ZABI NA CHAPTER 12 BY FADEELARH

ZABI NA CHAPTER 12 BY FADEELARH

Www.bankinhausanovels.com.ng 

ZAYD AHMAD FADOUL RESIDENCE

UNGUWAN RIMI GRA+

Zaune suke a falonta suna hira da qawarta Zarah..

Duka awa biyu kenan da Zayd ya tafi Lagos wanda jet dinshi na sauka ko fitowa bai yi ba ya kira ta a waya.

Yau din ita ce rana ta farko da suka samu zama bayan bikin ta.

“don Allah qawata kiyi haquri.. ni kam ba komai ya wuce ba yanzu??” Zarah ta fada cikin muryar roqo.

“eh komai ya wuce amma ai raina mun wayau kuka yi.. tell me something, since when have you known?” Ameera ta tambaye ta yayinda ta sa mata idanuwa.

Zarah tana murmushi tace “wallahi tun ranar da yayi proposing miki..”

“what??? you mean tun ranar Zarah?? and you didnt tell me?”

“Haba qawa ta.. da bakin ki fa kika fadi mun cewar bakya son auren mai arziki.. mun ji tsoro ne kar ki qi amincewa da shi..”

“aikuwa kun yi playing dina.. Ni kam I am glad na zama matar Ya Zayd kuma ya bani assurance din da nake nema… Kin ga dazu fa da zai tafi ya so mu je tare amma na qi..”

“what??? kenan kin gwammace ki zauna a nan shi kuma yana can??”

Shiru Ameera tayi yayinda take tunani.. ita kanta fa sai da ya tafi ta ji dama ta bi shi, Sossai tayi missing dinshi musamman da ta gan shi ta video call.

“Ke qawata, saurare ni ki ji.. a duk lokacin da zai yi tafiya ya nemi ku je tare please follow him.. ke close marking sossai yakamata ki dinga bashi.. duk wata kunya fa a yanzu ajiye ta zakiyi a gefe.. wannan soyayyar da kike yi mishi ita ce zaki zage ki nuna mishi.. yanzu da kika zauna a nan me kike yi? ke ba makaranta kike zuwa ba.. kina nan zaune a gida” ta harare ta sannan ta cigaba da fadin “ko dayake ba laifin ki bane.. baki shiga sahun matan aure bane tukun shiyasa.. da kin dandana wannan rayuwar wallahi na tabbatar maqale mishi zakiyi kamar chewing gum”2

Ameera wadda take kallon Zarah with a straight face ce tace “toh yanzu dai the damage has been done.. zan kiyaye gaba”

“yauwa qawa ta.. yanzu ma bata baci ba, Bari in kira miki wata mai gyaran jiki ta zo ta shirya ki kafin ya dawo jibin.. tunda dama ba’a kammala wancan ba kika samu accident din da har kika kwanta jinya.. ko baki so??”

“ina so qawa ta..” Ameera ta fada kai tsaye yayinda Zarah ta fashe da dariya tace “da kyau juliet.. na ga alama Yayana will be in trouble kenan”

Ameera tana dariya tace “ke toh son shi nake..”2

“na fi kowa sanin haka”

Aikuwa anan Zarah ta kira Aina’u Marwan.. wata shaharariyar mai gyaran jiki ce wadda tayi fice a garin Kaduna.. dayake harka ce ta kudi nan da nan ta nemi address sannan tace tana nan zuwa in the next 3 hours.

Bayan ta kashe wayar ne tayi ma Ameera bayani.

“nagode qawa ta” Ameera ta fada

“Meye abun godiya Ameera?? we are like sisters remember??”

Kafin Ameera tayi magana ne Zarah tace “ni kuwa ban tambaye ki ba.. ya labarin Layla??”

Ameera ta turo baki tace “toh wa ya sani.. jiya da muka je gida na ganta.. ko magana batayi mana ba ta wuce daki and daga nan bata qara fitowa ba.. I swear qawata tun ranar da tayi threatening zata kashe ni saboda Ya Zayd har yanzu tsoron ta nake ji.. tunda tana da saurayinta mai kudi ta haqura mana..”

STORY CONTINUES BELOW

Zarah tana dariya tace “tabbas saurayinta yana da arziki a inda babu masu arziki kenan.. ai sawun giwa ya taka na raqumi Ameera. Allah dai ya qara mata.. ba dai kwadayi da son abun duniya ta sa a gaba ba?? she never see anything..”

“Yauwa qawa ta.. don Allah zo mu je ki taimaka mun” Ameera ta fada yayinda ta janyo Zarah.

“with what???” Zarah ta tambaye ta yayinda take biye da ita.

“wallahi babu abinda na iya amfani da shi a kicin.. kin San qawar ki baqauya ce.. please come and help me explain some things don wallahi jiya da muka shiga tare da shi har ya gama hada mana desert ban fahimci komai ba a ciki..”

Zarah tana dariya tace “mu je in nuna miki qawata.. dukda ba wani barin ki zai dinga yi kina shiga kicin din ba don kuwa ya dade yana fadi cewar a fanin girki tabbas matar shi zata huta.. but amma ko don lokaci irin wannan idan yayi tafiya yakamata ki koya..”

“ai daga yau ma bazan qara barin shi ya tafi ya bar ni ba.. na dauki shawara qawata”2

Zarah ta fashe da dariya yayinda suka nufi kicin din inda ta shiga yi ma Ameera bayanin komai.

☆☆☆☆☆☆☆☆☆

Cikin qanqanin lokaci dai Ameera ta haddace komai na kicin din gidan nata.. dama dai kun san Ameera da qwalwa, kawai dai rashin sanin abubuwan ne. Hatta wasu ‘yan continental dishes Zarah ta koya mata.. wasu ta dan rubuta su yayinda Zarah tayi mata alqawarin kawo mata recipe book dinta.

Aina’u Marwan ma dai kamar yadda tayi musu alqawarin zuwa, ta zo din. Tuni ta fara aikinta a kan Ameera.. turarruka masu qamshin bala’i na wanka, na gashi da na shafawa a jiki. Nan da nan Ameera ta fara zabga qamshi.. Da zata tafi ne ta bata wasu sannan ta gwada mata yadda zata yi amfani da su.. sunyi Akan zata dawo washegari.

A bangaren Layla kuwa ko da ta shirya ta shafa kwalli kamar dai yadda aka umurceta kai tsaye City-shelters ta nufa amma bata samu ganin Zayd ba.. ko da suka ce mata yayi tafiya qaryata su tayi don kuwa bata ji labarin zasu yi tafiya shi da Ameera ba a gida tunda dai they are newly wedded and she is sure he wont travel without his wife.. tunaninta dai lallai sun boye mata ne.. Haka ta qarashi zaman jiran shi har ta gaji ta wuce gida da niyyan dawowa washegari.5

Sossai ranta ya baci, tana tafe tana zage-zage.

Ammi kuwa ta ji labarin Zayd yayi tafiya ya bar Ameera a gida wanda ta kira shi a waya ta dinga yi mishi fada.. haka ya dinga bata haquri tare da yi mata bayanin yadda ya dinga insisting su je tare amma ta qi.. da wannan dai ya fahimtar da ita sannan ta sassauta mishi.

Su Maheera kuwa motsi kadan sai sun kira Ameera ta video call.. Su kam Allah ya sani suna son Ameera!

Kamar dai yadda Zayd yayi ma Ameera alqawarin zai nemi alfarma a wurin Umma ta bar su Aliyu su je su zauna da ita kafin ya dawo, haka aka yi..

Sossai sukayi murna jin an ce zasu je gidan Ameera..

Su Ibrahim ma ko sallama basuyi ma Mama ba suka tafi, sun sani sarai idan suka fadi mata zasu je gidan Ameera tana iya hana su.. sun gwammace idan sun dawo tayi ta jibgan su.

Abinda basu sani ba shine duk wadannan abubuwan basu gaban Mama a halin da ake ciki.. tana can ta fara tsara irin facaka da zasu yi cikin naira ita da ‘yar ta idan Zayd ya zo hannun su.

Aikuwa da yamma driver ya je ya dauko su.

Da daddare Ameera ta dafa musu abinci mai dadi suka ci sannan suka zauna a falonta suka shiga kallon Indian film wanda suna kallo suna hira.

Aikuwa ko minti Goma sha biyar basu yi ba da fara kallon Zayd ya kira
ta a waya yayinda tayi excusing kanta.. tun su Ibrahim suna sa ran zata dawo har suka cire..

STORY CONTINUES BELOW

Ameerar ku dai tana can suna ta kwasan soyayya da Romeo din nata…2

☆☆☆☆☆☆☆

A yau ne Zayd zai dawo.. Tun da Ameera ta tashi daga bacci take cike da farin ciki marar misaltuwa.

Tun shekaran jiya da ya tafi har zuwa jiya da daddare sunyi waya ya fi a qirga.. Kai da safen nan ma wayar shi ce ta tashe ta daga bacci inda ya sanar da ita suna shirin barin Lagos.

Dukda gaba daya jiyan he was very busy with meetings tun safe har yamma, he still created time at intervals to call her..

Bayan sun gama breakfast da qannen nata ne ta wuce sashenta don yin wanka ta shirya tarban mijin nata.

Ko da ta shiga wanka tayi amfani da turarukan da Aina’u Marwan ta bata.. nan da nan kuwa qamshi ya dinga tashi..

Bayan ta fito ta zauna a gaban Vanity mirror nan ma mayyukan Aina’un dai ta shafa.

Dayake tun jiya ta tsefe kitson kanta ta wanke gashinta, a yanzu cikin man gashin da Aina’u ta bata ta shafa sannan ta taje shi ta daure da hair band.

Ji nayi tace “Dole ne in Kira Hannatu ta zo tayi mun kitso don kuwa shine rufin asiri na”

Ko da ta shiga dressing room bayan ta sanya inner wears dinta ta dade tsaye gaban wadrobe tana tunanin kayan da zata sa.

A qarshe dai wata material gown ta janyo mai masifar kyau.. Ko da ta sanya ta sossai tayi mata kyau kamar dama don jikinta aka qera gown din.

Fitowa tayi riqe da dan qaramin gyale matching color..

Gaban Vanity mirror ta koma ta fesa turarruka sannan ta qara kallon kanta a madubi tayi murmushi sannan ta juya ta fita.

Su Ibrahim wadanda suke zaune a first sitting room na gidan ne suka ga shigowar Ameera…

“wow.. Ya Ameera kin yi kyau” cewar Suleiman

Munnir ne yace “sai qamshi kike ta yi..”

tana murmushi tace “nagode qani na”

Ibrahim ne yace “black is indeed beautiful.. dagaske idan na tashi aure baqar mace zan dauko ba irin kalar Ya Layla ba wadda da ta dan sha wahala sai tayi ja..”2

Gaba daya suka fashe da dariya yayinda Ameera tace “ni dai babu ruwana..”

Suna cikin hira ne suka jiyo hayaniyar masu aikin gidan..

Aliyu ne ya miqe yace “bari in duba..”

Ameera wadda ta miqe da sauri tace “kar ka damu bari in duba.. I think its Ya Zayd”

Ko kafin ta iso wurin main door na gidan ne ta ji qarar doorbell… da sauri ta qarasa ta bude qofar suka yi ido hudu da shi..

Wani sanyi ya ratsa zuciyoyin su yayinda suke ma juna murmushi..

Sanye yake cikin wandon sweat da polo T-shirt.. yana rataye da jakar Macbook dinshi yayinda Bilal yake tsaye a bayan shi da trolley dinshi.. Dukda he looked exhausted sossai yayi kyau..

Ware hannun shi yayi yayinda ta ruga a guje ta shige jikin shi tare da rungume shi da qarfin gaske..

“Sannu da zuwa, wallahi I missed you”

Yana murmushi yace “me too.. bazan qara tafiya ba tare da ke ba Habibty”

Tana murmushi tace “nima bazan bari ka tafi ba tare da ni ba Ya Zayd”

“kin yi kyau sossai..”

“nagode Yaya”

Bilal wanda yake tsaye yana kallon su sai murmushi yake yi yana mamakin yadda suke fadin sunyi missing juna when tunda ya bar garin nan kullum suna maqale a waya except lokuttan da yake meeting..

STORY CONTINUES BELOW

Gyaran murya yayi sannan yace “Madam ina kwana”

Sai a lokacin ta tuna cewar Bilal yana wurin.. da sauri yayi breaking hug din yayinda ta bi ta rude.. Da qyar ta saita murya tace “lafiya lau.. kun dawo lafiya??”

“lafiya”

Ameera dai juyawa tayi zata koma ciki yayinda Zayd yayi saurin janyo ta jikin shi… da alama baya so tayi nisa da shi.

“Bilal kayi qoqari ka huta a gida.. you should take the whole of tomorrow please..” Zayd ya fadi mishi tare da jaddadawa.

“Okay Sir, thank you”

Gani nayi Bilal ya turo ma Ameera trolley wanda har ta miqa hannu zata ja Zayd yayi sauri ya riqe tare da fadin “I got this”

Bilal yayi ma Ameera sallama sannan ya wuce yayinda suka shiga ciki.

Su Ibrahim wadanda suke zaune a falo ne suka miqe tsaye suka yi mishi sannu da zuwa cike da girmamawa.. cikin fara’a ya amsa wanda tuni Munnir ya qarasa wurin shi zai karbi trolley din hannun shi yace “dont worry qani na… Yanzu dai bari in je in dan huta sai in zo muyi hira ko?”

Cike da murna suka ce “toh Ya Zayd”

Su kam Allah ya sani tun asali suna son Zayd… yanzu haka da yace musu zai zo suyi hira sossai suka ji dadi!

Janyo Ameera yayi suka haura sama zuwa sashen shi.

Suna shiga dakin shi na ga yayi saurin sakin trolley din tare da jefar da jakar Macbook din shi sannan ya janyo Ameera ya rungume ta very tight tare da sakin ajiyar zuciya.

“I love you Habibty” Ya fada muryar shi qasa-qasa.

Ita dai Ameera a duk lokacin da ta ji Zayd ya furta mata wadannan kalaman ji take yi kamar an sanya ta a aljannah.. wani mugun dadi yake ratsa ta.

“I love you too.. very much Yaya.”

Qara matse ta yayi yayinda yake ta shaqar qamshinta mai dadin gaske.. da alama dai turarukan Aina’u Marwan suna aikin su.

Tuni ya zare gyalen da ta yafa ya jefar yayinda yake shafa gashin kanta wanda ta daure shi a tsakiyan kanta.

Zuciyar Ameera sai bugawa take yi yayinda take jin wani sanyi yana ratsa ta.. gaba daya ta shiga wani yanayi a dalilin yadda yake ta shaqar qamshinta yayinda yake goge fuskar shi a gefen fuskarta da wuyanta.. Sai sakin numfashi take yi yayinda take ta lumshe idanuwa..

“Habibty ina daf da in daina zuwa ko ina..”

Ameera wadda take murmushi tace “why is that Yaaya??”

“Because of you.. I just want to be around you every single moment”

Fashewa tayi da dariya cike da murna tace “me too Yaaya..”

Wasa wasa dai sai da suka yi kusan minti Goma maqale da juna sannan ya haqura ya qyale ta amma fa ya qi sakin hannunta..

Bakin gadon shi ya ja ta suka zauna yayinda ya janyo pillow ya kwanta yana kallonta.

Ameera wadda take kallon shi ta ga muguwar gajiya a tare da shi.. idanuwan shi sun nuna alamun bai ma samu wani isashen bacci ba..

“Yaya na ga kamar ka gaji sossai ko??”

“sossai Habibty..”

Miqewa tayi tace “bari in hada maka ruwa sai kayi wanka.. idan kayi breakfast sai ka kwanta kayi bacci ka huta ka ji?”

Girgiza mata kai yayi kamar yadda yara suke yi yayinda tayi murmushi ta wuce bathroom dinshi.. shi kuma ya bi ta da idanuwa.

Ameera dai ko da ta hada mishi ruwan wanka a jaccuzzi bath ta zuba mishi turarukan wanka ta shirya mishi duk wani abinda zai buqata ta fito..

STORY CONTINUES BELOW

Gani nayi ta tsaya turus a dalilin ganin Zayd kwance yana bacci.. da alama ma yayi nisa.

Girgiza kai tayi tace “Allah sarki, bawan Allah ya gaji”

Wurin switch na AC ta nufa ta kunna sannan ta koma wurin shi ta janyo Duvet ta rufa mishi halfway sannan ta juya ta fita.

☆☆☆☆☆☆☆☆

Wasa-wasa dai yinin yau din Zayd yana ta bacci.. ko da ya tashi yayi wanka yayi sallah da Ameera ta tambaye shi abinci sai cewa yayi anjima zai ci.. daga nan ya koma bacci.

Ita dai duk a tunanin ta gajiya ce kuma tunda this is the first time she is seeing his mood this way sai tayi tunanin haka yake yi idan ya gaji..

Bayan sallan la’asar ne ta dage mishi akan sai ya ci abinci.. akan dole ta ja shi dinning suka zauna..
Zayd dai bai yi niyyan ci dayawa ba amma a dalilin dadin da abincinta yayi mishi ne ya ci dayawa.. Yana ci yana yabawa yana santi, ita kuwa har cikin ranta ta ji dadi domin kuwa bata sa ran zai yi mishi dadi ba considering how very good he is a wurin girki.

Bayan ya kammala ne ya sa ta kira mishi su Ibrahim suka zauna a falon shi.. Yana kwance a kan 3-seater kujera yayinda suke zazzaune suna ta yi mishi hira wanda yawanci shine yake tambayan su.. Dama dai Zayd is a good listener sossai ya natsu yana ta sauraron labaran yaran na makarantar su da kuma shirmen da suka yi na yarintar su.

Ameera dai tana zaune a kujerar kusa da shi tana kallon shi jefi-jefi yayinda take ganin kamar something is off a tare da shi.. har tambayan shi ta dinga yi ko akwai matsala amma sai yace mata he is fine.

Wuraren qarfe shida na yamma ne ya mayar da su Ibrahim gida da kanshi, before then kuwa sai da ya hada su da driver ya kai su Super market don su siyo duk abinda suke so. Su kuwa sun cika da murna.. babu qarya kam sun kwaso kayan kala-kala.

Ameera ta so ya bar driver din ya kai su gida tunda he looked tired amma yace kar ta damu..

A lokacin da suka isa gidan Abba kuwa ya tarar da Abba a waje tare da makwabcin shi Malam Zakari, da alama masallaci zasu je don haka ne suka wuce masallacin gaba dayan su.

A yau din kuwa Limamin su Malam Idris baya nan yana da wani uzuri don haka ne Zayd ya ja musu sallar cikin qira’ar shi mai dadin gaske.. shi ya ja su har sallan Isha’I.

Bayan an idar da sallah Isha’I ne ya samu Abba ya sanar da shi yana so ayi expanding din masallacin saboda mutane suna yawa kuma babu space.. ya buqaci ayi ma ‘yan committe magana akan za’a rusa masallacin gaba daya a gina qasa da sama tunda land din babu girma.. Sossai Abba ya ji dadin hakan.. A nan take yayi ma ‘yan committe din magana suka amince.. sai godiya suke yi suna sanya mishi albarka tare da yi mishi fatan samun zuri’a na gari.. Shi kuwa Abba murna suka dinga yi mishi ya samu sirikin arziki..

Tare suka jera suka koma gida..

Su Ibrahim suka kwashe kayan su a motar Zayd sannan suka shiga gida.. Abba dai ganin kaya masu yawa sai da yayi ma Zayd magana wanda shi kuma ya dinga bashi haquri.. A haka dai suka shiga gidan. 

Ko da ya gaisa da Umma sai da yayi tambayar kunun aya idan akwai a bashi..

Umma dai dama tayi mishi nashi special ta ajiye mishi a freezer don haka ne ta dauko mishi yana ta godiya.

A daidai wannan lokacin kuwa Layla tana daki ta jiyo muryar Zayd kamar daga sama.. A guje ta miqe ta shafa kwallin ta tare da ambatar sunan shi kamar yadda Malam ya ce..

Ko da ta shigo falon tuni yayi ma su Abba sallama yayi tafiyar shi.. Sossai ta ji haushi.

Kafin ma su Abba su kula da ita a falon ne ta koma ciki abinta.. Ta qudurta a ranta the only way to finish it off is in his company don haka dole ne ta datse shi a can..7

STORY CONTINUES BELOW

Ghen ghen ghen….

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆

Wuraren qarfe takwas da rabi na dare Ameera tana tsaye gaban vanity mirror dinta sanye cikin wata doguwar riga shara-shara wadda ta bi jikinta.. Ameera dai dukda batada body irin na Layla babu laifi she is not bad…

Kallon kanta take yi yayinda take tunanin yadda zata dinga sa irin kayan tana zuwa gaban Zayd..

Yanzu haka idan ka kalla da kyau har inner wears din jikinta kana gani ta cikin rigar.. toh amma da ta tuna da abinda qawarta Zarah ta fadi mata sai na ga tayi murmushi tace “I have no choice I guess”

Babu abinda take bazawa sai qamshi.. Gani nayi tana kallon stitches dinta closely yayinda ta saki ajiyar zuciya… babu laifi yana ta healing.

Agogo ta kalla ta ga qarfe tara saura kwata.. ta tabbatar Zayd ya dawo don haka ne ta dauki hularta ta sanya sannan ta fita.

Kai tsaye sashen shi ta nufa.. Ko da ta qwanqwaso qofar shi ta shiga gani nayi ta tsaya cak cike da tsananin tsoro a dalilin ganin shi da tayi kwance a ta gefen gadon shi a qasa.

Cikin tsananin tashin hankali ta ruga wurin shi a guje tana fadin “inna lillahi wa’inna ilaihir raji’un.. Ya Zayd what’s..”1

Kasa qarasa maganarta tayi a dalilin taba shi da tayi ta ji jikin shi yayi mugun zafi..

Zama tayi a qasan ta dago kanshi ta dora a bisa cinyar ta tana shafa fuskar shi.. idanuwan shi sunyi ja.

“Ya Zayd me ya same ka?? baka da lafiya? na shiga uku.. meyasa baka fadi mun ba?”

Tuni hawaye sun fara gangarowa daga fuskarta.

“hey relax Habibty, kai na ne yake ciwo kuma zai daina” ya fada yayinda ya gyara kwanciyar shi a kan cinyarta.

“a’a Yaaya don Allah ka zo mu je asibiti ko a kira likita..”

“kin san bana so ko??”

“toh ya kake so in yi?? zama zanyi ina kallon ka..”

“kiyi mun addu’a, I will be fine… kawai fa gajiya ce”

“kenan tunda ka dawo kana jin ciwo shine baka fadi mun ba??”

“kiyi haquri Habibty..”

“tashi ka koma kan gado kar bayan ka yayi ciwo”

Babu musu ya amince ta taimaka mishi ya koma kan gadon..

Hannunta ta dora a bisa gashin kanshi mai laushin gaske yayinda take birkitawa a hankali.. tana yi zuciyarta na bugawa.. Gaba daya ta shiga damuwa. Ji tayi kanshi yana qara zafi yayinda yake ta motsi alamar lallai ciwon kan yana matsa mishi..

Ba tare da bata lokaci ba tana dafe da kanshi ta fara yi mishi addu’a kamar haka “Laa Yusadda’uuna anha walaa yunzifuun”

(aya ce ta Goma sha tara a cikin suratul waqi’ah)

Haka ta dinga maimaitowa har sau talatin da uku.. daga nan ta koma karanto suratul takathur.. tana yi tana shafa kan shi a hankali, Cikin ikon Allah kuwa har zafin ya fara sauka..

Bakinta ta kai saitin kunnen shi tace “ina zuwa..”

“ina zaki je??” ya tambayeta muryar shi qasa-qasa yayinda idanuwan shi suke a rufe.

“Zan kawo maka apple ne..”

“what???” ya fada tare da bude idanuwa..

Tana murmushi ta dan ja gemun shi tace “yes Ya Zayd, Apple boosts one’s inner energy leading to the brain, I am sure it will help you”

STORY CONTINUES BELOW

Murmushi ya dan yi shima sannan yace “the love you have for apple though..”

Tana dariya tace “let me just come” ta sauka daga kan gadon ta wuce ta fita..

Gyara kwanciyar shi yayi, Sossai yake jin sauqin ciwon kan.. da alama dai addu’ar da Ameera tayi mishi ce tayi aiki.

Ameera ce ta shigo riqe da plate dauke da slices na Apple yayinda ta qarasa wurin shi kan gadon ta zauna..

“Yaaya ga apple din”

Bude idanuwa yayi sannan ya tashi zaune.. Ameera ta jingina mishi pillow a headboard na gadon sannan yayi resting bayan shi yana kallon ta cike da So..

Slice na Apple ta dauka sannan ta kai saitin bakin shi ya bude ta saka mishi..

“kin yi kyau Habibty.. I love your slim and beautiful body”

Murmushi tayi cike da murna tace “nagode yaaya”

A haka dai ta cigaba da bashi apple din har ya cinye shi tas..

Bayan ta mayar da plate din kicin ta dawo ne ta haye kan gadon tana kallon shi tace “Ya kan?? ya rage ciwo??”

“yes Habibty, it’s all thanks to you.. nagode”

“anything for you..” ta fada yayinda ta gyara mishi Duvet din da ya rufa da shi..

Ta juya zata sauka daga kan gadon ne ya cafko hannunta.. Da sauri ta juyo tana kallon shi. Zuciyarta kuwa sai bugawa take yi..

“Habibty tafiya zakiyi ki bar ni??” Ameera ta bude baki zata yi magana ne yace “…please ki kwana anan, I need you close to me”

A rude tace “but yaa…”

“pleas
e Habibty”

Ajiyar zuciya ta saki sannan tace “toh bari in je in sa kayan bacci”

Ba tare da ya saki hannunta ba yace “No.. kiyi bacci da na jikin ki..”

Ameera dai shiru tayi tana kallon shi.. lallai fa yau ake yin ta. Da farko tayi zaton it won’t be a big deal kwana tare da shi but yanzu da abun ya zama reality sai take jin wani iri..

Bata ankara ba ta ji ya janyota.. babu shiri ta kwanta gefen shi suna fuskantar juna..

Yau wace rana gata nan tare da Zayd suna kwance a kan gado daya a matsayin ta na matar shi.. dream come true for her.

Kamar ya san me take tunani yace “thank you for being my wife.. I love you so much Ameera” yayinda ya miqar da hannun shi ya kashe wuta sannan ya qara janyo ta ya matse ta a jikin shi gam ya gyara musu Duvet..

Ameera wadda zuciyarta take bugawa ji tayi yana tofa mata addu’a…

Bayan kusan minti Goma sha biyar Ameera dai bata yi bacci ba.. Sai motsi take yi tana gyara rigar jikinta, da alama she is not comfortable.

Bata ankara ba ta ji hannun shi a bayan ta yana zuge zip din rigarta ahankali.. hakan kuwa ya haddasa mata wata muguwar faduwar gaba yayinda jikinta yake rawa..

muryarta a shaqe tace “Yaaya..”1

“ssssshhhh..” ya fada yayinda yayi unhooking bra dinta yace “it’s making you uncomfortable.. remove it”8

Ameera dai sossai ta cika da mamaki.. Ya aka yi ya gane hakan?? ba ma wannan ba, ta ya zata cire a gaban shi toh??

Da ta tuna cewar cikin duhu ne sai ta tashi zaune ta sauke hannun rigar ahankali sannan ta cire bra din ta ajiye a gefe.. bayan ta mayar da hannun rigarta ne ta ja Zip sannan ta koma ta kwanta..

Tana kwanciya kuwa ya janyo ta jikin shi tare da matse ta gam.. this time both of them feeling very much comfortable!

Da alama dai yace ta cire ne because he wasn’t feeling comfortable just as she wasn’t too..6

Aikuwa ko minti biyar bata qara ba bacci ya sace ta…washegari!!

ZAYD AHMAD FADOUL’S RESIDENCE

UNGUWAN RIMI GRA+

Zaune yake a kan Ottoman na gadon dakin shi wuraren qarfe takwas da rabi na safe yayinda yake riqe da wayar shi yana video call da Zaheera.

Zayd dai ya farka bai ga Ameera ba.. da alama ta riga shi tashi ta bar dakin. Ciwon kan shi kuwa Alhamdulillah domin dai tun jiya da Ameera tayi mishi adduo’i ya samu sassauci sossai, a yanzu kuwa da ya samu one of the best sleep of his life sai ya warke garau.

A yanzu haka yayi wanka ya shirya cikin qananan kaya na three quarter da T-shirt ne kiran Zaheera ya shigo wayar shi.

“Sweetheart ina ta kiran ka a waya jiya ka share ni ko? wallahi I was worried ne, na ji jikina babu dadi and I sensed you might not be feeling well.. na kira wayar matarka ita ma she wasn’t picking”

“Sweetheart don Allah kiyi haquri, jiya kai na ya dinga ciwo.. na sha wahala sossai, ban ma san inda wayoyin suke ba.. Habibty kuma I am sure ta bar nata a dakinta ne..”

Yayi murmushi ya cigaba da fadin “…Nagode ma Allah da ya bani matar arziki.. addu’a kawai tayi mun and I felt some relief”

“and what happened next??” ta tambaye shi tana kallon shi in a mischievous way1

in a confused tone yace “ban gane what happened ba..”

Zaheera ta fashe da dariya tace “what is that doing on your bed??” ta nuna bra din Ameera da ta hango a kan gadon.

Da sauri ya juya ya dago bra din tare da fashewa da dariya yace “Ya salaam, Sweetheart yaushe kika lalace haka?? see nothing hap…”

“hmmm.. na gane, Allah ya kawo ‘yan uku”

“Ameen sweetheart..” ya fada yana dariya.

“ni kam dama na kira ne in ji lafiyarka.. let me go attend to Baby eeesh, gata can ina jin ta tana nema na”

“thanks sweetheart.. my regards to the kids”

A daidai nan ne Ameera ta shigo dakin.. Zayd wanda hankalin shi yake kan wayar bai kula da ita a tsaye ba

“insha Allah Sweetheart.. I love you so much”

“I love you too.. very much”

“Ba wani nan, So na ya ragu a zuciyarka tunda kayi mun kishiya..”

fashewa yayi da dariya yace “soyayyar ki daban ce Sweetheart.. You are..”

“Inna lillahi wa’inna ilaihir raji’un..” ya jiyo muryar Ameera wadda take a tsaye hawaye na bin fuskarta.

A rude ya tashi tsaye yace “Habibty..”

Tuni Ameera ta juya ta ruga a guje zata bar dakin yayinda ya bi bayan ta a guje ya riqo hannunta ya hada ta da bango..

STORY CONTINUES BELOW

“Ni ka qyale ni.. dama na sani cewar ba sona kake yi ba.. baka taba sona ba shine zaka auro ni ka wulaqanta ni.. kana soyayya da..”

Wayar hannun shi ya dago ya nuna mata screen din wanda hakan ya sanya tayi freezing a dalilin ganin fuskar Zaheera tana ta dariya.2

Runtse idanuwan ta tayi yayinda ta cika da tsananin kunya..1

Tana jin shi yace “Sweetheart kin ga abinda kika janyo ko?? kina nema ki kashe mun aure..”

“Subhanalillah.. Habibty kiyi haquri, Zayd naki ne ke daya, ke kadai kike mulki a birnin zuciyar shi so please calm down.. ni kam sai anjiman ku” tana dariya ta kashe wayar.

Ameera wadda take tsaye a jikin bango har a wannan lokacin idanuwanta a rufe suke yayinda hawayen ke ta bin fuskarta.

Wayar shi ya sa a aljihun shi sannan ya duqo da fuskar shi saitin nata ya qura ma innocent face dinta idanuwa..

Hannu ya sa ya share mata hawayen fuskar ta sannan yace “hey open your eyes and look at me”

A hankali ta bude idanuwa ta ga fuskar shi few inches away from nata.. Zuciyarta ce take ta bugawa yayinda soyayyar shi take yawo a jini da jijiyar ta..

“ke kadai ce macen da nake so a duniyan nan.. don Allah kar ki qara doubting soyayyar da nake yi miki kin ji??”

Daga mishi kai tayi alamar ‘toh’ yayinda tace “kayi haquri”

Shiru yayi yana kallonta yana wasu tunani.. Ameera wadda take kallon shi cike da mamaki ce tace “Yaaya why are you staring at me…” kafin ta qarasa maganarta kuwa ya hade bakin ta da nashi ya fara kissing dinta gently..3

Ulaaalaaaa..

Ameera dai freezing tayi na wasu few seconds yayinda numfashinta yake barazanar daukewa.. Gaba daya jikinta ya saki yayinda wasu abubuwa suke motsi a cikin ta.. Tuni ta shige wani planet na daban..

A hankali ta dago hannuwanta tayi hugging dinshi yayinda ta shiga mayar mishi da martani because dukda this is her first time experiencing this thing she just can’t resist..

Tun suna kissing juna gently har al’amarin ya koma much more intense.. Gaba daya sun birkita ma juna lissafi. Da zarar sun dan sarara don su kama numfashi sai kuma su koma su cigaba..

Ganin kamar tsayuwar ta fara gagagarar su ne yayi sama da ita… Bata ankara ba ta ji ya sauke ta a kan gado, har a wannan lokacin bakin su a hade yake..

Zare bakin shi yayi daga nata sannan ya koma kissing gefen fuskarta zuwa wuyan ta yayinda take ta sakin mumfashi…

Sanyin AC da ta ji ya ratsa fatar jikinta ne ya dawo da ita daga duniyar da ta shige.. Tuni Zayd ya raba ta da kayan jikinta..2

Aikuwa anan hankalinta ya tashi..

Jin yana addu’a ne ta qarasa rudewa.. muryarta tana rawa tace “Yaaya me zaka yi?? don Allah kayi haquri.. ban yi wanka ba..”

Zayd dai sai da ya gama addu’o’in shi sannan yace “there is no problem Habibty, rashin wankan naki bazai hana wannan ba..”

Ameera dai bata qara sanin abinda yake faruwa ba.. Zayd ya jefa su wata duniya wadda basu taba zuwa kusa da ita ba balle su shiga ciki, duniyar ma’aurata, duniya mai cike da soyayya da farin ciki marar misaltuwa.. a daidai wannan lokacin suka sadaukar
ma juna jiki da ruhin su gaba daya.. ta kasance shi sannan ya kasance ita.. Burin kowannen su a wannan lokacin su nuna ma juna soyayyar da suke yi ma juna, su faranta ma juna rai sannan su tabbatar su suke mulki a birnin zuciyoyin juna.. sunyi exploring juna like they have never done on anything else.. Sun raya sunnar manzo (SAW) cikin nagartacciyar soyayya mai tsabta.

STORY CONTINUES BELOW

Ameera bata taba sa ran haka abun yake ba.. ta sha karantawa cewar wasu matan har kusan fita hayyacin su suke yi saboda azaba amma a yau ta qaryata.. wannan abun ya fi kowanne abu dadi a duniya, toh bata sani ba ko qila bala’in son da take yi ma Zayd ne ya hana ta jin zafi ba, abinda ta sani dai shine bata qi su kasance a wannan yanayin ba har abada..

Zayd on the other hand ya gode ma Allah da ya bashi mata kamar Ameera wadda ta kawo budurcinta har gidan aurenta, ta bashi komai nata yayi yadda yake so da ita, ta jefa shi wata duniya wadda ko da wasa baya so ya fito daga cikin ta.. bai qi ya dawwama ba a ciki.. komai nata is so perfect. Babu abinda ya dinga yi sai sanya mata albarka tare da jaddada mata irin son da yake yi mata.

Bayan lokaci mai tsawo suna gurzar soyayyar su ne suka sassauta…

Rungume ta yayi gam kamar wanda yake tsoron za’a sace mishi ita..

Kalaman soyayya kuwa Ameera ta sha su babu iyaka… Lallai ta amince Zayd nata ne… ta cika da farin ciki marar misaltuwa. A haka har bacci ya kwashe su…

☆☆☆☆☆☆☆☆

Wuraren qarfe goma sha daya da rabi yana zaune daf da ita a kan gadon dakin shi yana ta kallon ta yayinda wata muguwar soyayyarta take bin jini da jijiyar shi… a yanzu ya tabbatar babu abinda yake so sama da wannan matar tashi da yake kallo.

Zayd dai minti Goma sha biyar da suka wuce ne ya farka ya shiga wanka.. Bayan ya fito ya shirya ne ya dawo kan gadon ya zauna yana kallon ta..

Hannushi ya miqar ya shafa gefen fuskar ta yayinda ta motsa kadan tare da bude idanuwan ta..

Murmushi ya sakar mata wanda itama ta sakar mishi.. Kamar wadda aka yi ma shocking kuma sai na ga ta zaro idanuwa yayinda tayi saurin tura kanta gaba daya cikin duvet din..

Fashewa yayi da dariya yace “Habibty?? are you serious?? kunya na kike ji??”

Ameera dai shiru tayi bata ce komai ba.. abubuwan da suka yi hours ago suke dawo mata.. how will she face him after all that??2

“Inna lillahi wa’inna ilaihir raji’un.. Yaaya don Allah ka tafi” ta fada cikin shagwaba yayinda ta qara takure kanta a cikin Duvet din.

Yana dariya yace “amma dai da wasa kike yi ko? na daya dai kin ga wannan daki na ne, na biyu kuma a matsayina na mijin ki I have the right to be wherever you are..”

Shiru ya dan yi sannan yace “wait.. kunya na kike ji??? after all you said and did dazu???”

“please Ya Zayd…. wayyo Allah, please dont stop..” ya fadi cikin irin muryar ta yayinda tayi saurin bude fuskar ta kamar zata yi kuka tace “Yaaya please stop..”

Yana dariya yace “toh na bari.. kiyi haquri kar kiyi kuka my Habibty..”

Ya duqo tare da sakar mata kiss a goshinta, kumatunta sannan bakinta yace “thank you very much for giving me all of you.. Yanzu ki tashi mu je inyi miki wanka..”

A gigice tace “please no.. I am not a small girl Yaaya.. zan iya yi da kaina”

“really??” ya tambayeta cike da mamaki yayinda ya matsa ya bata wuri yace “toh big garl.. tashi ki je..”

Ameera wadda take dafe da Duvet bisa qirjinta ce ta yunqura zata tashi amma ta kasa a dalilin mugun tsamin da jikinta yayi..

STORY CONTINUES BELOW

Kashe mata ido daya yayi yace “too weak to move I guess?”

“toh laifin wa??” ta fadi tana hararar shi

Yana murmushi yace “Kiyi haquri Habibty.. shiyasa nace zan taimaka miki don na san I am the guilty party here..”

Kafin tayi magana ne ya dauko ta cak kamar wata Baby ya wuce bathroom din da ita..

☆☆☆☆☆☆☆☆

Zaune suke a kan dinning suna breakfast..

Breakfast din da Ameera ta hada tun da safe wanda a lokacin da ta je kiran shi ne ta tarar yana waya da Zaheera wanda tayi misunderstanding and it led to a beautiful moment.. moment that will forever be glued to their memory for the rest of their lives.

A yanzu haka ko da suka zauna yayi sanyi amma fa haka nan suke cin shi don kuwa daga shi har ita yunwa suke ji sossai..

Haka dai ya dinga bata a baki yayinda shima yake ci har suka cinye..

Shi ya kai dishes din kicin yayinda take zaune tana jiran shi kamar yadda ya umurce ta..

Ita dai Ameera mamaki take yi sossai yadda Zayd yake yi mata komai a cikin gidan.. duk wani abinda yakamata tayi shine yake yi mata. A da tayi tunanin saboda aikin shi bazai bata lokaci ba amma he completely proved her wrong.. it looked as if he is not a busy person ma at all!

Ko da ya dawo hannunta ya kamo yace “zo mu je ki ga wani abu..”

Miqewa tayi tsaye tace “meye wannan Yaaya??”

“something special”

“toh bari in je dakina in canza kaya…”

“why??”

Ameera dai sanye take cikin one of his shirts wadda tayi mata girma sossai, sai da ya nade mata hannun rigar.. dayake dai babu kayanta a dakin shi shine ya ara mata wannan din.. babu komai a jikinta sai shirt din and she is not comfortable.

Cikin shagwaba tace “toh Yaya babu komai fa a jikina and…”

Janyo ta yayi jikinshi yace “ssssshhhh.. it’s better that way Habibty, ki dan sha iska kin ji.. don’t worry it’s just me and you a cikin gidan nan so ki saki jikin ki.. ba na riga na ga komai ba? idan fa ina so ma you will walk around all naked for me to..”

“what” ta fada cike da mamaki yayinda ta zaro mishi idanuwa.

Fashewa yayi da dariya yace “hey relax.. just kidding”

A haka dai ya janyo ta suka nufi wani bangare na gidan da bata taba zuwa ba.. tabbas gidan Zayd yana da girma, A yanzu ma zata iya cewa bata yi exploring 60% na gidan ba..

Yanzu haka inda suka je ya fi kamar a kira shi basement domin kuwa it’s an under ground building.

Ita dai ta ga sun wuce wani wuri kamar sports Arena.. domin kuwa ta sliding door din wurin ta hango wani danqareren indoor swimming pool sai kuma wani small basketball court.. she is sure there is more.

“kar ki damu.. zamu zo nan din anjima…” Ya bude wata qofa ya cigaba da fadin “….akwai more important..”

Bai qarasa magana bane Ameera ta saki hannun shi ta qarasa shiga wurin da sauri- wannan wurin dai yayi kama da Mini-bedroom tunda harda gado keda akwai a ciki.

STORY CONTINUES BELOW

Ihu ta saki a dalilin ganin abinda take masifar so a rayuwarta…

AQUARIUM

The largest one she has ever seen in her life.. and the first time she is seeing it in reality..

“Na shiga uku me nake gani?? am I dreaming??”

Yana biye da ita yace “you are not Habibty”

2

Ameera dai qarasawa tayi jikin bangon glass na aquarium din tana ta bin kifayen da suke ciki wadanda suke ta kai da komowa stylishly yayinda take shafa glass din.

“you like it??”

Juyowa tayi da sauri tana kallon Zayd wanda yake tsaye few inches away cike da tsananin murna tace “Yaaya I love it… ya aka yi ka san ina son wannan??”

“kin manta ke kika fadi mun??” ya qaraso wurinta ya tura ta jikin glass na aquarium din ya dafa wall din sannan ya duqo saitin fuskarta yace “ranar da muka ci bonus na MTN da nace ki bani labarin rayuwarki.. you told me everything you like and dislike..”3

turo baki tayi tace “ba wani bonus.. you just playe
d me ne ranan”

Cafko lips dinta yayi da nashi yayi smooching dinta briefly sannan yace “yeah whatever Habibty”

“you mean duk abinda na fadi maka a ranar ka..”

“… na riqe a kai na kamar karatu Habibty” ya qarasa maganar yana kallon ta cike da so da qauna.

Hannuwanta ta sagala a bisa kafadun shi ta zagaye su a wuyan shi yayinda take shafa bayan gashin kan shi cikin wani salo tace “I love you Ya Zayd.. I love you very much, bazan taba son wani abu sama da kai ba a duniyan nan Ya Zayd”

Yana murmushi yace “nima haka Habibty, I love you too, soo very much but there is a small problem??”

A rude tace “wane irin problem Ya Zayd??”

“here you go again Habibty.. kina ta kira na YA ZAYD, when I am not your brother.. ana zawjak Habibty” (ni mijinki ne)

tana murmushi ta birkita gashin kan shi wanda nan da nan yayi buzu-buzu tace “afuwan HABIBI, bazan qara ba”

“hey you just called me Habibi??” ya fada looking so suprised

“Na’am Habibi, ahbak jiddan.. la’aistaďi ‘il aysh biduunik” (eh masoyi na, ina sonka sossai, bazan iya rayuwa ba tare da kai ba)

Wani irin murmushi ya saki sannan yace “dama kin iya larabci shine baki fadi mun ba?”

“dan kadan na iya Habibi.. I learnt back then at islamiyya”

Girgiza kai yayi yace “hmmm.. yadda kika yi fluently I am sure kin iya sossai Habibty.. ki dinga yi mun kin ji?? kar ki damu idan bakiyi daidai ba ma zan dinga gyara miki.. haka Ammi da Abbu suka dinga yi ma juna lokacin da suka hadu.. he helped her with Arabic and she helped him with hausa and a little fulani.. gashi yanzu duk sun iya”

STORY CONTINUES BELOW

Ameera tana murmushi tace “insha Allah Habibi na..” tayi mishi kiss a kumatu sannan ta juya tana facing aquarium din tare da rungume hannun shi wanda ta zagaye su a cikin ta yayinda ya kwanto ta bayanta with his head slightly on her shoulder.

“wallahi Ina son aquarium dinnan.. very big and beautiful..”

Ta nuna daya daga cikin kifayen da suke ciki tace “ka ga wancan flat one din?”

“yes Habibty..”

“its called a labyrinth or Gourami”

“really??? wancan fa??” ya nuna wani wanda rabin shi orange color ne with a little bit of red.

“that’s a rainbow fish.. namiji ne shi and then that one” ta nuna wani mai wide fins wanda yake da dots na black and white a jikin shi tace “.. is a cichlid, it’s an angel fish”

“Wow.. Habibty, I am impressed sossai.. meyasa baki karanta oceanography ko hydrobiology ba?? anything that has to do with sea..”

Kafin ya qarasa magana ne ta fashe da dariya tace “Habibi if I study one of those where will I fit into in Nigeria??? precisely Kaduna.. River Kaduna??”1

Shima fashewa yayi da dariya yace “kuma fa haka ne.. whoa, not possible kam”

Murmushi tayi tace “thanks very much for everything you’ve done for me Habibi.. the love, the care, the…”

Juyo da ita yayi ya rungume ta sannan yace “no thank you for loving me unconditionally Habibty..” yana baza mata kisses yace “ni bari in dan kwanta while you are checking your aquarium out.. ina jiran ki”

Murmushi tayi tace “okay my love”

Zayd dai komawa yayi kan gadon ya kwanta yayinda yake ta kallon ta da yadda take ta bin glass wall din tana kallon different species na kifayen and how they move from one place to another.. Gaba daya ta zama lost in her own little world. She kept going from one side of the aquarium to the other..

Wayar shi na ga ya dauka yayinda ya bude camera yana ta snapping dinta.. Ameera wadda hankalinta yayi nisa bata san yana snapping dinta ba in his over sized shirt da ke jikinta.. she looked beautiful in it.. dayake dakin babu wadataccen haske sai hasken aquarium din da yayi reflecting ne ya bashi damar ganin figure dinta a ta cikin shirt din.. Haka ya qura mata idanuwa yana enjoying view din…

Tayi kusan minti talatin a tsaye gaban aquarium din yayinda Zayd yake kwance yana ta kallonta..

Gani nayi ta juyo ta nufi wurin shi bisa gadon sannan ta haye bisa jikin shi ta kwanta flat with her chest pressed against his’.

Wrapping hannun shi yayi around her yayinda suka kasance a hakan ba tare da sunyi ma juna magana ba..

Gaba dayan su wani sanyi ne yake ta ratsa su yayinda suke cike da jin dadin kasancewa a wannan yanayin.. they feel nothing but pure love and affection for eachother.

“Habibty” ya kira sunan ta ahankali.

“na’am”

“ina so muyi consulting Gynecologist don ta bamu shawara with regards to family planning and birth control.. I dont want you to conceive da wuri saboda school da kike zuwa and I feel you are too young to start dealing with stress na raino..”

“ssssshhhhh” ta dago kanta tare da sa yatsarta a bisa lips dinshi tace “kar ka damu da wannan Habibi, bamu buqatar ganin kowa because I am ready to conceieve.. I wanna give you a child- our child”

“amma Habibty, school fa? Na san burin ki shine ki gama da first class, dont you think hankalin ki zai kasu??”

“Ko kadan Habibi.. You are my priority and I can give up everything for you..”

STORY CONTINUES BELOW

“Ya Salam.. nagode sossai Habibty” ya fada yana murmushi.

itama tana murmushi ta binne fuskarta a wuyan shi tana wasa da gemun shi tace “ka san kuwa babban burin Umma shine ta ga grand child dinta??”2

Murmushi yayi yace “Just like my Ammi, kullum maganarta fa inyi aure in haifo yara- jikokinta”

“Zamu haifo musu Habibi, Allah yasa mu haifi twins Maza masu kama da kai..”

“No Habibty, mata dai.. masu kama da ke”

“wallahi I have always liked twins Habibi..”

“you got married to one and you shall give birth to sets..”

“insha Allah habibi na..”

A haka dai suka cigaba da hirar su kala-kala yayinda suke enjoying yanayin dakin.. A hakan kuwa tana kwance a bisa jikinshi bacci ya kwashe su.

☆☆☆☆☆☆☆☆

Basu farka ba sai wuraren qarfe biyu saura.. within the time of Zuhr don haka ba tare da bata lokaci ba suka wuce sashen Zayd suka yi wanka suka dauro alwala sannan ya ja su sallah.

Da kan shi ya je dakinta ya dauko mata doguwar riga marar nauyi.. kamar yadda ya hana ta sa inner wears da safe haka wannan karon ma, a cewar shi yakamata ta sha iska.. babu shiri ta zura doguwar rigar haka nan yayinda ya dinga yaba kyan da tayi..

Ameera dai a da tana yi ma kanta kallon mummuna amma tunda ta hadu da Zayd ya canza mata tunani.. she now sees herself as the most beautiful girl in the world. As long as her man sees her as the most beautiful, why shouldn’t she acknowledge it and be grateful??

Zayd dai Jan ta yayi suka nufi kicin inda ya zaunar da ita kan kujerar kicin island sannan yace mata “just sit here and watch how your husband cooks for you with so much love”

Tana murmushi tace “don Allah ka bari Habibi.. I am suppose to do this fa..”

“bana so kina wahala Habibty.. besides I enjoy doing this.. it’s my hobby”

Haka kuwa ta zauna tana ta kallon shi yayinda yake ta hada abinci kala-kala cikin qwarewa.. Yana yi suna hirar soyayya tana tambayan shi about kalolin abincin da yake hadawa yana yi mata bayani.. from time to time kuma yana zagayowa wurinta ya baza mata kisses, suyi smooching juna son ran su sannan ya koma.

qamshin girkin shi da ya cika ko ina ne ya sanya Ameera miqewa ta koma wurin shi harda cokalinta a hannu ta dinga dandanawa tana santi (tun ma kafin ya gama) shi kuma yana ta yi mata dariya.

Cikin qanqanin lokaci ya shirya abinci har kala uku- Pot
ato chicken stew, lamb saute with pasta sai kuma batter fried fish with cheese sauce all in very small quantities as usual..

Ita ta taimaka mishi suka jera neatly akan dinning..

Har ya zauna sai kuma ta ga ya tashi da sauri yace mata yana zuwa.. Kicin din ya koma ya dawo riqe da Goran kunun ayan shi da ya karbo wurin Umma jiya har Ameera tana yi mishi dariya.

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆

Zayd yana can suna gurzar soyayya kala-kala da matar shi yayinda Layla take can zaune a kamfanin shi sanye da kwallin malamin Hajiya Suwaiba a idanuwanta ta kasa ta tsare tana jira tayi tozali da shi..14

Tun da safe ta je kamfanin tana ta jira bai shigo ba.. da ta gaji da zama ne ta miqe jiki a sanyaye ta tafi..

Tana cikin napep zata je gida ne tayi tunanin zuwa gidan shi.. dukda bata san gidan ba bata sha wahalar nema ba tunda dai Zayd is a rich and powerful man.

Aikuwa dai ko da mai Napep ya shigo layin hatta kwaltan da aka shimfida sai suka ji ta daban.. Shi kanshi mai napep din sai da yace ‘danqari’

Ainihin GRA ce ta Unguwan rimi domin kuwa tun daga farkon layin har qarshe manyan gidaje ne masu kyan gaske ke bin juna sai dai gaba dayan su babu wanda ya kamo qafar na Zayd.. ga girma sannan ga kyau (abinka da mai qera gida da kanshi)

‘Yanzu Ameera ce a cikin wannan gidan??’ tambayar da take ta yi ma kanta kenan yayinda wasu hawaye masu zafi suka nemi fita amma tayi saurin mayar da su kar kwalli ya tsiyaye.

Layla dai jiki a sanyaye ta nufi bakin gate na gidan wanda tun kafin ta qwanqwasa ne wani qaton security ya fito yana kallonta cike da disgust..

Da alama dai ta CCTV camera ya ganta shine ya fito..

A yadda yake kallonta zaka rantse ya san ta a matsayin wadda ta wulaqanta mai gidan nasu ne..

Tabbas kusan haka din ne domin kuwa Maigidan nasu ya basu strict warning through Bilal wanda har hotunan su ya nuna musu na ita da mahaifiyarta akan ko da wasa kar su bari su taba gate din gidan ma balle su shigo ciki..3

“what is it??” ta jiyo muryar shi da qarfi cikin fada wanda har sai da zuciyarta ta buga saboda firgita ta da yayi.

Muryarta tana rawa tace “uhmm.. please I came to.. uhm.. I came to see your oga”1

Tsaki ya ja sannan yace “you cant see him. just go”

Ya juya zai koma ciki ne tace “i am his wife’s sister..”

mutumin ya juyo yace “and so??.. my friend leave this place before i release the police dogs”

Jin ya ambaci kare kuwa ta juya da sauri jiki a sanyaye.. wasu hawaye masu zafi ne suke bin kumatunta yayinda kanta yayi mugun nauyi.2

Ta tabbatar cewar an ba security din order ne tunda dai bai taba ganinta ba amma yayi treating dinta haka..

Hannu ta dora a kai tana fadin “na shiga uku ni Layla.. yanzu ya zanyi da rayuwa ta??”

A haka ta dinga tafiya tana kuka.. tafiya mai tsawo domin kuwa babu napep a layin (me zai kawo napep tunda unguwan ce ta masu kudi??) Ga uwar rana da take dukan ta a tsakar kai.2

♤♤♤♤♤♤♤♤

Toh fa…

Layla fa ta shiga matsala..

Har yanzu dai ta kasa ganin Zayd gashi kuma sai zirara kwalli take yi a banza..

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *