ZABI NA CHAPTER 12 BY FADEELARH

ZABI NA CHAPTER 12 BY FADEELARH

Www.bankinhausanovels.com.ng 

ZAYD AHMAD FADOUL’S RESIDENCE

UNGUWAN RIMI GRA+

Wuraren qarfe tara na dare Ameera tana tsaye a gaban daya daga cikin wadrobes din dressing room na dakinta daure da towel… Da alama wanka tayi.

Basu dade da dawowa daga gidan Abba ba..

Ko da Zayd ya koma gidan Abba zama yayi akayi hira sossai harda Abban.. Sai da suka yi dinner sannan suka bar gidan..

Ita kuwa Mama tana can cikin daki tana ta faman lallashin ‘yarta wadda duk ta bi ta haukace.. Ta qarfafa mata qwarin gwiwa akan lallai da zarar Hajiya Suwaiba ta ga Malam toh lallai Hanya zata yi musu kyau.

Ko da suka shigo gida kuwa Ameera wucewa tayi straight sashen ta don yin wanka.

Ameera tayi kusan minti biyar tsaye tana qare ma kayan baccin ta kallo.. Kayan bacci ne kala-kala har basu qirguwa..

Zaheera, Zarah da su Maheera ne suka jera mata su a wadrobe din tare da sauran kayan lefenta.. idan ka bude wadrobes din ka ga yadda aka jera kayan zaka yi zaton na sayarwa ne aka jera a shago..

Gani nayi ta sa hannu ta janyo wani pyjamas na riga mai dogon hannu da dogon wando cotton ta sanya sannan ta dauko hula ta sa a kanta tare da tura ta baya yadda bazata dinga taba stitches din da yake kan hairline dinta ba.

Ko da ta fito daga dressing room din sai gani nayi ta tsaya cak tana kallon shi cike da mamaki..

Yaushe ya shigo???

Zayd ne zaune a kan gadonta riqe da wayoyi a hannun shi.. Ga kuma kwalayen su a gefen shi bisa gadon harda sim cutter.

Sanye yake cikin three quarter sweat da T-shirt… sossai yayi kyau, Gashin nan nashi na larabawa ya sha gyara ya kwanta sai qyalli yake yi.. ya fito sak a balaraben shi. Duk turarukan da ta fesa bayan ta fito wanka sai ta ji ta daina jin qamshin su a dalilin na Zayd mai sanyi da dadin bala’i da ya cika ko ina..

Ameera dai zuba mishi idanuwa tayi babu ko qyaftawa yayinda tayi nisa a tunani..

Allah ma ya sani tana masifar son Zayd!

“Habibty wannan kallon fa??” ta jiyo muryar shi.

Ajiyar zuciya ta saki sannan tayi murmushi tare da wayancewa tace “me kake yi??”

Gani nayi ta qaraso wurin shi ta zauna kusa da shi a gefen gadon.

“Na kawo miki new phones ne shine nake sa miki sim card dinki a ciki..”

Ya miqa mata Samsung galaxy S21 ultra sannan yace “your main line is here.. na cire shi daga wayarki na sa miki a ciki” 

Ya miqa mata I-phone 12pro max yace “wannan kuma na sa miki sabon sim”2

Ameera wadda ta karbi wayoyin tana kallon shi tace “Yaya me zanyi da wayoyi har biyu? wallahi daya ma ta isa”

Ba tare da yayi responding to maganar da tayi ba ne yace “kinyi kyau sossai Habibty.. you are beautiful”

Duqar da kanta tayi tana murmushi tace “nagode Yaya..”

“again, this…” ya janyo kwalin Macbook pro (laptop) ya cigaba da fadin “…is yours too, tunda na cinye miki kudin ta lokacin da na kwanta a asibiti”

STORY CONTINUES BELOW

Cike da mamaki Ameera ta kalle shi yayinda tace “Ya Zayd???”

“what??”

“Ya akayi ka san kudin laptop…” ta dan yi shiru sannan ta miqe tsaye da sauri tace “wait, ka ji dukkanin abinda na fada a ranar???”

A yadda ta fadi maganar zaka rantse mutuwa zata yi idan yace ‘eh’

Shi kanshi ya dan cika da mamaki.. toh meye don ya ji?

“ofcourse I heard everything Habi..”

Gani nayi ta sa hannu a kai tace “inna lillahi wa’inna ilaihir raji’un.. Ya Zayd why???”

Daga nan ta fashe da kuka yayinda yayi saurin miqewa a rude ya janyo ta jikin shi yayi hugging dinta..

“Habibty why what?? meyasa kike kuka?? meye don na ji abinda..”

breaking hug din tayi yayinda ta janye daga gareshi tace “Ya Zayd dama ka aure ni ne don ka tausaya mun akan abinda na fada ranar ko kuwa ka aure ni ne saboda ka rama abinda Ya Layla tayi maka??? Ni dama fa na san ba sona kake ba, na sani cewar soyayya daya ce a duniya kuma ka ba Ya Layla.. it has always been about her, ko ranar da ka fara ganin mu you didn’t even look at me, it was just her.. why did you take advantage of me this way??”

Sautin kukan ta ne ya qaru yayinda Zayd yake kallonta confusedly.. it’s even as if bayada abinda zai ce mata!2

Da sauri ya riqo hannunta yayinda ta fizge tace “ni ka qyale ni.. wallahi da na san haka ne da ban amince na aure ka ba.. dama ni bana son irin wannan rayuwar..”

“Hey shut up… Me kika sani Ameera?? what do you know about what my heart wants? me kika sani akan abinda nake so?? You dont!”

Ajiyar zuciya ya saki sannan ya cigaba da fadin “please listen to me.. na sani cewar akwai abubuwa dayawa da yakamata inyi miki clarifying but how do you want me to justify all of my actions idan baki natsu kika saurare ni ba??”1

Ya dunqule hannunta cikin nashi yace “please Habibty ki zauna muyi magana.. duk abinda kike so ki ji zan fadi miki.. I promise to tell you everything..”

Ameera tana kuka ya janyo ta suka zauna yayinda ta sa mishi idanuwa.

“Yes it all started with Layla.. but believe me a ranar da na fara ganin ku tare I wished it started with YOU Ameera”

Ameera wadda take kallon shi cike da mamaki ce tayi freezing yayinda maganar shi ta taba zuciyarta.. me yake nufi???

“Ranar da na gan ku kun fito daga Cafè was not actually the first day da na fara ganin Layla.. it was almost five months before.. Ranar a Unguwar ku Malali, ina cikin mota tare da Bilal bayan mun duba wani gida da kamfani na yake ginawa na hango ta tare da qawayen ta.. Believe me, It wasn’t her beauty that captured my attention.. it was actually her action, wani abu tayi wanda I will forever respect her for that..”

Ameera wadda take kallon shi tuni jikinta yayi sanyi..

“I was going through some documents at the time sai na ji hayaniya.. ko da na dago kai sai ganin ta nayi ta kwashe wani mutum da mari yayinda ta nuna shi da yatsa tana masifa.. a gefenta na ga wata tsohuwa zaune a qasa tana riqe da qafan ta yayinda sauran qawayen ta suke dudduba lafiyar qafar.. Instantly na sa Bilal ya fita ya duba abinda yake faruwa.. he returned after a while ya fadi mun cewar mutumin ya bige tsohuwar da mashin dinshi ne shine Layla take yi mishi fada kuma a matsayin shi na mai laifi instead of apologizing sai yana qoqarin zagin tsohuwar and that was the reason why she slapped him.. Dayake mutane sun taru a wurin he couldn’t do anything to her and he had to apologize to the old woman..”

Zayd ya girgiza kai yana murmushi yace “her sense of humanity, compassion, courage and her self-confidence su suka birge ni.. and there, love at first sight happened. Instantly na sa Bilal yayi mun tracking dinta.. Na sa shi ya binciko mun komai about her…”

STORY CONTINUES BELOW

Ya dan yi shiru yana kallon Ameera wadda ita
ma shi take kallo.. Ganin yayi shiru ne tace “then??”

Murmushi yayi sannan yace “Ya binciko mun komai about your family and guess what..”

“what?”

“labarin ku da aka bani ne ya ruda ni.. what I expected to hear about Layla was what I heard about you and vice-versa… a wannan lokacin na sa a rai na an samu mix up ne a labarin and so I went ahead and fell deeply in love with her.. na so ìn hadu da Layla earlier than lokacin da na gan ku amma aiki yayi mun yawa, mostly ma bana qasar.. duk yawan aikin da nake yi a wannan lokacin I never forgot her.. A lokacin da na dan samu natsuwa ne nayi shirin zuwa wurinta don gabatar da kaina a matsayin masoyi. Zaheera told me ta fadi miki abinda ya faru tsakani na da Na’eema, I was in search of true love and so I had no choice but to hide my identity.. Ranar da na gan ku a gaban cafè, YOU, Ameera… you caught my attention, I was impressed by your mode of dressing and wallahi a wannan lokacin sai na ji dama Layla ce a irin wannan shigar.. Na qaraso wurin ku ba tare da na kalle ki ba saboda a wannan lokacin bana son abinda zai yi diverting attention dina daga kan wadda nake so.. Sallamar da nayi wadda ke ce kika amsa mun ita ta tsaya mun a rai Ameera, har na gama magana da Layla na tafi part of me was telling me cewar I was making a mistake toh amma the heart already wants what it wants right?”

Shafa kanshi yayi da hannuwan shi biyu sannan ya cigaba da fadin “…disguising myself was the most difficult thing I ever did in my life.. ban taba hawa mashin ba amma akan dole na koya.. har faduwa nayi akan shi but Allah ya taimaka ban ji ciwo ba.. Haka Bilal ya samu wani team suna yi mun make-up saboda dai in batar da Kamarni na, I knew what I felt for Layla amma kuma I was bad at expressing my feelings.. haka Bilal yake bani scripts na kalaman soyayya duk dai don saboda in samu soyayyar Layla.. again, lokutta da dama a dalilin ta nake barin Lagos ko Abuja just to come and see her.. all I wanted was for her to reciprocate my love amma ta qi.. she made it clear to me that all she wants is MONEY.. ta wulaqanta ni ta fadi mun munanan kalamai sannan ta kore ni..”

“do you still love her??” muryar Ameera tana rawa ta tambaye shi.

Wani irin kallo yayi mata sannan yace “hell no Habibty.. I dont love Layla, not anymore”

Shiru tayi bata ce komai ba..

“Baki yarda da ni ba ko???”

“Ya Zayd ka fadi mun gaskiya.. na sani cewar lokacin da ta kore ka har kwanciya ciwo kayi and you tell me you dont love her?”

Murmushi Zayd yayi yace “Layla was my first Love Ameera.. no matter how hard I try to deny it, I can’t.. I really loved her. A wannan lokacin zuciya ta ce tayi failing dina and I didn’t have control over it.. amma Wallahi yanzu bana son ta, ke kadai nake so..”

“Me zaka ce a game da suman da kayi a makarantar mu?? even after what she did to you fa komawa kayi wurinta sannan yanzu kace babu sonta a zuciyarka?? how do you expect me to believe this??” ta tambaye shi yayinda ta tsare shi da idanuwa.

Wani mahaukacin kishi ya hango a idanuwan ta..

Zayd dai bai san lokacin da ya fashe da dariya ba..

Shafa fuskar shi yayi da hannuwan shi biyu sannan yace “Zayd is in trouble today.. wannan interrogation din is getting so much intense..”2

Hannun ta ya riqo sannan yace “kamar yadda na fadi miki zuciyata ta kasa haqura da Layla, dukda ta kore ni I couldn’t just accept the fact. ke da kanki kin fadi mun cewar zuciyarki ta kasa haqura da ni dukda kin san cewar ni din saurayin Layla ne, you said har ki mutu soyayya ta tana cikin zuciyarki ko ba haka ba?” ya qarasa yana murmushi yayinda ya kashe mata ido daya.

Ameera wadda ta cika da kunya ta duqar da kanta a qasa yayinda ta ji ya cigaba da fadin “well that was it.. a ranar da na koma wurin Layla nayi niyyan fadi mata ko ni waye ne tunda dai kudi take so ni kuma ina sonta.. it will be a win-win situation for both of us.. Case dinta was different from Na’eema. Unlike Layla, Na’eema ta so ta kashe ni ne don ta gaji dukiya na.. I remember na roqi Layla akan ta bani few minutes of her time don muyi magana and she refused.. a wannan lokacin ne saurayinta ya zo suka wulaqanta ni and then..”2

STORY CONTINUES BELOW

Yayi shiru tare da runtse idanuwan shi ya bude yace “then I witnessed the most disgusting thing ever.. a gaba na cikin mota na ga Layla da saurayinta suna kissing juna..”

“Subhanalillah, what???” Ameera ta fada yayinda ta sa hannuwan ta guda biyu ta rufe bakinta saboda tsananin mamaki.

“Ya Laylar??” ya tambaya jiki a sanyaye

Tabbas ta san cewar Layla is loose amma bata taba sa ran tana aikata mugun aiki irin wannan ba.. who knows what else she does apart from that??

“I swear Habibty anan wurin na ji duk duniya babu macen da na tsana irin Layla.. a wannan spot din soyayyarta ta koma gagarumar qiyayya a cikin zuciyata.. Na suma ne saboda kai na da yayi mugun nauyi thinking about the worst mistake I would have made a rayuwa ta a wannan lokacin, Ameera I almost made a mistake of letting someone like her into my home.. da ace na fadi mata ko ni waye muka yi aure da shikenan..”

Da sauri Ameera ta riqo hannun shi tace “I am so sorry you had to go through all these Ya Zayd..”

Murmushi yayi yace “tanx Habibty, Ai gashi nan Allah ya musanya mun da ke..”

Ya qara matsowa daf da ita tare da dunqule hannuwanta cikin nashi ya kalle ta cikin ido yace “I swear Habibty ina son ki ba don tausayi ba, ina son ki ba don in rama abinda Layla tayi mun ba, ina son ki saboda kina sona tsakani da Allah, ina son ki saboda ina son halayyar ki, ina son ki saboda kina da riqon addini, ina bala’in son ki Ameera.. With you, I found true love. Ni naki ne don haka duk abinda kike so shi zanyi miki… You deserve everything good in this life my Habibty”4

Wani mugun farin ciki ne ya kamata a dalilin jin wannan kalaman nashi.. Babu abinda take yi sai gode ma Allah da ya cika mata burinta a duniyan nan.. ya bata Zayd a matsayin mijinta. Insha Allah zata kula da shi fiye da yadda zata kula da kanta don kuwa she considers him a very important person in her life!2

“I love you Ya Zayd.. I love you very much.. nagode da ka bani soyayyarka, it’s all i want a rayuwar nan, i will forever be grateful for..”

“are you sure soyayya ta kadai kike so a rayuwar nan??” ya tambayeta yana murmushi.

Cike da confusion tace “ban gane ba.. kana nufin nima..”

“sssshhhhh”

Yatsar shi ya dora bisa lips dinta wanda ya sanya tayi shiru tana kallon shi.

“Na sani cewar kina son kulawa ta Habibty.. kin sani cewar I am a busy person and I travel alot shiyasa baki so kika aure ni ba.. ko ba haka ba??”

Murmushi tayi tace “haka ne Ya Zayd amma kuma ai ba komai da mutum yake so bane yake samu.. I guess I will have to deal with that”

“hell no My Habibty, kulawar da kike nema zaki samu 100% I promise you, kin fi komai muhimmanci a rayuwa ta.. A yau idan kin ce kar in qara fita wallahi bazan qara ba.. Your every wish will be my command”

Kafin ya qarasa maganar shi ne ta fashe da dariya tace “a’a wallahi, I am not that selfish da har zan hana ka fita Ya Zayd kuma nagode sossai da..”

Bai bari ta qarasa maganar ta ba ya miqe tare da riqo hannunta yace “tsakani na da ke babu godiya Habibty, zo mu je inyi miki wani desert mai dadi.. I am sure you will like it”

A haka ya ja ta har zuwa kicin.. ita dai Ameera har yau bata saba da gidan ba, har yau sai ta ga wani sabon abun da bata taba gani ba. Ta tabbatar sai ta kwana biyu sannan zata gane kan gidan don kuwa idan aka barta ita daya ma zata iya bacewa..

Zaunar da ita yayi kan kujerar Island yayinda ya fara hada mata French apple desert..

Yana yi suna ta
hira.. Ko da ya dauko apples sai da ta ci guda biyu..

her favorite fruit!

Ta tambaye shi if she could help amma yace he got everything under control. Dama dai itama ta tambaye shi ne kawai amma ba don ta tabbatar akwai abinda zata iya taimaka mishi da shi din bane..

Ameera dai ta kasa gane komai a kicin din.. na’urori ne kala kala a ciki wanda ta kasa gane ko meye su balle ta san amfanin su.. tambaya ita ce- shin ta ya zata yi girki a cikin wannan kicin din?? A yadda take zaune ma ko Gas cooker baya gama gane ya take ba balle sauran abubuwa..

Akwai aiki a gabanta!

Bata ankara ba ta ga wani dan qaramin bowl na wani French apple desert a gaban ta tare da cutlery neatly arranged beside it..

Zama yayi ba tare da yace komai ba ya dauki fork ya diba sannan ya kai saitin bakinta.. tana kallonshi ta bude ya sa mata.

Lumshe idanuwa tayi yayinda take jin dadin desert din..

“Ya Salam.. Ya Zayd ina son wannan abun sossai..”

Yana dariya yace “Na san zaki so shi Habibty especially because APPLE is involved..”

A haka ya cigaba da bata a baki yayinda shima yake ci.. suna ta hira kala-kala..

Zayd da Ameera ko da suka shanye desert din basu tashi ba.. Hira sossai suke yi.. da alama dai they are trying to know the rest of the things da basu sani ba a game da juna!

Sai wuraren qarfe daya da rabi na dare ne suka ankara da cewar dare tayi sossai don haka ne ya raka ta har dakinta sannan suka yi ma juna good night ya tafi nashi dakin..Washegari!!

ZAYD AHMAD FADOUL’S RESIDENCE

UNGUWAN RIMI GRA+

Kwance take a cikin Duvet a kan lafiyayyen gadon dakinta wuraren qarfe goma na safe tana ta bacci yayinda yake zaune a kan gadon yana kallon ta.

Zayd yayi kusan minti ashirin da shigowa dakin.. Ganin tana bacci ne ya zauna yana ta kallonta kamar yana kallon TV.

Motsawa tayi yayinda tayi saurin bude idanuwan ta a dalilin qamshin turaren shi da ta ji..

“Ya Zayd, me kake yi anan??” ta fada tare da tashi zaune.

“Na zo ne in kira ki mu je muyi breakfast sai na ga kina bacci shine na zauna ina jira ki tashi..” ya fada yana murmushi.

“what? you mean zaune kake kana jira in tashi?? Haba dai Ya Zayd.. You should have woke me up ai.. who am I to keep you waiting??”

“MY QUEEN.. you are my queen Habibty. I can wait for you for as long as possible.. Kallon ki yana sa ni nishadi. I love you sooo much”

Murmushin jin dadi tayi yayinda tace “I love you too Handsome”

Daga kai tayi ta kalli agogo tana fadin “qarfe nawa..” bata qarasa ba ta zaro idanuwa sannan tace “Yaaya its past 10??? shine nake ta bacci ban..”

“Sssshhhh.. relax, ko kin tashi da wuri babu abinda zan bari kiyi… it’s cool Habibty”

Ya sauka daga kan gadon ya cigaba da fadin “Yanzu dai bari in hada miki ruwa kiyi wanka..”

Kafin tayi magana har ya wuce bathroom din ya barta sake da baki tana mamaki.. Ya hada mata breakfast sannan zai hada mata ruwan wanka? duk wannan fa ita yakamata tayi.. meyasa shine yake yi mata??2

Tana cikin wannan tunanin ne ya fito tare da fadin “toh bisimillah Habibty..”

Ameera wadda ta sauka daga kan gadon gani tayi ya tsaya.. da alama baya da niyyan fita.

“toh ka tafi..”

“meyasa zan tafi?? jira nake yi ki ce in zo inyi miki…”3

“what???” ta fada cike da mamaki tare da zaro mishi idanuwa..

Zayd dai fashewa yayi da dariya yace “Habibty ni fa mijinki ne.. duk abinda kike boyewa zan gani.. toh meye don na gani yanzu??”2

Saboda tsananin kunya gani nayi ta juya ta koma kan gadonta ta kwanta tare da shigewa duvet.

Yana dariya yace “like seriously?? toh shikenan.. na tafi, idan kin gama ina jiran ki a dinning”

Bata sauka daga kan gadon ba sai da ta ji motsin fitan shi.

Ko da ta shiga bathroom din everything was neatly set up for her.. ruwan da ya tara mata a jaccuzzi bath din sai qamshi yake yi na turarukan wanka.. Ameera dai saboda dadin ruwan da ta ji sai da tayi kusan minti talatin sannan ta fito.

☆☆☆☆☆☆☆☆☆

Zaune yake a daya daga cikin kujerun qayataccen dinning room din.. Macbook dinshi ce a gaban shi sai tea cup a gefe.. Ga breakfast din da ya hada neatly arranged a kan table din.

Zayd yayi nisa a aikin da yake yi ne ya jiyo qamshin turaren ta a kusa da shi.. nan da nan ya dago kai ya kalle ta yana murmushi.

“Ina ta sallama baka amsa ba..” ta fada tare da turo mishi baki.

STORY CONTINUES BELOW

“yi haquri Habibty, I was so carried away ne..”

Da sauri ya miqe tsaye ya ja mata kujerar da take kusa da tashi yace “sit”

Maimakon ta zauna sai gani yayi ta sa hannu ta janye Macbook dinshi da wayoyin shi ta mayar a rear-end na table din sannan ta dawo tace “komai yana da lokacin shi.. it’s time for breakfast yanzu”

Murmushi yayi yace “yes my queen.. kin yi kyau sossai.. wannan atamfar tayi miki kyau”

Ameera dai sanye take cikin atamfarta ta qaramar super wadda Abban su ya dinka musu da Sallah.. dinkin skirt ne da riga mai peplum.. sossai dinkin ya dace da dan jikinta.. bata daura dan kwalin atamfar ba sai ta yafa dan qaramin gyale a kanta.

“nagode Ya Zayd..” ta fada cike da murna.

Allah ya sani tana so ta ji yace mata tayi kyau.. wani mugun farin ciki ne yake samun ta.

Ko da suka zauna shine ya zuba musu abincin a cikin plate daya, as usual abinci ne ya dafa kala-kala. ita dai Ameera ci kawai take yi amma bata san sunayen su ba.. sossai girkin Zayd yake yi mata dadi.. ba don shi din mijinta bane amma tabbas nashi ya fi na Ammi dadi.

Masha Allah..

Bayan sun kammala ne suka tattara dishes din suka kai kicin.. Ameera har ta fara shirin yin wanke-wanke ne ya dakatar da ita tare da janyo hannunta suka nufi wani bangare na kicin din ya danna wani button sannan ya kalle ta yace “masu aiki zasu zo su wanke.. suna nan a quarters dinsu.. duk lokacin da kike buqatar su just press this and they will be here in no time”

Aikuwa nan da nan suka shigo cikin sallama ta qofar baya.. ita dai Ameera ta ga har mutum biyar.. Gwiwowin su a qasa suka gaishe su..

A nan dai Zayd yayi introduction din yakamata.. Daga nan ya ja matar shi suka fita su kuma suka duqufa aikin su.

☆☆☆☆☆☆

Zayd yana riqe da hannun Ameera zasu nufi sashen ta ne na ji yace “mu je ki hada kayan ki na kwana biyu zamu je Lagos yanzun nan”

“what?? ban gane Lagos ba Ya Zayd.. me zamu je yi a Lagos??” ta tambaye shi cike da mamaki

A daidai lokacin suka qaraso dakinta.

Ko da suka shiga zaunar da ita yayi a kan kujera sannan ya tsugunna a gaban ta yana fuskantar ta yace “kin manta ina da company a Lagos? the thing is I have a meeting sannan akwai wasu ayyuka da zan yi.. ina so mu tafi tare ne don bana son barin ki ke kadai kuma…”

Yatsarta ta dora akan lips dinshi tare da fadin “sssshhhh.. you are doing this because you want to show me how very much you care about me ko?? it’s okay.. abubuwan da kayi mun a yau dinnan ma sun tabbatar mun don haka kar ka damu just go.. ina nan ina jiran ka”3

“but..”

“but nothing Ya Zayd.. I will be fine. Ka san fa akwai mutane da zasu dinga zuwa.. tunda anyi bikin namu babu wani taro.. ka ga gwara in zauna saboda su ko??”

ita dai Ameera ta fadi mishi haka ne ba don dagaske haka din bane.. ta fadi ne don bata so ta bi shi.. ita dama asali irin abubuwan da bata so kenan shiyasa tun farko bata son auren rich and powerful person kamar Zayd… People like t
hem tend to be public figures!2

“toh zaki iya kwana ke kadai?? ko in kira Umma ta turo su Aliyu su zauna tare da ke before I return??”

Cike da murna tace “perfect Ya Zayd”

Hannunta ya riqo yace “come”

Ameera ta miqe suka nufi dressing room dinta wurin wani bango na glass.. tun jiya ta ga wurin sannan ta kula akwai wani button a jiki yana blinking..

STORY CONTINUES BELOW

Gani nayi ya danna button din yayinda wasu rubuce-rubuce suka bayyana akan glass din ko da na duba lambobi ne suka bayyana yayinda na ji yace “Habibty press 2112”

Ameera wadda bata san ko meye ba dai ta kai hannunta ta danna.. aikuwa tana dannewa glass din ya bude yayinda na ga Ameera ta zabura harda matsawa baya da sauri..

Zayd ne yayi saurin cafko ta ya dawo da ita gaban shi tare da dafa kafadun ta don kar ta gudu..

Hannuwan Ameera a bisa bakinta with her eyes wide open yayinda ta cika da tsananin mamaki..

Safe na kudi ta gani.. kudin ma ba ‘yan kadan ba, kudi masu yawan gaske.. Ko da wasa Ameera bata taba sa ran zata ga kudi masu yawan ko da rabin wannan ba..

“wannan duka naki ne Habibty.. na kashewa at any time…”

“Inna lillahi wa’inna ilaihir raji’un… Ya Zayd??”

“listen to me Habibty.. a duk lokacin da kike buqatar kudi, duk abinda kike so kiyi da su, ko wa kike so ki ba just go ahead.. kar ki damu da tunanin ko zasu qare.. idan sun qare zan zuba miki wasu.. don Allah kiyi amfani da su.. idan na dawo accountant dina zai bude miki bank account so I can be saving money for you there..”

Magana yake yi amma sam hankalin Ameera baya tare da ita.. ita ta sani cewar Zayd yana da kudi sossai amma bata taba sa ran haka ba.. a yanzu haka dukda bata iya lissafi ba kudaden da take kallo zasu kai miliyan hamsin.. ita kuwa me zata yi da kudi haka da har zata qarar da su sannan kuma wai zai zuba mata wasu a account.. ai this is not what she signed for!

Wayar shi ce da tayi ringing yayi saurin fiddowa daga aljihun shi.

Bilal ne!!

“hey I am coming.. ka bani minti sha biyar” ya fada sannan ya kashe.

“Habibty zo mu je ki raka ni in shirya.. ko kayana ban hada ba kuma ana jira na”

Ameera dai gaba daya ta zama speechless.. Zayd ya sani sarai bata fita daga shock na abinda ta gani ba toh amma ya zai yi da ita? the earlier she gets use to this kind of life the better..

Dakin Zayd da suka shiga sossai yayi mata kyau.. infact sashen shi ya fi ko’ina da ta gani so far kyau a gidan… dressing room dinshi kamar wani boutique..

Haka ya fara hada kayan shi ba tare da ya bar Ameera ta taimaka mishi ba.. Asali ma wuri ya bata ta zauna yayinda ta sa mishi idanuwa.

Allah ya sani Zayd yana birge ta.. gashi kyakyawa sannan komai nashi mai kyau.

Bayan ya gama hada kayan ne ya janyo ta suka koma dakin shi..

A nan ma zama tayi kan gadon shi tana ta qare ma dakin kallo yayinda yake kwashe wasu files wadanda zai yi tafiyar da su.

“Ya Zayd kayi mun wayau.. dakin ka ya fi nawa kyau”

“ba dakina bane Habibty, dakin mu ne da ni da ke… idan na dawo daga Lagos nan zaki dawo mu dinga bacci tare. Kin dai san haka yakamata ko?” ya fada ba tare da ya kalle ta ba.2

Ameera dai ta gane me yake nufi.. he is trying to tell her cewar ta shirya idan ya dawo they will consummate their marriage.

Shiru tayi ba tare da tace komai ba.. da alama ma tayi da-na-sanin yin maganar da tayi.2

Shi dai Zayd murmushi kawai yayi yana mamakin kunya irin ta Ameera..

**********

Har parking lot ta raka shi sannan tayi mishi addu’a.

Yayi mata alqawarin kiran ta a waya a duk lokacin da yake less busy..

Haka ya tafi suna kewar juna.. Just one day together amma suna ji kamar sun shekara tare.. Nothing physical has happened between them amma the conversations they’ve had were beautiful..

STORY CONTINUES BELOW

Ita dai Ameera ta tabbatar ita take mulki a birnin zuciyarshi, she’s got her assurance cewar yana sonta don haka ta gama samun komai a duniya

☆☆☆☆☆☆

GIDAN MALAM FAROUQ ABDALLAH

MALALI

A yau din dai tun da safe Zayd ya turo driver ya tafi da su Anty Khadeeja Airport..

Ya bada kudade masu yawan gaske a basu yayinda suka dinga godiya.. Abba dai ya ma rasa bakin magana.

Ya kira shi a waya yayi mishi godiya, shi dai Zayd baya son yawan godiya akan abun alkhairi da yake yi.. if only they know how very much he wants to get rid of his money ta hanyar taimako!!

A yanzu haka akwai abubuwa dayawa da yake so yayi ma Abba da dangin shi gaba daya amma kuma ya dan bada space ne for now saboda ya san Abban baya so.. but tuni ya riga ya gama tsara komai.. there is no way he is gonna leave his in-laws living such kinda life.

Da kyau dan arziki!

************

Wuraren qarfe Goma sha daya na safe Mama da Layla suna zaune a dakin Maman tare da Hajiya Suwaiba wadda ya dawo daga Hadeja.

Kallo daya zaka yi ma Layla ka gane tana cikin damuwa.. har ta rame saboda tsananin tashin hankali da take ciki.

“ashe yau din kika dawo???” Mama ta tambayi Hajiya Suwaiba

“wallahi kuwa Hajiya Hindatu.. ai in gaya miki maganar gaskiya mutane suna fama da matsaloli a rayuwar nan.. idan kika ga yawan mutane da suke jiran ganin malam sai kin riqe baki..”4

Ita dai Layla duk wannan ba shi bane damuwarta.. progress report kawai take sauraro.

“Ikon Allah, toh yanzu mun dace dai ko??”

Hajiya Suwaiba tana murmushi ta janyo Jakarta ta bude tare da fitar da wani kwalli tace “ina kyautata zaton hakan Hajiya Hindatu.. kin ga wannan?” ta miqa ma Layla kwallin sannan ta cigaba da fadin “da zarar kin ambaci sunan yaron sau uku sanna kika shafa kwallin kiyi qoqari ki hada ido da shi.. ina mai tabbatar miki shikenan”

Layla wadda ta ji wani mugun dadi tana murmushi tace “dagaske Hajiya?”

Hajiya Suwaiba tayi dariya sannan tace “ai malamina baya wasa da aikin shi..”

Ta kalli Mama wadda take murmushi tace “sai dai akwai ‘yar matsala kadan…”

“matsalar mene Hajiya Suwaiba??”

“aikuwa kudin nan basu isa ba.. dayake akwai kudin sarqar Hajiya Barira a hannu na shine na ba malamin in ya so yanzu da na dawo sai ki bani. Babu yadda ban yi ba da malamin akan in aiko mishi kudin daga baya amma ya qi..”3

“ai babu damuwa Hajiya.. ni kam tunda an samu yadda za’a yi ai shikenan… nawa ne cikon??

“dubu dari uku da hamsin ne..”3

“toh bari in dauko..”

Hajiya Suwaiba dai tana kallo ta ga Mama ta nufi wadrobe din da take ajiyar Ghana must go din kudi ta fiddo sannan ta zaro dubu dari uku da hamsin.. Wannan abu dai sai mamaki yake bata.. wato kudi ke da akwai masu yawa a cikin jakar.

Layla wadda take cike da murna ce tace “aikuwa nagode sossai Hajiya, ina mai tabbatar miki idan na zama matar Zayd bazan manta da ke ba”

Hajiya Suwaiba ta washe baki tace “da kyau ‘yar albarka.. ai da zarar kinyi yadda aka ce shikenan, tuni zai sako ita matar tashi sannan ya aure ki”

Mama ta miqa ma Hajiya Suwaiba kudin sannan ta zauna tace “yanzu dai bari wannan aikin ya yiwu sai mu koma kan waccan maganar.. ko ya kika ce??”

“aikuwa hakan za’a yi Hajiya Hindatu” ta fada yayinda ta zuba kudaden cikin jaka.

A haka dai suka cigaba da hirarakin su wanda yawanci duk gulma ce ta qawayen su.. ita kuwa Layla miqewa tayi ta nufi dakin ta riqe da kwallin ta cike da murna.

Nan da nan ta wuce bathroom don yin
wanka.. ta shirya zuwa kamfanin Zayd a yanzu, ta qudurta a ranta lallai yau dinnan Zayd zai zama nata!4

Abinda bata sani ba shine Zayd dai yana can cikin jirgi zuwa Lagos!!ZAYD AHMAD FADOUL RESIDENCE

UNGUWAN RIMI GRA+

Zaune suke a falonta suna hira da qawarta Zarah..

Duka awa biyu kenan da Zayd ya tafi Lagos wanda jet dinshi na sauka ko fitowa bai yi ba ya kira ta a waya.

Yau din ita ce rana ta farko da suka samu zama bayan bikin ta.

“don Allah qawata kiyi haquri.. ni kam ba komai ya wuce ba yanzu??” Zarah ta fada cikin muryar roqo.

“eh komai ya wuce amma ai raina mun wayau kuka yi.. tell me something, since when have you known?” Ameera ta tambaye ta yayinda ta sa mata idanuwa.

Zarah tana murmushi tace “wallahi tun ranar da yayi proposing miki..”

“what??? you mean tun ranar Zarah?? and you didnt tell me?”

“Haba qawa ta.. da bakin ki fa kika fadi mun cewar bakya son auren mai arziki.. mun ji tsoro ne kar ki qi amincewa da shi..”

“aikuwa kun yi playing dina.. Ni kam I am glad na zama matar Ya Zayd kuma ya bani assurance din da nake nema… Kin ga dazu fa da zai tafi ya so mu je tare amma na qi..”

“what??? kenan kin gwammace ki zauna a nan shi kuma yana can??”

Shiru Ameera tayi yayinda take tunani.. ita kanta fa sai da ya tafi ta ji dama ta bi shi, Sossai tayi missing dinshi musamman da ta gan shi ta video call.

“Ke qawata, saurare ni ki ji.. a duk lokacin da zai yi tafiya ya nemi ku je tare please follow him.. ke close marking sossai yakamata ki dinga bashi.. duk wata kunya fa a yanzu ajiye ta zakiyi a gefe.. wannan soyayyar da kike yi mishi ita ce zaki zage ki nuna mishi.. yanzu da kika zauna a nan me kike yi? ke ba makaranta kike zuwa ba.. kina nan zaune a gida” ta harare ta sannan ta cigaba da fadin “ko dayake ba laifin ki bane.. baki shiga sahun matan aure bane tukun shiyasa.. da kin dandana wannan rayuwar wallahi na tabbatar maqale mishi zakiyi kamar chewing gum”2

Ameera wadda take kallon Zarah with a straight face ce tace “toh yanzu dai the damage has been done.. zan kiyaye gaba”

“yauwa qawa ta.. yanzu ma bata baci ba, Bari in kira miki wata mai gyaran jiki ta zo ta shirya ki kafin ya dawo jibin.. tunda dama ba’a kammala wancan ba kika samu accident din da har kika kwanta jinya.. ko baki so??”

“ina so qawa ta..” Ameera ta fada kai tsaye yayinda Zarah ta fashe da dariya tace “da kyau juliet.. na ga alama Yayana will be in trouble kenan”

Ameera tana dariya tace “ke toh son shi nake..”2

“na fi kowa sanin haka”

Aikuwa anan Zarah ta kira Aina’u Marwan.. wata shaharariyar mai gyaran jiki ce wadda tayi fice a garin Kaduna.. dayake harka ce ta kudi nan da nan ta nemi address sannan tace tana nan zuwa in the next 3 hours.

Bayan ta kashe wayar ne tayi ma Ameera bayani.

“nagode qawa ta” Ameera ta fada

“Meye abun godiya Ameera?? we are like sisters remember??”

Kafin Ameera tayi magana ne Zarah tace “ni kuwa ban tambaye ki ba.. ya labarin Layla??”

Ameera ta turo baki tace “toh wa ya sani.. jiya da muka je gida na ganta.. ko magana batayi mana ba ta wuce daki and daga nan bata qara fitowa ba.. I swear qawata tun ranar da tayi threatening zata kashe ni saboda Ya Zayd har yanzu tsoron ta nake ji.. tunda tana da saurayinta mai kudi ta haqura mana..”

STORY CONTINUES BELOW

Zarah tana dariya tace “tabbas saurayinta yana da arziki a inda babu masu arziki kenan.. ai sawun giwa ya taka na raqumi Ameera. Allah dai ya qara mata.. ba dai kwadayi da son abun duniya ta sa a gaba ba?? she never see anything..”

“Yauwa qawa ta.. don Allah zo mu je ki taimaka mun” Ameera ta fada yayinda ta janyo Zarah.

“with what???” Zarah ta tambaye ta yayinda take biye da ita.

“wallahi babu abinda na iya amfani da shi a kicin.. kin San qawar ki baqauya ce.. please come and help me explain some things don wallahi jiya da muka shiga tare da shi har ya gama hada mana desert ban fahimci komai ba a ciki..”

Zarah tana dariya tace “mu je in nuna miki qawata.. dukda ba wani barin ki zai dinga yi kina shiga kicin din ba don kuwa ya dade yana fadi cewar a fanin girki tabbas matar shi zata huta.. but amma ko don lokaci irin wannan idan yayi tafiya yakamata ki koya..”

“ai daga yau ma bazan qara barin shi ya tafi ya bar ni ba.. na dauki shawara qawata”2

Zarah ta fashe da dariya yayinda suka nufi kicin din inda ta shiga yi ma Ameera bayanin komai.

☆☆☆☆☆☆☆☆☆

Cikin qanqanin lokaci dai Ameera ta haddace komai na kicin din gidan nata.. dama dai kun san Ameera da qwalwa, kawai dai rashin sanin abubuwan ne. Hatta wasu ‘yan continental dishes Zarah ta koya mata.. wasu ta dan rubuta su yayinda Zarah tayi mata alqawarin kawo mata recipe book dinta.

Aina’u Marwan ma dai kamar yadda tayi musu alqawarin zuwa, ta zo din. Tuni ta fara aikinta a kan Ameera.. turarruka masu qamshin bala’i na wanka, na gashi da na shafawa a jiki. Nan da nan Ameera ta fara zabga qamshi.. Da zata tafi ne ta bata wasu sannan ta gwada mata yadda zata yi amfani da su.. sunyi Akan zata dawo washegari.

A bangaren Layla kuwa ko da ta shirya ta shafa kwalli kamar dai yadda aka umurceta kai tsaye City-shelters ta nufa amma bata samu ganin Zayd ba.. ko da suka ce mata yayi tafiya qaryata su tayi don kuwa bata ji labarin zasu yi tafiya shi da Ameera ba a gida tunda dai they are newly wedded and she is sure he wont travel without his wife.. tunaninta dai lallai sun boye mata ne.. Haka ta qarashi zaman jiran shi har ta gaji ta wuce gida da niyyan dawowa washegari.5

Sossai ranta ya baci, tana tafe tana zage-zage.

Ammi kuwa ta ji labarin Zayd yayi tafiya ya bar Ameera a gida wanda ta kira shi a waya ta dinga yi mishi fada.. haka ya dinga bata haquri tare da yi mata bayanin yadda ya dinga insisting su je tare amma ta qi.. da wannan dai ya fahimtar da ita sannan ta sassauta mishi.

Su Maheera kuwa motsi kadan sai sun kira Ameera ta video call.. Su kam Allah ya sani suna son Ameera!

Kamar dai yadda Zayd yayi ma Ameera alqawarin zai nemi alfarma a wurin Umma ta bar su Aliyu su je su zauna da ita kafin ya dawo, haka aka yi..

Sossai sukayi murna jin an ce zasu je gidan Ameera..

Su Ibrahim ma ko sallama basuyi ma Mama ba suka tafi, sun sani sarai idan suka fadi mata zasu je gidan Ameera tana iya hana su.. sun gwammace idan sun dawo tayi ta jibgan su.

Abinda basu sani ba shine duk wadannan abubuwan basu gaban Mama a halin da ake ciki.. tana can ta fara tsara irin facaka da zasu yi cikin naira ita da ‘yar ta idan Zayd ya zo hannun su.

Aikuwa da yamma driver ya je ya dauko su.

Da daddare Ameera ta dafa musu abinci mai dadi suka ci sannan suka zauna a falonta suka shiga kallon Indian film wanda suna kallo suna hira.

Aikuwa ko minti Goma sha biyar basu yi ba da fara kallon Zayd ya kira ta a waya yayinda tayi excusing kanta.. tun su Ibrahim suna sa ran zata dawo har suka cire..

STORY CONTINUES BELOW

Ameerar ku dai tana can suna ta kwasan soyayya da Romeo din nata…2

☆☆☆☆☆☆☆

A yau ne Zayd zai dawo.. Tun da Ameera ta tashi daga bacci take cike da farin ciki marar misaltuwa.

Tun shekaran jiya da ya tafi har zuwa jiya da daddare sunyi waya ya fi a qirga.. Kai da safen nan ma wayar shi ce ta tashe ta daga bacci inda ya sanar da ita suna shirin barin Lagos.

Dukda gaba daya jiyan he was very busy with meetings tun safe har yamma, he still created time at intervals to call her..

Bayan sun gama breakfast da qannen nata ne ta wuce sashenta
don yin wanka ta shirya tarban mijin nata.

Ko da ta shiga wanka tayi amfani da turarukan da Aina’u Marwan ta bata.. nan da nan kuwa qamshi ya dinga tashi..

Bayan ta fito ta zauna a gaban Vanity mirror nan ma mayyukan Aina’un dai ta shafa.

Dayake tun jiya ta tsefe kitson kanta ta wanke gashinta, a yanzu cikin man gashin da Aina’u ta bata ta shafa sannan ta taje shi ta daure da hair band.

Ji nayi tace “Dole ne in Kira Hannatu ta zo tayi mun kitso don kuwa shine rufin asiri na”

Ko da ta shiga dressing room bayan ta sanya inner wears dinta ta dade tsaye gaban wadrobe tana tunanin kayan da zata sa.

A qarshe dai wata material gown ta janyo mai masifar kyau.. Ko da ta sanya ta sossai tayi mata kyau kamar dama don jikinta aka qera gown din.

Fitowa tayi riqe da dan qaramin gyale matching color..

Gaban Vanity mirror ta koma ta fesa turarruka sannan ta qara kallon kanta a madubi tayi murmushi sannan ta juya ta fita.

Su Ibrahim wadanda suke zaune a first sitting room na gidan ne suka ga shigowar Ameera…

“wow.. Ya Ameera kin yi kyau” cewar Suleiman

Munnir ne yace “sai qamshi kike ta yi..”

tana murmushi tace “nagode qani na”

Ibrahim ne yace “black is indeed beautiful.. dagaske idan na tashi aure baqar mace zan dauko ba irin kalar Ya Layla ba wadda da ta dan sha wahala sai tayi ja..”2

Gaba daya suka fashe da dariya yayinda Ameera tace “ni dai babu ruwana..”

Suna cikin hira ne suka jiyo hayaniyar masu aikin gidan..

Aliyu ne ya miqe yace “bari in duba..”

Ameera wadda ta miqe da sauri tace “kar ka damu bari in duba.. I think its Ya Zayd”

Ko kafin ta iso wurin main door na gidan ne ta ji qarar doorbell… da sauri ta qarasa ta bude qofar suka yi ido hudu da shi..

Wani sanyi ya ratsa zuciyoyin su yayinda suke ma juna murmushi..

Sanye yake cikin wandon sweat da polo T-shirt.. yana rataye da jakar Macbook dinshi yayinda Bilal yake tsaye a bayan shi da trolley dinshi.. Dukda he looked exhausted sossai yayi kyau..

Ware hannun shi yayi yayinda ta ruga a guje ta shige jikin shi tare da rungume shi da qarfin gaske..

“Sannu da zuwa, wallahi I missed you”

Yana murmushi yace “me too.. bazan qara tafiya ba tare da ke ba Habibty”

Tana murmushi tace “nima bazan bari ka tafi ba tare da ni ba Ya Zayd”

“kin yi kyau sossai..”

“nagode Yaya”

Bilal wanda yake tsaye yana kallon su sai murmushi yake yi yana mamakin yadda suke fadin sunyi missing juna when tunda ya bar garin nan kullum suna maqale a waya except lokuttan da yake meeting..

STORY CONTINUES BELOW

Gyaran murya yayi sannan yace “Madam ina kwana”

Sai a lokacin ta tuna cewar Bilal yana wurin.. da sauri yayi breaking hug din yayinda ta bi ta rude.. Da qyar ta saita murya tace “lafiya lau.. kun dawo lafiya??”

“lafiya”

Ameera dai juyawa tayi zata koma ciki yayinda Zayd yayi saurin janyo ta jikin shi… da alama baya so tayi nisa da shi.

“Bilal kayi qoqari ka huta a gida.. you should take the whole of tomorrow please..” Zayd ya fadi mishi tare da jaddadawa.

“Okay Sir, thank you”

Gani nayi Bilal ya turo ma Ameera trolley wanda har ta miqa hannu zata ja Zayd yayi sauri ya riqe tare da fadin “I got this”

Bilal yayi ma Ameera sallama sannan ya wuce yayinda suka shiga ciki.

Su Ibrahim wadanda suke zaune a falo ne suka miqe tsaye suka yi mishi sannu da zuwa cike da girmamawa.. cikin fara’a ya amsa wanda tuni Munnir ya qarasa wurin shi zai karbi trolley din hannun shi yace “dont worry qani na… Yanzu dai bari in je in dan huta sai in zo muyi hira ko?”

Cike da murna suka ce “toh Ya Zayd”

Su kam Allah ya sani tun asali suna son Zayd… yanzu haka da yace musu zai zo suyi hira sossai suka ji dadi!

Janyo Ameera yayi suka haura sama zuwa sashen shi.

Suna shiga dakin shi na ga yayi saurin sakin trolley din tare da jefar da jakar Macbook din shi sannan ya janyo Ameera ya rungume ta very tight tare da sakin ajiyar zuciya.

“I love you Habibty” Ya fada muryar shi qasa-qasa.

Ita dai Ameera a duk lokacin da ta ji Zayd ya furta mata wadannan kalaman ji take yi kamar an sanya ta a aljannah.. wani mugun dadi yake ratsa ta.

“I love you too.. very much Yaya.”

Qara matse ta yayi yayinda yake ta shaqar qamshinta mai dadin gaske.. da alama dai turarukan Aina’u Marwan suna aikin su.

Tuni ya zare gyalen da ta yafa ya jefar yayinda yake shafa gashin kanta wanda ta daure shi a tsakiyan kanta.

Zuciyar Ameera sai bugawa take yi yayinda take jin wani sanyi yana ratsa ta.. gaba daya ta shiga wani yanayi a dalilin yadda yake ta shaqar qamshinta yayinda yake goge fuskar shi a gefen fuskarta da wuyanta.. Sai sakin numfashi take yi yayinda take ta lumshe idanuwa..

“Habibty ina daf da in daina zuwa ko ina..”

Ameera wadda take murmushi tace “why is that Yaaya??”

“Because of you.. I just want to be around you every single moment”

Fashewa tayi da dariya cike da murna tace “me too Yaaya..”

Wasa wasa dai sai da suka yi kusan minti Goma maqale da juna sannan ya haqura ya qyale ta amma fa ya qi sakin hannunta..

Bakin gadon shi ya ja ta suka zauna yayinda ya janyo pillow ya kwanta yana kallonta.

Ameera wadda take kallon shi ta ga muguwar gajiya a tare da shi.. idanuwan shi sun nuna alamun bai ma samu wani isashen bacci ba..

“Yaya na ga kamar ka gaji sossai ko??”

“sossai Habibty..”

Miqewa tayi tace “bari in hada maka ruwa sai kayi wanka.. idan kayi breakfast sai ka kwanta kayi bacci ka huta ka ji?”

Girgiza mata kai yayi kamar yadda yara suke yi yayinda tayi murmushi ta wuce bathroom dinshi.. shi kuma ya bi ta da idanuwa.

Ameera dai ko da ta hada mishi ruwan wanka a jaccuzzi bath ta zuba mishi turarukan wanka ta shirya mishi duk wani abinda zai buqata ta fito..

STORY CONTINUES BELOW

Gani nayi ta tsaya turus a dalilin ganin Zayd kwance yana bacci.. da alama ma yayi nisa.

Girgiza kai tayi tace “Allah sarki, bawan Allah ya gaji”

Wurin switch na AC ta nufa ta kunna sannan ta koma wurin shi ta janyo Duvet ta rufa mishi halfway sannan ta juya ta fita.

☆☆☆☆☆☆☆☆

Wasa-wasa dai yinin yau din Zayd yana ta bacci.. ko da ya tashi yayi wanka yayi sallah da Ameera ta tambaye shi abinci sai cewa yayi anjima zai ci.. daga nan ya koma bacci.

Ita dai duk a tunanin ta gajiya ce kuma tunda this is the first time she is seeing his mood this way sai tayi tunanin haka yake yi idan ya gaji..

Bayan sallan la’asar ne ta dage mishi akan sai ya ci abinci.. akan dole ta ja shi dinning suka zauna.. Zayd dai bai yi niyyan ci dayawa ba amma a dalilin dadin da abincinta yayi mishi ne ya ci dayawa.. Yana ci yana yabawa yana santi, ita kuwa har cikin ranta ta ji dadi domin kuwa bata sa ran zai yi mishi dadi ba considering how very good he is a wurin girki.

Bayan ya kammala ne ya sa ta kira mishi su Ibrahim suka zauna a falon shi.. Yana kwance a kan 3-seater kujera yayinda suke zazzaune suna ta yi mishi hira wanda yawanci shine yake tambayan su.. Dama dai Zayd is a good listener sossai ya natsu yana ta sauraron labaran yaran na makarantar su da kuma shirmen da suka yi na yarintar su.

Ameera dai tana zaune a kujerar kusa da shi tana kallon shi jefi-jefi yayinda take ganin kamar something is off a tare da shi.. har tambayan shi ta di
nga yi ko akwai matsala amma sai yace mata he is fine.

Wuraren qarfe shida na yamma ne ya mayar da su Ibrahim gida da kanshi, before then kuwa sai da ya hada su da driver ya kai su Super market don su siyo duk abinda suke so. Su kuwa sun cika da murna.. babu qarya kam sun kwaso kayan kala-kala.

Ameera ta so ya bar driver din ya kai su gida tunda he looked tired amma yace kar ta damu..

A lokacin da suka isa gidan Abba kuwa ya tarar da Abba a waje tare da makwabcin shi Malam Zakari, da alama masallaci zasu je don haka ne suka wuce masallacin gaba dayan su.

A yau din kuwa Limamin su Malam Idris baya nan yana da wani uzuri don haka ne Zayd ya ja musu sallar cikin qira’ar shi mai dadin gaske.. shi ya ja su har sallan Isha’I.

Bayan an idar da sallah Isha’I ne ya samu Abba ya sanar da shi yana so ayi expanding din masallacin saboda mutane suna yawa kuma babu space.. ya buqaci ayi ma ‘yan committe magana akan za’a rusa masallacin gaba daya a gina qasa da sama tunda land din babu girma.. Sossai Abba ya ji dadin hakan.. A nan take yayi ma ‘yan committe din magana suka amince.. sai godiya suke yi suna sanya mishi albarka tare da yi mishi fatan samun zuri’a na gari.. Shi kuwa Abba murna suka dinga yi mishi ya samu sirikin arziki..

Tare suka jera suka koma gida..

Su Ibrahim suka kwashe kayan su a motar Zayd sannan suka shiga gida.. Abba dai ganin kaya masu yawa sai da yayi ma Zayd magana wanda shi kuma ya dinga bashi haquri.. A haka dai suka shiga gidan. 

Ko da ya gaisa da Umma sai da yayi tambayar kunun aya idan akwai a bashi..

Umma dai dama tayi mishi nashi special ta ajiye mishi a freezer don haka ne ta dauko mishi yana ta godiya.

A daidai wannan lokacin kuwa Layla tana daki ta jiyo muryar Zayd kamar daga sama.. A guje ta miqe ta shafa kwallin ta tare da ambatar sunan shi kamar yadda Malam ya ce..

Ko da ta shigo falon tuni yayi ma su Abba sallama yayi tafiyar shi.. Sossai ta ji haushi.

Kafin ma su Abba su kula da ita a falon ne ta koma ciki abinta.. Ta qudurta a ranta the only way to finish it off is in his company don haka dole ne ta datse shi a can..7

STORY CONTINUES BELOW

Ghen ghen ghen….

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆

Wuraren qarfe takwas da rabi na dare Ameera tana tsaye gaban vanity mirror dinta sanye cikin wata doguwar riga shara-shara wadda ta bi jikinta.. Ameera dai dukda batada body irin na Layla babu laifi she is not bad…

Kallon kanta take yi yayinda take tunanin yadda zata dinga sa irin kayan tana zuwa gaban Zayd..

Yanzu haka idan ka kalla da kyau har inner wears din jikinta kana gani ta cikin rigar.. toh amma da ta tuna da abinda qawarta Zarah ta fadi mata sai na ga tayi murmushi tace “I have no choice I guess”

Babu abinda take bazawa sai qamshi.. Gani nayi tana kallon stitches dinta closely yayinda ta saki ajiyar zuciya… babu laifi yana ta healing.

Agogo ta kalla ta ga qarfe tara saura kwata.. ta tabbatar Zayd ya dawo don haka ne ta dauki hularta ta sanya sannan ta fita.

Kai tsaye sashen shi ta nufa.. Ko da ta qwanqwaso qofar shi ta shiga gani nayi ta tsaya cak cike da tsananin tsoro a dalilin ganin shi da tayi kwance a ta gefen gadon shi a qasa.

Cikin tsananin tashin hankali ta ruga wurin shi a guje tana fadin “inna lillahi wa’inna ilaihir raji’un.. Ya Zayd what’s..”1

Kasa qarasa maganarta tayi a dalilin taba shi da tayi ta ji jikin shi yayi mugun zafi..

Zama tayi a qasan ta dago kanshi ta dora a bisa cinyar ta tana shafa fuskar shi.. idanuwan shi sunyi ja.

“Ya Zayd me ya same ka?? baka da lafiya? na shiga uku.. meyasa baka fadi mun ba?”

Tuni hawaye sun fara gangarowa daga fuskarta.

“hey relax Habibty, kai na ne yake ciwo kuma zai daina” ya fada yayinda ya gyara kwanciyar shi a kan cinyarta.

“a’a Yaaya don Allah ka zo mu je asibiti ko a kira likita..”

“kin san bana so ko??”

“toh ya kake so in yi?? zama zanyi ina kallon ka..”

“kiyi mun addu’a, I will be fine… kawai fa gajiya ce”

“kenan tunda ka dawo kana jin ciwo shine baka fadi mun ba??”

“kiyi haquri Habibty..”

“tashi ka koma kan gado kar bayan ka yayi ciwo”

Babu musu ya amince ta taimaka mishi ya koma kan gadon..

Hannunta ta dora a bisa gashin kanshi mai laushin gaske yayinda take birkitawa a hankali.. tana yi zuciyarta na bugawa.. Gaba daya ta shiga damuwa. Ji tayi kanshi yana qara zafi yayinda yake ta motsi alamar lallai ciwon kan yana matsa mishi..

Ba tare da bata lokaci ba tana dafe da kanshi ta fara yi mishi addu’a kamar haka “Laa Yusadda’uuna anha walaa yunzifuun”

(aya ce ta Goma sha tara a cikin suratul waqi’ah)

Haka ta dinga maimaitowa har sau talatin da uku.. daga nan ta koma karanto suratul takathur.. tana yi tana shafa kan shi a hankali, Cikin ikon Allah kuwa har zafin ya fara sauka..

Bakinta ta kai saitin kunnen shi tace “ina zuwa..”

“ina zaki je??” ya tambayeta muryar shi qasa-qasa yayinda idanuwan shi suke a rufe.

“Zan kawo maka apple ne..”

“what???” ya fada tare da bude idanuwa..

Tana murmushi ta dan ja gemun shi tace “yes Ya Zayd, Apple boosts one’s inner energy leading to the brain, I am sure it will help you”

STORY CONTINUES BELOW

Murmushi ya dan yi shima sannan yace “the love you have for apple though..”

Tana dariya tace “let me just come” ta sauka daga kan gadon ta wuce ta fita..

Gyara kwanciyar shi yayi, Sossai yake jin sauqin ciwon kan.. da alama dai addu’ar da Ameera tayi mishi ce tayi aiki.

Ameera ce ta shigo riqe da plate dauke da slices na Apple yayinda ta qarasa wurin shi kan gadon ta zauna..

“Yaaya ga apple din”

Bude idanuwa yayi sannan ya tashi zaune.. Ameera ta jingina mishi pillow a headboard na gadon sannan yayi resting bayan shi yana kallon ta cike da So..

Slice na Apple ta dauka sannan ta kai saitin bakin shi ya bude ta saka mishi..

“kin yi kyau Habibty.. I love your slim and beautiful body”

Murmushi tayi cike da murna tace “nagode yaaya”

A haka dai ta cigaba da bashi apple din har ya cinye shi tas..

Bayan ta mayar da plate din kicin ta dawo ne ta haye kan gadon tana kallon shi tace “Ya kan?? ya rage ciwo??”

“yes Habibty, it’s all thanks to you.. nagode”

“anything for you..” ta fada yayinda ta gyara mishi Duvet din da ya rufa da shi..

Ta juya zata sauka daga kan gadon ne ya cafko hannunta.. Da sauri ta juyo tana kallon shi. Zuciyarta kuwa sai bugawa take yi..

“Habibty tafiya zakiyi ki bar ni??” Ameera ta bude baki zata yi magana ne yace “…please ki kwana anan, I need you close to me”

A rude tace “but yaa…”

“please Habibty”

Ajiyar zuciya ta saki sannan tace “toh bari in je in sa kayan bacci”

Ba tare da ya saki hannunta ba yace “No.. kiyi bacci da na jikin ki..”

Ameera dai shiru tayi tana kallon shi.. lallai fa yau ake yin ta. Da farko tayi zaton it won’t be a big deal kwana tare da shi but yanzu da abun ya zama reality sai take jin wani iri..

Bata ankara ba ta ji ya janyota.. babu shiri ta kwanta gefen shi suna fuskantar juna..

Yau wace rana gata nan tare da Zayd suna kwance a kan gado daya a matsayin ta na matar shi.. dream come true for her.

Kamar ya san me take tunani yace “thank you for being my wife.. I love you so much Ameera” yayinda ya miqar da hannun shi ya kashe wuta s
annan ya qara janyo ta ya matse ta a jikin shi gam ya gyara musu Duvet..

Ameera wadda zuciyarta take bugawa ji tayi yana tofa mata addu’a…

Bayan kusan minti Goma sha biyar Ameera dai bata yi bacci ba.. Sai motsi take yi tana gyara rigar jikinta, da alama she is not comfortable.

Bata ankara ba ta ji hannun shi a bayan ta yana zuge zip din rigarta ahankali.. hakan kuwa ya haddasa mata wata muguwar faduwar gaba yayinda jikinta yake rawa..

muryarta a shaqe tace “Yaaya..”1

“ssssshhhh..” ya fada yayinda yayi unhooking bra dinta yace “it’s making you uncomfortable.. remove it”8

Ameera dai sossai ta cika da mamaki.. Ya aka yi ya gane hakan?? ba ma wannan ba, ta ya zata cire a gaban shi toh??

Da ta tuna cewar cikin duhu ne sai ta tashi zaune ta sauke hannun rigar ahankali sannan ta cire bra din ta ajiye a gefe.. bayan ta mayar da hannun rigarta ne ta ja Zip sannan ta koma ta kwanta..

Tana kwanciya kuwa ya janyo ta jikin shi tare da matse ta gam.. this time both of them feeling very much comfortable!

Da alama dai yace ta cire ne because he wasn’t feeling comfortable just as she wasn’t too..6

Aikuwa ko minti biyar bata qara ba bacci ya sace ta…

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *