daman Akwai shiri tsakaninmu meke Faruwa
Anya ba wani shiri take
Lokaci D’aya Saki jiki Dani.”
Yana tunanin jiyayi Ana kiran sallar magariba ya mik’e yayo Alwalla yanufi masallachi. Cike da mamakin haka.
Muneera tashiga D’akinta
Toilet tashiga tayo wanka
Tafito tare da Alwalla sallar magariba itama tanagama jawo wata rigata tayi doguwar marar nauyi, sakaf
Pink Gabanta tanada kwaliyar blue.
D’aure gashinta tayi da wani blue d’in ribbon
Wow Masha Allah duk da bawata make up tayi ba tayi kyau. Tafeshe jikinta da tureren mai sanyayya zuciya
STORY CONTINUES BELOW

Kitchen tanufa ta ida kwashema Yazeed farfesun cikin cooler
Itakam indomie tadafa kawai tajuye ta cikin plate tadawo palour tazauna tahauci d’auko wayanta tayi takira janan
“Hello besty Na kinsha ruwa lafiya yakuma kika isa gidan ?”
“Lafiya tawan dafatan kinfara aikatawa Abin?”
“Hmm nafara jinake kamar nadaina Besty. Ban iyawa.”
“A,a tawan bakiso kikara kwato yanci kikenan wajenshi.?”
“Inaso mana Besty.”
“Tom kikara Kara kinji ko.”
“Shikenan tom
Sai Monday in muhad’u school”
Nan sukayi bankwana takashe wayan.
Tashiga ta d’auraye yan plate’s D’in datayi Amfani dasu.
Tada sallar isha’i tayi
Shima Yazeed sai tayi sallar
Isha’i sannan yake shigowa
Baya Kamar minti 20 tagama sallah tasan yanzu yadawo daga masallachi,
Cire Hijabi d’in tayi ta d’auko wani blue D’in gyale D’an Karami takara feshe jikinta tanufi D’akin Yazeed.
Iskeshi tayi zaune ya kunna Kallo yanayi sallama. Tayi ta nufi inda yake
“Yaya Yazeed Gashi nakawomaka konabaka A Baki kanaso?”
Yazeed juyowa yakalleta
Muneera sai daji wani irin Abu yanayimata yawo cikin jiki.wannan Kallon dasauri ta kauda Fuska daga kallenshi.
“Yaya Yazeed kallo kake ne?”
“Eh Muneera.”
“Na zauna natayaka?”
“Hmm sai nace bazaki tayaniba Muneera.”
Kusadashi tazauna tana kallon
Bud’a cooler d’in takakawomashi yayi.
Muneera tajuyo takalleshi yadda yakeci A Hankali cikin natsuwa karaf suka Had’a ido dashi dasauri tajuya tacigabada kallo
“Bazakici ba?”
“Nakoshi ni
Yaya Yazeed nakane Kai kad’ai”
“Hmm tom nagode
My wife.”
Haka sukacigabada o
Kallo muneera duk da American film Ake itakam ba gwanar Kallon shiba.
Muneera bacci yad’auke ta Kujerar datake har tafad’a jikin yazeed batasani ba
Yazeed gyaramata kwanciyar yayi jikinshi.
Cikin Wata voice yafara Ki’ran Muneera
“Muneera!!”
“Tashi muje mu kw’anta”
Cikin Almun bacci ta Bud’e idanuwanta
Mik’ewa Tayi
“Good night yaya Yazeed.”
Tajuya tatafi
Binta yayi da Kallo har Tashige rigarshi ya Shaka k’amshin turerenta yaji
Cikin Farin ciki ya m’ike yashige cikin D’aki
Muneera itama tana shiga d’aki tasa rigar bacci tahaye Gado
Asuba tagari
_*Kuyi Hakuri dawannan pls gobe zakujini*_
Luv my fans❤😍😘
[5/10, 10:51 PM] Indoo k’auye: ❤❤❤❤❤❤❤❤❤
❣❣❣❣❣❣❣❣❣
❤❤❤❤❤❤❤❤❤
*YAZEED*
❤❤❤❤❤❤❤❤❤
Na
HAFSAT MUSA
(HAPSY BABY)
*_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
*_P.M.L_*.
171_175
STORY CONTINUES BELOW

_Yazeed yana kwanciya bisa gadonshi Abinda yafaru yau yashiga tariyo harda sarkin b’arayinan wadda yafi kowa iya sata yasaceshi_
*Washe gari*
Muneera ce tsaye kitchen tana Had’a breakfast d’in dazasuyi jin mutum Tayi bayanta kawai, dasauri tajuyo
Yazeed tagani
“Uhum uhumm Yaya Yazeed ka tsorata ni wallahi.”
“Sorry mekika girka ne?”
“Breakfast na nake Had’awa”
“Bari natayaki to”
“A,a yaya Yazeed kabari nayi ni kad’ai Don Allah kaga Aiki nane fa.”
“Uhum uhum ni sai natayaki”
Muneera tsaye Tayi tana Kallonshi yadda yakemata
“Hahaha Yaya Yazeed shagwaba zakayiman?”
“Eh mana”
“Gashi to kayanka man Albasa.”
Gani Tayi yafara nanad’e Hannu riga zai Fara yanka Albasa.
Gani tayi yana yanka Albasa
Dariya takeyimashi wai yana yankar Albasa.
Haka suka had’a breakfast d’insu itada yazeed
D’auko tayi tajera bisa dinning table
Yazeed shidai bin Muneera yake da kallo kawai lokaci d’aya ta canza mishi haka.
Jiyayi spoon daidai bakinshi dasauri yadawo daga tunanin da yatafi
“Yaya Yazeed tunanin mekake ne?”
“Babu komai”
Murmushi Muneera kawai tayi sukafara ci Abinchi.
Muneera satar Kallon Yazeed kawai take yadda yakecin Abinchi cikin natsuwa
Itadai nan ya burgeta.
Karaf suka Had’a ido dasauri takauce da barin Kallon shi
“Yadai kike kallona?”
“Babu komai”
Wayar shi tayi K’ara
Dubawa yayi
“Hello
Morning too
OK ganinan zuwa.”
Mik’ewa yayi.
“Yaya Yazeed inazaka.”
Ana nemana ne A office zanyi singing d’in wasu papers ne kinsa kuma yau Friday banzan D’ade ba.”
D’akinshi yashiga ya canza kaya yafito Muneera tana tsaye batasan fitowarshiba
Wani K’amshi taji dai_dai inda take dasauri ta juyo
Sai ta kusan shid’ewa ganin yadda suit D’in suka Amshi Yazeed
Ash colour ne.
Dasauri ta daidaita natsuwarta.
“Yaya yazeed har kafito ne?”
“Nafito.”.
Amsar jikkar tayi
” muje naraka.”
Haka suka fito har Harabar gidan Muneera taraka shi tadawo
Zama tayi Bisa Kujera tare da tagumi
“Meke damuna nidai nasan bana son Yaya Yazeed biyaya ce kawai nake mashi don nasamu Kaucewa daga Fushin ubangiji sai kuma Don na k’ara kwatar yanci na dacan baya yakirani Bagidajiya, yar Kauye,
Amma kwana biyu nan inajin wani Abu dangane dashi komai nashi cikin natsuwa babu kwarmaniya gashi inason namiji haka.”
Haka tai ta Tunani cikin Ranta.
Wayanta taji yana ringin
Dubawa tayi taga new number ne kin picking tayi
Jitayi Anata Kira dubawa tayi taga 5 missed call
D’agawa tayi.
Shiru tayi batayi magana
“Hello Muneera”
Wani Abu taji dayakirata Haka
STORY CONTINUES BELOW

“Yaya Yazeed Ashe Kaine?”.
“Bakida ma number ko?”
“Afuwan yaya Yazeed”
“Dama hakan nakiraki Ganinan office kewarki ta isheni kwana biyu kisabaman dake”
“Hmm yaya Yazeed kenan”
“Baki yarda ba kenan?”
“A,a nidai ban Fad’aba”
“OK shikenan sai nadawo bye bye” Kiss taji yasakar Mata yakashe wayan
Sagale tayi da waya A hannuta komai nashi cikin natsuwa”
Jitayi itama Gidan yayi Mata wani Kalah kunna Kallo tayi kkawai
Shikam Yazeed yana Kashe wayan murmushi yayi wani Nishad’i na shigar cikin Ranshi tare da Kaunar Muneera. Wadda koda raudha baiji shiba
(Hmm readers kunce wai ya labarin Raudha ne kubiyoni zakuji kotana wace duniya)
12:pm
Yazeed ne yad’auki jikarshi yafito domin duk ranar Friday 12pm time D’in tashin daga office.
Motarshi yanufa yashiga ya nufi Gida domin ya matsu yaganshi Kusada Muneera
Cikin. Nishad’i yake driving Har ya iso Gidan yayi parking din motarshi,
Yashiga cikin
Ga Kallo Anayi Amma Gidan shiru
K’ara shigowa yayi can yaga Muneera remot rike da Hannu Amma tayi Bacci
Murmushi yayi yanufi inda take
Tsugunawa yayi dai_dai Kusa da ita
“Muneera
Muneera”
Ahankali tafara Bud’a idanuwanta
“Yaya Yazeed harkadawo?”
“Eh Dama duk Friday da wuri nake nadawowa”
“Bari nakawomaka juice. Ko”
Mik’ewa tayi tanufi Firji ta d’auko mashi juice Yazeed idonshi yana gareta har tadawo daga D’auko juice D’in.
Ta tsiyaya mashi cikin cup,
“Yaya Yazeed gashi”
“Nagode my Muneera”
Murmushi tayi kawai takoma tazauna Kusada Yazeed,
Baajimaba ya mik’e
“Bari naje nafara shirin tafiya masallachi ko?”
“Agama lafiya”
“Bazaki tayani ba?”
“To Muje”
Haka suka nufi D’akin Yazeed.
“Kashiga nikuma zanfito maka kayan dazakasa”
“A,a Banyardaba har toilet zaki rakani”
Ganin ya tsareta da wannan idanuwanasa Wadda datayarda sunhad’u sai taji wani Abu yanayimata yawo cikin jiki,
”Nidai please kashiga Zan fiddo maka Kayan”
“Nidai A,a saikin tayani uhum uhum”
Hhhhh “yaya Yazeed kaganka kamar wani yaro”
Dakyar yaryada yashiga toilet d’in shi D,aya yanashiga itakuma tanufi ma’adanar Kayanshi,
Wani Farin yadi ne mai laushi Kamar kad’a tafiddomashi taje jeren huluna tad’auka mashi Bak’a,
Sai turare shima tafiddo ta aje Bisa Gado taaje tafito kawai takoma palour tazauna
Yazeed yana fitowa yaga kaya Aje Amma Muneera tafita Murmushi kawai yayi yahau shirya
Kayan dafiddo mashi yasanya wani Nishad’i yana shigar shi
“Wai yau Muneera kezabar Kayan dazansa”
Muneera ta zaune K’amshi tureren kawai taji tasan Yazeed ne Amma bata juyawa ba
Wani tautausan Hannu taji A kafad’arta
“Shine kika fito ko.”?
Uhumm ” to bana fiddo maka kayanka ba”
“Tobaki Bari na shirya”
Zagayowa yayi yazauna Kusa da ita
Muneera Kusan shid’ewatayi ganin kyau da Yazeed yayi Amma b’ata nuna ba,
Kallon ta yafarayi itama batasan lokacin da tazubamashi Nata ba.
Sud’auki Kusan Minute 10 Haka
“Yaya Yazeed lokaci natafiya fa.”
Gwarau Numfashi yasaki
Tare da Mik’ewa
“Bari naje Zan Biya Gida in Antashi”
“Adawo Lafiya kagaidaman Mimi, dady, Kaka, Sister Kace nayi missed nasu All”
Lakutar Mata Hanci yayi
Ni d’an Aike kine. “
“Tonazo Muje sai Nafad’a musu?”
“A,a
Muje kiyiman rakiya waje”
Haka suka fito tarakashi yaja mota yatafi itakuma takoma ciki.
Zama tayi bisa Kujera tsintar Kanta kawai tayi tana Murmushi ita Kad’ai jitayi Gidan ma yayi Mata Fad’i.
Yazeed shima haka ya tsinci Kanshi yana murmushi shi Kad’ai
Anatashi daga masallachi yanufi Gidansu
Palour ya iske Mimi da Kaka
Kusada Kaka yazauna
“,Granny Kina lafiya?”
“Meye Kuma garani?”
Hhhhh “bakisani ba”
“Kasan Banason wannan shegatartaka”
“Kiyi Hakuri kar Dady yaji to”
Yana dariya yafad’i Haka
“Mimi inayini”
“Lafiya lau Yazeed ya wajen y’ata?”
“Lafiya lau take”
“Kakus Muneera tace nagaisheki tace natafo dake ma”
.
“A,a tabari sai ta Haihu nazo naga ai tubarakallah ansamu rabo”
Mimi tashi tayi tabar Palour saboda Kunya,
Yazeed Sosa Kai kawai yayi
Suna Haka saiga Dady yadawo shima daga masallachi.
Haka suka zauna
Can saiga Ayman tafito daga D’aki
“Yaya Yazeed kaida sister kukazo?”
“Bakisan inda take ba ne?”
“Daga tambaya yaya Yazeed tokaje Dani nayi muku week end??
” A,a kibari sai wani Week D’in”
Cikin shagwaba tabar palour
Haka Yazeed cikin Farin ciki yabaro Gidansu,yanufi Gidanshi dominyak’agagara yaga Muneera
Yanashiga yaga batanan K’amshi Girki yaji yasan tana Kitchen
Kitchen D’in Yanufa…
Kitchen d’in yashiga A Hankali Ganin yadda tamaida hankali tana girki Ahankali ya lallabo ta bayanta ya rufemata idanuwa murmushi tayi kawai domin K’amshi tureren shi kawai yasanar da ita,
“Yaya Yazeed har kadawo?”
Dawowa yayi Gabanta ya tsaya
“Ya akayi kikasan nine?”
“Yaya Yazeed nasan baka wuce Kai ne kuma…”
“Kuma me?”
“Babu komai.”
“Uhumm uhum nisai kinfad’aman”
“Babu komai fa.”
Matsowa yayi daf da ita kowa yanajin Numfashi kowa.
“Fad’aman”
“Nafad’a maka Bari na ida girkina kar yak’one”
“Ina tsaye kina girki Dani za”ayi barikiga ma mezan miki yanzu?”
“Yaya Yazeed yanzu kadawo fa kabari na ida kingin Kad’an fa”
Duk dahakan sai natayaki fa
NaK’i wayonki yarinya”
Haka Yazeed ya ida taya Muneera girki Har suka Gama cikin Nishad’i
Shiga D’akinshi yayi yacanza wasu Kayan
Fitowa yayi,
Muneera kuma tana shirya Abinci A dinning
“Nidai natafi masallachi sai nadawo”
“Yaya yazeed sai kayi sallar isha’i sannan zaka dawo?”
“Eh mana”
“Shikenan ‘A dawo lafiya”
Bataji tahowarshiba jitayi Ansakarmata kiss A kunci kawai.
“Sai nadawo.”
Binshi tayi da ido har yafita
“Tafiyar shima Abin Kallo ce jiyadda yake yinta cikin natsuwa.”
Bisa Kujerar dinning d’in tazauna tagumi tayi
“Meyasa kwana biyu nan in inatare da Yaya Yazeed nakejin wani Abu yanayiman yawo?
Inkuma bayanan sai Naji babu D’adi?”
Haka Muneera tai tunani jitayi Antada sallah yasa itama mik’ewa tashiga ciki tayi watsa Ruwa tayi tafito da Alwalla tada sallah,
Itama tanagama tanufi wajen kayanta wata rigar Atamfa ce ta d’auko
Tasa Rigar babu D’ankwali kawai ta d’aura bisa K’anta,
Turaruka tadau’ko ta feshe jikinta dasu dawo palour tayi tazauna Ta kunna Kallo
kafin Afara sallar isha’i
tana zaune taji Ankira sallar isha’i,
Kashe Kallon tayi tashiga ciki dama da Alwallar ta
Tadawa kawai tayi,
Bayan tagama ne ta linke Carpet D’in sallar tare da Hijab D’in datayi sallar takaisu ma’ajinsu,
Takomo palour tazauna bata dad’e dazama taji K’arar Bud’e Kyaure tasan Yazeed ne Amma bata d’ago Fuska jitayi bai karasoba
D’aga idanuwanta tayi taga ko ya shiga D’aki ne
Taganshi tsaye
“Yaya Yazeed menene zakayi tsaye Bakin k’ofa?”
“Bakece Baki taso kika tarbeni ba.”
Gwalo Fuska tayi Almar mamaki
“Kai Yaya Yazeed yanzu sai nataso na tarbeka?”
“Eh mana”
STORY CONTINUES BELOW

Canza Fuska tayi kalar tausayi
“Kayi Hakuri wani Abu nataka A kafana yanzu.”
Basai lokacin da yakarasoba
Tsugunawa yayi kusada. Ita
“Meye kikataka
Wane kafane daga ciki?”
Wani Abu taji yanayimata yawo kama K’afar dayayi yarike Mata,
“Tashi muje Asibiti”
Dariya yaji tanayi
“Nayimaka wayo kakaarso dai”
“Lallah dama babu wani ciwo ko?kikasan narikece ko”
Kama kunnenta yayi
“Wash Yaya Yazeed da zafi fa.”
“Kinkara?”
“A,a natuba Bazan sake ba Allah”
Sakin kunnen yayi
Muneera Mik’ewa tayi
“Yaya Yazeed Kasan Abinci kai Kad’ai fa yake jira.”
“Tom muje.”.
Haka suka jera A bisa dinning table
Muneera tajawo Cooler tazuba Yazeed
Ajemashi tayi
Kallon ta yayi
” Banganeba ke bazakiciba?”
“Kaci kawai naci nima.”
Turo plate D’in yayi
“Yahaka Yaya Yazeed?”
“Nima bazanciba tunda bazakiciba”
“Tom zanci Bari nazuba”
“Tare nakeso muci nidai.”
Kallon shi
“Shikenan muci.”
Spoon ta d’auka tafari itama
Can Yazeed ya Aje spoon yakura ma Muneera ido
Tana D’agowa taga yana Kallonta itama kallonshi tacigaba dayi sun Kusan minute 15 Haka suna Kallon junan su
Tare suka Saki wani naunayan Numfashi
“Muneera”
Cikin wata murya yafad’i haka
D’ago Fuska tayi
*”ILUV YOU MY MUNEERA*”
Sadda K’anta kasa tayi jaji takasa yi mashi wata magana
Ture plate D’in tayi
Yazeed Kallon ta yayi
“Meye zaki ture plate?”
“Yaya Yazeed nakoshi.”
“Banyardaba kici konayimiki D’ura Allah.”
Zaro ido tayi
“D’ura Yaya Yazeed.”
“Eh mana don Haka ki ida ma cinyeshi Allah.”
Uhumm “Allah nak’oshi”
Mik’ewa taga yayi zaidawo kujerar datake
“Zanci to”
“Ki Makaro sai na ida Baki kuma.
Taso nan na ida Baki” haka yahad’ata da jikinshi yabata Abinchi niyyar Kuka yaga tanayi mashi,
“Allah nidai nakoshi.”
“Shikenan to Ai kinci dayawa. Amshi ruwa kisha.”
Abaki yabata ruwan.
Sunagamawa Kuma
Suka dawo palour suka zauna
Can Muneera tafara Hamma
“Yaya Yazeed inajin bacci.
*GOOD NIGHT”*
Haka ta Mik’e tanufi D’akinta
Yazeed binta yayi da kallo har tashige cikin Ranshi yace “tom me take nufin dahaka da Rana zatayiman komai Amma da dare yayi zata tafi D’akinta.”
Shima jin Kallon yayi Wani ba dad’i kashewa yayi ya tafi D’akinshi
Muneera tana shiga tasauya Kayan bacci ta haye Gado Amma me sai kuma ta nemi bacci tarasa a idonta
STORY CONTINUES BELOW

Yadda suke Rayuwa da Yazeed cikin kwanakin yafad’omata cikin rai
Wani dad’i taji yana shigarta
“Ba shakka cikin kwanakin nan nima zuciyata tafara fad’awa cikin son yaya Yazeed.”
Rintse idonta ta tuno yadda yake nuna mata soyayya kalah kalah.”
Sai tasamu kanta dayin murmushi ita Kad’ai kawai
Taja Blanket ta rufe Jikinta
Yazeed shima yana shiga tasauya Kayan bacci yahaye Gado ya kwanta Amma me shi yakasa bacci saboda kewar Muneera dayake jiyake dama yajita jikinshi suna bacci tare dayafi kowa Murna dahaka har bacci yad’aukeshi.
** ** ** ** ** ** ** **
** ** ** ** ***** **
Muneera tsaye tanagama shiryawa yau Monday tafiya school tafito tanajiran Yazeed domin har yanzu tun ranar ba a gyaramata motar ba
Kamar Kullum K’amshi tureren shi yasanar da ita dashi
Zuwanshi Lumshe ido tayi kawai Kafin ta Bud’e jitayi An dafata yayi
“Taso muje muyi breakfast D’in Haka Yakama Hannuta suka nufi dinning Kallon ta yayi
” yau ma inabakici dayawa D’ura Zan miki”
Haka sukagama Breakfast d’in suka tashi
Haka suka fito makale da Juna
Muneera ita wani Lokacin batasan lokacin da take Mak’a lemashi ba.
Haka suka shiga mota tare har cikin School yashiga
Daidai lokacin Janan tashigo har tayi parking ma
Motar Yazeed tagani yasata tsayawa yana zuge mirror D’in motar Abinda yabata
k’ara bata mamaki Ganin yadda suke dariya
Gani tayi Muneera ta Bud’e murfin motar ta fito ta sunkuyar da Kai tayi mashi
magana
Sannan yaja motar yabar Harabar school D’in
Duk tana tsaye tana Kallon su
Gani tayi Muneera zata fiddo waya kuma tasan ita zata nemata
Dasauri ta nufi wajenta.
Muneera jitayi Andafata daga baya dasauri tajuyo
“Besty kifa nad’auko waya nake bid’a”
“Ai Ina Kallon Ku tund’azu keda Yaya Yazeed fa “
Murmushi Muneera tayi
“Zomuje Class in muka fito Akwai magana.”
Janan dariya tayi “bashakka Muneera itama tafaraFad’awa cikin soyayya.”
“Besty.”
“Na’am Tawan”
“Wani Almu ake gane kanason wani?”
Janan tace
“Yawon Kallon juna
Kiji wadda kikeso kiji, bakisan yayi nisa dakai,
Farin ciki kodayaushe in yana kusadake,
Kulawa,
Kyautatawa,
Hmm ” Besty babu shakka to zuciyata tafara fad’awa cikin son Yaya Yazeed Bazan boye maki komai ba.”
Janan dariya takeyi har Muneera ta kulu
“Meyehaka zaki tisani Gaba kina Dariya.”
“Kefa dakanki kikace bazaki tab’a sonshi ba”
Hmm bakarya nafad’i hakan Amma Yanzu nakaryata kaina. “
“Tawan nagode Allah dakika dawo Hanya Musababin Baki shawarar ranan kenan Kuma nagode Allah tayi Amfani.”
Muneera tace “Gaskiya kuma gashi tayi Amfani nagode Allah da kika k’ara dawo Dani Hanya.”
Suna zaune wayan Muneera tayi K’ara tana dubawa taga kowaye murmushi tayi tad’auka “yaya Yazeed.”
Janan ta tsaye tana Kallon ikon Allah har Ayman ta K’araso wurin Janan nuni tayimata da Hannu datayi shiru
Tanagamawa taji sun d’au
Tafi
Dasauri ta juyo tagansu
“Meye Haka don nayi waya da Mijina” dariya suka Kara D’auka
K’arfe 5:30 pm suka tashi daga school Janan da Ayman sai muneera suka fito har wajen dakowa yayi parking
STORY CONTINUES BELOW

“Sister kishiga muje mana naga Baki shigo da mota ba?”
“Kije yanzu Yaya Yazeed zai zo d’aukana.”
Kafin tarufe Bakin sai Gashi ko”
Aika ma junansu Sakon murmushi sukayi
Janan da Ayman sai Kallon su suke
“Yaya Yazeed.”
“Ayman yakayi?”
“Babu komai Ina yini.”
Haka itama janan ta matso suka gaisa dashi
Yada’auki Muneera sukabar Harabar school D’in
Haka suma su Ayman sukaja suka tafi
Suna isa Gida tazube Bisa Kujera
“Wash nagaji yaya Yazeed”
“Bari nayimaki tausa to”
Dasauri ta M’ike “Aa nagode”
Tashige cikin D’aki Yazeed yabita da Kallo har tashige ciki,
Kamar Kullum suna zaune palour da daddare suna Kallo
Muneera bacci yad’ebata har ta Fad’a Bisa Yazeed
Fara shafatayi Ahankali jiyayi yafara shiga wani situation
Muneera ta Bud’e Idonta
“Yaya Yazeed Good night.”
Bata duba yanayin dayake cikiba ta nufi D’aki
Yazeed shima Mik’ewa yayi yanufi D’aki Amma me yakasa kwanciya kwata kwata
Soyake yaji Muneera jikinshi
Fitowa yayi yanufi D’akinta
Tunowa yayi tana masifar tsoron mage
Daidai window D’akinta yaje
Itakuma lokacin ta Kwanta
Kukan Mage tafara ji dasauri ta mik’e zaune domin babu Abinda ke bata tsoro duniya Kamar mage
Kara jitayi dasauri ta Mi’ke ganin inuwar tayi ta gifta
Dasauri tanufi k’ofa tabud’e
D’akin Yazeed tanufa buga mashi k’ofa tayi dasauri
Yazeed saidayabani dariya ganin yadda yataso kamar mai Bacci,
Yana Bud’ewa Muneera tafad’a jikinnshi
“Yaya Yazeed mage”
Kara rukukemayayi
“Mage Kuma?”
“Eh Kukan tanaji Wallahi
Kuma naga giftawarta”
Kara kwantar dayayi Bisa kirji shi K’ara tusa kanta ciki Abinka da ma duk gashi ne kirjin Yazeed
Riketa yanufi Gado da ita.
Luv My Fans❤🌷🌷
[5/10, 10:51 PM] Indoo k’auye: ❤❤❤❤❤❤❤❤❤
❣❣❣❣❣❣❣❣❣
❤❤❤❤❤💕❤❤💕
*_YAZEED_*
❤❤❤❤❤💕❤❤💕
Na
Hapsat Musa
(Hapsy Baby)
Pure moment of life writers
P.m.l
181_185
Yazeed rungume da Muneera yanufi Gado da ita rad’amata yayi cikin
“Kiyi Hakuri kibar kyarma kinji My baby tatafi kuma kinga na rufe k’ofar”
“Uhumm Yaya Yazeed Kasan yadda nake tsoron mage jinake kamar zata iske Wallahi”
K’ara shigar dayayi ita kirjinshi “yi bacci bazata zoba kinji ko My dear.”
Muneera ko k’ara shigewa tayi kirjin Yazeed kamar zata koma ciki
Ahankali yazeed yafara shafar kanta kamar yarinyar goye,
Yazeed saukar Numfashi tayaji dubawa yayi yaga bacci har ya d’auketa Kara rukukemeta kamar wani zai kwace mashi ita,
“Allah nagode maka daka nuna man wannnan ranar yau ga Muneera Kusa da ni”
STORY CONTINUES BELOW

Lumshe ido yayi yak’ara gyara musu kwanciya A haka har bacci yad’aukesu.
Mak’ale da juna
Ahankali yafara tada
“Muneera Muneera tashi muyi sallar”
Ahankali tabud’a idonta
Maidasu zatayi takoma Bacci
“Muneera Asuba tayi ki tashi muyi sallah sai ki koma baccin”
“Uhumm Ka Kyaleni pls bacci nakeji.”
“Anyi Haka Dole kitashi in Mungama sallar kin koma baccin”
Yaye Blanket d’in dasukayi rufa yayi
“Tashi mana”
Dakyar tatashi tana murza ido Almun baccin bai isheta
Tasauko daga Bisa Gadon
Hanyar fita yaga tayi
“Inazaki ne?”
“Zani D’aki ne nayi sallar ko.?”
“OK.”
Fita tayi tanufi D’akinta Yazeed duk yana binta da kallo har tafita,.
Toilet yashiga shima yayi Alwalla yanufi masallachi,
Itama tana shiga ta shiga tayo Alwalla ta tada sallar tata
Tana idarwa tayi Addu’a tashafa tadau’ke carpet d’in sallar
D’akin Yazeed takoma domin tsoron mage yanan bai tafiba
Tana tura Kyaure tahaye Gado tajawo blanket tarufe sai bacci wani sabo yad’auketa.
Yazeed yadawo daga masallachi yaniyyar hawa gado Kafin lokacin tafiya office Yayi
Mutum taji yanaduba yaga Muneera
Murmushi Yayi
“Duk tsoron mage sallah tayi ta dawo kenan uhumm Muneera manya.”
Haka shima yakwanta bacci yad’aukeshi.
7:00 am
Yazeed farkawa Yayi yaga 7 :am mik’ewa Yayi yaga Muneera bacci take kasarika cikin Kwanciyar Hankali
Mik’ewa Yayi yanufi toilet
Muneera Sama_Sama taji Almun ruwa dasauri ta mik’e kallon Agogo tayi taga 7: 5
AM
Dasauri ta diro daga Bisa Gadon,
“Yaya Yazeed har yashiga wanka. Bari naje na had’amashi breakfast”
Tafita daga D’akin
Kitchen tashiga
Ta D’ora ruwan zafi,
Nandai tahad’amashi Breakfast tafito tajera A dinning D’akinta ta Nufa ta watsa ruwa wata doguwar rigar marar nauyi tasa,
Bata d’aura d’an kwali ba tafito,tufke Gashinta kawai tayi tafesa turere marar K’amshi sosai
D’akin Yazeed tanufa iske wa tayi ya shirya zai Fesa turare dasauri ta isa gareshi ta Fesa mashi
“Morning yaya Yazeed.”
Kamota Yayi yahad’a da jikinshi
“My Beautiful wife kin tashi lafeeya?”
“Uhumm kafini sani tunda tare dakai na kwana.”
“Namanata fa to Bari nak’araji”
Hugging natayayi yahad’a da jikinshi Bakinta ya Nufa yafara Aikamata da Kissing ta ko Ina.
Muneera kuma takasa Hanashi
“Yaya Yazeed lokacin tafiya office nayi gashi bakayi Breakfast fa”
Ta firgita daganin yadda Idanuwanshi suka canza lokacin d’aya
Kama Hannushi tayi suka fita shikam yakasa magana A Kujera ta zaunar dashi
Had’a mashi tea mai Kauri tayi ta Mik’a mashi
Itama ta Had’a Nata
Shiru ya ratsa tsakaninsu sai kallon juna suke,
“Yanaga bakiyi shirin school ba?”
“Sai 11 zanshiga ne”
“Kuma kinga baayi gyaran Motan taki ba jiya na kira Engineer d’in
Yanzu yazakiyi?”
“Karka damu Yaya Yazeed nakira Besty ta wuto ta d’aukeni”pm”K’arfe nawa zaku tashi ne?”
”5:30 pm”
STORY CONTINUES BELOW

“Sai nabiyo nad’auki kenan”
Gyad’amashi Kai tayi kawai
M’ikewa Yayi Muneera d’aukar Jikka tayi suka fito
Readrs inkuga Muneera da Yazeed sai Ku d’auka sun dad’e suna soyayya nan
Gakuma matukar dacewa da sukayi da juna,
Har Bakin mota ta rakashi zai Bud’a yashiga jitayi An sakar Mata wani Hot Kiss A kumatu
“Bye bye My Muneera”
Sagale tayi tana Kallonnshi har yafita daga Harabar gidan
Juyawa tayi takoma cikin
Bisa Kujera tazube shafa inda Yazeed yasakarmata Kiss tayi
“Bazanyi K’arya ba shakka nima nafad’a cikin Son Yaya Yazeed *INASONKA YAYA YAZEED*”
Tunanin yadda yake bata kulawa dayan dayake nunamata so yasa ta murmushi tare da wata Kaunar shi dake shiga cikin Jikinta.
Palour tadawo tazauna d’aukar wayanta tayi
“Hello Besty”
“Tawan yane?”
“Motana na wuri gyara Kuma yaya Yazeed yafita kinga Aikin safe ne kuma mu sai 11 zamu shiga shine nace ki biyo tanan mu wuce”
” OK babu damuwa”
Nan sukayi bankwana ta kashe wayan.
Yazeed driving yake cikin Nishad’i basai nafad’a ba readers kunsan komai ya kema Murna.
Ahaka har ya isa office Yayi parking, d’in motarshi. Inda Ake
Takamar Yazeed tanan fa babu inda tatafi Amma Gaban Muneera babu ita
Ahaka har ya isa office D’inshi
Gyare kamar kullum sai K’amshi yake,
Aje jakar yayi Bisa table yanufi Kujera yazauna
Sectary ce ta shigo
“Morning Sir”
“Morning”
Mik’amashi Files tayi
Tayimashi bayani tafita,
Bud’asu yafarayi yana singing,
Muneera tana zaune palour
Tana Aikin tunanin Mijinta,
K’arfe 10:30 Am taga tayi mik’ewa tafara shirya Kafin janan tazo ta isheta da Mita,
D’akinta tashiga tad’aura towel tashiga wanka
Tana fitowa taji Almun Ana knock tasan Kuma janan ce Fitowa tayi tanufi wajen ta bud’emata, tana Bud’ewa
“Kinajin Ina knock tund’azu Amma baki bud’eman ba”
“Sorry Besty saboda mitarki na shiga wanka nan da wuri fa”
Haka suka shigo palour suna magana
Janan Bisa Kujera ta yada zango tazauna,
“Bari na shiga na idar ko”
“Ki idar dawuri kinsan malam d’inan basshi da sauki dayarigamu shiga shikenan.”
“Karki damu yanzu kuwa.”
Haka muneera tashirya cikin sauri domin tasan malamin basshi da mutunchi
Wata Atamfata Riga dazane pink and ash ta D’ora Hijab ash hmm basai nafad’a ba duk da ba kwalliya tayi tayi kyau
Turare ta Fesa wadda bashi da K’arfi wadda ita kad’ai zataji kamshi Abunta A matsayin na matar Aure
Domin bai daceba macen Aure ta Fesa turare mai K’arfi wadda wani namiji zaiji K’amshi shi ba A Addinin musulci babu kyau
D’aukar wayanta tayi da jakka tafito
“Tashi muje na idar.”
Janan ta M’ike sukafito
Suka shiga mota sai school,
Suna shiga Bada jimawa da shiga class d’in sai ga malamin yashigo domin basshi d’aukar raini ko kad’an sai Kace Dr Ahmed (ciwon so)
STORY CONTINUES BELOW

Bayan sunfito daga lecture ne wani wajene inda babu hayaniyar student suka zauna,
“Besty Wallahi Karatu inbaka dage kasa zakaganka k’asa war warsa saboda Wahala”
“Hmm Allah yataimaka kawai”
Wayar Muneera tahau K’ara tana dubawa taga Yazeed wani murmushi tasaki Kafin tad’auki wayan
“Hello Yaya Yazeed”
“My Muneera ganinan zaune office nakasa komai face tunininki Pls Muneera *KIYAR DA DANI* (Maman Ahmed)
Wallahi Ina k’aunarki *KECE FARIN CIKINA* (Aunty Khady) pls help me my Muneera”
“Yaya Yazeed I LUV YOU”
dasauri ta kashe wayan ta fad’a jikin Janan
“Aaa D’adi komai?”
“Besty inason yaya Yazeed Wallahi cikin kwana ukku yasakarmani da kaunar shi cikin raina”
“Allah yabarku tare ko Tawan”
Yazeed yana jin wannnan maganar zaune yake sai da yamik’e “hello Muneera” sai yaji shiru “tabbas Muneera tafad’amashi tana sonshi
” Allah Nagode maka yau muneera tace tana sona
Yana zaune cikin Murna dubawa yaga time d’in tashin su muneera yayi daga school jikkarshi yajawo yad’auki abinda zai d’auka yafito,
Karfe 5: 30pm sukatashi daga school suna tsaye da Muneera sai janan da Ayman saiga Yazeed yazo wata matsanaciyar kunyar Yazeed tashigeta Ahaka sukayi bankwana tashiga mota
Tunda tashiga batayi mashi magana yazeed sai satar Kallon ta baimata magana ba har suka isa Gida,
Suna isa tabud’e tafita
Yazeed murmushi yayi yabi bayanta kawai “Kinga man komai tunda kin furta kinasona”
Muneera tana shiga ta aje jakkar da hijabin tadau’ra towel tashiga toilet, tawatsa ruwa,
Yazeed shima D’akinshi yashiga yacire kayan yashiga wanka
Yana fitowa yaji yana ra’ayin coffee d’akin Muneera yashiga yace tahad’amashi Kafin yadawo sallah
Yana tura Kyaure yaga tafito d’aure da towel tsakar D’akinta mutuwar tsaye yayi duk Batasan da shigowar shiba,
Tanufi wajen mirror taje gashinta tafarayi tad’auki Mai tafara shafama Jikinta
Yazeed jiyayi bazai iya tsayuwa ba jikinshi na kyarma yakoma d’aki Gadon shi yahaye cikinshi yaji yafarayi mashi ciwo yafara mukurkusa Muneera tanagamawa taji Antada sallah Alwalla tayo tada sallah
Har Aka Kira isha’i tamaidata bata fita domin tasam Yazeed sai Angama sai dawo
Palour tafito tana kallo
Tana zaune Agogo ta kallah taga har 8:30pm
“Meya yaya Yazeed yake har yanzu baidawo ne?”
Tashi tayi tanufi D’akinshi
Taga koyadawo batasaniba
Tura Kyaure tayi tashiga ciki
Turus tayi Ganin mutum kwa’nce Bisa Gado dasauri ta isa Gareshi
“Yaya Yazeed meyafaru naganka kwa’nce?”
Yamutsa Fuska yayi Almar yanajin ciwon dakyar yayi sallar isha’i da magariba,
“Ban lafiya Muneera”
“Meyasameka yaya Yazeed?”
Muneera Dasauri Kuka tafara
“Muneera kuka Kuma?”
Yi shiru kinji ko naji sauki sorry my honey”
Tare da jawota jikinshi
“Muneera”
Cikin wata murya yakirata
“Na’am yaya Yazeed”
“Tashi kiyo Alwalla muyi sallah”
“Yaya Yazeed nayi sallah ni.”
“Wannnan dabam take jekiyo kinji ko”
Muneera mik’ewa tayi tanufi D’akinta tayo Alwalla shima yazeed dakyar ya mik’e yaje yayo Alwalla suka tada sallah
STORY CONTINUES BELOW

R’akaa biyu sukayi yazeed yadafa kan Muneera yayi Mata Addu’a kamar yadda dai Addinin musulci yakoyar da mu.
Yazeed sunagamawa d’aukar Muneera yayi yanufi Bisa Gado Muneera jikinta yafara kyarma
“Yaya Yazeed bacci zanyi”
“Muneera kece magani na pls kitaimakaman Don Allah”
“Yaya Yazeed wane taimako?”
Wani sako yafara Aikamata sako dayasata tayi shiru
Asuba tagari yazeed da Muneera…..
❤❤❤❤❤❤❤❤❤
*YAZEED*
❤❤❤❤❤❤❤❤❤
Na
Hapsat Musa
(Hapsy Baby)
Pure moment of life writes
Pml
186_190
Yazeed cikin wani yanayi ya kurama Muneera ido datake bacci wata daraja yaji takaru jikin zuciyar tare da wata matsanaciyar kaunar ta
A Hankali yafara tada ta
“My Muneera tashi muyi sallah”
Bud’a idonta tayi taganshi zaune dasauri ta maida su tarufe taja Blanket zata lullube da sauri ya janyeshi
“Tashi zakiyi muyi sallah fa”
“Tom kaje nizan tafi D’akina nayo ko”
Duk fuskarta tana lullube take wannnan Maganar
Murmushi yayi ya mik’e yashiga toilet yayo Alwalla,
Muneera mik’ewa tadiro daga Bisa Gado wata k’ara tasaki takoma tazauna, tareda Fashewa da kuka,
Dasauri Yazeed yafito ko idar da Alwalla bai yiba yafito
Yanufi wajen Muneera
Datake Kuka Bil haqqi
Rungumota yayi da jiki
“Meyafaru my munee?”
“Zafi daza sauko daga Bisa gado”
D’ora Bisa kafad’arshi yayi
“Shikenan yishiru kinjj daina Kuka zai daina muje nak’ara Had’a miki ruwan zafi da dettol”
D’aukar ta yayi kamar yarinya yanufi toilet da ita yahad’a ruwan zafi da dettol sannan yasata wata K’ara tasaki tareda runtse ido
“Sorry My Munee”
Haka tana Kuka har ruwan suka salllace sannan ya kyaleta tayi Alwalla yakuma d’aukata yakawota Bisa gado
“Bari nayo Alwalla sai nafito muyi sallah.”
Yanayo Alwalla yafito ya shimfid’a musu carpet suka tada sallah,
Suna gamawa kuma sukayi Addu’a yakuma d’auketa ya maida Bisa Gado
Muneera sai Ajiyar zuciyata take,
“Sorry my wife kinji ko Allah yayi miki Albarka zai daina kidaina Kukan pls”
Haka yaita rarrashinta Har Bacci yad’auketa kuramata ido yayi yana Kallon ta murmushi yasaki wadda ni Hafsat mai d’auko muku rahoton bansan ko na meye ba Amma kutambayi Sadnaf zata sanar muku.
Rungumota yayi
“I love my wife I love you so much”
Haka har bacci yad’aukeshi shima
Wayar yazeed keta k’ara cikin Bacci ya tashi yad’auki wayar dake Bisa looker yaga secretary d’inshi ke kiranshi
“Hello”
“Morning sir”
“Morning.”
“Sir K’arfe 11:am naga baka shigo ba ne wasu baki suna son ganinka tun 10:am”
Dasauri ya kalli Agogo dake D’akin yaga 11
“Sorry kibasu Hakuri sai gobe munhad’u yau Bazan samu damar zuwa ba namanta bankiraki bane.”
“OK no problem”
Yadatse wayan yakalli Muneera bacci kawai take Hankalinta kwa’nce
Saukowa yayi daga Bisa Gadon ya zira jallabiyanshi yagyra Muneera kwanciya yafita,
Kitchen yanufa yahad’a musu kalaci,
Haka yahad’a tea mai kauri tare da wainar kwai yanufo d’aki ajesu yayi palour yashiga ciki yatada Muneera,.
A Hankali yazauna yad’ora Muneera Bisa cinyar shi
STORY CONTINUES BELOW
“My Munee tashi muyi breakfast”
Ahankali ta bud’a ido taganta Bisa cinyarshi dasauri ta zame daga Bisa takoma Bisa pillow,
“My Munee tashi kiyi Breakfast fa”
Jintayi yi shiru batayi mashi magana
D’aukar ta yayi yanufi toilet kawai yayimata Brush,
Suka dawo palour Bisa jikinshi yad’orata yahd’a tea mai kauri yad’an fifita yarage zafi yafara bata A baki kauda Fuska tayi
“Allah Kima maido Fuskar nan sai na ida bakishi.”
“Ni na koshi fa”
” Kima yi Hakuri ki idar kinji my Baby”
.
Haka har ya ida bata sannan yahad’a nashi yasha
“My Munee”
“Inajinka”
“Meyasa tund’azu kinki yarda my had’a ido ne?”
“Bakomai”
“Uhumm”
Kallon Agogo tayi dasauri ta zabura zata Mik’e cikin runtse ido takoma tazauna
“Yaya Yazeed
11:,15 am yau nayi miss d’in
Lecture”
“Nima bakiga ban fita bane munyi late kisan Abinka da sabon Ango”
Dasauri ta m’ike tana d’angishi tafita daga d’akin ta nufi tana
Har ta Kulle Yazeed ya binta da Kallo Murmushi yayi kawai ya gyara zamanshi Bisa Kujera cikin wani Nishad’i da Fara’a
Ahaka har ta isa D’akinta d’aukar wayanta tayi dake Bisa Dressing mirror tayi
Missed call d’in Janan tagani da Ayman,
Dasauri tadanna Janan Kira
“Hello Besty”
“Wai meke Faruwa ne tund’azu inata call d’in ki no Answer ne?”
“Sory my Besty wayan nan d’aki ne nikuma banan.Ina gun Yaya Yazeed.”
“OK mai miji naga baki shigo school bane I hope lafiya”
”Wallahi tashi nayi da head ache ne”
“Ayya Allah sawakka “
“. GobeInsha Allah zanshigo” nan sukayi bankwana ta kashe wayan
Takira Ayman tace bazata samu shigowa ba sai gobe
Bisa Gado takoma tazauna tana tunanin Daren jiya da irin kulawar da Yazeed yayimata wata Kaunar shi taji tana shigar ta.
Hannu taji bisa kafad’ar ta dasauri ta bud’e ido Yazeed tagani.
“My Munee mekike tunani?”
Sadda Kanta kawai tayi tana wasa da zoben Hannuta
Kusada ita yazauna
“Nifa bangane wannan kunyar tawa dakikejiba Gaskiya. Daidai kunneta yasunkuya ya rad’a Mata wata magana,
Dasauri Muneera tad’ago sai ga Hawaye shar Afuska
” pls Yaya Yazeed don Allah kayi Hakuri.”
“To Adaina jin kunya inbahaka” yakashemata ido
Muneera cikin kuka tace “kayi Hakuri don Allah.”
Jawota yayi Jikinshi ya D’ora Bisa kafad’arshi
“Shikenan kiyi shiru kinji my sweet nadaina fad’ar hakan”
Sharemata hawayen yayi
“Tashi Muje palour”
Palour suka fito Muneera bisa jikin Yazeed datake k’wance shafa Kanta yake kamar yarinya tab’a jikinta yayi yaji yazafi rau.
“My Munee zazzabi kike tashi muje Asibiti.”
“Yaya Yazeed kabani parcetemol nasha zata sauka.”
D’aki yanufa yad’aukomata magani da ruwa yabata Tasha
STORY CONTINUES BELOW

“Sannu baby na kinji ko”
Suna zaune nan palour har Akayi sallar azahur nan cikin Gida yayita bai fita ba
“My muneera mai zakici ne na girka miki?”
“Yaya Yazeed banason komai”
“Baby kidaure kifad’i Abinda kikeso kinji”
”Zan shan Tea kawai”
”Shikad’ai “
Gyad’a mashi Kai tayi
D’aki yakoma kingin ruwan flssk yatsisiya ya had’amata mai Kauri haka yai tabata abaki.
“Yaya yazeed ina son Ganin Kaka dasu Mimi sai dady pls.”
“Kiyi Hakuri zan Kai kinji ko.”
“Wallahi nayi missing nasu fa”
“Zakije very soon baby kikara warwarewa.”
Sunan zaune palour har Akayi isha’i wajen k’arfe 8:30 pm Muneera tanajikin Yazeed
“Yaya Yazeed bacci nakeji.”
“Tom tashi Muje Mu k’wanta”
“Ni D’akina Zan k’wanta fa”
“Tsoro nakikeji.?”
Dakyar Muneera tayarda suka nufi D’akin Yazeed
Da tsoro ta hau gadon,
“Baby babu Abinda Zan miki ki kwantar da Hankali d’inki”
Jawota yayi jinkinsh Muneera tuntana jin tsoro har bacci yad’auketa
Yazeed saidai yaji saukar Numfashi ta Almun bacci yad’auketa
Murmushi yayi
“Baby rigima”
Sun tashi kamar yadda suka Saba sukayi sallah suka koma bacci
7:00am
Yafarka daga bacci
Kitchen yanufa yahad’a musu breakfast yanufi toilet yayi wanka
K’arar ruwa yatada daga bacci
Mik’ewa tayi ta nufi d’akinta taji jikin Nata dasauki yau Amma bata ida warwarewa
Yazeed yana fitowa yaga Muneera batanan yasan tatafi d’akinta
Tanashiga tashiga wanka tafito tana cikin shiryawa saiga Yazeed yashigo yana zuba k’amshi yake,
“Yaya Yazeed morning”
Dafa Kafad’arta yayi
“Morning my munee inazaki kitashiri haka.?”
“School ko Yaya Yazeed
“Keda bakki lafiya my munee”
“Naji sauki Ai”
“A, a pretty kibari kikarajin sauki kinji ko.”
“Uhumm ninaji sauki”
“Tom yau Akwai K’ari kenan?”
” Akwai Yaya Yazeed don Allah kayi Hakuri pls”
“Shikenan taso muyi Break sai muwuce inada baki suna jirana”
Haka suka jero suka fito sukayi Breakfast Yazeed duk Abaki ya bata muneera tun tanaji Kunya har tadaina dai.
Suka Gama ta nufi d’aki tad’auko Hijab D’in ta da jakka yaja su yakaita school
Yanayi parking
“My Munee ki Kular man da kanki kinji ko.”
“Nima ka kulamar dakanka.”
Ta bud’e murfin zata bita
“My Munee”
Juyawa tayi jitayi yakaimata wani kiss da kumatu Dasauri tafito
“Yaya Yazeed bakka da dama”
“Haka kika ce ko zamu had’e Gida”
Tab’e Fuska tayi
“Kayi Hakuri pls.”
Uhumm Ummm N’aki Hakuri.”
Yakwawayi Muryar ta
Cikin Nishad’i sukayi bankwana yabar Harabar school D’in
Cikin murmushi tajuya ta nufi cikin class bata d’ade da zama sai ga janan tashigo itama sufara d’aukar Karatu,
STORY CONTINUES BELOW

Sai k’arfe 12:30 pm suka fito sukoma k’arfe 2:00
“Wallahi Tawan yunwa nakeji Muje captria naci Abinchi.”
“Besty yau kuma da yunwa kikazo ne?”
“Bantsaya nayi Break bane shiyasa”
Kan Hanyar zuwa suka had’u da Ayman suka wuce tare
Muneera coke kawai Tasha
Suka taso suka tafo
K’arfe biyu suka nufi masallachi sukayi sallah kowa yakoma class,
Suka cigabada da d’aukar lecture,
K’arfe 5:00pm
Suka tashi daga school d’in
Muneera tafiddo wayanta kiran Yazeed tayi lokacin yana aiki yana dubawa yaga
*MY BABY* dasauri ya d’auka
“Hello baby.”
“Yaya Yazeed Antashi school gashi kuma 5 yanzu lokacin tashinka bai yiba Zan hau Nepep natafi.Gida“
“Shikenan MY BABY amma dole A gyara miki motinki don Banason Hawan nepep d’ina.”
“Sai kadawo.”
“Inadawo mezaki bani?”
“Babu komai”
Wata magana yayi Mata dasauri ta datse wayan tana murmushi.
Bankwana sukayi da janan
Tatafi tana sauri ne
“Sister Mimi da Kaka sunce kwana biyu kiyi musu strike”
“Allah sarki mimina jiya nace ma inason zuwa yace nakara Hakuri zanje.”
“Hmm shan love d’in ne baa dainanba”
Bugu takaimata
Nan ta tsaida nepep sukayi bankwana tatafi.
Tana isa Gida taaje jakkar ta shiga ciki ta d’aura towel tashiga wanka,
Tana fitowa bata shafa mai wata Riga ce gajera tasa
“Bari naje ko jallof ce nahad’a yaya Yazeed Kafin yadawo.”
Kitchen tashiga tayi markad’e A blander tad’aura girki Nan da Gida yad’au K’amshi
Cikin minute 10 tagama D’auko coleer tayi tajuyeta Duka takashe cooker gas d’in tad’auki cooler tafito,
Taaje Bisa dinning
Takoma palour tazauna
K’arar mota Yazeed taji
K’arar Bud’e k’yauren taji
Shiru taji tasan cewa zaiyi sai ta taso tarbeshi Kanta duke ta mik’e
Yahad’a da Jikinshi ya rungume Haka suka iso yana rungume da ita,
“My Baby nagaji Muje nayi wanka”
“Pls kaje Yaya Yazeed”
”Uhum saikin rakani”
Dakyar ta rarasheshi yashiga wanka Anfara K’iran magariba tafita taje tayi sallah
Shima Yazeed yana fitowa yazura jallabiya yanufi masallachi,
Kamar yadda yasaba sai anyi sallar isha’i yadawo
Yatarrada Muneera palour tana Kallon
“My Munee”
“Yaya Yazeed har kadawo Muje ka Abinchi kaci.”
Haka suka nufi dining suka ci Abinchi suna ciyar da juna.
Har lokacin bacci yayi suka tafi suka k’wanta.
*AFTER 1 MONTHS*
soyayya Ake zuba ba Kama Hannu yaro tsakanin Yazeed da Muneera Yanzu tadaina kunyar shi kula take dashi Kamar me,
Zaune yake palour yana Kallon Muneera ta fito daga d’aki bisa jikinshi ta k’wanta
“Uhum uhum”
Shafamata bayayi
“Menene?”
STORY CONTINUES BELOW

“ICE CREAM nakeso”
“Yanzu Munee baki ganin dare yayi ne? Kibari sai gobe.”
Direre Kafafuwa tafarayi zata Fara Kuka
“Shikenan kiyi Hakuri Bari natashi nasiyo maki karkimam Kuka”
Jallabiya yazira yad’au key d’in mota yafita yasiyomata
Yafito daga siyan ice cream d’in ne yaga wata Mace nad’aga Hannu Bakin titi kamar bazai tsaya ba
Yayi parking yafito
“Pls taimakan zakayi mota na ne yasamu matsala malam kadubaman”
Jiyayi kamar yasan mai murya nan Amma bai kawomashi ita bace
“OK Muje nagani”
Dasauri tajuyo
“Yazeed!!!!
Shima yajuyo Raudha!!!!!
WATA SABUWA INAFATAN KURIKE KOWACECE RAUDHA
INKU MANTA RAUDHA MATAR YAZEED TAFARKO
LUV MY FANS😘❣
[5/10, 10:51 PM] Indoo k’auye: *YAZEED*
Na
Hapsat Musa
(Hapsy Baby)
Pure moment of life writers
P.M.L.
191_195
Dasauri Yazeed yace
“Raudha kece?”
“Nice yazeed”
Cikeda mamaki yace meyakawoki. Nigeria ne?”
“Uhumm Yazeed kenan maganar mai tsawo ce”
Gyad’a Kai Almun bai damu ba “Muje nagaka motar taki My munee tana jirana nakaimata Ice cream.”
“Yazeed wacece kuma Munee?”
“Matata ce.”
Haka suka nufi wajen motar duk yaso motar ta tashi taki tashi
“Gaskiya wannan motar sai taga Engineer duk wani Abu dazanyi taki tashi”
Kallon Agogo yayi yaga har 9:15pm
Yasan muneera nacan najiranshi k’ila har tayi bacci ma
Raudha tana tsaye tana kallonshi
“Gashi kuma dare inbazaka damu aroman Wayanka nabaro wayana Gida nakira azo Ad’aukan”
Zaro wayan yayi ya Mi’ka Mata
Takira
Number tasa takira
number momyn ta Akan Akira driver yazo yad’auketa
M’ika mashi tayi
“Yazeed”
Juyowa tayi yakalleta
“Don Allah kayi Hakuri akan abinda yafaru Yazeed kayafeman”
“raudha karki damu ninayafemaki Abinda kikayiman kingin kuma tsakanin ki da mahallacinkine”
“Nagode Yazeed”
“Karki damu raudha yanzu kid’auka Tamkar komai ba faruba
Inasauri zani Gida my munee tana jirana.”
Wani D’aci taji yaziryaci zuciyarta akan Ambatar Muneera dayake.
“Shikenan
Yanzu kabani Number wayanka tunda kana saurin tafiya wajen my Munee ko?”
“Wallahi Kuwa rigima tasaman sai nasiyomata Ice cream”
Cikin sauri yabata number wayar don ta kyaleshi kawai.
Yaja motar yatafi har yakulle Raudha tana Kallon shi
Bada jimawa saiga Driver anturoshi Yad’auketa
Yazeed yana isa yayi parking d’in motar shi, yayimata key yashiga ciki,
K’arar kayan Kallo yaji dasauri ya isa wajen Muneera wadda bacci yad’auke Bisa Kujera
Ahankali yafara tada
“My munee tashi ga ice cream D’in nasiyo maki”
STORY CONTINUES BELOW

Ahankali tafara bud’a idonta
Dasauri ta janye jikinta daga nashi
Dasauri ya matsa gareta
“My muneera menene?”
“Uhum bakaine ba tunda kafita sayen Ice cream D’in kadad’e ba tun d’azu Ina jiranka”
Muneera cikin kuka tak’arasa maganar
“Oh my god”
Jawota yayi jikinshi
“Kiyi Hakuri mota ne ta tsaya fa sai Dana gyara Am sorry my preety”
Uhumm uhumm
“My dear sorry gashi kisha kizo Muje mu kwanta.”
“Nakoshi ni”
Zaro ido yayi
“Haba my Munee yanzu fa kika tadani nafita nasiyo maki shine zaki ceman kin koshi”
“Uhum bakaine ba katafiyarka kadad’e ba Ina ta jiranka”
Jawota yayi ya had’a da jikinshi
“Nafad’a miki Abinda ya tsaida ni fa am sorry my pretty”
D’auko robar Ice cream D’in yayi ‘
“Bud’a bakin nabaki.”
Bud’a bakin ta tayi yafara bata duk tana jikinshi
Har ta koshi
“Tom Bari nakaimaki sauram Acikin Firji ko?”
Gyad’a mashi Kai kawai tayi
Yazeed zuwa yayi yasa shi A Firji dawowa yayi yazauna Kusada ita “tom Aje A kwanta ko tashi muje.”
D’aukar ta yayi kamar baby girl yanufi d’aki da ita
Shinfid’ar da ita sama Gado
Yacanza kayan bacci
Yazo zai hawa gadon ne wayanshi tafara ringing yana dubawa yaga new number
“Kowaye Bazan d’agaba sai gobe yanzu lokacin my munee ne”
Kashe wayan yayi baki d’aya
Jawo Muneera yayi yahad’e da jikinshi yaja musu Blanket
Muneera Kara shigewa tayi jikin yazeed domin yanzu har tasaba kwanciya bisa kirjinshi ahankali yafara shafata kanta kamar yadda yakemata kullum
Bada jimawa yaji saukar Numfashi ta har bacci yad’auketa
“Hmm My Munee rigima”
Tunani yafada
“Tom meya kawo Raudha Nigeria ne itada dake Malaysia”
Tuna yadda yayi silar rabuwarshi da ita yayi
“Allah nagode maka da kayiman zabi mafi Alkairi
Kuma Bazan Kara bijerewa maganar iyayena ba domin naga isharar hakan nakin bin umurnin su naje nayi zaben tumun dare”
Addu’a yayi yashafa musu baki d’aya yakara kankame muneera a jikinshi kamar zaa kwace mashi ita
B’angaren Raudha Kuma har yazeed ya kulle da motar shi tana Kallon shi jitayi wani Kuka sai dasauri ta shige motar Kuka kawai tana tuna baya har suka isa Gida bud’e murfin motar kawai tayi tashige ko takan
Momyn dake zaune palour batayi ba tashige D’akinta
K’ofar tayi ma key haye watayi bisa gado ko takan takalmin kafar ta bata bi
“Wayyo na cuci kaina a Rayuwa yazeed Wallahi inasonka har gobe babu wani namiji cikinta in bakai ba duk namijin danayi tarraya dashi babu wadda Yakama k’afar ka wajena I love you my Yazeed”
(Nace kin makaro babu kowa cikin zuciyar yazeed yanzu kamar my Mune)
Batasan lokacin data d’auka tana Kuka ba dasauri ta Mik’e kamar a tsunkeleta paper D’in dake Hannu ta ta bud’a har tafara jikuwa da hawaye dasauri ta d’auki wayanta tasa number takira
Jitayi tashiga Murna tafara zata k’arajin sweet voice D’in yazeed
Amma sai taji ba’a d’aukaba
Kara trying tayi Amma sai taji switch off
Sai datayi Kira yakai 50 duk maganar d’ayace switch off
Wurga wayanta cike da haushi da taik’achin Haka har bacci yad’auketa hakan Bisa Gadon cike da son Yazeed (Wata sabuwa)
Yazeed yafarka kamar yadda suke tashi sukayi sallar Asuba
Suna gamawa muneera tadubeshi
“Yaya Yazeed Zan sha ice cream”
Zaro ido yayi “my munee shan ice cream yanzu?”
STORY CONTINUES BELOW

“Eh”
Tsayawa yayi yana kallonta cike da mamakin shan ice cream d’inta
“Uhumm uhumm kad’aukoman nidai”
Tashi yayi yabud’e firjin ya ida d’aukomata kingin d’ayar
Robar yakawomata
“Gashi to”
Amsa tayi tafara sha tsaye yayi yana Kallon ta har ta shanye shi duka
“Muneera wannan shan ice cream naki na Lafiya ne ko
Daga jiya zuwa yau kin shanye roba biyu?”
“Lafiya lau yaya Yazeed jinake shi kawai nakeso Wallahi.”
Haka suka koma bacci Kafin lokacin tashin su yayi
K’arfe 7:00 am suka Farka
Yazeed yashiga toilet itakuma Muneera ta fita ta had’a masu break sannan ta shirya,
Tana Kamallawa tashiga toilet tayo wanka tafito tashirya wata gown ce tasa baka, tayi rolling da yellow D’in mayafi,
Wow Masha Allah kunga wani kyau da Muneera tayi ga wani Haske tak’ara
Fitowa tayi tanufi d’akin Yazeed dayan yafito suyi Breakfast,
Tana shiga ta iske har ya shirya shima dasauri ta isa gareshi bud’a Hannu yayi tafad’a Bisa jikinshi,
K’amshi Jikinta yafara shak’a wani yanayi yaji yana shiga dajin K’amshi tureren Jikinta
“Yaya Yazeed time natafiya Muje Muyi Breakfast ko?”
“Shikenan my wife muje”
.haka suka jera suka nufi dinning table don sunyi breakfast
Muneera tana fara ci ta ture
Yazeed binta yayi da kallo
Dasan kona meye
“Yaya Yazeed Wallahi Bazan iyaci ba nakoshi”
“Mekikaci dazakiciman kin K’oshi”
“Zuciyana Naji tana tashi Wallahi Amai zanyi”
“Kid’aure kici kinji my muneera ko ruwan tea d’in ne”
Tana yamutsa Fuska tafara shan ruwan tea d’in mik’ewa “Bari nad’auko jakana.”
Wayan Yazeed ta d’auki k’ara
Number jiya ce yagani
Picking yayi
Baiyi magana ba
Dagacan B’angaren
“Hello Yazeed Raudha ce”
“OK yakike”
“Lafiya lau katashi lafiya”
“Lafiya”
“Jiya nakira ka tashiga Naji kuma switch off”
“Eh time d’in matana ne bana d’aga wayan kowa inabata time d’inta”
Wani yawu tahad’a mai d’aci a makoshinta
“Shikenan Zan k’iraka Anjima nasan yanzu ma kana Gabanta ko?”
“OK”
Datse wayan yayi
Dai_dai lokacin Muneera tafito
“Yaya Yazeed nagama muje”
Haka suka fita suka nufi makaranta Daganan ya wuce office
Yana ajeta yawuce office itakuma tanufi class itada janan suka Fara d’aukar lecture suna fitowa taji kanta yana ciwo ga wani jiri datakeji.
Dakyar take komai har janan da Ayman ta Lura da Muneera
“Tawan wai meke damunki haka?”
“Wallahi besty kasala kawai nakeji da jiri”
“Sannu”
Haka dai karfin hali har ta suka Kamallah lecture d’in
K’arfe 4:pm. Suka tashi
Kiran Yazeed
“Hello Yaya Yazeed plz zanbi Ayman gidan inason ganin Mimi dasu kaka”
“Kwanan fa ki kaje my pretty”
Kamar zatayi kuka “pls don Allah kaga sai kawuto nan da daddare sai mutafi Gida ko “
“Shikenan Akula wajen driving nasan Ayman dagudu da mota bani itama”
Mik’a mata wayan tayi
“Hello Yaya Yazeed”
“Kibaman Mata Ahankali nasan ki da tukin ganganci”
“Angama Yaya Yazeed “
Kashe wayan tayi sukayi bankwana da janan tashiga motar ta itakuma itada Ayman suka shiga mota suka nufi gida
Cikeda da Murna tashiga
Mimi tana zaune ta idar da sallar la’asar
“Y’ata ta kaina sannuki dazuwa”
Dasauri ta isa Wajen ta
“Mimi na Ina yini” “lafiya lau
Y’ata Nan Aka wuto ne”?
” Eh mimi nayi missing nakune”
“Nima nayi kewarki my dota”
Kinyi sa’a yau d’an Gidan ki akayi Ayman jeki d’auko muku shi kitchen “
“Wallahi Mimi dama yunwa nakeji”
Mimi Kallon Ayman tayi
“Aidama baki da Aiki sai cin Abinchi naga mijinki”
“Kai Mimi”
Nufar kitchen tayi ta d’auko musu Abinchi
“Mimi Bari naje B’angaren Kaka nafito”
“Shikenan jeki fito”
Ayman tace “nima Bari nashiga wanka kawai nashigomana da Abinchi nan wajen kaka”
“OK “
B’angaren kaka tanufa tunkafin ta isa tafara
“Kaka kaka”
Kaka dake palour zaune tace
“Wanake keji kamar Jumallah”
Tsayawa tayi “Kai kaka don Allah kidaina Kira da Jumallah Muneera zaki ce”
“Bana Kira Jumallah zance”
Zumboro baki tayi
Ta isa Wajen Kaka
Saman cinyar ta hau
“Miss you my Granny”
“Kinsan bagane wannnan Maganar nake ba”
Muneera dariya tayi Kai
“Kaka cewa nayi kewarki”
.”tokiyiman yaren dabazan ganeba”
Haka suka dinga fira can sai ga Ayman tashigo da Abinci
“Sister sakko muci Abinchi”
Muneera sakkowa tayi Ayman tazuba musu
Muneera tana Kai lomar Farko wani Amai taji yatasomata,
Dasauri ta Mi’ke ta nufi wajen duk Abinda taci dasafe sai data maido
Wani yunkuri yasaske Kamata
Kaka da Ayman suka fito
Ruwa Kaka ta Mik’a Mata Amshi Kuskuren bakin naki Amsa tayi ta Kuskure bakin
“Sannu sister”
Tana tashi wani jiri yad’ebata dasauri Ayman ta tarbeta”
Takamata suka shiga ciki
D’akin Kaka tanufa da ita
Kwanciya tayi “sister jaman bargon sanyi nakeji ki kasheman Ac pls”
Ayman kashewa tayi tafitadaga D’akin.
Kaka Tana zaune
“Kwanciya tayi ne?”
“Eh taceman tanajin sanyi”
“Tom Allah sawakka”
“Bari naje Kafin ta tashi”
Sungumar cooler d’in tayi ta nufi ciki
“Ayman yakika dawo da Abinchi ne?”
“Mimi munfara ci ne Muneera tafara Amai tana d’akin Kaka ta kwanta”
“Tofa Allah sawakka”
Karfe 6pm
Yazeed yashigo Cikin Gidansu mimi iske plour
“Mimi inayini.”
“Lafiya lau Yazeed”
Waiwaye yayi
Mimi Ina Ayman d’in da Muneera? “
“Ayman tana can wajen Muneera B’angaren inna
Wallahi Muneera ba lafiya!”
Dasauri ya Mik’e Mimi” meyasa meta?”
Bai tsaya jin Amsar ya nufi B’angaren Kaka….
Bai tsaya jin Amsar Mimi ba yanufi B’angaren Kaka,
Mimi binshi tayi da Kallo tayi murmushi irin na manya,
Yana shiga d’akin Kaka ya iske da Ayman a Palour
“Kaka inna Muneera?”
Kajika bakaga kowa sai ita “zaka Fara tambayata to tana d’aki kaji mai Mata”
D’akin Kaka yashiga Gadon ta ya Nufa yahaye sama
Bud’a blanket d’in da Muneera tayi rufa yayi tab’a jikin yayi yaji da zafi
“My Munee”
Ahankali tafara bud’a idonta
Shigewa tayi cikin jikinshi
Takara narke mashi
Ahankali yafara tab’a jikinta
“My Muneera meya sameki ne?”
“Inacin Abinchi da nida Sister kawai Amai yatasoman sai jiri, da zazzabi”
“Sannu kinji my Munee”
“Yaya Yazeed Zan sha Ice cream”
“Ice cream My Munee”
“Eh”
“Shikenan Bari natashi nasiyo maki shi dai zaki sha?”
K’ara shigewa tayi jikinshi domin K’amshi tureren shi wani d’adi yakemata yanzu
Rungume yayi yak’arayi
“Menene my baby?”
“Uhum bakomai”
“To Bari naje nasiyo maki”
Tashi yayi ya shimfid’ar da ita
Kiss d’inta yayi “bye bye my baby”
Muneera lumshe idonta tayi tanajin d’adin turaren Yazeed
Yazeed yana fitowa ya
“Mai Mata har kaganta bamu cinye ta ba ko”
Yazeed dariya. Yayi
“Kaka matana naganta kuma har naji sanyi ga ajiya Akara kulaman da ita zanje nadawo”
“Wallahi Yazeedu bakaji ko”
“Nidai Bari naje nadawo nasiyimata Abinda takeso “
Ayman dariya take musu kawai har yazeed yafita motar shi yashiga yanufi yasiyoma Muneera ice cream,
Roba Biyar yasiyo don ya Lura daga jiya wani shan ice cream take
Haka yawuce kaka Ayman batanan,
Yanashiga D’akin yaganta ita da Ayman,
Ayman tanaganin yazeed yashigo tatashi tabar D’akin
Nufar gadon yayi
“My Munee ga ice cream d’inan nasiyomaki ko”
Bud’a Mata roba Guda yayi
Matso da ita yayi jikinshi “matso nan nabaki”
Muneera dama Haka takeso tajita jikinshi K’amshi tureren shi kawai takeso
Yana cikin bata ice cream d’in wayarshj tayi K’ara yafiddo daga Alhjihu
Yana dubawa yaga Raudha ce wadda yagane number daga jiya zuwa yaganeta saboda Matsa mishi datake
Tsoki yaja ya maida wayan
Aljihu
“Yaya Yazeed meyafaru kake tsaki”
”Babu komai sha ice cream d’in”
Haka Yazeed yaba Muneera ice cream ta shanye duka
“Wannan Bari nasamiki A firjin d’in Kaka kan mutashi tafia ko?”
“Yaya Yazeed Mukwana nan pls”
Wani kallo ya watsamata wadda ita kad’ai tasan Ma’anar shi
“Bari naje sallahr magariba sai Anyi sallahr isha’i Zan dawo danawo sai mutafi”
“Yaya yazeed nima tadani nayi sallar B’angaren Mimi zantafi”
“Tashi to muje”
Haka yakamata tana cije baki suka fito Kaka bata Palour tashiga tayo Alwalla’
B’angaren Mimi suka shiga ya wuce masallachi Muneera tashiga d’akin Ayaman wadda yazama Nata ida kad’ai yanzu
Tana shiga ta iske Ayman rik’e da waya tana chart bugu takaimata
“Kitashi lokacin sallar magariba kizauna sai zuba chart kike”
STORY CONTINUES BELOW

“Wannan bugu dakika yimanani har kinsamu lafiya jiki ina mijin naki?”
“Yatafi masallachi sai Anyi sallar isha’i sai dawo”
Muneera nufar toilet tayi ta d’auro Alwalla tana fitowa Ayaman tashiga ta d’auro tata itama
Suka tada sallah
Muneera d’aukar Alqur anin da Ayaman ke Karatu tayi tafara Karatu bata Gama ba sai da Aka Kira sallar isha’i sannan tarufe tatashi tayi
Bayan tagama. Hawan Gadon tayi
batada d’ade da kwanciya bacci ya d’auketa nan sama Ayaman ta juyo zatayi Mata magana taga bacci take
Rike baki tayi
“Bacci yanzu daga kwanciya kuma”
Fitowa tayi Palour ta iske Mimi tana Kallon wani shiri da ake karfe 7 saura zama tayi
“Ayman ya wajen Muneera d’in”
“Mimi tana d’akima fa har tayi sallah ma daga kwanciya har bacci ya d’auketa fa”
“Tom Allah yakaro lafeeya”
Bada dad’ewa sai ga Dady da Yazeed sunshigo dayake shima dady baima shigowa sai An Kamallah isha’i sannan yake shigowa
Apalour suka zauna
“Dady”.
Na’am Ayaman Ina Yar uwar taki ne?”
“Tana d’aki Bacci takeyi ne.”
Sunan zaune Anjima kad’an yazeed mik’ewa yayi kawai yashiga d’akin
Dady da Mimi murmushi kawai suke
Dady kam wani dad’i yakeci
Burinsu. Ashe zai cika na had’a ya’ya’nsu yau ga Yazeed yana murna da auren Allah kenan.
Yana shiga ya iske Muneera tana niyyar Fitowa Palour maidata yayi
“Keda bakida k’arfin jiki Ina zaki ne?”
“Uhumm nasan dady yanzu yake dawowa zanje na Ganshi ne”
Rungumota yayi suka nufi gado
“My baby kinsan nayi missing naki over
Kissing d’inta yafarayi ta ko Ina
Tashi yayi yasa k’ofar key yadawo wajen Muneera .
Sai dayaji ya gamsu sannan ya kyaleta
Muneera yadawo daidai
” sannu kinji My Munee”
Tashi yayi ya had’ a Mata ruwan wanka yad’auketa yashiga da ita yayo Mata wanka sannan shima yashiga ya tsarkake jikinshi.”
Yafito daga wajen Muneera yadawo da har Bacci yafara d’aukarta.
“My munee”
Tab’a ta yafarayi Ahankali tafara bud’a idonta
“Tashi muje wajen Dady Daganan sai mutafi Gida ko”
A Hankali tafara sakkowa daga bisa gado suka nufi Palour
Mimi suna zaune suna Kallon news,
Muneera Kusa da dady taje durkusa
“Dady barka da dare”
“Y’ata”
“Na’am Dady”
“Anzo lafiya lau”
“Lafiya lau dady”+
Nan yaita janta da fira
Mi’kewa yazeed yayi
“Dady zamu tafi”
“Yazeed bazakarbata ta kwana ba bata lafiya fa”
“Mimi taji sauki fa.”
“Kibarshi yatafi da matarshi”
“Shikenan Allah yakiyaye”
Nan sukayi bankwana sannan suka nufi B’angaren kaka
Itama tana zaune Palour tana Kallon labarai duk da ba fahimtar mesuke takeba
“Kaka Kallo kike ne?”
Kallon yazeed da Muneera dake shigowa Palour tayi
“Ku kuma kamar bindi da jela”
Dariya kawai sukayi Yazeed ya bud’e Firji ya ida d’auko ma Muneera ice cream d’inta suka fito sukayi bankwana da kaka suka tafi.
Cikin mota ko suna tafiya saida Muneera ta shanye wata roba ta Ice cream.
STORY CONTINUES BELOW

“Wai My Baby Anya wannnan shan ice cream na lafiya ne?”
“Lafeeya lau Yaya Yazeed”
Suna cikin tafiya wayar yazeed tayi K’ara D’auka
“Ina Driving”
Yakashe wayan
Raudha tsaye tsakiyar D’akinta rike da waya
“Me Yazeed yake nufi basshi da lokacin nane dazan Kira wayanshi zai man haka”
Wani sabon son Yazeed taji yana shigarta jikkar tanufa tabud’e banilin naga tad’auko takafa Kai ta shanye
Can tafara fita hayyacinta
Tafara sambatu
“Yazeed inasonka wallahi dole nasake zama matarka Karo nabiyu wallahi nawane Kai d’aya bana wata shegiya ba
Muneera kuma suna shiga sukayi shirin bacci suka nufi d’aki
” yaya Yazeed inazuwa. “.
Durowa tayi ta nufi Palour ta nufi Firji d’aukar roba ice cream tad’auka takoma
Bakin gado takoma tazauna,
Yazeed tun Abinda yana bashi mamaki Har dai yadaina tashanye duka sannan takoma jikin yazeed sai bacci yadafeta shima yayi add’ua yaja musu Blanket.
Washe gari
Sun tashi da Asuba sunyi sallah suka koma bacci sai
Karfe 10:00 am suka tashi yau babu schoolMuneera ta nufi kitchen ta had’a musu breakfast tana Cikin soya kwai taji zuciyata yana tashi dagudu tafito Kafin ta iso sai Amai
Dasauri Yazeed yanufi Wajen ta
” my Munee Amai kike”
Muneera kasa Magana tayi
Babu komai Cikin Cikin
Rike cikin tayi
“Wayyo Yaya Yazeed cikina
Wayyo cikina”
“Tashi muje. Asibiti wannan ciwon naki yazo ya d’auke tashi muje muga likita. Ya duba ki”
“Yaya Yazeed…”
“Kinga bani sonji komai tashi muje”
“To Bari nayi mopping d’in wurin”
“Bari nayi tashi kije ki gyara jikinki kizo muje”
Tana mik’ewa jiri yad’auketa dasauri ya tarbeta
“Sorry my dear muje na shirya ki.”
Haka yanufi d’aki da ita wanka yayomata yafito da ita doguwar riga yaziramata wata ta Atamfa,
Sannan yafita yayi mopping d’in wurin da tayi Amai dama yakashe cooker gas d’in shima d’aki yashiga yawatsa ruwa yafito,
Yakoma d’akin Muneera yajawomata Hijabi tasa sannan suka nufi Asibitin dasuke zuwa wato _*SULTAN HOSPITAL*_
Wajen parking suka aje mota sannan suka shiga ciki Muneera tanajin jiri rungumata Yazeed yayi jikinshi suka nufa cikin Asibitin, Yazeed kiran Abokin shi yayi dayake doctor ne, yaji yanan,
Yabashi Amsa dayanan office d’in shi yanufa kawai dayakesan office d’in
Suña shiga suka gaisa
“My Friend ya madam ne?”
“Wallahi itace ma ba lafiya nace mutafo Asibiti nayi sa’a kuma kanan sai kadubaman ita”
“OK babu damuwa Abokina”
Juyuwa yayi yatambayi Munera yadda takeji ajikinta bayani tayi mashi
Waya yqd’aga yakira wata ma ai’kaciya bada jimawa sai gata tazo
“Am Saudat kuje tayi fitsari
A auna manshi”
“OK sir”
Tare da suka fita da Muneera tayi fitasari taba Saudat Acikin wata bottle,
Muneera tadawo office tazauna,
Can Anjima kad’an saiga Saudat tadawo d’auke da wata paper Mik’a ma doctor tayi tafita,
Murmushi doctor Haidar yayi
“Congratulations Abokina”
“Name kenan?”
“Madam tana d’auke da ciki na 3 Weeks”
Dasauri Yazeed yace
“Serious Haidar”
“Bawasa Yazeed madam nad’auke da juna biyu na 3weeks”
Wani d’adi yaji yaziryace mantawa yayi da Dr Haidar ya rungume muneera
Muneera kunya duk takamata rad’a mashi
“Yaya Yazeed bamu kad’ai ne ba fa”
STORY CONTINUES BELOW

“Sorry Abokina namanta kana Kusa tsabar murna ne zanga d’ana nima”
Dr Haidar nan yabasu shawara yadda zasu kula da babyn har lokacin dazata Fara zuwa awo yarubata Mata maguguna wadda yakamata ta sha,
Cikeda da Murna Yazeed yafito Murna kawai yake
“My Baby yanzu kinzama yar A lalaba komai yanzu ni Zan dinga yimaki kinji ko”
Muneera murmushi tayi kawai Yazeed dakanshi
Yabud’emata murfin motar tashiga suka Nufi gida
Suna cikin tafiya Muneera ta hango mangaro da sauri tace
“Yaya Yazeed mangwaro nakeso”
baya suka dawo yasiyi mata mangwaro sannan suka isa Gida tana isa kuwa ice cream d’inta tafara sha
Ba kautatawa ko
Suna zaune Palour bisa cinyar Yazeed wayarshi tahau Kara Har ya hardace number Ta tashi
“My baby ina zuwa”
Ciki yashiga wani kiran yasake shigowa
D’auka yayi bai yi magana
“Haba Yazeed meyasa kake man haka kace komai fa yawuce”
“Sorry aiki ne yayi man yawa ba sosai nake samu d’aukar waya ba”
“Ok tom yaushe zaka shigo muyi magana Yazeed pls”
“Ina Zan shigo ne”
“Gidako ko kabani Address d’inka nazo inda kake Yazeed”
“Kinga ina wani Abu yanzu Zan kiraki”
Yadatse wayar
Raudha bin wayar tayi da Kallo yadatse Mata waya
“Wai yau ni Yazeed ke wulakanta wa ko”
Girgiza Kai tayi tad’auki tutolin tabud’e murfi sai da shanye duka ta yada kwalbar
“Yazeed inasonka tilas kota wace Hanyace kamaidani matarka Karo nabiyu ko kuma matarka da kake takama da ita na salwatar da ita nida ita murasa ka duka”
Luv my fans💋
[5/10, 10:51 PM] Indoo k’auye: _*YAZEED*_
_*NA*_
_*HAFSAT MUSA*_
_*(Hapsy Baby)*_
*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
*P.M.L.*
_*dedicated to My bibie(yarima)so had’uwar jini*
_*Kin wuce k’awa kin koma y’ar Uwa wajena babu Abinda zance Allah yabar kauna tsakani na dake Luv you*_ _*wujiga wujiga*_😘
*201_205*
Yazeed yana latse wayar dayake da raudha tsaki yasaki
“Kowane tsautsayi yakaini bata number zata takuramin”
Palour yafito wajen Muneera Kusada ita yazauna
“My Baby mikekeso yanzu nayi maki ne?”
“Ice cream Zan sha yaya Yazeed sannan mangwaro”
“Shikenan Angama madam”
Mik’ewa yayi yanufi firjin yad’aukomata robar Ice cream
D’aukar mangwaro yayi yaje yad’aureyomatashi yahah’ado da knife da plate tagama shan ice cream tad’ora da mangwaro yana yanka Mata tanasha,
Har tagama sannan yagoge Mata hannu,
Muneera duk tana kallonshi wata kaunarshi taji tana shiga Dukkan wani sassan na jikinta.
Ahaka har Yazeed ya kauda wurin Muneera tana tunani jitayi An jawota fad’awa tayi jikinshi
“My Baby mekike tunani haka ne?”
“Yaya Yazeed yanzu mezakacine?”
“Karki damu baby na daga yau kidaina girki kinji KO har sai ki Haifa man Baby na”
Zaro ido tayi Alamun mamaki
“Nidai Yaya Yazeed A’a sai ranan danaji nak’ara jin sauk’i dai Amma Bazan barka har lokacin ba kadinga bin restaurant”
“Shikenan kinga sai nasomoki yar Uwa”
“Yauwa Yaya Yazeed Sister Ayman zaka d’auko man?”
“A,a indai yi Aure ko”
“Aure!?”
“Eh mana”
Wani masifattace Kishi taji yana yimata yawo Wadda bata tab’asani tanadashi
Yazeed ke Furta zai had’ata da wata nan dan idonuwanata suka canza
Dasauri Yazeed ya matso Kusada ita
“My Honey Am joking
Am sorry”
STORY CONTINUES BELOW

“Yaya Yazeed wata ranan zakayiman kishiya KO?”
“No my dear ki kad’ai ki isheni Rayuwa kinji ko kita haifaman baby’s kyakyawan kamar ki”
Tare da lakucimata Hanci
“Yaya Yazeed kaima Ai mai kyau ne”
“Kinga Ina biyemaki bana cin komai Bari natashi KO tea nadafa nasha”
Mik’ewa yayi ya Nufi Kitchen ya dafa ruwan
Har ya kule Muneera tana binshi da kallo tare da wata Kaunar shi.
WAISHIN MEYA DAWO DA RAUDHA NIGERIA NE??
*_TUNA BAYA_*
********************************************************
Lokacin da Yazeed ya furta yasaketa Saki ukku yagayamata kuma lokacin komawarshi Nigeria yayi, yafita yabar Mata d’akin
Zira kayanta tayi kafin tafito Har yabar Gidan tana Fitowa tashiga D’akinshi taga ya d’auki komai nashi
Gyad’a Kai tayi kawai Domin lokacin baya gabanta sharholiya kawai takeyi Palour tafito suka cigaba da tashewa da friends d’inta Har kowa ya watse,
Had’a kayanta tayi itama Cikin Akwati tanufi gidansu
Kawai tana Kuka tasanar da iyayenta wai Yazeed yayi mata Duka yasaketa Saki ukku yakoma Nigeria kuma
Bata fad’i laifin ta ba ita sai Sharri ma da taja mashi
Mahaifinta nan ya rarsheta yace tayi Hakuri Ita ta lik’e tace sai shi dama kuma shi Abinda takeso shi take Domin ita kad’ai ce yarshi,
Nan momy ta ta lallasheta
Tana d’auki Akwatin Kayan tanufi d’akin ta ta gyara shi duk dayake Kullum gyara yake ma Ana gyaramatashi kamar tanan,
Bayan kwana biyu tadawowar tane ta bud’e Akwatin Kayan ta ne sai tayi cin Karo da pictures d’insu dasukayi itada yazeed
Baki ruwa Dukkan su suna dariya sannan basu dad’e da aure ba,
Wata kewarshi taji taji tashige ta tare da wani sabon Kaunar shi gashi kuma yayi Mata nisa bata San inda zata ganshi ba
Daganan fa tafara kewarshi taji bata r’aayin tarayya da kowa ba kowa namiji ya tunkareta sai wulak’aci Yazeed kawai take ra’ayi
Daganan kawai tafara shan tutulion da damuwar tayi Mata yawa sai Tasha kwalba 6 lokacin d’aya
Raudha tazama cikakiyar yar maye( Fareeda musa)
Anahaka mahaifinta suka Had’a ta Aure da wani d’an Friend D’in shi dan wai tahuce haushin da Yazeed ya kunsa Mata,
Shima kanwar ja je
.kawayenshi zai Tara Palour ai tashan giya (waiyazubullah)
Itakam Raudha itama tunda badamuwa tayi dashi ba tafitar tasha tutolin d’inta sannan yadawo
Baya kusantar tama sai yana Cikin giya da cizo da Yagi haka zai samu biyan bukatarshi wajenta
B’aayi wata d’aya cikake ba
Ranan tahanshi K’anta gashi yasha giya yad’amata shegen duka ya sakota kuma ta dawo Gida
Dayake kowa d’an gata ne wajen maihaifin shi kowa baya gani laifi nashi,
Raudha takoma cikakiyar Yar shaye shaye yanzu babu ruwanta da harka da kowane namiji ma kodayaushe ita dai Yazeed kawai,
Anahaka komai na mahaifinta yadawo Nigeria A jahar Kaduna suka rankaya suka dawo dama asalin d’inshi d’an jahar Kano Aiki yakaishi maleyishia yanzu kuma yadawo dashi Nigeria suka tataro kayansu suka dawo, Cikin ranta tunani take gata Nigeria Bata san inda zata ga Yazeed kullum tunanin kenan
Ranan kwatsam tafito bid’ar maganin dazata sha motar ta ta tsaya Ashe rabon had’uwar ta da Yazeed
Taji Alwashin kuma sai ya maida d’akinta yazeed ma Nata ita kad’ai bana wata shegiya inhar kuma batasa mu sai dai suyi asarar shi daga ita har shegiyar matar dayake tinkaho.
(Hmm tirkashi wata sabuwa)
Dawowa labari
Muneera tana zaune har Yazeed yahad’a kalacin dazai sama Cikin shi yafito
Can B’angaren bisa Kujera yazauna suna zaune wayar Muneera tayi k’ara tana dubawa taga Mimi
“Hello Mimi na”
“Y’ata”
“Mimi Ina kwana”
“Lafiya lau yajikin naki?”
“Naji sauki Mimi”
Yazeed tasowa yayi daga inda yake karbar wayar yi
“My Mimi y’arki kawai kika sani?”
“Ai itace babu lafiya ko”
“Uhum Mimi Albishirinki”
“Goro Yazeed”
“Uhum kin Kusa samun Jika”
Dasauri ya datse wayar
STORY CONTINUES BELOW

Mimi murmushi tayi zaune suke da Ayman da kaka
“Yaran zamani”
Kaka tace meyafaru ne?”
“Uhum na buga ne naji jikin Muneera shine Yazeed ya karbi wayar yake ceman nakusa samu Jika”
“Alhmdlh Allah mungode maka Ai tunda naga wannan Amai da Muneera keyi nasan da magana Allah yaraba lafiya to”
Ayman ko D’aki tanufa cikin murna tajawo wayanta takira Muneera lokacin wayar na hannu Yazeed taki karba wai tayi Fushi meyasa yafad’ama Mimi
“Amshi nan Ayman nakiraki”
Zumboro baki tayi
“Kasan Mimi har tafad’a Mata Kasan kuma Halin Ayman da tsokana”
D’aga wayan yayi
“Hello Ayman”
“Yaya Yazeed Ina kwana”
“Lafiya lau Ayman”
“Ina sister Muneera ne?”
“Tashiga ciki ne
Jikin bata jin d’adinshi ne”
“OK zuwa anjima Zan Kira ta kular mamu da baby”
Tadatse wayan
Yazeed murmushi yayi
Ya matso Kusada ita
“Kinji Ayman tace ki kula da baby”
“Uhum Yanzu kasanar dasu inada ciki”
“To menene my baby bataya mu murna suke ba”
Jawo pillow Kujera tayi ta ta jefa mashi
Haka sukai jefe jefe.
Pillows dajuna Cikin so da Kauna. Har tagaji ta aje
“Yaya Yazeed Zan sha ice cream”
“Shikenan Bari nad’auko miki”
Tashi Yayi ya d’aukomata tasha
Ahaka har bacci ya d’auketa Yazeed sai dai yaga tana Bacci gyara Mata kwanciya yayi jikinshi yafara Kallo shima har bacci yad’aukeshi shima,
Sai da Azahar suka Farka sukayi sallah
Yazeed har dare yana mak’ale da Muneera a Palour
Muneera tana bisa kan cinyar Yazeed tana game a wayar shi gani tayi Ankira Mik’a mashi tayi “yaya Yazeed Ana kiranka”
Karb’a yayi yakashe wayan baki d’aya yakashe baki d’aya ya ajeta
“Yaya Yazeed meyasa kaka she waya ne?”
“Babu komai taso muje mu kwanta”
“Tom Yaya Yazeed”
“My baby nagaji da wannan sunan Yaya Yazeed An canza manshi nima”
“Uhumm Yaya Yazeed”
Uhumm nisai kicanza man sunan Allah “
“Hahhahaha
Kaga yadda kakoma kamar wani baby”
“Eh nidai kicanza konaki goyaki ma”
uhum shikenan kawo kaji na rad’a maka
Kuneeshi yakawo tafad’a mashi
Rungumota yayi jikinshi
“Tnx my dear wife”
Haka yad’auketa kamar baby girl suka Nufi d’aki ciki da so da kauna
***************************
Muneera bataje school ba sai Ranan Tuesday takarajin karfin Jikinta shima sai Ranan yafita office Yazeed domin yace kula yake da babynshi
Tsaye take tana shiryawa don tafiya school saiga Yazeed ya shigo yagama shiryawa shima bayanta ya gewaye ya dafa kafad’ar ta
“Baby na har kin Gama ne”
“Nagama yaya Yazeed…
Sorry My happiness”
“Uhum duk ranar dakikara Fad’in haka sai na ci tararki”
“Uhum muje naraka ko”
“Kina nufin kezakayi driving yau?”.
” Eh mana tunda angyra motan KO ajiyan mezaayimata me?”
“Kinagani Akwai Ajiyar baby tawa Zan barki kiyi tuki
Nizan dinga kaiki har ki Haifa man baby”
Shafa cikin yayi”
“My Happiness bakayi break ba”
“Karki damu Akwai kingin ruwa A Plastic nahad’a Nasha”
Cike da tausayi ta kalleshi fad’awa tayi jikinshi
“Yanzu saidai kasha Ruwan tea kawai”
STORY CONTINUES BELOW

“Karki damu baby na nafison lafiyar dakomai”
Haka tazura doguwar Riga black tayi rolling da mayafin rigar baki suka fito
Cike da so da kauna suka shiga mota suka Nufi school, ya ajeta
Suna tsayawa yaja glass d’in mota yajawo ta
“Pls my Munee kika kulaman da baby kinji ko”
Yasakar Mata wani hot kiss sukayi bankwana tafita
Yaja mota yanufi office itakuma tanufi class,
Sunfito lecture an had’u da Ayman da janan nan Ayman tafad’a ma janan Muneera tanada juna biyu
Cikin murna
Janan ta jawo Muneera
“Tawan Ashe munkusa zama uwaye”
Muneera tashi tayi tabar musu wajen kawai takira Yazeed ma suna Fira ta masoya
************************************************”*”””,
Haka Muneera keta rainon babyn ta Yazeed yana bata kulawa ta musaman kullum kauna ta tarairaiya Kara yawa take ga Cikin ta yau har yakai 3 month suna ta exam ta shiga level 2
Kullum batada lokacin kanta Karatu take kuma har yanzu Yazeed yahanata shiga kitchen wani bin yaje restaurant ko kuma yaje Gida yatafo da Abinchi ma
Yauma zaune take bisa cinyar shi tana duba wani books wadda zasuyi paper nan da there days
Shikuma Yazeed yanata shafa kanta kamar jaririya
“Yaya Yazeed zanci chips “
“Angama My pretty”
D’aukar key d’in mota yayi
Yafita itakuma tacigaba da Karatu domin kingin paper 2 su idar kuma masu zafi nene
Yazeed yafito daga restaurant rike da Ledar chips daidai shigar shi mota wata mota ta faka
Bakowabace Raudha ce tazo
Cin Abinchi dasauri ta koma motar Yazeed yana tada motar itama tada
Duk inda yabi tana biye dashi gani tayi yafito ya bud’e get sannan yashiga da motar
Murmushi tayi
“Tabass nan ne gidan Yazeed”
Murmushi tayi taja motar tabar unguwar,
Haka yashiga Gida Yazeed dasauri Muneera tataso ta gareshi
“Bana ce kidaina Gudu ba”
Haka yajata suka zauna yadinga bata chips d’in
Suka Gama suka nufi makwanci.
Yau su Muneera ke Kammalah Exam tafito tashiryane shima Yazeed tashirya
“My Baby yau Aiki yayiman yawa office kid’auki motar ki kitafi da itah Amma ayi driving A Hankali pls”
“Insha Allah My happiness”
Haka suka yi bankwana tashiga motar shima yashiga suka kowa yanufi inda daya
K’arfe 4:30 pm
Su Muneera suka fito daga
Last paper shikuma dai dai
Time d’in Yazeed ya Kamallah aiki Aikin dayake zato sai next week
Yaga babu Abinda zaiyi yatarara. Kayanshi yanufi Gida
Yana isa yaga Muneera bata dawo ba wanka yashiga kawai yana fito wa
Daga shi sai vest da gajeran wando yazauna Palour
Bai d’ade da zama yaji takun takalmi. Yana d’agowa yaga Raudha
Dasauri ya Mik’e
“Raudha!!!
“Na’am My Yazeed tunda guduna kake Yau Gani gaka”
“Waya gwadamaki inda nake?”
Matsawa daf dashi
Pls My Yazeed Wallahi Kai ne zabina kuma nasan kana sona
Bai Ankaraba yaji ta rungume shi
Muneera dake tsaye
Wata Ka’ra tasaki tazube sumama
Dak’arfi Yazeed ya ture Raudha yanufi wajen Muneera
YAZEED*_
_*NA*_
_*HAFSAT MUSA*_
_*(HAPSY BABY)*_
_*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*_
*_P.M.L._*
_*Dedicated to Nana A usaman*_
*_Nagode da kaunarki gareni babu Abinda zance maki nagode sosai luv you my kawata_*💓💖
STORY CONTINUES BELOW

_*206*__*210*
Da K’arfi ya ture Raudha daga jikinshi yanufi wajen Muneera data fad’i
Girgiza yafara
“My Munee my Munee”
Amma ko Alamun motsawa batayi ba
Dasauri ya Mik’e
Wajen Raudha yanufa
“Wallahi matana ta mutu wallahi sai na kasheki kema
Banasonki nafad’a miki bana sonki”
Dasauri yanufi d’aki yazira jallabiya yafito daga d’aki KO kallon inda Raudha tayi beyiba ya d’aukj Muneera kamar Yar tsanaysd’auketa mota da ita yasata sai Asibiti,
Ko dai_daita parking beyiba yafito rike da Muneera direct cikin Asibiti yashiga da Muneera
Nan dan Aka shiga da Muneera emergency
Yazeed shima kutsawa yayi yashiga d’akin nan danan Aka Fara ba Muneera taimakon gaggawa
Ba’ayi minute 20 sai ga shi tafara bud’e idonta A Hankali
Dasauri Yazeed yanufi wajen Muneera
“My Munee sannu”
Dasauri ta rintse idonta ta juya mashi baya.
Yazeed jikinshi yayi sanyi yasan yaga Abinda taga Abinda yafaru
“Haba My Munee.”
“Please Kakyaleni yaya Yazeed ka koma gurinta pls”
Fashewa tayi dakuka wani Azababatan Kishi nayi Mata yawo data rintse idonta gani take ga Raudha danan rungume da Yazeed,
Wani Kuka tafashe dashi
Yazeed rikecewa yayi ya isa wajenta
Rungumota yayi
“Pleased my baby kiyi shiru don Allah wallah”…
Kar ka ida Banason jin komai
“Ashe wannan dalilin dayasa kace na hau mota na tafi Kasan Abinda ka shirya ko?
Nasan Yaya Yazeed basona kake ba har yanzu ga zabin ka can shikenan katashi kaje gareta don Allah ka kyaleni pls”
“My mune.”
“Banason jin komai katashi Ko natashi nabarka maka d’akin meyasa ma ka kawoni Asibiti dasai ka kyaleni ma”
Doctor ne yashigo
“Ah madam yakike Kuka gashi kuma kinada juna biyu”
Juyowa yayi wajen Yazeed
“Yace my friend Aguji sa madam cikin damuwa kaga Akwai juna biyu jikinta komai na iya Faruwa gareshi Adaina sata b’acin rai.”
“Insha Allah za’a kiyaye doctor”
Yauwa zuwa gobe zamu Baku sallama jikin yak’ara samun sauki”
“Shikenan mungode doctor”
Doctor yafita yabar Yazeed da Muneera
“Pls My Munee kinji Abinda doctor yace kidaina shiga Damuwa kuma Abinda kike zato Wallahi bahaka bane Allah”
Wani Kallo ta watso ma Yazeed sannan ta maida idonta ta rufe kamar mai bacci
Yazeed Cikin sanyi jiki yafita daga d’akin wayar shi dake Gaban Aljihu yazaro
Number Mimi yakira
“Hello mimi”
“Na’am Yazeed”
Gaisawa sukayi tsakanin Uwa da d’a Mimi fahimtar Yazeed tayi yana Cikin damuwa
“Yazeed meyafaru?
Ya muneera ne?”
“Mimi muna Asibiti ma bata lafiya”
“Subhanallah!!!
Wane Asibiti kenan?”
“Asibiti damuke da kati”
*”SULTAN”*
“Eh”
“Ok ganinan zuwa yanzu”
Suka datse wayan
Yazeed motar shi yashiga yafito bakin hanya bai nisa yaga wata restaurant Fitowa yayi yasiyama Muneera chips Domin yasan daga shi sai Ice cream zata iya sha.
Gaba kad’an Akwai super market yaje shima yasiyo sannan yadawo Cikin Asibitin.
Suna gamawa waya da Mimi kuma Mimi wayar dady takira tashaida mashi muneera tana Asibiti cewa yayi tatafi gayanan zuwa,
Mik’ewa tayi tanufi d’aki tad’auko mayafi tana fitowa tayi cin Karo da Ayman
“Mimi inazaki?”
“Asibiti”
“Waye ba lafiya”
“Muneera ce yazeed yakirani yanzu yafada’a man”
*Mimi muje nima inazuwa Bari nagayoma Kaka”
“A’a karki fad’amata kinsan dai itama bakarfin jiki takeji ba muje muga yanayin jikin Muneera dai d’auko key d”in motar taki. Muje dai mufara ganin Jikin”
Dasauri Ayman tanufi d’aki ta d’auko key d’in mota tare da mayafi
STORY CONTINUES BELOW

Yazeed A Hankali ya tura Kyaure d’akin da Akwa kwantar dasu Muneera juyowa tayi
Tanaganin yazeed ne tayi saurin maida kanta, tare da rintse idonta,
Ahankali ya isa Gaban gadon yazauna gabon Gado yazauna
“My Baby tashi ga Chips da Ice cream kisha pls nasan bakici komai ba”
“Bazan Ciba”
“Please kidaure kitashi”
“Karkadameni don Allah bazan ci ba”
Wayar yazeed ne tayi k’ara yanadubuwa yaga Mimi ce
“Hello”
“Yazeed gamunan munzo kazo kaje damu”
“OK ganinan”
Tashi yayi yafita daga d’akin
Muneera Fashewa tayi da Kuka mai tsuma zuciya.
Badajimawa sai gashi yadawo muneera bata fasa Kukan ba
Muryar Mimi taji tare da Ayman dasauri ta goge Hawayen ta ta Mik’e
“Mimi”
“Y’ata sannu kinji ko”
Tareda nufar gadon tazauna Ayman tazauna
“Sister sannu”
“Yauwa sisi”
“Meye silar ciwo naki ne?”
Yazeed Kallon Muneera yayi gabanshi yana Fad’uwa jira yake yaji mezatace ne.
“Mimi tashi nayi kawai banajin Dad’in jikin ne dama hakanan natafi school saboda jarabawwa
Nashigi Gida ne wani jiri ya d’ebeni bansani ba”
Wani gwarau Numfashi yazeed ya aje tare da son Muneera
“Sannu kinji ko”
“Yauwa Mimi”
Yazeed matsowa yayi wajen gadon
“Mimi ga chips nan da Ice cream nasiyo tace bazata sha”
“Ahhh Muneera ba’ayi hakan ba daurewa zakiyi kici kinji ko Ayman mik’o man su gasunan”
Ayman Mik’a Mimi tayi
Bud’awa tayi
Tafara bata abaki tafaraci
“Mimi na koshi fa”
“Aa ba’ason masu juna biyu nazama da yunwa kinji”
“Mimi ga ice cream zata sha”
“Wannnan Kayan sanyi daina shan shi zakayi ma komai Ice cream daina sha zakiyi”
Dasauri ta kalli Mimi
“Eh daina sha zakayi saboda lafiyan Abinda ke Cikin ki”
“Mimi nifa bazan iya cin komai ba”
“Kuma shan ice cream dole kidaina Muneera sanyi nabugu babyn dake tare dake zaki iya haihuwarshi babu lafiya kirage kinji”
Sunkuyar da Kai kasa Kai kawai tayi can bayan sallar isha’i sai ga Dady yazo shima duba jikinta
Shima yatambayi meyasameta
Mimi ta fad’a mashi kamar yadda Muneera ta Fad’amashi
Nan bada jimawa zasu sukayi bankwana zasu tafi
“Mimi Abar sister pleased”
“A’a kinajin Yazeed yace gobe za’a sallameku”
Dady yace “kiyi Hakuri kinji my Dota Allah yak’ara sauki”
Nan sukayi. Bankwana Yazeed yafito yarakuso Dady motarshi yashiga sannan Mimi suka shiga motar dasuka zo sai da Yazeed yaga tashinsu sannan yajuyo yanufi d’akin da Aka kwantar da Muneera.
B’angaren Raudha kuwa yazeed yana sakinta daga shakar dayayi Mata yanufi wajen Muneera yad’auketa dirin motar shi kawai taji tasan yafita daga gidan,
Kujera tazauna
“Wallahi Yazeed Kaine Namijin da nakeso kayi Hakuri my yazeed”
Idonta suka sauka bisa wani Id card dasauri tad’auka Domin ta tabbbatar na Yazeed ne aikuwa taga shine don ida yake aiki.
Murmushi tayi
”Yazeed A Hankali Zan shawo kanka Domin nasan babu wadda kakeso Kamata”
D’aukar I’d card d’in tayi
Tayi copying Abinda ke ciki Awayanta sannan ta fita tashiga motar Cikin ranta tana Fad’in Allah yasa matar tashi tamutu
Cikin Fushi nakalleta nace sai dai ke.ki mutu duk da mutuwa da lokacin tayayi Ake tafiya babu wata sauran dabara ga Mutum.
[5/14, 8:44 PM] Indoo k’auye: _*YAZEED*_
_*NA*_
_*HAFSAT MUSA*_
*_(HAPSY BABY)_*
©
*_PURE MOMENT OF LIFE WRITES_*
*P.M.L*.
_*Dedicated to All my fans*_
_*Nagode da kaunar Ku gareni luv you All masoyana*_
💞💓💘
STORY CONTINUES BELOW

*211_215*
Yazeed yadawo daga rakiyar su Mimi A Hankali ya tura Kyaure yashiga D’akin da Aka kwantar da Muneera,
Nufar gadon yayi
“My Munee nasan ba bacci kike ba pls kibud’a idonki muyi Magana Don Allah my Baby”
Ahankali tabud’e idonta tajuya baya
“Inajinka meke tafe dakai ne yanzu inajin bacci ne”
“My baby Yakamata kinsan halina Wallahi bani na kawo Raudha a Gidan nan”…
“Banasonji komai tare dakai don Allah ka kyaleni pls narokeka kokaji nace wani Abu game da hakan ne? don haka ka kyaleni don Allah inajin bacci”
Yazeed rasa mai ce yayi
Yadad’e zaune ko motsawa batayi
Ba bacci takeba tanajinshi
Almun bud’e Kyaure taji Anmaida An rufe dasauri ta
Juyo taga Yazeed yafita
Mik’ewa tayi ta Had’a kanta da gado,
Wasu Hawaye masu zafi suka shiga zubomata tare da wani masiffatacen kishi
“Yaya Yazeed babu Abinda zakace nayarda dashi nasan haryanzu basona kake ba har naganka rungume da mace meye had’inka da ita”
Yazeed yana fitowa motarshi yashiga yamaida yarufe ya kwanta Ciki
Tareda runtse ido
“Why Muneera bazaki tsaya kiji bakina kiji mezan Fad’amaki ne Raudha kinji d’adi ki had’ani da matana na tsaneki Raudha muneera ki fahimce kiki tsayawa kiji tabakina why why Muneera”
Zuciyar shi cike da kewar Muneera.
B’angaren Muneera haka take ta Kuka tashi tayi tashiga toilet d’in Cikin D’akin ta da’auro Alwalla ta Ciro d’an kwali bisa kanta yazameta carpet d’in sallah
Tayi sallar magariba da isha’i sannan ta maida da nafila r’aka biyu
Taroki Allah Akan ya sausata Mata zuciyar ta dangane da rad’ad’in datake.
Anan k’asa bacci yad’auketa Amma Abu kad’an ta Farka tasaba kwana bisa kirjin Yazeed jitayi wani kalla kwanciyar babu d’adi
Ab’angaren yazeed shima yasaba kwana da matarshi Yau gashi zai kwana shi d’aya Acikin mota Domin bazai iya tafiya yabar ta
Haka B’angaren ma’aurata biyu kowa yayi bacci babu d’an uwanshi.zuciyar su cikeda kewar kowa.
_Washe gari…_
Kan Kunnesu suduka sukaji tada sallahr Asuba Yazeed yafito daga mota yanufi masallachin Asibitin,Domin yayi sallah
Itakam Muneera tashiga toilet tayo Alwalla tazo tada sallah
Bayan tagama ne takoma bisa gadon ta kwanta
Yazeed bai fito ba sai
Wajen Around 7 daga masallachi D’akin yashiga kawai tsayawa yayi bakin Gadon ya kurama Muneera ido
“My Munee ki yanke hunkuci batare da laifi na Wallahi babu wata mace ke cikin raina Luv you my baby”
Jawo Kujera yayi yazauna
Nan gabanta yad’ora kanshi bisa gado
Dayake ba wani baccin kirki yayi ba bada jimawa bacci ya d’aukeshi.
_Around 7:30 Am_
Muneera ta farka Dora hannu dazatayi taji shi jikin Kai dasauri ta duba taga Yazeed kwa’nce ya Had’a kanshi da gado
Tausayin mijinta taji lokaci d’aya kamar tare suke shima yafarka ido hud’u sukayi
“My Munee har kifarka ne?
Mikekeso kici yanzu kinajin Mimi tace kidaina zama da yunwa fa”
“Banacin komai Banason komai”
“Haba my Munee kidaure pls kinji ko”
Yana Aikin rarrashinta ne Aka turo Kyaure aka shigo doctor tare da wata nurse
“Ahhh madam jiki yayi sauki kenan ?”
Murmushi tayi kawai nan yakara dubata
“Madam kidaina saka damuwa kinga kinada juna biyu mai juna biyu bata zama da juna biyu
My friend Akula pls”
“Insha Allah doctor za’a kula sosai”
Yauwa yanzu kabiyoni office zani Baku takadar sallama Allah yakara lafiya “
STORY CONTINUES BELOW

“Madam A kula sosai”
Yazeed Bayan doctor d’in yabi yarubata mashi takadar sallama sannan yaje yabiya Abinda Aka kashe
Lokacin da yakoma har muneera tafito waje
“My Munee muje ko”
Batayi mashi Magana ba suka tanufi mota yazeed yabud’e Mata tashiga sannan yashiga shima,
Yarufe motar suka bar harabar Asibiti tunda suka Fara tafiya Muneera babu Abinda tace mashi yana cikin tuki wayanshi tayi k’ara samun wuri yayi yatsaya don ya Amsa wayan
“Hello Mimi
Morning
Antashi lafeeya
Eh ansallame mu gamunan Hanyar tafiya Gida ma
Ameen Ameen”
Sannan ya datse wayar yajuyo wajen Muneera yaga tana Kallon gefen titi
Sunfara tafiya ne yatsaya wani restaurant yashiga yasiyo chips yafito
Har suka isa Gida Muneera bata kalli inda yake ba bai ida parking ba tabud’e murfin tafita,
Yazeed binta yayi da kallo har tashige ciki girgiza Kai yayi
“My Munee kiki tsayawa ki fahimci ni ko”
Rufe motar yayi yafita shima
Muneera tana fita d’akinta kawai tashiga ta cire hijab da tad’aura towel tashiga wanka shima yazeed d’akinshi yashiga wanka yayo
Yana fitowa yazira jallabiya yafito yanufi D’akin Muneera daidai lokacin itama tafito daga wanka
“My Munee pls ga chips nan kidaure kici kinji ko”
Ya ajemata shi bisa mirror ya matso daf da ita “my Munee pls”…
Matsawa tayi tajuya tanufi Hanyar toilet tabarshi tsaye kawai
Cikin sanyi jiki Yazeed yafita daga D’akin
Muneera jin Almun yafita yasa tafito daga toilet d’in.
Nufar wajen kayanta tayi tazira wata doguwar Riga marar nauyi tafesa turere dama Muneera ba’a ma’aboyiciyar son Kitso bace gyara gashi tayi tanufi ta d’aure da ribbon
Hanyar Palour tafito tad’an gyarashi duk da baiyi Kura ba.
Jitayi Cikin yana Neman Agaji d’aki ta koma tad’auki chip’s d’in da Yazeed yasiya tafara ci Duka ta cinye shi,
Tazo Palour tad’auki ruwa Tasha D’akin ta koma ta kwanta bisa gado
Tunanin tashiga yi wasu Hawaye suka dinga zubar Mata daga Fuska
Batasan lokacin da Hawaye kemata zarya A Fuska ba
Shima Yazeed haka yakoma d’aki yana tunani karar Ana kwankwasa k’yaure yaji tashi yayi yanufi ya Bud’a Ayman ce da Janan
” Yaya Yazeed”
“Na’am”
“Morning”
“Kuntashi lafiya ?”
“Lafiya lau dama Mimi tace muzo nak’ara ganin jikin Sister ne”
“OK tana d’aki tunda muka dawo tace bacci zatayi”
Nufar D’akin suka yi itada Janan
Muneera dama taji maganar kafin su shigo tayi saurin goge Hawayen dasuke bisa Fuskar ta
Takoma ta kwanta kamar mai Bacci.
Ayman suka shigo
“Bacci ma take
Sister sister”
Ahankali tabud’e idonta kamar mai baccin
Dasauri ta diro bisa gado Ganin har da Besty ta
“Tawan bi Ahankali akwai Ajiyar baby mu cikin ki gaki kuma patient”
“Duk murna ganinku ce tajawo hakan muje Palour”
Haka suka fito Palour
Coleer da Ayman ta Aje ta Mik’a ma Muneera
“Gashi inji Mimi ferfesu tayi miki koni band’ad’a na ba tace na kawo miki”
“Allah sarki Mimi na”
Muneera tana Bud’awa wani K’amshi ya bugeta yaji kayan Had’i citta karamfani,
Haka tahauci babu Amai babu komai
Ayman da Janan kuma kallo suka bita dashi yadda ta ke cin
“Ku Amshi kuci kad’an pls Zan Aje zuwa Anjima naci kunji sister’s”
Haka suka d’anci Domin K’amshi dayake dole yabi ya ranka,
Sunan zaune har wajen k’arfe biyar sannan sukace zasu tafi
Cikin Fuskar tausayi Muneera tace
“Pls kar Ku tafi kubari sai Anjima don Allah”
.”duk yini damukayi miki baki Gani ba”
Dakyar suka tafi badon tasoba Ganin su yasa take rage wani Abu cikin zuciyarta,
D’aukar coleer d’in tayi kawai tanufi cikin d’aki wayar ta jawo tahau game tagaji kuma ta’aje
Yazeed shikam yakasa komai yadda Muneera ke Fushi taki bashi Fuskar ma dazai Mata bayani ma
Lap top d’inshi yajawo yafara Aiki koyarage kewar ta
Yana Cikin Aiki ne wayarshi tayi tsuwwa Almun Ana kiranshi
Raudha ce yagani Domin yasan number shi
Datse wayar yayi shiga ya yi
Black list d’in ta koda takira shi bazata samu ba kwata kwata.
“Kinzame Mani Annoba kin had’ani da Mata Raudha duk Ranan da nahad’adake bazaki ji d’adi ba”
Kiran sallar magariba yadata shi daga Aikin dayake yayi
Alwalla yanufi masallachi,
Haka itama muneera tashiga tayo Alwalla bata tashi ba sai da Akayi sallar isha’i
Jitayi cikin na buk’atar idomie kawai cire Hijab d’in tayi sallar tayi ta linke carpet d’in sallar
Tanufi kitchen tad’ora indomie d’in
Yazeed yana shigowa yaji K’amshi ya gauraye gidan
“My Munee ki girki ne”
Hanyar kitchen yanufa
Iske Muneera tana niyyar zuba indomie
“My Munee kidafa Dani zanci pls duk yau babu Abinda naci facin ruwan tea”
Batayi mashi magana Amma wani tausayin mijinta yadirar jin baici komai har yanzu
K’ara yawan indomie tayi duk Yazeed yana tsaye ya Had’a Hannushi da kirji
Juyawa Yayi ya nufi d’aki kawai
Muneera binshi tayi da Kallon haryafita
“Yaya Yazeed komai yafaru Kai kaja zuciyata tana matukar kishinka meyasa ka Aikata haka gareni naganka rungume da wata mace jikinka
Why why”
Kuka yazomata Haka tagama girkin ta d’ebi Nata
Tasa kingin cikin cooler tanufi waje Aje Nata tayi tanufi D’akin yazeed takaimashi……..
_Dedicated to My dear_,
_My sweet friend, my Jannart_
_Kaunar mu A jini take Ina Alfahari dake tawan kodayaushe so had’uwar jini_
_Luv you my Jannart_
_Allah yarayamana babyn_ _mu Janan_
Palour tafito ta’aje Nata sannan ta nufi D’akin yazeed
Takaimashi tura Kyaure tayi takaimashi zaune ta tarradashi yahad’a Kai da Kujera sallama tayi taaje mashi tana Ajewa kuma tajuya tafito daga D’akin,
Yazeed Yayi mamakin yadda ta had’omashi yad’auka bazata girka har ya niyyar tashi yaje restaurant yaci,
Yana Bud’a cooler wani K’amshi ya ziryaci Hanci shi.+
Haka yasa fork yadinga ci bai San lokacin da yacinye taduka sai dai yaga babu
komai “lailai naji yunwa ba laifi”
Muneera tana Fitowa daga D’akin yazeed d”aukae idiomie tatayi tanufi D’akin
Ahankali ta ke cinta cikin s’aa har tagama batayi Amai har tagama ci
Harda Karin ferfesu tak’ara
Muneera mamakin kanta kawai take irin wannan cin Abinchi da yasameta yau,
Tashi tayi tashiga toilet tayi Brush sannan tafito tad’auki plate d’in dataci Abinchi tanufi kitchen Bud’a cooler datakai ma Yazeed Abinchi tayi taga Babu komai
Mamaki tayi yadda ya cinye Abinchi suka
Fanfo ta Bud’a ta d’aurayesu sannan tagama takashe fanfo sannan ta nufi d’aki
Cinkaro tayi da Yazeed A Palour zaune yana Kallon
Ko Kallon inda yake batayi ba
Tanufi D’akin ta
Ta canza zuwa sleeping dresses,
Tahaye Gado takashe lantarki,
Yazeed shiru yaji Domin rabonda dasu raba shimfid’a tun lokacin da tazo mashi firgice tana tsoron mage,
D’akinta yanufa yana shiga ya kunna lantarki.
Muneera tayi d’ai_d’ai tana Bacci
Gadon yanufa domin koda yadata yasan ba kulashi zatayi ba,
Kashe lantarki yayi yahaye gado tare da yin Add’ua yagyara Mata kwanciyar tare da jawo jikinshi yaja musu blanket Yayi
Anatada sallar Asuba Yazeed yafarka Kallon yadda Muneera tashige kirjinshi Yayi
Kara rungume Ma Yayi
Muneera Kara shigewa tayi jikinshi itama cikin Bacci taji ta kamar jikin Mutum Ahankali ta Fara bud’e idonta jikin yazeed taji A zabure ta kwace kanta daga gareshi ta sauko daga bisa gadon
Cikin mamaki
Tace
“Wato tare dashi na kwana kenan shiyasa ko farkawa banyi ba”
Ko ta kanshi bata bi ba ta nufi toilet
Yazeed murmushi Yayi
“Zaki sauko My Baby luv so much”
Saukowa Yayi yanufi D’akin shi yazira jallabiya Yayi Alwalla yafito yanufi masallachi,
Itama Muneera tana gamawa tayi Addu’a tashafa takoma Bacci,
Yazeed yana dawowa daga masallachin D’akn shi kawai yazarce ya kwanta bisa gado kasa komawa Bacci Yayi domin har ga Allah yanajin yatakura tsakanin jiya zuwa yau fushin da Muneera keyi dashi
Bazai iya jurewa ba
_7:00am_
Muneera tafarka daga Bacci datakeyi wanka tashiga kawai tana Fitowa tazira wata t shirt da Wando there quarter_ pink and black wow Masha Allah readers duk da Muneera batayi make up tayi wani haske ga d’an karamin Cikin ta yafito Mata gwanin ban shaw’a
Kitchen tanufa Domin taci Alwashin yima Yazeed komai kar na Abinchi Fuska ce kawai bazai samu Wajen ta, zata cigaba da kyautata mashi
Tana shiga tad’ora dankali datayi saurin gamawa
Minti 10 yadahu yadda zata soya shi tsane shi ya huce
Tasoya
Wani ruwan zafi ta d’ora ta tea
Tajuyo wajen dankali ya huce ta fereshi sannan tafasa kawai tafara soyawa
Tayi mamaki Amai yadda bai taso Mata ba har tagama ta juye a cooler sannan tajuye ruwan zafin a flastic ta gyara wajen komai tsaf tsaf
Sannan ta d’ora indomie Domin daga jiya zuwa yau taji kawai itake masifar so
STORY CONTINUES BELOW

D’auko kayan datagama yi tajera A dinning table
Sannan ta kwaso indomie ta tanufi Da’ki
_7:30am_
Dasauri Yazeed yafarka yaga 7:30 am toilet yashiga kawai yayo wanka cikin minti 15 ya shirya cikin shirin office yafito Hanyar kitchen yanufa yasamu koda Ruwan tea yasha
Kallon dinning table Yayi yaga komai shirye da mamaki yanufi wajen dining table d’in yana Bud’a cooler K’amshi dankali data muneera tayi yabugar mai Hanci.
Ga kayan tea Nan duk ta jera komai da komai jawo Kujera Yayi ya Had’a tea mai kauri sannan ya d’ebi dankali
Sai dayaji babu wuri sannan yagoge bakinshi da tissue da Hannushi ya nufi D’akin Muneera
Tarrada ita Yayi tana cin indomie
“Kuma babyn yanzu indomie yadawo ma”
Cikin Ranshi yake wannnan maganar
Sallama Yayi
Leb’enta ya kallah yasan data Amsa mishi.
“My Munee natafi office”
Saidai tad’au tsawon minti 2 sannan tayi Magana
“OK Allah yakikaye”
Daganan bata k’ara furta komai sai wasa datake da fork d’in takasa cigabada ci
“Ameen my Munee bye”
Yajuya yafita murmushi yake kawai jin ta Amsa mishi.
Muneera yana fita rintse idonta tayi tana shakar K’amshi tureren Jikinshi dake Mata dad’i ko dayaushe mai yimata d’adi
Bayan kamar minti 15 datafiyarshi tashi tayi ta wanke kayan datayi Amfani dasu tayi D’akin Yazeed tanufa kawai tana shiga K’amshi tureren shi koda yaushe ya bugeta gyaran D’akin tayi tahaye Gado bada jimawa sai Bacci ya d’auketa saman Gado tatare
Shikam Yazeed Cikin mota tuki yake tunani yake yadda zasu ida shiryawa da Muneera yake Ahaka yar ya isa office
Yafara Aiki dake gaba sh wadda ya taramanshi da d’an yawa,
Muneera bata Farka dai sai wajen k’arfe 12:am
Tafarka daga Bacci dayake yad’auketa jiyatayi cikin ta yana buk’atar Abinchi
“Oh ni daga jiya zuwa yau cin Abinchi nake kawai nake”
Firji tanufa kawai ta d’auki kwalin holladia had’e da cake tazauna Palour taci sai data shanye kwallin duka had’e da cake, tayi mamaki yadda ta shanye wannan Babban kwali Duka,
Tana zaune Palour shiru ita d’aya k’aratun Alqur an tasanya tunda ga fatiha
Har Aka Kira sallar Azahur sannan ta mik’e tashiga ciki tayi sallah wani Bacci yasake d’ivar ta sai da l’aasar ta tashi
“Nidai ko ciwon Bacci gareni dai Abin kad’an Bacci”
Tanagama sallah kuwa
Toilet tashi ga ta wata ruwa
Tana fitowa daga toilet tashafa mai had’e da turare
Tagyra parking d’in gashin ta, rigar datasa ko gwiwar bata kawo ta fito had’e da wani sanyayaya K’amshi dake tashi Jikinta,
Hanyar kitchen tanufa kawai tsaye tayi tana Nazari Abinda zata girka ma Yazeed,
Tafi minti biyar tana Nazari jita kamar tafasa girki
Amma wata zuciyarta ta haneta Akan Hakan
“Bari kawai nayi mai sauk’i
Kuma nasan Yaya Yazeed yanason shi”
(Hmm Miji da Mata sai Allah)
kayan tashiga had’awa da duba taga duk tana dasu
Abinda ake Had’a _COUS_COUS, _SALAD_
_*Cous cous*_
_*Albasa*_
_*Salak*_
_*Gurji*_
_*Tumatir*_
_*Lemon zaki*_
_*Maggi*_
_*Gishiri*_
_*Attaruhu*_
_*Parsely*_.
_Yadda ta Had’a kuwa_:
_Tafara yayanka Albasa_ _yanka rawul, Gurji mahaka tayi masa shima salak d’in_
_Ta yanka da Tumatir d’in said datafa Ruwan zafi da mai, ta zuba cous_cous _a kwano sai ta juye ruwan zafi akai tarufe sai dayayi minti goma data ga Ruwan ya ya tsotse sai ta juye a. Wani kwano Ruwan data zuba shine daidai yawan cous_ _cous d’in_ .
_Sai tazuba Albasa, Tumatir_,
_Gurji, lemon zaki da kuma_ _Parsely, tai tajuyawa har_ _komai ya had’e sannan ta juye a cooler Domin bataso yasha iska_,
STORY CONTINUES BELOW

_Sannan ta Had’a da Fruit drinks.abubwan data Had’a sune_
_Abarba_
_Gwanda_
_Ayaba_
_Kankana_
_Lemon zaki_
_Lemon tsami_
_Kwa_kwa
_Sukari_
_Duk bayan ta feresu_
_Tasa A blander ta markad’e su tatace da rariya mai laushi ta D’an k’ara Ruwa da sukari da madarar ruwa, tajuye A jug tasaka Firji kafin Yazeed yadawo Yayi sanyi Sosai_
Duk wannan girki datayi jitayi bata buk’atar ko d’an d’ano su ma indomie kawai takeso Nan tad’ora minti goma ta dahu ta juye A plate
Tafito Palour ta zauna tana ci kayanta cike da jindad’in kayanta,
Tanagamawa ta Kora da wata ruwa ko plate d’in bata d’auke ba Nan saman Kujera Bacci yakuma sake d’auketa
_Around 6:pm_
Yazeed yatashi daga office komai ya Kamallah ya tatara Abinda zai d’auka yabar sectary yarshi key tarufe shikuma yanufi waje inda Yayi parking motar shi yashiga yaja yanufi Gida,
Yana isa Gida Yayi parking mota yashiga ciki
Palour shiru sai K’arar Ac kawai hango Muneera Yayi tana ta kwasar Bacci ga plate gabanta na Abinci
Nufar inda take yayi
Ya sunguna dai_d’ai
Fuskar ta yafara gyara gashi da yazubo Mata Kallo lips d’inta wadda ke matukar burgeshi kodayaushe
Ba sai lokacin da yahad’ashi danashi ba yafara tsotsa kamar sweet,
Can Muneera taji Ana tsosar Mata baki
Firgice ta Mi’ke taga yazeed har yafara fita hayacinsa ture shi tayi daga jikinta
“My Munee pls forgive me?”
Mi’kewa tayi kawai tashige d’aki yazeed bayanta yabi da kallo har tashige yadda komai Nata ke rawa
Yazeed jikinshi yaji duk babu kuzari bai San lokacin da yad’auka zaune ba
Tashi Yayi Cikin k’arfin hali yashiga d’aki wanka Yayi kawai yazira jallabiya Yayi Alwalla yanufi masallachi,
Muneera tana shiga d’aki ta maida ta rufe tayi kwanciyar
Itama sai taji Andata sallah ta Mik’e tayi Allawa
Kamar yadda tasaba sai datayi sallar isha’i sannan ta Mik’e
Waje ta Nufa kafin Yazeed yadawo ta shirya mashi Abinchi bisa dinning table komai tashirya sannan ta koma d’aki
Yazeed yana shiga d’aki yana niyyar d’aukar key yaje restaurant yasa mo Abinda zai ci
Kamar d’azu dasafe ya kalli dinning table yaga komai shirye nufar dinning table Yayi yana Bud’a cooler K’amshi ya bugeshi
“Allah sarki My Baby badai zaki barni da yunwa duk da Ana Fushi Dani wayyo Luv you so much”
Haka yazauna yanaci yana zuba santi shi kad’ai yakora da lemon juice wadda Yayi sanyi sosai sai dayaji babu wuri sannan ya tatara kayan ya Kai Kitchen
Nufar D’akin Muneera Yayi Amma yatarda ta rufe k’ofar key
“My baby”
Amma Muneera lokacin Har Bacci yasake d’ibar ta ma batasan yanayi ba
Haka yagaji ya koma d’aki
Ya kwanta bisa gado cike da kewar Muneera har bacci yad’aukeshi.
_After 2weeks_
Muneera duk wata kulawa tana ba Yazeed Amma fa babu Ruwanta dashi bata yarda ma su had’u kwata kwata zata shirya mashi Abinchi
Yazeed duk ya takura dahakan yau yasha Alwashin sai sun daidaita Insha Allah,
Yana zaune office yana Aiki
Sec tray d’inshi ta shigo
“Sir wata mace tazo tace tanason ganinka yanzu”
“Wacece?”
“Taceman Kai kad’ai takeson ganinka”
“OK kicemata tashigo”
“OK sir”
Tajuya tafita Bada jimawa saiga Anturo k’yauren office yazeed dake duke yana Aiki ko d’agowa bai yi ba
Jiyayi Anja Kujera Anzauna
“My yazeed”
Dasauri yad’ago ganin Raudha Yayi zaune bisa Kujera
Kamar yaga dodo haka ya Mik’e
“Raudha me yakawo ki office d’ina wama yafad’a miki inda nake ne?”
“My Yazeed garin masoyi baya….”
“Shut up”
Raudha sai data firgita wannnan tsawar da Yazeed Yayi Mata
STORY CONTINUES BELOW

“Raudha Abinda yafaru yariga yafaru tsakani dakai kin nemi yafiya na yafemaki meyayi saura to ?”
“Yazeed don Allah kayafeman kamaidani matarka Karo nabiyu Bazan sake Aikata Abinda nayi ba Kai nakeso Wallahi”
“Raudha kiyi Hakuri kinyi sake babu wata Cikin raina A yanzu Kamar Muneera itace cikin raina Ahalin yanzu Bazan iya had’ata da wata ba”
“Ya isa yazeed ka kyaleni hakan Don Allah”
Cikin Fushi ta ziri jakkar tabar office d’in tana kuka,
Yazeed komawa Yayi bisa Kujera
“Kiyi Hakuri Raudha Bazan iya had’a My Munee da kowa ba kinyi sake A Rayuwar ki”
Jiyayi kawai soyake yaga Muneera tashi Yayi yatarara kayan yafito yaba sectary d’in key yafita daga office d’in yanufi motarshi yashiga
Zaune Muneera tacin indomie dayaza meta kamar dole Kusan kullum sai taci sau biyu,
Zaune take da d’an Mini sirket sai Riga marar hannu
Kan yasha gyara Hankali ta
Kwa’nce don tasan. Ba yanzu yazeed kedawo ba
Sai K’arfe 6:pm
Yanzu kuma K’arfe 5:30pm
Har tashirya mashi Abinchi
Ta’aje
Jin k’ara bud’e Kyaure kawai taji dasauri tad’ago ido suka Had’a da Yazeed dake tsaye bakin k’ofar
Dasauri ta Mik’e zata shige d’aki
Yazeed dasauri yanufo inda take yatareta
“My Baby wannan punishment d’in Yayi yawa pls a sausata Mani”
Da’go ido takalleshi
“Yes My baby”
Rungumota Yayi
“Muneera kinsan inasonki
Wallahi yakamata tun ranar ki tsaya kiji ta bakina kinki
Muneera Wallahi bani nakawo Raudha Cikin Gidan”
Nan yafad’a duk yadda Akayi tazo da silar sake Had’uwarshi da ita A Nigeria
K’ara runkumemeta
“Pls my Baby kiyar da Wallahi kenakeso babu komai tsakani da Raudha lokacin da kika shigo mamatayi ta rungume ni”
Wani dogon Numfashi taja
“To meye silar dawowarka Gida da wuri?”
“Wallahi lokacin kaina keman ciwo kinji silar dawowa ta Gida”
“Pls My dear kiyarda Dani inasonki har Abda bazan b’acin ranki ba”
Tsakanin miji da Mata
Nan yararrasheta sai ga Muneera An lab’e jikin yazeed wadda tayi missing kwana biyu
Yazeed ko masallachi bai jeba Ranan A Cikin Gida sukayi sallar shida Muneera
Bayan sungama ne sukafito Palour suka zauna saiga yazeed Ana bashi Abinchi A baki
Bayan sungama suka dawo Palour suka zauna
Yazeed k’ara jawo Muneera jikinshi Yayi
“Miss you so much My dear”
“Uhumm”
“Menene to tare da shafa cikin ta kinga baki ci Abinchi mekekeso yanzu?”
“Indomie”
“Indomie tare ta zaro ido
Baki jimawa da cinta fa”
“Nidai ita nake so uhumm”
Kamar zatayi Kuka
“Shikenan tashi mu shiga kitchen d’in”
Haka suka shiga suka girka indomie taci sannan Hankali ta ya kwanta,
Suka zauna Palour suka d’ayin kallo Muneera jikin yazeed tana bacci d’aukar ta Yayi suka nufi d’aki suka kwanta,yau kowa zuciyarshi cike da Farin ciki,
_After 6 Months_
Muneera tsaye Cikin kitchen dakyar take d’aga kafarta saboda girman Ciki dake Jikinta
Yazeed ne yashigo
Tare da tausayi ta Ganin yadda Cikin ta Yayi girma
STORY CONTINUES BELOW

“My baby nace kidaina girki Amma kinki ji ko?”
“Yaya Yazeed bakaji yadda Mimi tace ba itada Kaka nadinga motsa jikina fa”
“Amma Aikin ya isa hakan pls”
“Nidai kabarni na ida pls”
Tajuya zata nufi Firji taji kafanta ya rike takasa d’agata ma
“Yaya Yazeed kafana”
Dasauri ya iso gareta
“Tashi muje Wallahi bazaki k’ara sa ba muje”
Amma Muneera takasa tashi
Can mararta taji da kugunta su d’au wani Azababatan ciwo
“Wayyo Yaya Yazeed Mutuwa zanyi kayafeman Don Allah ka kaini gun dady su yafeman wayyo Allah”
Tsabar rikecewa Yazeed yayi dasauri yazo Palour yad’auki waya number Mimi yabud’a kawai
“Mimi Muneera bata lafiya kitaimakeni kar narasa ta pls kuka yafashe dashi”
“Yazeed kashe wayan Ganinan zuwa yanzu”
Dasauri Mimi takashe wayan
Takira dady tafad’a mashi
Cikin sauri tashiga wajen Kaka tafad’aamata
Sannan tashi ga mota kawai tatafi
Cikin sauri tashiga Gidan Yazeed
Murya tajiyo A kitchen dasauri tanufi can
Yazeed ne ya rungume Muneera sai Kuka suke,
“Yazeed d’aukar ta muje mota”
D’aukar ta Yayi suka nufi mota
Mimi tayi driving
Yazeed kuma yana baya ya runkumeme Muneera
Suna shiga Asibiti Aka turo gadon d’aukar marar lafeeya
Za’anufi Labour Room da Muneera
Rike Hannu Yazeed tayi kawai
Yazeed yace sai anshigdashi
Laboour room
Saida Mimi ta rarasheni sannan ya Hakuri
_After 1hour_
Yazeed sai zarya suke shida Mimi haryanzu shiru babu wadda yafito
Turo K’yauren Akayi
Dasauri Yazeed ya isa gareshi
“Haidar ya matana?
Am sorry my friend….
[5/24, 12:13 PM] Indoo k’auye: *_YAZEED_*
_*NA*_
_*HAFSAT MUSA*_
*_(HAPSY BABY)_*
©
_*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*_
*_P.M.L_*.
*221_225*
“Am sorry my friend haryanzu muna k’okarin Amma har yanzu haihuwar bata zo ba ka k’ara Hakuri”
Tare da dafa kafad’arshi
Yawuce bada jimawa kuma yazo yakoma labour room d’in
Yazeed wuri yasamu yazauna ya had’a Kai da kafafuwanshi
Mimi girgiza Kai tayi ga tausayin Muneera ga na yazeed tanayi duk sunyi shiru Mimi had’e da tagumi jiran kawai suke a fito suji mai za’ace.
_After 1 hours_
Wata nurse ce tafito daga D’akin yazeed da Mimi kamar su fad’i suka tashi suka tare ta suji yayane
“Ku kwantar da hankalinku tasauka tasamu baby boy
Yanzu muna b’ukatar kayan baby ne”
Yazeed Nan danan ya washe Fuska “ya matata to ?”
“Duk suna lafiya lau sai yanzu tana bacci ne zaku yanzu kayan baby za’a bamu”
Dasauri Mimi tanufi mota dama tunda Yazeed yace Mata Muneera bata lafiya tad’aukosu tatafo dasu
Mik’a Mata tayi tajuya ta koma Ciki
Yazeed kam shidai Farin ciki yaga Muneera kawai
Bada jimawa saiga Nurse d’in tafito rungume da baby cin kayan shi nad’e nad’e da shawul sai tashin K’amshi yake,
Mik’a Mimi tayi
“Gashi tom”
Cikin murna Mimi tasa ta Amshi Jik’anta
Yazeed dasauri ya matsa kusada Mimi yana Murmushi, sai dai yakasa cewa tabashi ya gani dakanta ta fahimci abinda yakenufi, tace
“Gashi Allah yarayamana shi”.
” Wow!Mimi yaron yana Kama Dani ko?”
Mimi harareshi tayi
“Bansani ba katambayi yaron mana.”
Sosa k’eya ya mik’a mata yaron
Yace “Allah yarayamana.”
STORY CONTINUES BELOW

“Ameen kafin tafarka daga bacci Bari naje Gida yanzu dama jiya nayi ferfusu sai nahad’o Mata da ko tea”
“Shikenan Mimi sai kindawo”
Doctor Haidar ne yafito
“Cocrat my friend Hankali ya kwanta madam ta haihu ko”
Yazeed murmushi kawai yayi tare da cewa
“Thanks my friend”
Doctor haidar yace zaku iya shiga mu canza Mata d’aki zuwa na Hutu kan zuwa Anjima ko zuwa safe sai sallama tunda babu problem d’in komai tare da itah”
Tare suka shiga d’akin da Aka maida Muneera sukayi
Dasauri Yazeed ya isa ga Muneera datake bacci
Kuramata Ido mantawa da Mimi yayi dake tsaye,
“Sannu my secret luv so much tare da kwanciya jikinta”
Mimi yaji tace
“Amshi baby nan naje nadawo kafin tafarka”
Cikin kunya yazeed domin shi ya manta da mimi ma
Amsar baby Yayi Mimi tajuya tafita Yazeed shimfid’ar da yaron yayi Kusada da Muneera cike da so da kaunar su ya had’e ya rungume su.
Mimi mota tashiga tanufi Gida
Tana shiga ta iske Ayman da Kaka zaune Palour sunyi jugum
Dasauri Ayman ta mik’e tana ganin Mimi
” Mimi yajikin sister? “
Kaka tayi shiru tana jiran Abinda Mimi zata ce
“Alhmdlh tahaihu lafiya baby boy nan”
Ayman daka wani tsalle tayi tare da fad’awa bisa Kujera
“Alhmdlh Allah mungode maka Bari nakira janan”
Tare da Nufa d’aki da Gudu
Kaka murna take tace “me Akasamu kiyiman da yaren dazan gane”
Mimi dariya tayi “Ansamu d’a namiji”
“Alhamdullah to yanzu wakika baro Asibiti ne”
“Yazeed nabaro Amma nazo d’aukar mata Abinda zataci in tafarka ko”
“Shikenan Amma kar kibiye ma yazeedu da Ansallamoku Nan zaki nufo da itah dasan yazeedu ba Barin ta zaiyi tayi. Jego ba”
Cikin kunya mimi tawuce da maganar da Kaka tayi
Kitchen tanufa kawai ta zafafa ferfesu A oven tad’aura ruwan zafi a cooker gas Nan dan suka tafasa tajuye a flastic tahad’a komai na tea sannan tasamu basket ta jera kayan
D’akin Ayman ta Nufa
“Ayman bani. Kayanki wadda zasuyi ma Muneera”
Dasauri Ayman ta mik’e tad’auko wata sabuwar Atamfa wadda bata tab’a sa ta tafeshe da turere taba Mimi,
“Mimi gata nima Inan zuwa muda Janan tace na jirata gayanan”
“OK sai kunzo Bari nakoma kafin tafarka”
Haka Mimi tafito Janan da riko Mata kayan tayi tashiga wajen kaka
Kaka kara maimata matake kan ta wuto da Muneera Gida
Yazeed k’wance yahad’a jikin baby da Muneera jikinshi yanajin d’umin su cike da murna
Ahankali muneera tabud’e idonta dasauri Yazeed ya mik’e
“Baby love kinfarka sannu”
Almun mik’ewa takesoyi
Dasauri Yazeed ya matsa kusada ita yahad’a ta da jikinshi,
Kwantar da kanta tayi bisa shi
“Yaya Yazeed Ina babyn namu?”
Juyowa yayi bayanta yad’auke Baby sai bacci yake ga K’amshi tureren yanatayi nad’ad’e da showel,
Mik’a matashi yayi.
“Baby love ga babyn”
Sa hannu tayi ta k’arba ta kuramashi ido Wata kaunar yaron taji tana shigar ta
Bacci kawai yake
Had’asu yayi da baby ya rungume bakin d’aya
_*”LUV SO MUCH MY BABY*_
Kinga man komai ga baby na rike da ke Allah yayi maki Albarka”
Kissing d’inta yafarayi ta ko ina Amsar babyn yayi ya aje bisa gado
Yarungumota tsam tsam a jikinshi
Dai_dai turo Kyaure Mimi rike da kaya tashigo yanayi dataga Yazeed da Muneera yasata Komawa da baya
Muneera dasauri ta kwace kanta daga wurin Yazeed wadda keneman fita daga haiyacinsa
“Yaya Yazeed Mimi ce tashigo fa?”
Dasauri yagyra rigarshi ya saisata natsuwar shi
“Bari nazo”
STORY CONTINUES BELOW

Mik’ewa yayi yafito daga D’akin
Yana sosar k’eya yawuce Mimi binshi tayi da harara tashige D’akin .
Tana shiga Muneera ta sadda Kai
Mimi murmushi tayi irin nasu na manya
“Sannu Muneera kinji ko”
Tare da nufar gadon tad’auki babyn
“Kai maigida baka tashi daga bacci ba haryanzu?”
Muneera kanta yana k’asa dai tana watsa da Hannuta
“Muneera yanzu babu inda yake maki ciwo ne?”
“Eh Mimi banajin komai”
“Yauwa Haka ake so ai”
Yazeed yashigo yana susar k’eya
“Mimi kindawo.”
“Nadawo marar kunya”.
Yazeed dariya tare da cewa cikin Ranshi ” Kai Mimi nida matana”
“Muneera tashi mushiga toilet d’inan nagasa miki jikinki da ruwan zafi kafin mukoma Gida Ayi mai dalilin”
“Amshi nan karike yaron mufito”
Yazeed dasauri ya Amshi gudan jininshi
Mimi taja Muneera suka shiga toilet
Ruwan zafi ta Tara masu d’an yawa
Tad’auki towel tafara gasa Mata ko inah najikinta
Mimi nad’ora towel
Muneera tace “wash Mimi”
Mimi tace “Hakuri zakiyi fa inki kina son jikinki”
Haka tadaure aka gama suka fito daga wankan
Yazeed yana rungume da babyn shi
Mimi Kallon shi tayi
“To rasa kunya sai kabata wuri ta shirya ko bani baby nan”
Yazeed m’ika yayi ya mik’e
“Mutum da matarshi za’a Hanashi”
Office Haidar yanufa Kawai
Muneera ta shirya sai kace ba ita ta haihu ba
Mimi ta had’a tea mai zafi ta tura mata
“Amshi nan maza kisha da zafi”
Doctor Haidar yashigo yaga jiki yayi sauk’i sosai basu sallama yayi
Yazeed Amsar baby yayi yayi masa hud’uba
Mimi ta shiga had’a kayan dasuka zo dasu tayi
Basuda yawa tahad’a taba yazeed yakai Mota
Suka shiga mota itada Muneera Yazeed zaiyi Driving
Sunfara tafiya Mimi
Tace “Gida zakayi damu fa”
“Mimi wane Gida?”
“Wadda Aka Haifa ciki mana
Domin can Muneera zata koma har ta tagama wanka”
Wani birki Yazeed yasaki Allah kad’ai ya tsaresu
“Mimi tomezaihana Kaka ta koma can gidan tadinga kula da kula da ita”
“Bazata koma ba umurnin kaka ne da Dadyn ku”
Yazeed wani takaichi ya ziryaceshi jin Muneera zata koma Gida sai tagama wanka
Shiru yayi har suka isa bai k’aracewa uffan ba
Muneera dariya takeso yi gumtseta ganin yadda Yazeed ya sha K’amshi,
Mimi bud’e motar tayi tafita rike da babyn
Yazeed yajuyo wajen Muneera
“Baby love yanzu shikenan zanyi nesa dake fa”
“Yaya Yazeed yazamuyi
Umurnin ne fa”
“Aidama haka kikiso kiyi nesadani ko”
“Yaya Yazeed…..”
“Kinga Banason jin komai kibarni da Abinda yadameni”
Bud’a murfin mota tayi tafita cikeda da tausayin yazeed
Yazeed tana fita yaja motar dagudu yafita daga gidan
Muneera ta juyo taga yadda Yazeed yaja motar yafita
Itakuma Muneera tashiga ciki…..
YAZEED*_
_*NA*_
_*HAFSAT MUSA*_
_*(HAFSY BABY)*_
©
_*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*_
*_P.ML_*.
*226_230*
Muneera girgiza kai tayi
“Yaya Yazeed kacika girma”
Tajuya tashiga ciki
Tanashiga taradda kaka, Mimi sai Ayman dasauri Ayman tataso ta iso wajen Muneera
“Sannu my Sister da haifamana baby boy”
STORY CONTINUES BELOW

Muneera murmushi tayi kawai tanufi wajen kaka tazauna
“Kaka”
Kaka dake rungume da jariri yanata bacci
N’aam Jumallah sannu kinji ko badai kinji wani matsala jikinki yanzu ko”
“Eh”
“To madallah Ina yazeedu?”
“Yaje yadawo ankirashi office ne”
(Kaji muneera)
“Toh Allah yataimaka yaraya shi”
Mimi tace
“Muneera ga d’aki can Angyara kije kikara hutawa kinji ko”..
” tom Mimi tashi tayi tanufi d’aki domin wani bacci takeji”
Amsar shi yaji d’umin mahaifiyarshi anjima kifara bashi Abinci”
Amsar baby tayi tanufi d’aki dashi tabar Ayman Palour
Tanashiga tahaye Gado tare da baby wani Bacci yad’auketa
(Nace Muneera Sannu nakuda badad’i duk ban tab’a junta ba)
Yazeed yana fita cikin fushi Gida kawai yanufa yayi parking, d’in motar shi yafito,
Yashiga cikin Palour ya yadda zango bisa Kujera tare da dafe kanshi
“Wai Mutum da matarshi Amma zatayi nesa dashi”.
Shakar K’amshi Palour yadinga wadda muneera kullum sai ta feshe da tureren wuta babu rana kobata lafiya tayi k’arfin hali gyarashi
Shiyasa koda yaushe cikin K’amshi tureren wuta yake
Tashi yayi yashiga toilet yayo wanka d’auko hollidia yayi tare da cake yafara ci badon yakoshi ba Don Muneera ta Saba da had’eden Abinchi wadda zai wuni yana santi.
K’iran sallar magariba yadatashi ya mik’e yanufi masallachi sai yagama sallar isha’i sannan yafito
Babyn shi kawai yaji yanson k’ara Gani mota yashiga kawai yanufi gida,
Yana shiga ya iske Mimi da dady Palour
Wajen Dady yanufa ya tsuguna gabanshi
” dady barka da dare”
“Yauwa Baban baby”
Dasauri ya sunkuyar da kanshi jin Abinda dady yace
“Tom Allah yaraya ya Albarkacin baby kajiko”
“Ameen dady”
Yad’an dad’e zaune sannan yatashi yashiga d’aki
Kaka ya iske zaune sai Ayman dake like da waya can gefe
Muneera rike da cooler tuwo da miya wadda miyar tashi tashin daddawa Muneera batasan shigowar yazeed ba
“Kaka nakoshi”
Daurewa zakiyi kici Kafin yafad’a cikin ga kunun kanwa yanajiranki”
Muneera tura tuwon take
K’amshi tureren taji na Yazeed dasauri ta d’ago taga ya harde bakin k’ofa
Kur’a mashi ido tayi tana Kallon shi
“Mikeke kallo bakin k’ofar?”
Kaka juyawa tayi ganin Yazeed tayi
“Kiceman marar kunya mijinki kikagani”
Yazeed ida shigowa yayi yazauna kusada Kaka
“Kaka menayi na rashin kunya?”
“To kazo katasamu gaba kana Kallo ne”
“Matana nake kallo Ai bake ba ko”
Jariri ne yafara kuka dasauri Yazeed ya Mik’e ya nufi inda aka sa mishi d’an gadonshi
“Ikon Allah”
“Menene kaka jinayi yana kuka fa”
Mik’a Muneera shi yayi Amshi nan rarasan man manshi”
Amsar tayi tafara ririgashi
Kaka tace d’aga rigar kibashi Abinchi shi Gani Muneera nuko nuko d’aga rigar take
Kaka tasowa tayi daga inda take zaune
Tad’aga rigar ta sama yaron A baki
Nan dan ya cafe yafara sha
“Wash kaka da zafi fa”
“Aihaka zakiyi Hakuri har ki Saba fa”
Yazeed duk yana Kallon yadda suke
Kaka tajuyo wajen Yazeed
“Mara kunya”
“Kaka menayi?”
Waikayi tsaye kana Kallon Mata ai shiysa nacema “Hafsat tawuto da ita nan.”
Suna zaune haka Muneera itadai sai cije baki take saboda zafin datajeji
Bayan tagama shayar da shi tagoge mashi bakin shi ta maida shi A d’an gadonshi ya cigabada Bacci.
Dady yashigo shida Mimi
Dasauri Yazeed ya mik’e yakoma kusada muneera,
“Inna nad’auka kinkoma ne”
“A’a”
“Yazeed wai kayi ma yaron Nan hudu’ba kuwa?”
“Eh Dady yaci sunan uncle Umar ne”
“Allahu Akbar
Yazeed Allah yayi maka Albarka yaraya Umar yasa yasa yayo mai irin halin Allah yajinkaka d’an uwana yau burimu ya cika babu Kai”
Dady Mik’e yayi yabar d’akin domin mutuwar d’an uwanshi tadawo mashi sabuwa,
Mimi tabi bayanshi
Muneera kuwa dama tunda Yazeed yace sunan shi Umar faruq, Hawaye suka fara Mata zarya A Fuska.
Kaka itama tunowa da d’an datayi yasata Hawaye itama Mik’e tayi Akabar Yazeed da Muneera d’akin dama yazeed bai d’ade da shigowa ba Ayman tabar d’akim,
STORY CONTINUES BELOW

Yazeed matsowa yayi kusada Muneera dake kuka tunowa da Mahaifinta datayi
Dasauri ta fad’a jikin yazeed
Ta fashe da kuka
“Yaya Yazeed nagode da wannan karammawa dakayi nagode Allah yajikan Baba..”
“My baby meye nagodiya karki manta nima fa mahaifi na ko
Don haka kidaina yiman asarar Hawayen ki yanzu tsakanin dashi Add’ua shida umma kodayaushe kinji ko
My beautiful lady”
Nan yararesheta tadaina Kuka Amma tana jikinshi k’wance shikam yana shafar kanta kamar wata baby
Jawota suka kwanta bisa gado tare
Bacci yad’aukesu suduka haka.
Can sukaji K’arar buga Kyaure yazeed shimfid’ar da Muneera yayi yagyra Mata kwanciya yanufi k’ofar ya bud’e
Mimi ce tsaye
“Yazeed dare ya farayi fa baka tafi ba”
“Yanzu zani Mimi”
Tajuya takoma
Yazeed yakoma cikin d’aki
Kissing d’in Muneera yayi sannan yanufi gadon Baby yayi mashi kiss sannan yafito yayi masu saida safe yashiga mota yatafi cikeda da kewar matarshi da yanzu tare da junansu zasu kwana.
Yana shiga yayi parking yafito wanka kawai yashiga yafito yazira kayan bacci yahaye gado Amma yakasa bacci saboda Muneera Bata kuwa
Ayam ce tashigo taga Muneera ta dafe dafe pillow ga baby yana Kuka Ahankali tafara tadata
“Sister Sister”
“Yaya Yazeed uhumm”
“Kitashi bashi bane ba to”
Bud’a idonta tafarayi A Hankali taga Ayam Kusa da ita
“Ina Yaya Yazeed?”
“Yatafi gida ma
Amshi nan bashi Abinci shi yaci ko nakira Kaka”
Amsar baby tayi tasa mashi Abaki yafara sha yanagamawa ta kwantar dashj gabanta tanajin d’uminshi”
“Sister bani Aron wayan ki nakira Yaya Yazeed”
Ayman Mik’a Mata tayi
Number yazeed kawai takira
Ringi biyu ya d’auka
“Hello Yaya Yazeed”
Na’am My Munee kashe nakiraki”
“Tom”
B’aa jimaba yakirata
“Yaya Yazeed shine katafi ko”
Yazanyi my Munee Mimi ce tazo taceman dare yayi fa Mutum da matar shi Amma babu ikon ya kasance tare da itah yanzu kiganni nakasa bacci saboda nakasa jinki kusada dani”
“Yaya Yazeed Kayi Hakuri nima nayi kewar ka fa”
“Uhum ina my Boy na?” “gayanan A Kusada Dani yana bacci”
Kishafaman kanshi kafin gobe insha Allah “
Haka suka dinga fira sukayi bankwana takashe wayan
Ajema Ayman wayar tayi wadda tuni tayi bacci itama tagyra kwanciya tayi Addu’a tashafa ma itada babyn ta sai bacci
Asuba tagari.
_K’arfe :7 30am_
Muneera Bacci kawai take Kaka tashiga tadin ta
Jumallah tashi ga ruwan wanka can toilet muje
Tashi tayi kawai tanufi toilet d’in itakuma Mimi tad’auki baby tayimashi wanka yana d’anyara kuka anayi Mashi wanka dai_dai shigowar yazeed cikin shirin office ya isa wajen Mimi yagaidata
“Mimi bai lafiya yake kuka ?”
“Lafiyar shi lau tsoron Ruwan dai yake Wani yaron yanayi hakan”
Haka tagama mashi wanka Duk Yazeed yana zaune har ta shiryashi yanata K’amshi tureren
“Amshi nan mai d’a tund’azu sai Kallo shi karbi nan”
Cikin kunya yakarbeshi daga Hannu Mimi itakuma tashiga Kitchen ta idar da Breakfast
Mik’e yayi ya nufi d’akin iske Muneera Yayi Tasha make up Kamar Bata haihu ba kaka tana gabanta ta tisamata Ferfesu had’e da Kunun k’anwa
Tana sha
Gaisa Kaka yayi
Muneera ta juyo tagaida shi Ayman dake shirin school itama tagaidashi
Saida Yazeed yayi Breakfast sannan yanufi office
Nan makwafta suka dinga shigo Anayi ma Mimi barka.
_*RANAR SUNA*_
Yaro yaci sunan Umar Faruq(sultan)
Sai fatan Allah yaraya shi
Anyi taron na kece raini
Dady da Yazeed sun kashe Kudi’ na Sosai Anci Ansha
Kowa yazo sunanyasan An kashe kudin
Na hanging su Salma b Umar, Nana A Usman ,
Dangi Juna&yazeed fan’s
Tare da Yar Gata ce Fan’s Club, Sulaihat, Fateema Zahra, Hafsat musa fan’s,
Ummun Yusuf, Zahra bintu mahamad,Aunty Saheeba,jiddayen Mama,Hafsat Mahmoud (Name sake)
Daga can B’angaren guda kuma yan Pure moment of life writers ne,rumfar su Dabam.
Muneera sai godiya takeitada yazeed ga masoya Dukkan wadda suka hallata wadda sunan su bai Fad’uwa cikin wannnan litafin Dukkan su Muneera da Yazeed suna godiya halatar bikin sunan yaron su.
[5/24, 12:16 PM] Indoo k’auye: _*YAZEED*_
_*NA*_
_*HAFSAT MUSA*_
*_(HAPSY BABY)_*
STORY CONTINUES BELOW

©
_*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*_
*_P.M.L_*
*_LAST PAGE_*
*231_235*
Tunda taron suna ya watse yazeed ya maida da Gidan Dady wajen hirar shi, shi A dole yazo ganin d’anshi
Tun Mimi tana shiru har soma Fad’in .
“Inda bakar mana sintiri a gida , zamu canza masu wurin zama , wato mu bakajin nauyi mu ko?”
Yazeed yace “Mimi kuma ya manta Babanshi ne inda ban zuwa ?”
Dariya Mimi tayi tana Kallon Yazeed, a zuciyarta ko dad’ine fal!
Tasan harda ganin uwar ke kawoshi sai ta tuna can bayan lokacin da ya nuna tsantsar tsana ga Muneera yakafe bayasonta shi saboda tana yar kauye yanzu komai ya zamo labari.
“Don Allah Ku koma gida, haryanzu Baku Gama wanka ba ? Komai Mutum baya yinsa ta dad’i duk rashin ki kusadani My Munee basan wata Mata ce ta kirkoro wanka gidan Nan ba wallahi.”
“Yaya Yazeed kayi Hakuri kaga yanzu mukayi sati ukku, saura mu sati ukku kuma, don haka rabi kenan, saura rabi.”
“Amma My Munee ban tab’a sanin baki tausayi na sai yau sati ukku kikeso naka’ra baki kusa dani ? Lalai Kama”
“Allah da gaske haka Ake sai nayi Arab’in in nagama sannan na koma, wasu har sittin suke na.”
“Ai dai nikam sai nad’auke d’ana inhar saikiyi Arbain zaki koma kisha zamanki, don Allah yagani inada buk’atar Kusa, “
Kallon satayi tace “yaya Yazeed sai dai kayi Hakuri kam, Amma Kasan Kaka da Mimi, bazasu tab’a yarda nakoma kafin Arbain,”
Wani kallo yai Mata ya gwada wasa fa yakare, yanzu zance gaskiya yake Mata
“To shikenan nidai Zan musu magana, Amma idan sukace zasu cigabada da rike ki sai su gwadaman inda Addini yace ayi haka. Don haka siddan baza’a jefa mutum cikin Wani hali ba”
Ya mik’e yabar d’akin,
Muneera binshi tayi da kallo ranta ya sosu, don me Yaya Yazeed zai d’au zai d’au wannnan zance da zafi?
Sai kace ita ta kafa Al’adar?
Tasa ransa a bace yake,
Don ko sake d’aga sultan bai iyiba yabar d’aki
Agogo takalla taga 11 saura na dare Kusan kullum sai yakai haka ko tsoron hanya bayayi, kwanciya tayi tare da rintse idonta,sultan taji yafara kuka d’aukar shi tayi tabashi madarar data had’amashi,
Sannan sukayi shirin Bacci suna shirin bacci sai ga Ayman tashigo
“Sister har yaya Yazeed d’in yatafi ne?”
Muneera tab’e baki tayi tahaye Gadba
“Eh”
Wayar Ayman tasake k’ara hayewa tayi gadon ta na
Har Bacci yad’auke Muneera Bata Gama wayar ba
Washe gari, Kamar yadda kaka tasaba yimata wanka haka tayimata Mimi kuma tayima sultan,
Suka shirya sai tashin K’amshi suke
Kallon k’ofa take taga Yazeed ya billo Amma shiru,
Har wajen k’arfe goma shiru baizoba tasan fushi YYayi
Wajen k’arfe 12 saiga Janan tashigo dasauri Muneera ta tashi ta taro suka zauna Palour
“Tawan kinga yadda kika koma kuwa kamar baki haifi
” baby sultan ba”
“Kai Besty bana son sharri fa”
“Allah kuwa dagaske nake”
“Uhumm ya school d’in ?”
“Kibar mu na wahala”
“Zan koma very soon kar nahadu da Carry over”
“Gashi kuma exam d’in first semester tatafo”
“Shikenan Allah taimaka kikawoman Hand out d’inki naduba kafin Anfara test nakoma kinga bazan sha wuya ba”
Mimi dake tafowa rike da coleer A Hannuta
Har kasa Janan ta durkusa tagaida Mimi
Cikin Fara’a Mimi ta Amsa
“Ina Hajiya meenaral?”
”Tanan lafiya lau tana gaisheku sosai “
“Muna Amsawa Amshi nan Muneera maza kincinye Duka”
“Tom Mimi “
Amsar cooler tayi
“Janan Bari nazubo miki naki”
STORY CONTINUES BELOW

“Sister wai ina Ayman tana d’aki itada sultan kinsan yanzu takoma yar waya kullum tana like da waya”
Muneera tana Bud’awa taga ferfesu ne yaji su citta da karumfani, sai daddawa tuni tasaba da cinshi, tahau ci
Saiga Ayman tafito rike da baby sultan A Hannuta
Ganin Janan nan suka zauna sukai ta fira Muneera Abin kad’an ta kalli k’ofa taga yazeed Amma shiru
Sai tabari k’ila sai da daddare zai zo
“Tawan Bari naje Haisam yakirani ga yana hanyar zuwa gida”
“Hmm kaji Amaryar Haisam A Mik’a Mani gaisuwa ta to”
“Zayaji muma dai munkusa Auren nida My Haisam sai Abar so o’o takalli B’angaren Ayman dake zaune”
“Hmm shiru nayi na kyaleku nima nawa gwanin yanan mai baki d’aya zanyi”
Nan Janan tayi musu bankwana tatafi
Har dare babu labarin Yazeed bai zoba Muneera Bata damu A Fuska Amma cikin ranta ta damu sai dai Bata nuna ba.
_Bayan kwana biyu_
Cikin kwana biyu nan yazeed bai zo ba Muneera ta damu matuk’a da rashin zuwa Yazeed zaune take d’aki sultan yana hannu Mimi
Wayarta tajawo number yazeed takira
Saida Aka jima sannan yad’aga
Lafiya lau suka gaisa
“Yaya Yazeed wai meke Faruwa kwana biyu najika shiru ko baka lafiya ne?”
Saida Aka jima sannan yayi Mata magana
“Lafiya lau nake Bana gari ne”
“Banganeba baka gari”
“Inan Abuja nazo Wani meeting ne”
Muneera takaichi yakamata dasauri ta kashe wayar tajefa bisa gado
“Wai yaya Yazeed yakeso meyasa yakemata haka?”
Haka sukayi sati tun tana b’oye bai zoba tun tana b’oye damuwarta har takan zauna ta buga tagumi tana tunani, don gaskiya daga ita har Sultan sunyi kewar shi.
Ranar dayacika sati ne, tana zaune d’aki tana Aikin tunani, tasa sultan gaba Ayman taje gidan wata yar department d’insu Biki,
Kwatsam! Taji muryar shi Palour shida Mimi,
Kamar ta mik’e tafito da gudu taganshi Amma tayi za manta, saboda ita Fushi take don me zai sharesu?
Ad’aki ya shigo ya samesu bayan yagama gaisawa da Mimi da kaka,
Yana shigowa yaji Wani Abu yabi ilahirin jikinshi, domin kuwa Gani yayi kamar A canza Masu, sun k’ara kyau da cika, da Alama dai su Hankali su kwa’nce basu da mu da shi ba.
Wata doguwar Riga ce A jikin ta Atamfa mai kalar blue and yellow tabi Jikinta ta lafe ko ina yafito da kyawun surarta cikinan shafal Kamar ba itace ta haihu ba siririn hannu ne dashi Amsa d’inki sai kace (Ready made,)
Ta tufke gashinta, sai jeler gashin sai yawo take tsakiyar bayan ta,
Fuskar ta sumul! Sai sheki take Tamkar yadda fatar Jikinta tayi yak’ara Wani haske da sheki!
Yakeyi, domin taga nesa yasan inda ya tab’a Fuskar ta laushin da zaiji ko meye sirrin?
Wata zuciyar tace masa, wane sirri kuma?
Kawai ta kwantar da Hankali ta, shiyasa tak’ara kyau gwamma sultan shi jinjiri ne baisan me Ake ciki ba Amma uwar tasani ta share ka ,
Kallon sa tayi tace
“Sannu da dawowa”
Aranta itama Kallo shi takeyi , bai damu dasu ba tunda har yayi tafiya yayi sati, bai damu yakira ta ba,
Taga har Wani bul!bul!
Yayi wai shi yaje Aiki.
Kai tsaye takowa yayi yad’auki sultan dake shimfid’e yakare mashi kallo ya manna mashi kiss a fuska had’e da shafa kanshi sannan ya maidashi cikin d’agadonshi.”
“Yaya muna zamun kalau zaka zo ka d’aukar manshi?”
“Yaya zaki ganni, kinuna baki damu dani ba?”
Yafad’a idonshi cike da Al’a Murra, idan ta tsaye biyemashi Hawayen datake makalewa sune zasu biyo Fuskar ta don Haka Mik’ewa tayi dasauri fice daga d’akin gaba d’aya tunda d’anshi yazogani.
STORY CONTINUES BELOW

Hannuta ya jawo da K’arfi, sai da tataho gareshi, yariko bayanta yahad’a da jikinshi, idanu yazuba Mata yana Kallon ta itama shi take Kallo tana haki Kamar tayi gudu, zatayi magana ne yasa yatsan sa d’aya yarufe Mata baki, had’e da shafa labbanta dayake matukar so.
Gani yayi Kamar sun Kara Wani light pink gawani K’amshi tureren datakeyi na mussam
Lokaci d’aya suka shiga nuna junansu kewar dasukayi,
Can yadaure yasaki lips d’inta
“Zaki shirya mu tafi ko kuwa kizab’i kicigabada da Azabatar da mu ?”
Kunya yarufe ta sosai ita kanta batasan tayi missing nashi ba Haka sai yanzu don haka baya tajuya mashi tana murmushi sannan ta fice d’akin Yazeed yabi Bayan ta yana murmushi yashafa :kanshi
Tabbas yau bazai bar gidan nan ba sai Anbashi matarshi ko sungama ko basu Gama ba gama ba
Saidai duk zakeawarsa yaka musu da Mimi data kafe sai ta k’ara sati d’aya shi yarasa Abinda Muneera take musu a gida dasuka riketa kawai sunsa tayi Wani kyau sannan sai fama Hanashi suke,
“Kaka Wallahi inason Ganin indo ina yawan tunanin ta a raina”
“Kiyima Baban Ku magana zuwa jibi sai muje ko”
“Shikenan to”
Muneera taje ta iske tayi mashi magana yace tashirya jibi sai Yazeed yakaisu
Jibi nayi suka shirya yazeed yakaisu
Muneera taga Kauye duk ya canza Mata,
Amma gidan su Aminiyarta baicanza Mata ba can suka shiga Akabar Yazeed mota rike da sultan yana tsegumi Angajiyar mashi da d’an
Innar su indo takarbesu Amma Bata ganesu muneera sai tayi Mata bayani nan Aka rakata gidan Aminiyarta indo.
Tare da suka shiga da Muneera da Kaka sai Ayman
Indo tana gindin Murhu tana hura wuta sallama Muneera tayi indo tad’ago Fuskar ta dake Hawaye saboda hayaki datake
Tsayawa tayi tana Kallon su
Can dai kallon ta yatsaya da Kaka
“Kaka kece”
Nice dasauri ta rungume kaka
“Kaka ina Jummallah take? ina Aminiyata wadda kullum tana raina”
Jitayi anjawo Hannuta d’agowa tayi suka tsura junansu kallo
“Indo Ashe zaki iya mantani Ganinan nice Aminiyarki jumallah runguma juna sukayi suka fashe da kuka
Sai da Kaka da Ayman suka rarrashesu sannan sukayi shiru,
Nan tsakar gida sukayi shimfid’a suka zauna
Indo takawo masu ruwa tunkuya masu sanyi suka sha,
“Indo ina Tanimu?”
“Bayan tafiyarki Tanimu yasha jinya da rashin ki sosai da taimakon Allah ya warware
Yarokeni dana Aure shi koyrage rad’ad’in rashin ki inyana gani na
Nan na Aminche Akayi Aure mu dashi har yanzu muna tare Amma Allah bai bamu haihuwa bahar yanzu”
“Indo kin cika Aminiya ta kwarai nagode da wannan halacci dakikayi indo “
Shigowa Akayi tare da sallama Muneera bazata manta muryar Tanimu shine sab’e da Kayan Aikin nima.
Gaisawa sukayi zai wuce ciki.
Info tace “mai gida baka gane Jumallah da Kaka ba?”
Dasauri yajuyo
“Jumallah kece nake gani?”
“Nice Tanimu ya Bayan saduwa?”
Nan suka gaisa da Tanimu Sosai Muneera tashi tayi tafito wajen Yazeed dake cikin mota rike da sultan,
Tare suka shigo da Yazeed cikin gida
Yanayi dayaga suna ciki
Yazeed yaba Tanimu kud’i masu yawa wadda zasu isheshi jari yayi wata san’aa Tanimu yayi godiya matuka. Sannan Muneera tabata sunan garin datake har unguwar datake dayake Tanimu yad’ayi primary kuma yand’an ganewa nan Yazeed yarubata mashi Address d’insu da unguwar dasuke,
Nan suka jima sannan su Muneera suka shiga makwafta inda ake Mutunchi duk yazeed yayi masu Alheri,
Indo da Tanimu har wajen gari suka rako sannan sukayi bankwana cike da kewar juna.
Muneera sai dare suka isa suna isa gida Mimi had’a Ruwan zafi tayi Muneera tashiga Mimi kuma tayi ma sultan,
Yazeed bankwana yayi musu ya tafi gida,
Sati nazagoyawa Mimi tace tashirya zasu gidan kanwar ta
Wayyo Allah Yazeed yazo yaga batanan Kamar ya fashe da Kuka part d’in dady yanufa kawai Kamar Yayi mashi Kuka Nan Dady
Yace
“Kayi Hakuri yau bazaka wuce ba sai da iyalanka,”
Da magariba suka iso sun zo sun samu ya tatara kayan Duka Kayan su ya tafi dasu,
Muneera duk kunya takamata,
Ai za kewar tayi yawa Yazeed ko A jikin sa. Yanzu ko share_ share bazai barta
Tayi va
“Gobe Mimi ta turo Ayman ta tayaki”
Yarungimi sultan sukayi gaba”
STORY CONTINUES BELOW

Muneera ta tsorata da Yazeed don ita kam sai yadda hali yayi da ita nan a shirye take da bakanta.
Hmm!
Nidai Hafsat, saidai na tatara Kayana saboda tsoro, don yau filin na Mayan ne nabar Yazeed da Amaryar karninsa ko za su fi sakewa don Haka na koma masu gadin baby sultan don nasan lamarin nasu , zai wuce tunanina,
Bayan wata shidda sultan yak’ara girma sai kace d’an one year Muneera Andage Karatu Sosai har sun shiga level two,
Anyi Bikin Janan da saurayinta Haisam,
Sai Ayman da Doctor Haidar Abokin Yazeed wadda sai daga Yazeed yagane shike son Ayman
Soyayya da kulawa Muneera da Yazeed Kamar me.
_*AFTER FIVE YEARS*_
wasu kyakywan yara nahango zaune Palour can yarinyar ta Mik’e zata Fara Kuka can nahango Muneera tafito daga d’aki tak’ara Wani kyau Masha Allah dasauri yarinyar tataho wajen Muneera
“Umma Kinga Yaya sultan yashanye man chocolate da Abba ya siyoman”
“Sultan meyasa kashanye mata Mata ne”
“Umma itabani fa”
“Sorry Kinji baby na Bari Abba ya tashi yasiyimaki”
“Umma hardani nima”
“Baza’aje dakaiba”
Yazeed ne yafito daga d’aki dasauri sultan yaje wajenshi
“Abba Wai Umma tace baza’aje dani ba kasiyaman Chocolate “
“Sorry sultan sai muki zuwa da da Sultana d’in”
Direre kafafuwa tayi tafarayi
“Sorry Baby na dake za’aje kinji ko
Yazeed suka fito cikin shiri tare da sultana wadda taci sunan Mimi aka
Suka shiga mota suka tafi,
Sun shiga sun siyo chocolate sunfito kicibus sukayi da wata Mata
Yazeed janye hannu sultana yayi dake hanya
Jiyayi ance
” yazeed” dasauri yajuyo
“Raudha”
N’aam Yazeed wanna baby’s d’in ka ne?”
“Eh”
“Meye sunan su ?”
“Umar Faruq da Hafsat
Amma sultan da sultana ake cemusu”
“Allah yaraya”
Nan taja hannu su suka shiga super market d’in takarayomasu siyaya tafito dasu
“Yazeed kayafeman Abinda yafaru don Allah bayan Bari na office d’inka nafad’a harkar shaye shaye fiye da da nike yi Maihaifina yayi Nadama domin shine sanadiyar sani wanna halin
Anahaka bana gida natafi Wajen yawona gobara takama gidanmu komai ya kone har da iyeyena suka kone
Nayi kuka da Rashinsu daganan nafara shiga taskun Rayuwa da Wahala babu inda zan rab’a naji d’adi wani babban malami yaganni bisa titi yadda nake Wahala yad’aukeni yakaini gidanshi nai ta neman yafiya daga ubangiji na nan nashiga islamiyya
Har wani babba Mutum dattjo yafito yanasan Aure na bqbu gardama na Aminche mukayi Aure dashi yarmu d’aya Rukkayya gatan”
“Masha Allah Raudha dama tuni nayafemaki Abinda kikayiman Allah yayefemana nima Harda kin bin umrnin iyaye da zabin dasukayi man shiyasa naga hakan”
Nan yayimata kyautar kud’i yaja Hannu sultan da sultana suka shiga mota
Har suka kulle Raudha na Kallo su Fashewa tayi da kuka tana danasani A rayuwar ta da yanzu wannan yayan natane
Tak’ara godema Allah dayafawo daga ita Hanya maidaidaciya.
Yazeed suna shiga yaji Palour shiru cema su sultan yayi su tsaya Palour Bari yaje kunna musu Kallo yayi yashiga ciki.
Muneera Bacci take har inda take yataka hayewa gado yayi tare da jawo Muneera
“My Munee wanna Bacci Nan kodai Ansamar ma sultana yar Uwa ne?”
*
“Hmmmm A’a gajiya ce nayi Yaya Yazeed”
Tashi yayi kulee k’ofa yadawo jawotayi
“Yanzu kuwa zan sauke maki ita”
Muneera tazama cikakiyar yar jarida Amma yazeed yace baza tayi Aiki ba
Soyayya suke Tamkar kar su rabu da juna
Yazeed kullum kaunar Muneera yake karayi
Cikin Ranshi
Yagode ma Allah da Muneera tasake zama matarshi Karo na biyu
Har Abada Ranshi kuwa yakance nagode ma Allah sosai gaba ko waye naga zai raina zabin iyeyenshi ko ya raina mace na Hanashi”
Alhamdullahi godiya ta musamman ga Allahu (S.WT)
dayabani Ikon Ganin karshen wannnan labarin mai suna Yazeed