ZABI NA CHAPTER 10 BY FADEELARH
GARKUWA HOSPITAL
SULTAN ROAD
Zayd ne ya shigo asibitin hankalin shi a matuqar tashe.. Da ganin yanayin shi ka san akwai matsala.. Sanye yake cikin wandon sweatpant baqi da farar Jallabiya doguwa wadda ta bala’in yi mishi kyau dukda kuwa yana a hargitse.
Asali dai Zarah ce tayi ta Kiran wayar Ameera dazu bayan an tafi da ita asibiti.. A lokacin Aliyu ya shiga dakin Umma shine ya ji wayar tana ringing.. Ko da yayi answering ya sanar da ita abinda yake faruwa sannan ya fadi mata asibitin da ya san suka je (GARKUWA HOSPITAL) dayake dai Abban su yana da NHIS a asibitin duk nan suke zuwa.. aikuwa a rude ta kira Zayd ta sanar da shi.. Yanzu haka ya riga ta isowa saboda ya fi ta kusa da asibitin..
“who is the senior doctor in charge here??” yayi tambayar demanding a straight forward answer.
Nurses din da suke tsaye a reception gaba dayan su suna kallon shi yayinda suka kasa magana.. Dukkan su sun sanya mishi idanuwa babu ko qyaftawa, da alama suna checking dinshi out ne.. Ganin lallai hankulan su sunyi nisa ne na ga ya buga slab din da yake gaban su cikin fada yace “are you deaf?? I said who is in charge here??”
Gaba dayan su sai da suka zabura yayinda suka rude. Hatta patients da Visitors din da suke Reception din sai da suka juyo suna kallon shi..
Daya daga cikin su ce tace “sorry sir, its doctor George and he is in the ER along side other doctors right now”
Gani nayi ya shafa gashin kanshi da hannuwan shi biyu sannan yace “I am here for a certain Mss Ameera Farouq.. take me to her”
Da sauri Nurse din tace “just a minute please” Computer dinta ta shiga dubawa don ganin inda aka kwantar da wadda yake nema din yayinda sauran nurses din suka sa mishi ido.
“she is in the ER right now and is receiving an immediate medical attention..”
“what’s ER?” yayi tambayar yana kallon ta
Gaba dayan su sai da suka yi mamakin yadda aka yi bai San ma’anar ER ba considering the fact that he is a learned person.
“Emergency Room Sir” cewar daya daga cikin su.
“Ya salaam..” ya fada a hankali yayinda ya qara shafa kanshi da hannuwan shi biyu.
Su dai nurses sai kallon shi suke yi suna mamakin kyau da haduwa irin nashi kamar shi yayi kanshi.
“take me there right now” Ya fada hankalin shi a tashe
“Sir, no one is allowed in..”
“okay, I will find my way” daga nan ya juya ya fara bin dakunan asibitin yayinda nurses din suka biyo shi suna bashi haquri akan ya dakata har likitocin su fito.
A lokacin da ya qaraso Emergency room din da Ameera take ne su Abba wanda suke zaune suka jiyo hayaniya.. Ganin Zayd yana qoqarin shiga dakin ne Abba yayi saurin miqewa ya riqo hannun shi..
Nurses din kuwa suka tsaya cirko-cirko suna gode ma Allah da aka dakatar da shi.
“Abba me ya same ta? na ji ance tana emergency.. wane irin faduwa tayi?” yayi tambayan wadda daga ji kasan yana buqatar amsa cikin gaggawa.
Babu shiri Abba ya fara bashi labarin abinda ya faru har lokacin da suka kawo ta asibiti..
“wannan wane irin faduwa ne mai qarfi? tura ta aka yi kenan ko kuwa ruwa ne ya zuba ta zame??”
STORY CONTINUES BELOW
Abba yace “Tabbas babu ruwa kuma bana ji ture ta aka yi… tsautsayi ne dai. Ka kwantar da hankalin ka Zayd.. insha Allah she will be fine..”
Runtse idanuwan shi yayi ya bude tare da sakin ajiyar zuciya..
Hango Umma yayi zaune a kan kujera tare da Ibrahim suna ta share hawaye.. Ba sai an fadi mishi ba da ganin ta ya gane mahaifiyar Ameera ce don suna kama..
Da sauri ya qarasa wurinta ya duqa har qasa ya gaishe ta.. ita dai ta amsa shi amma bata gane shi ba. Ibrahim ma gaishe shi yayi yana yi mishi kallon sani amma bai gane shi ba..
“Zayd ne.. na san baku taba haduwa ba” Abba ya fada
Umma dai qara kallon Zayd din tayi tana mamaki.. ashe ma balarabe ne?? Ibrahim ma sossai ya cika da mamaki.. Zayd din da yake zuwa wurin Yayar su Layla shine wannan??
“Allah sarki.. aikuwa bamu taba haduwa ba”
Sai a lokacin ne Zayd ya tuna bai gaida Abba ba..
Da sauri yace “Abba ai bamu gaisa ba, ina wuni”
Abba yayi murmushi yace “da ka zo a hargitse ta ya zamu gaisa???”
Dukda hankulan su da suke a tashe sai da suka murmusa yayinda Umma take yaba hankalin Zayd din.. kasancewar shi mai arziki bai nuna alamun girman kai ba ko alama.
A daidai lokacin ne Zarah ta qaraso itama hankali a tashe. Tare da driver ta zo don kuwa Mustapha yayi tafiya amma tana sa ran dawowar shi gobe.
Har qasa ta duqa ta gaida su Abba sannan ta kalli Zayd tace “how far? how is she??”
“No news yet.. tana emergency”
“Subhanalillah.. Allah ya bata lafiya”
Gaba dayan su suka ce “Ameen”
Daga nan kowa yayi shiru cike da damuwa yayinda suke ta yi ma Ameera addu’a.
Zayd dai kasa zama yayi.. komawa yayi can bakin qofar emergency din yana ta zarya..
Tuni ya kira iyayen shi ya sanar da su abinda ya faru.. aikuwa sossai hankalin su ya tashi, sunyi akan gobe da sassafe zasu iso amma fa dukda haka duk bayan lokaci sai sun kira sun ji halin da ake ciki..
Lokacin da aka kira sallan magrib ne mazan suka wuce masallacin asibitin gaba dayan su yayinda su Umma suka jira su dawo kafin su je suyi suma…
☆☆☆☆☆☆☆☆☆
Wasa wasa dai har qarfe takwas na dare likitoci suna ER tare da Ameera. Abinda ya fi tayar musu da hankali shine nobody is saying anything.. babu likita ko daya da ya fito daga dakin. Zayd yayi yunqurin shiga ER din countless times amma Abba yana dakatar da shi.. Gaba daya ji yake yi kamar ya mutu..
Ga Ameerar shi rai a hannun Allah sannan gashi a last wurin da yake so ya bude idanuwa ya gan shi- ASIBITI
Wuraren qarfe takwas da rabi ne aka bude qofar ER din.. wasu likitoci guda biyu suka fito..
Zayd wanda yake tsaye daf da qofar ne ya tare su yana fadin “what took you so long?? how is she? what happened to her??”
Su Abba ma tuni sun taso sun zagaye likitocin suna jiran jin bayani.
“Please calm down Sir.. she actually hit her head hard.. we’ve stopped the bleeding from the head injury and we got it stitched.. Right now she is unconscious and will be that way for a while so please be patient.. And yes, she fell hard on her wrist which resulted to a dislocation but we have done a reduction procedure and hopefully, it will heal within a short time..” Dr George yayi musu bayani.
STORY CONTINUES BELOW
Gaba dayan su dai jikin su ne yayi sanyi.. Ita dai Umma wadda bata gane abinda likitan ya fada ba sai Zarah ce tayi mata bayani. Zayd kuwa shafa kanshi yake yi yayinda yake qoqarin comprehending maganar likitan..
shin wane irin faduwa ne da ya zo da tsautsayi m
ai qarfi haka?? he still thinks there is more to the story da Abba ya bashi toh amma ta ya za’a gano ainihin abinda ya faru??
“is it too soon to ask about her memory status??” Abba ya tambayi likitan
“Our neurologists ran some tests on her and we are more than 98% sure that there wont be memory loss…”2
Shi dai Zayd tunanin shi yayi nisa a wannan lokacin.. he is already thinking of moving Ameera out of the country don ta samu ganin qwararrun likitoci.. haka kawai ba zai iya risking zaman jiran lokacin da zata tashi ba.. what if she doesnt wake up??1
“Hey doctor, can she be moved out of the country?? I uhm, I honestly dont think I can sit back and wait for her to regain consciousness for only God knows when..”
“Presently Sir, I think it’s not a good idea because moving of the head can result to further problems and we wouldn’t want that.. Please be patient Sir, We have the best team attending to her and I assure you she will regain consciousness the soonest.. it only depends on how fast her body system reacts to the medication she is receiving right now”
Ajiyar zuciya Zayd ya sauke tare da girgiza kai yace “Okay then can we see her??”
Tun kafin likitan yayi magana yace “…I wont take no for an answer..”
Dr. George dai tunda ya ga Zayd ya gane shi don kuwa shi din ma’aboci bin labaru ne don haka ya san shi ya san mahaifin shi ya kuma san kamfanin shi wanda yake one of the best a qasar nan baki daya..
Ya sani cewar ko zasu kwana suna dragging in the end dole ya haqura ya bari su gan ta.
“Okay, I will let you see her but not now.. presently, the nurses are preparing to take her to her ward”
“You make sure you take her to the very best you have..”
“as you say Sir”
Su Abba suka yi ma likitan godiya yayinda suka yi tsaye suna jira a fito da ita.
☆☆☆☆☆☆☆☆
Wuraren qarfe goma na dare Ameera tana kwance a kan gadon dakin da aka kwantar da ita.. Wannan daki dai yana daya daga cikin special dakunan asibitin.. Daki ne babba wanda yake dauke da well furnished waiting room da kewaye mai kyau.. it’s a VIP ward!
Likita dai ya basu damar shiga su ganta amma kuma one person at a time.. Zayd dai daurewa yayi ya bar Umma da Abba suka shiga before him amma fa yana nan tsaye daf da qofar throughout.
Umma da ta fara shiga ta fito sai gani suka yi tana ta zubar da hawaye.. Zarah ce ta riqe ta yayinda take ta lallashin ta.. Hakan kuwa sossai ya qara tayar ma Zayd da hankali. Shi kanshi Abba da ya shiga ya fito jikin shi duk a sanyaye.. tunda suka haifi Ameera bata taba shiga hali irin wannan ba..
************
Jingine da qofa ya tsaya yayinda ya qura mata idanuwa cike da tsananin tashin hankali..
Ameera wadda take kwance kanta nade da bandage yayinda aka nade hannunta mai targade shima da cotton bandage.. Cannular ce maqale a dayan hannun ta.. Na’urar EKG a gefe tana monitoring heartbeat dinta.
Zuciyarshi ce take zafi ganin Ameera kwance cikin wannan yanayin..
He cant do anything to save her.. can he??
Runtse idanuwa yayi sannan ya bude… babu abinda yake fadi sai “hasbunallahu wani’mal wakeel”
Ajiyar zuciya ya saki sannan ya taka zuwa gadonta ya zauna a kan kujerar da take gefen gadon ya qura mata idanuwa..
STORY CONTINUES BELOW
A hankali ya dago hannun shi zai taba ta sai kuma na ga yayi saurin fasawa..
“Ya salaam, I cant even do this.. atleast not until she becomes my wife right??”
Gani nayi ya shafa fuskarshi da hannuwan shi biyu sannan ya sa mata idanuwa.
“Habibty don Allah kar ki dade kwance a kan gadon nan..”
Rage murya yayi yace “please do it for me.. ban taba fadi miki ba- I hate the sight of hospitals and everything that has to do with it.. ban san meyasa ba but I feel suffocated duk lokacin da na shigo asibiti. please fight and regain consciousness soon so we wont have to stay long”
Shiru ya dan yi sannan yace “and hey, Akwai abubuwa dayawa da nake so in fadi miki kuma ina fatan hakan bazai canza the way you feel about me ba..”
Daga nan kuma sai yayi shiru yayinda ya qura mata idanuwa yana wasu tunani.. har kusan tsawon minti biyar…
Murmushi na ga yayi sannan yace “I just remember the other day da nake kwance a kan gadon asibiti- ranar da kika yi confessing soyayyar ki zuwa gareni.. a tunaninki ban ji komai ba but I am sorry I heard everything and kin san me? instantly na san cewar na samu matar aure, irin matar da nake nema kuma wadda ta dace da ni. You were so wrong to think it’s always about physical appearance, No it’s not.. its definately about the innermost beauty. Ke kyakyawa ce ciki da waje and I cant wait to have you a matsayin mata ta, uwar ‘ya’ya na… Ya salaam, I will be beyond happy. I LOVE YOU TOO Habibty, ina bala’in sonki saboda ke ce mace ta farko da take sona tsakani da Allah a matsayin da kika san ni- TALAKA…” 3
Murmushi yayi yace “initially I was mad at myself for doing stupid things just to find true love a wurin Layla but luckily for me it wasnt in vain tunda na same ki.. I promise to give you everything you want… ZAYD IS ALL YOURS HABIBTY”
Wayar shi ce tayi ringing yayinda na ga ya duba.. Bilal ne don haka yayi saurin answering..
Ji nayi yace “okay Bilal, I’m coming”
Tashi tsaye yayi yace “Habibty ina zuwa..” Ya juya ya fita..
Da ya fito ne Zarah ta miqe zata shiga har tana fadin “Yayana ai nayi zaton bazaka fito ba..”
Girgiza kai kawai yayi yana murmushi sannan yace “Zan ga Bilal in dawo..”
☆☆☆☆☆☆☆☆
Tun wuraren qarfe Goma sha daya ne Zayd ya sallami Zarah wadda ta so ta kwana amma ya hana.. dayake driver dinta ya kawo ta shine ya mayar da ita.
Bilal ne ya mayar da Abba da Ibrahim gida… Ibrahim shima ya so ya kwana amma Zayd yace mishi ya tafi shi zai zauna tare da Umma.. Dukda baya son asibiti gwara ya zauna don kuwa ya sani cewar ko ya je gida hankalin shi bazai taba kwanciya ba..
Dayake Bilal ya kawo duk wani abinda zasu buqata har abinci, everything was in order!
Umma da Zayd dai zama suka yi a waiting room na dakin da aka kwantar da Ameera suna ta hira.. idan ka gan su zaka rantse uwa ce tare da danta suke hira.. Sossai suka saki jiki da juna don kuwa kamar ma sun manta cewar sirikan juna ne..
Motsi kadan fa amma Zayd yana tashi ya shiga dakin Ameera ya duba ta sannan yayi mata addu’a ya dawo.. Haka duk bayan lokaci Umma tana ji iyayen shi da ‘yan uwan shi suna kiran shi a waya suna tambayan shi jikin Ameera.. Umma dai ta ji dadin hakan domin kuwa ta tabbatar ba shi kadai ba hatta ‘yan uwan shi suna son Ameera, atleast burinta shine ‘yarta ta samu namiji wanda zai so ta tsakani da Allah sannan ya daraja ta kuma da alama ta samu..
Zayd ya sanar da ita su Ammi zasu zo duba Jikin Ameera washegari.. Umma dai tayi mamakin jin hatta mahaifin shi ma zai baro abubuwan da yake yi ya zo duba Ameera.. Lallai Ameera zata fada hannun arziki.
Dayake an shirya ma Umma gado a cikin dakin Ameera can ta kwanta yayinda Zayd ya dauro alwala ya duqufa salolin dare as usual tare da yi ma Ameerar shi addu’an samun sauqi.
GARKUWA HOSPITAL
SULTAN ROAD+
Wuraren qarfe Goma na safe ne su Abba suka iso. A wannan lokacin Zayd ya koma gida. Bilal ne ya je har gida ya dauko su.. Mama da Layla basu so zuwa ba amma Abba ya tilasta musu lallai su shirya.. a haka suka dinga turo baki suka shirya suka bi su. dayake motar da Bilal din ya dauko su da ita Range Rover ce dukkanin su sun samu wuri harda su Aliyu. Layla dai jikinta duk a sanyaye.. har suka iso kuwa bata bari sun hada ido da Bilal ba don kuwa bala’
in kunyan shi take ji.
Ko da Mama da Layla suka ga jikin Ameera sossai suka yi farin ciki don kuwa sun tabbatar lafiya ba yanzu ba.. it means they have time to work their plan..
A lokacin da suka fito daga dakin Ameera kasa zama a waiting room din suka yi Musamman Layla wadda take gani kamar kowa ya san ita ta tura Ameeran ta fadi don haka ne suka bada excuse na cewar zasu fita su sha iska.. Haka suka fita ba tare da sun gaisa da Umma ba balle suyi mata ‘ya mai jiki’
Basuyi minti biyar da fita bane Su Ammi suka iso.. Bilal shine yayi organizing drivers din da suka dauko su daga airport.. dayake a cikin private Jet din Abbu suka zo securities dinshi guda biyu kawai ya dauko.
Tunda suka shigo asibitin kuwa aka tabbatar lallai wani babba a qasa ya shigo.. Yawanci wasu sun san His excellency A.M Fadoul, wasu kuma labarin shi suke ji… gaba daya dai asibitin hirar familyn ake yi.. Nurses kuwa har so suke aiki ya kai su ward din Ameera don dai kawai su ga beautiful family din.
Dukkanin su sai da suka shiga suka ga Ameera sannan suka dawo waiting room.. in no time sirikan sukayi getting along da juna yayinda suka shiga hira kamar wadanda suka dade da sanin juna..
Maheera da Meher dai maqalewa suka yi a wurin Umma sai tambayoyi suke ta yi mata akan Ameera ita kuma tana ta basu amsa yayinda Ammi take ta qoqarin hana su ganin cewar hankalin Umman ba a kwance yake ba yana kan rashin lafiyar ‘yarta amma Umma tace mata ta qyale su.. ita kam she is glad Ameerar ta zata samu kulawa a wurin dangin mijin nata.
Zaheera dai tana zaune a kusa da Ammi tana ta jiran isowar Zayd.. tunda suka iso ta kira shi a waya yace mata yanzu ya shigo yana wurin likita and he is almost done. Ita dama haka take, as soon as ta zo wuri very close to twin brother din nata bata taba kwantar da hankalinta sai ta gan shi, a bangaren shi ma haka ne.. Tun suna yara haka suke.
Makaranta ita ta fara raba su.. a wannan lokacin kuwa ji suka yi kamar zasu mutu. Sun dade sannan suka saba da rashin juna a kusa at all times. Daga baya kuma Zaheera tayi aure wanda hakan ya qara nisantar dasu daga juna.. they had no choice but to get use to the situation amma fa kullum sai sun yi video call.. Duk ranar da basu yi ba kuwa basu samun kwanciyar hankali.. They are so much connected da har suna sensing idan dayan su yana cikin damuwa.
Abba kuwa yana zaune a gefe tare da Abbu tare da su Ibrahim suma suna hira… Yawanci Abbu ne yake ta yi ma yaran tambayoyi suna amsawa.
☆☆☆☆☆☆☆☆
Zaune suke a wasu kujeru a dogon corridor na wani bangare na asibitin suna hira..
“Ke gaskiya na amince wannan yaron kudi gareshi sossai.. wannan irin babbar mota da aka dauko mu cikin ta ai ban taba ganin irin ta ba..” Mama ta fadi.
STORY CONTINUES BELOW
“Hmm.. Mama ai baki ga komai ba. Kin ga kamfanin shi?? guda uku fa yake da su a cikin qasar nan.. ai wallahi na tabbatar Abba ya san da haka shine aka yi mun munafinci” cewar Layla.
“Kar ki damu Layla.. ai fa komai zai zo musu qarshe. Zayd dai ke zai aura don kuwa a yadda na ga wannan baqar banzar a kwance na tabbatar ta fi kusanci da gawa akan mai rai”
Layla ta fashe da dariya tace “Wallahi Mama sossai na ji dadin ganinta a haka.. na tabbatar ko bata mutu ba zata yi kusan sati biyu ma bata farfado ba.. gwara da na turata ta fadi”1
Mama ta kalle ta da sauri tace “au, ashe dama ke kika tura ta shine na tambaye ki jiya kika ce mun baki san me ya faru ba???”
Layla ta turo baki tace “na dan tsorata ne da farko Mama.. amma daga baya na gane everything happened to my advantage.. wallahi haushi ta bani lokacin da na ganta ta fito daga dakin Umma zata je kicin din sai kawai na bi ta”
Mama tana murmushi tace “kinyi daidai Layla ta.. zan ga yadda za’ayi auren kuwa”3
Muryar shi ta jiyo a gefen su wanda ya sanya ta zabura ta miqe tsaye..
Zayd ne yake magana da wani a waya yayinda ya wuce su ba tare da ya ko kalle su ba..2
Mama wadda ta ga yadda Layla ta zabura tana kallon kyakyawan saurayin da ya gifta su ce na ji tace “ya haka? waye wannan da na ga kamar kin zabura da ganin shi? kin san shi ne??”
“Zayd???” Layla ta fada cikin tambaya yayinda ta dafe kanta.
“Na shiga uku Mama Zayd ne.. Allah yasa bai ji mu ba”1
“Wai tsaya, wannan kyakyawan balaraben shine Zayd din?? shine ko a lokacin da ya zo miki a talaka baki riqe shi ba?? haba Layla.. wannan ai ko albarakacin kyau bazaki yi saurin korar shi ba” Mama ta fada yayinda ta bi bayan shi da kallo har ya bace musu.
Wani irin kallo Layla tayi ma Mama tace “haka ma zaki ce yanzu?? ba ke kika ce idan ba mai kudi ba kar in saurari kowa??”
“eh toh haka ne.. amma dai gaskiya ya cuce mu da ya boye asalin shi.. kai gaskiya da sake, dole ne mu raba yarinyar nan da shi don kuwa wallahi kalar ki ne.. qwarya ai dole ta bi qwarya”
“Ni duk ba wannan ba ma Mama.. kin tabbata bai ji abinda muke fadi ba??” Layla ta tambayeta cike da fargaba
“bana jin haka Layla.. a yadda ya wuce ma bana tunanin ya gan mu”
“ko zamu bi bayan shi ne??”
“toh tashi mu je.. ai yakamata ma mu gaisa ya san ni da kyau”2
Daga nan suka miqe suka bi bayan Zayd zuwa ward din Ameera.
☆☆☆☆☆☆☆☆
Tsaye suke rungume da juna yayinda suke ma juna magana a hankali..
Zayd dai tunda ya shigo dakin Zaheera ta ruga a guje ta rungume shi cike da murnar ganin shi.. kamar kullum tambayar juna suke yadda suke wanda idan suna yi babu mai jin su.. Wani lokaci ma kamar da zuci suke magana don kuwa duk yadda ka so ka saurari abinda suke fadi baka ji..
da na kanga kunnuwa na daf da su ne na ji yana tambayan ta “where is Ridwan, Riyaz and baby eesh?”
“Suna gida tare da Labiba.. na ga tunda asibiti zamu zo bai kamata mu zo da yara ba”
“oh yes, true”
Gaba dayan su da suke waiting room din kallon su suke yi.
Abba ne yace “lallai akwai shaquwa a nan”
Abbu yana murmushi yace “sossai.. a yadda suka taso ban taba tunanin zasu iya rabuwa na tsawon lokaci ba tare da an samu matsala babba ba”
Umma ce tace “ai dama haka ‘yan biyu suke.. suna matuqar son junan su”
STORY CONTINUES BELOW
Meher wadda take tsaye tare da ‘yar uwarta a kusa da su ce tace “hasanan Ya Ukhti..” (ya isa haka nan yaya [Zaheera])
Zayd wanda yake facing dinsu ne yayi musu gwalo yayinda suka bata rai..
Maheera tace “Meher just leave them alone.. zo mu koma”
Sun juya kenan suka jiyo muryarshi..
“sorry princesses..”
Da sauri suka juyo suka ga ya ware hanayenshi yana kallon su.
Aikuwa a guje suka qaraso suka yi hugging dinshi.
“how are you??” ya tambaye su
A tare suka ce “we miss you Akhiyy”
Murmushi yayi yace “me too my princesses.. kun ga Habibty??”
“eh mun gan ta kuma munyi mata addu’a.. Umma tana ta bamu labarin ta” Maheera ta fada.
Breaking hug din yayi yayinda yace “I am glad.. let me greet our parents”
Qarasowa yayi ya tsugunna a kusa da Abbu da Abba ya miqa musu hannu suka yi musabaha.. Su Ibrahim ma suka gaishe shi ya amsa.
“kun iso lafiya??” ya tambayi Abbu
“Lafiya lau Zayd.. ya mai jikin??”
“Alhamdulillah Abbu.. Shukran liqudumik” (nagode sossai da zuwan ku)
“dont worry Son..”
Murmushi yayi ya koma wurin Ammin shi ya zauna tare da bata side hug yace “Cutie how are you??”
Ammi wadda ta riqe hannun shi t
ace “lafiya lau my baby.. how are you holding up??”
“Fine Ammi.. likitoci sun ce akwai progress sossai.. hoping she regains consciousness and we leave this place the soonest”
“Insha Allah she will.. na san ka da yadda baka qaunar asibiti”
Umma tana murmushi tace “aikuwa kam.. jiya da yake bani labarin yadda yake boyewa idan yana ciwo saboda rashin qaunar zuwa asibiti nayi mamaki”
Murmushi yayi yace “Umma bazaki gane bane..”
“kai dai ba wani nan.. kawai dai matsoraci ne” Umma ta fada yayinda suka dinga yi mishi dariya.
Miqewa yayi yana dariya yace “bari in duba Habibty..”
“zaka gudu dai” cewar Ammi yayinda suka cigaba da yi mishi dariya.
Zayd yana shiga dakin Ameera ne suka qwanqwaso qofa suka shigo.. Mama ce tare da Layla.. Gaba daya dakin suka juyo suna kallon su.
Layla da Mama dai ganin yanayin mutanen da suke cikin dakin da yadda suka sanya musu ido duk sai suka rude.. ba sai an fadi musu ba sun gane cewar dangin Zayd ne.. dama tun a qofar shiga sun ga securities tsaye..
“Sannun ku ina kwana” Mama ta fada yayinda ta qarasa shiga. Ita kuwa Layla tsayawa tayi bakin qofar tana ta qare ma su Zaheera da Ammi kallo. Dukkanin su suna sanye cikin jallabiyoyi masu kyau da tsada yayinda suka nade kawunan su da gyalen jallabiyoyin nasu.. sun fito sak a larabawan su.
Zaheera dai tana ganin Layla ta gane ta don kuwa har hotonta Zayd ya taba nuna mata.. tunda ta kalle ta sau daya kuwa bata qara kallon ta ba don kuwa ta mugun tsanarta..
“Lafiya lau” Ammi ta amsa yayinda Abba yayi gyaran murya yace “wannan ita ma mai dakina ce.. abokiyar zaman Umman Ameera”
Ya kalli Layla wadda take tsaye bakin qofa cikin fada yace “Ke baki iya gaisuwa bane??”
A rude tace “uhm.. ina wunin ku. Wai, ina kwana”
Maheera da Meher ne suka fashe da dariya yayinda Zaheera tayi tsaki wanda Ammi ce kawai ta ji.
STORY CONTINUES BELOW
Ammi ta kalli su Maheera tace “what’s funny??”
Meher tace “mun ga kamar ta rude ne Ammi.. she said..”
“it was only a slip of tongue.. dont do this again” Ammi tayi addressing yaran.
Layla dai ji tayi kamar ta koma don kuwa sossai yaran suka wulaqanta ta.. wuri ta samu kusa da Mama ta zauna tana ta qare musu kallo.. da ganin yanayin su ka ga asalin abinda ake kira HUTU..
Su Ibrahim ne suka miqe suka fita daga dakin yayinda Abba da Abbu suka cigaba da hirar su.. yawanci hirar qasar mu Nigeria.
Ammi ma tana ta hira da Umma yayinda suka bar Mama shiru tana kallon su.. duk yadda ta so ta tsoma bakin ta cikin hirar ta kasa.. da alama dai bad energy din su ita da ‘yarta is all over.1
☆☆☆☆☆☆☆
Zayd ne ya fito daga dakin Ameera yayinda yake latse-latsen wayarshi..
Daga Mama har Layla qura mishi idanuwa suka yi kamar mayu..
Ita dai Layla soyayyar shi ce take tsuma a cikin zuciyarta yayinda Mama take mamakin asarar da ‘yarta tayi wanda ta qudurta lallai sai ta gyara musu harka..
Bayan ya kammala ne ya dago kai ya kalli Zaheera wadda tace “Sweetheart, ta’al wajlis ma’iyy” (Zo ka zauna tare da ni)
Murmushi yayi ya nufi wurin ta ya zauna yayinda suka riqe hannun juna suna magana.. maganar da hatta Ammi da take kusa da su bata ji.
Layla dai sai kallon su take yi.. ta kula Zaheera sai danna mata harara take yi a duk lokacin da suka hada ido.. ta tabbatar lallai ta San labarin ta ne.. Gaba daya duk ta bi ta tsargu.
Gaba dayan su babu wanda ya kula cewar Zayd bai gaida Mama ba domin kuwa duk sunyi nisa a hirar su.. Mama dai ganin tabbas Zayd baya da niyyar gaishe ta ne tace “sirikin nawa babu gaisuwa ne??”
Zayd wanda ya ji ta sai yayi kamar bai ji ba har sai da Ammi tace “Babyna baka ji ana yi maka magana ba??”
A lokacin ne hankulan kowa ya dawo wurin su yayinda ya dan bata rai yace “ban ji ba.. waye ke magana??”
“Ni ce.. Maman Layla, nace bamu gaisa ba. Ya mai jikin?”
“Alhamdulillah.. Likitoci sun bamu tabbacin Insha Allah zata farfado very soon kuma muna nan muna yi mata addu’a akan Allah ya kare ta daga sharrin mahassada”2
A yadda ya fadi maganar da yadda Zaheera take ta hararar ta ne Ammi tayi sensing wani abu.. something is wrong! there is something the twins are not telling her and she needs to find out.
Suna nan Zarah da Mustapha suka shigo. A yau da safe ne ya dawo don haka ta tsaya ta jira shi suka zo tare..
Har qasa suka tsugunna suka gaida su Abbu tare da tambayar mai jiki yayinda su Maheera suka gaishe su.
Zayd ya tashi ya nufi wurin abokin nashi suka gaisa tare da rungume juna briefly sannan suka fita suna magana.
Ita kuwa Zarah kusa da Zaheera ta koma ta zauna yayinda suke magana.. Da gani dai zaka tabbatar sun San juna sossai.
Layla dai mamaki ne ya cika ta.. wato kenan Zayd abokin mijin Zarah ne sannan ita ma Zarah ta San familyn su Zayd very much?? lallai an bar ta a baya!!
☆☆☆☆☆☆☆
AHMAD MUHAMMAD FADOUL’S RESIDENCE
UNGUWAN RIMI GRA
Zaune suke a danqareren falon gidan yayinda suke hira. Basu dade da shigowa ba.. idan ka ga gidan zaka rantse dama akwai mutane a ciki don kuwa it’s spotlessly clean.. Masu aikin gidan dai dukda babu kowa a kullum sai sun gyara ko ina.
Tare da Zayd suka dawo wanda ya biyo su ne don yana so ya tattauna wata Very important magana da iyayen shi…
wacce magana ce??
Kamar kullum sai da suka yi sallar Magrib cikin jam’i sannan suka nufi Dinning suka ci abinci wanda chefs ne suka dafa.. Ammi dai haka nan ta ci ba wai don yayi mata dadi ba.. ita dama abinci idan ba ita tayi ba ko kuma Zayd yayi bata wani jin dadin shi… ba ita daya ba kuwa dukkan su haka abin yake a wurin su!
Bayan sun gama ne suka dawo falo suka shiga hira wadda yawanci duk ta su Ameera ce.
Ammi wadda take zaune a kan kujera 2 seater ce ta kalli Zayd tace “ni kuwa Babyna sai na ga kamar baka kyauta ba yadda kayi ma Maman Layla magana a asibiti.. na san ka da fara’a da mutane amma na ga kamar her case was different.. ko akwai abinda tayi maka ne?”
Zayd ya kalli Zaheera wadda itama shi take kallo..
Zaheera tace “dama bai baku labarin abinda ya faru ba?? toh bari ni in fadi muku”
Zayd ya girgiza kai yace “sweetheart please…”
Ta Harare shi tare da fadin “what?? wallahi sai na fada.. gwara ma su san wahalar da wawiyar yarinyar nan Layla ta baka..”
aikuwa daga nan Zaheera ta basu labarin abubuwan da suka faru tsakanin Layla da Zayd har lokacin da ya dawo ma Ameera…
Ba Ammi ba kawai hatta Abbu yayi mamaki..
“Yanzu abinda kayi going through kenan bamu da labari??? dan nawa da nake masifar ji da shi aka wulaqanta mun bani da masaniya?? kai kuma you had to endure so much for the foolish girl?” Ammi ta fada ranta a bace
“Kiyi haquri Ammi.. I didnt know what to do ne. I fell madly in love with her shiyasa amma komai ya wuce ai.”
“well, it’s a good thing komai bai tashi a banza ba tunda ka samu Ameera” Abbu ya fada
Maheera ce tace “mu kam mun fi son Habibty dinka.. tunda tana sonka mu ma muna sonta sossai”
Zayd yayi murmushi yace “thanks princess”
Ammi Wadda ranta yake a bace har a wannan lokacin ne tace “wani ikon Allah fa tunda na gan su basu kwanta mun a rai ba.. aikuwa daga uwar har ‘yar sunyi kyan dan maciji..”
Meher ce tace “what does that mean Ammi??”
Zaheera tace “it’s for you to find out” tare da yi mata gwalo… Maheera ce ta kalli Meher tace “kar ki damu.. we will resort to Google! we have to find out somehow”
Yaran dai haka suke yi.. da zarar sun ji sabon abu a Hausa ko larabci hankalin su baya kwanciya sai sun gano ma’anar shi.. da alama they are set on a mission to finding this out!
Ni kuwa nace ‘Allah ya bada sa’a ‘yan biyu’
Zayd ne yayi gyaran murya yace “Abbu ina da request and please dont say no”
“Go ahead son”
“Ina so gobe bayan sallar Juma’a a daura mun aure da Ameera..”9
Gaba dayan su suka ce “what???GARKUWA HOSPITAL
SULTAN ROAD
Zaune yake a kan gadon da take kwance yayinda yake kallon fuskarta.. kusan minti goma sha biyar kenan da ya shigo dakin ya sa mata idanuwa.+
A yau bayan sallan juma’a aka daura auren Zayd Ahmad Fadoul da Ameera Farouq a masallacin Sultan Bello na unguwar Sarki akan sadaki naira dubu dari.4
Zayd dai da qyar yayi nasarar shawo kan mahaifin shi ya amince aka daura mishi aure da Ameera a yau din.. Da farko Abbu ya qi saboda a cewar shi an riga an gayyaci mutane akan next week bai kamata a dawo da date din baya ba sannan ya za’ayi a daura mishi aure da matar da batada lafiya bata ma san inda kanta yake ba amma Zayd yayi insisting akan ayi kawai in yaso sai a ba mutane haquri afterall idan sun sa ma auren albarka sun gama mishi komai.
Akan rashin Lafiyar Ameera kuwa babu shiri ya basu labarin abinda ya ji Mama da Layla suna fadi a asibiti, the major reason why he wants to marry her sooner ya ga tsiya..2
(tabbas ya ji dukkanin abinda suka fadi)2
Su Abbu dai sunyi mamakin Mama da Layla sossai sannan sun yi tir da halin su.. sossai suka qara tsanan su musamman Ammi da Zaheera..
Ko da Ammi tayi maganar kayan lefe sai cewa yayi a kai gidan shi kawai idan ta je gidan zata ga kayanta.. dama dai tun farko baya son idea na a kai before the wedding don kuwa it will blow his cover..
Da wannan ne Abbu ya zauna da Abba ya roqe shi wanda da farko shima bai amince ba, same reasons as pointed out earlier by su Abbu din shima su ya gabatar amma Abbu ya fahimtar da shi kar ya damu.. Aure dama idan lokacin shi yayi babu mai tsayarwa. Dama dai Allah ya tsara cewar lokacin auren kenan.. fatan su shine Allah ya sanya albarka ya kuma ba Ameera lafiya.1
Hannun ta mai dauke da Cannula ya riqe a ahankali yace “Habibty Finally you are mine.. insha Allah babu wanda ya isa ya raba mu sai mutuwa.. itama bana fata ta dauke ki kafin ni”
Ahankali ya saki hannun ta ya shafa gefen fuskarta sannan yace “na sani cewar idan kika farka kika ji komai zaki ji haushi.. look, I know you deserve to know the truth about me even before now amma wallahi tsoro nake kar ki ce kin fasa aurena.. I promise you duk abinda kike so, duk yadda kike so inyi zanyi…”
Duqowa yayi saitin kumatunta ya sakar mata wani soft peck..
Instantly kuwa Ameera ta motsa yayinda ta bude idanuwan ta wadanda suka yi jajawur..
“Ya Salam.. Habibty you are awake??? Alhamdulillah..” ya fada cike da murna yayinda yayi saurin ja baya yana kallonta.
Ameera dai qoqarin daga hannunta tayi mai targaden amma ta ji yayi mata wani iri sannan ga dayan hannun dauke da cannular..
Mayar da idanuwan ta tayi ta rufe a dalilin kanta da yake yi mata ciwo..
Zayd dai ganin ta mayar da idanuwa ta rufe ne ya kai hannun shi kan kumatunta yace “Habibty please dont.. don Allah ki bude idanuwan ki.. ina ke yi miki ciwo??”
Bude idanuwanta ta qara yi ta qura mishi su tana qoqarin gane waye shi.. Ga shi dai yayi kama da Zayd dinta amma kuma ba shi bane.. meyasa yake taba ta bayan hakan bai dace ba.. toh ko dai sato ta aka yi?? ina su Umman ta??
Da sauri na ga ta fara juye-juye tana qoqarin gane inda take.. kanta ne ya cigaba da azabar ciwo yayinda ta fashe da kuka..
“wayyo Allah kaina…”
STORY CONTINUES BELOW
Zayd wanda ya rude ne ya sauka daga kan gadon yana fadin “Subhanalillah.. Habibty sorry bari in kira doctors su..”
Kafin ya qarasa magana likitoci suka shigo da sauri.. (dayake dai na’urar su ta sanar da su Ameera ta farfado shiyasa suka iso)
Su Umma ne suka biyo bayan likitocin yayinda suke tambayar abinda yake faruwa..
Ganin Ameera suka yi tana ta kuka dafe da kanta tana fadin “wayyo kaina”
Shi kuwa Zayd yana riqe da ita yana qoqarin calming dinta down yayinda yake fadin “doctors please do something.. she is in pain”
Su Umma dai tsaye sukayi cirko-cirko a rude suna ta fadin ‘sannu Ameera’
Dr George ne ya kalli Zayd yace “please sir can you step outside while we..”
“wait what??? why should I step outside when my wife is in pain?? is my presence really affecting your job here?? please just do your…”
“Babyna zo mu fita mu basu wuri suyi aikin su..” Ammi ta fada yayinda ta janyo hannun shi tana yi mishi bayani.
Ita dai ta sani sarai idan ba janyo shi tayi ba bazai fita ba tunda dai shi ba ma’aboci zuwa asibiti bane balle ya san tsarin su.
☆☆☆☆☆☆☆
Waiting room na dakin Ameera cike yake da ‘yan uwa da abokan arziki.. don ma anyi sa’a wasu suna zuwa suna tafiya.. (the likes of qawayen Umma da makwabtan su)
Aunties din su Ameera (qannen Abba) sun iso tun da rana.. Dama dai ana biki saura kwana uku suka yi niyyan zuwa amma a dalilin kwanciya asibiti da Ameera tayi ne suka kamo hanya a yau.. Da suka iso kuma suka ji har an daura auren ma.
Haka ‘yan uwan Ammi ma sun zo daga Adamawa..
Abubakar Sadiq mijin Zaheera ma ya zo tare da yaran su.. tare da shi aka daura auren Zayd.
Abbu kuwa ana gama daurin aure ya wuce Abuja don shirin tafiya qasar Russia.. tafiyar da ta taso mishi cikin gaggawa.
Gaba dayan su sun yi cirko-cirko suna jira..
Zayd dai yana nan tsaye jikin bangon dakin Ameera daf da qofa yayinda yake ta shafa kanshi yana bubbuga qafan shi cikin tsananin damuwa.. Abokin shi Mustapha ne a gefen shi yana ta qoqarin calming dinshi down.
Bayan kusan minti Goma sha biyar ne likitocin suka fito.. Gaba dayan su suka rufe shi da tambayoyi..
“please calm down, she is doing fine now.. the headache has subsided and it is no cause for concern. Another good news is Her memory is intact and her dislocated wrist has healed..”
“okay can we see her?”
“uhm right now she is requesting to see UMMA.. her mom I guess??”
Ammi ce tace “yes its her” yayinda Zayd ya runtse idanuwan shi.. Ya sani cewar akwai matsala daga irin kallon da Ameera tayi mishi.. a yadda ya kula ma kamar bata gane shi ba.. for the first time yayi regretting batar da kamarnin da yayi.
Ko da Umma ta shiga gani nayi Zayd ya juya ya fita daga waiting room din yayinda Mustapha ya bi shi.
Zaune yake a kan wata kujera dafe da kanshi yayinda yayi zurfi a tunani
“hey what’s wrong??” Mustapha wanda ya zauna a gefen shi ya tambaye shi.
“abokina a yau nayi regretting batar da Kamarnin da nayi.. she didnt recognize me at all, she looked at me like a stranger.. Yanzu ta ina zan fara?”
“calm down ZAF, duk wannan fa mai sauqi ne.. ka riga ka gama mai wuyan tunda har ta zama matar ka.. na tabbatar Umman ta zatayi updating dinta and trust me dukda zata ji haushi I am sure zata sauko.. Cheer up our latest ango, ka gode ma Allah amaryar taka ta farfado.. if I were you right now I’d start arranging for our honeymoon trips around the world”
STORY CONTINUES BELOW
Wannan maganar ce ta sa Zayd yin murmushi bai shirya ba yayinda yace “No my friend.. I will have to make sure we are good..”
☆☆☆☆☆☆
Umma ce zaune a kan gadon rungume da Ameera wadda take kuka.
Umma dai ta bata
labarin abubuwan da suka faru har zuwa yau din da aka daura mata aure da Zayd..
Tabbas burinta ya cika Zayd ya zama nata toh amma ita ba wannan Zayd din take so ba..
“Umma meyasa kuka daura mun aure da shi bayan kun sani cewar da lafiya na qalau bazan amince ba?? kin sani cewar bana son auren irin wadannan mutanen.. ta ya zan zauna tare da shi? rayuwar mu ba iri daya ba, mutumin da bazai samu lokaci na ba balle ya kula ni.. wallahi bazan iya ba..” ta fada tana ta kuka.
Umma wadda take lallashinta ce tace “kiyi haquri Ameera, Zayd bazai taba wulaqanta ki ba domin kuwa yana bala’in son ki.. ba fadi yayi ba, gani muka yi kuma a cikin kwanakin nan biyu duk wanda ya ga halin da ya shiga da abubuwan da yayi zai tabbatar yana son ki.. Gaba daya duk wata hidimar shi ya ajiye ta saboda ke.. meyasa zakiyi tunanin bazaki samu kulawa ba a wurin shi?? don Allah ki daina fadin haka.. addu’a zakiyi akan Allah yasa hakan shine zai fi zama miki alkhairi”
A haka dai ta dinga lallashin ta wanda da alama a banza Umma take yi don kuwa she didnt look like someone that is ready to accept the present situation..2
toh fa..
☆☆☆☆☆☆☆☆
GIDAN MALAM FAROUQ ABDALLAH
MALALI
Kwance take a dakinta tana ta browsing labarin Zayd kala-kala..
A Google ta gano labarin shi tas da achievements dinshi a rayuwa.. Kamfanin shi is the best in Africa presently kuma yana taka rawar gani a GDP na Nigeria.
Kusan duk wasu manyan gine-ginen da aka yi a qasar Dubai kamfanin Zayd yana cikin wadanda suka qera su.. dukkanin sabbin gine-ginen da aka yi a Palm Jumeirah, Deira Island da Palm Jebel Ali kamfanin Zayd is involved..
Mahaifin shi Ahmad Muhammad Fadoul yana da rijiyoyin mai sama da guda goma wanda ya gada daga wurin mahaifin shi a qasar Saudiya not to mention other properties..
fita tayi daga page din sannan ta shiga Instagram.. Gaba daya dai jikinta yayi sanyi.. wai yau Zayd din da take wulaqantawa shine ya mallaki dukiya haka.. shine Ameera zata aura nan da sati daya…
“aikuwa wallahi ko kashe ta zanyi sai na kashe ta don kuwa bazan…”
Bata qarasa magana bane na ga ta tashi zaune hankali a matuqar tashe yayinda ta dafe qirjinta wanda ya fara bugawa da qarfin gaske..
Hotuna ta gani a Instagram din wai an daura auren Zayd da Ameera a yau..3
Ihu ta sa yayinda ta saki wayarta ta sauka daga kan gadon.. a dalilin mugun sanyin da qafafuwan ta sukayi ma zubewa tayi a qasa tana ta rusa kuka…
Mama wadda ta jiyo ihunta ce ta shigo dakin da sauri ta ga ‘yarta a qasa tana ta birgima har ta fara fita hayyacin ta.
“Ke meye haka??? me ya faru??”
“na shiga uku na lalace Mama.. an daura auren Zayd da Ameera yau”
“ban gane an daura auren su ba.. ba sati mai zuwa bane??” Mama ta fada cike da mamaki.
“wallahi an daura auren su Mama.. mutuwa zanyi idan ban auri Zayd ba..”1
“Ke wai me kike fadi?? an daura aure a gidan nan shine ban sani ba?? me Abban ku yake nufi da ni da har za’ayi daurin aure bai sanar da ni ba?? toh wai tsaya ta ya za’a daura aure da yarinyar da ba’a tabbatar zata tashi ba???”1
“Mama don Allah ki taimake ni..” Layla tana kuka dafe da qirjinta yayinda jikinta ya dauko mugun zafi..
Mama wadda itama take a rude gani nayi tayi tagumi yayinda tayi nisa a tunani.
Da sauri ta miqe ta fita daga dakin ba tare da tace komai ba.. Bayan minti biyu ta dawo riqe da waya a kunne tana magana da Hajiya Suwaiba..
“eh wallahi.. toh yanzu ya kike gani za’ayi?? ni wallahi yanzu ma ko batar da yarinyar ayi don kuwa gwara ta mutu ma gaba daya mu huta..”
Shiru tayi tana sauraron bayanin Hajiya Suwaiba sannan tace “toh yanzu dai kina nufin sati mai zuwa idan kika dawo babu matsala ba’a yi latti ba?”
Murmushi tayi sannan tace “yauwa Hajiya suwaiba.. kar ki samu matsala idan dai kudi ne akwai su.. aiki mai kyau kawai muke so a yi mana, Allah ya dawo da ke lafiya. ita kuma zan ce mata ta kwantar da hankalinta.. nagode sossai”2
Bayan ta kashe wayar ne ta koma wurin Layla ta dago ta.. A yanzu har ta fara kyarman Zazzabi.
“share hawayen ki Layla ta.. Hajiya Suwaiba tace kar ki damu, ba aure ba ko a cikin cikin shi aka sanya mishi ita malaminta zai ciro ta.. Zayd dai baya da matar da ta wuce ki”
Cikin kuka Layla tace “dagaske za’a iya raba su dukda sunyi auren??? bana so in ji labari daban fa Mama”
“Kar ki damu.. yanzu hau gado ki kwanta. bari in dauko miki maganin zazzabi ki sha”
Haka Layla ta koma cikin bargo tana ta kuka..
Mama ta kawo mata magani ta sha sannan ta zauna a gefen ta.
“kenan ‘yan iskan yaran nan sun san da zancen daurin auren shine basu fadi mana ba.. ni dai na ga yau sunyi shirin zuwa masallaci da wuri kuma zuwa aka yi da mota aka tafi da su.. bari su dawo gidan nan sai na ci qaniyar su. haka kawai wannan ‘yar iskar matar duk ta asirice mun su sun daina gani na da mutunci.. Shi kan shi Abban naku idan ya dawo sai na ji dalilin shi na boye mun wannan zancen.. munafukan banza kawai.. wannan auren na dan lokaci ne, tabbas ko barin duniyar zata yi sai dai ta bari don kuwa babu wadda zata zauna da Zayd a matsayin Mata sai ke..” Mama tana ta fadin maganganu cike da masifa.
Wayar Layla ce tayi ringing ta duba.. Sunan Haleema ta gani..
ko da tayi answering tun kafin tayi magana Haleema tace “ke ashe an daura auren Ameera da ZAF?? dama yau ne bikin ba next week ba??”
Layla wadda ta fashe da sabon kuka kasa magana tayi..
Haleema wadda ta gane it’s a bad timing ce tace “Allah sarki qawata.. sorry. Zan kira ki another time when you are much better..” daga nan ta kashe wayar.
Layla dai jefar da wayar tayi ta cigaba da rusa kuka.. Tuni zazzabin da Mama take gudu ya rufe ta.. hankalin ta duk ya bi ya tashi ganin yadda Layla ta fita hayyacinta cikin qanqanin lokaci..2