ZABIN SAMHA CHAPTER 1

 ZABIN SAMHA CHAPTER 1

Samha Abdullahi Bamanga, zaune take cikin aji a seat din dake row na biyu da littatafai zube a gabanta. Sanye take cikin kananan kaya. Bakar riga da pink skirt ne a jikinta kuma kayan sun amshe karamin jikin ta, sai dan karamin bakin dankwalin data daura a kanta. Gyara zaman glasses din dake manne bisa fuskarta tayi, tana cizon murfin biro dinta a hankali kamar yanda ya zame mata jiki. Gabadaya tunaninta baya kan abunda ake koyarwa. Hankalinta da tunaninta sun karkata zuwa ga Amjad Tafida dake zaune a seat din gaba.
kurawa gefen fuskar sa ido tayi, koh kyaftawa batayi, fuskarsa take tabi da kallo tana jin kamar ta janyo shi kusa da ita tasa hannu ta shafo kyakyawar fuskarsa ko zata samu sassauci a zuciyarta. Gangar jikinta ne yake ajin amma ruhinta gaba daya ta tafi da tunanin amjad. Tana wata uwa duniyar tunaninshi.+

Ba karamin crushing samha takeyi akan Amjad ba don tun suna aji daya ta kamu da sonshi. Amjad kyakyawa ne sosai kuma na ajin farko, kasancewarsa Hausa Fulani. Gashi shuru shuru bashida hayaniya. Yana daya daga cikin dalibai masu kokari sosai a department din. Duk ajinsu babu wanda yakeda GPA daya kamo nashi. First class student ne shi.

Lecture hall din Maths301 yayi shiru. Babu abunda kakeji sai muryar Professor Adeyinka Bayode wace take ta faman yi musu bayani. Bayaerabiya ce matar kuma ta dan jima tana koyar da maths a department din saboda kwarewarta a course din. Rubutu ta farayi da marker a board Ga projector a gefenta yana haskaka musu duka course outline din.Daliban da suke cikin ajin sun kai kusan sittin da wani abu, Kowa ya nutsu yayi shiru ana sauraron ta.

Seat mate din samha, khadija yakasai wace ta kasance aminiyar ta dan taba ta fara magana a hankali yanda Proff Adeyinka bazata ji su ba.
” keh , proff fa na kallon ki,   samha….
Amma inaaa samha bata ajin. Proff Adeyinka kamar ance ta juyo sai idanuwanta suka sauka kan samha dake ta faman kallon amjad. Ranta ne ya bace, don ita bata son tana koyarwa taga ba a mayar da hankali. Kiran sunan samha tayi tace ta tashi tsaye. Shuru kakeji, har yan aji suka juyo suka fara kallonta. Amma ita kam bata ma San sunayi ba. Zuwa inda take zaune Proff Adeyinka tayi ta buga desk din dake gabanta da karfi, firgigit samha tayi ta farfado daga duniyar tunaninta.
Dariya yan ajin suka fara yi. Don yanda ta firgita har ta kusan fadowa daga kan kujeran zamanta.

” stand up my friend!, ina koyarwa kina wani abu daban koh, you’re very stupid. Proff Adeyinka ta fada a tsawace.

Mikewa samha tayi jikin ta na rawa, gaba daya kunya ya rufe ta, musamman yanda taga kowa na mata dariya. Amjad ma ya jiyo amma shi Kura mata ido kawai yayi yana kallonta. Ji tayi kamar kasa ta bude ta shige ciki.

” I’ll deal with you later, meet me in my office after this class. Proff Adeyinka ta fada mata sa’anan ta barta a tsaye ta cigaba da koyar da class din.1

Bayan an gama class samha tabi Proff  office dinta kamar yanda ta umarce ta. Anan tayi ta faman yi mata fada, akan rashin mayar da hankalinta da takeyi kan karatu, nasiha tayi mata sosai sa’anan ta sallameta.

Tana fitowa daga office din akayi ringing siren na makarantar allamar za ayi short break kafun next lecture.
Staircase ta fara haurawa don komawa aji sai ta hadu da khadija wace itama ta sauko kenan zata je cafetaria. Khadija tana ganinta nan take ta fara mata fada tana fadin ” Haba samha why will you always allow this to happen, nasan kina son amjad amma sai kinyi har mutane sun gano hakan? Idan har yan aji suka gano wlh Zaki zama topic har zaman ajin ya gagaremu daga ni har ke da Amina”.

Ajiyar zuciya samha tayi sa’anan tace ” naji besty, amma bazaki gane baneh, idan na ga amjad gabadaya rasa yanda zanyi nakeji. I can’t seem to control my feelings over him”.

Khadija tace “Na gane amma still kiyi kokari kina controlling feelings dinki, kalla yanda proff Adeyinka tayi embarassing dinki dazu, wlh kwata kwata banji dadin haka ba”
Samha ta bata ansa da ” toh naji khady, i’ll try my possible best. Amma it’s not easy wlh. Akoda yaushe idan na ganshi, sai in dinga ji kamar kara hura mun sonshi akeyi cikin zuciyata.”
” karki damu samha, don’t loose hope, watarana amjad zai zama naki, da yardar Allah. Amma for now, just keep it low. Kinji.”
Samha bata ce mata komai ba ta gyada kanta.
Khadija tace ” wai nikam ina Amina ne tazo muje cafeteria muci abinci, yunwa nakeji wlh, Ko breakfast banyi ba na baro gida. Muna aji fa tace zata tattara takardunta ta karaso amma har yanzu taki saukowa gashi yunwa duk ta adabeni, kinga samha, Bari inje in kirata, ki jira mu anan, yanzu zamu sauko.”
Bafi 2 minutes ba khadija da Amina suka sauko daga bisani su uku suka nufi cafetarian tare. Three musketeers kenan da samha, khadija da Amina. Aminan juna ne sosai kowa ya San su tare a makarantar. Tun suna aji daya suka kulla kawance tsakaninsu. Kasancewar department dinsu daya suna karanta statistics, Kullum suna tare cikin makarantar kuma tare sukeyin komai abunsu.
Khadija fara ce, batada jiki amma tana da tsawo sosai. Samha itama tanada tsawo amma ba sosai ba, duk ta fisu haske gata siririya mai karamin jiki don bazaka ce ta kai 18 years tana 300 level ba. Wani irin sirittacen kyau ne da ita wanda ko kallo daya kayi mata sai ka so ka sake kallonta. Manyan idanuwanta da dan karamin bakinta ne suka kara kayata baby face dinta. Amina kuma itace gajeruwar cikinsu, baka ce kuma tanada dan jiki, itama babu laifi tanada kyau.
Samha bafulatana ce Yar Adamawa ainin sunanta Fatima amma dayake sunan kakarta aka saka mata yasa ake kiranta da samha. Mahaifinta Alhaji Abdullahi Bamanga mutumin jada ne dake garin yola yayi shekara uku kenan da rasuwa. Dan kasuwa ne tun yana nan da rai kuma a lokacin yayi tashen kudi. Samha ita kadai ce mahaifinta ya haifa.Tun rasuwar shi Daga ita sai mahaifiyarta fanneh suke zaune a gidansu a nan Lagos.
Khadija yakasai Yar kano ce babanta captain ne na Marine Navy. Bai cika zama ba, kullum yana kan ruwa. Suma zaune suke a cikin Apapa din.
Amina Tajjudeen rabin ta Yoruba ce , kuma haifafiyar garin Lagos ce. Mahaifinta shine yoruba , mahaifiyarta kuma bahaushiya ce. Mahaifin Amina babban lawyer ne mai zaman kanshi, suma suna da gida a Apapa GRA. Tun da suka fara Arrayan kawancen su ta kulle sosai. ARAYYAN UNIVERSITY babbar private university ce a marine road, Apapa GRA dake garin Lagos. Tsohuwar makaranta ce sosai domin an gina ta tun May 27th, 1997.
Makaranta ce wanda sai wane da wane ke iya saka yayanshi suyi karatu. An kayace makaranta kamar a turai aka ginata, kai hatta mallaman makarantar yawancinsu turawa ne suke koyar da daliban. Shiyasa makaranta tayi suna har tayi ficce fiyye ga tunanin mai karatu. Babu kabilar da zaka nema ka rasa hatta turawan da suke mazauna garin lagos duk sun saka yayansu saboda kwarewar mallaman da irin illimin da ake kwasa a makarantar.
Tun lokacin mai makarantar marigayi Alhaji Arayyan ke da rai yake kula da makarantan har Allah ya dauki ransa yayansa maza biyu kacal da suka rage mishi a duniya wato muazzam da mubashir suka cigaba da kula da makarantar har ta kawo yanzu.
Tare suka karasa cafetaria sukayi order abinci suka fara ci. Tataunawa suka fara yi akan lamarin kawarsu da Amjad. Samha ce ta katse maganarsu tana fadin ” na gaya muku ku bar wanan maganar, babu yanda za ayi hankalin Amjad yazo gareni, kunfi kowa sanin yanda na jima ina dawainiya da sonsa. Amma shi bai ma san ina motsi a doran kasan nan ba. kuma Bayan haka ina gaya muku Amjad yafi karfina nesa ba kusa ba, ku dubeni fa, ya wuce class dina. Bayan munada irinsu su zee  a wanan department din, taya zai kalle ni. Ai Ban ma gaya muku ba, ranan nazo wucewa na jiyo su billy suna hira suna fadin wai amjad yazo har gidansu billy sun fita tare dashi da zee. Danaji wanan maganar bakusan yanda naji a lokacin ba, kinsan dashi da billy cousins ne kuma kowa yasan yanda zee take bibiyarsa tana faman nunawa tana sonshi.”
Khadija ce ta bata ansa da”So fa ba daganan take ba samha. Ba sai lallai mutum yanada kyau zaka so shi ba. Kyaun hali shine komai. Kuma kinga daga ke har amjad din duk kun hada. Ga kyaun fuska ga kyaun hali. Bakiga yanda Kowa ke yabonsa a department dinnan bane Kuma dan Allah ki kyale shashashar nan wai ita zee, ki ma daina kawosu a ranki don duk karya suke, amjad bazai taba sauraran ta ba. Nasan shi da billy cousins ne amma wlh amjad ya wuce ajin zee. Ke har wani ganin kyaun zee dinan kikeyi? Haske ne fa kawai a tattare da ita, amma ni wlh bata mun kyau. Gata da shegen iyayi da dagin kai, wata rana sai nayi maganinta cikin makarantar nan, don ta kawo mun wuya kawai Ina jiran ran da zata tabo ni ne” khady ta karasa maganar cike da zafi. Daman itace masifafiyar cikinsu, bata bari ta kwana indai an tabo ta.

“A’a kiyi hakuri khady, ki kyalesu they are not worth our time. Yanzu dai mafita zamu nema akan amjad da samha. Kuma I have a plan Ku matso kuji. Amina ta fada tana dubansu fuskarta dauke da murmushi.

” shoot muna jinki” khadija ta fada bayan sun Matso kusa da ita.

Amina ta fara magana a hankali yanda students din dake next table din baza su jita ba ” yauwa kuna jina koh, tunda samha bazata iya furta wa Amjad cewa tana son shi ba, why not ta rubuta letter, ta zaiyane masa duka feelings din da take ji akanshi. I think tanan zai fi fahimtar ta.”

Zaro ido samha tayi sa’anan ta fara girgiza kai allamun bazata iya ba ” kina nufin in rubuta love letter na bashi? Sai kace wata yar karamar yarinya? Ai an daina wanan yayin, ko anayi ma Gaskiya bazan iya ba. What if baya sona yayi rejecting dina, ya zanyi? Gaskiya a’a.”

” ki saurareni kiji samha, this is the perfect plan. Wai toh so kike ki dauwama cikin wanan wahalalen son nashi da kike fama dashi? Ai ke zaki cigaba da wahala, don bai ma san kinayi ba, ni a tunanina gwanda kin rubuta kin bashi ya karanta. Amina ta katseta.

“Gaskiya bazan iya ba Amina. Amjad bazai soni ba, babu wani letter da zan rubuta na bashi. Look at me fa, Ku dubeni da kyau, amjad ya fi karfina nesa ba kusa ba. Babu yanda za ayi ya soni”. Samha ta sake fada tana kallonsu.

Salati khadija ta sake tana fadin ” Sai faman cewa kike amjad yafi karfin ki. Ta yaya? wallahi samha kina raina kanki dayawa. Ai dani ke da Rabin kyaunki, babu wata wata kai tsaye zan tunkari amjad in fada mishi sirrin dake cin ruhina. Ke har miss Arayyan da nayi contesting na last year naci na doke wanan zee din da aka bawa.”

Suna cikin maganar su sai ga Amjad ya shigo cafeteria din shi kadai. Daman akoda yaushe zaka ganshi yana tafiyarsa shi kadai, babu ruwansa da kowa. Bazaka taba ganinshi yana tafiya da wani aboki ko makamancinsa ba. Sanye yake cikin English wears. Jan sweater ya saka da wando baki, yayi kyau sosai kamar kullum Kasancewar shi yanada tsabta sosai a koda yaushe zaka ganshi fess fess. Amjad baki ne, bashi da haske. Yanada madaidacin tsawo kuma bashida jiki. Idanuwansa ciki ciki dasu zakaga yana lumshe su akoda yaushe kamar mai jin bacci. Ga Dogon karan hancinsa data kara baiyanar da kyawun halittar fuskarsa.
Snacks da drinks yayi order ya nema wuri ya zauna ya fara ci. Kunnuwansa sanye da earpiece yana ci yana danna wayarsa. Bai wani jima ba,  kusan 10mins yayi, yana gama cin abincinsa ya mike ya bar cafeteria din.

Samha kam, tun shigowar amjad, ta nemi natsuwarta ta rasa har sai da ya fita. Ajiyar zuciya ta sake tana fadi a ranta, ya zanyi da raina akan son Amjad nikam.

Amina ce ta katse mata tunani tana fadin ” kin gani ko samha, gaskiya ya kamata ki farga ki san me kikeyi kafun wata tazo tayi  miki wuf dashi, ke kinga kallon da aketa binshi dashi kuwa tun shigowarsa cafeteria dinan. Wallahi karki tsaya wasa.
Kina jina koh, we need to plan this out amma ba a nan makaranta ba, zamuyi shi a gida cikin sirri. Idan an tashi a school zuwa anjima zamu zo gidanku nida khady sai mu hada kai mu rubuta letter din. Inada kalamai a kwakwalwata Wanda zasu rikittashi ya mance calculations na maths din Dr kabir.”A Cewar Amina. Gabadaya suka sa dariya, ita kam samha jikinta yayi sanyi bata ce komai ba.

Bayan sun gama cin abunda ke gabansu suka duba time sukaga har lokacin next lecture dinsu yayi. Tashi sukayi suka koma aji. A Haka sauran students suka fara komawa classes dinsu. Mallamai suka cigaba da shiga aji suna bada darasi.

Karfe uku na rana samha ta gama lectures dinta. mahaifiyar ta Anty fanneh tazo daukarta da mota.
Kullum ita ke kawo samha school, kuma ita take dauko ta, wani sa’in idan batada lokaci sai samha ta dauki daya daga cikin motan gida tazo school. Amma anty fanneh bata cika son samha tana tuki da kanta ba. Ta fiso ta kawota da kanta.

Anty fanneh kyakyawar mace ce doguwa, fara kasancewarta shuwan Asali. In ka kalle ta bazaka ce tanada yarinya Yar shekara goma shatakwas ba. Yar gayu ce sosai. Sanye take da bakar abaya tayi wrap round da karamin gyale. shades ne a fuskar ta saboda ranar da ake zabgawa a garin. Parking din hadadiyar motarta tayi a gaban department, tana jiran fitowar samha.
Samha na hango motar mom dinta tayi sallama dasu khady, haka suka rabu akan cewa zasu zo gida anjima. Tace to sai ta gansu, ta karasa wurin motar ta bude kofan ta shiga hade da sallama.
“Walaikumassalam samha, ya lectures din yau, hope dai babu wani stress sosai?” Anty fanneh ta tambayi diyarta cike da so da kauna. Tana matukar kaunar samha har cikin ranta, tun rasuwar mijinta taja yarta a jiki sosai, Komai ta bukata tana mata. Kwata kwata bata son abunda zai bata wa samha rai. Anty fanneh manager ce a first bank. Ana ji da ita a bankin sosai don tun kafun tayi aure take aiki tare dasu, har ta kai ga samun matsayin manager a yanzu.

“Lafiya lau Ammi, ya office yau?” Samha ta tambayeta tana kokarin saka seat belt.

“Lafiya lau baby” dayake haka take kiran samha wani sa’in tun tana karama. ” yau babu aiki sosai a office bakiga nazo daukan ki da wuri ba” ta bata ansa tana reversing din motar suka dau hanyan gida.

Hamma samha ta fara yi tana kokarin rufe baki sa’anan tace “gaskiya Ammi ina jin yunwa, kuma sinnasir nakeso naci”. Ta karasa maganar a shagwabance.

“okay zuwa anjima zanyi mana sinnasir din, amma for now tunda kina jin yunwa bari mu tsaya mu siya fast food a Hubmart.
” Toh ammi, amma zakiyi dayawa saboda su khady zasu zo anjima. Akwai assignment da zasu zo mu duba tare.”

“Toh shikenan” Anty fanneh ta bata ansa.

Tsayawa sukayi a hubmart sukayi takeaway da Dan wasu abubuwan da basuda shi a gida. Suna gamawa suka wuce gida.
A bakin gate din wata babbar gida sukayi parking. Mai gadi ya bude musu gate suka shiga sukayi parking.

Suna shiga cikin gida Anty fanneh ta kira Yar aikin gidanta lami da ta shirya kitchen din zuwa anjima zata tayata girki. Lami ta ansa mata da “toh hajiya”.

Samha ta dauki take away din abincinta da Dan fruits ta haura sama zuwa dakinta.
Ajiye jakar makarantar ta tayi, ta fara cire kayan jikinta. Ta shiga bayi tayi wanka ta dauro alwala ta fito ta goge jikinta ta saka kaya ta fara sallah.

Tana iddar wa ta jawo ledar abincin, ta bude ta fara ci. Fried rice ce da salad, da naman kaza. Dayake ta debo yunwa sosai, ta cinye abincin. Tana gamawa ta tattara ta kai shara, ta dauko fruits dinta ta fara ci, tana son fruits sosai musamman Apple, don haka basu rabuwa da apple a gidanan.

Bayan ta dan huta ta sauko kasa ta same su anty fanneh da anty lami a kitchen suna kokarin hada abinci. ” sannu da aiki ammi, sannu da aiki Anty lami” ta gasishesu, suka amsa da yauwa.

“Baby bude fridge ki dauko mun su carrots, lami in kin gama wanke naman, ki Karba carrots din ki fara mun slicing. Lami ta ansa mata da toh hajiya.

Bude fridge din samha tayi ta ciro carrots, ta dauko wuka zata fara slicin kenan sai taji allamar mai gadi na bude gate, mota ta shigo.

” Ammi bari na leka kamar su amina ne suka iso” ammi ta ansa mata da toh je ki duba.
Ai kuwa su dinne, driver din gidan su khady ne ya kawo su.
Samha taje ta tarbe su sa’anan ta shigo dasu cikin fallo. Anty fanneh ta fito daga kitchen fuskarta dauke da fara’a tana musu sannu da zuwa. Su khadija suka gaisheta, ta ansa musu tana tambayensu ya nasu iyayen. Suka ansa mata da suna nan lafiya.

Bayan sun gama gaisawa samha ta haura dasu sama zuwa dakinta. Anan suka fara rubuce rubucen su akan yanda zasuyi su shawo kan Amjad. Bayan sun kamalla rubuta letter din, samha ta dube su tana fadin. “Yanzu taya zan bashi letter dinnan? “
” ban gane taya zaki bashi letter din ba, da kanki zaki mika mishi mana, mudai zamu raka ki amma a boye don baza mu bari ya gan mu ba. Kinsan yana shigowa school da wuri ya dan fara karatu kafun lectures. Saboda haka timing din shi zamuyi, lokacin mutane basu fara shigowa school ba sai ki mika mishi” A cewar Amina.

Zufa ne ya fara karyo wa samha, tana fadin “gaskiya I can’t face him with this, Bazan iya ba”.

” kinga calm down samha, this plan will work. Kin San me kawai ki mika mishi kiyi tafiyarki, ba sai kin tsaya yi mishi bayanin komai ba. Koma mai ya kamata ki fada mishi ai mun rigada mun rubuta, shidai nashi ya karanta ya bamu ansa.”A cewar khady.

” don’t worry we got this, muna nan tare da ke” amina ta fada tana ruko hanun samha.

Rungumo su samha tayi tana godiya da karfin guiwar da suke bata. Suna cikin haka tace tana zuwa bari ta sauka kasa. Bayan yan mintuna sai gata ta dawo hanunta rike da plates din abinci, sai kamshi abinci ke yi. Tare suka zauna sukaci. Suna gama ci suka dan taba hira yamma nayi suka shirya bayan sun sake kwantar ma samha da hankali sauka kasa sukayi sallama da Anty fanneh sa’anan suka wuce gida

A Daren ranar dai samha bata runtsa ba. Tana ta tunanin Amjad da yanda abubuwa zasu kasance tsakaninsu gobe.

Washe gari da sassafe samha ta tashi ta fara shirin ta na zuwa makaranta kasancewar tanada morning lecture a ranan kuma ga abu mai muhimanci da ta saka a ranta yana jiranta. Anty fanneh da wuri itama take fita zuwa office. Don haka Suna gama breakfast, Suka fita tare ta sauke samha a school, Itama ta wuce office.

Samha na shiga school bafi 5 minutes ba sai gasu khadija suma sun shigo. Daman tun da ta shigo school kirjinta ke ta faman bugawa da karfi. Har tayi niyan ta fada wa su khady ta fasa, sai kuma tasan baza su ma saurareta ba don haka ta hakura.

Suna ajiye jakansu cikin locker, amina ta fito da letter din Wanda aka ninke cikin envelope, harda fesa masa turare.
Khady ce tace ” kunga yanzu nan da yan mintuna zai shigo yaje departmental library. So zaki tsaya idan yazo wucewa sai ki mika mishi. Mu kuma zamu tsaya ta bayan office din admin, muna hango ki daga can, ki kwantar da hankalinki komai zai tafi kamar yanda muka tsara, kinji besty. Amjad kamar ya gama zama naki ne insha Allah.”

Haka suka yarda da wanan tsari, amina ta mikawa samha letter din suka sauka kasa. Daidai wurin gindin bishiyar fruits dake bayan department dinsu ta tsaya. Su kuma su Amina suka tsaya ta bayan office din admin.

Samha na tsaye zuciyarta sai bugawa takeyi kamar zata huda kirjinta ta fito. Sai faman gumi takeyi. Tana tsaye har kusan 5 minutes bai zo ba sai data kai kusan minti goma sa’anan ta hango shi yana zuwa. Juyawa tayi ta kalle su khady, Wanda suka daga mata hannu alamun ta cigaba da tsayuwa, ta jira ya karaso. Cike da fargaba ta jiyo takunsa alamun yana gab da isowa inda take. Fitowa tayi daga bayan bishiyan ta tsaya a gefe. Tana ganin ya karaso ta mika hannunta rike da letter din kanta a sunkuye ta rufe idanunta gam don bazata iya kallonsa cikin ido sa’anan tace “Amjad, ga sako nan dan Allah ka karba ka karanta…”

Kusan minti biyu tayi a tsaye taji shiru ba’ace mata komai ba kuma letter na nan a hanunta ba karba ba. shirun data jine yasa ta bude idanunta a hankali da dago kanta cike da fargaba. Zuciyarta sai faman bugu takeyi kamar zata huda kirjinta ta fito.
Me zata gani?
Maimakon taga Amjad tsaye a gabanta sai kuma taga akasin haka. Idanuwanta ne suka sauka kan wata bakuwar fuska.
Wani saurayi tagani tsaye a gabanta, hanuwansa rungume bisa faffadan kirjinsa ya kura mata ido, sai faman binta da kallo yakeyi. Fuskarsa dauke da alamar tambaya. Bata taba ganinshi a department din ba sai yau. Tama rasa ta inda ya bullo, kawai ganinshi tayi a gabanta kamar wani aljani. Toh ina amjad din? ta tambayi kanta.
Nan danan cikinta ya kulle, cikin in’ina ta soma tambayarsa” Aa..mjjad fa, inaa..yake?
Bai bata ansa ba still yana tsaye yana kallonta.

Haba nan da nan tunaninta ya dawo mata. Bata San sanda ta sake yar karamar kara ba ta kwasa a guje ta bar wurin, bata lura ba garin gudu letter din ya fadi daga hannunta.
Abunda bata sani ba shine Amjad ya saka earpiece a kunnenshi yana Sauri ya karasa library bai lura da ita a tsaye a wurin ba har ya wuceta. Su khadija ma tun da sukaga yanda abubuwa suka sauya suka bar wurin babu shiri.

Shi kuwa saurayin data gudu ta barshi tsaye a wurin, abun har yaso ya bashi dariya musaman ihun dayaga ta sake da kuma yanda ta kwasa a guje. Sunkuyawa yayi ya dauko letter din daga kasa, ya bude ya fara karantawa. Abun da yagani rubuce a ciki ne ya daure mai kai kuma ya mugun bashi mamaki. Nan da nan kuma ya fahimci abunda yake faruwa. Mata sunada matsala ya fada a ranshi, Saka letter din yayi cikin aljihunsa ya kara gaba.

Ita kuwa samha bata tsaya ko ina ba sai cikin aji, sai faman haki takeyi tsaban gudu da fargaba. Tana ganinsu khady a class din bata San sanda ta saka kuka ta daura hannu a kai tana fadin ” nashiga uku, yau na tozarta, wani irin abun kunya na jefa kaina ciki yau? Daman na fada muku wanan abun shirme ne bazai yu ba, gashi amjad dinma ko kallo na baiyi ba ya wuce ya barni ina tsaye”

Rarashinta suka fara suna fadin ” kiyi hakuri samha, ai bai ganki ba, akwai earpiece fa kunnenshi shiyasa bai jiki ba. Muna ganin komai. Ki kwantar da hankalinki.”

Dagowa da Sauri samha tayi tana kallonsu ” da gaske kuke bai ganni ba? Gyada mata kai sukayi a tare.

Sai taji hankalinta ya dan kwanta. Share hawayenta tayi tana ajiyar zuciya.
Khadija ce tace ” tsaya ma mu tambayeki tukuna, waye wanan muka ganki tare dashi bayan amjad ya wuce.

” wlh nima ban San shi ba, nifa ganinshi kawai nayi a gabana kamar wani aljani. Ban ma san ta inda ya bullo ba. Kuma daga ganin shi ba dan set dinmu bane.A cewar samha.

“Ni na sanshi” amina ta fada.

Juyo wa sukayi suna kallonta .
“A ina kika sanshi ke kuma?” suka tambayeta har suna hada baki.

“Yaron VC ne, shine dan mai makarantan nan”. Ta basu ansa.
Maganar da amina tayi ya daure musu kai don Su Kansu ba wani sanin mai makarantar sukayi ba don bai cika zuwa lokacin da dalibai suke nan ba.

Amma kince yaron mai makarantar ne kuma na ganshi kamar half caste, ruwa biyu ne fa shi ni kuma nasan VC din makarantar nan bakin fata ne. Inji samha.

Eh mana, mamanshi ai ba Yar nan bace, Lebanese ce. Daga can VC ya auro ta. Amma yanda nakeji kamar basu tare kuma shiyasa ya dawo hannun mahaifinshi, da yana can Baze university dake garin abuja, sai yazo baya jin magana kwata kwata, shine baban nasa  yasa aka mishi transfer ya dawo nan makarantar dan ya sa mai ido sosai. Sunanshi Sabah. Wanan semester aka mishi transfer ya fara zuwa makaranta. Amma yana Computer science 400 level.

Samha da khadija Kallon amina kawai sukeyi.
“Ke kuma a ina kika samu wanan labarin, mu muna nan makarantar bamu sani ba” Khady ta tambayeta.

” ai ba kowa bane ya sani, yawanci mallaman makarantar nan ma basu sani ba. Nifa ta dalilin baban mu ne ma na sani.kinsan yana harka da yan gidan sosai. Musamman hajiyansu”. Amina ta basu amsa.
“Allah yasa ba department dinmu yake ba dana shiga uku don a gaban shi komai ya faru.” Samha ta fada tana rike kanta.

“Karki damu I don’t think yanada wanan lokacin tunda ba wai saninki yayi ba”a cewar amina.

Da wanan suka kwantar da hankalinsu. Amjad na shigowa aji samha ta fara Satan kallon shi. Tana son ta fahimce ko dazun bai ganta din bane da gaske. Harkokinsa ta ga ya cigaba dayi bai ma kalla inda take ba. Nan ne hankalinta ya kwanta sosai. Tasha alwashin baza ta kara kwatanta makamancin abunda tayi yau ba.
Class dinsu na first period maths306 ne. Dr kabir ne ya shigo fuskar sa a daure kamar bai taba dariya ba. Assignments dinsu suka fara fito dashi suna submitting. Sa’anan ya fara koyar da ajin. Idan akwai abunda samha tafi tsana a rayuwata shine topic din da suke kanyi yanzu. Kwata kwata bata ganewa.

Amma sanin halin Dr kabir yasa ta nutsu, ko bata gane ba, tana nuna alamun ta gane. Excuse ta dauka tace zata je bayi, Dr kabir yace ya bata minti biyar taje ta dawo. Ai kuwa da Sauri ta tafi bayi nan da nan ta fito. Cikin Sauri tana kokarin haurawa steps bata ankara ba taci karo da mutum. Takardun dake hanunsa suka tarwatse a kasa. Amjad ta gani tsaye a gabanta.

Gabanta ne yayi mugun faduwa bata San sanda ta fara bashi hakuri ba. Tsugunawa tayi ta fara tattaro takardun dake yashe a kasa. Shima tsugunawa yayi yace mata kada ta damu, zai kwashe da kanshi.  Amma bata bari, ta cigaba da tattarawa. Sai da yayi da gaske tukuna ya samu ta bari, tsayawa tayi tana kallonsa har ya gama kwashewa ya mike. Murmushi ya dan sakar mata bai sake ce mata komai ba ya wuce yayi hanyar office din Dr kabir.
Samha wani irin dadi taji ya ratsa ta ganin murmushin daya sakar mata. karasawa aji tayi cike da farin ciki. Tana shiga aji Dr kabir ya bita da kallo ya duba agogo, Da ya so yayi mata magana akan jimawa datayi don ta wuce 5 minutes din daya bata, sai kuma ya share.
A haka classes ta cigaba. Dr kabir ya gama ya fita, next lecturer dinma ya shigo shima ya koyar. Har lokacin break dinsu yayi.
Su amina ne suka lura da yanayin samha wace sai faman fara’a take,tambayarta suka fara yi suna fadin “wai ke ya mukaga kinata washe baki sai faman murmushi kike tayi kamar wanda aka mata babbar albishir”

” guess what, amjad yayi mun magana dazu nan” ta fada tana tsalen farin ciki kamar wata karamar yarinya.

“What?? How come, tayaya?? Suka tambayeta suna zaro ido.

Nan ta zayane musu abun da ya faru dazu. Murna suma suka fara yi, Suna ta faman tsokanarta suna dariya.

Khady ce ta danyi shiru ta dube samha tace ” wai samha, tsaya tukuna ban ma tambayeki ba ina letter dinnan yake?

Zaro ido samha tayi ta dafa kirji tana fadin ” innalillahi wa ina illahi raji’un”.
Ita kam tama manta da wata letter, don tunda abunan ya faru da safe bata sake kawo wata letter a ranta ba. Cikin hanzari ta bude  jakarta ta fara dubawa.
Wayam babu alamun letter din a ciki. Zazzago da abubuwan jakarta tayi kiirjin ta na faman bugu, nan ma babu alamar letter.
Mikewa samha tayi tana fadin “Ku jirani bari naje na duba wurin bishiyan inda na tsaya dazu.” A gurguje ta bar ajin ta sauka kasa ta je wurin bishiyan ta fara dube dube. Zufa ce ta dinga karyo mata, kirjinta na bugawa tana fada a zuciyanta “ya Allah karkasa wani student koh mallami yaga letter dinan, ya Allah kasa masu sharan makarantar sun gani sun zubar a bola. Addu’an data dinga yi kenan tana dube dube .

Abun da bata sani ba shine, Sabah yana tsaya daga building din department dinsu ta balcony yana hangota. Kura mata ido yayi sosai yana kallon duk abunda takeyi. Nan take ya gano cewa letter din tazo nema. Wani dabara ne ya fado mishi akanta. Ya fara murmushin mugunta shi kadai yana aiyano abubuwa a ranshi.

A haka samha ta gama dube dubenta bata gani ba har ta hakura, jiki babu kwari su khady suka karaso suna tambayarta ko ta gani. Girgiza musu kai tayi, idonta ya ciko da kwalla . Tare suka rungumo ta suna bata baki akan cewa insha Allah babu Wanda zai gani, killan ma cleaners din makarantar sun share. Da wanan tunani, jiki babu kwari suka tafi cafetaria don cin abinci.

Haka ranar samha ta yini babu walwala har ta koma gida. Washe gari tazo school nan ma tana expecting wani ya tunkareta akan maganr letter din saboda sunanta dana amjad na rubuce a ciki harda signature dinta. Shiru taga babu Wanda ya tunkareta akan maganar. Wanan ta bar wa kanta cewa babu Wanda ya gani. Ta cigaba da harkokinta hankalinta kwance. Har ta soma manta wa.

Bayan kwana uku, ranar jumm’a da safe tana tafiya ita kadai ta zo wucewa ta gaban Computer science department dayake daga maths department sai computer science so tana yawan wucewa tanan. magana taji ta bayanta ana fadin,
” keh” banza tayi da mai maganar bata juyo ba ta cigaba da tafiyarta.
” keh, Magana fa ake miki, koh baki ji ne”. Taji an sake fadin.
Tsayawa tayi cak, ta juyo a hankali don taga wanda yake mata irin wanan kira na yan tasha.
idanunta na sauka kan mai kiran nata gabanta ya fadi ta zaro ido tana kallonsa, sai kuma ta dake, ta basar. Sabah ta gani jingine a jikin wata hadadiyar bakar power bike, hanunsa biyu cikin aljihunsa, idanunsa kyam akanta.

” yes how can I help you? Ta tambayeshi fuskarta babu walwala.
Murmushi yayi Wanda ya kayata kyakyawar fuskarsa har dimple dinsa guda biyu dake gefen kumatun sa, saida suka lotsa. Numfashinta ne yaso ya dauke mata ganin irin baiwar kyau da Allah ya masa. Masha Allah ta fada a ranta.

Dagowa yayi daga jinginan da yayi a jikin bike din ya fara takowa har yazo ya tsaya inda take. Dago kanta tayi tana kallonsa don Sabah dogo ne sosai ko kafadarshi bata kamo ba. Kallon juna suka fara yi. Idanuwansu suka sarke cikin junansu har na tsawon minti biyar babu wanda yayi magana tsakaninsu. Ganin yayi shiru bashida niyar magana kuma zai bata mata lokaci yasa ta juya ta fara barin wurin. Har ta danyi nisa ta sake jin muryasa ya doke kunnenta.

“Nasan kina neman wanan abun. Daga masoyiyarka wace tafi kowa kaunarka a duniya zuwa gareka masoyina Amjad ” taji ya fada.

Juyowa tayi da sauri tana dubansa. Hanunsa ta gani rike da letter dinta qiriqiri yana karanto abunda ke rubuce ciki.

Kirjinta ne ya soma bugawa da sauri sauri. Amma tayi kokarin saita kanta, don bata son ya gano cewa tana cikin fargaba. Kirkiro murmushin karfin hali tayi a fuskarta ta fara takowa har inda yake sa’anan tace ” lah letter na, nagode sosai bawan Allah ni kaina bansan inda na ajiye ba don na nema na rasa, nagode sosai, Allah ya…” ta fada tana kokarin fuzge letter din daga hanunshi.
shima fuzgewa yayi ya kara daga hanunshi sama inda bazata iya kaiwa ba.
Girgiza mata kansa yayi still yana murmushi sa’anan yace ” Haba yan mata, godiyan me kuma kike mun? Kar dai kina tunanin nazo na tsaya da sanyin safiyar nan domin na kawo miki wanan letter din? C’mon na zata kinfi haka wayo. Toh bari kiji in ma mafarki kikeyi toh inaso ki farka.”
Samha daure fuska tayi jin kalamansa sa’anan tace ” wani irin magana ce wanan mallam, kaga ka bani letter na na wuce”

” Haba saurin me kikeyi? Ki tsaya ki saurareni tukuna. Kinga Wanan letter din? zan iya baki ita a bisa sharadi daya.” Sabah ya fada mata.

“Wani sharadi kenan?” Ta tambayeshi kai tsaye.

Gyaran murya yayi sa’anan yace ” ina so ki zama baiwata.”

” what??” ta katse shi.

“Yes kinji ni da kyau. Baiwa ta nake so ki zama duk wani aike, rubutun notes, da assignments ke zaki dinga mun. Kuma duk inda zani zaki dinga raka ni”.

Jin maganar shi tayi banbarakwai kamar maganar marasa hankali,wani irin duba ta dinga binshi dashi tana mishi kallon masu tabun hankali . ” mallam dakata, wace irin maganar rainin hankali ce wanan sai kace maganar yara. Kanada hankali kuwa, ko ka sha wani abu da safen nan ne?Ka dube ni kace na zama baiwar ka. Anya kanada lafiya kuwa kasan me kakeyi? Hmm ni ban ma ga laifin ka ba, laifi na ne dana tsaya sauraronka, ka bani letter na, na tafi.” Ta fada mishi fuskarta a daure.

“Naga Allama kamar har yanzu baki fuskanci abunda ke kasa ba ko?, toh bari in miki dalla dalla.Kinga wanan letter din?  in har kika ki amincewa da bukatata, Zanyi photocopies dinsu har guda dubu in rabawa yan department dinku ke harda namu. Sai kowa yasan me yake tafe tsakinki da amjad din da kuma irin mutuwar son da kike masa. Kuma nasan bazaki so hakan ta faru ba” . Ya karasa maganar yana murmushin mugunta.

Kallo ta dinga binshi dashi nan ta ga taga alamun da gaske yakeyi. Idan kowa ya samu copy din letter dina ai ta shiga uku, sai dai tabar department din don bazata iya juriyan dariyan da za mata ba. Nan da nan ta fara tunanin mafita daga wanan abun dake shirin faruwa.
“Ina jiran ansar ki, kin amince ko baki amince ba?” ya tambayeta.

Shiru tayi ta cigaba da kallonshi na yan mintuna sa’annan tace ” naji amma kadan bani lokaci nayi tunani a kai.”

” Ai bake zaki fada yanda za ayi ba, ni ke da wanan ikon Don haka babu wani lokacin tunani da zan baki, minti nawa ne kinyi kin gama. So yes or no?kar ki bata mun lokaci” ya ce mata.

zuciyarta na bugawa tunani kala kala na mata yawo a kai bata san sanda ta ce mishi yes ba.

“Good girl” ya bata ansa yana cigaba da murmushin mugunta.

“Toh zaki iya tafiyarki sai na neme ki” ya fada mata.

Juyawa tayi ta fara tafiya tana tunanin irin masifar data jefa kanta ciki. Wai shin meke shirin faruwa da ita ne kamar a mafarki, me wanan yake nufi da ita ne. Ko dai kawai yana son yayi mata wasa da hankali ne? Haka kawai daga sama yazo yana so ya dagulamata lissafi? Nan take ta fara nadamar rubuta wanan letter din don duk letter dinne ya jawo mata wanan masifar tana zaman zaman ta. Amma Nasan yanda zanyi na kwace letter na cikin ruwan sanyi, bari dai na bishi a hankali. Ta fada a ranta.

Tana haduwa dasu khady ma bata gaya musu ga yanda sukayi da sabah don tasan zasu iya tunkararshi, shi kuma yaji haushi yayi posting letter din. Don haka taja bakinta tayi shiru.
Tana gama last lecture dinta a gurguje ta fita daga makarantar don kar ma ya ganta yace zai sata wani abu. Bata ma kaunar wani abu da zai kawo mata tunaninshi ko kuma ya sake hada ta dashi.

Yau ta kasan ce Tuesday a cikin sati. Samha har ta soma mantawa da abubuwan da suka faru a wancen satin tsakaninta da sabah don taji shi shiru bai sake nemanta ba ko ya sake mata magana har ta soma sakawa a rai cewa daman barazana yake mata yanaso ya mata wasa da hankali ne. Shiyasa ta share shi ta cigaba da harkokin gabanta. Yau zaune take cikin aji, sai faman rubutu takeyi tana kokarin kammala notes dinta. Su khady da Amina suna zaune suna jiranta don su sauka kasa tare.+
Kamar daga sama taji ana fadin ” Wacece Samha Abdullahi?”. Dagowa tayi tana duban wanda yayi tambayar. Haka zalika ma waenda suka rage a aji suka juyo suna kallon mai tambayar. Shima student ne amma da allamun ba department dinsu yake ba.
David lawson dake zaune a baya ne ya bashi amsa da ” Gata can a zaune a gaba”.

Harara khady ta watsawa david tana ce mishi ” waya tambayeka, zan buge ma baki yanzu”. Dayake akwai wasa a tsakaninsu.

David shima harara ya galla mata.

Samha ta tsura wa student din ido har ya karaso gabanta sa’anan yace”sabah yace ki sameshi a rest room na department dinsu.

Zaro ido su khady sukayi suna kallon student din sa’anan suka mayar da dubansu ga samha. “Sabah kuma? Toh meye hada samha da sabah, me zata mishi?”

Bai basu ansa ba yayi tafiyarshi ya barsu a wajen.
Mikewa samha tayi tana kokarin bin bayanshi. Khady ce ta riko hanunta tana fadin ” keh ban gane ba ina kuma zakije, badai wurin sabah din ba? Meye hadinki dashi Kin san waye shi kuwa? Nayi bincike na musaman fa akan shi kuma an tabbatar mun da ba mutunci ne dashi ba. baya ragama kowa, kinsan inada friends a baze university kuma yawanci an sanshi a can. Please karki fada tarkon sabah dan Allah kiyi zamanki.”

Ajiyar zuciya samha tayi ta zame hanunta daga rikon da khady ta mata sa’anan tace
” yanzu zan dawo khady, kudan bani minti biyar bari inje inji meke tafe dashi.”

Tana gama fadin haka ta fita daga ajin. Su Amina suka bi bayanta da kallon mamaki.
Tana sauka kasa straight computer science ta nufa, taje rest room din. Nan ta sameshi zaune ya kishingida akan kujerar zama, kafafun shi daya kan daya, idanuwanshi a lumshe kamar mai bacci.

Tsayawa tayi tana kare mishi kallo, sanye yake cikin white Tshirt da bakin wando , kayan sunyi fitting dinsa sosai. Sai black jacket daya dora kasancewar daren ranan anyi ruwan sama ko ina ta dau sanyi.
Sumar kanshi ta kura wa ido yanda ya kwanta luu luu kamar na baby.
Sai gashin giranshi daya cika ya kwanta. Hancin shi straight, sai karamin bakinsa dayayi fitting fuskarsa ya kara fito to ainun kyaun halittar fuskarsa, komai nashi daidai kamar shi yayi kansa. Sai dai bakin hali ta fada a kasan ranta. Harara ta watsa mishi tana kara jin haushinsa.

A hankali ya bude Idanuwanshi farare tass dasu suka sauka a kanta, ganinta yayi tsaye a kanshi.

Dagowa yayi daga kwanciyan dayake yana shafo lallausar sumar kansa sa’anan yace ” yan mata ya naga kinzo kin tsaya mun aka kinata bina da kallo, lafiya?”

Dan rainin wayo ta fada a ranta” ba kai bane ka turo a kirani ba” ta bashi ansa ranta a bace.

“Da kuma nace akira ki sai ki zo ki wani tsaya mun aka kaman wata bishiya?”
Ajiyar zuciya yayi sa’anan ya tura hanunshi cikin aljihu ya ciro yan dubu dubu ya mika mata ” ban son wani dogon surutu ungo nan jeki cafetaria kiyi mun take away guda hudu na abinci, daga nan ki wuce snack bar ki siyo snacks da soft drinks ki kawo mun nan ina jiranki, kuma na baki minti biyar kiyi ki dawo”.

Bude baki tayi tana kallon shi cikin mamaki da takaici sa’anan tace ” ban gane ba, take away hudu fa kace? tayaya ma zan ruko kayakin nan ni kadai?”

” wanan kuma ba damuwata bace.Kisan yanda zakiyi ki riko su, in ma tafiya biyu zakiyi wanan ya rage naki .Kuma batun take away hudu danace kiyi wanan babu ruwanki. keh nifa bana son yawan tambayoyi. Oya yi ki tafi, kina bata mun lokaci yunwa nakeji” ya fada mata sa’anan ya koma kwanciyarsa ya barta a tsaye.

Wani tukukin bakin ciki ne ya rufeta.ji tayi kamar ta hau kanshi ta shako shi tsabar takaici. Haka ta fita daga rest room din zuciyarta na tafarfasa.
Tana zuwa cafetaria tayi order na take away guda hudu. Daganan taje snack bar ta siyo snacks da drinks din kamar yanda ya bukata.
Da kyar ta iya rike ledodin ta kawo mishi rest room. Wanan karon bashi kadai ta tadda ba, yana zaune tare da friends dinshi su uku. Yana ganin shigowarta ya duba agogon hanunshi sa’anan ya dube ta ita kuma ta dauke kanta. ” kinyi lati minti biyu amma zan daga miki kafa na yau”.

Harara ta galla masa, shi kuwa ya karba ledan daga hanunta. Abokananshi suka fara binta da kallo daya bayan daya. Da taga kallon yayi yawa ta fara kokarin barin wajen.
“Ai ban baki izinin tafiya ba” ya dakatar da ita.
Jawo kujera yayi kusa dashi ya mata alamun data zauna.
Zatayi musu taga ya kafe ta da daradaran idanuwansa, ba dan taso ba ta nema wuri ta zauna.

“Wow SB, ina ka samo irin wanan hot babe din haka, wani department take? Daya daga cikinsu ya tambayi sabah.
Murmushin daya saba yi ne yayi ya dube samha wace ta daure fuska tamau kamar bata taba dariya a rayuwarta ba.

“Guys meet samha, baiwa tace ita zata dinga tayani yin komai a makarantar nan as from today. Samha meet my guys wanan ya nuna guy din na farko shine shinoh, wanan kuma zack, sai Abba. Murmushi suka sakar mata. A ranta tace ina ruwana da su tana takaicin sunan baiwar daya kirata dashi.

Abba ne ya kare mata kallo yana lashe lips insa yace ” yane baba zaka bani na dana wanan hot chick din”

Nan dana nan murmushin dake fuskar sabah ta dauke, ya daure fuska sa’anan yace ” wai baku ji me nace bane?  Ce muku nayi baiwata ce ni kadai. She belongs to me alone” ya karasa maganar yana kallon su dayan bayan daya.
Shiru dukansu sukayi babu wanda ya sake cewa komai. Samha kuwa Allah Allah ta dinga yi ta samu ta bar wajen.
Ledan takeaway ya mika musu, suka bude suka fara ci. Mika mata takeaway daya yayi, tayi banza dashi. Shareta yayi ya ciro snacks ya fara ci .
Duba agogon hanunta tayi taga sha biyu saura, lokacin next lecture dinta ya kusa sa’anan ta mike tace mallam inada lecture yanzu. Bata tsaya sauraransa tayi gaba abunta.

“Wow, SB yarinyar nan fire ce fah, ina ka samota haka” zack ya tambaya yana mamakin barinta wurin kai tsaye. Shi daya san yanda yanmata keh rububin su tsaya inda sabah yake baya basu fuska ballantana yabi takansu amma wanan ko ajikinta.
Murmushi sabah yayi yace ” ku barni da ita, zan gyara mata zama a makarantan nan ne. Bata sanni bane.
Dukansu suka kwashe da dariya don sun san zai aikata.

Samha na shiga department kai tsaye ajinsu ta nufa ta zauna. Tana takaicin abubuwan dake faruwa da ita yan kwanakin nan.
Su amina ne suka zo suka zauna kusa da ita suna tuhumarta akan tafiyarta wurin sabah.
Ajiyan zuciya samha tayi. Wata zuciyan ne ke fada mata da ta fadawa kawayenta ko zata samu mafita amma tana tsoron abunda zai biyo baya. Daga karshe dai ta yanke shawaran fada musu.
Nan danan ta zayane musu komai dake faruwa tsakaninta da shi tun last week har baiwar dayake kiran ta dashi.

Wani irin ashar khady tayi ta mike tsaye tana hucci” ina dan iskan yake, wlh sai na koya masa hankali. What nonsense?!!ya dubeki yace zai mayar dake baiwarsa,Ke kuma kika yarda samha? Wlh kin ban mamaki, shine baki sanar damu tuntuni ba sai yanzu?.

“Wallahi ya sani a gaba ne khady, yace in har ban amince da bukatarsa ba zai tona mun asiri. Samha ta fada muryarta kaman zatayi kuka.

” toh wallahi ya debo ruwan dafa kanshi, keh ba dan VC ba ko kakan VC ne yau sai ya gane kuranshi, sai yayi dana sanin zuwanshi wanan makarantar. Kam uban can. Khady ta fada tanata zazzaga ruwan bala’i.

Kamo hanun khady amina tayi don ta zauna saboda yan aji har sun fara juyowa suna kallon su. ” please ki rage murya musan yanda za ayi mu shawo kan alamarin nan”. Amina ta fada mata.

Neman wuri khday ta samu ta zaune still tana faman masifa.

” khady calm down, shiyasa nake ta fargaban fada muku don nasan haka zakiyi reacting”.

“Ai dole nayi reacting haka, magana sai kace wani wasan yara? Ai daya tunkare ki da farko da kin fuzge letter a hanunshi kin yayyaga sai muga abunda zaiyi blackmailing dinki dashi . Ke kika bashi wanan damar wlh. Amma yau dina za ayi ta takare ko ni ko shi a makarantan nan.” Khady ta bata ansa.

” a’a khady mu bi komai a hankali har mu rabu dashi lafiya. Bar ganin abubuwan dayake fadamun kamar da wasa amma ni nasan da wata manufa ya tunkare ni, he’s bored ne ya rasa abunda zai yi ne shiyasa yakeso ya mayar dani abar wasansa. Ni kuma i’ll play the game along with him daga baya kuma zan bashi mamaki. Zan nuna mishi i’m more matured than him. Amma for now zan biye mishi kawai. Samha ta fada tana dubansu.

Ajiyan zuciya dukansu sukayi sai khady tace ” Toh naji amma nidai gaskiya babu abunda zai hanani tunkararshi yau wlh. Kun dai ji nayi rantsuwa.

Samha tayi tayi khady ta hakura ta bar maganar tunkararshi amma kememe taqi tace sai tayi. Haka ta hakura ta kyaleta. Suna gama lectures din rana, suka fito suna so suyi photocopy handouts dinsu can hanyar English department suka nufa sai ga sabah nan tafe yana takun nan nasa cikin kasaita, tafiya yakeyi shi kadai babu alamun wata damuwa ko tashin hankali a tattare dashi.
Samha na hangoshi nan take hankalin ta ya tashi ta kamo hanun khady tana girgiza mata kai allamun ta kyaleshi kawai su wuce.

Fizge hanunta khady tayi kai tsaye babu tsoro ko shakka ta nufa inda yake tahowa taje ta tsaya a gabansa ta tare masa hanya. Shi kuwa ganin mutum tsaye a gabansa ne yasa shima ya tsaya. Sanda ya gama Kare mata kallo tsab sa’anan ya dubi bayanta daga can gefe ya hango samha da amina a tsaye suna kallonsu. Nan take ya gano cewa tare da samha take.
Gyara tsayuwarsa yayi da kyau ya cigaba da kallonta yana jiran yaji me zata ce.

Kallon shi sama da kasa tayi ta fara zazaga ruwan bala’in ta inda take shiga ba nan take fita ba. Harda barazanan zata kira mishi yan sanda in har be kyale kawarta ba.

Ko kalla bai ce mata ba tana ta zuba ruwan bala’i. Yasan da guys dinshi nanan babu abunda zai hanasu su koya mata hankali shi kanshi yasan don yana cikin good mood ne shiyasa ya kyaleta. Shiru yayi bai ce mata komai ba har ta gama yayafa ruwan balainta tayi shiru tana hucci. Yanda ya kafe ta da dara daran idanuwansa ne ko kyafta wa bayayi ne ya dan bata tsoro amma ta dake tana jiran taji me zai ce.
Shuru yayi ya cigaba da kallonta kusan minti biyu bai ce mata komai ba sa’anan ya girgiza kai ya bita gefen ta ya wuce ya kyaleta tsaye a wurin.
Idan abunda khady tafi tsana a rayuwarta shine kyaliya, kwata kwata bata so. Wanan abun dayayi ba karamin haushi ya bata ba, ji tayi kamar ta cire takalmin kafanta ta jefe bayanshi dashi dashi.
Su samha ne suka karaso inda take da sauri suna tambayarta.
“Kyale dan iskan ai bazai ce komai ba, nadai mishi tattass kuma nayi mishi warning da kyau akan ya fita harkan ki. Idan na sake ganinshi kusa dake sai na hada mai zafi a makarantan nan”.

Dariya su samha suka saka suna fadin khady bakida dama wlh, kice kin tsorata shi da kyau.
Itama dariya ta fara yi don tasan ba karamin karfin hali tayi ba wurin tunkararshi.

“Amma fa samha guy dinan nada kyau… whaaaattt??? Kinga hasken shi kuwa, har sheki yakeyi ga idanuwanshi daya kafe ni dashi har naji tsoro kamar ba mutum ba”. Khady ta fada.

” a’a ko kin kyasa ne kinga faduwa tazo dai dai da zama” amina ta tambayeta tana dariya.

“Wa? Allah ya sauwake inji inason mutum mai mugun bakin hali fitinane irin shi ai gwanda na dawwama a hakan babu namiji a rayuwata, ballantana ma ina ni ina jinsi larabawa yan lebanese. ya tafi can ya karata.” Khady ta fada tana tabe baki.

Ita kam samha dariya ta cigaba dayi bata sake cewa komai ba ba har suka karasa cafe din sukayi photocopy. Suna gamawa suka sake komawa class domin yin last lecture dinsu na ranar.
Haka ranar ta wuce sabah bai sake neman ta har tagama lectures dinta ta tafi gida.
Washe garin ranan da waninsabon rainin hankali sabah yazo mata dashi. Bayan ya aika an kira mishi ita yace ta biyoshi class. Haka tabi bayanshi suka shiga 400 level class dinsu. Nan take kallo ya dawo kanta, don sun san ba ajin take ba. Zama yayi a row na biyu, yace ta zauna kusa dashi. Shinoh zack da Abbah ma suka zauna ta gefenshi. Lecturer ne ya shigo ajin ya fara lecture. Sabah ya debo takardunsa ya ajiye mata a gaba yace ta fara rubutu. Badan taso ba haka ta bude ta fara rubutun.

Lecturer ne ya lura da ita yaga bakuwar fuska, yace ta tashi tsaye yana tambayarta Meye take nema a ajin. Ko tayi batan hanya ne. Jikin samha na rawa ta mike a hankali kamar wanda kwai ya fashe mata a ciki. Rasa abunda zata ce tayi ta fara iina. Oya zo ki barmun aji, lecturer ya fada yana nuna kofa. Kafun kace meye Zack ya buga hanunshi da karfi akan desk din dake gabansu yace ma samha ki zauna babu inda zaki. Abun ya bawa kowa mamaki, lecturer cire glass din dake sanye a idanunshi yayi tsabar mamaki don ya tabbatar da abunda kunuwansa suka jiyo masa.

Sabah kuwa murmushi yakeyi abunsa yana kada kafarsa daya be ce komai ba. Shinoh ne ya kalla lecturer yace “tana tare da sabah so babu inda zata”.

“Uban waye sabah” lecturer ya tambaya ranshi a bace akan rashin kunyar da suke masa a aji.

” Alhaji muazzam Arrayan shine uban nasa” Abbah ya bawa lecturer ansa.
Nan danan lecturer din ya zaro ido, duka ajin kowa yayi shiru suna kallon abun mamaki.
Lecturer din bai sake cewa komai ba ya juya ya cigaba da koyarwa cikin takaici. Yasan saboda makarantan private ne shiyasa yaran sukeyin abun da sukaga dama. Suna ganin iyayensu manyar mutane ne sunada kudi so babu mai taka musu birki. A ranshi yace da fedral university nake da hakan bata faru ba don sai ya sa an koresu daga makarantar, amma cikin ruwan sanyi zaiyi maganinsu, ya aiyyana a ransa.
Samha kuwa abun yayi mugun bata mamaki da tsoro data ga lecturer din ya kasa yin komai daya ji an ambaci sunan mahaifin sabah.
Kallon sabah ta fara yi cike da mamaki, shi kuwa ya jiyo ya kalle ta ya kashe mata ido daya. Tsaki taja a ranta ta cigaba da rubutu tana rokon Allah mafita daga sharrin sabah. Hour daya da rabi sukayi a class din lecturer ya sallamesu.
Tana ganin an gama class din kamar ta zuba ruwa a kasa tasha takeji haka ta dauki jakarta cikin hanzari zatayi gaba ai kam sabah yaki barinta ta tafi ” ina zakije kuma? Ai baki gama duty naki na yau ba. Inada timetable dinki nasan lectures biyu gareki yau kacal. So kinada free time. Yanzu ungo wanan” ya mika mata wata takarda dauke da doguwar list.
” ki siyo duk abunda kika gani rubuce a ciki” ya fada mata.
Bai sake ce nata komai ba ya ciro wayarsa kirar iphone 11 max ya fara latsawa.

Itama bata ce masa komai ba tayi tafiyarta. Ba karamin siyaya tayi ba har dasu chocolates da biscuits. Kuma ta san ba wani bukatansu yakeyi ba. Yana yin hakan ne don kawai ya muzguna mata.
Haka ta riko ledoji a hanunta da kyar wasu mutanen ma har kallon ta sukeyi a hanya.
Tana cikin tafiya tazo dab da garden dake jikin department dinsu taji an sa mata kafa nan da nan tayi tuntube ta fadi kasa warwas. Kayan da ta riko a hanunta suka tarwatse a kasa. Cikin jin zafi ta dago kanta tana son ganin wanda ya sa mata kafa.
Wata yarinya ce ta gani tsaye a kanta. Fuskarta a daure ta daura duka hanunta bisa kugu cikin shirin fada.Doguwa ce sosai kuma fara, sanye take cikin riga da wando farare kafafunta sanye cikin black sneakers. Fuskarta a daure tasha make up sai faman gallawa samha harar takeyi. Samha cikin zafin rai ta fara tambayarta ” mallama lafiya? Me na miki da zaki zo ki samun kafa haka ki kadani.

” an saka miki kafa din” yarinyar ta bata ansa.
” me namiki?” samha ta tambayeta.
” nazo ne na ja miki kunne kuma na miki kashedi, daga yau sai yau ban so na kara ganinki kusa da sabah. Sabah ba tsaranki bane, dubeki kucaka dake kinzo kina wani rabuwa dashi. Me zai ci dake ke? Toh bari kiji in gaya miki sabah nawa ne ni kadai, babu wace macen da ta isa tazo kusa dashi sai ni. Keh wallahi wallahi, ko ta department dinshi naga kin kara bi sai na saba miki a makarantan nan.
Sunana Aliyah, sabah shine abokin rayuwata,ki tambayi su shinoh zasu gaya miki tarihin mu. Don banqi kowa ma ya mutu ba indai akan sabah ne ba. Ta fada tana hucci.

Samha ta tsaya galala tana kallon ikon Allah. Yau ana wata ga wata, don gaba daya kanta ya daure tana son ta fuskanci inda maganar yarinyar ta dosa.

” mallama dakata kiji, ce miki nayi ina son sabah ne ko me? Ni da kinsan hukubar danake ciki a tattare dashi baza kizo kina mun wanan shirmen maganar ba. Toh bari kiji kar ki sake zuwa ki tunkare ni da wanan banzar maganar . Gashi can kuje ku karata. Tana gama fadin haka ta tattara kayan da suka zube a kasa tayi gaba ta barta a wurin ranta a bace.
Ita kuwa Aliya bin bayan samha tayi da kallo tana cizon leben ta na kasa, a ranta tana kitsa yanda zatayi maganin samha ta rabata da sabah shi kuma sabah ya zo gareta.
Samha tana isowa inda sabah yake ta sameshi a kishingide kamar yanda ya saba hutawa. Jefar da ledodin tayi a gaban shi ranta a bace. Shinoh da zack suka bita da kallon mamaki.
Sabah ya dube ta yana tambayarta akan dalilin jimawarta haka. Jawo daya daga cikin ledan yayi ya ciro chocolate din dayake matukar so, gani yayi duk ya farfashe.

Sake duban ta yayi yaga sai girgiza takeyi tana faman cika da batsewa. ” ya naga chocolates dina sun farfashe?” ya tambayeta. Shiru tayi bata bashi ansa ba.
” tambayarki fa nakeyi” ya sake jefo mata tambaya.

Cikin jin haushi tace ” mallam ban sani ba, ka sani a gaba, idan chocolate kakeso wanda bai farfashe ba babu abun da ya samu kafafunka ka tashi kaje ka siyo da kanka. Ni karka sake mun wata tambaya. Kaga tafiyata. Tayi fuuuu ta tafi ta barsu a wajen.
Abba ne cikin zafin rai ya mike zai bi ta , sabah ya dakatar dashi.
Sabah ranshi inyayi dubu ya bace akan abunda samha ta mishi. Ji yayi zuciya ta kawo masa amma yayi kokari ya danne.
Shiru yayi ya zauna yana nazari.

Ana cikin haka, sai ga Aliyah ta sawo kai fuskarta dauke da murmushi ta nufo inda sabah yake zaune. Bata ganin kowa sai shi. Zama tayi kusa dashi tana mishi magana amma ko kallonta baiyi ba ballantana ya tanka mata. Zack ne ya fara mata alamun data bar wurin ta kyaleshi don baya cikin good mood komai zai iya faruwa. Banza tayi dashi ta cigaba da yiwa sabah magana.
Sabah dayaga tana neman ta cika shi da surutun banza da wofi data saba yi mai, wani irin tsawa ya daka mata sa’anan ya mike daga inda take ya bar wurin jikinshi har tsuma yake tsaban baccin rai.

Aliyah ba karamin firgita tayi da tsawan daya mata ta bi bayanshi da kallo.
Zack ne ya matso inda take yace ” haba Aliyah ai na fada miki kidan ja da baya da shi don na san baya cikin mood mai kyau but you didn’t listen. Ke kin fi son kullum kina zuwa wurin sabah yana wulakantaki?.

Harara Aliyah ta galla ma zack taja tsaki ta tafi ta barshi a wajen.
Zack kuwa girgiza kansa yayi don idan da sabo ya saba da halin Aliyah. Asalin sunanshi shine zakari danfulani amma suke kiranshi da zack, duk cikinsu yafi kusanci da sabah haka zalika tun kafun su kai haka yake dawainiya da son Aliyah. Amma ita kwata kwata in ba sabah ba bata ganin kowa da gashi. Kasancewar Aliyah tare dasu sabah suka girma. Tun suna yan kanan suke unguwa daya. So hata makarantan da suke zuwa ya kasance daya. Har baze university ma tare suke, tana jin anyiwa sabah transfer ta saka mahaifinta a gaba sai lallai itama ta dawo Arrayan don bazata iya nesa dashi ba. Haka Aliyah ta taso tana dawainiya da son sabah har suka kawo haka amma har yau ta kasa shawo kansa.

Samha tana barin su Sabah kai tsaye tayi hanyar  departmental garden dinsu ta samu wuri ta zauna tayi tagumi tana tunanin mafita daga lamarin sabah.

Wayar ta ce ta fara ringing ta katse mata tunani, ta ciro daga cikin Jakarta. Sunan khady ta gani a rubuce a screen din wayar, dagawa tayi ta kara a kunnenta.

Khady ce ta fara tambayarta inda take don har sun gama lectures suna so su wuce gida. Kai tsaye tace su tafi kawai ita ba yanzu zata tafi gida ba akwai abun da zata tsaya yi su hadu gobe. Tace toh shikenan sai Allah ya kaimu. Sukayi sallama ta katse wayar.
Ajiye wayar tayi kusa da ita tana dafe kanta don har ciwon kai ta fara ji a lokacin. Bata son su hadu dasu khady su fuskanci damuwarta shiyasa tace musu su wuce kawai.

Amjad ya fito daga library kenan zai wuce sai ya hangota zaune ita kadai ta dafe kai alamun tana cikin damuwa. Karasawa yayi inda take zaune ya tsaya.

Ita samha jin tsayuwar mutum a kanta ne yasa ta dago da Sauri a zatonta Sabah ne yazo zai mata rashin mutunci sai taga akasin haka. Amjad ta gani tsaye a gabanta kamar a mafarki.

Nan take bugun zuciyar ta ta karu, mamaki ya cika ta. Don bata taba zaton zata ga Amjad tsaye a gabanta haka ba.
Murmushi ya sakar mata Wanda ya kara bayana kyawunsa ya mata sallama ta ansa mishi. Hanunshi duka biyu ya tura cikin aljihu. Yayi shiru yana kallonta sa’anan yace.

” sorry hope ban takura miki ba nazo wucewa ne naga kamar kina cikin damuwa shine nace let me check on you, hope dai komai lafiya?”. Ya tambayeta.

Murmushi ta sakar masa sa’anan tace mishi ” yes I’m fine wlh, I’m just trying to concentrate ne, nazo waje shan iska ne”.

Sai yace “okay, sunana amjad, last time da muka hadu a kan stairs ina Sauri naje office din Dr kabir ne shiyasa ban tsaya munyi magana sosai ba, nasan sunanki samha koh? If I’m right. Ina yawan ganin ki a class amma magana bata taba hada mu ba”.

” haka ne sunana samha. Kuma you are right magana bata taba hada mu ba kam. Nice to meet you amjad ta fada mishi” fuskar ta still dauke da murmushi.

” it’s a pleasure. ni na gama lectures dina zan wuce yanzu. I’ll see you some other time ko”. ya fada mata
Tace toh shikenan. sallama sukayi ya bar wurin.
Samha ji tayi kamar ta tashi tayi tsalle tsabar farin ciki. Nan da nan ta nema bakin cikin da take ciki ta rasa. Daukar Jakarta tayi ta bar wurin sai fara’a take kamar wace aka mallaka mata gida a aljannah.

Bata sani ba ashe duk abun da ke wakana tsakinta da Amjad Sabah yana tsaye ya na kallon su.
Wani irin tukukin bakin ciki ne ya rufe shi daya gansu tare. Nan take haushin dayake ji alokacin ta karu dari bisa dari.
Nan kuma ya fara tambayar kansa toh haushin su na me yakeji? Kodai kishi yake ji? Nan take kuma ya kawar da wanan tunanin don yasan so ne ke kawo kishi,shi kuma yasan ba son samha yake yi ba. Kawai dai ya mayar da ita abar wasansa ne don samun nishadi. Tsaki yaja ya bar wurin.

Samha tana isa gida a ranan ta wuce daki tayi wanka tayi sallolinta sa’anan ta kwanta a gado tana ta faman tunanin amjad har bacci ya dauke ta. Ita kanta ammi ta lura da changes a tare da diyartata yau dinan yanda ta ga tana cikin farin ciki tun suna hanya har suka iso gida.
Bayan samha ta haura sama, shiru shiru Anty fanneh tana jiran taga saukowarta, bata ganta ba. Sai ta haura sama ta nufi dakinta. Tana bude kofa taga tayi rasherashe akan gado sai faman bacci takeyi. Girgiza kai ammi tayi ta fita daga dakin tana fadin baby kenan.

An kusan kiran sallar magrib samha ta farka ta tashi ta shiga bayi ta wanke bakinta sa’anan ta dauro alwala. Ana kiran sallah tayi sallanta. Tana zaune kan sallaya taji wayarta ta fara ringing akan gado .Mikewa tayi ta dauko wayar taga ammi ke kiranta, ta daga. ” Toh sarkin bacci sai ayi kokari a tashi ayi sallah.

“Nayi sallah fa ammi, yanzu na idar” samha ta fada mata.

“Toh yayi kyau, idan kin gama abunda kikeyi ki sauko kasa ki sameni a parlour” ammi ta fada mata.

“Toh ammi, gani nan zuwa” ta bata ansa sa’anan ta katse wayan.

Mikewa tayi ta bude wardrobe dinta ta ciro kaya riga da wando na bacci masu laushin gaske. Ta daura hula akan ta sa’anan ta sauko kasa.

Anty fanneh kishingide take akan kujera tana kallon wani programme a Tv.
Samha taje ta kwanta a jikinta cike da shagwaba tana fadin “Ammi gani nan”.

Kallon ta ammi tayi tace ” baby ya naga kamar kawana biyun nan kin dan dishe, kina shiga rana ne haka sosai?” Ta tambayeta tana kare wa jikinta kallo.

Tabe baki samha tayi tace “Ammi babu ranar danake shiga. Kawai stress ne fa na makaranta.”

“Toh kiyi kokari kina avoiding shiga rana sosai kar ki bata skin dinki” ammi ta fada.

Murmushi samha tayi tace ammi kenan. “Naji zan rage shiga”.

Shiru ne ya dan ratsa su sa’anan ammi tace ” yauwa samha, akwai maganar mai muhimanci danakeso muyi dake.”
Dagowa samha tayi daga kwanciyar data yi tana duban mahaifiyarta. ” Toh ammi ina jinki”

Anty fanneh ta dan nesa sa’anan tace
“samha kinga yanzu kimanin shekara kusan hudu kenan da rasuwar mahaifinki kuma har yau ban sake jina daidai. Kullum addu’a nakeyi Allah ya kai haske kabarinsa. Samha naso mahaifinki kamar raina, kema kinsan da hakan. Ban taba tunanin akwai abunda zai raba mu ba amma mutuwa tazo ta raba mu. Amma haka Allah yaso. Kuma baka iya ja da hukuncin Allah.Yanzu dai maganar danake so na miki shine. Ina so na sake yin wata auren samha.”

A zabure samha ta juyo tana kallon mahaifiyata don bata taba kawowa a ranta cewa wanan maganar zasuyi ba, bata taba tunanin ammi zata sake sa batun wani aure a ranta ba.
“Aure fa ammi, wa zaki aura kuma ammi?” Samha ta tambayeta muryarta na rawa.

Ajiyan zuciya ammi tayi tace ” wani ne wallahi kusan sati biyu kenan yake nema na. Tun randa yazo branch dinmu ya sameni a office muka tattauna akan matsalar dayake samu a business account dinshi, ya nuna yana so na, kuma har da aure”.

“Yanzu ammi kin amince masa zaki aureshi kenan?” Samha ta tambayeta.

“Eh toh ban bashi ansa kai tsaye ba. Nace mishi ya dan bani lokaci nayi shawara tukuna. Kuma kinga kusan kullum sai ya kirani yaji ya nake.”
Ruko hanuwan samha tayi duka biyu cikin nata sa’anan ta cigaba da fadin” samha wanan auren danake so nayi ba wai zai canza komai bane. Kinga bazan cigaba da zama haka ba babu miji ba. Aure shine mafita da rufin asirin gareni, bama ni kadai ba harda ke samha. A addinance kema kin san ba haramun bane wana auren dane ke so na karayi. Kinga kece kadai kika rage mun a duniya, banida wata da zan zauna nayi shawara da ita akan irin wanan abun sai ke ya’ta . Inason full support dinki kuma da addu’a . Sa’anan cikin yan kwanakin nan na dan zauna na karanci yanayin mutumin Kuma naga allamun bashida matsala yanada mutunci sosai.”

Shiru samha tayi tana nazari dukan abunda mahaifiyarta take fadi.
Gabadaya kanta ya mata nauyi ta rasa me zata ce nan take hawaye suka ciko idanuwanta zuka fara zubowa don tuna mahaifinta datayi.
Ammi ma hawaye ne ya ciko idonta, ta jawo samha jikinta tana rarashinta tace  “baby wanan ba shi bane yake nufin na manta da daddynki ba. Yana nan cikin raina a koda yaushe kuma zai cigaba da kasancewa cikin raina har abada amma you need to understand why i have to get married again. Please baby”.

Sun dau kusan minti goma suna sheshekar kuka ammi na rarashin samha.
Samha ce ta dago tana kallon mahaifiyarta sa’anan tace ” babu komai ammi, ni bazan iya jada hukuncin Allah ba. Addu’a zanyi kawai Allah ya tabbatar da alkhair. Kuma Allah ya jikan Abuiy na.
Na baki goyon baya dari bisa dari ammi.” Ta fada tana sharewa amminta hawaye.

Anty fanneh ba karamin dadi taji ba akan amincewar samha. Don daman tunaninta daya shine samha. Amma gashi ta shawo kanta cikin sauki. Godiya ta dinga yi ga Allah daya bata yarinya mai hankali da hangen nesa irinta.
“Nagode baby, Allah ya miki albarka. I love you so much my daughter”. Ta fada tana sumbatar kanta.

“Ameen, i love you too Ammi” samha ta fada tana kara rungumota.

Bayan sun gama magana. Ammi ta ce ta tashi ta debo musu abinci suci. Kitchen samha ta nufa ta debo musu abinci. Shinkafa da miya ce da soyayan plantain da kifi a gefe. Tare suka ci suna ta hira tsakaninsu abun sha’awa. Yanda anty fanneh takeyi da samha kai kace kawaye ne su ba diya da uwarta ba. Don ba karamin shakuwa bane tsakaninsu. Suna gama cin abinci, ammi ce ta fara jin bacci ta mata sai sa safe ta haura sama zuwa dakinta. Samha itama dakinta ta wuce. Tayi sallar isha’i sa’anan ta zauna bisa kan gado. Tana ta tunani kala kala. Ita tasan duk duniya babu abunda tafi so kamar farin cikin mahaifiyarta. Ta sa a ranta, indai wanan auren akwai alkairi a cikinta Allah ya tabbatar.
Nan take kuma tunanin amjad ya fado mata, lumshe idanunwanta tayi a hankali tana tunanin suffofinsa. Nan kuma tunanin sabah da abunda ya faru yau ya zo mata. Tsaki taja tana fadin gaskiya ya kamata ta kawo karshen wanan rainin hankalin da sabah yake mata. Wata zuciyar ce ta bata shawaran data fadawa amjad sirin dake ranta kawai. Kowa ma ya huta, ta fita daga tarkon sabah.
Da wanan shawaran ne ta kwanta har bacci yayi nasarar daukanta.

Washe gari, tana isa makaranta bata wani bata lokaci ba ta fara neman sabah.
Anan restroom inda ya saba zama da gang dinshi ta tadashi. Bata ma kula da su shinoh dake zaune a gefen sa ba tazo ta tsaya a gabansa. Yau sanye yake da kaya riga da wando all black. Hata sneakers dake sanye bisa kafafunsa black ne. Ya saka shades baki ko kwayar idanunsa baka gani. Sumar kanshi yasha gyara don sai sheki yakeyi. Hanunta ta daura kan kirjinta tana kare mishi kallo up and down, Sa’anan tace “mallam nazo ne mu warware komai dake tsakaninmu, kana jina ko daga yau sai yau karka kara turo wa a kirani akan wata Aiken ka na banza, kuma karka kara kiranan da sunan wata baiwa. Ka fita daga harkata babu ni babu kai daga yau. In har kana tunanin dan letter na wajenka ne zai sa na cigaba da maka biyaya toh tun wuri ka canza tunanin. Dan na rigada na yanke shawaran fadawa amjad sirrin dake cin ruhina. Zan fada mishi komai, kowa ma ya huta”.

Shiru ko ina yayi, su shinoh suka fara kallon juna cikin mamaki. Don sai yau sukaji gaskiyar alamarin because sabah bai taba fada musu akwai wata letter a kasa ba. Murmushi sabah ya fara yi sa’anan ya fashe da wata irin dariya. Suma su shinoh suka biye mishi suna dariyar. Sai da sukayi dariyar data ishesu sa’anan sukayi shiru sabah ya dubeta. Hakan dayayi ba karamin kona mata rai yayi don tasan dariyan nasu na rainin hankali ne, sun mayar da maganarta shirme.

” yanzu kina ganin zaki iya tunkarar amjad kice kina sonshi? Kuma kina tunanin wanan ne zai sa ki fita daga tarkona na kyaleki? Girgiza kansa ya farayi yana fadin ” toh yarinya gwamma ki canza shawaran ki domin Idan kikayi gaggawan budiremun na miki alkawari zan baki mamaki a makarantar na. So tun yanzu na baki options zabi kuma ya rage naki.”

Babu wata shawara da zan yi na rigada na fada maka daga yau sai yau ka fita daga harkata. Babu ni babu kai” tana gama fadin haka ta juya ta fita ta barsu a wajen.

Tana barin wajen straight aji ta wuce zuciyarta fess, babu wata sauran damuwa. Yau zata yar da kwallon mangoro da huta da kuda. Nan ta same su khady ta zayyane musu komai. Suma suka nuna jindadinsu akan hakan datm.

Tunda ta je tayiwa sabah kashedi har yinin ranar bata sake jin duriyar sa ba.
Har ta fara tunanin ko ya dauki maganarta da gaske ne ya fita harkarta. Da wanan tunanin ta yini ranar tana farinciki har tagama lectures ta koma gida.+

Washe gari da wuri ta shigo school da safe tana shiga ajinsu bata tadda kowa ba don ko su khadija basu iso ba.
Ta nema wuri ta zauna ta fara bude littatafanta tana nazari.
Bayan yan mintuna taji shigowar mutum cikin ajin, dagowa tayi taga amjad ne ya shigo. Suna hada ido, bata san sanda ta sakar masa murmushi ba shima ya mayar mata, haka ya karaso yazo ya zauna kusa ita suka gaisa.
Taji zuciyarta kamar ta narke jin amjad kusa da ita. Farin cikin rayuwarta.

” nazari kikeyi?” Taji Ya tambayeta.

Tace mishi “eh ina dan duba maths din dr kabir ne, kasan tests dinshi ya kusan matsowa.”

Murmushi amjad yayi yace ” ai kam test dinshi ya kusan matsowa, naji class rep yana cewa kamar cikin satin nan za ayi fixing”.

Zaro ido samha tayi tace “cikin satin nan?, ai wlh ban gama iya solving din calculations din daya bamu ba. Tun jiya naketa fama”.

“Ina yake baki matsala let me see if i can explain it to you” ya tambayeta.

Ciro lecture note dinta tayi daga cikin jakarta ta bude ta fara nuna mishi inda yake bata matsala. Nan ya fara mata bayani dalla dalla yanda zata fahimta. Dadi ta dinga ji yana ratsa ta don yanda yake mata bayanin yasa ta kara fahimtar course din sosai. Suna cikin haka su khady suka shigo cikin ajin suka tadda su.
Bude baki sukayi cikin mamaki da sukaga amjad da samha suna zaune tare. Samha ta musu allama da ido da suyi shiru su wuce karsu ce komai. Don ita bata son amjad ya fahimce komai.
Karasowa su khady sukayi suka gaisa da amjad din suka nima seat a bayansu samha suka zauna cike da mamaki.

Ba jima ba Lokacin lecture dinsu yayi, lecturer din ya shigo ya fara koyar dasu. kusan two hours suka dauka suna lecture din daga bisani lecturer din ya gama ya sallamesu aka tashi a ajin.

Amjad ne ya juyo ya tambayeta ko zata sauka kasa zuwa cafetaria. Jikinta na rawa tace mishi eh zata je. Yace mata toh bisimillah su tafi tare.
Ta juya inda su khady suke zaune a baya suna binsu da kallo ta ce musu ita da amjad zasu je cafeteria, suka ce mata toh su fara tafiya suma idan sun gama notes dinsu zasu taho.

Tare suka bar ajin ita da amjad suka fara sauka kasa. Dai dai wurin notice board taga dalubai sun tsatsaya ana kallon abun da aka mana a board, sai dariya kowa keyi. Tace wa amjad kamar fa akwai notice da aka manna suje su duba board din. Suna karasowa nan kallo ya dawo kansu, daluban suka fara nuna su da hannu suna dariya.

Abun ya daure wa samha kai don bata fahimce abunda sukewa dariya ba, haka ta kusa kai cikin jamma’ar taje ta ga wa idanunta abunda ke faruwa.
Mutuwar tsaye tayi data ci karo da abunda aka manna a board. Letter dinta ne qiriqiri tagani manne a jikin board din, harda hoton ta dana amjad an manna kowa na gani.
Amjad ma yazo ya tsaya kusa da ita a gaban board din.Ganin letter din dayayi da sunansa a rubuce harda hotunansu yasa kanshi ya daure ya juyo yana kallon samha cike da mamaki.

Samha kuwa tama rasa yanda zata yi, ji take kamar kasa ta bude ta shige don kunya. zuciya ce ta dibeta bata san sanda ta kwasa a guje ba, students din kuwa sai dariya suke ta faman yi mata. Amjad ganin ta kwasa a guje ya soma kwala mata kira yana kokarin binta amma inaaa ko sauraronsa batayi ba ta cigaba da gudu hawaye na gangaro mata a fuska.

Har su khady ta gani a hanya suna kokarin tsayar da ita, bangaje su tayi ta cigaba da gudu kamar wata zarariya.
Wuri daya tasa a rai da niyan zuwa kuma mutun daya zuciyarta ke hasko mata da taje ta tunkara. Tasan babu wanda zai mata wanan ta’asar in ba sabah ba.
Cikin yan mintuna sai gata a department dinsu, kai tsaya inda ya saba kebewa da abokananshi ta nufa, ai kuwa ta ci sa’a ta sameshi zaune yana hira dasu. Tana isowa bata tsaya watawata ba ta daga hannu ta sakar masa lafiyayun mari har guda biyu a fuska. Koh shakka bata ji ba.

Sabah yana zaune kawai yaji saukan mari. A zabure ya mike tsaye, ganin samha yayi a gabansa idanuwanta shar shar da hawaye tana kallonsa cike da tsana. Har ta daga hannu zata sake kai mishi wani marin ya cafke hanunta ya rike. Ita kuma ta fizge hanunta daga nashi tana hucci. Su shinoh sake baki sukayi suna kallon abun mamakin dake faruwa agabansu.
“Keh Meye haka, bakida hankali ne ko kin sha wani abu ne?”Sabah ya tambayeta a tsawace, don ranshi in yayi dubu ya bace.

Itama tsawa ta daka masa ta fara masa masifa “meyasa kayi posting letter dina sabah?  Eh? wani irin nishadi hakan ta jawo maka? Hakan dakayi ya saka jin kai wani ne ko meye? Toh bari in fada maka wanan abun dakayi ya sake tabbatar mun da baka taba samun farin ciki da so a rayuwar ka ba shiyasa baka son kaga wasu suna cikinta. Daman ka kudiri niya zaka cimun mutunci ka tozartani a makarantan nan. Toh yau burin ka ya cika. Yanzu wani riba kaci daka aikata hakan? Sai ka gaya mun riba da kaci daka tozartani a bainin jamma’a dan naki amince maka. Allah ya wadaran mai hali irin naka, kuma sai Allah ya saka mun, Mugu kawai azalumi”.

Tun data fara mishi masifar ta ambato letter, nan da nan ya gano inda zancen nata ya dosa. A da yayi niyan ya fada wani abu sai kuma ya fasa ya gyara tsayuwarsa ya matso kusa da ita yana kallonta ido cikin ido sa’anan yace ” yanzu daman kinzo nan ne dan ki fada mun wanan shirmen? Kuma an gaya miki hawayen da kike zubda zasu tabani ne? Naji ni mugu ne ni azalumi ne sai meye?kadan kenan daga cikin abubuwan da zaki dinga fiskanta a cikin makarantar nan indai bazaki yi yanda nakeso ba”
Kara matsowa yayi sosai dab da ita har suna iya shakar numfashin junansu yasa hanu ya kamo fuskarta sa’anan ya fada mata a hankali ” gwanda ma ki shirya don idan sabah yace yana son abu toh babu mahalukin daya isa ya hanashi, kuma in ya kafa doka babu mai iya tsalaketa”.

Buge hanunshi tayi daga rukon dayayi mata ta tureshi.Wani irin kallo ta dinga binshi dashi sa’anan taja tsaki ta tafi ta barshi a wajen.

Tana fita ta samu wuje ta rushe da wani irin kuka mai cin rai. Tana danasanin rubuta wanan letter datayi a rayuwarta.

Su khady kuwa hankalinsu a tashe yake ganin irin gudun da samha tayi ta wuce su, zasu bi bayanta kenan sai ga amjad shima yazo cikin sauri ya taddasu. Tambayarsa sukayi akan abunda ke faruwa nan ya zayyane musu komai. Suma ransu ya bacce sosai musaman khady amma suka danne suka ce bari suje su nemota tukuna.
Anan wajen bayan department dinsu sabah suka hango ta zaune kan grass ta kifa kai tana ta faman kuka. Khady ta dubi amjad tace mishi “kaje ka rarasheta, don kaine kafi cancanta ka kasance tare da ita a wanan lokacin. Bai ce komai ba, Cikin sauri ya karasa inda take zaune ya tsuguna a gabanta ya kira sunanta a hankali taki dagowa don ita kunyar kowa ma takeji a lokacin. Musaman ma shi bazata iya hada ido dashi ba.
Rarashinta ya fara yi yana bata baki har tayi sauki da kukan. Hannu yasa ya dago ta, fuskarta har tayi jaa tsabar kukan data sha dayan hanunshi ya zira cikin aljihu ya ciro handkerchief ya soma goge mata hawayen dake kwance bisa fuskarta yana bata hakuri.

Cikin muryar kuka ta fara fadin ” Amjad kayi hakuri wlh banyi niyan saka ka cikin wata matsala ba har ga Allah. Wlh ba laifi na bane….”

“Shhh, ba sai kin mun wani bayani ba. I understand”. Ya fada mata yana sakar mata murmushi.

Wani dadi ne taji ya rufeta taji radadin zuciyarta ta ragu. Bata taba zaton zai dauki abun haka sai ma taga ya mayar da abun kamar ba komai ba. Bayan ya gama share mata hawayenta ya kamo hanunta ya bude ya ajiye mata handkerchief din cikin tafin hanunta. Samun wuri yayi ya zauna kusa da ita, yana dan janta da hira har ta samu ta dan sauko.
Suma su khady suka karaso inda suke suma suka fara rarashinta har suka sa ta manta da abunda ya faru. Amjad ya karfi number wayarta yace ta kwantar da hankalinta idan ta isa gida zai kirata. A hakan suka rabu.

Shi kuwa sabah, tun barin samha wurin ya kasa sukuni duk ya nema nutsuwarsa ya rasa. Maganganunta suka dinga mishi yawo a kai musaman inda take fada mishi bai taba son wani a rayuwarsa ba shiyasa bai san muhimancin so ba. Maganar ta jima tana mishi yawo a kai. Gabadaya ya rasa meke mishi dadi.

A ranar dai samha ta yini kamar wata mara lafiya. Data je gida ma anty fanneh ta lura da yanayinta ta tambayeta tace mata babu komai lafiyanta lau kawai kanta ne ke dan mata ciwo. Anty fanneh ta dauki magani ta bata tasha. Ko data haura sama zuwa dakinta bayi ta fada ta watsa ruwa a jikinta tabi lafiyar gado tayi bacci. Zuwa yamma ta farka ta jita garau, wayarta ta dauko taga miss calls har guda biyar. Daya daga ciki bakuwar number ce, sauran kuma su khady ne suka kirata.
Bakuwar number ta fara kira, ringing biyu aka daga taji muryan namiji. Nan ya sanar da ita cewa amjad ne. Mikewa tayi da sauri ta zauna da kyau jikinta har rawa yakeyi don jin muryasa. Ya fara tambayarta ya takeji a lokacin tace mishi she’s fine. Tana magana tana lumshe ido kamar yana gabanta.
Nan ya dinga bata baki yana kwantar mata da hankali. Bayan haka tayi mishi godiya sosai sukayi sallama.
Neman layin khady da amina tayi suma suka kara kwantar mata da hankali. Suna gama wayar sai taji gaba daya ta nema damuwarta ta rasa.

Mikewa tayi ta dauko jakar makarantar ta fito da takardunta ta fara nazari. Bayan ta gama ta mike ta tattara takardun tana cikin mayar dasu jaka sai taga handkerchief din da Amjad ya goge mata hawaye dashi dazu. Daukowa tayi ta rungume handkerchief din a kirjinta. Tana tuno kallamansa masu kwantar mata da zuciya.

Bayi ta shiga ta wanke masa handkerchief din tsab ta shanya. Daga bisani ta sauka kasa ta samu anty fanneh wace har sun gama girki da lami.

Abinci samha ta debo ta zauna ta ci suka dan taba hira da Mahaifiyarta. Anan anty fanneh take sanar mata da yanda sukayi da mutumin dayake nemanta. Tace yau ma sai dayazo har office suka zauna suka sha hirarsu. Yanda anty fanneh take bata labarin yanda sukayi cike da farin ciki yasa samha itama taji dadi, kuma taji mutumin ya kwanta mata a rai duk da dai bata ganinshi ba, don yaushe rabon dataga mahaifiyarta cikin walwala haka tun rasuwar mahaifinta.
Nan anty fanneh tace mata ai mutumin yanada yaro saurayi shekararsa ashirin da biyu shima yana zuwa makarantar su. Kuma yace gobe zai tura dan nasa har gida yazo ya gaisheta. Samha tace babu matsala Allah ya kaisu goben. Suna gama hirarsu samha tayiwa anty fanneh sai da safe ta haura sama zuwa dakinta.
Sallolinta tayi bayan ta idar ta mike ta shiga bayi ta watsa ruwa a jiki ta soma shirin bacci, bayan ta saka kayan baccin ta tabi lafiyar gado ta kwanta. Ranar dai ta kwana cike da mafarkin Amjad dinta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *