ZABIN SAMHA CHAPTER 11
Shiru Madina tayi daga bisani ta cigaba da fadin ” i was wrong, bai kamata na fadawa Sabah wanan maganar na cewa muyi pretending muna soyayya saboda kar iyayyen mu su gane ba.”
Shiru Samha tayi tana sauraronta don itama jikinta ne yayi mugun sanyi data tuno cewa suma they are hiding their relationship from their parents .
“Big sis…Anty na..” Madina ta soma kiran Samha, amma ina Samha ta rigada tayi zurfi cikin tunani. Sai da Madina ta dan tabota tukuna tayi firgiti ta dawo hayacinta.
Madina ta dubeta tace “Big sis lafiya kuwa? Inata magana naji kinyi shiru”
Murmushin yake samha ta sake sa’anan tace “lafiya wlh. I’m okay. I just zoned out ne kawai”.
Madina tace “okay, daman inaso na fada miki cewa inaso dani dake da Sabah mu zama good friends, da fatan dai babu matsala zaku karbe ni hannu bibiyu?”
Gaban Samha ne ya fadi dataji Madina tace tanason ta kulla abota da Sabah, kar dai kirkinta yanaso yajaza mata? Murmushin karfin hali ta sake kirkirowa ta sakar mata sa’anan tace “babu matsala Madina. You’re always welcome”.
Itama Madina murmushin ta sakar mata tace ” nagode sosai Big sis”
Samha tace mata babu komai, sallama sukayi daga bisani Samha ta karasa department dinsu cike da sanyin jiki.
Tana shiga cikin class, bata tadda su khady ba, ciro wayarta tayi daga cikin jaka ta soma nemansu a layi.
Bugu daya khady ta daga, Nan suka sanar da ita cewa suna cafetaria.
Cikin yan mintuna kadan sai gata nan a cafetaria din.
Karasawa tayi inda suke zaune, itama ta samu wuri ta zauna sa’anan ta zabga wani uban tagumi.
Khady da Amina suka kalli junansu sa’anan suka dawo da dubansu gareta suka soma tuhumarta akan abunda yake faruwa.
Ajiyar zuciya ta sake sa’anan ta zayane musu duk abunda ya faru.
Cike da mamaki suke binta da kallo, Samha ta karasa maganar da ” ni wallahi gabadaya ma na rasa yanda zanyi, I thought this arranged marriage crises is over sai gashi madina ta sawo kai, ga kuma yar’uwarsa shafa da duk tabi ta tadda hankalin kowa akansa. I think I’ve meddled too much. Ni maganar ma da Madina da fada mun dazu ne yake damuna, there’s something wrong about what she said, na kasa fahimta”.
Khady ce tayi saurin katseta tana fadin ” ai kece Samha, atimes you do too much. Gashi kinje kinata yaba Sabah a gabanta ba dole taji ya burgeta tanaso ta hada abota dashi ba”
Samha ta mararaice fuska tace ” toh ya zanyi? Kema kinsan banason ana misunderstanding dinsa, shiyasa nayi mata wanan bayanin, kuma naga duk tabi ta damu, harda da’an kukanta fa”.
“Toh ai gashinan, keda ajayi work dinki. Gashi kina neman ki kwan ciki”. Khady ta karasa maganar tana hararanta.
Amina ce dake zaune a gefe ta danyi dariya tace ” na zata ni kadai ce a cikin mu nake irin wanan shirmen. Gashi har Samha ta zartani”.
“Ai keda ita ban san me yake damunku ba, baku neman shawara kafun kuyi abu” Tsaki khady taja sa’anan ta cigaba da fadin
“Ai ni Sabah yayi mun daidai, gwanda daya fada mata kai tsaye, kinga the more she diskikes him, the better it is for you. Don gaba ta kaiki”
“Toh ai Madinan tace akwai wanda takeso”. Samha ta fada tana dubansu daya bayan daya.
Turo baki khady tayi bata sake cewa komai ba don ita already ta rigada ta gama jin haushi.
Amina ce ta soma fadin “karki damu Samha, nasan da kyakyawar niyya kika aikata hakan ba tare da kinsa komai a ranki ba don haka ki cigaba da hakuri, don mai hakuri shine mawadaci, komai zai tafi normal da yardar Allah”.
Samha murmushi ta sakar mata sa’anan tace “shiyasa nake sonki Amina, akwai ki da iya kwantar wa mutum hankali, ba kamar khady ba, sai tayita yiwa mutum masifa da fada” ta karasa maganar tana watsawa khady harara ta gefen ido tana turo baki.
Khady wace ta cika tayi fumm tace “iyeee, wato Amina ce kadai ke iya kwantar miki da hankali. Toh shikenan, nagode. Daga yanzu nasan Zaman da zan dinga yi daku, musamman ke Samha”.
Dariya suka sa tare suka soma binta da baki, ita kuma sai faman kumbure kumbure takeyi tana cewa su kyaleta tasan matsayinta a yau.
A haka dai suka cigaba da hiransu suna zolayan junansu har lokacin tashinsu yayi.
************************
Da dare misalin karfe takwas da rabi, Samha tana zaune akan desk dinta a daki tana kokarin ta kamala assignment din da aka basu a school.
Sanye take cikin lalausan kayan bacci riga da wando mai dauke da kwaliyan cartoon din spongebob.
Kayan baccin sunyi mata kyau sosai, Ga doguwar sumar kanta data sha gyara ta zubesu har gadon bayanta, sai faman shekki takeyi tana fitar da kamshi na musamman.
Tana zaune tayi zurfi cikin rubutun da takeyi, from time to time take dago kanta tana kurawa chocolate din da Madina ta bata ido, gabadaya hankalinta ya kasa kwanciya ta kasa samun sukuni saboda tunanin dan hiran da sukayi tare da ita a school. Ji takeyi kamar idan tayi wasa zata iya rasa Sabah.
Shi kuwa Sabah, shima har yayi wanka yayi shirin kwanciya, tunanin kanwar nasa ne ya adabeshi, nan take sai yaji yana bukatar yaga kyakyawar fuskarta ko zai samu yayi bacci da kyau.
Babu shiri ya mike yaje wurin wardrobe dinsa ya dauko jalabiyansa coffe colour ya sanya sa’ana ya dauko turarensa na oud insense ya feshe duk illahirin jikinsa dashi. Sai faman baza kamshi yakeyi.
Ga farar fatar jikinsa ta karayin fresh tana fitar da shekki na musamman.
Fitowa yayi daga dakinsa yayi hanyar zuwa dakin Samha.
Yana zuwa daidai bakin kofar dakinta yaja ya tsaya, hannu yasa ya fito da wayarsa daga cikin aljihu ya soma nemanta a layi.
Samha tana zaune sai faman rubuce rubuce takeyi taji wayarta ta soma kara a kusa da ita.
Dauko wayar tayi tana dubawa taga Sunan Sabah datayi saving as ” My heart” mai dauke da heart emojis ❤️❤️ ya bayyana.
Cikin sauri tayi picking call din ta kara a kunnenta.
“kanwata…” taji sanyayen muryansa ya doki kunnenta.
Tana jin sautin sanyayar muryansa mai shiga jiki ta lumshe idanunta sa’anan ta bude su a hankali tana jin wani abu yana mata yawo a duk illahirin jikinta, amma ta yi kokari ta danne tace ” nida kai we’re living under the same roof, sai kuma ka dinga wani kirana a waya?” Ta karasa maganar tana harara tana murguda masa baki tamkar yana gabanta.
“Oh haka ma kika ce? Toh shikenan, bari na shigo ciki kawai”.
Zaro ido tayi tana fadin “No! Ammi da Abbah suna gida, karka kuskura ka shigo ……”
Amma ina Sabah ko tsaya sauraronta baiyi na, hannu yasa yana kokarin murda kofar.
Samha tana ganin haka, ta daka Wani irin tsale, ta zabura ta mike daga inda take zaune cikin sauri tana kokarin ta karaso ta sawa kofar key.
Tana isa, Sabah yana bude kofar, sai kawai taji saukan soft lips dinsa akan nata.
Kusan mutuwar tsaye Samha tayi a wurin, shi kuwa ko ajikinsa, Hannunsa ya daura akan waist dinta yana shafan wurin a hankali yana cigaba da kissing dinta.
Wani abu Samha taji ya tsargar mata tun daga cikin kwakwalwarta har zuwa ko wani sashi na jikinta, bata san sanda ta lumshe idanunta ba.
Kissing dinta yayi na kusan 3 minutes sa’aan ya dago yana dubanta fuskarsa dauke da murmushin nan da yake kara kayace asalin kyaun halittar fuskarsa.
Tsayawa tayi tana kallonsa da dara daran idanunta taga ya kashe mata ido daya, sa’anan yasa hannu yaja kofar dake tsakaninsu ya rufe.
Kafafunta ne suke nema su gagareta don haka tayi saurin jingina da jikin kofar tana ajiyan numfashi.
Sabah shima jingina yayi a jikin kofar ta waje sa’anan ya kara wayar a kunnensa.
Itama kara wayar tayi a kunnenta tana sauraronsa kirjinta na bugun uku uku tace “sabah meye haka? Yanzu dasu Ammi sunzo sun ganmu fa?”
Sabah ya saki murmushi sa’anan yace ” nasha gaya miki, idan nasa abu a raina zanyi toh nothing can stop me. Don haka ki shirya don yanzu ma na fara”
Samha shiru tayi tana sauraronsa sai faman ajiyar numfashi takeyi.
Sabah yace ” me kikeyi har yanzu bakiyi bacci ba? Kin manta gobe munada hiking da zamuje na team club? You should get some sleep don gobe idan kika gagara tashi, I won’t be held accountable”.
Murguda masa baki Samha tayi tamkar yana gabanta tace “Ai basai ka fada ba daman yanzu nake shirin nayi baccin. Sai da safe!”
Har zata katse wayan taji ya kira sunanta ” Samha…”
“Menene kuma!” Ta tambayeshi a dan tsawace tana harare harare.
Sabah yayi murmushi yace ” duk da kofar nan dake tsakanina dake, i can still feel you next to me, you don’t know what you’ve done to me, but my mind is at ease now danaga pretty face dinki, sai da safe”.
Yana gama fadin haka taji ya katse kiran.
Tsayawa tayi tana karewa wayar kallo don Maganganun daya gaya mata a yanzu ba karamin kara kashe mata jiki sukayiba. A kullum Sabah kara dalmiyar da ita cikin kogin sonsa yakeyi. Komai nasa ba karamin burgeta yakeyi ba, most especially behaviour dinsa da kuma yanda yake tafiyar da alamrinsa.
Cike da sanyi jiki ta karasa cikin dakin ta nema wuri ta zauna, kirjinta na bugawa.Washe gari da safe misalin 11:30 pm, Samha tsaye take tare da sauran yan basketball team nasu.
Yau ta kasance ranar da zasuje hiking, kuma wanan hiking din ta zamewa yan team din ta’ada, ko wani lokaci idan competition tana gabatowa sai sunje sunyi wanan hiking din don su motsa jiki kuma su samu intense practice a wajen.
Ko wani team member sanye yake cikin track suit, black and white.
Samha da Aliyah kuwa, a matsayinsu na team managers suma sanye suke cikin track suit dinsu black and white, sai yar karamar gyale da samha ta yafa, ita kam Aliyah p cap dinta ta sanya abunta don babu ruwanta.
Suna tsaye suna jiran team captain dinsu wato Amjad ya karaso, don shi kadai kawai ake jira sai Sabah. Already coaster bus din da zai kaisu yazo yana jiransu.
Bafi minti biyar ba sai ga Amjad nan ya karaso cikin sauri Teacher Sameer yana biye dashi.
Samha tana dagowa sukayi ido biyu da Sameer. Kallonshi takeyi cike da mamaki don batayi expecting zuwansa wajen ba.
Suna karasowa Amjad ya soma basu hakuri akan latin da sukayi kuma tunda makaranta tayi mandating outside school activities dole sai akwai malamin da zaisa ido don haka Sameer yayi volunteering zai bisu kuma ya zama team advisor dinsu.
Zack ne ya taba shinoh yace “kaga wanan malamin wai shinan zaiyi supervising dinmu. Anya zai iya hiking dinan kuwa, kar muje fa ya suma mana a hanya.”
“Ai kam gwanda mu gayawa Amjad ya taho mana da stretcher in case”. Shinoh ya fada yana dariya.
Amjad ya dubi Samha da Aliyah yace “Team managers, what do you think?”
Murmushi Samha ta sake sa’anan tace “Hakan ma yayi don nasan Sameer sosai a da, yana son sports. Don da saura kadan ya samu shiga wani pro basketball team amma hatsarin daya samu yaji ciwo a kafa ne yasa bai cigaba ba yayi give up. Amma he’s very good”
Sameer ya karaso inda take yana murmushi yace “Samha ashe baki manta ba kenan? Kin tuna lokacin da kike karama sai kiyita yiwa amminki magiya akan cewa sai kin bini munje mun buga kwallo?”
Dariya Samha ta sake tana rufe fuskarta cike da jin kunya. Shi kuwa ya cigaba da zolayenta yana tuno mata da yarantar ta.
Basu lura da Sabah ba wanda ya tuko bike dinshi ta daga can gefen titi yayi parking, kura musu ido yayi yana kallon yanda Samha taketa faman murmushi itada Sameer.
Wani irin tafarfasa yaji zuciyarsa na masa nan take yaji wani irin azababen kishi ya lulubeshi.
Samha ce ta fara hango shi, tana dagowa sukayi ido biyu dashi, nan da nan tasha jinin jikinta, murmushin dake manne bisa fuskarta ta dauke. Kirjinta ne ya soma mata wani irin mahaukacin bugu dataga irin kallon da Sabah yakeyi mata da Sameer, don ita kadai tasan ma’anan wanan kallon dayake musu.
Sabah yafi 10 minutes a wajen yana jingine akan bike dinsa idanunsa kyam akansu.
Samha babu shiri tacewa Sameer tana zuwa sa’anan ta karaso inda Sabah yake tsaye ta soma kokarin yi masa magana amma yayi banza da ita. Shidai kawai focus dinshi akan Sameer yake.
Amjad ne yasa sauran team members din suka fara shiga cikin katuwar coaster bus dazai kaisu camp garden.
Bayan kowa ya shiga cikin bus din, Amjad ya karaso shima ya soma kokarin yiwa Sabah magana da akan ya shigo cikin bus din su tafi, don shi kadai ake jira.
Samha ma tasa baki tace “Sabah kazo muje mana”.
“Ku rabu dani kuyi tafiyarku, i’m going alone!” Yana gama fadin haka ya juya a fusace zai tayar da bike din nasa.
Karan horn din mota da sukaji ne ya dakatar dashi.
Gabadaynsu suka juyo suna kallon motar da tazo tayi parking a gefen hanya.
Madinah ce ta fito daga cikin motan ta karaso cikin sauri zuwa inda Sabah da Samha suke tsaye. Sanye take cikin riga da wando pink masu kyau kuma kayan sunyi fitting dinta sosai don Madina babu laifi tanada tsawo.
Sabah yana ganinta ya kara daure fuska a fusace yace “ke kuma meya kawoki nan?”
“Binku zanyi”. Ta fada mishi kai tsaye tana murmushi.
Sauran yan team din da suke zaune cikin bus, suna ganin madina suka soma fitowa daga cikin bus din daya bayan daya, harda Aliyah don itama tana son taji abunda ya kawota.
Sabah ya dubi Amjad yace “kai kacewa yarinyar nan ta biyo mu?”
“Kasan Aliyah tana masscom department, so ita zata dinga tayamu documenting duka activities dinmu”.
“Wake ta Aliyah? Tambayarka nakeyi akan wanan yarinyar datace zata bimu”.
“Oh wai Madina kake nufi, jiya tazo tace zatayi applying a team dinmu, toh kuma kasan we need helping hands as much as we can, shine nayi accepting dinta na bata aikin manager itama, kaga sai ta dinga taya su Samha”.
Tsaki kawai Sabah yaja, sa’anan ya tayar da bike dinsa ya bata wuta yaja ya tafi ya barsu a wajen.
Tsayawa sukayi suna bin bayansa da kallo har ya bace musu daga gani, musamman Samha wace take bin bayansa da kallo cike da takaicin abunda yayi.
Amjad ne ya saki ajiyar zuciya sa’anan yace kowa ya koma cikin bus din su tafi, lokaci na tafiya.
Suna shiga cikin bus din, Madina ta likewa Samha suka zauna wuri daya.
Ita kuma Aliyah ta zauna kusa da Zack, don cikin coaster bus din, ko wani row akwai seat biyu side by side.
Bayan kowa ya zazauna, driver ya tayar da bus suka dau kan hanya.
Sun danyi nisa da tafiya, Samha tana zaune tayi shiru tunani kala kal na mata yawo aka tana kokarin ta fahimci dalilin dayasa Madina tace zata bisu.
Kallon madinan tayi sa’an tace “Madina, meyesa kikeso kiyi joining basketball team namu?”
Madina ta da’an dubeta fuskarta dauke da murmushi tace ” ai na fada miki ranan, i just want to be friends with you and Sabah. Tunda kina nan, nima ina nan, Inaso na kasance tare daku”.
Samha zaro ido tayi jin abunda ta fadi, can kasan ranta tace “so, saboda useless kindness dina ne yasa ta sake jikinta haka?” Wata zuciyar tace mata. “Ai inkin lura Madina bata san komai ba. Kilan bada wata manufa takeso tayi abota daku”. Wata zuciyar kuma tace mata “Anya kuwa? Are you sure about that?”.
Madina ce ta katse mata tunanin da takeyi tace “Big sis, wlh tsoro nakeji. Bansan kowa anan ba sai ke”.
Shinoh dake zaune a bayansu ne ya jiyota yace “Haba gimbiya, kyace baki san mu ba. Ko har kin manta da wanan handsome face din da kika gani ne ranan?” Ya karasa maganar yana shafo fuskarsa yana daga mata gira daya.
Madina kawar da fuskarta tayi gefe tana da’an murmushi.
Shinoh ya cigaba da zolayenta yace “daman inaso na tambayeki madina, meya sameki ranan da numfashinki ya dauke kike kokarin suma?. Ko bakida isashen lafiya ne?”
Madina ta da’an yi shiru sa’anan tace “inada anemia ne shiyasa, kuma ranan i was very nervous”
“Oh Ayya, karki damu daga yanzu I’m going to take very good care of you kinji”. Shinoh ya fada mata yana washe baki.
Abba ne ya katseshi yace “kai dallah mallam rufe mana baki, duk kabi ka ishe mutane da surutu. Meye zaka iya tsinana mata in banda ka cikata da surutu?”.
Dawo da dubansa ga madina yayi sa’anan ya cigaba da fadin “karki damu Madi, gani nan ki dauke ni a matsayin yayanki, ki manta da shirmen wanan yaron, ni zan kula dake”.
Dariya suka sa a tare, shinoh ya soma musu dashi yace bai isa ba, shine yafi cancanta ya kula da ita.
Zack shima ya dubeta bai san sanda yace “Madina kinada kyau sosai. Masha Allah”.
From nowhere yaji an zungure mishi kai, juyowa yayi yaga Aliyah dake zaune kusa dashi tanata faman hucci tace ” a gabana kake cema wata tanada kyau?”
“Toh meye? Ai gaskiya na fada”. Ya fada mata yana shafo inda ta zungure mishi kai .
” Toh ni bana so, wai tsaya ma tukuna, daga ina ta bullo ne wai saboda ni gaskiya bata mun ba”. Aliyah ta fada tana tabe baki.
“Ai itace wace kakar Sabah take kokarin ta hadashi suyi aure. Baccin haka ma akwai wata cousin dinshi ma da take bala’in sonsa amma kema kinsan halinsa sarai duk basu gabansa”.
“Anya kuwa? Ka tabbata? Komai fa na iya faruwa. There’s uncertainty written all over it”.
“Kedai kice you’re too sensitive. Me kuma zai faru?”.
“Ba wani zancen i’m too sensitive, besides taya ma zaka soma hada yarinya ajebo kamar Madina da Sabah wanda kowa yasan zama dashi sai ka shirya. Kaima kasan wanan hadin bazai yu ba, it’s hard against soft. Ai shiyasa nima nayi loosing dinshi zuwa ga Samha. Don wanan madina da nake gani take takenta she has more firepower than Samha. Karka sha mamaki itama ta jawo hankalin sabah zuwa gareta”. Ta karasa maganar tana watsawa inda su Samha suke zaune harara.
Zack bai ce mata komai ba yayi shiru yana kallon wani direction daban.
“Yanaga kayi shiru baka ce komai ba”. Aliyah ta tambayeshi.Ajiyar zuciya ya sake sa’anan yace “toh me kikeso nace miki Aliyah, naga kamar har yanzu you’ve not gotten over Sabah. Har yanzu kina sonshi koh?”
Shiru Aliyah tayi ta kawar da fuskarta gefe, don bata san ansar da zata bashi ba. Tasan gaskiya ya fadi, don ita dai a baki ta hakura da Sabah amma can kasar zuciyarta tasan bazata taba daina sonshi ba.
Haka suka karasa sauran tafiyan, kowansansu yayi shiru da abunda yake masa yawo a zuci.
Samha dake zaune a gefe ta wurin window tayi zurfi cikin tunani, karan bike din Sabah taji dab da window dinsu, cikin sauri ta leko ta ganshi yana tafe dab dasu, idanunsu ne suka tsarku cikin junansu, ya kura mata kyawawan idanunsa yana kallonta har na dan tsawon minti biyu daga bisani ya karawa bike dinsa wuta, ya wuce su.
Jikin Samha ne ya kara yin sanyi, ta rasa ma inda zata sa kanta taji dadi don kwata kwata bata son hakan yana faruwa tsakaninta dashi.
Suna isa camp garden, inda zasuyi hiking dinsu. Daidai wurin gate din bus dinsu ya tsaya yayi parking, suka soma saukowa daya bayan daya.
Already Sabah shi ya rigada ya rigasu isa, don haka suna shiga ciki suka ci karo dashi.
Tsaye yake rataye ta jakansa a kafadarsa, Samha tana ganinshi taja birki ta tsaya tana kallonsa, shima ido ya kura mata.
Aliyah ce ta karaso inda yake tana murmushi tace mishi sauran yan team fa sun rigada sun fita har sun soma shirye shiryen workout din da zasu yi. Itama yanzu zata je tayi joining dinsu.
Sabah ya danyi shiru yana dubanta sa’anan yace “toh shikenan, ki jirani. Bari na shiga ciki na ajiye jakana tukuna”.
Aliyah ta gyada masa kanta tace “toh”.
Har ya soma takowa zai wuce ciki, Madina tazo ta tareshi tana murmushi tace “Sabah bari na tayaka rike jakanka”.
Shiru yayi yana kallonta daga bisani ya dawo da dubansa ga Samha suka hado ido.
Ciro jakar yayi daga kafadansa, Madina har ta mika hannu zata karba taga ya mikawa Samha jakan yace “Samha, ungo shiga mun da wanan ciki”.
Jiki babu kwari Samha tasa hannu ta karba, idanunta akan Madina wace taja jinin jikinta, Gabadaya Samha sai taji babu dadi.
Juyawa tayi ta soma kokarin shiga ciki taje ta ajiye mishi jakan.
Shi kuma ya juya tare da Aliyah suka soma tafiya.
Madina bata dadara ba, still tabi bayansu ta soma kwalawa Sabah kira.
Tsayawa yayi cak sa’anan ya juyo yana dubanta harta karaso.
Itama Samha tsayawa cak tayi jin ta kira sunan Sabah sa’anan ta juyo tana dubanta .
Madina fuskarta dauke da murmushi ta soma fadin “daman Sabah inaso nayi maka godiya akan yanda ka fada mun gaskiya ranan, naji dadi kuma nagode kwarai da gaske”.
“Bakiji haushi ba kenan?”
Ta girgiza masa kanta tana murmushi tace “ko kadan. Ai duk laifi nane, bai kamata nazo na tareka da irin wanan maganar ba, kuma daga baya na zauna nayi dogon tunani akai kuma na gano wani abu”.
“me kika gano?” Sabah ya tambayeta.
“Na gano cewa, idan har kana son mutum it’s impossible to hide your feelings, dole zai bayana, haka zalika ma idan baka son mutum you can’t pretend or force yourself to like that person, so rejecting me was the right thing to do. Thanks for not letting me have my way.”
Sabah kura mata ido yayi na da’an lokaci sa’anan yace “toh naji amma me ya kawoki nan? Me kika zo yi? Kina tunanin zaki iya aikin manager na team dinan? Are you capable? Ko kuma waman ma yana daya daga cikin tsarinki and it’s another attempt of you having your way”.
Yana gama fadin haka ya juya ya barta tsaye a wajen. Aliyah ta mara masa baya.
Jikinta ne yayi mugun sanyi, kwalla suka soma ciko mata a idanu kamar zatayi kuka.
Samha na ganin haka ta karaso cikin sauri zuwa inda take tsaye ta soma rarashinta tace ta rabu dashi kawai ta fita daga harkansa, daga gani baya cikin good mood ne”.
Madina tasa hannu ta goge kwalar daya samu nasaran gangaro mata tace “toh shikenan big sis, nagode”.
Samha ta dan sakar mata murmushi sa’anan tace “zo muje mu nemowa yan team abunda zasuci da rana kafun su dawo daga training.
Haka taja hannun Madina suka tafi tare.
Sabah da Aliyah suna karasowa suka tadda already yan team sun hadu zasu fara training shi kadai ne kawai ake jira.
Sameer yana ganin sun iso, a matsayinsa na babba kuma malaminsu, ya mike ya soma addressing dinsu kamar haka ” tun kafun muzo nida Amjad mun tsaya mun tatauna akan basis of this training. We need to focus on each player’s physical strength, flexibility, da kuma endurance for target training”.
Tunda Sameer ya fara magana Sabah ya tsaya yana masa wani irin kallo mai cike da tsananin jin haushinsa, kwata kwata baiso Sameer ya biyosu wanan training din ba, ji yake da yanada bindiga a hannu dayasa ya harbe shi ko zai samu sassaucin radadin da zuciyarsa take masa. Baisan meyasa idan wasu suna admiring din Samha dinsa, sai ya dinga jin dadi ba amma da zaran yaga Sameer kusa da ita, he feels threatened gabadaya sai ya kasa samun sukuni.
“Okay now, zamuyi assigning teams one on one defense. Ko wani player ya tsaya da opponets dinsa”. Sameer ya fada yana kallon yan’ team din daya bayan daya.
Ko wani team member yayi positioning kansa a inda ya kamata ya tsaya tare da opponent dinsa.
Amjad shine opponent din Sabah don haka ya tsaya yana facing dinsa.
Bayan Sameer ya tabbatar da kowa yana kan postion dinsa, yasa whistle a bakinsa ya hura.
Nan da nan wasa ta barke tsakaninsu, Suna bugawa Sameer yana guiding dinsu yanda ya kamata suna passing kwallon.
Aliyah na tsaye a gefe don ita take musu video kuma take daukan su hoto.
Sabah yana tsaye sai faman aika ma sameer harara yakeyi. Sameer kuwa baima san yanayi ba, don gabadaya concentration dinsa yana kan wasan da ake bugawa.
Sai daya zo kan Amjad da Sabah zasu buga tukuna, ko wanan su yayi positioning.
Amjad yana rike da kwallon yana facing din Sabah.
Sameer har ya kai whistle din bakinsa zai hura, Sabah ya dakatar dashi yace “coach, tunda kai kayi designing din exercise dinan, idan nayi challenging dinka, kana tunanin kanada ability din da zaka iya kwatan wanan ball din daga hanuna?”
Kowa yayi shiru aka tsaya ana kallon kallo cike da mamakin Sabah da yace zaiyi challenging din Sameer.
Murmushi kawai Sameer ya sake don ya rigada ya gano inda zancen Sabah din ya dosa don haka yace ” the question is not about my ability, but my intention”.
“Kanada ita?!” Sabah ya watso mai tambayar a dan tsawace.
“Ina ruwanka!” Sameer shima ya watsa mai tambayar a tsawace.
Ko ina yayi tsit, Kowa a wajen sai daya ja jinin jikinsa ganin irin kallon da Sameer da Sabah suke watsawa junansu.
Zack ne ya matso kusa dasu shinoh ya soma magana kasa kasa yana fadin “wai meye matsalar SB da wanan guy dine?”
Abba yace “nima wlh ban sani ba, tunda muka zo kaga kallon dayaketa watsa mishi kuwa?”
A fusace Sameer yaje ya kwace kwallon daga hannun Amjad ya jefewa Sabah sa’anan yace “Bisimillah”.
Sabah ya capke ball din ya dago yana kallonsa da idanunsa da suka rikide tsabar masifa da kishi dake cinsa.
Sauran yan team din suna tsaye a gefe suna kallonsu.
Sabah yana rike da kwallon ya nufoshi gadan gadan, shima Sameer haka ya nufoshi
Sabah ya kara wuta yana kokarin yaje ya jefa ball din cikin raga, har sun iso dab da jinansu from nowhere yaji Sameer ya kwace ball daga hannunsa.
Sabah tsayawa yayi cak yana zaro ido don jin abun yayi kamar film yana mamakin yanda akayi Sameer ya kwace ball din daga hanunsa.
Sauran yan team din ma kallon kallon ne ya barke tsakaninsu suna mamakin yanda akayi Sameer ya kwace kwallon daga hanun Sabah.Bangaren su Samha kuwa. Bayan ita da Madina sunje sun siyo wa yan team abunda zasu ci.+
Zaune suke daidai bakin wani ruwa dake cikin wurin suna dan taba hira.
Samha ta dubi Madina tace ” Madina, ranan kince kinada wanda kikeso. Waye shi?”
Madina ta da’an saki murmushi sa’anan tace ” eh inada wanda nakeso, saboda a lokacin dana fara haduwa dashi, sai da zuciyata ta buga, don ban taba jin haka a game da wani da namiji shiyasa nan da nan i fell for him”.
Samha tayi murmushi sa’anan tace ” so ya kuke dashi yanzu, kuna dating ne?”
Madina ta da’an girgiza mata kanta tace “a’a nifa yanzu haka ban ma san inda yake ba. Ko kamaninshi ma ban gama tabbatar wa ba”
Cike da mamaki Samha ta soma kallonta tace “kai Madina, ban gane ba”.
“Kinsan inada heavy eye glass prescribtion. Bana gani sosai sai da taimakon wanan eye glass din”
Cikin sauri Samha ta mike, tazo ta tsuguna dab da Madina tana kallon cikin kwayar idanunta cike da mamaki tace “yanzu kina nufin baki ganina da kyau kenan?”
dariya madina tayi sa’anan tace ” ina gani mana, yanzu haka sanye nake da contact lens cikin idanuna. Bari kiji yanda haduwar namu ta kasance. A ranar na fito cikin layin mu ina tafiya ni kadai kenan ban ankara ba motarsa tazo saura kadan ya kadeni don na shiga hanya kai tsaye ne ban lura ba, a sanadiyan haka ne na fadi glasses dinsa suka fashe, shine ya fito ya taimakamun har ya kaini eye clinic aka mun wasu, daba din shi ba ban san ya zanyi ba a ranar. He rescued me like a knight in shining armour”.
Samha ta jinjina mata kai tace “wow, yanzu kina nufin guy dinan is a total stranger to you kenan? Baki san sa ba, Kuma a hakan kike sonsa?”
“Kwarai kuwa. Sonshi nake sosai kuma kullum addu’ata da fatana bai wuce Allah ya kara hadani dashi ba. Banyi loosing hope ba Big sis, don har yanzu inaji a jikina cewa nan bada jimawa ba zan kara ganinshi, kuma idan na ganshi babu abunda zai raba ni dashi insha Allah”.
Samha tayi shiru tana kallonta, jikinta ne kara yin sanyi ganin yanda Madina taketa faman zuba akan wanda ma bata sanshi ba, bai ma san tanayi ba. “She’s just like the old me, living in a world of fanatsy, creating an idealized person. Love only exists in her imagination”. Samha ta fada can kasan ranta tana kallon Madina.
“Wato wanda Madina ta dage tana kirarin cewa tanada wanda takeso ba komai bane illa fantasy?” Suka ji muryan Aliyah a bayansu.
Tare suka jiyo suka ganta tsaye tayi folding hanayenta bisa kirjinta tana kallonsu. Ashe duk maganar da sukeyi tana tsaye tana jinsu bata ce komai ba.
Karasowa tayi inda suke zaune sa’anan ta cigaba da fadin “wanan unrealistic love din dakikeyi har ina zata kaiki? kuma har yaushe za tayi miki lasting? baki tunanin wata rana waenan feelings din zasu iya transferring zuwa ga wani?” Ta karasa maganar tana kallon Samha.
Nan da nan Samha ta gano abunda take nufi, wato Feelings din madina zai iya canzawa zuwa ga Sabah kenan?
Cike da tashin hankali Samah ta soma kallonta.
Madina ta mike tana murmushi tace “kinji maganar da mukeyi kenan?”
Aliyah kallonta tayi na da’an wani lokaci sa’anan ta dawo da dubanta ga Samha sa’anan ta soma magana cikin harshen turanci tace “Samha there’s one kind of rival that is hardest to beat, and that is without you realizing, she’s already between you two. And when you look at her innocent expression, you can’t condemn her”.
Samha shiru tayi tana jinta cike da tashin hankali don tasan warning kawai Aliyah take mata akan Madina tayi taka tsantsan da ita don komai zai iya faruwa.
Ita kam Madina kallonsu kawai takeyi cike da rashin fahimtar abunda Aliyah ta gama fadi. Ta juyo tana duban Samha tace “Big sis ban gane ba, meye Aliyah take nufi? Kodai kema kinada wanda kikeso ne?”
Samha tayi sauri ta mike don bata son Aliyah ta fada wata magana madina ta gano don haka ta soma fadin “Aliyah ya naga kin dawo da wuri haka? Har kun gama training dinne?”
Aliyah tace “a’a basu gama ba, sunayin retreat endurance exercise ne zasu fara hiking har zuwa saman waenan duwatsun, ni kuma na gaji bazan iya hawa ba shiyasa na dawo”.
Samha tace “toh”.
Bangaren su Sabah kuwa bayan sun gama hiking sun hau can saman duwatsun, Amjad yaja shi gefe yace “Sabah ya naga you’re acting different today? What’s wrong?”
“Different kamar ya?”
“Abubuwan da kakeyi ne yau kwata kwata sai a hankali, meyasa idan kaga Teacher Sameer kake gagara samun nutsuwa? You’re so insecure around him?”
Wani irin kallo Sabah ya watsa mishi sa’anan ya juya ya soma tafiya.
Maganar Amjad ne ya tsayar dashi inda yake fadin “ni Sabah din dana sani baya haka, he’s always confident around others. I’m not used to seeing an unconfident Sabah, kaima nasan you’re not used to it either”.
Sabah bai ce masa komai ba ya gyada kansa sa’anan ya cigaba da tafiyarsa zuciyarsa na masa tafarfasa, tunani kala kala na masa yawo a ka.
Bangaren su Samha kuwa, Samha ce ta dubi Madina tace “Madina bude wancan jakan, akwai wasu drinks dana taho mana dasu suna ciki ki kawo”.
jiki na bari Madina ta mike tace “toh Big sis.” Sa’anan ta karasa inda jakan yake ta bude ta ciro drinks din sa’anan ta soma takowa inda su Samha suke zaune, bata ankara ba kafarta na dama ya buge wani bottle water da aka sha aka rage ya fadi ruwan ciki ya soma zuba kota ina”.
Tsayawa tayi cak tana kallon yanda ruwan yake zuba. Aliyah taji haushi tace “dan Allah duba, wai a hakan Amjad yake son wanan yarinyar tayi mana aikin manager?”
Samha ta dubeta tace “Haba Aliyah, ya zaki ce haka?”
“Menene? ai gaskiya na fada”. Aliyah ta fada tana watsawa madina harara.
Kwalla ne suka soma cikowa Madina, Samha ta mike taje ta tsaya kusa da ita tace “kiyi hakuri Madina”.
“Babu komai big sis, banga laifinta ba ai gaskiya ta fada”.
Ta dago tana duban Aliyah tace “nagode Aliyah, you’re also a good person who doesn’t tell lies”.
Hannunta tasa cikin aljihu sa’anan ta ciro box of chocolates din ta mikawa Aliyah.
Aliyah ta dubeta tace “bana son chocolates”.
Madina ta dan saukar da hannunta kasa sa’anan tace “toh shikenan, bari naje na wanke fruits din can na dawo.”
Tana gama fadin haka ta dauki baskets din dake cike da fruits ta fita ta barsu a ciki.
Madina na barin wajen, Samha ta juyo a fusace tana kallon Aliyah tace “Haba Aliyah meya…..”
Aliyah bata bari ta karasa maganar da takeson yi ba tace “kawai bana sonta ne, yarinyar bata mun ba. Kema kin dage kina wani mata dariya kina biye mata, sai ta janyo hankalin Sabah zuwa gareta tukuna idonki zai bude”.
Samha tace “kai Aliyah,bana tunanin hakan zata kasance. Madina fa babu ruwanta”.
“Tsaya nan kina cewa babu ruwanta, nidai na gaya miki. Jikina na bani cewa idan har kika kuskura yarinyar nan ta samu kusanci da Sabah to taki ta kare. I’m just warning you”. Tana gama fadin haka ta juya taje ta nema wuri ta zauna.
Samha shiru tayi tana nazari daga bisani tace “naji but i’m still worried about her, bari naje na dubota”.
Bangaren Madina kuwa, daidai wurin bakin ruwan ta ajiye basket din fruits din sa’anan ta nema wata katuwar dutse dake kusa da bakin ruwan ta zauna. Chocolates din data mikawa Aliyah taki karba ta kurawa ido tana fadin ” wai daman akwai mutane a duniyan nan da basu son chocolates kuma basu son Madina?”
Sabah ne yazo wucewa ya jiyo ta tana magana ita kadai, tsayawa yayi cak yana kallonta. Ita kam sai faman surutun ta takeyi bata ma san yana tsaye yana kallonta ba.
Har ya juya zai tafi sai ya jiyota tana fadin “inaga bayan an gama wanan hiking din i’ll just give up, tunda na nuna musu inaso nayi abota dasu amma duk sun kini, babu wanda yakeso yayi muamala dani”.
Jin abunda ta fadi ne yasa jikinsa yayi sanyi, ya soma takowa har yazo ya tsaya a bayanta sa’anan ya kira sunanta yace
“Madina..”
A firgice ta waiga tana kokarin mikewa bata ankara ba tsantsin wurin yajata sai jin kanta tayi cikin ruwan.
Wani irin ihu ta sake tana daga hanayenta sama. Babu shiri Sabah shima yabi bayanta ya fada cikin ruwan, swimming yayi har inda take sa’anan ya samu nasaran kamota ya cirota daga cikin ruwan.
Duk tabi ta firgita sai faman zaro ido takeyi tana karkarwa. Sabah ya kaita kan dutsen ya zaunar da ita.
Ita kuwa sai faman karkarwa takeyi, dagowa tayi yana dubansa, sai ta soma ganinsa dishi dishi. Gabadaya features dinsa bata gani da kyau. Sufansa da take gani a wanan lokacin tamkar wanda ta gani ranan data fadi akan titi mota ta kusan bugeta.
Sabah ya dubeta yace “Are you okay?”
Mitsike idanunta tayi sa’anan ta bude su, still bata iya ganinshi da kyau don haka tace mishi “a’a, contacts dina sun fadi cikin ruwa. Bana gani da kyau”.
Tari ta somayi tana kame jikinta, sabah yayi sauri ya cire bakin jacket din jikinsa ya lulubeta dashi sa’anan yace mata yana zuwa.
Cikin ruwan ya koma ta daidai baki bakin yasa hannu yana lalube ko zai ci karo da contacts din nata.
Ita kuwa, kara janyo jacket din zuwa jikinta tayi tana jin daddaden kamshin turarensa na bugun hancinta.
Daidai wurin hanun jacket din ta laluba taji babu button.
Cikin sauri tasa hannu ta ciro button din datake dauke dashi a ko wani lokaci, don tun lokacin data tsinta button din bayan ya tafi ya barta a eye clinic din ta adana shi.
Tana manna button din akan hannun jacket din taji yayi fitting daidai.
Nan da nan taji kirjinta ya buga, zuciyarta ta soma raya mata cewa Sabah ne guy din daya taimaketa ranan data fadi. Shine guy din data jima tana mafarkin kara haduwa dashi.
Wani irin sanyi dadi ne ya ziyarce ta nan take datayi realizing cewa he’s the one bata san sanda ta mike ta kamo hanunsa cikin nata ba tana fadin “Alhamdulillah, at last i’ve found you. Daman kaine wanda na jima ina mafarki na kara haduwa da?! Daman all these while kana nan kusa dani ban sani ba? I’m so happy wlh Sabah. I’m so happy it’s you”.
Sabah tsayawa kawai yayi yana kallonta.
Daidai lokacin da Samha ta bullo kenan taci karo dasu a hakan, Madina tana rike da hannunsa tana aika masa da murmushi.Bugun kirjin Samha ne ya karu, nan take taji bazata iya kara koda minti daya a wajen ba don haka kafun su ganta, ta juya ta soma tafiya jikinta a mugun sanyaye.
Sabah ne ya juyo yana duban Madina wace taketa faman murna kamar zata hadiye shi. Ya dawo da dubansa ga hannunta inda ta rikeshi gam yace “mallama ya haka? Cika mun hannu mana”.
Madina ta sakar masa hannu, tana murmushi cike da zumudi ta soma fadin ” Kaga yanda Allah yake tsara abunsa ko, we are really connected and destined for each other Sabah, ranan dana fadi kan hanya har glasses dina suka fashe kaine ka taimaka mun, tun daga lokacin naketa mafarkin Allah ya sake hadani dakai. Ban taba tunanin kaine wanda daddy na yakeso ya hadani aure da ba.”
Sabah d yayi shiru yana kallonta ya saki ajiyar zuciya yace “i thought i made myself clear ranan, it doesn’t matter ko kece yarinyar dana taimakawa ranan ko kuma yarinyar da tsofin mu suke son su hadani aure da. I’m not interested in you, bana sonki”. Ya fada mata kai tsaye.
Wani irin zafi Madina taji a cikin kirjinta dajin kalamansa ta marairaice fuska tace “Sabah please don’t do this to me, tunda nake ban taba jin zuciyata ta buga akan wani da’ namiji ba sai akanka. Inasonka, pls Ka dan bani dama mu fahimci juna, kilan na samu gurbi a cikin zuciyarka”.
“Bazai yu ba”. Ya sake fada mata kai tsaye.
“It’s okay, I don’t want to give up don akan sonka zan iya yin komai” Madina ta fada mishi tana kallon cikin kwayar idanunsa.
Sabah shiru yayi yana kallonta bai sake cewa komai ba.
Samha tana karasawa ta nema wuri ta zauna jikinta a matukar sanyaye. Aliyah ce ta bita da kallo tana mamakin ganinta haka.
Samha har tayi zurfi cikin tunani sai ga Sameer nan ya karaso inda suke yazo ya tsuguna a gabanta yana tambayarta abunda yake damunta.
Har ta bude baki zata bashi ansa, sai ga Sabah nan ya taho, Madina tana biye dashi.
Tsayawa yayi ciruss yana kallon yanda Sameer ya tsuguna a gaban Samha, nan take yaji kishin ya sake taso masa sabo. Zuciyarsa na masa tafarfasa, Har wani dishi dishi ya soma gani tsabar kishin da yake cinsa.
Itama Samha juyowa tayi tana kallonsa, sa’anan ta dawo da dubanta ga Madina dake tsaye kusa dashi. Nan take itama taji wani irin kishi ya rufeta ta kawar da kanta gefe.
Sameer shima shiru yayi yana kallonsu don yama rasa me zai ce.
Suna cikin haka, sai ga sauran yan team nan sun karaso, Gabadayansu a gajiye suke don ba karamin training suka sha ba.
Samha da Aliyah ne suka mike suka soma serving dinsu abinci, itama Madina tazo ta sa musu hannu.
Nan hira ta barke tsakaninsu, sunata raha akan training din da suka sha yau.
Shikam Sabah wuri ya samu a gefe ya zauna, ya cika yayi fumm, yaki kula kowa zuciyarsa sai faman tafarfasa yakeyi. Samha tazo tana kokarin yi masa magana ma yayi banza da ita yaki kulata har ta gaji ta kyaleshi.
Madina ta dago tana dubansa, itama tana so tayi masa magana amma tana shakka don taga yanayin nasa ne sai a hankali.
Hannu tasa cikin jakarta ta ciro chocolates ta soma rabawa kowa a wajen.
Aliyah dake zaune kusa da zack ta watsa wa Madina wani irin kallo tace “wlh na tsani ganin yarinyar nan, kwata kwata ban kaunar ganinta, ko dayake kune kuka janyota ai, daman ku maza haka kuke ba daman kuga farar mace”.
Zack ya dubeta yace ” kuma ai mata kunfison irin kalan namijin da zaiyita wahalar daku”.
Harara Aliyah ta watsa mishi don tasan da ita yake kuma tasan inda maganar nasa ya dosa don haka ta mike ranta a bace tace “wai zack meke damunka ne yau?! Tun muna hanya kaketa wasu maganganun da ban gane kansu ba”.
Zack yayi shiru ya kura mata ido yana kallonta.
“Kayi shiru kana kallona!” Ta fada mishi a da’an tsawace.
Zack yace ” kawai… i’ve been thinking da nima inayin abubuwa kamar SB, da kilan nema sona ya shiga zuciyarki”.
Aliyah tayi shiru tana kallonsa don tama rasa me zata ce masa.
Bangaren Samha kuwa, tsaye take a gefe gabadaya ji tayi abun duniya ya isheta, taji gabadaya trip dinma ya fita a ranta tana so su koma gida kawai.
Sameer ne yazo ya tsaya a kusa da ita yana tambayarta ” samha wai meye ke damunki ne naga duk kinbi kinyi wani iri? Ko akwai wani matsala ne?”.
Samha ta da’an kirkiro murmushi tace masa ba komai.
Sameer bai gamsu da ansarta ba don haka yace ” kin san meye Samha. Ran dana fara zuwa makaranta na ganki, a tunanina baki chanza daga yanda na sanki a da ba, daga baya sai kuma na gano cewa you’ve changed alot”.
“Kamar ya?”
“Yanzu naga rai da rai baki cikin walwala, kuma ba haka na sanki a da ba.”
Samha ta da’anyi murmushi tace “ni kuma baka canza mun ba, kana nan yanda na sanka. Still very considerate and matured”
“Allah ko? Toh nidai yanzu ki fadamun menene ke damunki?”
Samha tace mishi babu komai. Sameer bai daddara ba haka ya sata a gaba da tambayoyi yana kokarin yaji abunda ke damunta, dayaga batada niyan fada mishi yasa ya soma janta da hira har ya samu ta sake jiki sosai suka soma hira suna dariya tare.
Hakan da sukayi ba karamin kular da Sabah yayi ba don duk hiran da sukeyi idanunsa na kansu, ya cika yayi fumm jira kawai yake ta fashe.
Bayan sun gama hutawa, Amjad yazo yayi announcing komawarsu yace driver yazo yana jiransu.
Haka kowa ya mike ya shirya sa’anan suka soma shiga cikin bus din daya bayan daya suka kama hanya.
Sabah kam daman shi ko takansu baibi ba, bike dinsa ya tayar a fusace ya kara mata wuta ya tafi ya barsu. Tuka power bike dinsa yakeyi mai shegen gudu sai faman kara mata wuta yakeyi kamar zai tashi sama. Tuki yakeyi amma hankalinsa baya jikinsa, gabadaya tunanin Sameer yakeyi da yanda Samha ta sake jiki dashi tanata faman kyalkyale dariya, Yaji gabadaya hankalinsa ya kara tashi Yana hango bus dinsu ya taho, ya rage gudun da yakeyi yaje yasha gabansu.
Babu shiru driver din ya taka birki ganin yanda Sabah yazo yasha gabansu ya tsaya akan hanya.
Suma kansu da suke cikin bus din sai da suka firgita.
Sabah ya sauko daga kan bike dinsa yayi parking sa’an ya karaso cikin bus din. Binsa da kallo aka somayi amma bai bi takan kowa ba, Kai tsaye inda Samha take zaune kusa da Madina ya nufa.
Madina tana ganinshi ta soma murmushi don a tunaninta wajenta yazo don haka ta soma Murmushi tana aika masa da wani irin kallo mai cike da so da kauna.
Sabah yazo ya tsaya a gabansu idanunsa kyam akan Samha yace “keh, taso mu wuce gida”.
Samha tayi shiru ta tsura mishi ido tana kallonsa daga bisani tace “au wai dani kake?”
“Da waye? Ki tashi mu tafi nace”.
Babu shiri Samha ta mike ta tattaro jakanta sa’anan tabi bayansa suka sauko daga cikin bus din tare.
Sameer yabi bayansu da kallo cike da mamakin issa da gadara irin na Sabah.
Tare suka karasa shida Samha zuwa inda yayi parking bike dinsa.
Samha ta dubeshi tace “kana nufin ni zan hau wanan katuwar mashin din mai uban gudu? Kallan naje na fadi na karya wuya? A’a wlh.”
Sabah ya sake ajiyar zuciya yana dubanta yace “zaki taka kenan?”
Samha ta girgiza masa kanta.
Hannu yasa Ya ciro wata katuwar helmet blue colour, ya mika mata yace “toh ungo nan ki sanya, for safety”.
Samha ta kurawa helmet din ido tace ” saboda ni ka siyo wanan helmet din?”
Sabah ya gyada mata kansa yace ” ban jima da siyanta ba”.
Samha ta da’an turo dan karamin bakinta gaba tace “toh ni bana son wanan kalar”.
Sabah yaja tsaki yace “ke nifa bana son feleke, bakiga har design akayi mata na musamman ba”.
Samha ta kurawa helmet din ido taga an mana mata sticker din star tace “ya naga an sa mata design din star?
Bai bata ansa ba ya tura mata helmet din ya hau kan bike dinsa yace “ni kinga tafiyata tunda naga alama baki shirya tafiya ba, kin tsaya kina watso mun tambayoyi kamar wata yar’jarida”.
Harara Samha ta watsa mishi tana turo baki ta sanya helmet din akanta sa’anan ta hau bayansa ta zauna.
Sabah ya tayar da bike din suka kama hanyar zuwa gida, Wani irin gudu yake shararawa akan titi tamkar zasu tashi sama. Addu’a kawai Samha takeyi, Allah ya kaisu gida lafiya.