ZABIN RAI CHAPTER 1
This book is free from beginning to end.2
*** *** ***
A hankali ya bude idonsa sai kuma ya maida idon ya rufe har sai da wayar ta sake ringing. Wannan karon yayi saurin bude idon ya sauka daga kan gadon yana kallon kyakkyawar mace dake gefensa tana bachi, hannu ya kai kamar zai shafa fuskarta sai kuma ya fasa sakamakon wayarsa da tai ringing. Kallon kwayar yai kamin yabkai hannu ya dauka.+
“Sadam kai kadai muke jira fa”
“On my way Dad”
Ya fada yana shafa sumar kansa, sannan ya aje wayar yana hamma, da alama bachin be isashe ba a haka ya tashi ya nufi bathroom, a gaggauce yai wanka ya fito sanye da bathrobe ya nufi gaban madubi. Cikin kankan lokaci ya shirya ya feshe jikinsa da expensive perfume, wani bangare ya nufa na bedroom, hannu ya kai ya danna wani dan karamin maballi dake gefensa gurin sai ga wata katuwar kofa mai cushion ta rabu biyu, ciki ya shiga ya sai gashi cikin wani dan madaidacin dakin mai dauke da kayan ado na zama kama daga kan tufafi, agogo, takalma, hulluna, glasses and so on.
Cikin kananna kaya ya shirya dark blue T-shirt and white jean, takalmin dake kafarsa ma dark blue ne kamar yadda facing cap dinsa take, fito yai daga dakin yana kokarin saka ma hannunsa agogon, gaban madubi ya zo ya tsaya yana kallon kansa. He look so cute and adorable, so cool and calm. Tufafin jikinsa sun karbeshi sosai. A cikin madubin yake kallon mace data taso daure da zanen gado ta nufo inda yake tsaye.
“Don’t touch me”
Ya fursa fuskarsa a hade. Ko da wasa bata tai gigin kai hannunta ta taba shi ba, sai kawai ta bata fuska. Barin gaban madubi yai ya koma dan karamin dakin sai gashi ya fito rike da da bandir din yan dari dubu ya jefa mata, sannan ya juya ya danna maballin dazun dakin ya rufe. Gaban madubi yaje ya dauki makullinsa da atm dinsa ya saka aljihu.
“Zan shigo da Friends dina anjima karki yarda na tararda ke a cikin dakin nan”1
Yana fadar hakan ya nufi kofar fita sai kamshin turare yake, gaban tinting windows ya nufa ya kai hannu ya daga curtains din yana hango wani dan karamin gida, hankali ya maida sosai yana kallon wata matashiyar yarinya da ke zaune saman kujerar tsakar gida irin ta mata, hannunta rike da bulala ta hade rai sosai tana kallon kananan yara dake gabanta. Baya iya jiyo abunda take cewa amman ga dukan alamu horo take musu, hannayensu suka taro tana dukansu a hannun daya bayan daya, mahaifiyarta ce ta fito daga dakin dake kusa da su rike da av ta zabga mata a gadon baya, wani irin tsalle ta daka ta tashi tsaye ta shige dakin da gudu tana dariya.
Murmushi yai ya saki curtains ya juyo fuskarsa da annuri ya nufi wani dakin sai gashi ya fito rike da wata yar karamar jaka mai dauke da kayan wasan tennis.
Main door ya nufa ya bude ya fito daga falon, da dan sauri yake taka katon stairs din yana saukowa kasa. Tun kamin ya karaso ya danna key din hannunsa bakar motar mai bakin gilashi tai tsuwa, front seat ya fara budewa ya saka jakar sannan ya zagayo ya shiga driver side ya tashi motar.
*** **** ***
Tana ta murza gurin da Umma tai mata bulalar kamar tai kuka.
“Gaskiya Umma kina min cin fuska haka kawai a gaban yara za ki dake ni”
“Ai shine daidai da ke, haka kawai dan zalunci za ki tara yara cikin rana kina musu hoto, kamar haihuwarsu ki kai”
Ta kalli wanda ya fada mata haka ta murguda masa baki.
“Wai kai Ya Nabeel ba Abbah yace ka daina shiga sabbagata ba, bari ya dawo Wallahi sai na fada masa”
“Mtsssss”
Yaja tsaki tare da tashi hannunsa rike da rike da tecno spark 3 ya fice. Ta yi kwafa
“Ba Nabeel ba Nabila”
Ta fada tana kara murguda baki kamar yana gabanta, ta sake murza gurin da Umma tai mata bulalar tana bata fuska kamar wata karamar yarinya.
“Zinneera”
“Na’am”
Ta amsa kiran da Umma tai mata da fushi ita a ala dole an daketa.
“Zo ga wayarki tana ringing”
Da gudu ta fita daga dakin ta nufi inda ta bar wayar ta dauka tana rawa kamar ba ita ce take fushi ba.
“Assalamu Alaikum”
Ya kara wayar a kunne tare da sallama sannan ta shige daki. Saman gado ta fada tana murmushi.
“Na yi marmarin muryar nan, yau duk ban ji Sahibata ba”
Ta dan bata rai.
“Bana ce ka daina ce min Sahiba ba”
Yayi dariya.
“Yi hakuri Sahiba ba zan kara ba”
“Wallahi zan kashe wayar”
“Yi hakuri na daina, yanzu dai fada min me da me Babyna tai yau?”
Ta yi murmushi tana mai jin sonsa har cikin zuciyarta.
“Taje makaranta, bayan ta dawo ta ci abinci sannan tai wanke wanke, sai kuma ta dawo tsakar gida tana yi ma yara horo”
“Au ba zaki daina wahalar da yaran mama ba ko?”
“Ee din, ai basa jin magana”
“Ke jin magana kike yi? Shiyasa kullum Nabeel yake zaneki”
“Ai Abbah yace duk ya sake shiga saggata sai ya sa kafar wando daya da shi”
“Amman Abbah be kyauta ba, ai ke sai da horo”
“Au haka ma za ka ma zaka ce?”
“Yi hakuri Babyna, fada min me kike son na zo miki da shi anjima”
“Zuciyarka, ka cireta daga kirjinka ka saka ta a hannunka ka zo min da ita yau ita na ke so”3
“Consider it done, I love you”
“I love you more Little Boy”2
“What…!”
Ya amsa da karfi sai tai saurin kashe wayar tana dariya….
____________________________________________
How are about this journey?
😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍3Gaban wani katon gate ya tsaya, sau daya ya danna horn, sai ga mai gadin da gudu ya zo ya bude masa gate din yana daga masa hannun duk kuwa da kasancewar gilashin motar tinting ne, na waje baya ganin na ciki sai dai shi na ciki yana gani na waje.+
Komai a kebance yake a gidan, an tsara shi kamar wani karamin kamfani, gidane plate mai farin fenti sai dai an kawata ko ina da fulawoyi, a dayan bangaren kuma babu komai sai tarin motoci na alfarma, yamma da motocin wata yar karamar kofar garden ce. Yana faka motarsa wasu yara suka zo da gudu suka zagaye motar suna tsalle, murmushi yai ya bude motar ya fito ya zagayo inda suke tsaye.
“Hi kids”
Yasa hannunsa aljihu.
“Ohhh sorry na manta daga gida na ke ban zo muku da komai ba”
Ya fada yana bata fuska irin yadda yara suke yi, sai suka sa dariya sai daya daga cikin yaran ya ce.
“Amman zamu yi wasan tennis ko?”
“Yes boy ga kayana nan na zo da su, an gyara mana fili?”
Ya fada yana shafa kan yaron.
“Ee Daddy yasa an gyara mana bangare daya cikin Garden”
“Okay kuje ku buga kamin na zo”
Ya mikawa wacce ta fisu girma makullin motar, ta karba da sauri suka bita gurin bude motar suka dauka. Main door ya nufa wata katuwar kofa ce mai kyau da kyali wacce ta kara fitar da kyaun farin fentin kasancewarta baka, hannu ya kai ya tura ya shiga. Murmushi da annashuwar dake fuskar mahaifiyarsa ne suka fara masa lalle marhabun, kana kallonta kasan tana cikin jindadi da kulawa, domin jikinta da yanayin, gurin da take zaune tufafin jikinta sun nuna haka. Kusa da ita yaje yai side hugging dinta.
“Morning Sweetlove”
“How is my Favorite doing?”
Ya saketa yana masawa.
“Am doing fine”
“Ya yanayin garin? Kasan Nigeria akwai zafi ba kamar can ba, musamman sokoto nan”
Ya daga kafadunsa.
“Akwai zafi gaskiya, amman ba irin zafin da zai hanani zama ba, dama can ina kokarin koyon zama cikin zafin ai dan na san ba can zan daumma dole wata rana zan dawo gida, gashi kuma na dawo”
“Haka ne, ka yi breakfast?”
“Yeah ai kin san ni bana wasa da cikina, sai dai ace bana ci da yawa, tun takwas na safe nai breakfast”
“Good, ka shiga ciki mahaifinka yana da baki yana jiranka”
“Okay”
Ya nufi kofar fita, kasancewar part din mahaifinsa yana can yamma da wannan part din, duk da kasancewarta akwai hanyar da kan sada mutum da part din, shi be cika bi ba sai idan ta kama dole saboda dogon corridor ne shi kuma be cika son hanya haka ba.
Glass door ne a gurin, na waje na hango na ciki kamar yadda na ciki yake hango na waje amman idan an daga curtains. Door bell ya danna hakan a hankalto da Daddy ya dauki dan karamin remote din dake saman glass center table mai kamar na ac ya danna sai kofar ta bude. Nan kam sallama yai kamin ya shigo sai duk suka sam masa har Daddynsa.
“Good morning Dad”
Daddy yai masa wani kallo sai ya dan sosa kai.
“Sorry Ina kwana?”
“Kwallahiya zaka ce shine gaisuwar sakkwatawa”
Sai duk suka sa dariya har dattawan dake cikin falon. Yana kokarin zama Daddy ya nuna masa mutumen dake dama da shi.
STORY CONTINUES BELOW
“Kalli nan tabashi ne, so shima baban ka ne”
“Ina kwana”
Ya gaisheshi, sai ya sake nuna masa dayan wanda yafi tsufa.
“Wannan kuma kanen kakana ne”
“Wow long life Sir, Allah kara maka lafiya”
Ya fada yana murmushi.
“Daman da sune nake son ka gaisa dan kasan yan’uwa, idan an kwana biyu zaka shirya kaje har can kauye ka gaishesu”
“Okay”
Wata kofar aka bude wacce ke cikin falon, sai ga waya kyakkawar budurwa wacce ba zata wuce goma sha bakwai ba mai kama da Sadam ta fito dauke da tea ta nufo inda Sadam yake.
“Mummy’s favorite”
“SweetSis”
Ya fada yana kallonta da murmushi a fuskarsa.
“Gashi inji Sweetlove”
Ya mika masa tea dake hannunsa.
“Fada mata na gode”
“Okay”
Sai kuma ta kalli Tsohon da Daddy ya kira da kakansa ta tabe fuska ta ce1
“Ni wannan miji tun dazu sai kallona yake”
Daddy ya zageta da hannu sai tasa dariya ta fice daga falon da sauri, su kuma suna dariya. Yana zaune a gurin ana labarin kauye, shi dai babu abunda yake ganewa kawai dai yana jinsu ne wani sunan ma har dariya yake saka shi, baya son ya tashi kar Daddy ya ga laifinsa a dole ya zauna a gurin har aka kira sallah azahar. Bayan sun yi sallah Daddy yai musu alheri ya saka driver ya kaisu har kauyen daman haka yake musu a duk lokacin da suka zo.
Garden ya nufa sai wayarsa tai ringing, cirota yai daga aljihu yai picking.
“Sadiq ya?”
“Daidai na zo ban ganka ba na tararda wata, daman kana aje mata ne”
“To ni dutse ne da zan ci na koshi kuma na kwanta lafiya kalau, am old enough fa ba zan iya cutar da kaina ba, ita kadai ce ita ma din jiya na fara”
“Gaskiya be dace ba, ya kamata ka canja”
“Ka fada mata tai gaggawar barin gidan nan kamin na zo”
“Kai ka kawota ai kai ya kamata ka fada mata ai, ni na bar gidan ma, idan ka dawo ka kirani sai na zo a tsara”
“Okaya”
Ya maida wayar aljihu yana kallon yaran da ke aikin buga tennis din maza da mata yana murmushi.
ZINNEERA POV.
Tana gama wayar ta taso ta fito waje tana kalle kalle.
“Ungo abincin ki”
Umma ta mika mata wake da shinkafar dake cikin plate, kin karba tai.
“Ni gaskiya bana son wake, kullum abu daya ni gaskiya na gaji”
“Wanken ne kullum abu daya? Jiya ba shimkafa da miya nai ba?”
“Ni bana so ni na restaurant nake so”
Dariya Umma ta saka ita da Larai da Tahir, Aleeya ta ce
“Sai ki kir Sadiq ki ce masa ya siyo miki na restaurant”
“Ai kinsan zai iya, yanzu nan ina kiransa zai kawo min, ni a can ma nake son ya kaini na ci kuma Wallahi ba zan raga ba, ko na raga sai dai na kulle a leda na zo da shi, dan ba zan ci abincin dubu biyu ko dubu da dari biyar zama daya na raga shi ba”
Nabeel dake zaune gefe daya yaja tsaki.
“Aike duk wanda yace ya daukeki ya kaiki restaurant sai ya sha kunya, bakauyar banza”
Ta bata fuska
“Umma kim gani ko?”
“Nabeel wai ba babanku yace ka daina shiga saggarta ba? Bana son fitina Wallahi ku dinga abu kamar kananan yara”
Cewar Umma tana kokarin rufe tukunya. Juyawa tai ta koma daki tana gunguni ita ala dole ba za ta ci wake ba. Haka ta wuni har dare bata ci komai ba saboda bata son wake da shimkafa.
Misalin tara wayarta tai ringing, da sauri ta dauka already tun takwas tai kwaliya ita mai saurayi wai zai zo hira.
“Babyna gani nan kofar gida”
“Okay gani nan zuwa”
Tana aje wayar ta dauki Hijab dinta ta saka ta kalli Umma.
“Umma ga Sadiq nan yanzo”
“Tau sai na dawo”
“Umma na fesa turaren Ya Nabeel?”
“Bana iya kin san ya saba cewa ki daina daukar masa abu ko? Yanzu ya zo yace zai dakeki Mahaifinki ya taso da fada”
Ta buga kafa.
“Umma nawa turaren fa ya kare”
“Sai ki fadawa Abbanki, kina yar University za ki ce baki da turare? Wuce kije ai tun baki saba saka turaren ba yake son ki yasan yadda kike”
“Ina zuwa zai ce wari na ke”
“Ya ce din”
Sai ta buga kafa kasa, ta sake buga, ta buga sannan ta fita daga dakin kamar zata yi kuka. Sai dai na kaiwa bakin kofar ta sauya fuskarta zuwa murmushi saboda ta hango ZABIN RAI, shima murmushi yake sakar mata har ta iso yana ginjine jikin motarsa 406.
“Assalamu Alaikum”
Ya masa sallama da muryar da yake jin ta fi ko wace murya kwantar da hankali da dadin sauraro a gurin.
“Babyna kin yi kyau sosai”
Ta rufe fuskarta da tafin hannayenta, sai ya ciro abu a aljihunsa ya mika mata.
“Bude ido ga zuciyar na zo miki da ita”
Sai tai saurin bude idon ta sauke su kan karamar bakar ledar dake hannunsa.
“Karbi mana”
Ya fada yana danna dariyar dake son kubuce masa, dan yasan halin Babyn tasa. Da dan tsoro ta kai hannu ta karbi ledar tana tabawa, jin tai kololon abu da ruwa ruwa ciki, da sauri ta wurgarda ledar tana ihu.
_______________________________
Ga masu tambayar na kudi ne ko kyauta? To wannan littafin kyauta ne, daga farko har karshe. Comments dinku kawai nake so😍”Wait wait wasa na ke miki papaya ne a ciki”
Ta bata fuska ta turo baki.
“Amman shine ka bani tsoro”
Ya mika hannu ya janyo ta ta fado kirjinsa.
“Sorry Babyna ba zan sake ba”
“Wani zai iya ganinmu fa”
Ta fada tana kokarin zame jikinta.
“Ba wanda zai ganmu”
Ya kara rumgumeta sosai yana sauke ajiyar zuciya.
“Ina son ki sosai Zinneera”
“Ina son ki Aleeya ina son ki Habiba ina son ki Ramatu, mace nawa ka fadawa haka”
Ya saketa yana dariya.
“Kin fara ko?”
“Ee ai gaskiya ce haka kuke kuje gurin wannan ku ce suna son ta kuje gurin wannan ku ce kuna son ta, ko ranar nan ma da ka kirani ai Aleeya ka ce min”
Ya sake yin dariya, sai ita tai dariya.
“Kaga ni ko? Dariya tana maka kyau shiyasa yan matan nan suke lake maka”
“Ni kam kinga na san a makarantar da kika fara yanzu, da Unguwar nan, na san akwai maza da yawa masu sonki, amman hakan be taba damu na ba, saboda na san ni kadai ne a zuciyarki, da zan hadu da mata dari kullum su ce suna so na, ba zai taba damuna ba, domin ni ke kadaice a gabana”
“Kai ma ai kasan wasa nake yi ko? But seriously am jealous, Sadiq kana da kyau sosai mata da yawa zasu yi crushing kanka, ni ba zan juri ganinka da wata mace ba, ko yar’uwarka ce”
“Eyyye Babyna an fara wayo har da su kishi haka”
Sai ta rufe fuskarta, sai kuma ta bude idon.
“Au da can bani da wayo?”
“Aa da baki da shi da ai ba zaki rika fada da Nabeel kullum ba”
Ya karasa yana mata gwalo, ta bata fuska har da rumgume hannayenta.
“Sorry”
Ya fada yana kama kunnesa alamar yana bata hakuri.
“Yi hakuri wasa nake miki, kawai na yi marmarin wannan fushin na ki ne, kin san ni komai na ki burgeni ya ke, fushinki dariyarki duk kyau suke miki, wani lokaci idan ina gida ko office na kan dauki wayata nai ta kallon hotunanki, ina jin nishadin haka, wani lokacin na kan tuna wani abu daya faru wanda ya kan saki dariya ko fushi sai na rika aina yanayinki, hakan yana kara min kaunarki. Har mahaifiyata ta sani, idan nai dariya sai ta ce Zinneera ko”
Ya karasa yana murmushi.
“Na san nafi ko wace mace a duniyar nan dacen masoyi, hakika ban yi kuken Zabin rai a matsayinka na wanda zan aura ba, wani lokacin na kan yi unkurin auna irin son da nake maka, amman sai na rasa silekin da zai dauki nauyin son balle har na iya irin kwatankwacin son da na ke maka, Umma tana yawan ce mun na yi dacen samun abokin rayuwa irinka, Abbana yana yabon kyakkawan halinka, sai dai ni kuma ina jin kamar akwai wata rana da son ka zai min illa, zai rufe idon na kasa gani a lokacin da ganin yake da muhimmanci, ya maida ni kurma a lokacin da jin ke da muhimmanci”
“Ko da mafarki, wani abu be taba tsikarata na ji akwai wata rana da zan yi zullumi ko dardar da son ki ba”
“ba zullumi na ke da dardar ba, har abada Zabin raina shine zabi bani da haufi akan zabarka a matsayin abokin rayuwa na san bazan yi nadama, a duk lokacin da nake tsara irin rayuwar zamantakewar auren da za mu yi sai na ji wani abu ya tsaya min, ban san ko minene ba, ban san mi wannan abun yake nufi ba”
STORY CONTINUES BELOW
Ya kai hannu ya rika hannunta.
“Kishi ne?”
Ta daga kai ta kalleshi idonta cike da kwalla.
“Ba ni da tabbacin ko minene”
“Ko ma minene ya tafi can ya bar min matata da ita kadai zan rayu”
Hango hasken motar da tai ne yasa tai saurin janye hannunta daga rikon da yai mata taja baya.
“Ina ganin Abbah ne fa”
Sai yai saurin gyara tsayuwarsa. Kusa da 406 dinsa Abbah ta faka golf 3 dinsa ta jigila ya fito rike da bakar leda, yana kawowa kusa da su Sadiq ya risina har kasa ya gaisheshi, ita kuma ta karbi ledar ta shiga da ita. A baki kofar dakin ta tsaya tai gyaran murya irin yadda Abbah yake idan ya dawo gida sannan ta kwaikwayi muryarsa tai sallama.
“Assalamu alaikum”
“Allah ya shiryaki”
Cewar Umma tana girgiza kai. Sai tai dariya ta aje mata ledar ta juya, tana fitowa Abbah na kawowa bakin tsakar gida, sun sun tai da kai sannan ta fice. Hasketa Sadiq yai da motarsa hakan yasa tai saurin komawa sai ya danna mata horn yai ma motar key ya wuce yana daga mata hannu. Cikin daki ta dawo ta zauna kusa da Abbah tana kallon ledar da Umma ke kokarin budewa.
“Abbah mi ka siyo min?”
“Yar lele lemu da abaya ne”
Ya dan bata fuska
“Kai Abbah na fada maka yau agashe nake so fa”
“To yau Katsina muka je, bamu dawo da wuri ba, wannan ma tasha na siyo kar na shigo gidan haka nan”
“To mun gode Allah kara arziki”
Ta fada tana murmushi, tare da kai hannu ta dauka sai Umma ta buge mata hannun.
“Ba na ce ki rika jira ana baki abu ba”
“Ka gani ko Abbah sai ta rika min abu kamar ba Babana ya siyo ba”
“Kyaleta ai sabuwar Uwa zan kawo miki”
Umma tasa dariya.
“A kawo uku mu zama hudu ai dai ni ce uwargida ba komai”
Gaba dayansu dariya suka yi. Sannan Umma ta tashi dan hada masa ruwan wanka.
Washe gari ma tun da asuba ya bar gidan saboda aikinsa na direbansa ci da yake. Zinneera kam bata tashi ba sai kusan bakwai ta tashi a gaggaucw ta shirya dan suna da lacca 8am. Wani farin lace ta saka da Hijab ta fito rike da jaka da littafai a hannunta.
Nabeel na zaune kusa da makwarara yana wanki baki, sai yasa mata dariya.
“Sannu yar makaranta a rayata jaka a rike takardu a hannu”
“Yes kara a san yanzu Jami’a na ke, na wuce ajin yara”
Ya sake kyalkyalewa da dariya.
“Dan baka sababa, ana ganinki za a ce wannan daga gani yar kauye ce, yar kauyen ma ta can ciki kauye ji wani dress na ki, blue Hijab farin lace chaiii”
Sai ta soma bata rai, sai ta kalli kanta ta kalli Umma.
“Umma kin gani ko?”
“Ke kike kula shi ai, zo ki sha koko ki wuce”
“Eyy tab koko Wallahi State University nan duk yayan manya ne, babu mai shan koko a cikinsu, gaskiya ni ba zan sha ba”
“To zo ga dumame”
Ta buga kafa a kasa.
“Haba Umma dai, ni ba zan sha ba”
“To sai me?”
STORY CONTINUES BELOW
Nabeel ya tambaya.
“Abani dari biyu naje makaranta na karya”
“Idan kina son dari biyu zo nan ki gaisheni, ki risina har kasa zan baki dari biyar ma”
“Dan Allah da gaske?”
Taje ta risina gabansa kamar yadda ya bukata.
“Yaya Nabeel ina kwana? Ya gida? Ya gari ya gagarin gari? Ya office din? Su Umma da Abbah sun tashi lafiya? Ya komai da komai?”
Sai kawai yasa mata dariya.
“Walallaliya tashi ki ban guri”
Ta tashi tana murguda masa baki.
“Ban yafe gaisuwar ba, kuma Wallahi sai Allah ya saka min”
Ta nufi kofar fita daga gidan gaba daya.
“Tafiya zaki yi baki karya ba”
“Ee ni ba zan ci dumame ba ina yar jami’a haba dai Umma”
Ta fice tana ta gunguni. haka ta bi titi fuskarta babu annuri. Ta gabanta ya bi ya wuce yana sanye da vest da guntun wando kansa sanye da facing cap, gudu yake kadan kadan irin na exercise.
“Kai Mutum”
Ta daka masa tsawa. Sai ya juyo ganin ita ce yasa yayo baya daidai ita ya tsaya.
“Baka ganin yadda ka wuce ni kamar zaka bugeni”
“Amman dai ban buge ki ba”
“Eyyye wato har wani gilashin rashin mutumci ka kasa ko? To bari ka ji na fada maka ni a unguwar nan kaf na fi uban kowa tsiwa da rashin kunya, dan naga alamar kamar kai bako ne, ka yi hankali da ni, kuma wannan ba dabi’ar kwarai ba ce ka fito daga kai sai vest sai short wai kana Exercise, ji jikinka duk waje ko kunya baka ji ba? Mtssssss ka ma bata min lokaci ni jami’a zan je”
Ta sa kai ta wuce tana taron Mai Napep ta barshi nan tsaye yana kallon kansa. He see nothing wrong with his dress, a safiya ce kuma ya saba haka sai dai idan nan ne za masa sa’ido. Sai kuma yai murmushi tuna yadda take drama da yan gidansu ashe har a waje za ta iya yin haka.
Har cikin State University ya kai ta ciro kudinshi ta bashi, sannan ta fiddo wayarta ta dake ringing, tai picking.
“Hi Darling”
“Hello Baby”
“Please tell me something tell me something tell me something please”
“I love you”
“Oh gosh..”
Ta zauna bakin wani aji dake kusa da ita.
“I love you too, fatar ka tashi lafiya”
“Lafiya kalau, ya su Umma? Nabeel be taba min ke ba yau?”
“Ya taba, ai kasan kullum sai yayi, na ma bar masa gidan ina jami’a”
Dariya yai sai kuma yai saurin gintse dariyar.
“Babyna da an taba ki kice jami’a ku ne yan 100l”
Fushi tai sai ta kashe wayar, ya raina mata da wayo. Misalin hudu da ta kama hanyar gida, babu ko taro a jakarta dan kudin napep ne ta ci abinci da su a cafeteria, sai dai hakan be hanata tsada mai napep ba ta fada masa inda zai kaita, suna tafe tana nasa fira har suka iso. Bata yarda ya kawo ta har kofar gida ba, ta ce ya sauketa sai ta fita tana fadin.
“Mai Napep ni fa ba zan biya ba, ka yi fira da ni kuma ni matar aurece dan haka ka yi firar kudinka”
Mai Napep din ya yi dariya ya dauka wasa take sai da yaga ta fara tafiya da gaske sannan ya kwala mata kira.
“Ke Malama zo ki bani kudina ko nai miki rashin mutunci Wallahi”
Ta juyo ta dawo.
“Ni zaka ma rashin mutunci? To tsaya”
Ya sa hannu cikin jakarta ta dauko wayarta ta kira Nabeel yana picking ta ce.
“Abban Siyama zo gani nan gurin Dahiru mai nama, dan Napep din da ya kawo ni ya min maganar iska ci, yanzu kuma wai zai taba ni”
“What are you crazy?”
Nabeel ya fada daga can cikin wayar, ita kuma ta kashe wayar tana rawar kafa ta rike kumkuru.
“Ka jira mijina ya zo, zai shuka maka rashin mutumcin”
“Amman ke baki da tarbiya Allah hada ki da warinki”
Ya shiga Napep dinsa ya wuce yana baza mata kura. Sai da daina ganin kurarsa sannan tai dariya ta kama hanyar gida tana kallon yadda hadari ya hadu sama. Ko kamin ta isa har an fara yayyafi da gudu ta shiga gida ko sallamar arziki ba tai ba.
“Allah ya shiryaki ya baki Natsuwa Zinneera”
Cewar Umma ganin yadda ta shigo wani firgi firgi da ita ta jefar da jakar hannunta ta fito da gudu ta nufi bandaki saboda fitsarin da ya cika mata mara. Kamin ta fito daga bandakin han gwace da ruwa kama da bakin kwarya, cikin ruwan ta tsaya tana rawar indiya tana wanka da ruwa sai shafo kanta take da gashin be wuce na fakin ba, tana jujjuyawa kamar wata karamar yarinya.
Duk abunda take yana tsaye jikin windows yana kallonta yana murmushi shi dai tana sashi nishadi for no reason kiriniyarta tana burgeshi, abunda take ko kanenta basa yinsa. Wata uwar tsara aka yi sai gata ta nufi daki da gudu, sai kuma ta dawo da gudun saboda Umma ta korota karta jika mata daki, jikin kofar taje ta tsaya ta durkusa tana ba Umma hakuri tana marairaice fuska kamar zata yi kukan gaske. Wannan karon dariya yai ya jingina da kujerar da yake zaune.
“Umma Wallahi Abbah ya ce na daina tsayawa cikin sanyi”
Ta fada tana marairaicewa kamar zata narke a gurin.
“Ai kin san da tsanyin kika shiga ruwa”
“Fitsari na je yi fa, shine aka sako da ruwa”
Umma ta dauke kaita daga barin kallonta ta maida hankali gurin carbin da take ja a hannunta. Ganin hakan yasa Zinneera komawa cikin ruwan tai ta wankanta har aka gama sannan ta sake tsayawa jikin kofar tana rokon Umma ta bata zanen daurawa, daker Umma ta kukata har ta jefo mata zanen, bandaki ta shiga ta cire tufafin jikinta ta ɗaura zane ta fito, tana dariya abunda tai ɗazun ne ya dawo mata a rai. Da ɗai ɗaya ta shiga shanya kayan tana ta ƙyalƙyatar dariya.+
“Allah yasa dai ba haukace mana za ki yi ba”
Cewar Umma wacce ta fito rike da kwanonin abinci daga dakinta ta kawosu harabar da ake wanke-wanke. Zinneera ta kalleta tana cigaba da dariyar.
“Wallahi Umma yau na kusa haukata mai napep din da ya kawo ni”
“Me kika masa?”
“Kin san ko da na fita ban karya ba, da kudin dawawar na karya na shiga Napep ban bashi kudi ba ina ta fira da shi har muka kawo, sai na ce masa yayi hirar kudinsa, da ya nuna zai min tijira na fira Ya Nabeel na ce gani nan wani zai taba ni, sai ya ji tsoro ya gudu”
Umma ta tsaya kallonta tana mamkin ikon Allah.
“Zinneera anya ke kadai kike kuwa? Ki sa mutum ya kawo ki har kofa gida kuma ki ce ba za ki bashi kudi ba? Anya wannan Makaratar ta ki zata daure ma? Abu kike kamar marar hankali”
“Kin san dai Abbah ya ce a daina ce min mahaukaciya ko?”
Ta fada tana turo baki. Umma ta girgiza kai.
“Addu’a yanzu kuma ban san wacce zan miki ba, Allah ya shiryaki in kina da rabon shiryuwa amman abunda kike ba na masu hankali ba ne, Na san Sadiq da yasan yadda kike a zahiri ba zai yarda ya kawo kudin tambaya a gidanku ba, dan babu wanda zai so auren mahaukaciya”
Har cikin ranta Umma ke wannan maganar dan a ganinta Zinneera bata da cikakken hankali ko kuma tana da aljanu, sam bata mata kallon mutum kamar kowa a rabin mutum take kallonta.
“A haka yake so na ni burge shi ma na ke”
“Aa kawai dai yana fada miki haka ne saboda ba yadda zai yi kuma Allah ya dauki son ki ya saka masa a zuciya, amman mutum mai natsuwa da hankali kamar Sadiq ba zai so mace irinki ba, a gaban kowa kina iya shuka rashin mutunci, mutum ko ya haifi ubanki sai ki cire ta ido ki rakka masa rashin tarbiyarki, kowa kina iya fada da shi a gaban kowa, baki kunya kowa ga rashin kunya kamar ya kasheki, bakar magana ko kamar da ita aka haifeki, abunda kike ko Aleeya da Larai basa yinsa”
“Amman Umma kullum ni kike ganin bana da mutunci, su baki ganin abunda suke min, sai dai ni ko harar mutum nai sai ki ce na cika fitsara ko bani da hankali, Ni bari ma na shirya na wuce islamiya na huta”
Ya karasa tana nufar dakinsu.
“Da yafi miki, shi ma Mai Napep din wani abu yai miki kika zalince, Lahira kyaji da hakkinsa marar mutunci”
Tana shiga ta shirya cikin uniform dinta na islamiya purple, ta dauki jakarta ta rata ta fito tana murzawa fuskarta mai daga bakin kofa. Har ta nufi kofar fita daga gidan bata ji Umma ta ce mata Allah ya tsare ba balle dawo ki ci abincin. Sai ta juyo ta kalli Umma.
“Ba zaki ce na dawo na ci abincin ba ko?”
Ko dagowa Umma ba tai ta kalleta ba balle har ta samu damar amsa mata, ita kuma ta juya ta fita cikin fushi tana ta gunguni.
STORY CONTINUES BELOW
“Umma sai ta dinga ganin laifina, suma mutane idan baka haukace musu ba, ba zasu shafa maka lafiya ba, amman ita bata ganewa, kuma ita ma fa tana da masifar nan, kenan nima ai gado nai”
Tana ta mita har ta isa Islamiyar, sannan ta fara boye boye ganin ana dukan yan latti.
“Kai na fa girma yanzu, jami’a na ke, sai kuma na dinga tsoron bulala no way”
Ta fito kai tsaye ta nufi cikin makarantar inda ake dukan dalibai, malamai biyu ne tsaye a gurin dayan ta sanshi shi yake karantar da su a ajinsu, dayan kuma mutumen da ta ganine dazun da safe yana exercise. Bata bi bayan wadanda ake ma bulalar lattinba ta biyo ta gefe zata wuce ta cikin gate din makarantar, idonta na kansa shi ma ita yake kallo hannunsa rike da bulala, tana daf da wuce shi ya fisgota ta dawo baya.
“Ke kika fi kowa ne? Ba ga sauran nan ba ana dukan yan latti”
“Ina ruwanka”
Bulalar da ke hannunsa ya doka mata, sai da tai tsale, ta bude baki ta sake wata maganar ya sake shauda mata wata, da gudu ta koma inda ta fito tana hararashi.
“Bakin mugu azzalumi, ji mutumen nan daga kawo shi yau yau har ya fara dukan mutane, daman daga ganinsa bakin hanya na san bashi da mutumci. Hmmm kut baka san wace Zinneera ba Wallahi”
Kasa kasa take maganar, ta yadda ita kadai zata ji, shi dai baya jin abunda take fada ya dai hango bakinta na motsi, murmushi yake a zuciyarsa daman he just want to see her sad face, tsiwarta na burgeshi, ko ba komai yasan za su kulla takun saka a tsakaninsu.
Haka ta biyo hanyar dawowa gida, itakam da a mata bulalar latti kara bata je ba, idan ka hadu da ita a hanya tana tafiya sai ka dauka natsatsar yarinya, domin kanta a kasa yake tafiyarta ma a kuntse kamar mai natsuwa. Umma na ganinta tasan za ayi dayan biyu ko dai tayi latti ko kuma ta canja shawarar zuwa makarantar ne, domin ta saba haka.
“Au dowowa kika yi?”
“Umma to na yi latti kuma an kawo wani shegen malami sabo daga fara zuwa sai dukana yake”
“Idan ba ki yi abun duka ba zai dakeki ne? Ke dai kam Allah ya shirya ki, duk yarinyar da ke da shekara goma sha bakwai ta san ciwon kanta, zaka tana abu kamar sauran mutane amman ban da ke, kinji haushi kikam”
Bata ce komai ba, ta jingina jikin kofar tana wasa da hannun jakar da ke ratayi a kafadarta. Ji take kamar da ta kai tsakar gidan Umma rufeta zata yi da duka.
“Umma yunwa na ke ji”
“In kin ga dama sai kije ki dauki abincin ki ci”
Da sanda ta wuce dakin dafa abinci ta dauki abincin ta fito ta shige dakinsu.
Be tashi daga makarantar ba, sai shida yau shine zuwansa na biyu a makarantar tun da ya dawo yai requesting yana son ya rika karantar a nan ganin ita ce kusa da shi, domin ya saba a can ma yana karantar a masallaci, tun a ranar suka amince amman ba fara zuwa ba sai jiya da yau. Daga makarantar family house ya wuce daman Abbah ya kirashi tun da ruwan saman suka dauke ya sanar masa cewar yana nemansa akwai inda za su je da magariba.
Sai da yai sallah a masallacin da ke unguwar Lodge road sannan ya shiga gidansu, as usual falon Momy ya fara wucewa, yana shiga sanyin ac da kamshi mai dadi suka yi welcoming dinsa. Babu kowa falon sai tv dake ta aikinsa.
Saman sofa ya zauna ya kai hannu ya dauki hot tea da ke cikin mug ya kai bakinsa yana murmushi kama ganinsa kasan hankalinsa yana wani gurin ne.
“Miya saka murmushi haka”
Ya dago ya kalli Momy wacce ta fito daga bedroom sanye da farar atamfa, hannunta rike da da gilashinta.
“Evening Mom”
“Evening favorite, tell me what the secret?”
Ta fada bayan ta zauna. Sai ya fadada murmushinsa.
“You know i won’t lie, actually wata yarinya na daka a makaranta hakan ya sani farinciki”
“What how?”
“The story is like this, ina son fushinta, tana da wauta ga ban dariya, ga jan magana, ga fada, ga rawa ga karatu ga waka ta iya yi akwai tsiwa, Mom everything about is perfect, dazun ta tare ni tana min tsiwa wai na wuce ta kamar zan takata saboda ina exercise, 0-1 kenan yanzu kuma ta yi latti a islamiya na zaneta kin ga 1-1 kenan, and i know dole zata yi wani abu dan ta rama”
“Wow what a super story you have ever told, so tell me did she know you have crush on her”
“What, no Mom she’s under 20, and we are… I don’t even know her name”
“Really, a ina take?”
“A nan unguwar ta ke”
Momy ta yi murmushi.
“I don’t care if she’s from a rice family or poor, all i care is my favorite has crush on her…”
“No Mom… You got me wrong”
“Everyone can got you wrong except your own Sweet Mother, i know who’s my son. So kaje ciki Daddy ka yana son ganinka zaku je gaishe da Gwaggonka, idan kun dawo zamu yi magana da kai”
“Ba zan dawo ta nan ba”
“Fine”
Ta fada tana daga kafadunta fuskarta da murmushi. Sai ya mike tsaye yana fadin.
“Mom baki fahimta ba, i… I… O.. ”
A haka maganar ta makale ta ki fito har ya fice daga falon. Momy ta bishi da kallo tana murmushi.
“Dawowarka ta yi rana kenan, Favorite you can’t deny it”
Gilashin da ke hannunta ta saka a idonta ta matsa ta dauki mug din da ya aje ta soma sha…
COMMENT SHARE.Tun da tai kwaliyar take ta faman fifita a fuskarta, wai kar tai gumi duk iskan fankar dake dakin be wadatar da ita ba. Ita dai kar tai gumi kwalliyarta ta goge Abubakar (Sadiq) be zo ya gani ba, ta yi jiran kiran wayarsa har ta gaji be kira ba, Nabeel sai dariya yake mata shi da Aleeya. Ita kuma ta cika kamar ta fashe dan takaici, baro musu dakin tai ta nufo gurin icen guava ta zauna ta soma kiran Abubakar a wayarta ganin har tara na kokarin wuce bata be zo ba. Ringing daya ya dauka.+
“Hello Baby”
“Mai sunan Baba miya han ka zuwa yau?”
“Wallahi Baby ba ni da lafiya, Fever ya rufeni yanzu haka kwance nake sanyi na ke ji”
“Innalillahi Wa’inna ilaihiraji’un, Subhanallahi ka sha magani?”
“Ee na sha”
“Ko na zo na duba ka?”
“Aa ba sai kin zo ba, ki yi zamanki anjima kadan na san zai sauka”
“Allah ya sauwake”
Ta aje wayar ba dan ta gamsu da sauki ba, a take ta soma jin kamar ita ce bata da lafiyar, hankalinta duk ya bi ya tashi. Ji tai bata da natsuwa indai bata je ta duba lafiyarta ba. Amman kuma bata da kudin mashi kuma ta san dare ne yanzu gata da tsoron dare. Tashi tai ta nufi dakin dakin Umma, agogon dakin ta fara kallo tara da yan mintuna ya nuna mata, daman ta san indai Abbah ya wuce tara to ba zai dawo ba sai sha daya ko sha biyu wani lokacin ma har karshe daya yana kaiwa idan ya dauki passengers na nesa. Jikin kofar ta tsaya tana ma Umma magana kamar wata munafuka.
“Umma wai Abubakar ya ce na siya mishi kwai da kwai (awara) kamin ya zo”
Umma ta jiyo ta kalleta.
“Abubakar din ne ya ce a siya masa awara?”
“Ee”
“Zo bude aljihun gado ki dauko naira dari ki siyo masa”
Cike da jindadi ta karasa gurin da Umma ke ake kudi ta bude ta dauki naira dari kamar yadda ta fada mata sai ta dawo dakinsu ta dauki katon Hijab dinta ta saka, ta zura talkamin roba ta fice da sauri. Bakin titi ta fito ta tari mai Napep wandabke dauke da mutum biyu.
“Alu quarters zaka kai ni”
“Dari biyu”
“Kai Wallahi dari ne, dan Allah ka taimaka ko babakin Titi ne ka aje ni sai na karasa da kafa, dan Girman Allah ka taimaka min”
Girman Allah data hada shi da shi ne yasa ya ce ta shigo, suka kama hanyar daman mace daya a can za a sauketa dayar kuma a Badoo. Idonta ta mayar gurin titi amman hankalinta na can gurin Abubakar zuciyarta nata raya mata irin halin da yake ciki. A kusa da gidansa aka ajeta kasancewar gidansa na kusa da titin ne.
“Na gode”
Sannan ta cire takalminta ta zura da gudu saboda duhun da ke gurin, @360 ta isa bakin kofar gidansa. Ta shiga buga masa da karfi kamar wacce tai sata aka biyo bayanta, sam hankalin be bata ta kira shi a waya a sanar masa tana waje ba. Kamin ya bude mata har ta fara kuka, dan har ga Allah gani take wani zai zo ya mata wani abun ne a nan. Sai da ya bude haskem falonsa ya hasko waje, be gama tantance ita din ce ko bata ita ba har sai da yaga ta shigo da sauri tana haki.
“Baby mi ya kawo nan?”
Ya tambaya bayan ya maida kofar ya rufe. Sai ta soma sosa kai.
“Ba ka ce baka da lafiya ba”
“Amman ai na ce karki zo, ya akayi ma Umma ta barki kika zo?”
“Bata san na zo ba, karya nai mata”
“To kin koma yanzu tun da kin ganni, idan wani ya ga shigowarki a unguwar nan ma ai sai yai mana wani zargi”
“Amman ai ba komai zamu yi ba, mu ba yan iska ba ne”
STORY CONTINUES BELOW
“Ba kowa ya san da hakan ba, idan aka ga mace da namiji sun kebe sai a yi musu daukar yan iska, ki koma gida yanzu”
Ta taba fuskarsa.
“Ka ji sauki?”
“Eh na ji sauki”
“Ka ci abincin?”
“Ee na ci”
“Ko na dafa maka”
“Haba Baby dan Allah ki wuce gida mana”
Ya nufo kofa ya bude mata.
“Amman tsoro ma ke ji, ka raka ni bakin titi”
“Ina rakaki za a ce an ganni na fito tare da mace na raka titi”
Ta dan bata fuska.
“Amman ni tsoro na ke ji”
Sai ya saki kofar ya dawo inda take tsaye yana mata magana a hankali.
“Yanzu Baby in ban da yautarki karfe tara da rabi na dare za ki baro gidanku ki zo nan haba Baby”
“Na dauka sosai ne”
“Ko sosai ne be kamata ba tun da ba aure muka yi ba, yaushe zaki fara banbance abu mai kyau da marar kyau ne, ya kamata ki rika tunani irin na mutane mana”
“Na ji tsoro sosai ne, har jin nai kamar nice bani da lafiyar ma”
Ta fada hawaye na sauko mata. Ajiyar zuciya ya sauke a hankali.
“I know you care for me and i care for you too, amman abunda na ke ina kokarin tsiratar mana da mutunci mune ba wai ina kokarim korarki ne dan wani abun ba, yi hakuri ki yafe min, zo muje ciki ki zauna”
“Aa ni zan tafi indai tafiyana zai saka farinciki zan tafi, amman ka kula da kanka kanji? Kuma ka ci abinci ka sha magani”
“I will i promise you this, i love you”
Ta saki hannunsa ta nufi kofar ta bude tana ta waigensa har ta fice. Shi kuma ya nufi gurin kujera ya zauna, a nan wani tunanin ya zo masa, idan wani abun ya sameta fa? Ko wani ya tareta a hanya ga gurin da duhu, da wani abu ya sameta kara a ganshi da ita inyaso ayi masa duk zargin da za a masa. Saurim tashi yai ya bude kofar cikin rashin kuzari irin na marasa lafiya ya fiton waje amman ko kufanta be gani ba. Ciki ya koma ya dauki wayarsa ya kirata zuciyarsa cike da tsoron abunda zai sameta. Tana dauka yaji hayaniyar ababen hawa hakan yasa shi jin natsuwa.
“Kin kai titi”
“Ee na kai gudu nai”
“Akwai mutane a gurin? Kina jin tsoro har yanzu?”
“Aa nan akwai mutane ai da abun hawa”
“Okay take care of yourself, i love you”
“Thank you”
Ta kashe wayar, tana ta tunanin yadda zata koma gida, tun da babu ko sisi a hannunta kuma ta san yanzu dare ne idan tai mai adaidai wawanci yai mata sakarci asirinta ya tonu a gida.
*** *** ***
Ko da ya shiga part din Daddy sai suka dauko wata hirar basu fita ba sai bayan sallah isha’i, Daddyn ya shiga motarsa dan Sadam ya fada nasa cewar daga can gidansa zai wuce. Alu quarters suka nufa gurin Gwaggo Larai, a can suka dade suna gaisawa,tana da fira da Daddy dan Sadam ba wani saninta yai ba, hasalima shi sai yau ya fara ganinta. Guraren goma saura yai mata sallama ita da Daddy ganin firar ta su ba mai karewa ba ce ya kamo hanyar gida.
_What do you do when you cant let go, what do you say when you don’t know how you felt and you know nobody knows how you feel_
Like you by Tatiana manaois. Ita ce wakar da yake saurare a cikin motar, dake cike da sanyin ac da kuma kanshin turarensa mai dadin shaka. Unexpected ya hango Zinneera gafen titi tana tafiya kana ganinta kasan tsorace take, har ya wuce ta sai yai parking gafen titi yana kallonta a nearby mirror har ta iso inda motarsa take sai ya zuke gilashin motar.
STORY CONTINUES BELOW
“Ke zo nan”
Kamar daman can jira kawai take ya kirata, sai ta karawa kafafunta mai, hakan yasa shi saurin fitowa daga motar ya cire facing cap din dake kansa.
“Kidan ba ko zo nan, idan kika je makaranta gobe sai na zaneki sosai”
Jin hakan yasa ta dan tsaya ta juyo dan ganin ko wanene. Mutumen nan ne na makarantarsu kuma na unguwarsu. Dawowa tai inda gurin motar ta tsaya.
“Ke da wa kika zo nan?”
“Ni kadai”
Ta fada tana dan turo baki.
“Ina zaki je yanzu?”
“Gida”
“Shiga mota muje”
He said, kind of commanded her. Daman tana neman wanda zai kaita gida duk da kasancewar bata san halinsa ba. Sai ta bude motar ta shiga front seat ta zauna. Shi kuma yai motar key suka hau titi yana tafiya a hankali kamar baya so su saurin isa gida. Sai da suka yi dan nisa sannan ya kai hannu ya rage volume din wakar dake tashi.
“Ina kika fito”
Ya tambaya ba tare da ya kalleta ba.
“Gurin saurayina”
Hakan yasa shi kallonta da kyau, sai kuma ya dauko facing cap dinsa ya saka a kansa.
“Amman ba komai muka yi ba, ni ba yar iska ba ce shi ma kuma ba dan iska ba ne, kawai na je duba shi ne bashi da lafiya”
Yayi shiru kamar ba zai sake tambayar komai ba.
“Gidanku an san kin zo?”
“Aa ba a sani ba, kuma daman bama da na komawa da kasa zanje”
Dariya yai sai dai ko kadan be kalli inda take ba. He was imagining yadda zata ta kai kanta tun daga Alu quarters har Abdullahi fodio road da kafa.
“Yanzu idan iyayenki suka ji ko kuka ganki kin fito gurin wani me zaki yi?”
“Fada musu za ka yi?”
Ya daga kafadunsa yana dan mire baki.
“Nima ban sani ba, amman shi ya ce ki zo?”
“Aa fada ma yai min, wai na koma kar mutane su gani”
“To me zaki fadawa iyayenki idan sun ganki?”
“Kai me matarka za ta yi idan ta ga ka dauko ni?”
“Ni ai ba ni da mata, idan kuma kina so na shikenan”
“Aa ni ina da miji”
“Wacan ai ba miji ba ne, duk wanda zai kira mace kamarki ta iskoshi ai ba miji ba ne”
“Wallahi shi ba dan iska ba ne, kuma ba shi ya kirani ba, ni na je da kaina, karka sake ce masa dan iska”
Ta fada a tsawace. Sai ya faka motarsa dai dai road din Clapperto road.
“Fitar min daga mota, haka kawai ki min tsawa saboda wani katon banza”
Da taga da gaske yake sai ta koma ba shi hakuri.
“Yi hakuri to”
Sai yai ma motar key ya hau titi.
“Dazun kika ce na wuce ki kamar zan bankeki ko?”
“To baka ga yadda kake guduba ka saka wasu tufafi kana wani tallatar kanka”
Ya lasa lebensa yana wani shegen murmushi.
“Dan iska ne ni kenan?”
“Ni dai ban ce ba”
“To ko dai na miki ne?”
Ya fada yana kallonta tare da daga mata gira, sai ta zaro ido shi kuma ya sake daga mata a karo na biyu.
“Har kofar gidanku zan saukeki”
“Aa fada za a min”
“Sai dai a ayi miki fada, kin san abunda kika yi be kyau kika aikata kuma”
Ya fada daidai lokacin da ya faka motarsa kofar gidan. Sai ta kalleshi.
“Ashe kasan gidanmu?”
Be ce mata komai ba, ya fita ya zagoyo gefenta ya bude motar.
“Fito”
Kamar ba zata fito ba, dan tana tsoro wani ya ganta, sai kuma ta daure ta fito, yana rufe motar yai mata key ta nufi kofar gida. Sai karo tai da Nabeel da ke tsaye yana kallonsu.
“Na shiga uku”
“Gidan Uban wa kika fito? Waye can mutumen?”
“Taimakona yai ya kawoni gida”
“Wuce ciki”
Ya matsa gefe ta ratsa ta wuce cike da tsoro.
“Sai kin fada min gidan ubanda kika je, babu inda ban aika nemanki ba a unguwar aka ce baki nan, sai yanzu zaki dawo karfe goma da ta kwata ina kika ce”
Umma ta tambaya a tsawace irin tsawar nan da ke razanar da yaro.
Sai ta durkusa saman guiyoyinta ta fashe da kuka.
“Abubakar ne ba shi da lafiya shine na je duba shi”
Umma tasa salati.
“Yanzu dan baki da hankali zaki bar unguwa uwa unguwa kije duba namiji dam be da lafiya, Nabeel zo nan sa bulala ka zane min yar iskar yarinyar nan, indai haukace na fiki hauka da wawanci”
Ta karasa tana kwalama Nabeel kira, daman yana tsaye bakin kofa umarni kawai yake jira sai gashi ya shigo tsakar gidan ya doso inda Zinneera take, ita kuma ta saka ihu iya karfinta.Babu inda ba aji ihunta ba, tun Nabeel na dukanta har ta soma bashi tausayin, domin ba dukan wasa yake mata. Babu kalar kukan da bata yi wani zakaji shi kamar na mage wani kamar na kare bayan ta gama na mutane. Mutanen da ke shigowa ne ke ta batawa Umma hakuri akan a kyaleta, bata fadawa kowa gaskiyar dukan da ake mata ba, sai cewa tai wai Nabeel ta zaga shiyasa ya zaneta. Masu bata laifi na ta yi daman ansan halinta indai tsiwace da rashin jin magana ta bata ji bata gani.
A dakinsu tai ta aikin kukanta, tun tana jira Umma ta shigo ta rarrasheta har ta gaji ta hakura dan kanta ta daina kukan. Misalin karfe goma sha daya na dare Abbah ya dawo, tana jin motsin shigowarsa amman bata tashi ba dan tasan bata da gaskiya.
Bayan kamar minti talatin ya shigo dakin a hasale, tana ganinsa tai saurin tashi zauna tana matsar kwalla.
“Ba ni wayarki, wato iskancin na ki da rashin kunya kara yawa yake ko?”
Sai kawai ta fashe da kuka sai a yanzu ma ta tuno da wani zancen wayar data baro a motar Sadam.
“Ba magana nake miki ba”
Wani mugun zabura tai sakamakon tsawar daya daka mata iya karfinshi.
“Ban… San… Ban san….. Inda… Take… Ke.. Ba… ”
Ta amsa cikin muryar kuka kamar zata shude.+
“Wannan wane irin rashin kunya ne, ki taka da kanki zuwa dakin saurayi? Wannan sam ba tarbiya ba ce”
“Wallahi Abbah ba mu komai ba, komai ba mi yi ba, ko dan iskancin da ake ganin kamar mun yi na rantse da Allah ba mu yi ba…”1
“To miya kaiki inda yake…? Shi ya kiraki”
“Aa ni ce naje da kaina, saboda bashi da lafiya ne sai hankali ya tashi”
Wani kallo yai mata irin kallon nan na har yanzu baki da wayo, ya juya ya fice daga dakin. A dakin ta kwana sallah isha’i ma sai can tsakar dare ta fito tai alwala ta koma cikin dakin tai sallah. Da gangan ta bi ta kan Aleeya ta taka mata hannu, haushi kowa take ji a cikin gidan tun da ita kadai aka daka akan laifin da take gani na rashin dalili tun dai ba su yi komai ba.
Washe gari, wuri ta shirya cikin blue atamfa da farin Hijab, amman tai zamanta a dakin ta ki fitowa har sai da Abbah ya fita, sannan ta fito cikin kafarta mai ciwo tana dinshigi, bata jin gaisuwa yau tun da an taba ta jiya da dare, dan haka kawai ta zo jikin kofar Umma ta tsaya tana turo baki kamar ana ja mata shi.
“Umma ba ni kudin makaranta”
Wata uwar harara Umma ta watsa mata sannan ta daga fillo ta jefo mata dari hudu na napep.
“Yau ma ida kinje daga makarantar ki wuce gidanshi”
Bata dai ce komai ba, ta shiga tsakar dakin ta dauki kudin ta fice tana ta gunguni. Bata san Umma ba zata ce mata ta dawo ta karya ba, ko da suna abun arziki ba kullum take ce mata tsaya ki karya ba balle yau da take fushi da ita. Aleeya dai dake aikin gyara wandon uniform dinta ta kalleta ta ce
“Ba zaki tsaya ki karya ba”
Kamar jira take ta juyo kanta fuskarta da hawaye.
“Eh ba zan tsaya din na ci ba, ina ruwanki bakar munafuka, kin jidadi an dake ni ko Allah Sai ya saka min, bakar annamimiya, hegiya mai fuskar an wuta, da wasu hakora nata kamar kasuwar cibabe…”
Fitowar Umma ne yasa ta gintse maganar ba dan ta gama, Aleeya dai ta tsaya tana mata kallon mamaki, ita take neman yi mata abun arziki ta maida shi na fada.
“Halin ne na ki baki fasa ba ko? Yar’uwarki kike cewa mai fuskan yan wuta? Wato duk dukan da aka miki jiya baki natsu ba ko?”1
Sai ta fashe da kuka tana nuna Aleeya.
STORY CONTINUES BELOW
“Umma fa kanwata ce amman ace tana min dariya dan an dake ni, kamar ni ma ace ana dokana Wallahi hakan be yi ba, duk wace ta kai jami’a Wallahi ta wuce duka, ga yan makarantarmu can babu wacce ake dukanta sai ni…”
“Saboda da yan makarantarku suna da hankali da tunani irin na mutane, ke ko baki da ko daya, kuma indai duka ne yanzu kika fara shanshi dan ni da ke mun sa kafar wando daya a gidan nan… Ke shiga ki kira min Nabeel ya zo gata nan ta fara siyar da halin”
Umma ta karasa tana kallon Aleeya, sai Aleeya ta nufi dakin tana kiran sunansa, Zinneera na ganin hakan tai saurin saka kafarta ta fice daga gidan tana dingishi da sharar kwalla kamar irin yarinya an daketa din nan. Da gudu Aleeya ta fito daga dakin tana kiran sunan Umma.
“Umma Ya Nabeel ba zai iya tashi ba, kin ga bayansa duk buloli kamar an bashi kashi”
“Innalillahi Wa’inna ilaihiraji’un”
Umma ta fada sai duk suka dunguma sukai dakin, kwance suka same shi ruf da ciki jikinsa ba riga sai tambarin bulalo kamar wanda aka kwana a duka.
*** *** ***
Sai da tai nisa da gidansu tana kokarin taron Napep sai kawai ta ga Sadam gabanta sanye da short da vest kamar dai jiya, sai facing cap dake kansa da Earpiece dake makkale a kunnensa.
“Good morning pussycat, miya samu Ƙafarki?”
“Ban sani ba”
Ta fada kai tsaye. Ya dan bata fuska kamar yadda tai yana marairaice murya.
“Haba fada min mana”
“Na ce ban sani ba, ai lokacin da ka kawo sai da na ce maka ka aje nesa da gida amman ka ki, sai da kasa a aka dake ni, kuma ba ni wayata da ka sace”
“Nifa ban satar miki waya ba, kawai dai sai da na isa gida na ganta kuma ba damar na dawo dan dare yayi sosai”
Ya mika mata wayar. Sai ta karba tana hararrarshi.
“Ko kunya baka ji wai kai ta tallar tsirarcinka, ji yadda kake yawo a unguwa”
Ya kalli kansa ya kalleta.
“Ke dai ko kin loba ne, kin ga ruwan da ke miki bula”
“Ba ruwan da ke min bula ba, ruwan da ke min ja”
Ta fada tana shiga cikin Napep din. Sam bata lura da wayar bata da sim ba sai da ta isa scul ta dauki wayar da zimmar kiran Abubakar sai taga babu layi ciki.
“Lallai ma wannan yaron wato cire min layi yai ko? Kam uban nan aiko yau zan maka rashin mutunci…”
Ta fada cike da mugun jin zafin abunda yai mata har tana jin kamar ace yana kusa da ita ta shuka masa rashin mutuncin nata.
“Hmmm baka san wacece ba, yaro kana wasa hmmmm”
Ta nanata hakan ya fi a kirga, duk ta cika ta batse fuskarta babu annuri. A haka ta shiga lacca sai sha daya suka fito, tana jin wata iri matsanaiciyar yunwa, amman ba damar siyen abinci tun da bata da kudi sai na komawa, cikin dari biyu ta komawa gida ta yanke shawarar siyen pure water na biyar. Daga inda take zaune ta kira yaron dake dauke da kular ruwa saman kai.
“Kai zo nan”
Sai da yaron yanzo ta aje littafan hannunta.
“Suna da sanyi?”
“Eh taba ma jiki”
Yaron ya fada, sai ta ta dauka ta shanye daya sannan ta mika masa dari biyu. Ya karba ya saka hannunsa aljihun ya ciro kudi ya kirga dari da casa’in ya mika mata.
“Kai nawa zuwan suke?”
“Goma”
“Wallahi ba zan siye su goma ba”
Yasa hannu ta canke dari biyunta ta watsa masa canjinsa. Yaron ta rashi ya kwashe kudinsa ya saka aljihu, sai da ya dora kular ruwan akai sannan yai mata Allah ya isa!
“Kam uba ni zaka yi ma Allah ya isa? ”
Aiko da sauri ta mike tsaye ta ture kular ruwan da ke kansa ta fadi kasa, sai yaron ya fashe da kuka, nan take hankalin kowa ya dawo kansu, wata yar ajinsu ta nufota tana tambayar ba’asi.
“Sis miya faru?”
“Wai Pure water zai siyar min a goma, na ce ba zan siya haka ba shine yake min Allah ya isa”
“Ai yanzu hka ake siyar da ruwa ko’ina, bari na bashi”
Yarinyar na sa hannu a jakarta sai Zinneera ta riketa.
“Wallahi ba za a bashi ba, tun da yai min Allah ya isa”
“Amman ke ba ki da mutunci ne, duk siyen ruwan da kike baki taba sanin goma suke ba, sai da kika shanye ruwan yaro za kice ba zaki biya ba, kuma za a biyashi ko ce ba za a biya ba, bayan kin gama ture masa ruwan a kasa”
Wani matashin saurayi ya fada. Sai ta watsa masa harara.
“Eh ban da mutunci, sai ka je ka dauko na gidanku ka ara min, kai kana da mutunci zaka tsoma bakinka cikin fadan da ba naka ba”
A take ya wanke mata fuska da mari, aiko wani irin tsale tai ta dire kamar ba mai ciwo a kafa ba, ta dafe kunci tana wani irin ihu, a take ta cire Hijabinta ta sha damara ita ala dole sai ta rama, ana rikonta yana son ta kubuce tai dambe da da namiji…“Innalillahi Wa’inna ilaihiraji’un”3
Shine abunda Umma ta fada ganin irin kwancin bulolin da ke bayan Nabeel.
“Miya same ka Nabeel?”
Umma ta tambaya idonta na cika da hawaye zuciyarta kuma cike da al’ajabi. Daga kwance da yake rub da ciki ya soma magana a wahalce.
“Wallahi Umma dukana akai jiya da dare har garin Allah ya waye”
“Waya dake ka?”
“Wallahi Umma ban sani ba, amman jiya ban yi bachi ba, dukana akaita yi har safe, kamin a dake ni din ma sai da akai ta kaini sama ana sakoni ina faduwa, ina ta ihu amman babu mai jina, daga baya kuma na gan ni cikin daji mai duhu ga kura da zaki sai sun zo kamar za su cinye ni sai na gan ni a dakin nan, sai kuma na kara ganina can sai kuma na gan ni a nan, babu kalar ihun da ban yi ba amman babu mai jina, daga baya kuma nai ta jin kamar an dannemin kirji na kasa tashi sai dagani ake sama ana jefowo da na fado kife shine akai ta dukana a baya har safe, Wallahi Umma jikina ko’ina ciwo yake ko motsi bana iya yi”1
Ya fada hawaye na fito ta gefen idonsa. Umma ta zauna kusa da shi tana kallon bayansa.
“Kai ka cire rigar daman? Wannan abu ko gamo kai”
“Ni ina zan sani, ko Sallah asuba zan yi ba”
Ya amsa a wahale. Aleeya kallon tausayi take masa, a dayan bangaren kuma tana dariyar yadda yake raki rabon da ta ga hawaye a idonsa har ta manta, ta san halin yayan nata mugune na karshe indai aka ce dukansu zai yi ba ya musu da sauki, musamman idan aka ce Zinneera zai doka, amman yau gashi shi ma ya sha dukan ya ji yadda suke ji, wani karin abun dariya ma babba da shi amman an masa wannan dukan har da su hawaye lallai ta san ba karamin duka ya sha ba.+
“Sannu Ya Nabeel, gaskiya ka ji jiki”
Umma ta rafka uban ta gumi tana fadin.
“Ina ganin gamo kai?”
“Ni na fi tunanin ko dan na da….”
Sallamar da akai ne ya hanashi karasa maganar. Daga cikin dakin Umma ta amsa Aleeya kuma ta fita tana amsawa.
Wasu yan mata ne su uku dayar na sanye da abaya, sauran biyu kuma na sanye da gown din atamfa.
“Abubakar ne ya kawo mu, zamu gaisa da Zinneera ne, mu kanensa ne”
Dayar ta fada wacce ke sanye da bakin gilashi.
“Okay, amman Zinneera bata nan ta tafi makaranta sai dai idan ta dawo”
Umma ce ta fito tana musu lale martabun.
“Sannunku da zuwa, ku shigo daki mana”
Sai duk suka gaisheta. Wacce tai magana dazun ta sake cewa.
“Aa mun gode, Abubakar yana waje yana jiranmu, sai dai in mun dawo”
A tare suka juyo suka fito daga cikin gidan, sai suka samu Abubakar tsaye jikin motar yana jiran fitowarsu.
“Wai bata nan ta tafi makaranta”
“Kai amman Babyna tayi saurin zuwa gashi na kira wayarta kashe, muje na kai ku makarantar sai ku gaisa a can”
Ya bude motar ya shiga, sai suma suka shiga yai mata key, yana driving suna fira har suka isa State University. Department dinsu ya nufa ko da yaje ya samu ta shiga lacca hakan yasa ya dawo ya fada musu ta shiga class.
“Kun san yadda za ayi? Ku bari sai anjima na san lokacin ma ta koma gida sai muje can ku ganta”
“No Yaya ni zan bar garin nan 12, sai dai mu dawo ko zuwa goma ko sha daya, dan gaskiya ina son na ga matar nan ta mu, labarinta kawai muke sha ya kamata dai yau mu ganta face to face tunda mun zo garin”
STORY CONTINUES BELOW
“Okay no problem”
Ya fada yana daga kafadunsa. Cikin motar ya koma ya maida su gida, shi kuma ya koma gidansa da ke Alu quarters ya shirya ya wuce office. Misalin goma da rabi suka sake kiranshi sai yaje ya dauko su ya nufo scul din da su.
Department din ya sake nufa ganin dalibai a waje yasa jindadin sai rabon ido yake ko zai ga babynsa, but unfortunately sai hangota yai ana rikonta kanta ba dankwali Hijab dinta a kunkuru tana tsalle sai ta riko wani. Da sauri ya karasa gurin sisters din suna biye da shi.
“Lafiya miya faru?”
Shine abunda ya tambaya sai daya daga cikin matan da ke rikonta ta fada masa abunda yake faruwa. Hannu ya mika ya rikota yana girgiza ta.
“Zinneera Zinneera”
Sam bata jin abunda yake fada, kuka kawai take kamar wata karamar yarinya.
“Marina yai marina yai wayyo Allah”
Shine kawai abunda take fadi. Sai ya saketa ya juya gurin mutumen cikin bacin rai.
“Amman kai wawa ne Wallahi ina ruwanka da abunda ke tsakaninta da yaron ko dukansa tai ina ruwanka da zaka saka hannu ka mari mace dan kana katon banza”
“An mareta zo ka rama mata idan ka isa, ku kuke daure mata gindi tana yi ma mutane iskanci kala kala ko? To Wallahi sai na ci ubanta cikin makarantar nan matukar bata canja hali ba”
Ana rufe masa baki yana fadar hakan, wani kallo Abubakar yai masa, ba zai biye shi ba dan a akwai kurciya a yanayinsa amman har ga Allah ya ji zafin marin da yai ma babynsa, malaman ne suka shiga fadan akai ta ma yaron fada daga baya kuma aka dawo gurin Zinneera, Abubakar ala ala kawai yake kar ta zagi wani daga cikin malam.
“Ba ya ci sai ya ci ubana ba? To ya zo ya ci ubana zan rakashi na bashi mai da yaji”
Ta fada tana kwance Hijab din dake kugunta ta saka. Sai Sadiq (Abubakar) ya kama hannunta ya jata zuwa gurin motarsa, wannan friend din tana tana biye da su a baya rike da jakar Zinneera, sai da suka kusa isa sai kawai ta bankare tai baya kamar zata fadi sai da ya riko.
“Yanzu fa ya sha marin banza, ya mareni a banza”
Ta fada cikin wata irin murya tana numfashi kamar wacce za a cirewa rai. Zaunar da ita yai a gurin ya rika fuskarta.
“Za a rama miki trust me”
“Wa zai rama min?”
“Za a rama miki ki yarda da ni kawai, yi hakuri ki daina kuka gaban mutane kar a mana dariya kinji Babyna”
Kai ta gyada masa ta share hawayenta. Sannan ta tashi tsaye ya bude mata front seat ta zauna ya karbi jakarta dake hannun yarinya ya saka mata a ciki, sisters dinsa suka shiga baya shi kuma ya shiga mazaunin direaba yaja motar.
“Yaya wannan ita ce matar da zaka aura?”
Daya daga cikinsu ta tambaya tana tsire baki, Sai Zinneera ta juyo ta kallesu daman ta gansu tun dazu amman hankalinta be bata ta tambaye shi su waye ba ko ta tsaya ta tantacesu ba sai yanzu.
“Eh ko wata zaki canja masa?”1
“Gaskiya dai baki dace da shi ba”
“Ai sai ki nemo masa wacce ta dace da shi, kuma Wallahi ko kina so ko baki so sai na aureshi sai dai ki mutu”1
“Wallahi ba zaki aureshi ba, dan Yayanmu ba zai auri marar tarbiya ba”
“Kam uban nan, ni ce ba ni da tarbiya? Wallahi bari mu fita cikin motar nan sai na miki shegen duka”1
“A haka za ki min dukan ai ko da jijjiga kurna ta fi magarya, marar hankali kowa”
Sadiq ya taka burki da karfi ya faka motarsa gefen titi, ya juyo ya kalleta.
STORY CONTINUES BELOW
“A gan idona zaki kira Zabin raina, marar hankali marar tarbiya? Fitar min a mota”
Ya fada a tsawace, ba ita kadai ba su duka suka bude motar suka fita, ba tare da damuwa ba yai ma motar keys ya hau titi tare da rikon hannun Zinneera.
“Babyna dan Allah ki rika natsuwa irin abubuwan nan da kike ki daina bana so”
“Yanzu ba gabanka ta kirani mahaukaciya ba”
“Da baki yi abunda kika kai ba, ai ba zata kira ki mahaukaciyar ba, ba zan lamunci kowa ya fada miki magana marar dadi ko ya ci zarafinki ba, amman dan Allah ki daina halayen nan please”
Ta fisge hannunta.
“Fine kai ma kana ganin bana da hankali ko? Sauke ni bana son ka kaini gida”
Sai ya kalleta cikin damuwa.
“Daga magana? I’m sorry”
“Ni dai ka sauke ni kawai”
Be sauketa ba, be kuma sake ce mata komai ba sai da ya isa cikin unguwar sannan ya sauketa kofar gidansu. A kufule ta bude motar ta fita, shi dai da kalli ta bita har ta shige gida sannan ya sauke ajiyar zuciya ya tashi motar.
Da tsingilta ta shiga gidan tana sallama can cikin makoshinta. Daga Umma da ke wanke wanke har Nabeel da ke wance karkashin itaciyar mangoro be dago ya kalleta ba. Dakinsu ta wuce ta aje jakarta sai kuma ya fito ta nufo inda Umma take ta risina zata karbi wanke wanke.
“Kawo na wanke”
“Tashi tashi kar raina ya bace”
Da sauri ta tashi tsaye dan ta san halin Umma idan ranta ya bace duk abunda ke gabanta zata iya dukanta da shi.
“Umma yi hakuri dan Allah, ba zan sake zuwa gidansa ba, jiyan ma saboda na duba lafiyarsa ne dan Allah ki yi hakuri”
Sai a lokacin Umma ta dago ta kalleta.
“Da karki yi da ki yi duk uwarsu daya Ubansu daya a gurina, ni dai na yi budurcina lafiya na kare babu wanda ya taba kuka da ni, idan ma kika je kika kwaso abun kunya ke ta shafa ba ni ba, tun da na haife ki Zinneera ban huta ba tun kina karaka kullum cikin kawo min kararki ake, yanzu kuma da kika girma kina son hawan jininki ya kasheni, duk yarinyar da ta kai kamarki ta san ciwon kanta tana da hankali ta san ciwon kanta amman ban da ke, kullum haukarki kara yawa take, Wallahi ke kan kinji haushi rayuwa…”
Ta bata fuska sosai, ita a rayuwarta bata ganin abunda take as rashin hankali ko rashin natsuwa, ita dai a daidai take ganin take.
“Wuce gidan Maman Ramatu ki karbo min kudin adashena”
Umma ta fada mata tana hararta. Ita kuma ta cira kafarta ta nufi kofar fita ranta na sosuwa da bakaken kalaman da Umma tai mata.
*** *** ***
Dariya yai yasa yatsansa yana zagaye bakin mug din dake cike da tea.
“Allah Mommy I’m jealous, jiya fa kamin na cire layin kira uku yai mata raina ya ba ce sosai”
“Favorite ana kishin mace ba tare da ta sani ba? Baka tsoron tai maka fada idan ta ga ka cire mata sim?”
“Ai fadan nake son tai min ni tsiwarta tana burgeni sosai”
“Yanzu ka yarda na fika gaskiya ko? Ta tabbata son ta kake”
Mikewa yai tsaye yana dariya ya nufo downstairs, a nan ya samu kansa a harabar gidan, domin falon da dakin da komai na gidan a sama suke.
“Na yarda ina kishinta”
“Ka yarda son ta kake, duk mace da kake jin dadin ganinta take burgeka to son ta kake, kuma idan baka sonta mi zai kawo kishin?”
STORY CONTINUES BELOW
“Shikenan sonta na ke”
Daga can cikin wayar Momy tai dariya.
“Wannan kam, anjima ka zo Daddynku ya ce zai kuje gurin wata gwaggonku”
Ya nufi gate yana fadin.
“Oh Daddyn wai su dangin nan basa karewa ne, tun na dawo kusan kullum sai munje wani gurin”
“Ai gwaggwanin ne naka da yawa, kuma kai baka sansu ba shiyasa yake son kana zuwa kasan halin babanka da son danginsa”
“Okay zan zo… Oh my God Mommy gata nan tana zuwa”
“To a gaishe min ita, kamin mu aiko gidansu”
Dariya yai ya kashe wayar yana jan gate din. Murmushi yake yana kallon kafafuwanta kamar mai kirga takun da take, kanta na kasa hannayenta cikin Hijab idan ka hango kamar mai cikakkiyar natsuwa.
Sai da ta iso kusa da shi sannan ta daga kai ta kalleshi.
“Ina sim dina da ka cire?”
Ya rumgume hannayensa, yana cigaba da kallonta cike da burgewa.
“Ni ban daukar miki sim ba”
Har ta zaro ido zata masa masifa sai kuma ta danne zuciyarta, tana ta kokarin ganin ta zama yarinyar kirki kamar yadda Umma ta ke so.
“Dan Allah ka bani abuna, ku kuke min abu amman idan na yi fada a rika cewa ba ni da hankali”
“Waya ke cewa ba ki da hankali?”
Ya tambaya yana kallon lips dinta, yana lasa lebensa.
“Kowa haka nan yake cewa wa bani da hankali bana ni da mutunci”
“Duk wanda yake ce miki hakan nan, be san kimarki ba ne, amman abunda kike babu rashin hankali ciki ni burgeni ma kike?”
“Da gaske?”
“Amman har Sadiq cewa yake na rika yim abu na masu hankali”
“Waye Sadiq”
“Wanda zan aura”
“Wannan dan iskan da kika je gani? Shine ya kira ki dakinsa ko?”
“A a, ba shi ya kirani ba fa, ni naje dan kaina gashi nan ma sai da aka saka Ya Nabeel ya dakeni, kuma yau wani ya mareni a makaranta”
“Me kika masa?”
Ya tambaya da serious face. A take ta zayyana masa abunda ya faru har ya kai ga ya mareta, da kuma dukan da Nabeel yai mata, ya ji haushi sosai a take ya fusata har jin yai kamar ace a gabansa ne.
“Fada min waye ubanshi a garin nan da zai saka hannunsa ya mareki?”
“Ban san waye shi ba”
“Ki bincika cikin makarantar ku sunansa sunan mahaifinsa da kuma unguwarsu”
“Me zaka masa?”
“Na rama miki mana, ko baki so”
“Ina so?”
Ta fada da far’ah, tana waigen bayanta.
“Bari dai inje inda aka aike na na dawo”
“Fada min sunanki”
Ya tambaya yana kallon kirjinta.
“Zinneera”
“Ni kuma Sadam Sadam Adamu Kazaure”
“Sunan wani kawonmu mu Alhaji Adamu”
Yayi murmushi.
“Na nan gidana ne idan kin dawo ki yi knocked sai na fito”
Ta daga kai tana kallon katon gidan.
“Laaa kai ke da gidan nan, amman ana cewa babu mutane a ciki, ashe ma kusa da mu kake kana da mata hala?”
“Aa sai dai in na aureki”
Mtsssssss taja wani dogon tsaki.
“Kai ni fa nina da miji ko dan ja ganni haka ka dauka bani da miji ne?”
Dariya yayi ya bi bayanta da kallo, har sai da ta karya kwana sannan ta juyo ya dawo cikin gidan.
“Za’a rama miki yarinya babu wanda ya isa ya tabaki yanzu kam”
Stairs din ya taka ya shiga falonsa, hannu ya mikawa yarinyar da ke zaune saman kujera, sai ta taso ta nufo inda yake tana wani irin karairaya, kamin ta kawo kusa da shu ya hade yawun bakinsa sau hudu, sannan ya saka hannunsa ya rika kunkurunta yasa babban yatsansa yana wasa da gefen fuskarta, sai kuma ya saka mata yatsan a baki kamin ya cire ya hade bakinsu….Da sallama ta shiga gidansu Maman Ramatu. Sai da suka gaisa sannan ta fadawa mata abunda ya kawo ta.
“Wai Umma ta ce na zo na karba mata kudin adashe”
“Allah sarki, ai nasan ta yi hakuri kudin ne har yanzu ba a hada ba Wallahi, ki ce mata tai hakuri idan na hada kudin zan aiko mata”
“Tau”
Ta amsa tana juyawa da zimmar tafiya.
“Sai anjima”
“To a jima da yawa”
Tana fitowa kofar gidan sai ta ga Sadam tsaye yana kallonta fuskarsa da murmushi, ta yi mamakin ganinsa sosai bata dauka yana nan yana binta a baya ba.
“Biyoni kai?”
Ya gyada mata kai, sai ya mikamata sim dinta dake hannunsa.
“Na gode”
Ta fada bayan ta karba. A nan ma kan ya gyada, sai kawai ta kama hanya rike da sim din shi kuma yana tsaye a gurin yana kallonta. Har ta bar kwanar gidan bata waigo ba, ba macece mai tafiya tana yawan waige waige ba, tana maida hankalinta a gabanta idan tana tafiya, wannan yasa mutane suke mata kallon mai hankali da natsuwa.
Da sallama ta shigo gida murya can kasa kasa, Umma ta amsa mata ba tare da ta dago ta kalleta ba.+
“Umma ta ce wai kudin ba su hadu ba, kiyi hakuri idan sun hadu zata aiko miki”
“Tau”
“Umma baki raba abinci da ni ba?”
Ta tambaya kalar tausayi.
“Na raba da ke amman nan gaba kadan zan daina dafa abincin da ke, dan ba zan cigaba da ciyar da mahaukaciya ba”1
Wani irin kololon bakinciki taji ya taso mata akan wannan furucin da Umma tai, har ga Allah ita dai tana ganin kanta a mai hankali sam bata ganin abubuwan da take akwai rashin hankali ko natsuwa a cikinsu.
Hanyar kitchen ta nufa sai Umma ta kwala mata kira.
“Zinneera dazun kanen Sadiq sun zo nemanki basu same ki ba, kila su dawo yanzu dan haka karki yi wani wawanci kanen miji su tarar da ke ba a kintse ba”
“Ai sun je makaranta”
“Kin gansu?”
“Eh tare ya dauko mu ya sauke su a hanya saboda dayar tace min wai ban dace da shi ba”3
Umma ta tsaya kallonta.
“Wani abun ki kai, da baki yi wani abun ba da babu yadda za ayi ta kalleki haka kawai ta ce baki dace da shi ba”
“Fada ta tarar muna yi da wani dan department dinmu, amman Wallahi Umma shi ya mareni kuma ban masa komai ba…”
Bata karasa ba Umma ta tari nunfashinta.
“Yauwa ai idan ba ki saida hali ba, ba ki amsa sunanki ba, idan baki ja mana zagi ba to hankalinki ba zai taba kwanciya ba, Allah ya wadaran halinki Zinneera Wallahi kin ji haushi kowa yana kokari yai taka tsantsan da kanen miji amman ke kin zubar da mutuncinki tun kamin ki shiga cikin gidan ma, bari Abbah kin ya zo karatun nan ma ba zaki cigaba ba, dan in akai sake sai ki kwaso mana abun kunya tunda ba hankaline da ke ba, kara a zo ayi ta tare ni dai na gaji da ke, na gaji da rayuwar nan taki, kara in aure zai miki yai miki idan kuma daukeki zai yi ya kai wani gurin na dauke ni dai na gaji da ke na gaji da halin nan na ki Zinneera…”
Umma ta fada idonta cike da kwalla. Fasa shiga kitchen din tai sai ta nufi dakinsu ita ma nata idon cike da kwalla, saman katifarsu ta kwanta a take hawayen idonta suka soma zuba.
“Ni dai Allah yasa na mutu na hutu, kowa cewa yake ba ni da hankali, Umma ta tsane Abbah ma yanzu ya fara tsanata kowa yana min kallon mahaukaciya, har Sadiq din ma”2
STORY CONTINUES BELOW
Har cikin ranta take wannan maganar da ace mutuwar zata dauketa a yanzu da ta hutu a nata tunanin dan duniyar ta fara isarta, kallon mahaukaciyar da ake mata abun yana ci mata rai. Kuka tai sosai irin kukan nan na boye wanda baka jin sautin kukan sai dai hawaye kawai. Bayan ta gama kukan ta share hawayenta ta nufi jakarta ta dauka ta bude ta fiddo wayarta ta saka sim din. Tana kunna wayar kiran Sadiq ya shigo, she can’t rejected haka kuma ba zata iya barin kiran ya katse ba tare da ta dauka ba duk kuwa da kasancewar tana fushi da shi.
So she decided to pick the call tayi kamar ba zata yi magana ba.
“Babyna, Babyna, Babyna ki yi hakuri ba zan sake ba, bana nufin wai baki da hankali kawai dai ina son na nuna miki abunda kika yi ba ki kyauta ba ne, baby are you still there?”
Sai kawai ta fashe da kuka. Hakan ya kara daga masa hankali yana sonta sosai baya son abunda zai bata mata rai ma balle har ya kai ga tayi kuka, a tunaninsa abunda ya fada mata ne dazu ya saka ta kuka.
“Baby am so sorry, ba zan kara ba dan Allah ki yi hakuri”
“Sadiq kowa kallon mahaukaciya yake min ban san miyasa ba, na san nidai ina da zafin rai amman Wallahi ni ba mahaukaciya ba ce, amman Umma har fushi take da ni, ni dai na gaji da rayuwar nan…”
“Ki yi hakuri komai zai wuce kinji?”
Ta daga kai kamar ance yana gabanta yana kallonta.
“Zan yi magana da Umma zan ce ta daina ce miki haka kinji Babyna”
“Tau…”
Ta amsa da muryar kuka.
“Amman ki daina kuka bana jindadi kinji”
“To na daina”
Ta share hawayen da gaske.
“Fada min mi kike son na siyo miki anjima idan zan zo?”
“Bana son komai”
“Baki hakura ba kenan ko? In siyo miki ice cream kina so?”
“Eh da nama”
“Yauwa Babyna i love you so much”
“I love you more”
Sai da ya sumbanci wayar sannan ya katse kiran. Ajiyar zuciya ya sauke a hankali ya jingina kansa da sitiyarin motar, ji yake kamar ya unkura da maganar auren Zinneera wanda ya san iyayenta ma za su so jala amman ba wannan damar, aurenta ne kawai yake ganin zai hutarta da ita daga halin da take ciki domin shi kadai zai iya da abasar, ya san babynsa bata da cikakken hankali amman a gurinsa tafi mai hankali sau dubu saboda ita yake so.
_Zaka samu yancin kanka daga lokacin da ka biyani kudina, karka kuskura yin wani abu ba tare da ka biyan kudin fansar kanka ba_
Ringing din da wayarsa tai ne ya matse masa tunani, kamar wanda aka jefo daga wata duniyar haka ya zabura, ya cire hular kansa ya shafa kan sannan ya karba kiran.
“Hello Mama”
“Kana ina?”
“Wani abun ne?”
“Taya zaka wulakanta yan’uwanka a gaban matar da zaka aura, matar mahaukaciya wacce bata san ciwon kanta ba”
“A gurina macece ce mai hankalida natsuwa Mama, kuma babu wacce ta fi min ita a cikin matan duniyan nan indai a matsayin matan aure ne”
“Amman sai ka wulakanta yan’uwanka a gabanta? Wane irin rashin mutunci ne wannan?”
“Bata fada miki abunda tace mata ba? Ita ta fara tsargarta ita kuma ta rama”
Wani dogon tsaki Mama taja ta kashe wayar.
*** *** ***
Duk abunda yake hankalinsa yana can gurin Zinneera domin yayi da ita zata dawo idan kuma ta dawo zata buga gate din ya fito, hakan yasa ya raba hankalinsa biyu, amman har yai abunda zai yi da yarinyar be ji ta dawo ba. Bayan ya gama ya sallameta ya shiga bathroom yai wanka ya fito daure da tawul ta har ya shirya ya fito falo sanye da kananan kaya da facing cap kamar kullum, yarinyar da ya sallama bata bar gurin ba.
STORY CONTINUES BELOW
“Ke ba na sallame ki ba?”
“Eh so nake sai na gama hutawa nai wanka sai ma wuce”
“Aa ni ba a min wanka a gida, ki kwashe kayanki kije can wani gurin ki yi wankan ki, and lemme remind you something, idan na ce a bar min idan bana son na maimata magana if not duk wulakancin da nai miki ke kika so”
Ya fada yana mata wani kallo na wulakanci da kyama, sai ka ce ba shi ya gama amfani da ita a yanzu ba.
“Out”
Ya furta yana nuna mata kofa. Kamar marar galihu haka ta kimtsa kanta ta fice har yi masa sallama.
“Baku san darajar kanku ba, mace da ke da tsada amman kun zubar da kanku a banza”
Ya fada yana jan tsaki. Sai da tabbatar ta bar Unguwar gaba daya sannan ya sauko kasa ya fito harabar gidan ya shiga motarsa mai bakin gilashi ya dauki hanyar family house dinsu.
Yau kam sun sha fira da Mommy, 80% na firarsu akan Zinneera ne, dan Mommy ta lura yana son firar sai kawai ta biye masa.
“Kasan me halinta yarinyar nan daya da Zinneera Wallahi”
“What? What did you just said?”
“Nace halinsu daya da Zinneera”
“Wace Zinneera?”
“Zinneera dai yar Umma”
“Mummy wannan ma Zinneera sunanta, gidansu yana bayan gidana, gidansu karamin gida ne haka akwai ice a gidan kuma a university take yarinya wata fara ba zata wuce 17 years ba”
Mommy ta zaro ido tana dariya.
“Favorite ita ce, tana da wa Nabeel da kanwa Aleeya da Larai da kuma Aliyu”
“Ban san sunansu ba, amman tabbas tana da yaya namiji”
“Amman son ba unguwar da kake zaune suke ba, ita tana Abdullahi Fodio road”
“Yes Mommy a can na ke”
“Amman ka ce min arkilla layout kake? Ba can Mahaifinka ya ce ka zauna ba?”
“Yes Mommy i lie…. Due to some reasons…”
Ya fada yana sosa kansa cike da kunya.
“Amman ni da Daddynka mun dauka can kake zama fa”
“No Mommy ina zaune a Abdullahi fodio road ne, a nan ai yarinyar ta ke”
“Idan a wacan gidan kake zaune, to Zinneera ce yar’uwarka yar gwaggonka, tana zuwa gidan nan ai sosai, makarantar da ta fara ne yasa ta daina zuwa, amman da nan take weekend saboda tana sakewa a nan fiye da gidansu”
Tashi yai ya koma kusa da Mommy ya zauna.
“Mommy ita ce Wallahi, yarinyar tana masifar burgeni, Mommy kirata ki ce ta zo gidan nan please, oh i forgot Sim dinta na gida”
Ya furta yana yarfarda hannu.
“Amman idan yar’uwata ce zan jidadi sosai gaskiya, dan xan kara samun kusanci da ita…”
“Kuna da family da yawa Favorite kai baka sansu ba, suma kuma basu san ka ba, shiyasa Daddynku yake shiga da kai Family dan ka san kowa”
“Yes yes na tuna dazu ta fada min tana da Uncle Adamu, a lokacin da na ke fada nata sunana Sadan Adamu Kazaure”
Maganar yake baki har kunne, baya iya misalta irin jindadinsa a yanzu.
“Bari naje na fadawa Daddy kin ce muje can gurin wannan Gwaggon miye sunanta ma?”
“Safiya, amman Umma muke kiranta, but Favorite idan Daddynku ya ji ba inda yake ce ku zauna kake ba zai maka fada, and you know bana son haka”
“Karki damu Sweetlove fadansa ba zai yi effecting dina ba, i am in love”
Ya fada yana dariya sai ya tashi ya nufi kofar fita da sauri, jikinsa har rawa yake zuciyarsa na zillo kamar zata fito.
Da kallo Mommy ta bishi tana sauke ajiyar zuciya.
“Indai har ta tabbata Zinneera ce Favorite you’re late…”
Ta furta cikin yanayin damuwa.
______________________*May Allah accept our good deeds, forgive our transgressions and Sins and ease the suffering of all peoples around the globe. Zinneera, Sadam and Sadiq na muku Barka da Sallah😍*
*** *** ***
A jikin kofar shiga part din Daddy ya tsaya ya daidaita natsuwarsa, sannan yai knocking kofar. Yayi tsayuwar minti biyar zuwa uku kamin kofar ta bude masa. Sai da ya jira cover shoes din da ke kafarsa sannan ya karasa cikin falon da sallama.
“Wa’alaikussalam”
Daddy ya amsa masa ba tare daya dago ya kalleshi, hannunsa rike da kofin lemu, dayan hannunsa nata aikin bude magazine din dake saman center table idanuwansa sanye da farin gilashi.
Kusa da shi Sadam ya zauna a yadda suka jera sai ka rantse wa da kane ne, sam ba zaka ce Daddy yana da babban da kamar Sadam ba saboda kyaun jikinsa da kuma jindadin da yake ciki. Kamaninsa ne kawai suka banbanta da na Daddy domin fuskar Mommy ce shimfide a fuskar Sadam babu inda ya ragota da komai.
“Daddy barka da rana”
Ya fada cikin tsantsar ladabi yana kai idonsa gurin magazine din da Daddy ke kallo. Sai a lokacin Daddy ya dago ya kalleshi fuskarsa dauke da murmushi.
“Barka dai Mr Kazaure”+
Sadam yai murmushin daya bayyana hakoransa jin Daddy ya kirashi da family name dinsu. Daddy ya dauki magazine din dake gabansa ya mika masa. *Kazaure Limitless company* Shine rubuce a fuskar magazine din cikin manyan harufa, sai kuma hoton kamfani da akai ado da shi a gaban magazine din, daga can kasa kuma an raba hotunan kashi hudu dayan hoton ya kumshi abubuwan da suke cikin kamfanin ne dayan kuma hoton Sadam ne an rubuta Mr Kazaure, hoto na biyu da na uku kuma suna dauke da abubuwan da kamfanin yake siyarwa ne. Wadanda suka hada da sarkar gol da kuma yan kunne diamond. Cike da mamaki ya kalli Daddy.
“What this?”
“Open and see”
A take ya bude magazine din ya soma dubawa, yana cikin dubawa Daddy ya ce
“Kamfaninka ne da zamu bude next month”
Sadam ya lumshe ido alamar be jidadi ba.
“Daddy maganar kamfanin dai…? I thought mun gama maganar nan tun muna waje”
“Not yet, ba zan hana aikin gwanati ba kamar yadda kake so, amman for now zaka kula da wannan kamfanin ne kamin aikin ya zo, and ko bayan aikin ya fito ba zaka bar kamfanin ba”
“Dad please…”
“No Sadam na gina reshen kamfanin nan ne a nan Sokoto saboda kai, so ba zaka bani kunya ba”
“Yes Dad…. Sure.. ”
Ya aje magazine din tare da tashi yana sauke ajiyar zuciya, yanayinsa na nuna rashin jindadin da yake ciki, zumudin daya zo da shi na zancen zuwa gidansu Zinneera sai ya nemi zumudin ya rasa, maganar bude kanfanin nan ta shafe komai.
Cikin rashin walwala da sakewa ya dawo part din Mommy, be sameta a falo ba, kai tsaye ya wuce dakinta, tana zaune saman kasaitaccen royal bed dinta Suraiya na zaune kusa da ita suna kyalkyalar dariya, da alama fira take ma Mommy, kallo daya Mommy tai masa ta karanci damuwa a tare da shi.
“Favorite miya faru?”
Zaunawa yai saman kujerar dake facing din gadonta yana kara bayyana mata damuwarsa tare da shafa kansa. Suraiya ta tashi ta koma kusa da dan’uwanta ta zauna tana kallon yanayinsa.
“Mommy’s Favorite miya faru?”
Sai da ya busar da iskar bakinsa sannan ya kalli Mahaifiyarsa wacce hankalinta ya gama tashi ganin danta cikin damuwa.
STORY CONTINUES BELOW
“Mommy na ɗauka mun gama maganar kamfanin nan tun ina waje, and now Daddy ya dawo da issues din, wai by next week za’a bude kamfani kuma ni zai barwa ragamar imagining…”
Lumshe ido Mommy tai tana murmushin tare da sauke ajiyar zuciya jin dalilin bacin rai mai sauki ne, Suraiya kuma ya rumgume shi tana ihu.
“O My god, Mommy’s Favorite so that’s mean Daddy kai ya ginawa kamfanin nan congratulations”
Ya dafe kansa.
“No Doctor ba zaki gane ba, nifa ma tsani zuwa meeting dauko wacan sa hannu a nan kula da wannan tura wannan karbi wannan kana da meeting a kaza karka rasa kaza dole a samo kaza, zuba hannun jari this and that i completely hate it”
“Favorite…”
Mommy ta kira shi a hankali sai ya dago ya kalleta.
“Mahaifinka yana son ka a kamfanin nan please don’t disappointed him, ba zai hana ka aikin da kake so ba, na masa magana yace min idan aikinka ya fito zaka iya zuwa office idan ka kawo sai kaje kamfani he just wanted you to be part of it, kasan yana da yayan yan’uwa amman ya zabi ka kula masa da wannan you should atleast say yes to him, but idan baka so i will talk to him sai mu samu wata mafitar, amman ku din nan ku uku ku kenan Allah ya bashi, kuma kai ne namiji idan baka masa ba wa zai masa?”
Yai shiru alamar tunani kamin yaja wani dogon numfashi ya sauke.
“No zan yi domin ku, i promise”
“Thank you Son Allah maka albarka”
Ya tashi tsaye sai Suraiya ta kira.
“Mr Kazaure”
Juyowa yai ya kalleta daman ta kan kirashi haka idan tsokanarta ta motsa.
“Mommy tace na samu in-law”
Shafa kansa yai yana dariya.
“Har kin tuna min ya kamata na tambayi Daddy inda zamu je yau, ina son na hadu da ita as my cousin”
“Who’s that lucky girl?”
Suraiya ta tambaya yana wara ido.
“You shouldn’t ask that, kawai ki jira ki gani”
Ta ware hannayenta irin bata fahimta ba, tana kallon Mommy bakinta sake. Mommy ta daga mata kafada irim itama bata sani ba.
“Kaji Mommy yanzu kamin na shigo ba gulmana kuke ba…”
Sadam ya fada yana dariya, sai duk suka sa dariya, shi ma ya wuce yana dariyar. Suraiya ta dawo kusa da Mommy
“Dan Allah wacece Mommy?”
“Zinneera…”
Suraiya ta zaro ido tare da rufe baki.
“Amman Mommy ba tana da miji ba? Ko an fasa da wacan ne?”
“Ba a fasa ba, shi kanshi be san an mata engaged ba, and bana son fada masa Wallahi saboda zai ji ba dadi, kuma kin san idan Daddy ku yaji zai masa fada ne yace ya kyaleta tana da miji balle ma yar yar’uwarsa ce kin san kumayadda yake jin yan uwansa”
“So sad kuma da alama yana son ta sosai Wallahi”
Suraiya ta fada cikin yanayin damuwa.
“Yana son kan, yai ta bani labarinta dazun nan na fada masa cewar yar’uwarsa ce kin ga yadda yai ta farinciki kamar zai hade ni”
“Amman Mommy ai kara a fada masa da wuri kar yai zurfi cikin sonta at the end abun ya taba shi”
Mommy tai shiru bata sake cewa komai ba,sai dai fuskarsa na nuna tsantsar damuwar dake ranta, domin ko kadan bata son damuwar yaranta balle kuma Sadam da take jinsa har kasan zuciyarta…
STORY CONTINUES BELOW
Daya fita Part din Mommy komawa gurin Daddy yana masa godiyar kamfani, Daddy yayi mamaki ganin farincikinsa bayan dazu ko da ya fita yana cikin damuwar dake nuna baya son kamfanin.
“Ko dai kun hada kai da Mommynka ne amin zagon kasa na san dazun baka farinciki da kamfanin nan ai…”
Daddy ya fada yana kallonsa ta saman gilashin dake idonsa, sai Sadam yasa dariya.
“No Daddy kawai ta fahimtar da ni ne”
“Kasan fa kai da Mommynka sai Allah, ba yarda zan yi da ku ba”
“Daddy idan baka yarda da ni ba, ai ka yarda da Yarka Suraiya you can ask her a gabanta akai komai”
Daddy yai murmushi tare da kai hannu ya shafa kafadar Sadam.
“Allah ya maka albarka, baka san yadda ka sani farinciki ba”
“Anything for you Dad, Allah kara maka lafiya”
“Amin”
Dukansu murmushi ne shimfide a fuskarsu.
“Yau babu inda zamu je Daddy?”
Daddy yai masa kallon rashin fahimta.
“I mean gurin yan ‘uwa zirar da muke”
“Oh idan kana free anjima zamu je gidansu Umma wata gwaggonka ce ya kamata ita ka santa kanwata ce uwarmu daya da ita”
Wani irin annuri ne ya cika fuskar Sadam.
“Okay Daddy, zuwa bayan i’sha’i zamu je ko?”
“Yes”
“Allah kara maka lafiya thank you so much”
Ya fada fuskarsa dauke da murmushi sannan ya tashi ya fice zuciyarsa fari kal…
ZINNEERA POV.
Tana gama wayar da Sadiq bachi yai gaba da ita a gurin, bata farko ba sai da aka soma kiran sallah la’asar, as usual yau ma zabura tai ta tashi abu mai wahala kaga Zinneera ta farka normal kamar yadda mutane suke yi, a firgice take farkawa daga bachi kamar wacce aka biyo. Ganin Umma zaune kusa da ita yasa ta dan natsu tare da kawar da kanta.
“Zinneera kin farka?”
Umma ta tambaya cikin muryar kuka tana kallonta. Hakan yasa Zinneera sake kallonta dan tatace abunda ta ji, shin kuka ne take ko ba kuka ba.
“Umma miya faru? Ko wani ya mutu…?”
Ta tambaya da sauri.
“Aa ba komai, kawai dai ina tausayin rayuwarki ne da tawa, ban san ranar da zaki zama mai hankali kamar yadda nake son ki zama ba, ni kuma ba san ranar da zan daina kyamar wannan halin na ki ba, kalaman da mai miki dazun sun yi tsauri na san sun bata miki rai, amman Zinneera ke yata ce dole ko wace uwa ta ji zafin abunda kike a mace mai shekarunki, ko ba komai ke amana ce a gurina zan fi kowa jindadi idan kika natsu kamar sauran yan mata, bana miki komai dan bana son ki sai dan ki gyara halinki, ku biyar da na haifa Wallahi na fi kaunarki da saura Zinneera, amman bana jindadin abunda kike yi”
Zinneera ta sadda kanta kasa tana wasa da yatsunta, har ga Allah ita dai bata ganin abunda take ba daidai ba ne, kawai iyakar abunda ta sani Umma ta tsane ta dan kawai bata sonta, kamar yadda Nabeel yake takura mata wani lokacin.
“Ni nasan komai daidai na ke yi, kawai dai ina da rashin hakuri ne, sai ku rika cewa nayi kaza na yi kaza”
Ta fada kasa kasa, Umma tayi murmushi tare da share hawayenta.
“Tashi kije ki yi sallah, ga abincin ki can”
Tana unkurin tashi suka ji sallamar Abbah, ita da Umma suka hada baki gurin amsa masa, sannan suka fito tare Umma ta karbi ledar hannunsa tana masa sannu da zuwa.
STORY CONTINUES BELOW
“Sannu da zuwa yau ba nesa aka je ba?”
“Gusus naje, yanzu dai zan dauki lodim kaduna…”
Ya fada yana kallon Zinneera wacce ta jingina da kofa tana kallonshi kamar wata marainiya. Har ya dauke kai kamar ba zai ce mata komai ba, sai kuma ya ce.
“Ina line yake? Ba nace ki ba ni layin ba?”
Sai ta juya ciki ta dauko wayar ta mika masa da hannu biyu. Yana karba ya wuce dakin Umma ta rufa masa baya.
“Dama ka bar mata wayar har sai idan ta kara”
“Ba zan bar mata wayar ba, ai da wayar tai amfani taje can inda yake…”
Umma ta zauna yana fadin
“Ni sai na ga abunda Zinneera take kamar mai iskokai jiya Nabeel……”
Umma bata karasa ba Abbah ya daga mata hannu.
“Aa bana so, karki kawo min wannan maganar, kowa da yadda Allah yake halittarsa, ba wani zancen iska a ciki”
“Amman kana ganin abubuwan nan da take na masu natsuwa ne?”
“Idan yanzu aka mata aure zata natsu ta daina komai, hankali zata yi da an mata aure, so nake na samu natsuwa zan yi magana da iyayensa daman shine yake ta jan abun ni ban so ta fara makaratar nan ba tare da aure ba…”
“Idan kuma ta kasa zaman aurenfa? Ba fata nake ba,amman ni kadai nasan abunda na ke gani akan Zinneera bata abubuwa na masu hankali da natsuwa, Wallahi yarinyar ba daidai take ba, nima ada na yi tunanin ayi mata aure amman ina tsoron abunda zai biyo baya…”
“Babu abunda zai faru, ke ai har kin fita rashin hankalin shi wannan abun da take har wani a abun magana ne? Ni ban san abunda yasa ku mata kuke da karamar kwakwalwa ba, komai ku dauka ku dorawa aljanu, to bana son wannan maganar kar na sake ji….”
Ya fada yana nunata da yatsa kamin yasa kai ya fice a fusace.
“Innalillahi wa’inna ilaihirraji’u”
Shine abunda Umma ta nanata tana dafe kanta. Kamar daga sama ta ji muryar Zinneera take tsaye jikin kofar dakin.
“Ni kara ma amin auren ina so, ni ina son auren”
Kallo daya Umma tai mata ta dauke kai tana jin wani kololon bakinciki yana taso mata. Zinneera kam har cikin ranta take maganar iyakar gaskiyarta kenan a ganinta idan aka mata aure ita da Sadiq shikenan zata daga ta bawa Umma guri ba zata sake ganin laifinta ba.
SADIQ POV.
Freezer ya bude ya dauko gorar ruwa ya kafa bakinsa ya daga gorar sama yana sha. Can kuma ya sauke yana haki kamar wanda yai wani aiki ya gaji, a hankali hawaye suka fito daga cikin idonsa suka sauko masa. Bayan hannunsa yasa ya toshe hancinsa ya lumshe ido. Bayan kamar minti biyu ya bude idon ya karasa shanye ragowar ruwan sannan ya rufe freezer ya dora gorar sama ya nufo bedroom dinsa. Bakin gado ya zauna ya kai hannu ya bude bedside drawer sai ga wani dan karamin kwali fiddo kwalin yai ya bude, yar karamar bindiga ce a ciki pistol ido ya tsurawa bindigar yana tuna wadanda kalamai da ba kasafai yake son tunasu ba.
_Ka tafi da bindigar, idan ka biyan kudin zan karbi abata, amman ka sani karya alkawari daya zai iya saka ka rasa daya daga cikin mutanen da kake zauna_
Ya busar da iskar bakinsa yana juyar kallonsa wani bangare na dakin.
_Miliyan ashirin shi ma dan kana bako ne, da ace mun dade da kai da miliyan dari zan sa maka ko dari biyu_
“Ni yanzu ina zan samu miliyan goma ma ba balle ashirin…”
Ya furta a fili yana jinginawa da gadon… Ya dade zaune a gurin yana ta tunani kala kala a gida yai magariba, sai kusan Isha’i yai wanka ya shirya cikin wasu tufafin ya fita shima dan yana son zuwa gurin sahibarsa ne Zinneera….
*** *** ***
Umma tayi tuninin karbe wayar da Abbah yai zai sa Zinneera ta shiga damuwa amman sai taga kamar mai farinciki yasa ta, ta san wannan baya rasa nasaba da zancen auren auren da taji Abbah nayi cewar zai mata.
Farinciki ne shimfide a fuska da kuma zuciyar Zinneera, gani take idan an mata auren ta hutada komai. Abincin ma kasa ci tai tsabar farinciki da jindadi, haka ta shirya ta wuce islamiya Umma dai kallonta kawai take tana mamakin irin halinta.
Kowa ya ganta yau a islamiya yasan tana cikin farinciki, sai dai bata fadawa kowa dalilin farincikin nata ba, bulalar latti da take tsoro ma yau tsayawa tai aka mata sam ba zaka ce ita ba ce. Sai ana daf da tashi sannan Sadam ya shigo makarantar kasancewar be faro family house dinsu da wuri ba.
Ba ajinsu yake ba, dan haka ba shi tabbacin Zinneera ta shigo makarantar ko bata shigo ba, lokaci lokaci yake misalta irin mamakin da zata yi idan ta ganshi a matsayin dan’uwanta har aka tashi daga islamiyar hankalinsa na can gurinta. A bakin gate din makarantar ya hango tare da dalibai yan’uwanta. Ido yasa mata sosai ta nan ya lura da tana dan dingishi a tafiyar da take. Wata karamar yarinya ya tara ya nuna mata Zinneera yace taje ta kira masa ita.
Yarinyar taja Hijabinta
“Ke …wacan malamin na kira ki”
Zinneera ta kalleshi irin kallon na ban san ka, sai kuma ta sakar masa murmushi ta nufo inda take tana rike da littafanta da kur’anenta. Shi kuma ya daure fuska sosai dan baya son daliban ko malamai su zargi wani abu.
“Ba na ce ki dawo dazu ki karbi layinki ba?”
“Na zo ai ka bani”
“Ni..?”
“Eh amman baka min magana ba”
“Ni …”
Ya nuna kansa cike da tsananin mamaki, domin shi dai yasan be bawa kowa layin ba, hasalima be sake sakata a idonsa tun da yai da ita zata je ta dawo ta buga gate din ta karbi layin.
“Amman kin tabbatar ni na baki layin? Ko wasa kike?”
“Wallahi da gaske nake har na shi na yi nayi waya da Sadiq, dazun ma Abbah ya karbe wayar”
“Ba ni na baki layin nan ba Zinneera…”
Ya fada yana girgiza kai.
“To waya ba ni”
Ta fada tana zaro ido tana masa wani kallo kamar ba ita ba. Idonta na shiga cikin nasa yaji wani shocking kamar na wutar lantarki. Saurin kawar da idonsa yai sai kuma ya sake kallonta. Wannan karon be ji komai ba, but idonta na kanshi kamar zata cinye shi. Ya hura mata iska cikin idon yana murmushi
“Cutest wuce kije gida, amjima zan baki mamaki”
“Mamakin me?”
“Sai anjima za ki ji”
Yana fadar hakan ya zuba hannayensa cikin aljihu ya dauki hanyar gidansa yana wani takun kasaita da daukar hankali…
_________________________________
Me Sadiq yake boyewa?
Ya Sadam zai yi idan yaji Zinneera tana da mijin aure?
Me muke tsammanin zai faru gaba…?SADAM POV.
A hankali yake tawa kamar mai tausayin kasa, daidaikun mutane da baben hawa dake kai kawo a tsakanin unguwar zuwa babban titin daya hada manyan motoci. Abu daya ke masa yawo a kwakwalwa, zancen Sim din da Zinneera tace masa an bata waya taba? Tace shi bayan kuma be san ya bata layin ba, ba shaye shaye yake ba balle har yai tsammanin ko ya bata shi ba a hayyacinsa ba.
“Indai da gaske an bata sim din ai ba zan ganshi ba, bari na duba gurin da na aje shi”
Ya fada a fili yana fiddo wayarsa dake ringing yai picking call din ya kara a kunne.
“Sadiq”
“Kazaure kana ina?”
“Gani hanyar gida na fito daga islamiya”
Daga dayan bangaren Sadiq yasa dariya.
“Are you kidding me islamiya fa kace malam?”
“Yes, you know yadda nake son zama malamin islamiya ai, a can ma ina karantarwa, a wani masallaci na yan istabul”
“Oh men kayi abu mai kyau ban tsammaci zaka iya a haka anan ba, kawai dai ban jidadin sabon shafin rayuwar lalata wacce ka budewa kanka”
“Itama zan daina da na yi aure”
“Har sai ka yi aure Sadam?”
“To ya zan yi ai kasan ba zan zauna ima cutar da kaina ba, ba zan iya hade kwadayi a yanzu ba i can’t”
“Amman kara ka daina tun wuri domin idan ya zame maka jiki ba zaka iya dainawa ba ko da kana da auren ne, kazo kana wasan boya da matarka”
Har Sadam ya bude baki zai yi magana sai yaji wata murya a bayansa tana masa sallama cikin tattausan lafazi.
“Assalamu Alaikum”
Waiyowa tai ya kalleta a lokacin da yake daf da kai hannu ya tura gate din gidansa. Kyakkyawar budurwa sanye da uniform din makarantar Babus Salam wato islamiyar da ya soma karantarwa. Littafin dake hannunta ta mika masa.
“Ga littafin ka daka baro”
Sai da ya kalli Littafin sannan ya kalleta ya ce
“Ba nawa ba ne”
“Amman inda ka zauna ka bar shi”
“Ba nawa ba ne, ban je da littafi ba a nan ma tarar da shi maybe na wani ne cikin malaman”
“Okay yi hakuri na tsayarda kai”
Dan murmushi yai mata kadan ya juya ya tura gate din ya shiga yana maida wayar akunnensa
“Da wa kake magana?”
“Ina ruwanka.. Kaji mutum da gulma”
“A’a wai naji idan ka samu sai mu fara shirin aurar da kai”
“Wannan Daliba ce but to be honest, akwai wata yarinya da nake so”
“Da gaske?a ina take?”
“A nan take, ban san miyasa nake son ta ba, kawai dai abunda na sani ina sonta sosai kuma ina jin nishadi da farinciki idan na ganta, kiriniyarta na burgeni…”2
Ya fada yana murmushi idanuwansa na ayyana masa sifofin Zinneera.
“Mashallah haka na ke son ji, da alama kuma kana son ta sosai”
“Yes Sadiq ina sonta sosai, zan iya yin komai dan na mallaketa, amman abun ya zo gidan sauki domin yar’uwata ce”
“Wow hakan yai kyau, u can’t wait to see her”
“Yes amman fa bata san ina sonta ba”
“Amman ai ya kamata ta sani na san ba zata yi rejecting naka ba”
STORY CONTINUES BELOW
“Maybe I’m sure…”
“Idan ma baka fada mata ba ni zan wakilce kana fada mata, dan ba zan yarda mu yi losing wannan damar ba”
“Nima ai ba zan bari wannan damar ta wuce ni ba, ya aikin ka?”
“Aiki yana nan yadda yake kasan mai aikin jiha ba wani cigaba mutum ke samu ba, albashin ma wani lokacin ba isar mutum yake ba”
“Karka damu childhood friend, Abbah zai bude kamfani next month, as long as ina kula da shi nan zaka dawo da aikinka”
“Wow Friend da gaske?”
“Da karya”
Sai Sadiq yasa dariya cikin jindadi ya ce
“Allah yasa alheri aiko da naji dadi Wallahi”
“Karka damu we will talk about it later… Akwai abunda zan duba yanzu”
Daga haka ya katse kiran, ya kai hannu ya tura main door ya shiga, sai da ya hau stairs din ya shigo falon sannan ya wuce dakinsa. Gurin daya aje sim din ga shiga dubawa, amman be ga komai ba.
“Impossible…. How…. “
Ya furta a fili with so much confusion. Bedside drawer ya nufa ya bude, da haka ya zagaye dakin yana kai bincikar ko’ina har inda baya sa rai….
ZINNEERA POV.
bayan wucewar Sadam itama ta kama hanyar gidansu ita kadai domin abokan tafiyarta sun kama hanya tuni ganin malamin ya tsayar da ita. Tafiya take tana murmushi har yanzu bata daina jindadin maganar Abbah ba, sai ayyana yadda Sadiq, zai ji take, lokaci zuwa lokaci take ayyana yadda zata yi, zaman auren da kuma irin rayuwar da zata yi a gidan angonta Sadiq. Kamar daga sama taji sallama a bayanta, abun ka da mai shegen tsoro sai tai saurin juyowa a firgice gabanta har dukan uku uku yake. Kallon firgici take masa shi ko mutumen ya marairaice fuska ido raurau, ba za akirashi karamin yaro ba, sai dai kuma ba babban bane da za a yi tsammanin yana aure da yaya.
“Dan Allah baiwar Allah ki taimaka min da abinci yunwa na ke ji”
Maganar yake jikinsa na karkawa alamar yunwa yake ji da gaske. Baya baya tai tana masa kallon tsoro.
“Ni bana da komai a nan, amman ba ri na samo maka a gida…”
Sai da ta juya sai kuma ta juyo ta kalleshi, tufafin jikinsa tsummane irin wadannan da basu yage sosai ba, ga gashinsa ya tirmishe ya cika sosai alamar yana bukatar aski, idonsa duk sun fito sosai yana mata wani kallo da ba za’a kirashi lafiyayyen mutum ba, fari ne tas irin farin nan da ba ayi ma kallo daya. Saurin juyawa tai wai kar yaga kallon yayi yawa ya zo ya makareta. Sai ta kara cira kafartata kara sauri zuciyarta sai zillo take, tana tafiya yana binta a baya kamar mai dafafenta….
Umma na aikin tuka tuwon shimkafa tana kallon Nabeel dake sanye da gajeren Wando ba riga sakamakon kwafin bulolin dake jikinsa, a wahalce yake juyawa, zaman ba dadi haka ma kwanciyar ba dadi, as well as tsayen ma baya masa dadi har yanzu jin yake duniyar na juya masa.
“Wai ka fada cewar ba zaka samu zuwa aikin ba? Kar suga shiru”
Umma ta tambaya.
“Eh na yi waya da wani abokina na fada masa”
“Ni wannan abun yana bani mamaki, wannan dukan ba na mutum ba ne Nabeel, tunda babu wanda ya shigo gidan, gashi kuma kace kana ta ihu ba mu ji ba, tsabar bacin rai dazun Abbanku be ko tsaya na fada masa abunda aka maka ba, wai baya son ina cewa Zinneera tana da aljanu, amman abunda take yarinyar nan kamar ba yin kanta ba ne”
A take idon Nabeel ya cika da kwalla ya marairaice fuska kamar zai fara kuka.
“Dan girman Allah dan darajar Annabi Umma ki daina maganar nan, Wallahi tsoro nake ji kar su kara min anjima da dare Wallahi ni kadai na san abunda na ji kuma na gani wata kasar aka kaini inda naman daji ba nigeria ba…. “
STORY CONTINUES BELOW
Yana rufe baki Zinneera na shigowa gidan kamar an korota, hakan ya razanar da Nabeel ya tashi daga karkashin bishiyar da yake zaune ya falfala da gudu dakinsa ya turo kofar, a zatonsa sune suka hau kanta su masa wani dukan. Aleeya tasa wata mahaukaciyar dariya ganin yadda Nabeel duk yabi ya firgice… Umma da ke aikin kwashe tuwo ta kalli Zinneera wace ke kokarin risinawa kusa da ita tana dafa ta.
“Umma wani mahaukaci ne ya biyo ni wai na bashi abinci…”
“Mahaukaci?”
“Eh gashi nan kofar gida daga islamiya ya biyo ni…”
Zinneera bata gama rufe baki ba Umma ta saki tuwon da take mulmula ta tashi tsaye suka falfala da gudu daki ita da Aleeya ruka rufo kofar. Aka bar Zinneera nan tsaye tana rabon ido, bayan kamar minti biyu sai Umma ta bude kofar dakin ta fito ta nufo inda Zinneera take sai ga mutumen ya shigo aiko Umma ta karawa kafafun mai ta zo taja hannun Zinneera ta shigar da ita dakin ta sake maida kofar ta rufe daga ita har Aleeya jikinsu zanzana yake.
“Wallahi Zinneera baki jin magana, kin ga kinje kin mana jaye jayen mahaukaci”
Umma ta fada cikin yanayin dake nuna alamar tana daf da fashewa da kuka.
“Wallahi Umma ban ce masa komai ba, kawai shi ya biyo ni yai min magana… “
Windows Umma ta bude tana lekensa, already ya zuba tuwo a plate dinsu tana kokarin zuba miya ne suka hango shi, yana zuba miyar kubewar ya juyo ya kalli windows din da suke tsaye sai Umma ta duke dan kar ya hangota, Zinneera ce kawai tsaye jikin windows din tana kallonsa kamar yadda yake kallonta. Murmushi ya sakar mata sannan ya juya ya fice daga gidan gaba daya.1
“Ya dibi tuwon ya fice”
Ta fadawa Umma. Sai a sannan Umma ta taso tana lekan wajen ganin ba kowa yasa ta kwalawa Nabeel kira. Amman shiru be amsa mata ba kamar ma baya cikin gidan gaba daya. Duk wata aya ta tsari da Umma ta sani sai da ta karanta ta tofawa Zinneera sannan ta bude dakin ta fito, Zinneera na fitowa Umma ta maidata.
“Ke koma ba, Aleeya leka waje ki gani ko yana nan”
Aleeya ta koma can bayan Zinneera.
“Lallai Umma ni da baki so zaki ce na koma je da leko ita wannan ai cewa kikai ta koma”
Aleeya ta fada tana dan turo baki. Sai kawai Zinneera ta kai mata duka.
“Ni zaki cewa Wannan baki san sunana ba ne hala?”
Ita kuma ta mayarwa Zinneera dukan daman can sun saba, indai fada ne tsakanin ita da Zinneera sai Umma ta gaji da rabasu, kuma Zinneera ce ake bugewa saboda ita ce marar jiki sai tsaye, Aleeya kuma cubby ce ba tsayi.
“Au bakin abun ne zaku fara tun yanzu, muna ta mahaukaci kuna ta doke doke dan iskanci?”
Sai da Umma ta katsa musu tsawa sannan suka daina, ba dan Zinneera ta gamsu ba, dan ita bata ki akai gobe ana fadan ba. Daker Umma ta karasa kofar gidan ta leka taga ba kowa sannan ta ja gidan ta rufe… Hakan be san Nabeel fitowa ba sai da aka kira sallah magariba, a sannan ne Umma take labarta masa abunda ya faru dan shi be fito ba ma balle yasan wainar da ake toyawa.
Can bayan sallah isha’i Umma, Zinneera, Aleeya, Nabeel da Larai, da Aliyu suna zaune tsakar gida suna firar nigeria, Zinneera kam tana can wata duniyar tana tunanin yadda zatai zaman aurenta agidan Sadiq, suka ji tsayawar mota a kofar gidan, ba motar Abbah bace dan sun san baya kawo ta har kofar gidan can wani gidan yake parking dinta. Ba kuma Sadiq ba ne domin shi ma baya kawo motarsa kofar gidan, dayan biyu dai ko dai Kawo Adamu ko kuma wani dabam, amman hakan be hana Nabeel jin tsoro ba. Sai da akai knocked kofar gidan sannan Zinneera ta tashi taje ta duba sai ta bude kofar tana murna.
“Eyyye Uncle Adamu”
Tsananin daukin da take har bata lura da Sadam dake bayan Uncle Adamu ba.
“Yata yar albarka kina lafiya ko?”
STORY CONTINUES BELOW
“Lafiya kalau Uncle Aure za amin… “
Kai tsaye ta fada ko irin kunyar nan babu yadda kasan ba saman kanta take ba. Uncle Adamu ya bude baki yana dariya cike da mamaki indai dan shirme ya saba da shirmem yarsa, tana sakewa da shi sosai shi da Mommy domin suna bata lokacinsu akanta bata taba requesting abu bata samu ba indai gurin Mommy ne ko Uncle Adamu. And they are the only people and Abbah da suke ganin komai da take a normal person take.
Dariya sosai Abbah yake, dan be dauka da gaske ne ba, ko ma da gaske ne, be dauka tana so ba.
“Waya ya isa ya aurar da ke kina kina cikin karatu”
Kamar tace wani abu sai kuma tai shiru tana kallon Umma wace ke masa sannu da zuwa baki har kunne. Dayar tabarmar Aleeya ta dauko ta shimfida masa tana gaisheshi. Sai daf da zai zauna sannan Zinneera ta lura da Sadam na dan ta tantance shi ba, domin hasken gulab din be haske ko ina na gidan ba. Matsawa tai kusa da fuskarsa ta lekesa sai ya sakar mata kayataccen murmushinsa.
“Laaaa kai… “
Sai kuma tai shiru kar Umma tai mata fada tace ta yi rashin hankali ko natsuwa.
“Kin san shi ne?”
Uncle Adamu ta tambaya yana murmushi. Sai tai shiru tana kallon Umma. Sadam dake kokarin zama kusa da mahaifinsa ya ce
“Eh ina karantarwa a makarantarsu ne Islamiya ta san ni a can”
Daddy ya kunna wayarsa ya haska fuskar Sadam.
“Kin gane waye wannan?”
Umma ta kura masa ido sosai tana son ganowa tabbas taga fuskar sani amman ya dan kwanta mata
“Sadam ne”
Daddy yayi dariya.
“Ashe, zaki gane danki”
“Akwai inda jinina zai shiga a duniyar nan ma rasa gane shi? Yaushe ya dawo?”
“Be dade da dawowa, yau dai nace masa nan zamu zo yaga gwaggonsa”
“Mashallah Sadam ka canja sosai kamar na kai ba…”
Daga haka sabon fira ya balle, Umma ta gabatar masa da Nabeel da Zinneera sannan Aleeya da sauran kansu wato Larai da Aliyu…
“Zinneera makaranta tasa kin daina zuwa gidanmu ko?”
Zinneera ta sun kuyar da kai alamar kunya, tana wasa da yatsunta.
“Ai fa dan kauye yayi agogo, da an taba ta sai ta fara cewa ita yar jami’a ce, jami’ar ma cireta za a yi a ai mata aure… “
Cewar Umma. Hakan yasa Sadam tattara hankali gaba daya ya maida gurin zancen da Umma ke yi. Daddy yayi murmushi
“Kuna bani dariya Wallahi yarinya kamar wannan za a ce ayi ma aure yanzu? Karfa ki manta karatu ta fara”
“Abunda take ne, sai a hankali shiyasa Abbansu yake ganin idan an mata auren zata natsu…”
“Zinneera fa lafiya kalau take, kowa da irin halintarsa, amman shi Sadiq din ya shirya ne?”
‘Sadiq….’
Sadam ya maimaita sunan cikin ransa, gabansa na mugun faduwa, gumi na kokarin karye masa.
“Yanzu dai sai mahaifinta ya masa magana zamu ji…”
“Waye Sadiq?”
Umma na rufe baki Sadam ya jefo mata tambayar kamar ba daga bakinsa ta fito ba.
“Wanda aka tsaida mata zata aura…”
Daddy ya amsa masa, wani irin dogon numfashi Sadam yaja ya kasa saukewa, a take yayun bakinsa suka kafe, kokuwa ya soma yi da numfashinsa kamin ya samu damar aika ma Umma wata tambayar with hoping Umma ta amsa masa akasin yadda yaji.
“Yanzu ita wannan karamar yarinyar har ana mata miji?”
“Eh tun shekara biyu da suka wuce, Zinneera ai ba yarinya bace shekara 17 fa”
Umma ta fada tana dariya… Kasa zama Sadam yai a take ya tashi tsaye yana ciro wayarsa aljihu.
“Daddy bari naje wani guri na dawo abokina zai ban sako”
“To karka dade nima ba dadewa zan yi nan ba, idan kuma dare yayi sosai sai dai ka wuce gidan tun da kun gaisa, sai a rika biyo kuna gaisawa”
“Okay…”
Ya amsa numfashi sama-sama, da sauri ya fice daga gidan a wajen gidan ya tsaya ya daga kansa sama sama yana jan fresh air dake gurin, ya cikawa bakinsa iska ya busar.
“Oh No no no”
Sai kuma ya nufi gidansa da sauri, kamar wanda aka koro haka ya shiga gidan ya hau sama ya nufi freezer dinsa ya bude ya dauki gorar ruwa ya sha, ya zuba sauran a kansa saboda wani zafi da yake jin ya taso masa…