ZABI NA CHAPTER 6 BY FADEELARH

ZABI NA CHAPTER 6 BY FADEELARH

Wani ikon Allah kuwa tun daga wannan ranar Layla ta fita harkar Habib gaba daya.. idan ya kira wayarta bata picking, haka idan ya aika mata text message bata replying. Idan ya je school wurinta bata fitowa.. Haka saqonnin da yake ba Haleema ta bata duk bata sauraron ta.. Abin mamaki sai gashi kullum tare da Layla ake lectures har a gama…1

Ameera ta ji dadi sossai ganin yadda ta mayar da hankali akan karatu musamman don saboda an kusa fara jarabawa. Qawayen su Yusrah da Maryam sunyi mamakin yadda Layla ta canza.. sun kula kwana biyu Habib ya daina zuwa.. Ko da suka tambayeta sai ce musu tayi sunyi fada ne. Su kam har ga Allah sun ji dadi don kuwa daga Yusuf har Habib basu kwanta musu a rai ba. Fatan su shine Allah yasa kar su shirya..

A bangaren Habib tun yana sa ran Layla zata haqura ta biyo shi har abin ya fara bashi tsoro.. Ya kula dagaske fushi tayi kuma da alama bazata sauko ba.. sossai ya shiga damuwa sannan ga muguwar sha’awar ta da ke addabar shi. Gaba daya ya kasa mu’amala da wata mace tun daga wannan ranar, hatta Fiddy da yake jin dadin kasancewa da ita ya kasa samun natsuwa tare da ita.. Ya qudiri niyyar dawo da Layla cikin rayuwar shi ta kowacce hanya.

A cikin ‘yan kwanakin kuwa Mama ta kula Layla ta daina kawo kudi.. Ko da ta tambaye ta sai tayi mata qaryar yayi tafiya ne.

Har ga Allah Layla tayi missing din Habib.. wani lokaci idan ya kira wayarta ko ya aiko mata text message sai ta ji kamar tayi responding.. Kalaman da yake aiko mata ne suke qara tabbatar mata da lallai yana son ta kuma yana son auren ta amma kuma abinda ya faru tsakanin su fa?? Wannan abu dai ya tsaya mata a rai, tabbas wannan abu yayi mata dadi bazata yi qarya ba, kai har mafarki take yi na abin.. takan tashi bacci da muguwar sha’awar son sake yin wannan abu..2

Akwai lokuttan da take ji kamar ta koma ma Habib su cigaba da rayuwar su tunda dai Haleema ma tana yi kuma babu wanda ya sani sannan the most important thing is akwai pills din da zasu iya hana ta daukan ciki..

Subhanalillah…

A wannan lokacin Layla ta zama so confused.. Na daya ga feelings dinta da take qoqarin yin yaqi da shi, gashi kwana biyu ta daina kama kudade sannan kuma ga nacin shi Habib din da kuma pressure da Haleema take applying…

Shaidan ne yayi galaba a kanta inda ta bada kai bori ya hau..

Tuni ta amince ma Habib suka koma gidan jiya.. Ya masifar jin dadin wannan abu don kuwa har ya fidda ran qara samun ta..1

A yanzu kuwa musamman yake zuwa makaranta ya dauke ta su tafi gidan shi suyi iskancin su son ran su sannan ya bata kudi ya dawo da ita school.

Yusrah da Maryam basu ji dadin shiryawar Habib da Layla ba.. Gaba daya hankalinta baya kan karatu. Sun yi musu nasiha ita da Haleema amma sam sun qi saurarar su. Ameera tana kula da yadda Layla bata zama class sam-sam. wannan abu yana baqanta mata rai.. qawarta Zarah ce tace ta daina damuwa da ita tunda dai tayi nisa bata jin kira kuma ma idan tana sa kanta cikin hidimar Layla babu abinda yake qara janyo mata ita da mahaifiyarta sai baqin jini.

Ita dai Mama tana nan kullum tana boye kudade cikin Ghana must go a wadrobe… kullum tana cikin sanya ma Layla albarka. A yanzu ta dinka manyan atamfofi dayawa wanda idan ta sanya ta shiga qawayenta sossai suke respecting dinta.. dama dai abinda take so kenan1

Abba dai bai san abinda yake faruwa ba.. ita kanta Umma ta dai ga Mama tana sanya manyan atamfofi idan zata fita amma bata san ina take samun su ba…

STORY CONTINUES BELOW

Wannan kenan!!

☆☆☆☆☆☆☆☆

After a while…

KADUNA STATE UNIVERSITY

A yau wuraren qarfe sha daya na safe Ameera tana zaune a class tana hada assignments din da aka yi submitting zata kai ofis din lecturer din su.

A wannan lokacin kuwa babu lecture sai na 12-1 don haka Yawancin ‘yan ajin duk sun fita don shan iska yayinda wasu suke zaune a class suna ta hira..

Layla da clique dinta ma suna nan zaune a class din suna ta hira.. ita kam zaman jiran Habib take yi wanda suka yi zai zo ya dauke ta su tafi gidan shi as usual.

Ameera dai bayan ta gama jera assignments din ne ta dauki Jakarta ta rataya sannan ta kwashe su ta fita..

Bayan ta kai ma lecturer din tana dawowa ne wayarta tayi ringing.. Sunan qawarta ta gani.

Nan da nan tayi answering.

“Zarah ina missing dinki wallahi.. haka kawai kika qi zuwa yau”

a dayan bangaren ne Zarah tace “wallahi ba haka bane.. dagaske sweetheart ne zai dawo yau shine nake dan shirya mishi.. akwai wani emergency abu da zai zo yi ne shiyasa ma ban san da dawowar nashi ba sai yau da safe. Kiyi haquri qawata.. ya lectures din??”

A lokacin kuwa har Ameera ta dawo class.. dayake ana surutu sossai a ciki sai ta tsaya a waje jikin railings tana kallon mutane a qasa kowa da abinda yake yi…

“Fine fine.. nayi miki submitting assignment din naki da kika turo driver ya kawo mun”

“Nagode sossai qawata”

“toh yanzu dai bazamu je siyan laptop din ba kenan sai gobe??”

Sunyi akan Zarah zata raka ta siyo laptop.. dama tun da dadewa Umma tayi mata alqawarin zata siyo mata gashi a yanzu yawanci assignments dinsu ta laptop din suke yi.. kullum tana kan hanyar zuwa business centre don ta samu tayi assignments din. Mama ta bata ATM card dinta ta tafi da shi tunda basu san akan nawa zata samu ba.

“insha Allah qawata, Gobe sai mu je.. don Allah kiyi haquri please”

“hey it’s okay.. aikin lada kika tsaya yi. Aikin da zai shigar da ke aljannah idan kika…”

Kamar an ce ma Ameera ta kalli Garden wanda yake kusa da parking lot sai ta hango shi..

ZAYD

“Wait, me nake gani ne? Me yake yi anan???” ta fada cike da mamaki.

“Qawata ke da wa kuma???”

“Zarah wallahi Ya Zayd na gani a garden.. me ya zo yi???”

“Ba dai wurin Layla ya zo ba bayan cin mutuncin da tayi mishi??? amma dai gaskiya wannan Zayd din baya da zuciya.. da zan gan shi kuwa sai na zage shi tas na rashin hankalin da yake yi… ana soyayya dole ne wai???”

“Zarah calm down.. not necessarily ita ya zo gani. I will hang up now, zan kira ki anjima”

Bayan ta kashe wayarta ne ta qura mishi idanuwa babu ko qyaftawa.

Zaune yake a kan daya daga cikin kujerun da suke garden din riqe da wayar shi yana latsawa.. Sanye yake cikin wandon blue jeans wanda ya sha wahala da kuma wata shirt wadda idan ka kalle ta da kyau zaka gane ta sha wanki wanda ya ci ace an haqura da ita ma. Dukda haka kuwa yayi masifar kyau daga inda take hango shi..

Wata muguwar soyayyar shi ce take kai da komowa a zuciyarta.

Abin mamaki dukda yanayin shigar shi bai hana matan da suke giftawa kallon shi ba.. Wasu ma har pointing at shi suke yi suna magana. Haka kawai sai Ameera ta ji haushi.. Kenan suma suna son shi ne??1

STORY CONTINUES BELOW

Zayd wanda yake zaune yana ta dialling lambar Layla amma ta qi picking.

Kamar an ce ya dago kai sai ya hango su ita da Haleema zasu je parking lot.. Da sauri ya miqe ya qarasa wurin su.

Ita dai Layla ganin shi kawai tayi a gaban ta..

“Baby how are you??” ya tambaye ta yayinda yake kallon ta har yana dan murmushi.

Saboda tsananin mamaki ma kasa magana Layla tayi…

Haleema kuwa qura mishi idanuwa tayi kamar wadda take yi mishi kallon sani.

“Yanzu fisabilillah don ka wulaqanta ni shine zaka biyo ni makaranta?? wai ba na fadi maka bana yi ba?? dole ne?? ina ka taba ganin namijin da bayada ko sisi ya faranta ma mace in a relationship?? don Allah ka tafi ka bani wuri kafin mutane su gan mu tare” ta fada cike da masifa.

“please kiyi haquri.. akwai important abinda nake so in fadi miki ne. Just few minutes of your time is all I need and that’s all”

Kafin Layla tayi magana ne Haleema tace “Layla wannan waye???”

Tsaki ta ja sannan tace “wani dan naci ne.. talakan banza… “

Ta nuna shi daga sama har qasa sannan tace “can you imagine wai a haka sona yake yi.. na kore shi ya qi tafiya.. mutum kamar kudin cizo”

Zayd dai runtse idanuwan shi yayi ya bude sannan yace “don Allah kiyi haqu..”

“Hello pretty”

Gaba dayan su suka juya direction din da suka jiyo muryar.. Habib ne tsaye yana sanye cikin qananan kaya na wandon sweatpant baqi da shirt, yayi masifar kyau sannan sai baza qamshi yake yi.

“Sweetheart sai yanzu ka qaraso?” ta fada yayinda ta nufi wurin shi.

Bayan sun gaisa da Haleema ne na ga ya sa ma Zayd idanuwa kamar yana yi mishi kallon sani shima.1

Da sauri yace “Baby waye wannan?? his face looks familiar”5

Fashewa tayi da dariya tace “what? ah inaaa.. ai baka san wannan ba. he is a nobody”

“okay toh me kuke yi tare? kin san fa bana so in ga kina tsayawa da maza especially low class like this one”

Hannun Habib ta riqo tace “please forget him and let’s go”

Zayd dai gani nayi yayi freezing a tsaye a dalilin ganin yadda Layla ta riqo hannun Habib.. He was so shocked that he couldn’t move.

Haleema wadda take dariya tace “babe sai mun yi waya anjima” sannan ta kalli Habib tace “take care of my friend”

Yana murmushi yace “you know I always do..”

Haleema dai wurin motarta ta nufa itama.. da alama fita zata yi.

Habib ya zagaya ya bude ma Layla ta shiga sannan ya zagayo ya shiga… Zayd yana nan tsaye yana kallon su..

Dayake motar tint ce, baka ganin abinda yake faruwa a ciki.. Yana shirin juyawa ya tafi ne ya ga an sauke glass na gefen Layla..

Zuciyar shi ce ta buga a dalilin abinda ya hango.. Habib da Layla suna kissing juna, irin intense kiss dinnan.

“Subhanalillah” abinda ya fadi kenan yayinda yayi saurin juyawa.

Habib dai ko da ya tabbatar Zayd ya gan su sai ya dage glass din sannan ya ja motar suka bar wurin.

Gaba daya jikin Zayd ya fara rawa.. Dafe qirjin shi yayi daidai saitin da zuciyarshi take wadda take ta zafi tana barazanar faso qirjin nashi… Kan shi kuwa juyawa ya fara yi yayinda ya fara yi mishi azabar ciwo.1

STORY CONTINUES BELOW

Ko da ya daga qafar shi daya failing dinshi tayi don kuwa sanyi tayi qarara.. aikuwa anan ya zube qasa sumamme..

toh fa…

Ameera wadda take kallon su daga sama ce ta sa ihu yayinda ta sauko a guje.. ko kafin ta qaraso students duk sun zagaye shi ana tattaba shi don tabbatar da lafiyar shi..

“he is alive.. can someone please identify him  we need to take him to the dispensary”

“Ya Zayd! Ya Zayd!!” tana kuka ta qaraso wurin yayinda ta shige cikin cunkoson mutanen da suka taru a kanshi..

“Ameera kin san shi ne??” Sameer class mate dinta ya tambayeta.

“Yes Sameer he is my brother, please help him.. we need to take him to the dispensary”

“school dinnan yake??”

“No”

“then we will have to take him to a hospital don dispensary na school bazasu yi attending to him ba without ID card” Sameer ya fada yayinda ya kalli guys din da suke wurin yace “help me please”

Da sauri suka dauko Zayd suka kai shi motar Sameer suka sanya shi a ciki yayinda Ameera ta bi bayan su ta shiga motar.

Da sauri Sameer ya tayar da motar suka bar makarantar.. Hankulan kowa a department din ya tashi yayinda suke ta maimaita abinda ya faru.

Ameera dai ko da suka kama hanya Sameer ya tambayeta asibitin da zasu je sai tace mishi ya kai su nearest asibitin da ya sani domin kuwa what matters a wannan lokacin is Zayd’s life and nothing more.. Monarch Hospital ne the closest he could think of a lokacin don haka ne ya wuce da su can.

☆☆☆☆☆☆☆☆

MONARCH HOSPITAL

Nurses ne suka tura stretcher din Zayd zuwa wani daki yayinda wani likita ya rufa musu baya. Ameera tayi cirko-cirko a tsaye tana ta rusa kuka…

Sameer wanda yake tsaye a gefenta ne yace “Hey Ameera relax.. insha Allah nothing bad will happen.. please ki daina kuka”

Girgiza kai kawai tayi yayinda ta shiga jero addu’o’i kala-kala.

Bayan kusan minti talatin ne Likita ya fito daga dakin da aka shigar da Zayd.. A guje Ameera ta qarasa wurinshi yayinda Sameer ya bi bayan ta.

“Doctor how is he???”

“He will be fine dont worry.. right now he needs some rest”

“but can I see him?”

“No, not yet. why dont you go settle the bill before you get to see him later??”

Sai a wannan lokacin Ameera ta tuno cewar yakamata tayi depositing kudin treatment dinshi. Don ma Allah ya taimaka ganin halin da yake ciki sun karbe shi ba tare da sun tambayi katin shi ba da sauran su..

Girgiza kai tayi tace “I will do just that doctor”

Tare da Sameer suka nufi reception din inda suka fadi lambar dakin shi sannan aka duba ta computer don ganin expenses na treatment din da ake ba Zayd.

“you are to deposit the sum of N89,300 ma’am”

“What??” Ameera ta fadi yayinda ta kalli Sameer wanda shima ya zaro idanuwa.

Asibitin Monarch dai babban private hospital ne wanda yake da kyau sossai.. Yawanci masu kudi suka fi zuwa asibitin domin kuwa akwai su da kayan aiki da qwararrun likitoci…1

Sameer dai ko da ya lalubo wallet dinshi ya duba duka Naira dubu bakwai ne a ciki.. A account dinshi kuwa naira dubu ashirin da biyar ta rage mishi na pocket money din da mahaifin shi yake bashi every month..

Yana kallon Ameera yace “I think za’a samu dubu talatin da biyu a hannu na.. ke fa?”

Da sauri Ameera ta bude hand bag dinta ta fito da ATM din Umma da ta bata wanda yakamata ta ciro kudi ta siya laptop.

“kar ka damu Sameer, let’s use this. dama laptop zan siya da kudin.. I can buy it some other time”

Anan dai Ameera ta bayar da katin ATM din aka cire kudin ta POS aka bata receipt. Daga nan suka koma suka zauna zaman jiran ganin Zayd.

Wayar Sameer ce tayi ringing ya duba.. Sunan Mummyn shi ya gani. Da sauri yayi answering.

“Yi haquri Mummy gani nan zan je in karbo.. na kai brother din wata course mate dina asibiti ne”

Shiru ya dan yi sannan yace “eh da sauqi”

Ya girgiza kai yace “okay Mummy.. I am on my way”

Bayan ya kashe wayar ne ya kalli Ameera yace “I have to go Ameera, akwai saqon da zan karbo ma Mummy and it’s kinda urgent”

“Ba komai Sameer, nagode sossai”

Ya miqe tsaye yace “bari in karbi number dinki zan kira anjima in ji jikin nashi”

Aneera ta bashi number dinta sannan ta qara yi mishi godiya.

Bayan ya tafi ne ta koma ta zauna tayi tagumi yayinda ta fada duniyar tunani.

“Shin son da Zayd yake yi ma Layla yayi zurfin da har zai shiga wannan halin saboda rejection dinta?? does he love her this much even after knowing cewar bata qaunar shi??? Zai taba son wata ko da rabin yadda yake son Layla kuwa??? does that mean she will never have a chance with him?”MONARCH HOSPITAL+

Zaune take a kan kujerar da take gefen gadon da yake kwance yayinda ta qura mishi idanuwa.

Likita dai yayi mata bayanin cewar jinin shi ne ya hau a dalilin tashin hankalin da ya shiga sannan akwai alamun stress a tattare da shi don haka ya bata shawara akan a kula da shi sossai.

Kusan tsawon awanni hudu kenan Zayd yana bacci.. tsawon wannan lokacin Ameera tana nan zaune tana jiran a bata damar ganin shi… Gaba daya hankalinta a tashe yake. A nan masallacin asibitin tayi sallar Azahar da la’asar.

Zayd dai har a wannan lokacin da Ameera ta shigo dakin bacci yake yi… Cannula ce maqale a hannun shi yayinda ledar ruwa take sagale a wani qarfe.. A yanzu haka yana kan leda na biyu kenan.

Kyakyawar fuskar shi take ta kallo yayinda soyayyar shi take bi jini da jijiyar ta. Cikin dan qanqanin lokaci har ya rame.. dukda yana kwance a gadon asibiti yayi masifar kyau.

“Ya Zayd meyasa kake nema ka halakar da rayuwar ka saboda Ya Layla?? someone that doesnt care about you.. For crying out loud it’s not the end of the world don tace bata sonka.. wai baka san akwai masu sonka bane??? Ya Zayd kana da hali mai kyau, to me you are perfect in every aspect, Ya Layla doesn’t know what she has missed.. she doesn’t even deserve a kind hearted soul like you.. Ya Zayd why does it have to be her?? saboda ita kyakyawa ce? saboda tana da jiki mai kyau? saboda ita fara ce?? saboda tana da dogon gashi??? is it all about the physical appearance?? what about the feeling??”1

Shiru tayi yayinda take share hawayen fuskarta sannan ta cigaba da fadin “How I wish ranar ni ka gani, how I wish ni kace kana so, But No, a ranar ko kallo ka baka yi ba, it was as if I was invisible, as if I didnt exist.. was it because I was all covered up in Hijab??, saboda ni baqa ce??, bani da kyau??, saboda I was looking all dull?? Ya Zayd shin ka san cewar tun ranar da na fara ganin ka nake sonka?? ka sani cewar a kullum da sonka nake bacci da shi nake tashi??? shin ka san yadda zuciya ta take zafi a duk lokacin da Ya Layla ta wulaqanta ka?? Ka san yadda nake ji a zuciya ta ganin ka kwance a kan gadon nan a dalilin wulaqancin da Ya Layla tayi maka?? Ya Zayd do you know how very special you are to me?? do you know that I can sacrifice my everything just to see you happy? Ya Zayd meyasa baka ce ni kake so ba??”

Gani nayi ta kwantar da kanta kan gadon da yake kwance daf da hannuwan shi tana kuka yayinda ta cigaba da fadin “Ban taba yin soyayya ba, ban san meye soyayya ba sai a kanka Ya Zayd.. Allah ya sani nayi qoqarin in cire ka daga zuciya ta knowing cewar kai saurayin Ya Layla ne but it wasnt just possible.. it’s as if soyayyarka wani chip ne da aka dasa shi permanently a cikin zuciya ta.. Ya Zayd please tell me, ya kake so inyi da rayuwa ta?? ta ya zan cire ka daga cikin zuciya ta?? If only one day zaka zo kace kana sona Ya Zayd, if only that day you will ask me to marry you wallahi I wont think twice before accepting saboda ina bala’in sonka.. I love you for who you are and what you are.. I love you more than Life itself Ya Zayd.. Kai ne ZABI NA a koda yaushe. See, Unlike my sister ni ban damu da rashin arzikin ka ba, arziki na Allah ne na sani kuma ma ni bana sha’awar auren mai arziki.. Kawai ina son in auri namijin da zai bani lokacin shi.. Idan har zan samu soyayyarka da lokacin ka wallahi bani da sauran matsala a rayuwa ta. Na sani cewar bazaka taba so na ba and again na sani cewar har in mutu bazan taba daina sonka ba kuma bazan taba son wani kamar yadda nake son ka ba.. A matsayina na wadda take sonka zan cigaba da yi maka addu’a akan Allah ya hada ka da wadda zata so ka tsakani da Allah ta kula da kai.. Ni kuma zan cigaba da rayuwa cikin soyayyarka, I will continue to dwell in your love till the day I die..”5

STORY CONTINUES BELOW

Wayarta ce da take ta ringing ta dawo da ita daga surutun da take ta yi..

Da sauri ta dago kanta ta kalli Zayd wanda yake ta bacci yayinda tayi saurin share hawayen ta. Jakarta ta bude ta ciro wayar wadda har ta gama ringing. Sunan Umma ta gani don haka ne ta kira ta.

“Ameera wai ina kika shiga ne yau ga ‘yar uwarki ta dawo gida tace bata gan ki ba… siyan laptop din ne har yanzu??” Umma ta fada cike da damuwa

“Umma don Allah kiyi haquri.. na manta ne ban kira ki ba in fadi miki abinda ya faru” ta fada cikin wata irin murya wadda ta tabbatar ma Ummanta da lallai kuka take yi..

“Subhanalillah.. me ya faru??? ya na ji kamar kina kuka?? kina ina ne???”

“Ina asibiti ne tare da Ya Zayd.. ya zo makarantar mu ne yau shine Ya Layla tayi mishi wulaqanci a gaban mutane.. da ya kasa jurewa ne ya suma sai muka kawo shi asibiti. Nayi amfani da kudin Laptop din da kika bani na biya mishi kudin magani.. Don Allah kiyi haquri Umma”

“Haba Ameera meye na bani haquri.. Ran dan Adam ai ya fi komai muhimmanci.. Yanzu ya jikin nashi???”

“da sauqi Umma.. amma har yanzu bai farfado ba, bacci yake yi”

“toh abinda nake so da ke shine ki dawo gida yanzu zuwa anjima idan Abban ku ya dawo sai mu je mu duba shi a asibitin.. nima bari in dafa mishi abinci kafin nan”

“toh Umma, gani nan dawowa”

Bayan ta kashe wayar ne ta sa a Jakarta sannan ta miqe tace “Allah ya baka lafiya Ya Zayd.. bari in je gida in dawo.. Allah yasa ka farfado kafin mu dawo”

Ko da ta kai bakin qofa juyowa tayi ta kalle shi tare da sakin ajiyar zuciya sannan ta juya ta fita.

Tana rufe qofar kuwa Zayd ya bude idanuwan shi ya tashi zaune…4

Gani nayi ya daga hannuwan shi guda biyu zai shafa fuskar shi amma ya kasa a dalilin hannun shi mai dauke da Cannula.. Cike da tsananin tashin hankali na ga ya zare Cannula din daga hannun shi ya jefar yayinda ya zaro torchlight phone dinshi daga cikin aljihun shi.

Ko da ya duba 27 missed calls ya gani.. duka missed calls din came from one person

Bilal..

Da sauri yayi dialling lambar Bilal din.. Bugu daya kuwa yayi answering.

“Hello Sir, Kana ina ne ina ta kiran ka a waya baka yi picking ba??” you got me worried gashi kuma I am not able to track you”

“Relax.. wayar tana silent ne ka san bana son qarar ta.. cika mun kunne take yi”

“Kana ina ne yanzu???”

“I really dont know Bilal.. I am in some hospital..”

Ya sauka daga kan gadon yana qoqarin duba wani abin da zai sa ya gano sunan asibitin. Idanuwan shi ne suka kai kan file da ke maqale a gadon yayi saurin dauka ya duba.

“Monarch Hospital..”

“Subhanalillah.. me ya faru da kai?? are you okay??”

“I am fine, please come and pick me up now.. ka san bana qaunar asibiti.. I am starting to suffocate already”

“I am on my way Sir”

Bayan ya kashe wayar ne na ga ya koma kan gadon ya zauna yayinda ya dafe kan shi tare da runtse idanuwan shi… Motsi kadan sai in ga ya shafa gashin kanshi da hannuwa biyu.. Gaba daya baya cikin natsuwa..

Ko meyasa??? oho

Miqewa yayi ya dinga kai da komowa a tsakar dakin na tsawon lokaci.. Daga baya kuma ya koma jikin bango ya jingina yayinda ya cigaba da shafa kan shi yana bubbuga qafar shi..

STORY CONTINUES BELOW

Ji nayi yace “Oooh Bilal.. where are you??”

Qofar dakin aka bude wanda ya sanya shi dago kai da sauri… Bilal ne ya shigo tare da likita.

Cike da mamaki likitan yace “what have you done to yourself Mr. Zayd?? you are not supposed to take off the cannula…”

Zayd ya nufi wurin su da sauri tare da buga kafadar likitan yace “I am fine doc” ya kalli Bilal yace “Please handle everything ASAP sai ka same ni a mota”

“Okay sir” Bilal ya fada yayinda ya miqa mishi key din mota ya karba ya fita da sauri kamar wanda ake chasing.

A wannan lokacin kuwa Likitan ya zama confused ganin yadda Bilal yake ta girmama Zayd.. Bilal is looking all classy and sophisticated sabanin Zayd wanda zai iya rantsewa talaka ne toh amma kuma actions sun nuna ba hakan bane…

Ni kaina na dan zama confused.. what’s happening??6

“So doc.. can I get the bill???”

Likitan wanda fuskar shi take displaying mamaki har a wannan lokacin yace “his sister already paid for his treatment..”

“Sister???” Bilal ya fada cike da mamaki.

Wacce sister yake nufi??

“uhm okay thank you.. so then I am free to go right??” Bilal ya tambayi likitan.

“No, you need to get his drugs from the pharmacy and please he needs to avoid too much stress, it’s actually not doing good to him…”

A haka dai suka fita inda likitan ya cigaba da yi mishi bayani.

Ko da Bilal ya karbi magungunan an ce mishi ba sai ya biya ba domin kuwa duk cikin expenses din da aka riga aka biya ne.

Haka ya tafi yana mamakin abinda ya faru.. who could it be that did all this??

Magungunan ma ya dai karba ne kawai amma ya sani cewar Zayd ba sha zai yi ba… if there is one thing he hates its definately the sight of hospitals and everything that has got to do with it!!

toh fa…

☆☆☆☆☆☆☆

GIDAN MALAM FAROUQ ABDALLAH

MALALI

Wuraren qarfe Goma da rabi na dare tana kwance a bisa cinyar Umma a kan gadon dakin Umman tana ta kuka.

Umma wadda take shafa kanta ce take ta lallashinta yayinda take tausaya ma ‘yarta da yadda ta qwallafa rai akan Zayd.

Kamar dai yadda Umma ta tsara Abba yana dawowa ta sanar da shi halin da Zayd yake ciki.. Sossai ya damu domin kuwa ya dauki yaron tamkar dan da ya haifa.. yana bala’in son shi. Nan da nan yace musu su shirya bayan sallan magrib sai su je su duba shi tunda dai ya sani sarai yaron baya da kowa a garin nan kamar yadda ya fadi mishi. Umma kuwa ta dafa abinci ta shirya a warmers. Bayan sallar magrib suka tafi asibitin a cikin keke napep din da yake kai su Ameera school.

Ko da suka je kuwa sun tarar babu Zayd.. Hankalin Ameera yayi matuqar tashi. Likitan ya sanar da su cewar wani ya zo ya tafi da shi sannan bai gama receiving treatment dinshi ba.. Su Abba sunyi mamaki amma kuma suka yi tunanin qila daga gida aka zo aka tafi da shi ko makamancin hakan.. Da wannan ne suka dawo gida yayinda suke ta yi mishi addu’ar samun sauqi.

Aikuwa dai suna dawowa Ameera ta rushe da kuka.. kukan da take ta matsewa a gaban Abba.

“Ameera ki daina kuka haka mana.. na tabbatar duk inda yake yana samun sauqi” Umma ta fada yayinda take ta shafa kanta.

“Umma toh wai me zai sa ya bar asibitin bayan bai gama karbar treatment din shi ba? yanzu ina zan gan shi don in ji lafiyar shi??? kin ga fa da na zauna tare da shi da bai tafi ba.. yanzu shikenan babu yadda za’a yi in san halin da yake ciki??”

“Ameera kiyi haquri ki cire tunanin yaron nan daga zuciyar ki.. ina so ki mayar da hankalin ki kan karatun ki, kin ga jarabawar ku ta matso don haka bana so kiyi wasa.. Ban ji dadi ba da kika afka tarkon son wanda bai san kina yi ba amma kuma babu yadda zamuyi tunda dai haka Allah ya qaddara miki”

Ta daga ta tare da zaunar da ita tana fuskantar ta tace “ina so kiyi mun alqawari Ameera.. ina so kiyi mun alqawari cewar zaki manta da Zayd sannan ki mayar da hankali kan karatu.. Don Allah kiyi qoqari kin ji?”

Ameera wadda take share hawayen ta ce tace “toh Umma.. zanyi qoqari. Ki taya ni da addu’a. Shi kuma Ya Zayd Allah yasa duk inda yake yana cikin qoshin lafiya da kwanciyar hankali”

“Yauwa Ameera ta.. yanzu dai gobe ki je ki siyo laptop din tunda akwai kudin da zasu isa ki siya a cikin account din”

Zaro idanuwa Ameera tayi tace “dagaske Umma??? ba gwara mu dan bari zuwa nan gaba ba? kin dade kina tara kudin ki sannan…”

“Yi mun shiru.. don wa nake sana’ar da har nake tara kudin? ba don ku nake yi ba?? meye amfanin tarawa idan har bazan biya muku buqatun ku ba?? toh kar in qara jin kin fadi haka.. gobe idan kin tashi daga makaranta ki je ki siyo laptop don nima na gaji da yawo zuwa shago kina yin aikin makaranta a kullum.. gwara ki natsu a gida kiyi duk abinda zakiyi… Allah yayi muku albarka”

Ameera ta rungume ta gam tace “Nagode sossai Umma.. Allah ya biya ki da gidan Aljannah.. kuma Allah ya qaro miki lafiya”

“Ameen Ameera ta..”

♤♤♤♤♤♤♤♤

Ayyah poor Ameera…

Gaba daya ta bayyanar ma Zayd da sirrin zuciyarta amma kash, Bai ji ba.. so sad!!7

But wait, tana barin dakin ya farka.. shin kuna gani ya ji confession dinta ko bai ji ba???11

Bilal??? waye shi???

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *