ZABIN SAMHA CHAPTER 13

 ZABIN SAMHA CHAPTER 13

Yau kwana biyu kenan da tafiyar Madina.

Amjad, Zack, Aliyah da khadie zaune suke a cikin class suna tataunawa.

Zack yace “tab daman Teacher Sameer da Samha sunyin sharing irin wanan past din? Amma Amjad, kace Khaleesat din tanada kyau sosai?” Ya karasa maganar yana murmushi yana shafa sajensa.

Harara Aliyah ta watsa mishi tace “meye haka kuma?”

Hakuri ya soma bata yana sosa kai.

Tsaki ta buga mishi sa’anan ta dawo da dubanta ga khadie tace “khadija ya kike tunanin za’ayi kenan?”

Zack yace “ya kamata mu taya khaleesat kwato soyayyarta daga wurin teacher sameer, ko ya kuka ce?”

Dukkansu suka gyada kai suka yarda da wanan shawaran.

Sameer kuwa yana cikin office dinsa sai faman trying  number khaleesat yakeyi amma sai yaji a kashe. Gabadaya hankalinsa a tashe yake ya gagara samun sukuni.

Yana zaune yaji anyi masa knocking a kofa, dagowa yayi yana duban kofar sa’anan ya bada izinin shigowa.

Su Zack ne yaga sun shigo suka soma gaishe shi, ya nuna musu wurin zama.+

“Ya lafiya?” Ya tambayesu.

Khadie tace “munzo ganinka ne Teacher Sameer”.

“Akan batun Khaleesat ne”. Aliyah ta fada mishi kai tsaye.

Wani irin jimm yayi ya kawar da fuskarsa gefe.

Khadie ta cigaba da fadin “gaskiya teacher Sameer you need to do something about this, karka bari Khaleesat ta kubuce maka. Tun wuri gwanda kasan abunyi”.

Ajiyar zuciyar Sameer ya sake sa’anan yace ” banjin zata saurareni kuma, i’ve disappointed her too much”.

Aliyah tace “karka manta Teacher Sameer, khaleesat ta baka tsawon hour ashirin da hudu ka nemeta, kaga you still have time to go after her, don’t give up”

Khadie tace “yau ne birthday din Samha, kaga daga yanzu zuwa gobe ya kamata kayi fighting love din dake tsakaninka da khaleesat”.

Shiru yayi yana sauraronsu daga bisani yace “toh shikenan. I’ll give it a try”.

Godiya yayi musu sosai da sukazo suka bashi wanan shawaran da karfin gwuiwan.

Sameer yana tashi daga school straight gidansu Samha ya nufa don ya bata birthday gift dinta.

Daman ya kira Anty Fanneh a waya ya sanar da ita zuwansa.

Cike da fara’a Anty Fanneh tarbe shi a parlour suka zauna.

Bayan sun gaisa, ta soma tambayarshi ya makaranta. Yace mata lafiya lau alhamdulillah”.

“Samha fa?” Ya tambayeta.

“Wlh dazun ta fita na aiketa, amma bazata jima ba yanzu zata dawo”.

Sameer yace “okay daman na kawo mata sakonta ne na birthday”.

Anty fanneh tace “oh ni, Sameer kai dai baka gajiya”.

Dariya kawai Sameer yayi, Anty fanneh ta mike tace mishi tana zuwa sa’anan ta karasa kitchen.

Bangaren Su Samha kuwa, tsaye suke ita da Sabah a cikin SuperSaver supermarket, Sabah yana kokarin yiwa matar dake tsaye a gaban counter din magana yace mata sunzo karban cakes din da akayi order.

Matar tace “birthday cakes ne?”

Sabah yace mata “eh”.

“Toh shikenan, bari nasa ayi muku boxing dinsu”.

Tana gama fadin haka tace su bata yan’mintuna sa’anan ta shige ciki.

Samha ta juyo tana aika masa da murmushi, kallonta yayi ta gefen ido sa’anan ya kau da kai yace “kefa zaki dauka, don bazan iya daukan kayan nauyi ba”.

Samha turo baki tayi, zatayi magana sai ga matar nan ta fito hanunta dauke da wata katuwar kwali mai dauke da cakes ta dire a gabansu.

Samha tasa hannu ta dafe kwalin, zoben da Sabah ya bata wanda yake makale a da’an yatsan tane ta tsurawa ido, tayi shiru tana nazari. Tunani takeyi ko ta cire zoben don bata son Anty Fanneh ta gani ta soma mata wasu tambayoyi. Sai kuma ta tuno da maganganun Sabah a inda ya zira mata zoben yace mata karta cire ta tabbatar tana sanye da ita kullum.

Ajiyar zuciya ta sake, Sabah ya dauki kwallin cake din suka fito daga cikin supermarket din tare.

Suna tafiya zasu karasa inda yayi parking mota yaga tayi shiru bata ce komai ba.

Sabah ya dubeta yace “lafiya ya naji kinyi shiru haka?”

Ajiyar zuciya ta sake sa’anan ta dago tana dubansa da dara daran idanunta tace “kawai tausayinka nakeji ne”.

Harara ya watsa mata sa’anan yace “Tausayina name kuma?”

“Kawai na tuna abubuwa da dama ne kuma…”

Bai bari ta karasa maganar ba ya katseta da “meye haka, throwback zamu farayi ne ko meye? Ko duk cikin tuna baya na birthday din ne?”

Marairace masa fuska tayi kamar zatayi kuka tace “Haba Sabah”.

Kura mata fine eyes dinsa yayi yana aika mata da wani irin kallo mai cike da tsantsan so da kauna, bata san sanda ta sake murmushi ba ta zagayo bangaren damansa ta tsaya.

kanta a sunkuye cike da tsananin jin kunyarsa ta mika masa hannunta na dama.

Kura wa hannun data mika masa ido yayi  daga bisani ya kalleta, yaga ta kasa hada ido dashi.

Murmushi ya dan sake sa’anan ya tabe baki yace “kin miko mun hannu ya kikeso nayi da waenan kayakin? Baki ganin hanuna a cike suke? You’re so inconsiderate.” Ya fada yana aika mata da hararan wasa.

Tsayawa tayi ta juyo tana dubansa sa’anan ta kira sunansa a hankali.

Shima tsayawa yayi yana dubanta.

Samha tayi shiru daga bisani ta soma masa magana cikin harshen  larabcin da Madina ta koya mata.

“Zuciyata tana son Sabah, kuma tana son ta kasance tare dashi har abada”

Shiru Sabah yayi yana kallonta cike da mamakin jin abunda ta fadi, don shi yasan a bakin Madina ya taba jin wanan kalmar.

Murmushi Samha ta sakar masa sa’anan tace “Madina ce ta koya mun, kuma nasan ma’anarsa, fata ce mai kyau”.

Sabah shiru yayi daga bisani yace mata “taho mu tafi”.

Tare suka karasa inda yayi parking suka shiga cikin mota ya ja.

Bangaren su Sameer kuwa, Anty fanneh ce ta shigo hannunta dauke da tray na lemu masu sanyi.

Sameer yace ” Anty da baki wahalar da kanki ba, yanzu fa nake shirin tafiya.”

Anty fanneh tace “Haba Sameer, dan Allah ka zauna, yaushe rabon da mu ganka har mu samu mu zauna haka?, dukda dai nan ba gidan daka saba zuwa bane, ai still bata bace ba. Nan ma gida ne”.

Dariya kawai Sameer yayi, Anty fanneh ta soma janshi da hiran yaushe gamo.

Suna cikin hira Anty fanneh tace “Sameer na tambayeka mana”.

Sameer ya dago yana dubanta yace “ina jinki Anty”.

“Game da Samha ne, kwana biyun nan na rasa gane kanta, kamar akwai wani abun da yake damunta tana boye mun”

Sameer yayi shiru daga bisani yace “Anty duk yanda kuke tare da mutum dole akwai wasu abubuwa da bazai iya fito filli ya furta maka ba, dole ya barma cikinsa a matsayin Sirri. Samha yar’ kice Anty, kuma na tabbata abunda yake damunta ya danganci kuricya da kuma yanda ta taso taga kanta ciki ne. Saukin kai irin na Samha da kuma kyawawan halayenta duk daga wurinku ta dauko daga keda Marigayi”.

Kwalla ne suka ciko cikin idanun Anty Fanneh tayi shiru tana sauraronsa.

Sameer ya cigaba da fadin “kinga yanzu Samha girma takeyi, kullum kara mallakan hankalin kanta takeyi, akwai wasu abubuwan da dama da zakiga yana damunta amma bazata iya fito fili ta furta miki ba, karki damu Anty, wanan abun is normal among teenagers, she’ll be fine insha Allah. Saboda Samha yar mallam ce, itace sanyin idaniyansa tun tana karama”.

Murmushi Anty fanneh ta sake tana kokarin mayar da hawayen da suka cika mata ido tace “hakane Sameer, Samha itace sanyin idaniyanmu”.

Suna cikin wanan maganar sukaji anyi sallama an shigo. Samha ce da Sabbah suka karaso cikin parlourn hannunsu rike da ledojin siyayan da sukayi.

Sabah yana ganin Sameer ya tsaya curuss yana kallonsa. Shima Sameer kallon Sabah din yakeyi daga bisani ya dawo da dubansa ga Samha wace taketa faman murna tana murmushi ganinsa a gidan.

Sabah yayi saurin hadiye abunda yaji ya taso masa, yayi kokarin danne zuciyarsa don yanzu ya rigada yasan Samha tashi ce, kuma Samha tamkar kanwa take a wurin Sameer don haka ya karasa ya bawa Sameer hannu suka gaisa.

Anty fanneh da Samha suka shiga da kayan ciki, aka soma shirya shirye.

Ba wani serious party akayi ba, don daga Samha, Sabah, sai Sameer ne zaune a parlourn. Samha ta danyi kwaliya ta saka gown dinta cream colour mai ratsin green flowers, sai dauri data sha, tayi kyau sosai.

Katuwar Cake din aka ajiye a tsakiyar table, sai wasu kanana guda biyu da aka ajiye a gefe da kuma small chops.

Ba jima ba sai gasu khadie sun shigo hanunsu rike da gifts suka karaso ciki suka rungumeta.

Waka suka soma mata na happy birthday, suna tsokanarta tana cewa su bari, Sabah kam sai faman mata dariya yake yana daukansu hotuna.

Lokacin da akazo yanka cake, aka ce tayi addu’a. Addu’oi Samha ta soma jerowa, ta fara yiwa Amminta addu’a da sauran abokanan arziki da sukazo tayata murna. Na ukun kuma shiru tayi ta soma karanto addu’an a zuci.

“Ya Allah ka cika mun burina na naso na kasance tare da Sabbah har abada”.

Kura mata ido Sabbah yayi kamar yasan abunda take karantowa kenan a zuci.

Tana gama addu’ar, Anty fanneh itama tayi nata sa’anan Samha ta yanka cake anata tafa mata.

Bayan an gama yanke cake, kowa ya soma mika mata gift dinsa, zoben da Sabah ya bawa Samha Anty fanneh ta kurawa ido don bata taba ganin Samha da zobe a hanunta ba, shiru kawai tayi bata ce mata komai ba.

Bayan su khadie sun mika mata gifts suka wuce don dare ya soma yi. Shima Sameer ba jima ba yayi sallama dasu ya fice.

Sabah ne ya waiga bai ganshi ba don daman yanata so yayi magana dashi.

Cikin sauri yabi bayansa, a harabar gidan ya tadda shi yana kokarin shiga motarsa yace “Sameer”.

A hankali Sameer ya juyo yana dubansa cike da mamaki yace “Wow this is unusual, ban taba jin ka kirani da sunana ba sai yau”.

Sunkuyar da kansa Sabah yayi daga bisani ya dago yace “meyasa ka tafi ko sallama?”

Sameer yace “bakomai, kawai ina sauri ne akwai inda zani, budurwata na jirana”.

Sabbah yace “hmm in har dai kanada budurwa kamar yanda kake kirari….”

Sameer bai bari ya karasa ba yayi dariya yace “ban gane in har indada budurwa ba, kana nufin banida farin jini da yan mata zasu bini ne ko meye?”.

Murmushi Sabbah yayi sa’anan yace “ai farin jinin nake ne yayi over, don nima ya sani cikin tashin hankali”.

Dariya kawai Sameer yayi yana girgiza kai jin abunda ya fada.

Sabah yasa hannu cikin aljihunsa ya ciro karamar diary daya tsinta na Samha ya mika masa yace “this is for you”.

Shiru Sameer yayi ya kurawa diary din ido daga bisani ya karba diary din yana fadin “bazan taba mantawa ba, nine na taba bata wanan diary din tun tana karama ta dinga rubutu a ciki”.

Sabah ya tabe baki yace “karka damu, ai cike take da memories dinka, duk rubutun da akayi ciki akanka ne, shiyasa naga babu wanda yafi cancanta daya samu diary din sai kai”.

Shiru Sameer yayi ya kura masa ido daga bisani yace “kodai kana tsoro baka son Samha ta rike diary din saboda duk memories dina ne a ciki?”.

Hararan wasa Sabah ya watsa masa sa’anan yace “toh sai meye? Daman na gano manufarka tun farko. So kake ka kwace mun ita, amma ta Allah ba taka ba”

Dariya kawai Sameer yayi yana girgiza kai yace “Sabah kenan, toh inaso ka saurareni da kyau yanzu. A lokacin da Mallam ya bar mun rikon Samha a hannu, yayi expecting dina na riketa ammana kuma na kullan mishi da ita tamkar ciki daya muka fito. Kuma all these years, nasan i’ve lived up to his expectations. Amma yanzu, zan damka ta a hannun wanda zuciyarta tafi so kuma wace zuciyarta take muradi. Don’t disappoint me Sabbah, saboda in har ka kuskura wani abu ya samu Samha ko ta zubda hawaye a dalilinka toh wlh zaka ansa query a hannuna”.

Sabah yayi murmushi yace “kai kam ka cika son wa’azai. Naji zan ansa query to sai kayi sauri kaje, ina budurwarka tana jiranka?”

Dariya sukayi a tare, Sameer ya mika masa hannu sukayi sallama sa’anan ya shiga motarsa ya tafi.

By the time Sabah ya dawo parlour, kowa ya rigada an watse.

Samha kadai ya samu a parlour Zaune ita kadai ta kurawa sauran cake din dake gabanta ido tana tunani.

Bata san sanda yazo ya zauna kusa da ita ba, kamshin turarensa ne ya fargar da ita ta juyo tana dubansa cikin sauri.

“Har ka dawo?”

“Eh Tunanin me kikeyi haka?”

“Bakomai, kawai jiranka nakeyi”. ta bashi ansa kai tsaye.

“Toh a bani cake dina naci”.

Bata masa musu ba, Plate ta dauko da wuka ta soma yanka masa cake din. Kura mata ido yayi yana kallon yanda take yanka cake din a hankali cikin nutsuwa, komai nata ba karamin burgeshi yakeyi ba.

Tana kokarin sa mishi cake din a plate, bata ankara ba icing duk yabi ya bata mata hannu.

Mikewa tayi taje zata dauko Tissue ta goge, Sabah yayi saurin dakatar da ita, from nowhere taji ya janyota ta fada bisa jikinsa.

Wani irin mahaukacin bugu kirjin Samha ya somayi nan take a wajen.

Wani irin kallo Sabah yake aika mata dashi yana sauke ajiyar zuciya. Kokarin kwatar kanta ta somayi, ya kankameta gam a jikinsa, bata ankara ba taga ya kamo hannunta cikin nashi, yatsanta daya bace da cake icing yakai zuwa bakinsa ya soma lasa a hankali yana sucking fingertips dinta.

Wani irin shock Samha taji tun daga tsakiyar kanta har zuwa tafin kafanta, nan take ta tsinci kanta cikin wani irin yanayi wanda bazata iya missaltawa ba. Gabadaya shock din da takeji a jikinta ya hanata kwakwaran motsi.

Shi kansa Sabah wani irin zallar shaukinta wanda bai taba ji bane yaji yana circulating a tsantsar jikinsa.

Sai daya gama lashe icing din daga yatsunta tass tukuna ya tallafo fuskarta ya mana mata soft kiss a baki sa’anan ya rada mata a kunne “Happy birthday Baby”.Kunya ne ya lulube Samha ta sunkuyar da kanta kasa.

Sabah ya matsa baya ya jingina da jikin kujera ya lumshe idanunshi yana sauke ajiyar zuciya a hankali yace “kanwata…..”

Da kyar Samha ta iya dago kanta ta zuba mishi manyan idanunta, kura mishi ido tayi tana kallon flawless face dinsa wanda idanunshi a lumshe yake yana mayar da numfashi a hankali, nan take taji sonsa ya sake mamaye zuciyarsa. Babu macen da zata ga Sabah bataji matsanancin sonshi ya kamata ba, komai nashi daban yake da sauran maza har yau bata ci karo da namiji daya tattara komai irin nasa ba. Tabbas yanzu ta rigada ta gama tabbatar wa kanta cewa bazata iya rayuwa da wani da’ namiji in bashi ba, sonsa a jininta yake.

Jin shirun yayi yawa ne yasa ya bude kyawawan idanunsa ya sauke su akanta. Dagowa yayi yana matso kusa da ita ya kamo hannunta cikin nashi yana shafawa a hankali yace ” Kanwata yaushe zamuyi aurenmu?”+

Shirun dayaji tayi ne yasa ya cigaba da fadin “gaskiya idan Abba ya dawo zan fada mishi ya sanar da Mami, ke nakeso. Kuma a barmu muyi aurenmu”.

Zaro ido Samha tayi ta soma girgiza masa kanta tace “No Sabah… we can’t. Da wani ido kakeso na kalli Ammi? Kaima kasan bazasu taba amince mana ba”.

Sabah yace ” Toh sai me in sunki amincewa? I don’t care, we’ll just do it our own way, aure tsakanina dake ya hallata. Ko sunqi ko sunso ke nakeso kuma ke zan aura, and that’s final”

Samha jin maganar nasa tayi kamar daga sama, cike da tashin hankali ta soma girgiza masa kanta tace “bazan iya ba Sabah…”

“Don’t say that kanwata…wanan itace kadai mafita a garemu idan har nida ke muna so mu cimma burinmu, nidai kawai amincewarki nake bukata, ki bar komai a hannuna, i’ll handle it. Don’t you love me?”

Samha rasa me zata ce mishi tayi wasu hawaye masu zafi suka soma zubo mata.

Hankalinsa ne ya soma dagawa ganin yanda take zubda hawaye don haka ya janyota ya matseta gam a jikinsa ya kwantar da ita daidai saitin zuciyarsa dake faman aikin bugawa. Hannu yasa ya soma share mata hawaye yace ” ki saurari yanda zuciyata take bugawa akanki kanwata, bazan iya rayuwa babu ke ba, haka nan Allah ya jarabceni da matsanancin sonki, kuma a yanzu haka banida wata buri daya wuce na mallakeki a matsayin matata ta sunnah. Please ki amince zaki aureni”.

Suna cikin haka suka soma jin muryan Anty fanneh tana kokarin saukowa kasa. Babu shiri Samha tayi saurin kwace jikinta daga nashi ta mike tsaye kirjinta na harbawa.

Anty fanneh ta karaso ciki fuskarta dauke da murmushi ta nema wuri a gefen dining ta zauna, ta soma bude album din hotunan dake hannunta tana fadin “yau tuna baya za’ayi. Bari muga hotunan birthday girl”.

Mikewa Sabah yayi daga inda yake zaune fuskarsa dauke da murmushi ya kashewa Samha ido daya sa’anan ya karasa wurin dining ya janyo kujera daya ya zauna kusa da Anty fanneh, jiki babu kwari itama Samha ta karaso wurin ta tsaya.

Hoto na farko suka soma dubawa inda Samha take rungume jikin mahaifinta suna murmushi, kamarsu daya tamkar an tsaga kara, komai nashi Samha ta dauko.

Anty fanneh ta kurawa hoton ido hawaye na cikko mata idannu amma tayi kokari ta danne tace “zuwan Sameer yasa na tuna abubuwa da dama da suka faru a baya”.

Sabah ya kurawa hoton Samha ido yace “ashe daman kanwata tun tana karama takeda kyau haka?”

Cikin sauri Samha ta kai mishi dukan wasa tana mishi alamu da ido da yayi shiru, kirjinta na harbawa don tsoro take karya furta wata magana, Anty fanneh ta soma suspecting.

Amma Anty fanneh kwata kwata ma hankalinta na kan hotunan da suke kallo bata dau maganar nasa da wata manufa ba tayi dariya tace “jiya ba yau ba, kaga yanda kanwar taka ta girma ko Sabah?”

Dariya Sabah shima yayi, zaiyi magana sukaji anyi sallamar Abba ya shigo hannunsa rike da wata katuwar Teddy da gift box yana fadin “oyoyo where is my birthday girl, ga gift nan Abbah ya kawo mata”.

Gabadaya suka sa mishi dariya, suna mishi sannu da zuwa.

Cike da zumudi Samha ta karasa ta karba teddy din da gift box din daga hannunsa tana mishi godiya.

Abba yace “sorry ban dawo da wuri ba, nasan nayi missing”.

Zama yayi suka soma hira ana raha daga bisani anty fanneh ta mike taje kitchen ta hada musu dinner suka zauna kan dining suka soma ci.

Suna cikin cin abincin Abba ya soma sanar dasu batun tafiyan da zasuyi shida Anty Fanneh zuwa kano suje su gaishe da yan’uwansu don tunda akayi biki basu samu sunje ba.

Anty fanneh tace ” tunda weekend ne, zamu iya tafiya gabadayan mu, Samha ko ya kika ce? Nasan kin jima bakije maiduguri ba, kawu Grema kullum sai ya tambayeki. Sabah kaima ka shirya muje kaga yan’uwa”.

Kai tsaye Sabah ya bata ansa yace ” kiyi hakuri Anty amma gaskiya bazan iya zuwa ba”.

Abba yace “akan me? Toh ka shirya tare zamuje”

Sabah ya bata fuska yace “gaskiya Abba banida ra’ayin zuwa wani maiduguri yanzu, so nake ma naje Abuja wajen kawu mubashir”.

“Toh ai sai ka bari idan mun dawo sai kaje”

Anty fanneh tayi saurin sa baki tace “Alhaji tunda ya nuna baya son zuwa a kyaleshi kawai. Wani zuwan ba sai muje tare ba”

Abba yace “shi ke iko damu ko muke iko dashi? Ba isa a gaya masa magana ba sai yaja? Wanan tafiyan ai it’s for his own benefit ne, ya samu yaje yaga yan’uwa. Sabah dan’ki ne kuma dan’uwan a wajen Samha, kinga kuwa ai dole yaje ya gaisa da yan’uwanki”.

Sabah ya dago yana duban Anty fanneh yace “Anty kiyi hakuri idan na bata miki amma gaskiya banida ra’ayin zuwa Maidiguri yanzu”

Ran Abba ne ya soma bacci cikin kakausar murya ya kira sunanshi “Sabah!….”

Anty fanneh tace “dan Allah alhaji ka rabu dashi, tunda yace baya son zuwa it’s fine. Karka tilasta mishi”. Ta karasa maganar tana sakar masa murmushi.

Ajiyar zuciya Abba ya sake bai sake cewa komai ba.

From nowhere zukaji Samha itama tace “nima bazani ba”.

Cikin sauri suka juyo suna dubanta. Samha ta cigaba da fadin ” munada test da zamuyi ranar monday, kuma munyi dasu khadija zamu hadu muyi karatu tare”.

Anty fanneh tace “toh shikenan, tunda kwana biyu kawai zamuyi muje mu dawo, zaku iya zama ai keda yayanki”.

Da hakan suka dakatar da maganar nasu aka dauko wata hirar ta daban.

Bayan sun kammala cin abincinsu, su Sabah sun haura sama zuwa dakinsu, ya rage daga Anty Fanneh sai Abba.

Abba ya dubeta yace “honey… please kiyi hakuri da halayen Sabah, yaron nan ban san meke damunshi da taurin kai ba. Amma inaso ki dadda hakuri, don yanayin daya taso yana daya daga cikin dalilin dayasa yake behaving haka amma with time nasan zai canza”.

Anty fanneh tayi murmushi tace “karka damu Alhaji, wlh babu komai. Ni na zata ma zakaji haushi da Samha tace itama bazata ba, amma it’s okay”.

Abba yace “ni sai nake gani kamar yaran nan basuyi ammana da auren nan namu ba, kwata kwata basu nuna support dinsu”.

Jikin Anty Fanneh ne yayi sanyi amma tayi kokari ta danne abunda taji ya taso mata ta kirkiro murmushi tace ” a’a Alhaji banjin yaran nan zasu qi suga farin cikin mu”.

Murmushi Abbah ya sakar mata cike da jin dadi yace “Hakane matata, taho muje”.

Haka suka haura sama zuwa daki.

************************

Washe gari da safe, Sabah da Samha suna kan hanyarsu ta tafiya makaranta, Sabah ne yake driving. Suna isa harabar makarantar yayi parking sa’anan ya juyo yana dubanta yace “what are your plans? Ina kikeso kije wanan weekend din?”

“Ba inda zani”. Ta bashi ansa kai tsaye.

“Ina kince zakuyi karatun test ke dasu Khadija”

“Babu wani karatun test da zamuyi, kawai dai na fada hakan ne”

Sabah ya dubeta cike da mamaki yace “wato karya kikayi wa Anty kenan. You’re getting very naughty fa kanwata”.

Samha ta sunkuyar da kanta kasa sa’anan tace “Actually akwai inda nakeso naje ne ni kadai”

“Ina kenan?”

“Tsohon gidan mu”

“Me zakije kiyi?”

“Kawai…. i just need to visit there ne. An kwana biyu, kuma banson su Ammi su sani”.

Sabah yace “kin cika tunani dayawa kanwata. But don’t worry, zan raka ki”.

Dagowa tayi suka hada ido ya sakar mata murmushi, itama murmushin ta sakar masa cike da jin dadi suka fito daga cikin motar suka karasa department tare.

Bangarensu Anty Fanneh kuwa, zaune suke a parlour tare da Mami wace bata jima da shigowa ba. Don Abba ya sanar da ita tafiyan da zasuyi tace bari tazo suyi sallama.

Mami ta dubi Anty fanneh tace “Fanneh yanzu keda muazzam tafiya zakuyi kubar yaran nan su kadai a gida?”

Anty fanneh tace “yaran ne sun nuna basu son zuwa Mami, shiyasa nacewa Alhaji kar a takura musu tunda ba wani jimawa zamuyi ba, kwana biyu kawai zamuyi mu dawo”.

Mami katuwar ajiyar zuciya ta sake don ita kwata kwata bata gamsu da batun a tafi a barsu su kadai a gida ba tace “toh nidai a ganina fanneh, yaran nan suna matsayin wa da kanwa ne a baki amma idan aka bi didigi ansan cewa ba jini bane ya hadasu”.

Anty fanneh cike da rashin fahimta tace “toh ai mami, gani nayi yaran nan suna shiri sosai, kuma akwai shakuwa sosai a tsakaninsu”

Mami tace “toh ai shakuwan ne naga tana  neman tayi yawa fanneh, ba yau na soma lura da hakan ba”.

Shiru Anty fanneh tayi tana kallon mami tana kokarin ta fahimce inda maganar nata ya dosa, ai kuwa nan take zuciyarta ta kawo mata light, gabanta ne ya fadi cikin sauri tace ” dan Allah Mami, kar zuciyarki ta raya miki wani abu daban, Sabah da Samha babu abunda yake tsakaninsu illa shakuwa irin na yan’uwan taka”.

Mami giirgiza mata kanta tayi tace “a’a Fanneh, ina tsoro kin san halin yaran yanzu, ace zaku tafi ku bar yara balagagu haka su kadai a gida? kema ki duba ki gani fanneh, gaskiya da sake”.

Shiru Anty fanneh tayi tana sauraron Mami zuciyarta na harbawa da karfi don bata taba kawo irin wanan tunanin cikin ranta a game da yayanta ba, musamman ga Samha don tasan irin tarbiyan data bawa diyarta. Zuciyarta ne ya da’an sosu tace ” Mami, ban san cewa irin kallon da kike yiwa ya’ta ba kenan, nasan kin sowa Sabah Madina saboda ta fito daga gidan mutunci, amma itama Samha batada banbanci da sauran yara, nasan irin tarbiyan dana bata har ta taso dashi”.

Mami tace “ba haka nake nufi ba Fanneh, nasan ko wani yaro da irin tarbiyan daya taso dashi, baccin haka ina son Samha sosai kuma yanzu haka ta rigada ta zama jika a wajena, kawai dai hankalina bai kwanta bane da batun barinsu su kadai a gida”.

Anty Fanneh tace “Mami, nasan halin ya’ta sarai, a hannuna ta taso kuma nasan irin tarbiyan dana bata. Na yarda da ita kuma nasan bazata taba aikata wani abu da zai zubda mutuncinta ba, kuma batun Sabah shima bana kokanto akan tarbiyansa ba, dukda nasan yanada wuyan sha’ani nasan yanada hankali sosai”.

Mami ta sake ajiyar zuciya sa’anan tace “toh shikenan fanneh. Allah yaja mana gaba, Kiyi hakuri da maganar danayi bai kamata ace nayi irin wanan tunanin ba, tsufa ne yazo mun,tunani sun soma yimun yawa. Fatana dai yanzu Allah ya kaiku lafiya kuma ya dawo daku lafiya”

Anty Fanneh ta kirkiro murmushin karfin hali tace “Ameen Mami nagode”.

Da haka suka rufe chapter wanan maganar.

Washe gari asabar, ta kasance ranar dasu Anty Fanneh zasu tafi maiduguri, tun safe suka farka aka soma shirye shirye don jirgin safe na missalin karfe goma sha daya zasu bi.

Bodyguards din Abba ne suka zo suka soma fito da akwatina suna shiryawa cikin mota.

Sabah tunda ya sauko suka gaisa ya koma dakinsa bai sake fitowa ba.

Samha ce ta rako su Ammi har cikin gida, Ammi tana fada mata ta tabbatar da sun rufe ko ina a gida, da kuma gas tana gama girki ta tabbatar ta kashe komai tunda sophie yar aikin gidan bata nan tayi tafiya zuwa kauyensu.

Samha tace “insha Allah Ammi duk zan kula”.

Anty fanneh tace “ki kula da kanki, jibi insha Allah zamu dawo da safe”.

“Toh Ammi Allah ya dawo daku lafiya, ki gaishe mun dasu kawu Grema”.

“Ameen ameen, insha Allah zasuji”.

Shiru tayi tana kallon diyarta maganganun da sukayi jiya da Mami yana dawo mata fal a rai. Wani irin tsoro da fargaba ne taji ya ziyarce ta kurawa Samha ido.Zatayi magana, sukaji muryan Sabah ya fito yana fadin “Samha bake kika daura ruwan zafi a wuta yanata tafarfasa?”

Cikin sauri Samha tace “Ammi Allah ya kiyaye hanya kuma ya saukeku lafiya, zan kiraku idan kun isa, bari naje na duba abunda na daura a wuta”.

Ammi cike da sanyin jiki tace “toh, ki kula”.

Daga mata hannu Samha tayi sa’anan suka karasa cikin mota itada Abba, driver yaja suka tafi.

Cikin sauri Samha ta koma cikin gidan, ta karasa cikin kitchen Sabah na biye da ita a baya.

Tunda su Anty Fanneh suka bar gidan ta kasa samun nutsuwa a cikin zuciyarta gabadaya hankalinta a tashe yake, Abba ne ya lura da yanayinta yace “yadai Fanneh? Ya na jiki shiru tunda muka baro gida ko bakida lafiya ne?”

Murmushi Anty Fanneh ta kirkiro tace mishi babu komai.

Bangarensu Samha kuwa, tsaye take cikin kitchen sai faman yanke yanke takeyi.+

Sabah na zaune a parlour yana kallon wani tasha a Tv, shiru parlourn babu abunda kakeji sai sanyin Ac dake tashi a parlourn.

Jin shirun yayi yawa ne yasa ya waiga ya hangota cikin kitchen ya soma kwada mata kira yace “keh… wai me kikeyi cikin kitchen dinan ne tun dazu?”

“Dinner nake kokarin hadawa”. Ta bashi ansa kai tsaye sa’anan ta cigaba da abunda takeyi.

Juyawa yayi ya kalli agogon bango yaga sha biyu saura. Remote din dake hannunsa ya jefar a gefe sa’anan ya mike ya karaso cikin kitchen din, yana isa ya kamota ya juyo da ita yana nuna mata agogo yace “duba lokaci, it’s just 12pm and you’re making dinner?”

Harara ta dan watsa mishi hade da tureshi gefe tace “ni ka rabu dani, yanzu nakeso na hada dinner din”. Juyawa tayi ta cigaba da yanke yanken nata.

Ajiyar zuciya ya sake ya juya ya soma tafiya hade da fadin “zo nan”

“Mene?” Ta tambayeshi.

“Cewa nayi kizo! ko baki jine?”

Tsaki ta buga sa’anan ta ajiye wukar ta biyo bayanshi suka shigo cikin parlourn tana watsawa bayanshi harara.

“Ki zauna” ya fada mata.

Har ta bude baki Zatayi musu taji ya fizgo hannunta ya jefar da ita kan kujeran. “Bacci nakeso nayi, anjima munada long journey”. ya fada sa’anan ya mike kan kujeran ya daura kansa bisa cinyarta yana ajiyar numfashi.

Zaro ido Samha tayi tana kallonsa kirjinta na harbawa tace “meye haka Sabah?” Muryanta tamkar zatayi kuka.

“Elephant leg-pillow” ya fada mata yana dariya hade da gyara kwanciyarsa kan cinyar nata.

Marairaice masa fuska tayi hade da kai masa bugun wasa a kafada “waye mai kafar elephant?”

“Naki mana… it’s so comfortable”.

Turo baki tayi hade da fadin “you’re so childish wlh”.

“Allah yasa baza’ayi ruwa gobe ba” ya fada hade da lumshe idanunsa.

Juyawa Samha tayi ta daga labulen window dake bayansu taga hasken rana na kokarin fitowa. Jin yayi shiru ne yasa ta da’an sunkuya tana leka fuskarsa taga har bacci yayi awon gaba dashi yana ajiyar numfashi tamkar wani baby. Ashe da gaske baccin yakeji. Murmushi ta da’an sake tana girgiza kai tana karewa kyaywar fuskarsa kallo tana jin wani irin sanyin a ranta hade da zazzafar kaunarsa na kara shigan mata rai.

**********************

Bangaren su Anty fanneh kuwa, har sukayi boarding jirgin ya tashi ta gagara samun nutsuwa cikin ranta.

Abba ne ya kamo hannunta yana shafawa a hankali ya soma kokarin kwantar mata da hankali, tasan bazata iya bude baki ta fadawa Abba gashi abunda yake damunta ba don haka tayi shiru ta bar wa kanta komai, har jirgin nasu yayi landing still hankalinta bai kwanta ba. Yayanta Alhaji Grema ne yazo har airport yayi picking dinsu ya kaisu babbar family house dinsu dake bukar marte can cikin maiduguri.

*****************

Da rana misalin karfe biyu, Sabah da Samha ne tsaye a bakin ruwa, suna kallon yanda ruwan tekun yake tashi kuma yake zuba. Ga bishiyoyi ko ta ina iska nata kada su, sanyi ne sosai yake ratsa wurin, gani yayi ta soma kaduwan sanyi tana kankame jikinta, a hankali ya kamo hannunta cikin nashi ya soma shafawa a hankali daga bisani ya ciro jacket dinsa ya lulubeta dashi yana fadin “sorry baby, yanzu sanyin zai ragu”.

Lalausar Murmushi ta sakar masa ta daura kanta bisa kafardarsa tana ajiyar numfashi, shi kuwa ya kara matso da ita kusa da jikinsa yace “inaso ki shirya, nayi mana booking flight daga nan zamu wuce Abuja”.

Cikin sauri ta dago kai tana dubansa cike da mamaki tace “ban gane ba, Abuja fa kace? Me zamuje muyi a Abuja kuma?”

“Kedai ki shirya, i have a surprise for you”.

“A’a Sabah, Su Ammi suna gab da dawowa, jibi fa zasu dawo. Idan suka dawo basu tadda mu a gida bafa?”

“Bazamu jima ba, muna gama abunda zamuyi gobe insha Allah zamu dawo. Baza su san ma munyi tafiyan ba”.

Shiru Samha tayi tana nazari sa’anan ta girgiza kai tace “gaskiya bazan iya ba…”

“Please Samha.. wurin fa uncle zamuje, kawun Abba. Already ma yana expecting mu.”

“Toh ka fada mun me zamuje muyi mana”.

“Nace ki bari idan mun isa zaki san koma meye”.

“Sabbah….”

“Shhh..” ya katseta yana kamo hannunta cikin nasa “Trust me kanwata. Kema kinsan bazan taba yin wani abunda da zai cutar dake ba, Ki yarda dani”.

Kalamai masu dadi yasoma binta dashi yana shafo hannunta har ya samu ya shawo kanta tayi shiru tana sauraronsa.

“Toh you promise gobe din zamu dawo? Unfailingly?”

“Yes i promise. Insha Allah goben zamu dawo”.

“Toh ai ban shirya kayana ba”.

“Karki damu, kome kike bukata zamu samu a can, yanzu dai kawai yarda ki nake nema, by 3 ya kamata muna airport. Jirgin zai tashi” ya fada yana duba agogon hannunshi yaga ma uku saura.

Tana kallonshi ya soma neman layin daya daga cikin driver din gidansu yace yazo ya kaisu airport. Babu musu driver din yace toh. Within30 mins sai gashi nan yazo yayi picking dinsu.

Tunda suka dau hanyar airport jikin Samha ya soma bari, damuwa fal ranta, amma idan ta dubeshi taga babu wata damuwa a tattare dashi sai taji hankalinta ya da’an kwanta don tasan Sabah bazai taba yin wani abu dazai cutar da ita ba, ko babu soyayya tsakaninsu, ita kanwarsa ce.

Check-in sukayi daga bisani sukayi boarding jirgin. In the next one hour suna Abuja. Straight gidansu Uncle suka sauka. Uncle dattijon mutum ne sosai kuma retired police, shine yayan Mami kuma akwai shakuwa sosai tsakaninsa da Sabah. Indai Sabah ya samu hutu haka toh gidanshi yake zuwa, tasu dai tazo daya.

Tarba na musamman uncle yayi musu, ya karbe su hannu bibiyu musamman Samha wace kallo daya yayi mata yaji yarinyar ta shiga ransa. Babbar yarsa Bilkisu wace ake kira da ummi saboda sunan mami data ci ne ta sauko kasa suka soma gaisawa.

Ummi ta dubi Sabah tace “barka da zuwa Sabah, ya kuka baro mutanen gida?”

“Kowa lafiya lau, alhamdulillah”. Ya bata ansa fuskarsa a sake, duk cikin cousins dinsa yafi shiri da ita don Ummi tanada saukin kai sosai, batada matsala. Uncle ya dubeta yace “ga kanwarki Samha, itace yarinyar matar da kawunki ya aura”.

Cike da jin kunya Samha ta gaisheta, Ummi ta ansa mata fuskarta a sake.

Bayan sun gaisa, Uncle yace takai Samha zuwa dakinta. Babu musu suka haura sama.

Bayan barinsu Samha parlourn, uncle ya juyo yana duban Sabah. Kusan 10 mins shiru babu wanda yayi magana. Uncle yayi gyaran murya yace “Sabah naji meke tafe dakai. Amma ka tabbata bakasan mahaifinka yasan da wanan maganar?

“Uncle, wanan kadai ce hanyar da zan iya bi na cimma burina, zuciyata ta samu abunda takeso. Abba da mami bazasu taba amince mun da wanan maganar ba shiyasa na kawo kukana gareka don nasan Kai mai iya sharemun hawayena ne. Uncle please ka taimaka mun, ka taimaka wa rayuwata. wlh rayuwata tana cikin hadari in har mudin ban samu abunda zuciyata takeso ba, zan iya rasa raina don bazan iya rayuwa babu ita ba”.

Shiru uncle yayi hade da sauke nanauyar ajiyar zuciya yana nazarin abunda yace “yanzu a shirye kake kenan”.

“A shirye nake uncle koma meye akace nayi zanyi”.

“Toh yanzu ita yarinyar ka sanar da ita?”

“Eh toh… ban fada mata ba tukuna. Nadai nunar mata zamuzo mu gaisheka ne, amma gobe insha Allah zan sanar da ita komai. Nasan itama tana cikin tsaka mai wuya kamar yanda nake ciki, bazan samu matsalar wurin shawo kanta ba”.

“Toh shikenan Sabah, Allah ya kaimu goben lafiya.”

“Ameen ameen”. Sabah ya ansa masa sa’anan ya mike ya nufi dakin saukan baki inda ya saba sauka a duk sanda ya iso gidan.

A daren ranar dai Sabah bai runtsa ba, tunani kala kala na masa yawo akai yana tunanin yanda zaibi ya bullo ya shawo kan Samha har ta amince da batunsa. Itama bangaren Samha, kasa runtsawa tayi zuciyarta fal da tsoro da fargaba, bata taba yin irin wanan kasadar ba wai tayi tafiya ba tare da ta sanar da Ammi ba. Daga bayane wani irin wahalalen bacci ya samu nasaran awon gaba da ita.

Washe gari da safe misalin karfe 8, ummi tazo ta tashe ta ta kawo mata breakfast ta karya sa’anan ta hada mata ruwan wanka ta shiga bayi ta watsa ruwa a jikinta ta fito ta tadda wasu hadadun kaya less dinki gown daidai size dinta an jera su akan gado. Ummi ce tazo ta tayata shiri sa’anan taja hannunta suka shige wani daki, dakin dauke yake da akwatina sets sunkai kala goma sha hudu har da yan kai, cike da mamaki Samha ta juyo take kallonta tace “Anty Ummi waenan akwatunan fa?”

“Duk naki ne”

A razane Samha ta dago tana dubanta kirjinta na bugun tara tara tace “nawa fa kikace?”

“Kwarai kuwa naki ne”.

Zatayi wata magana, wayarta ta soma ringing. Sabah ne ke kira.. cikin sauri ta daga ta kara a kunne hanunta na rawa.

“Kina ina? Kizo uncle nason ganinmu”

Tare suka sauko da Ummi zuwa parlour kirjinta na harbawa, hankalinta bai gama tashi ba sai data karaso taci karo da kanin mahaifinta Madibbo zaune a parlourn tare dasu Sabah. Idan bazata manta yau kimanin kusan shekara biyar kenan rabonta data sanya shi a idanunta. Tun rasuwar mahaifinta da suka juyawa Amminta baya lokaci har suna neman su kwace Samha daga hannunta, Ammi taki amince musu sam tace ita zata kulan da diyarta da kanta, don tasan idan tabar Samha a hannunsu ba karamin wahala zata sha ba.

Cike da mamaki take kallon modibbo tace “kawu modibbo? Kai nake gani? Wai meke faruwa ne?” Ta soma tambaya hankalinta a matukar tashe. Shima Modibbo cike da mamaki yake kallon Samha yaga ta girma ta kara kyau sosai kamar ba ita.

Sabah ne yayi mata allamu data karaso ciki ta zauna. Jikinta na bari ta karaso tazo ta nema wuri a gefe ta zauna.

Bayansu sun gaisa, Uncle yayi gyaran murya ya soma fadin “Abunda yasa na kirawo ki nan Samha bai wuce akan alakar dake tsakaninki da Sabah ba. Sabah yazo mun da wani bakon lamari daya dangance zamantakewarku. Na jima ina tunanin akan wanan maganar daya zo mun da ita. Ya nunan mun harga Allah ke yakeso da aure, kuma inada masaniya akan duk abunda ke faruwa har auren da Bilkisu kakarsa taso ta hadashi da yar gidan zubair. Nasan kwanan nan iyayyenku sukayi aure, kuma bazaku so wani abun dazai tauye musu farin cikinsu ba, shiyasa shi Sabah yazo ya sameni da wanan maganar a matsayina na kawun mahaifinshi. Na daya dai inaso ku sani cewa aure ya hallata a tsakaninku, ba haramun bane ace yau kun waye gari kun mallaki junanku a matsayin mata da miji, don haka saboda gudun dana sani don ba’asan wani irin hali wanan lamarin zai iya jefaku ba yasa na amince masa da wanan batun. Ga kawunki nan mallam modibbo tun daga Adamawa Sabah ya gayato shi, kuma shi zai tsaya muku a matsayin waliyyi. Shima mun zauna mun tattauna dashi yace baiga aibu a wanan zancen ba, inyaso daga baya da kaina zan kira iyayyen naku nayi musu bayanin komai. A da nayi niyan na tunkaresu da wanan batun amma Sabah ya nuna mun rashin yi’war haka don yace hakan ba karamar fitina zata haddasa ba”.

Ai tunda Uncle ya bude baki ya soma magana Samha take kallonsu daya bayan daya hankalinta a matukar tashe, zuciyarta tamkar zata harba ta fito. Juyowa tayi tana kallon Sabah wanda ya kura mata ido yana kallonta shima hankalinsa a tashe.Uncle dayaga duk tabi ta tayar da hankalinta ta rude ne yasa ya soma mata nasiha yana kokarin kwantar mata da hankali yace wanan kadai itace mafita garesu kuma Allah yasa shine yafi zama mafi alheri a wajensu.

Sosai ya dinga mata nasiha wanda yasa gabadaya jikinta yayi sanyi. Ita tunaninta daya Ammi. Da wani ido zata kalleta idan ta dawo? Ita a yanzu haka ma ta shirya aure ne? Gabadaya tunaninta a hargitse yake.

Uncle ne ya fadawa Sabah daya jata suje suyi magana a private. Dayan parlourn suka nufa shida Samha suka zauna ya soma kokarin kwantar mata da hankali. Ai bata san sanda ta fashe mishi da kuka ba tana fadin “Sabah me kakeso muce wa Su Ammi da Abbah? Wanan ai cin amana ne da wani ido kakeso mu kallesu idan sun dawo? Sabah aure fa? Aure fa ba abun wasa bane”.

Ajiyar zuciya Sabah ya sake yace “nasan da haka Samha, amma ki duba ki gani. Wanan itace kadai mafita garemu. Uncle kawun Abba ne don haka bamuda matsala. Idan komai ya lafa daga baya za’a sanar dasu. Samha i love you, ina matukar sanki tamkar raina, banjin zan iya rayuwa da wata ya’mace inba ke ba. Mami bazata tsaya kan Madina ba, a shirya take ta hadani aure da duk yarinyar da zuciyarta ta raya mata. Ni kuma gaskiya bazan iya bari tayi controlling rayuwata haka ba. Ni yanzu haka a shirye nake da nayi komai indai zan mallakeki a matsayin matata ta sunnah, banki na ba’ta da kowa ba. ki yarda dani kanwata bazan taba cutar dake ba. Idan an daura mana auren yanzu zamu koma gida batare da sun san abunda ya faru ba, sai daga baya za’a sanar dasu. Please i need your support kanwata, let’s achieve our dreams together. Ki amince zaki zama matata”.+

Hannu yasa ya soma share hawayen dake ta faman zubo mata. Sai faman sheshekar kuka takeyi tana tunanin Ita tasu kalar soyayyar kenan? Da irin wanan kaddarar tazo musu?

Kara maso da ita kusa dashi yayi yana cigaba da lalashinta yana bata baki har ya samu kukan nata ya lafa yace “babu abunda zai canza Kanwata, we’ll return back to our normal lives idan an daura auren kinji? Bazamu taba bari su sani ba”.

Da haka dai da siyasa ya cigaba da lalabata har ya samu ta tsayar da kukan nata. Ta dago tana dubansa, har cikin ranta takejin sonsa na kara huda tsokar dake makale bisa kirjinta. Ita kanta tasan tana ba’lain son Sabah, sonsa a jininta yake, bazata taba iya rayuwa babu shi ba. Kuma tasan irin halin data shiga lokacin da mami taso hadashi aure da Madinah.

“Me kikace kanwata? Kin amince?” Ya kafeta da mayattun idanunsa masu shegen kyau da haske yana kallonta.

Duk da tsoro da fargaban dake cinta hakan bai hanata daga mishi kanta ba tace “na amince, Amma bazamu taba nunar musu ba ko Sabah. Kadau alkawari?”

Farin ciki kuwa tamkar ya zuba ruwa a kasa yasha dayaji tace ta amince “na dau alkawari kanwata, kuma nagode kwarai da gaske da kika amince zaki zama matata. I love you so much my heartbeat”.

Kallonshi kawai takeyi tana ganin yanda duk yabi ya rikice kamar wanda aka mai kyauta da gidan aljannah. Ita har yau mamakin yanda Sabah yake sonta takeyi don a ganinta, yafi karfinta don mata waenda suka fita class da komai bai sauraresu ba ya nace yace sai ita.

Before you know it, cikin ruwan sanyi akaje aka daura auren dasu uncle a masalaci bisa sadaki dubu dari biyu kacal da Sabah ya biya.

Ba karamin kudi Sabah ya bawa kawu modibbo ba ya sallameshi sai faman washe baki yakeyi don shi daman gaba ta kaishi. Sabah daya kira Samha kuwa ya sanar da ita an daura har karamar zazzabi tayi don taci kuka harta gode Allah. Anty Ummi ce taketa faman rarashinta dan gyaran jikin ma da takeso ta yiwa Samha da kyar Samha ta yarda tayi mata sai faman kuka takeyi.

Sabah yana dawowa Samha tasa shi a gaba tanai mishi kuka akan lallai sai sun koma gida don hankalinta kwata kwata baya jikinta.

Da uncle yaji labarin a ranar zasu koma shima ya goyi bayan dasu koma. Kayan lefen dai duk a gidan uncle aka bari ba taba ba. Godiya sosai Sabah ya yiwa uncle yaja amaryarsa sukayi gaba. Sai dai kuma kash suna isa airport suka tadda anyi canceling flight din nasu sai zuwa gobe. Samha tamkar ta kurma ihu ta daura hannunta aka tace “shikenan abunda naketa gudu kenan gashi zai faru. Mezan fadawa Ammi idan ta dawo bata tadda mu a gida ba?”

Zuwa sabah yayi ya soma duba sauran airlines din ko za’a samu jirgin dazai tashi a lokacin amma duk suka ce babu flights sai washe gari saboda bad weather.

Samha ta kuma fashe mishi da kuka tace “dan Allah Sabah ko mota ne muje mubi, na shiga uku yau! wayo Allah na”

“Ke dallah rufewa mutane baki, uban waye zaije yabi hanya da yanda kasa take ciki yanzu? So kike a zace mu a hanya ko me? Kinga ki kwantar da hankalinki, gobe insha Allah da sassafe zamu shirya mu wuce, kinga sun kara rescheduling flight din zuwa karfe tara na safe so just be patient, mu da’an kara hakuri, na tabbata su Abba bazasu dawo ba sai zuwa yamma”

“Toh yanzu gidan uncle zamu kuma komawa?” Ta tambayeshi hawaye sharshar bisa fuskanta.

“In baki so sai nayi mana booking hotel”.

“A’a nidai mu koma gidan uncle”.

“Toh shikenan”

Haka suka kuma komawa gidan Uncle suka kwana, Anty fanneh sai faman neman layin Samha take taji gabadaya a kashe layin bata shiga. Hankalinta yakai koluwar tashi, Gabadaya sai takeji a jikinta kamar babu lafiya game da yar’ta. Abba tasa a gaba tace mishi sai lallai sun koma washe gari da safe. Abbah abun dai ya daure mishi kai, ya gagara sanin meye dalilin dayasa take daga hankalinta haka. Bai kara cewa komai ba ya bada order da ayi musu booking jirgin sassafe don shima yanada aikin da zai wuce yayi a office ana jiranshi.

Washe gari tun karfe bakwai da rabi Abbah da Anty Fanneh suka biyo jirgin Azman first class zuwa garin eko. Kirjin Anty fanneh sai faman bugawa takeyi da karfi tankar zata huda kirjinta ta fito.

“Wai ke fanneh meke damunki ne haka? Gabadaya duk kinbi kin aza wa kanki damuwa da tashin hankali, wai Samha wani zai cinyeta ne ko meye? Ina tana tare da yayanta a gida?”

Ajiyar zuciya Anty fanneh ta sake sa’anan tace “mudai kawai mu karasa gida Alhaji, wlh my mind is not at ease.”

“Toh shikenan, nidai bazan shiga gida ba saboda akwai urgent meeting dazanje nayi attending, idan mun kammala zan dawo”.

Anty Fanneh tace toh shikenan “Alhaji

A gida aka ajiye Anty fanneh daga bisani driver yaja ya tafi da Abba.

Tun kafun ta karasa shiga cikin gida ta soma trying number Samha baya shiga still. A tunaninta tana sama a dakinta tana faman baccin data saba ne, tana tura kofar ta shiga taga wayam, dakin Sabah ta nufa ta soma knocking taji kofar a garke. “Toh ina yaran nan suka shiga da sanyin safiyan nan”.

Layin Sabah ta soma kokarin kira amma ba’ayi picking ba, hankalinta yayi mugun mugun tashi. Ta fito harabar gidan ta soma tambayar securities suma suka ce basu san inda suke ba. Komawa parlour Anty Fanneh tayi ta zauna tayi jugum jikinta sai faman bari yakeyi. Tunani kala kala ne kawai ke mata yawo aka.

Sai misalin karfe goma da rabi su Samha suka iso gida, Samha na ganin alamun Anty fanneh ta dawo gida kusan yanke jiki tayi ta fadi tsabar fargaba. Cikin sauri ta karasa parlourn, Sabah na biye da ita suka tadda Anty Fanneh a zaune tayi jugum.

“Ammi…. kun dawo…” Samha ta fada muryanta na rawa tana kokarin karasawa inda take.

Anty fanneh bata juyo ta kalle ta ba, cikin sanyin murya wanda Samha bata taba jinta dashi ba tace “Daga ina kike cikin sanyin safiyan nan Samha?”.

A rikice Samha ta soma kokarin yi mata bayani tana i’ina tace “Daman…ddaman..”

“Daman me?!” Anty fanneh ta daka mata tsawa hade da mikewa tana facing dinta ta zuba mata lafiyayun mari har guda biyu.

Har cikin ransa Sabah yaji saukan waenan marin. Cikin sauri ya karaso yana fadin “dan Allah anty karki dake ta, ni ya kamata ki mara ba ita ba don duk laifi nane, nine naja ta muka fita zuwa point road siyan abu”.

“Da uban safiyan nan kuka fita? Uba me kuka je siya a point road da sassafe?! Na dawo gidan nan ban tadda kowa ba hankalina a tashe ko securities ma cemun sukayi basu san inda kuke ba! Sai faman kiran layunku nake a kashe! Kunsan yanda hankalina ya tashi kuwa?!” Sai faman zazzaga ruwan bala’i Anty Fanneh takeyi ta inda take shiga ba tanan take fita ba.

Ita kam Samha sai sheshekar kuka taketa faman yi hannunta dafe da kuncinta. “Ammi dan Allah kiyi hakuri ki yafeni, bazan kuma ba”.

Cikin kakausar murya Anty fanneh ta soma fadin tana nunata da yar yatsa “ni ba mutuniyar banza bace haka zalika ni ban yiwa ya’ta tarbiyan da zata dinga fita tana yawo a gari ba tare da izinin iyayenta ba. Anjima Abban ku zai shigo, kunci sa’a ba tare dashi muka dawo muka tadda gidan babu kowa ba da kun gane kuranku. Ni zan haura sama”.

Tana gama fadin haka ta juya a fusace ta tafi ta barsu a wajen. Yinin ranar dai Samha tayi magiyan, tayi ban hakurin wajen Anty fanneh da kyar dai ta samu ta sauko. Ko da dare ma tana zaune cikin dakinta tayi jugum abun duniya duk yabi ya isheta, tana tunanin irin wanan halin data jefa kanta ciki, wai yau ta zama matar aure? Ba tare da sanin mahaifiyarta ba, idan bazata manta ba tasan Amminta taci buri akan bikinta don kullum wakarta kenan Allah ya nuna mun ranar aurenki Samha. In kaiki gidan mijin, da kuma dakinki da kaina. Sai gashi yau an waye gari tayi aure ba tare da saninta ba, cikin boye, cikin siri.

Tana cikin wanan tunanin wayarta ta soma kara kusa ta ita ta daga ta kara kunne.

Muryar Sabah ne taji ya doki kunnenta yace ” matata..,”

Shiru tayi bata ce komai ba, wasu hawaye masu zafi suna gangaro mata bisa kunci tasa hannu ta soma sharewa. Shima shiru yayi yana sauraronta babu abunda kakeji sai sautin ajiyar numfashinsu.

Wani irin iska mai zafi Sabah ya busar ta waya yana jin zuciyarsa na kara masa radadi don yasan saboda shi ne ta shiga cikin irin wanan halin.

“Ya fuskar taki? Hope it doesn’t hurt? Kiyi hakuri kanwata nasan duk saboda nine kika shiga wanan halin, ni kaina banso hakan ta faru ba amma haka Allah ya kaddara, kiyi hakuri with time insha Allah everything will be fine. Komai zai zama tarihi. Koda sun juya mana baya Samha ni bazan taba juya miki baya ba. Ke tawa ce ina matukar sonki ke kadai ce a zuciyata”.

Sheshekar kukan da takeyi ne ya tsaya tayi shiru tana sauraronsa bata ce komai ba. A hakan har ya gama kwantar mata da hakali da kalamansa masu sanyaya zuciya yayi mata sai da safe ya katse kiran. A daren ranar daga shi har ita basu runtsa ba. Yanda sukaga rana haka sukaga dare.

*******************

Washe gari da safe ta kasance Monday, Samha tayi shirinta na zuwa makaranta ta sauko kasa ta tadda Ammi tana shirya dining. A hankali ta karaso tana fadin “ina kwana Ammi….”

“Ina kwana” Ammi ta bata ansa ba tare da ta juyo ta kalleta ba.

Jikinta ne ya kara mugun sanyi data ga yanda Anty fanneh ta ansa mata gaisuwar. Har yanzu bata sauko daga fushin ba kenan.

“Ammi akan abunda ya faru jiya dan Allah kiyi hakuri ki yafemun. Wlh Bazan kuma fita ba tare da izininki ba”.

A hankali Anty Fanneh ta juyo tana dubanta, nan take kuma taji tausayin yar nata ya kamata. Gani tayi duk tabi tayi wani iri kamar ba ita ba, daga jiya zuwa yau har wata yar’ karamar rama tayi.

“Babu komai Samha, komai ya wuce amma please daga yau karki kuma, ban taba tsintar kaina cikin tashin hankali ba irin na jiya tun rasuwar mahaifinki. Kuma banji dadin yanda na daga hannu na mareki ba, abunda ban taba yi ba don nasan tun kina karama ke mai biyayya ce gareni”.

A hankali Samha ta karaso wajen Ammi ta rungumeta tace “insha Allah Ammi bazan kuma ba, ya maiduguri da mutanen gida da su Kawu Grema? Da fatan kowa na lafiya”.

“Lafiyansu lau sunata tambayarki, wai yaushe zaki zo nace sai kin samu hutu tukuna”.

Murmushi Samha ta sakar tace “insha Allah wani zuwan kuma tare zamuje Ammi”.

Suna cikin wanan maganar wayar Anty Fanneh ta soma ringing akan kujera, karasawa Anty Fanneh tayi taje tayi picking wayar ta kara a kunne. Kafun kace me, wani irin jiri ne ya kwasheta bata san sanda wayar ta fadi a hannunta ta sulale kasa a sume ba.

Wani irin razanan kara Samha ta sake tayo kanta a guje tana fadin “innalillahi wa ina illahi raji’un! Ammi! Ammi…..Ammi! Dan Allah Ammi ki tashi karki mun haka! Ammi…”

Sabah dake kokarin saukowa kasa ne yaji ihun Samha ya sauko a guje yazo ya tadda su. Babu shiri securities suka shigo suma, Sabah yasasu aka fitar da Anty Fanneh sai asibiti.

lagoon hospital dake Liverpool aka kaita straight emergency likitocci suka karbeta. Samha na kokarin binsu cikin emergency aka dakatar da ita. Sai da Sabah yayi da gaske tukuna ya samu ta da’an dawo cikin hayyacinta ya tsuguna a gabanta ya kamo hannunta cikin nashi yana faman aikin rarashinta ita kuwa sai faman kuka takeyi tana fadin duk laifinta ne, duk ita ta jawo Ammi ta shiga wanan halin.

Suna cikin haka sai ga Abbah nan shima ya shigo cikin sauri hankalinsa a matukar tashe yana fadin “ina matata take?

“Abba an shiga da ita emergency”. Sabah ya bashi ansa.

Ganin yanda Samha tabi ta tayar da hankalinta idanunta duk sun kunbura ne yasa Abba yaji tausayinta shima ya shiga rarashinta. “Karki damu Samha, insha Allah babu abunda zai sameta. She’ll be fine mu Cigaba da addu’a”.

Yana cikin wanan magana sai ga Doctor nan ya fito ya karaso inda suke da wata nurse tana biye dashi.

“Doctor ya jikin matata?” Abbah ya soma tambayarsa hankalinsa a dage.

“Da sauki Alhamdulillah, fatigue ne na rashin bacci da kuma slight anemia ke damunta amma don’t worry she’ll be fine. Yanzu haka tana bukatan hutu sosai saboda babyn dake cikinta. Anci sa’a ma cikin bai zube ba.”

Dammm! Kirjinsu ya buga aka soma kallon kallo, Samha ta kalli Sabah kirjinta na harbawa shima ya kalleta don jin maganar likitan sukayi banbarakwai tamkar daga sama.

Abba ne yake kallon likitan yana zaro ido yace “da gaske likita? Matata ciki ne da ita?”

“Kwarai kuwa. Baka sani ba? Ai Cikin yakai 13 weeks yanzu”.

Cike da mamaki Abba yake kallon likitan yace “har 13 weeks?”

“Yes 13 weeks”

Wani irin dadi ne ya rufeshi ya juyo cike da murna yana kallonsu Sabah yace “Sabah! Samha! Kunji Amminku tana dauke da baby”. Murna kamar ya kashe Shi sai faman zuba yakeyi.

Su kuwa Sabah da Samha tsaye suke suna kallonshi sun kasa cewa komai don gabadaya jikinsu yayi sanyi.

Godiya Abba ya shiga yiwa likitan, Samha ta tambayi likitan ko zata iya shiga ciki ta ganta. Likitan yace eh zata iya shiga ciki ta duba ta.

Cikin sauri ta karasa cikin dakin da aka kwantar da ita.

Bayan shigan Samha ciki, Sabah ya juyo yana duban mahaifinsa wanda zuciyarsa fal take da farin ciki. Shiru Sabah yayi bai ce komai ba. Abba ya dubeshi yace “Sabah ya?”.

Jimm yayi daga bisani yace “Abba idan bazaka damu ba inaso na tare a dayan gidana dake island”.

Mamaki ne ya cika Abba ya dago yana dubansa yace ” ban gane ba. Wani ya takura zamanka ne anan?”+

“A’a Abbah, gani nayi lokaci yayi daya kamata ace nima na samu muhalina nakaina. Kaga yanzu Mami tana magana za’a damka mun kamfanuka na family su dawo hannuna. So i need to settle down”

“Baby boy anya kuwa? Har yanzu fa da sauranka. Zaka iya zama kai kadai cikin wanan makeken gidan? Toh ka bari idan Kanika ya dawo daga hutun dayaje lebanon wurin mahaifiyarku sai ku koma tare”.

“Gaskiya Abba nafisan na zauna ni kadai, Jabbar yana iya dawowa gida ku zauna tare a madadina”

Shiru Abba yayi daga bisani yace “toh maganar auren naka fa?”

“Zanyi nan bada jimawa ba insha Allah”.

Abbah yace “Toh shikenan. Allah ya nuna mana lafiya. Ka samu ka nutsu ka zabar wa kanka mace ta gari, mai hankali da addini wace tasan ya kamata. kaga Mami itama she’s expecting nothing less from you”.

“Insha Allah Abbah. Zanyi iya kokarina”. Sabah Ya fada sa’anan suka cigaba da tataunawa.

Bangaren Samha kuwa, Tana shiga ta tadda Anty Fanneh kwance akan gado tana ajiyar numfashi, ga ruwan drip an saka mata. A hankali ta karaso tazo ta zauna gefenta ta ruko hannunta tana fadin “Ammi….”

“Na’am Samha na”.

Muryan Samha na rawa kwalla suka ciko mata idanu tace “ya jiki Ammi?kiyi hakuri Ammi nasan duk laifinane duk ni na jawo kika shiga wanan halin”.

“Shhhh Baby…. karki kuma fadin haka. Nasan stress ne kawai suka mun yawa but insha Allah i’ll be fine. Ina Abbanku yake?”

“Suna waje tare da Sabah”.

Gyada kai kawai Anty fanneh tayi don gabadaya jikinta yayi weak. Gashi ta rame ta sake yin fari. Fatar jikinta fresh.

Bafi 10 mins ba sai gasu Sabah sunyi sallama sun shigo tare da Abbah. Cike da damuwa Abbah ya karaso wajen da Anty fanneh take kwance ya kamo hannunta yana tambayarta ya jiki. Tace mishi da sauki. Cikin murna ya soma sanar da ita abunda likita yace . Da farko da Anty Fanneh ta dan ji tsoro don bata taba tunanin tanada cigan ciki ba. Abba ne ya soma kwantar mata da hankali yana bata baki.

Har likitan ya kuma shigowa ya dubata. Bayan ya gama, Abbah ya soma tambayarshi ya jikin nata. Likitan yace zata da’an kara kwana biyu a asibitin don tana bukatan bed rest sosai.

Da yamma misalin karfe shida Abba ya umarce Sabah daya kai Samha gida su samu su huta kuma su nema abunda zasu ci, don tun safe suke wanan asibitin. shi zai tsaya da Anty Fanneh tukuna, zuwa anjima zai zo gida ya dubasu. Zuwa lokacin ma Anty fanneh ta da’an warware don tun dazu aketa hira da ita kamar babu abunda ya faru.

Samha da bazata tafi ba, Ammi tace karta damu, ta tafi gida kawai tunda yanzu ta da’an samu karfi a jikinta. Kuma Abba zai zauna da ita.

Tun a cikin mota Sabah ya kafe Samha da idannu yana tambayarta abunda zata ci, tace mishi babu komai, ya kuma tambayarta tace mishi babu. Wanan karan dai wani irin kunyarsa takeji da ita karan kanta batasan meye dalilin haka ba.

Tsayawa yayi a dominos yayi musu ordern pizza sa’anan suka wuce gida.

Suna isa gida Samha ta fara haurawa  Sama zuwa dakinta ta fada bayi ta watsa ruwan zafi a jikinta haka zalika shima ya shige dakinsa yaje ya watsa ruwa ya fito daure da towel daya daura bisa waist dinsa, daya kuma ya rataye bisa wuyansa. Zama yayi a gefen gado ya lalubo wayarsa ya soma nemanta a layi.
Sai da wayar tayi ringing kusan sau biyu tukuna ta daga ta kara a kunnenta. Deep voice dinsa ne taji ya doki dodon kunnenta yace “kina ina?”

“Ina daki”.

“Toh kizo dakina ina son ganinki”.

Zatayi wata magana yace “bana son jin wani musu. Kizo yanzun nan”. Yana gama fadin haka ya katse kiran.

Tabe baki tayi ta mike taje gaban madubi ta soma shafa duk ilahirin jikinta da manta mai dadin kamshi sa’anan ta dauko turarenta ta feshe jikinta. Kayan baccinta soft cotton pajamas mai dauke da design din spongebob riga da wando ta sanya sa’anan ta dauko Katuwar hijab ta daura akai ta fito tayi hanyar dakinsa.

Sallama tayi ta shiga dakin ta sameshi zaune a gaban gado daga shi sai towel yana latsa wayarsa. Faffaden kirjinsa ta soma jin karo da, cikin sauri kirjinta na harbawa ta juya zata bar dakin taji ya daka mata tsawa yana fadin “keh! Ina kuma zaki?”

Cak ta tsaya amma taki juyowa, muryanta na rawa tace “haba Sabbah, ai sai kamun warning, baka sa kaya ba fa”.

Shiru yayi bai bata ansa ba, ya mike yazo ya tsaya dab da inda take tsaye ta juya masa baya.

Saukar numfashin dataji bisa wuyanta ne yasa ta ta juyo a razane tana fadin “wayyo!”.

“Keh ki nutsu banson rainin hankali, wai wani wayyo sai kace wacce za’a yanka”.

Tsaki ya buga sa’anan ya juya ya tafi ya barta a wajen, yaje wardrobe dinsa ya ciro abayansa ya sanya, ya dauko turare ya feshe duk illahirin jikinsa dashi tana tsaye tana kallonsa yaje ya zauna bisa gado yayi tapping katifar yana fadin “come sit.

A hankaki ta karaso har tazo ta zauna kusa dashi. Shiru ne ya ziyarsu ya juyo yana dubanta ya kafeta da mayattatun idanunsa masu bala’in kyau da haske. Kallonta yayi sama da kasa daga bisani yace “wanan zumbulelen hijabinfa sai kace wace zata islamiyya”.

“Sanyi nakeji” ta bashi ansa tana turo dan karamin bakinta.

Bai damu ba ya kamo hannunta cikin nasa ya soma murzawa a hankali yana kallon cikin kwayar idannunta. Itama kallonsa takeyi sa’anan ta soma fadin “yanzu Sabah ya zamuyi? Kaga yanzu Mun kusan samun kani ko kanwa. Ammi zata haihu.”

“Kema nan bada jimawa ba kin kusan samu” ya fada yana kashe mata ido daya.

Zari ido tayi tasa hannu tana da’an dukan kafadarsa tace “meye haka Sabah..nifa bana so”

“Me kenen…. bakiso ki haifo mun babies kyawawa kamar ki? I want babies as fresh as you babe, kedaman you’re already my first baby”.

Kunkuni ta soma mishi cike da shagwaba tana turo baki hade da aika masa da hararan wasa.

Dariya ya sake yana kara matso da ita dab dashi yace “Kanwata… inaso ki sani cewa ba’a son ra’ayi na bane nida ke muka fada cikin wanan hallin. Kaddarar mu ce kawai tazo a hakan. Kuma inaso kamar yanda na rungume wanan kaddarar kema ki rungume ta don har yau i’m not regretting  having you in my life, zuwanki cikin rayuwata ba karamu alkairi bane, nafi kowa farin ciki da aka wayi gari yau ke matata ce tho we didn’t follow the right procedure but it’s worth it. With time nasan our parents will understand why we had to do this. Allah ya albarkaci rayuwar aurenmu, Ina mutuwar sonki kanwata kuma bazan taba gajiya da nuna miki yanda zuciyata take sonki ba. Zuciyar Sabah tana matsanancin sonki”.

Duk maganganun nan da yakeyi, shiru kawai tayi tana kallonsa, idanunta cikin nashi tana karewa kyakyawar fuskarsa kallo, daga kwantaciyan sumar kansa har zuwa manyan eyes dinsa masu dauke da long lashes kamar na baby.wani irin sonsa ne kawai takeji yana kara horuwa cikin ranta. Tabbas yanzu ta gama tabbatar wa kanta cewa Sabah shine ZABIN ta, yayanta kuma abokin rayuwarta. Duk runtsi bata tunanin zata iya rabuwa dashi. He’s hers and she’s his.

Kiss taji ya manna mata bisa goshinta yana lumshe idannu sa’anan ya budesu ya zubesu cikin nata yace “Taso muje kasa muci abunci, nasan kina jin yunwa, tun safe rabonki da kisa wani abu a ciki”. Ya karasa maganar hade da mikewa yana kamo lalusar hannunta cikin nashi.

Babu musu ta mike tabi bayansa suka sauko kasa tare, pizza daya siyo musu daga dominos ya bude musu suka soma ci, dayake Samha yunwa takeji sosai ta zage ciki taci sosai abun har yaso yaba Sabah mamaki don yasanta bata wani damu da cin abinci ba. Mikewa yayi yaje fridge ya dauko musu yogurt kwali biyu da glass cup ya tsiyaya musu suka soma sha, ya janyo remote ya kunna tv suka soma kallon wani tasha da ake nuna wani movie. Shiru ko ina babu motsin da kakeji sai karan tv da sanyin Ac daya bibiye parlourn.

Basuyi 10 mins da fara kallon ba, Samha ta soma gyangyadi tsabar gajiya, Sabah ya matso da ita ya daura kanta bisa kafadanshi yana shafan bayanta a hankali. Before you know it, nan danan bacci yayi awon gaba da ita.

Kura mata ido yayi yana kallon yanda take ajiyar numfashi a hankali, daga ganinta kasan ta gaji dayawa. Nan take yaji tausayinta ya kara kamashi. Yasan duk saboda shi ta shiga wanan halin, amma bari komai ya lafa. He’ll make it up to her.
Da wanan tunanin ya gangaro da dubansa har yazo ya tsaya bisa small pink lips dinta, yanda numfashinta yake fita a hankali yana sauka kan wuyansa ba karamin tada masa da hankali yakeyi ba amma yayi kokari ya dane. Don yasan her mind is too tired for anything yanzu. Shima da wanan tunanin, wani irin wahalalen bacci yayi awon gaba dashi.
Bangaren su Abba kuwa, barin Anty fanneh yayi a asbiti yace bari yaje ya dubo su Sabah a gida daga nan ya canzo kaya ya dawo. Anty Fanneh tace toh sai yadawo. Yana isa gida, securities suka bude mishi gate ya shiga yayi parking sa’anan ya fito ya karasa ciki. Tun daga bakin kofar shiga parlour ya soma jin sautin karan tv na tashi.

A hankali ya bude kofar yayi sallama ya shiga. Abunda yaci karo dashi a parlourn ne yayi mugun bashi mamaki ya tsaya curuss yana kallo ko kwakwaran motsi ya kasa yi. Sabah ya gani zaune kan kujera tare da Samha wace ta daura kanta bisa kafadansa tana bacci da hannayensa zagaye bisa kafadanta. Duk sunyi nisa cikin baccin da sukeyi.

Wani irin tsoro da fargaba ne ya ziyarci Abba nan take daya gansu kwance a hakan. Tunani kala kala suka soma masa yawo aka. A hankali ya karaso inda suke kwance ya soma tapping Sabah yana kokarin tayar dashi..”Sabah, baby boy…”

A hankali Sabah ya bude idanunsa suka sauka kan mahaifinsa, cikin sauri ya mike a sanadiyan haka Itama Samha ta farka, tana ganin Abba nan take ta rude.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *